yi masa ƙorafi har na gaji ya kasa dainawa, in na yi magana sai ya ce ai bai sani ba ne, ko game da zuwa sha'anin dangin shi, gajiya suka yi suka ƙyaleni, da suka fahimci ba ma su kaɗai ba hatta nawa dangin ba kasafai na ke shiga ba, ganewan suka yi ko gajiya suka yi da abu ɗaya suka kyaleni ban sanin musu ba.
Kitchen na koma, daman yara saboda yau jumma'a ne drink suka tafi da shi da Bicuit, sai tea da suka sha da biredi kafin su tafi, doya na fara ferewa zan soya mu sha tea da shi, ina feran doyan ya shigo kitchen ɗin yana faɗin"Fushi kika yi?
Banza dashi na yi, saboda ya ba ni haushi, burin sa na yi ta laifi a idon danginsa shi kuma ya na jin daɗi.
Zuwa ya yi ya rumgumeni ta baya. Lokaci ɗaya yana ɗora kansa saman kafaɗana bayan ya rankwafa.
"Sorry, kin ji ko?
Taɓe baki na yi kafin na ce"Ba dai da man so kake yi ko da yaushe na zama mai laifi a wajen ƴan'uwanka ba? To ai shikenan."
Matse cikina ya yi da hannayensa da ya saƙalo ta cikina. Sannan da ƴar murya ya ce" To ai na ce ne ban sani ba, kin sani da yawan mantuwa."
Mirmishin gefen baki kawai na yi, ba tare da na yi magana ba ya yi ta taƙalan mgana da ni na yi masa gim daga e, sai a'a kawai na ke amsa masa, sanin halina ya san in raina ya baci haka na ke yi sai ya sake ni yana faɗin" Bari na je na yi wanka. Zan je Rano."
Sai da na ji ya ambaci Rano sannan na ɗago ina kallonsa kafin na ce"Uncle Abba bai kira ka ba?
Kai ya girgiza kafin ya ce" Ya kirani amman bai yi mini maganar ba, amman in mun haɗu zan tuna masa."
Kai na jinjina, ba tare da na yi magana ba shi kuma ya fice daga kitchen ɗin, bayan ya rufo mini ƙofar. Na bi shi da kallo kawai, a baya ne ba na ƙaunar na ji ya ce zai je Rano duk da tushen shi ne, saboda GIMBIYA, amman tunda yanzu ta yi aure ban damu da yawan zuwan shi ba, in na yi duba da irin ayyukansa na kwangilan gine gine in an samu yana zuwa ko Uncle Abba ya yi masa hanya, tun da shi har gobe ya na garin Rano kuma a nan ya gina ƙaton gida duk da bai yi aure ba.
Gun bayan lamarin da ya faru tsakani na da Ma'u da yadda Alhajinmu ya goya mata baya. Tun da na dawo gida ban wani saki ba, ko Jidda sai da ta ce Umma ko ba ki da lafiya ne? Gabaɗaya zuciyata ba ta mini daɗi, ballatana da gabaɗaya ƴan gidanmu suka goya ma Ma'u baya, Yaya Hamza ne kaɗai bai shiga maganar ba shi daman sai a yi abu goma bai saka baki ba, mutum ne mai fahimta shi ya sa ko a baya nake ƙaunar Yaya Hamza saboda hallayarsa ɗaya ne a cikin dubu. Shi da Yaya Auwalu za a daɗe ana abu ba su maida kai ba.
Yaya Abubakar har sake kirana ya yi, bayan na ɗauka zagina ne kawai bai yi ba akan Ma'u. Su Yaya Murja kar a ji labari. Yaya Aina har cewa ta yi za ta iya yanke ni akan Ma'u.
A group ɗin Gidanmu an fi kwana uku maganar kawai ake tattaunawa. Ban san ina suka samu cikakken bayanin abin da ya wakana tsakaninmu da Alhajimu ba, sai ga shi Yaya Murja na maida yarda aka yi, to har na yi mamaki Ma'u ce ta faɗa mata ta na jin daɗi haka. Yaya Aina har ta na cewa gwara da Alhajinmu ya yi min haka ƙila zan shiga tairayina.
A mganar nan mutane biyu ne suka ce nima ya kamata a duba maganata ƙawar Ma'u ta yi magana domin tozarci. Yaya Balki da Amina. Sauran kuma duk iyalan Ma'u ne, shi ya sa nima na sauya musu matsayi. Rahila dai ba ta saka baki ba wannan karon, domin ta san halina wallahi sai na yanketa. Sai na yi amfani da shawaran da na yanke a cikin zuciyata akan na shiga na yi magana na ƙara ba ma Ma'u hakuri a gaban kowa kamar yadda take yi min amman munafuki shi daman a koda yaushe yana shirye ne.
Sai kawai ta rigani shiga ta yi magana, hakuri ta ba ma kowa sannan ta ce a bar maganar daga karshe ta yi tagging ɗina kafin ta ce"Komai ya wuce, zumunci da ni da Sadiya har aljannah ko ƴar'uwata?
Ban yi wani mamaki ba, sanin ba tun yau ba Ma'u ta kware a iya acting ba sai nima na fito muka yi acting ɗin a tare, kai tsaye na ce"Kowa ya yi hakuri mun daidaita barakan dake tsakaninmu da ƴar'uwata Asma'u."
Sai gashi sun fito suna murna, Yaya Murja ni kaɗai nasan haushinta da nake ji, har da cewa Allah Sarki Ma'u mai hakuri ce daman, ke kuma Sadiya a rage zafin zuciya. Ita da Yaya Abubakar Ma'u kamar ƙanwar uwarsu, ko da ya ke shi Yaya Abubakar akwai tsohuwar soyayya, ita kuma Yaya Murja har da son abin duniya, tunda Mijin Ma'u na da kuɗi ana zuwa ana maula dole ta riƙa zama mai goyon bayanta, ni fa a gidanmu na riga na san halin kowa sannan na yi ma kowa wajen zamansa wallahi.
Har na gama soya doya raina a ɓace ya ke, na kwashi komai zuwa Dinning, sannan na koma Bedroom sai na iske Yusuf suna waya da Uncle Abba sai na ce ya ba ni mu yi magana kan dai maganar fara zuwa na ganin likita asibitin Shika dake Zaria ne. Sai ya ce sun sake magana da Dr. Fadel ya ce in ta bashi lokaci zai kira mu ya sanar da mu.
"Ki kwantar da hankalinki Sadiyan Yallaɓai. Da zaran ta saka lokacin ganin ki zan sanar ma Tafida kin ji ko?
Sai na gyaɗa masa kai kamar ya na ganina sannan muka yi sallama na miƙa ma Yusuf wayarsa. Tiolet na shiga nima na fara wanka ko da na fito baya falon. Sai na samu daman shiryawa a tsanake.
Riga da wando na saka na material Daman ni in dai ba fita zan yi ba, ba na saka kaya masu nauyi.
Kalan kayan maroon ne, sai na yi amfani da bakar hula mai raga raga, kaina har lokacin ban yi kitso ba mai zuwa har gida ta yi mini kitso ta yi tafiya ne, ni kuma ko sake wanke shi a gida ban yi ba, tunda na iya ina da kayan wanke kan, har su Jidda ni nakan wanke musu kai na gyara musu.
Takalmin gidana mai taushi na saka bayan na fesa turare mai ƙamshi na fita zuwa falo Yusuf na jira na mu karya sannan ya fita. Ni na zuba masa doyan sannan na haɗa masa tea ɗin, sannan na haɗa ma kaina na zauna kujeran gefensa.
Ban ɗaure fuska ba amman ban kuma saki fuskar ba, ganin yanayina yasa sai ya rika takala na da magana sai dai in bishi da ido kawai.
"Ko za ki shirya yau ki je ki gaida Nene, in na dawo daga Rano sai na biya ta gida mu dawo tare."
Kai na gyaɗa kafin na ce"To shikenan sai na shirya na je ɗin."
Yana mirmishi ya shafa kumatuna kafin ya ce"To a saki fuskar, shan kunin ya isa haka."
Kalamansa suka ba ni dariya, sai na murmusa, mun cigaba da karyawa mun gama kenan na kallesa ina faɗin"Wata kwangilar a ka samu a Rano kuma?
Ya na miƙewa ya ce"Ban sani ba. Abba ya ce na shigo mu je mu gani."
Sai na gyaɗa kaina kafin na ce" Allah ya sa a dace? To su dai waɗancan masu payment ɗin shuru ko?
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce"Wallahi shuru. Amman ban cire rai ba tun da sun ce ko da yaushe zan iya jin su." Fatan alheri na yi masa amman ban yi ɗoki ba domin ni nasan yanayin aikin shi, sai a yi shekara ana cewa za a biya shuru amman fa aka biya muna warkewa masha Allah tunda kuɗi ne ba kaɗan ba, kuma in aka samu aikin ana yin shi muna shiga hali tunda kuɗin shi zai ɗauka ya yi amfani dashi a karkashin kamfaninsa na HM. TAFIDA AND SON'S LIMITED. office ɗinsa na can hanyar zoo road kan titin Zaria Road.
Ni na raka shi har bakin mota kamar yadda muka saba, ya ba ni 2k ya ce na hau adaidaita zuwa gidansu da ke Gwammaja, muka rabu bayan ya rumgumeni ya sumbaceni, nima na maida masa martani, yana ɗaga min hannu nima ina ɗaga masa da fatan Allah ya kai shi lafiya ya dawo mini dashi lafiya.
Bayan tafiyarsa na koma cikin gida, falon farko na zauna saboda ka da Saude ta zo ta yi ta buga gida ina ciki ban sani ba, sai na kunna kallo tunda akwai wuta a tashar arewa 24 suna haskawa wani film hausa mai suna Ahalil kitab duk da na kalli Film din amman ina son waƙoƙin ciki sai na zauna ina kallo har na ji buga gida na je na buɗe ma Saude muka shigo tare, na zauna na cigaba da kallona ita kuma ta fara aikinta.
Kafin azahar ta gama min komai, ni har barci ma na yi a saman kujera anan falo da za ta tafi na ba ta 500 na ce ta hau abin hawa, tafiyarta ba dadewa su Jidda suka dawo daman na yi ma Salisu maganan zai kai su Alu Venue anguwan su Anty Maimuna sai ya ce mini bari ya je ya yi sallar jumma'a ya dawo kan nan sun shirya.
Sai murna suke yi tunda na ce can za su yi Weekend,tunda akwai jikokin yarta na fari Mardiya suna wajen Anty Maimunan ne sa'anin Baby ne, sannan autan ta ma sa'ar Jidda ne Afiyatu.
Ban yi musu girki ba, Coorfleck na ce su sha bayan sun sauya kaya sun yi sallah. Kayan su suka saka iri ɗaya shadda mai ruwan ƙasa da na ɗinka musu da sallah da ta wuce da mayafansu, iri ɗaya har takalminsu iri ɗaya ne, na faɗa ma Jidda su yi kitso a can saboda na san ba da wuri za su dawo ba. Ban san me ya sa Anty Maimuna ta ke kulafacin su Jidda ba, ko don Baby ita aka yi ma takwara? Ko kuma daman can ita mai son yara ce gaskiya.
Ɗaya da rabi na rana Salisu ya dawo ya ɗauke su suka tafi. Suna tafiya nima na shirya na saka wata atamfata hollad mai ruwan ganye, sai na yi amfani da green ɗin mayafi jaka da takalmina kuma na saka baƙi, key ɗin gidan da na ɗauka sai da na tabbatar da na kashe komai na wuta sannan na fita na rufe get ɗin da makulli, ban samu adai daita ba sai da na taka zuwa babban titi, anguwan shuru daman haka take to ta masu kuɗi ce, kowa na gidajenshi shi ya sa ƙawa ko ɗaya ban da shi a rukunin nan sun shigomin lokacin da muka tare amman ni da ya ke halina sai ni sau ɗaya na taba shiga gidan gefen mu gidan maman muhsana, da ta haihu na yi barka. Allah ya halliceni mace mara sson shige ma mutane, ko yan gidanmu in ba wani abu ya faru ba, ba kasafai nake zuwa ba, gwara na yi zama na a gida in yi barci ya fiye minim
Drop na ɗauka zuwa Gwammaja. Muna tafe na ji wayata na ringing a jaka na ɗaukota na duba sai na ga Zaituna ce Matar Yaya Abubakar. Na yi mamakin ganin kiranta domin ni dai ban wani yi da ita na fi yi da Anty Khaleesat ɗin Yaya Hamza. Ita Zaituna akwai kwaɗayi da surutu da an ce kace kace shi ya sa ban cika sakin mata ba, sannan daman ina jin haushin mijinta shi ya sa na ɗauka a dakune ban sakar mata fuska ba.
Bayan mun gaisa, sai na yi shuru ina jiran abin da za ta ce.
"Kina gida ne Sadiya?
Yamutsa na yi kafin na ce"A'ah me ya faru?
Kai tsaye ta ce"Ayya daman ina kusa da anguwarku ne, mun zo suna gidan wata ƴar'uwarmu ne, na ce bari in kira ki in kina gida, sai na biyo."
Daga yanayin yadda take magana kamar a wahale, na fi tunanin ƙila sun je ne ma ba abinci za ta ce ina kusa bari ta kirani ta daɓo gayyar danginta su zo min gida, na ji daɗi da ba na gida saboda ita ma Zaituna ƴar ƙashin bayan Ma'u ce.
"Ai ko ba na gida, ina hanya za ni Gwammaja gidan su Yallaɓai."
Sai ta ce to shike nan, daman ta ɗauka ina gida ne, daga nan muka yi sallama.
Na kashe wayata ina hararan wayar kamar ita ce a ciki, na tuna ko faɗan da muka yi da Ma'u a gidan Rahila, suna yan gaba gaban saka bakin cewa ni ce ba ni da gaskiya.
Wayata na mayar jaka, ni kaɗai ina ƙunƙuni ni fa su san halina duk wanda ya ci tuwo da ni wallahi miya ya sha, ga su ga Ma'un duk za su ci ubansu.
Mai adaidaita bai direni ko'ina ba sai ƙofar gidan Iyayen Mijina da ke Anguwan Gwamnaja. Na sauko daga adaidaitan ina miƙa mi shi kuɗin shi na ji an kira sunana.
"Anty Sadiya.."
Ina juyawa sai na ga Adnan ne, sai da na sallami mai adaidaitan ya tafi sannan na nufe shi, ya na tsaye a ƙofar gidan shi da abokonsa guda biyu sun sha manya kaya ƙila daga masallacin jumma'a suke.
"Adnan manyan kasa, yaushe a gari?
Na faɗa ina kallonsa yana dariya ya ce"Jiya na shigo garin. Ina su Jidda?
Ina amsa masa da cewa sun tafi gidan Anty Maimuna, abokansa suka gaisheni na amsa, jakar hannuna ya karɓa muka jera zuwa get ɗin gidan.
Gidan Marigayi Alhaji Muhammad Inuwa babban gida ne, mai bene sama da ƙasa. Ko haraban gidan wargajeje ne, duk da mai gidan ya fi shekara ashirin da rasuwa, gidan bai rankwafa ba, saboda ya hayyafa, kuma ƴa'ƴa sun tasa, in wannan bai kawo ba wannan zai kawo, shi ya sa ƙyallin gidan har gobe bai daina haskawa ba.
Muna tafe ne zuwa cikin gida Adnan na yi min hira makaranta. A ABU ZARIA ya ke karatunsa na Engniaring, a tsakar gidan muka ga Jawahir na shanyan ƙananun kayanta da ta wanke.
Tana ganina ta washe baki ta na faɗin" Anty Sadiya."
Na amsa ina faɗin"Au kema kin zo hutun ne? Ko guduwa kika yi?
Dariya ta saka tana faɗin" Kai Anty Sadiya, da ne fa yanzu ai mun zama ƴan makaranta."
Adnan ya ce"Tunda ba ki son bokon ki yi aure mana ko Anty Sadiya? Kai na gyaɗa ban yi magana ba Jawahir ta balla ma Adnan harara lokaci ɗaya ta na faɗin" To ai sai ka zo ka yi min auran ubana."
Yana ƴar dariya kafin ya ce"Ko ba ki faɗa ni ubanki ne, domin zan iya ɗaura miki aure."
Suka kacame da gaddamansu na saƙo da saƙo ni kuma ina ta dariya. Jakata na karɓa hannun Adnan ina faɗin"Bari na karisa, su Hajiya Iya ba sa nan ne na ji gidan shuru?
Jawahir ta ce" Maman Farko ba ta nan an yi musu rasuwa, Iya kuma ta kwanta ne Nene kuma ki haura sama ta na ciki."
Wuce su na yi, na bar su suna musu, ya na cewa shi ubanta ne, ita kuma ta na cewa Allah ya kyauta ya zama babanta.
Shashen ƙasa Hajiya Iya ne da Mahaifiyar su Jawahir marigiyayiya Hajiya karima Allah ya jiƙanta, sama kuma Hajiya Nene da Maman Farko suke bangaren sama, amman a ƙasa akwai ɗakunan baki daga can haraba kuma akwai ɗakunan mazan gidan.
Sama na haura, ƙofar shashen Nene ne a farko tun kafin na shiga na jiyo hayaniya, ina sallama bayan na cire takalmi na sannan na shiga babban falon na Nene. Hauwa na gani zaune a falon sai fama take yi da yara, Hauwa matar ƙanin Yusuf ne mai bi masa, Muttaƙa. Sai ƴaƴan Halima da su ban ga uwarsu ba, ina ga su kaɗai aka kawo Nene ba ta falon ma gabaɗaya.
Hauwa na ganina ta tare ni da mirmishi, karamar ƴarta, Sahla ta nufoni ta na min oyoyo na taro ta ina ƴar dariya saboda yarinyar ta gane ni, duk in da ta gani ta riƙa gwarancin mgana kenan, suna zuwa gidana sosai nima ina zuwa saboda Hauwa tawa ce, duk cikin Facalolin gidan ba ni da kamar Hauwa.
A bangaren Matan gidan ba ni ba ce Babba ba, akwai Matar Yaya Usman Zabba'u, sai ni sannan Muniran Yaya Nasir sai Hauwa da tsakanin auren mu da na su shekara shidda ne. Amman ina son Hauwa saboda muna da kamaceceniyar hallaya, ba ruwanta tana da sanyin hali duk da yar uwa ce tun da ƴar rano ce a can Mutaƙƙa ya auro ta.
Gaisawa muka yi faram faram kamar yadda muka saba in mun haɗu.
"Ina Nene?
Sai ta ce mini ta shiga ciki ta kwanta.
Yaran Halima na kallah kafin na ce"Tare da Haliman suke? Na ga ban ganta ba?
Sai ta ce mini "A'a su kaɗai baban ya kawo ya ce Haliman ba ta jin daɗi"
Sai na ce Allah ya sauwake, sai da na ji Hauwa na faɗin ƙila ma Haihuwa ce.
Baki na saki domin ni har ga Allah ban san tana da ciki ba, har sai da na furta ma Hauwa. Ta na dariya ta ce" Kin daɗe baki ganta ba ne? Ni mun haɗu a walimar sabon gidan Anty Suwaiba, a can ne na ganta da cikin".
Kai na jinjina kafin na ce" Ni kin san ban samu zuwa ba."
Sai ta gyaɗa min kai, hira muka cigaba yi, amman hankalin Hauwa na ga yara, ita yayanta huɗu, sauran ta ce suna gida tare da babansu da Sahla kawai ta zo amman sai wahala take yi da yayan Halima da ba sa jin mgana.
Muna zaune muna hira Walid da wayonsa ya fi shekara biyar ya yi fitsari a cafet, mamaki ya isheni ganin Hauwa ta miƙe jikinta na rawa ta na masa faɗan me ya sa ya yi fitsari a zaune bai zai yi magana ba?
Sai kawai yaron nan ya fasa kuka ya nufi bedroom ɗin Nene, na saki baki galala ina kallon abin mamaki.
Ina kallo Hauwa ta je ta diɓo ruwa ta zo da towel tana tsane fitsarin ina zaune ko motsi ban yi ba, na yi wannan wahalar a baya amman ban yi wahalan ƴaƴan ƙannen miji da yayyensa ba, na yi dai na uwar mijina a baya amman a yanzu wallahi na daina, in ba a gode na baya ba a barshi.
Falon duk sun yi kaca kaca dashi sai da ta share, sannan ta dawo ta zauna Walid dai tun da ya shiga bai fito ba, Salha da Afra kuma Hauwa ta ce su sauka kasa su je wajen Anty Jawahir.
Sai da suka bar falon sannan na kalleta kafin na ce"Wai sannu da aiki."
Mirmishi ta yi mini ba ta yi magana ba..ni kuma da ban iya shuru na ce"Ke wai har yanzu ba ki daina wannan wahalan ba? Uwarsu na can gida tana hutawa, ke kin baro na ki yayan wajen ubansu, kuma kin zo nan kina hidiman na wasu."
Dariya ta yi kafin ta ce"Kai Anty Sadiya ba ki da dama."
Daman haka ta kan kirani, kai na girgiza kafin na ce"Tab. Wallahi Hauwa ba ƙanwar miji ko y'ar mijin da zan yi ma bauta, na yi ma mahaifiyarsa ita ce dole na, ko ita na yi a baya yanzun ma sai abin da ba a rasa ba."
Cewa ta yi" Allah ko? Na ɗaga mata gira sai muka yi dariya har da tafawa ƙasa ƙasa ta ce"Nene ce kafin ta shiga ta kwanta tace mini na kula da su, gwara ke Sadiya haɗuwan juction kuka yi da Yaya Tafida, ni fa yar uwa ce abu kaɗan zan yi a taso min shi ya sa."
Taɓe baki na yi kafin na ce"Kina da aiki. Ni fa sanin da na yi ko na yi ko ban yi ba sai an yi sururtu shi ya sa da gangan na ke ƙin yin abin,tun da ko ka yi ba godewa suke yi ba su yi ta bin ka da ƙananun maganganu. Ballatana ni da na yi ƙaurin suna."
Dariya muka saka har muna ƙara tafawa, bajewa muka yi a falon Nene muna ta hira kiran sallar la'asar ne ya tashe mu, ni ce na leka ɗakin Nene ta na barci ga Walid a gefenta sai na bubbuga gefen gado ba ta da nauyin barci ta buɗe ido, sai ta ganni.
"Lokacin sallah ya yi Nene."
Kafafunta ta sauko ƙasa ta na faɗin"Sadiya? Yaushe kika zo?
Rankwafa na yi cikin ladabi kafin na ce"Tun dazu, Hauwa ta ce kin kwanta."
Sai ta mike, ɗankwalinta ya zame kanta cike da furfura, ni na ɗauko mata ɗankwalin na bata ta ɗaura lokaci daya tana fadin"Ina su Hauwa'un na ki? Ko sun je gidan Maimunan ne yau?
Da e, na amsa mata sai ta jinjina kai kafin ta ce"Tafida ya je Rano ko? Ko ya dawo ne?
"A'a Nene, sai ya dawo zai biyo ta nan mu koma gida."
A sanyaye ta ce Allah ya maido su lafiya.
Nene dattijuwa ce ce za ta haura 60 da huɗu haka, jikinta ya yi tubus saboda hutu da jin daɗi amman tana da hawan jini ga sugar, amman da ka ganta ka ga ƴa'ƴanta saboda da ita suke kama barin ma Mazan, matan ne su ka ɗan ɗauko kamanin mutanen Rano.
Ni na riƙeta har Tiolet sai da ta shiga sannan na fito, a ɗakin da muke sauka na falon Nene muka shiga muka yi alwala ni da Hauwa, muka yi salla, muna zaune muna ɗan taba hira haka sama sama ni da Hauwa.
*Janafty*
*TURKEN GIDA.*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)*
https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC
No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.
*🅿️05*
Ni da Hauwa muna Gwammaja gidansu Nene har bayan sallar isha'i. Maman Farko ba ta dawo ba, Nene ta ce daman ta ce sai an yi uku za ta dawo wani kawunta ne ya rasu, sauran ƴa'ƴan nata ma da surukanta suna can gidan gaisuwan tare da ita. Hajiya Iya kuma na shiga mun gaisa bayan ta tashi.
Akwai wata ƴar dattijuwa Dije mai yi musu aikace aikace da girki amman ba kwana take yi ba zuwa take yi ta tafi, ranar ma ko da na zo ba ta nan an kira ta a waya jikanta ba lafiya.
Ni da Hauwa muka gyara shashen Nene muka yi girki, saboda yara ne sannan ga Nene ga su Jawahir da daman kamar a ɗakin Nenen suke duk da ita Jawahir a bangarensu ta ke kwana in ta zo gida hutu a School of Nursing na ABU kongo take karatunta tana Aji biyu.
Sai wajen tara na dare Yusuf suka shigo gidan tare da Muttaƙa, da Musabahu, ko kafin su shigo ina ta kiran Yusuf ban samu ba, dare ya yi sannan ni na gaji da zaman hankalina ya koma gida ga yaran Halima ba sa jin mgana Hauwa ce ke ta fama da su, ni dai ina zaune nima fama na ke da kaina, girki dai na ta ya Hauwa muka yi saboda Nene.
Gaisawa kawai muka yi da su Muttaƙa, na ce ma Yallaɓai ya zo mu wuce gida sai ya ce bari ya shiga ciki su gaisa da Nene, saboda ita ta na ciki mu kaɗai ne a falon muna bidiri, sai da mangariba ne ma Jawahir ta shigo nan muna tare da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 31