ina kallon Munnira da ta kwashe da dariya har ta na bani hannu muna tafawa cikin dariya ta ce" Shegiya Hauwa ta zama yar gari. Maza gaya mana sirrin."
Hauwa na dariya ta ce" Shawarwarin ku ne fa, sannan daga Rano akan ɗan aiko mini da gumba da sauran abin da ba za a rasa ba. Sai wacce Sadiya ta haɗa ni da ita na kan ɗan siya mganin infection sai kaza in na samu kuɗi kuma Alhamdulillah ina ta ganin canji."
"Allah Hauwan Mutaƙƙa ?
Na faɗa ina kallonta sai kawai ta ɗaga mini kai. Tare muka saka dariya Munnira har ta na ɗaga kafa saboda dariya kafin ta ce" Ke Sadiya yaushe Hauwa ta yi baki haka? Kuma abin ɗanwaken zagaye ne? Hauwa kaɗai kike so ta gyara ban da ni ko?
Ina ɗaga hannuna sama na ce" A'ah ita ta min mgana ta ce tana so saboda ranar tana gidana aka aiko min da saƙon. Sai ta ce min tana so sai na haɗa su kema in kina so ai ta kwana gidan sauƙi waya kawai za a yi mata."
Munnira sai ta gyara zama kafin ta ce" To wai kuma yana yi sosai?
Na kalleta ban yi mgana ba Hauwa ce ta ba ta amsa da cewa" To ai ke tunda kin riga kin saka wasi wasi ko kin siya ba zai yi miki aiki ba."
"Ko?
Haka ta ce tana kallon mu ni ko sai na gyara zama ina faɗin" Gaskiyan Hauwa. Kuma son kuɗi ne ba zai barki ki yi gyaran ba karki kashe kuɗi ko? Zauna Nasir ya samu wasu ƴan kudaɗe ya nemi chanji lokacin za ki yi bayani ne."
Tana dariya ta ce" Haba. Ai ya yi ƙanƙanta da Mata biyu. Yallaɓai dai ke kan hanya daman ana ta cewa tunda Yaya Usman ya buɗe hanya Yallaɓan ki ne zai biyo baya."
Wani kallo na yi mata sai ta kama dariya Hauwa na taya ta. Nuna ni take yi tana faɗin" Ta firgita ta. Kin gan fa Hauwa."
Ta faɗa tana nuna ni ture hannunta na yi ina faɗin" Firgitan me? A kaina za ta zauna? Allah ya kawo ta lafiya."
Hauwa da Munnira na ta danne dariya haushi ya kamani na ce" Wai dariyan na menene kuma? Ko kin ji labarin auren ne ni ban sani ba?
Da sauri Hauwa ta ce" A ina? Wallahi wasa ne kawai ba abin da muka ji."
Hararan su na yi domin na ga sun maida ni abin zolaya. Munnira ce ganin na haɗe rai ina faɗin" Ko za a mini kishiya sai an yi miki Munnira in sha Allahu."
Da karfi ta amsa da cewa" Wallahi ba Amin ba. Cab"
Ina mirmishi na ce" Au ashe ba daɗi? Sai ta marairai ce tana faɗin" Daga Wasa? To a bar mganar kawai."
Ni kuma na ce sai an yi ta. Munnira uwar kishi ta ce ita fa ta tsani labarin kishiya. Ganin na na ce ina cewa Nasir sai ya yi aure nan kusa in sha Allahu Hauwa na taya ni sai kawai ta sauya mganar da cewa" Na ce ba ya mganar kayan gyaran can ɗin? Ina ga zan siya nawa nawa ne?
Ni da Hauwa har muna tafawa saboda dariya sai da na gama ja mata aji sannan na yi mata bayanim ingancin kayan gyara na Hajiya Surayya Halin yau.
Cikin mamaki Munnira ta ce" Da gaske suna da kyau? Ba su dai cutarwa ko?
Kai tsaye na ce" In da suna cutarwa da tuni sun cutar da ni. Ke Munnira ki cire wannan tunanin a ranki na matan da ba su san kansu ba. Yanzu mata sun fahimci muhimmamci gyara a jikinsu wanda ba zai zama cuta a gare su ba. Kin ga mganin infection ɗin nan yana da kyau duk bayan wattani uki mace ta riƙa shan shi. Saboda shi infection 90% na mata muna dashi sannan mu ke zuwa gidajen biki da suna muna mu'alama da banɗakuna mabambamta. Kin ga kowani lokaci za mu iya ɗauka sai mun dage da mgani sannan maganar gyara Munnira ba wanda zai cutar dake ba yar gumbar nan ta mata ɗan kazan nan na haɗin uwargida ba komai a cikinta sai itatuwan maganin da zai ƙara miki Ni'ima. Bayan nan za ki riƙa gyaran ki a cikin gida kayan marmarin nan ki riƙa shan su madara su rage kayan ganye da sauran su duk suma suna taimakama wajen dawo da ruwan jikin mu kin gani nan duk bayan wata uku sai na siya mganin infection na sha sannan na bi da kayan gyara bayan kuma ina yin nawa dubarun a cikin gida hatta fatata ban zauna ba bayan wani lokaci ina siyan mayukan gyaran jiki domin kaina da kuma Mijina. Ba kuma domin shi ɗin ba sai domin ka riƙe wannan martaban da Allah ya ba ka na ƴ'a mace. Sannan yana da kyau ka yi gyara domin ka farantama mijinka Munnira ba sai an kawo maka wata ka haukace ba. Wanda ko da watan ta zo sai dai ita ta yi gasa da ke ba dai ki yi da ita ba tunda komai ta zo ta iske ki kin san shi kuma kina yi saboda haka ki yi ma kanki faɗa ki gyara jikin ki da kanki saboda martaban ki Munnira"
"Gaskiya ne Sadiya mganar ki Haƙƙun."
Hauwa ta faɗa tana mai jinjina kai. Munnira da ta yi tagumi ta na saurerena sai ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce" Kuma gaskiyan ku ne. To zan dage in sha Allahu. Kuma kamar na fara ganin wani alamu a wajen Nasir duk da bai yi mini mgana ba."
"Alamun me?
Na tambaya ina kallonta.
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce" Yanzu ba ya daɗewa da mun fara mintina goma sai ya sauka kuma da ba haka ya ke yi ba"
Ni da Hauwa muka kalli juna kafin na maida kallona kan Munnira ina faɗin" You see. Akwai sanyi ajikinki kuma a yadda na fahimta ba ya wani jin daɗin ki yana dai yi ne saboda fita haƙƙi ki sai kin dage Munnira"
Tuni ta natsu tana faɗin" To zan dage gaya mini mafita. Allah Sadiya ba na ƙaunar kishiya"
Yadda ta yi mganar ne cikin tausayi ya sa muka tsintsire da dariya ni da Hauwa kamar za ta yi kuka ta ce" Don Allah ba dariya ba. Ku taimaka mini."
Sai na gyara zama ina faɗin" Za mu taimake ki amman ke ma sai kin miƙe kin taimaki kanki."
Sai ta ce ta ji duk za ta yi nan take na ɗauko wayata na kira Hajiya Surayya Halin yau. Bayan mun gaisa sai na ce zan haɗa ta da Munnira domin ta yi mata bayani ina ba ta wayar sai na ce ta shiga ciki yadda za ta samu damar yi mata bayani sosai. Sun ko jima suna waya sannan Munnira ta kawo min wayar nan Surayya ke faɗa min za ta fara shan na infection kafin haɗin kayan gyaran ya biyo. Mun rabu akan Munniran za ta karɓi lambar wayarta su ƙarishe mgana.
Washegari ma ta ce za ta aiko ma da Munnira saƙon ko ba ta saka kuɗin ba tunda ta hannuna ne.
Duk mai bukatar mganin infection sadidan, ko mganin gyaran uwargida da amarya contact Surayya Halin yau.
+234 803 277 3332.
Kano Nigeria.
Nuna Gwammaja har wajen ƙarfe goman dare. Domin da mazajen namu suka shigo gidan can bayan sallar isha'i gabaɗyansu suna falon Nene da ƴan'uwansu suna ta hira a tsakaninsu. Mu kuma muna ƙasa mun yi sallah mun koma muna ta zaman hira. A lokacin mganar haihuwa muke yi sun sin ina son na ƙara haihuwa ko daga yadda na ke kan hanyar yawon asibiti. Hauwa ce ke tambayata ya ake ciki ne yanzu? Kai na rausayar kafin na ce" To ana dai kan gwaje gwaje duk da kamar guda biyu suka rage amma Likitan tana ta ba ni tabbacin ba matsala ko ma akwai ba wacce za ta gagare su ba ne."
Tare da Munniran suka haɗa bakin faɗin" In sha Allahu ma ba wata matsala."
Sai na amsa da Allah ya sa cikin wani yanayi na ce" Yallaɓai na son yara sosai. Biyu sun yi masa kaɗan ni na sani."
Hauwa ta ce" Amma ai ba ya nuna damuwa ko?
Sai na gyaɗa mata kai Munnira ce ta karɓe da cewa" Yallaɓai fa bai da damuwa. Damuwar su ne su Anty Bahijja. Ni da na ji ma wani batu amma dai ba ri na yi shuru."
Sai na kalleta gabana ya faɗi saboda na san tabbas abin da ta ji ya shafe ni.
Da sauri Hauwa ta ce"Gwara ki yi shurun Munnira. Ni ma da na je Rano cikin azumi na ji batun a gida."
Sai kawai na kallesu kafin na yi mgana Munnira ta ce" Au kema? To me za a ɓoye mata ai mgana ce ba cewa muka yi ya tabbata ba. Kuma zaman tare kenan gwara mu faɗa mata ta san halin da ake ciki ko da ta faru ma ta san in da za ta bullo ma lamarin."
Cikin ɗauriya na ce" Wai menene? Ku faɗa min ai ban isa na hana Allah ya yi ikon shi ba."
Hauwa ce ta kalleni kafin ta ce" A bakin Autar gidanmu na ji wai ƙannen Gimbiya ke faɗin Tafida za ta aura. Da na ce ban san da wannan mganar ba Innamu ta ce itama ta ji kuma a bakin makusantan ita Hajiyar Tafidan an ce daman tun farko Hajiya Nene da Hajiya tafidan sun so su haɗa zumunci na auran Gimbiya da Tafida Allah bai yi a wancan lokacin ba. Mutuwar mijinta ya nuna cewa rabon Tafida ce."
Ina kallon Hauwa amman na kasa mgana Munnira ta karɓe da cewa" Nima haka na ji wallahi. Kun san wacece ta min mganar?
Hauwa ce ta girgiza mata kai ni dai ko motsi ban yi ba
"Suwaiba ce fa kwanaki da ta zo gidana ta ke min zencen. Wai Anty Bahijja ta ce wannan karon Gimbiya Rabon Tafida ne. Shi ya sa ma wai ƙila aka dawo da ita wajen Nene."
Hauwa ta ce" Ni kaina na yi mamakin dawowarta. In aiki ne ai ba kullum ta ke zuwa ba kuma tunda tana da mota za ta iya zuwa a ranar kuma ta koma gida."
Munnira ta ce" Har Nasir na yi ma mgana ya ce mini shi bai sani ba gulma ce ta mu ta mata. Amma wallahi Sadiya na hango gaskiya ba rami me zai kawo mganar rami? Da man ta yi ta shige masa ni fa wallahi haushi ta ke ba ni."
Hauwa ta yi tagumi kafin ta ce" Ni kaina na fara hango hakan. Mganar fa daga bakin ƙannen Gimbiyar ta fito. Kin ga ko sun ji ana mganar ne."
Ganin yadda na yi shuru kawai ina sauraran su ya sa Hauwa ta dafa kafaɗata tana faɗin" Kar ki damu Sadiya. Ni na san ko auranta Yallaɓai ya yi ba za ta sha gaban ki ba."
Munnira ta taɓe baki kafin ta ce" Ni wallahi da wata ta waje ne wacce ba a sani ba. Amma wannan Gimbiyar fa ban so. Sai Sadiya ta zama mujiya Allah su Anty Bahijja ware ta za su yi daman ya ya a ka cika?
Hauwa ta yi ajiyar zuciya kafin ta ce" Da wannan kuma da wanman."
Munnira cikin jin haushi ta ce" Har fa wani suna take kiran shi Daddy shi kuma ya ce mata me ne ma?
"Daughter"
Na faɗa ina kallon Munnira da ta yi tsaki kafin ta ce" Ke kuma wai duk kika ƙyale? Suna waya to?
Sai na gyaɗa kaina kafin na ce
" Suna yi mana."
Gabaɗayansu suka kalleni cikin mamaki sai na yi mirnishi kafin na ce" To ai ban isa na hana shi yin waya da ita ba tunda yar uwanshi ne ko da na aure shi suna tare. Hauwa Munnira daman tun da na ji Mijin Gimbiya ya rasu da irin hidiman da ta ke yi ma yarana na san gwara na shirya domin watan wata rana ko Yallaɓai bai yi tunanin auranta ba za a tusa masa tunanin. Bakomai in ma ya auro ta fatana Allah ya zaunar damu lafiya abu ɗaya na sani ba zan yi ma Yallaɓai baƙin ciki domin ya ƙara aure ba. Sannan ba zan yi faɗa da dangin shi ba amma na kudiri niyar in sun yi mini hallaci na yi musu in ba su yi mini ba wallahi ba zan yi musu ba sai dai gayyar ta watse."
Munnira ta ce Hmm! Ta ma kasa mgana Hauwa ce ta ƙara ba ni hakuri da cewa kar na damu tana da tabbacin Yallaɓai ba zai taɓa juyamin baya ba. Kallonta kawai na ke yi amman ban yi magana sai dai kuma a cikin raina sai da na ce Namiji ne fa mai chanza launi daga baƙi zuwa fari lokaci bayan lokaci.
Muna cikin yin mganar ne Yallaɓai ya kira ni a waya ya ce na fito za mu tafi ya na faɗa min yara har sun yi barci. Jin haka yasa gabaɗayanmu muka fito zuwa ɗaƙin Nene muka yi musu sallama su Suwaiba nan duk anan gida za su kwana. Mu muka fara tafiya Hauwa Musbahu ne zai kai su gida ko a fuska ban nuna ma Yallaɓai wani abu ba har muka koma gida. Marwa na bari da Baby na ce ta yi mata shirin barci.
Ni da Yallaɓai muka wuce bedroom ɗim mu kafin mu kwanta sai da muka yi soyyyarmu sannan muka yi wanka muka kwanta duk da yadda na ke jin wani abu ya tsaya min a ƙasan zuciya amman ban nuna masa ina ƙoƙarin gaya ma kaina gaskiya. Ban isa na hana shi abinda Allah ya ce ya yi ba. Sannan ba zan yi masa baƙin ciki domin ya ƙara aure domin samin wasu zuru'an ba. Amman a ƙasan raina ina tunanin saboda akwai ta in da na gaza ne. Na gaza ta bangaren ba shi zuru'a masu yawan da ya ke fata.
Washegari tun safe muka shirya. Na yi abinci shinkafa da miya da nama sai salat ɗin da na saka shi a wani filet Babba muka rufe da leda Karfe goma a Ɗorayi ta yi mana Yallaɓai ya kai mu, ranar kaya iri ɗaya muka saka da ni da yara har Marwa Atamfar da Yallaɓai ya yi mana mai adon ja a jikin ta.
Na yi kyau sosai gashi daman na ɗan rame kaɗan sai kayan ya zauna a jikina riga da sikat na yi.
Duk sammakona sai da na tarar da Yaya Balki a gidan mun je ba daɗewa sai ga Ma'u itama da na ta gayyar yaran sai ƙanwarta Zainab sai Anti ƙila can ta yi mata salla Itama da abinci niki niki. Wannan sallar daman su Yaya Hamza ba su zuwa salla gida sun fi zuwa a sallar layya. Can ba jimawa sai ga Zaitunan Yaya Abubakar sai ga Yaya Murja ta ƙarshen ita ce Yaya Aina da ƙannen Marwa gifa fa ya cika ya yi albarka tun da kaf ɗin mun mun zo da yaran mu sannan har Datti a gida ya yi salla Alhajinmu ya ji daɗi bakin shi har kunnen gashi ga jikokinshi suna ta fira Gwaggo ma ta kasa zama sai ina za ta saka damu take yi.
*Janafty*
*TURKEN GIDA.*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Kz6koexT4Yj4o2zO4xVzrU
INA MATAN DA SUKA DADE SUNA NEMAN MAGANIN SANYI WATO INFECTION MAI KYU BASU SAMUBA, ANYI MAGANI ANYI MAGANI HAR ANGAJI, TOH KICE ALHAMDULILLAH, SABODA ALLAH YA HADAKI DA MAGANIN DA ZAI MAGANCE MIKI KO WANE IRIN CUTTAN SANYI WATO INFECTION DA YA KAMAKI CIKIN SATI GUDA DA YARDAN ALLAH. SHIGO GIDAN BUZAYE WAHALANKI TA YANKE HAJIYA💃💃
INA MAI NEMAN KAYAN GHARA ZAFAFA, MASU INGANCI, MASU KARFI, WANDA ZAI KANKARO MIKI MUTUNCINCI DA KIMARKI, WANDA ZASU DAWO DA HANKALIN ME GIDA GAREKI, SU SA YA MAKALE MIKI DA ZAZZAFAN SOYAYYANSHI, YA DINGA SAKE MIKI KI WARWASA YANDA KIKE SO💃💃 TO ER UWA SHIGO GIDAN BUZAYE KIGA IKON ALLAH DON KUWA ALLAH YA KAWO MIKI KARKEN MATSALANKI NA RASHIN DACEWA DABAKYAYI NA KAYAN GHARA😁💃💃 KUSHIGO GIDAN BUZAYE KU GYARA KUGA IKON ALLAH
*🅿️20*
Rahila ce jirgin danƙaro ita ce karshen zuwa har sai da na yi mata tsiyan tana kusa amma itace ƙarshen zuwa. Tana dariya ta ce
" Ni fa na ɗauka ni ce ma farkon zuwa kawai sai na ga gida ya cika." Muna ta mata dariya ni da Ya Balki.
Amina ta kira waya da ta ji gida cike kowa da kowa na nan kamar ta yi kuka ta ce ta yi missing. Ta so zuwa amma ba ta samu dama ba sai dai ta ce sallar layya in sha Allahu da ita za a yi.
Ya Auwal kuma ni na kira shi a waya ya ce sun ɗan fita da laila ne da yara gidan shuru sallar duk ba daɗi sai ya ce na kunna data ya kira Video call nan ne fa suka gaisa da kowa har da Gwaggo da Alhajinmu an kai musu sun yi mgana da juna.
Ya Hamza kuma na kira wayarsa ba ta shiga ba sai na kira na Khaleesat. Ita ke faɗin ya kwanta ashe bai jin daɗi zazzaɓi kuma ya hana a faɗa ma kowa. Muna cikin wayar ya tashi sai ta bashi wayar dukkanmu muka karɓa muka yi masa sannu da jiki ya ce ya ji sauƙi ya je asibiti maleria ne an yi masa allura kuma an bashi mganguna. Ba mu jima muna mgana da su ba tun da bai jin daɗi daga nan muka yi masa sallama da fatan samun lafiya. Datti dai za su fara jarabawa Jiya da yamma ya koma makaranta.
Dukkan mu muna ɗakin Mama daman yawancin in dai mun zo gida mun fi zama ɗakin Mama. Gwaggo na ɗakin Alhajinmu suna ta fama da yara. Hira muke yi na can garin mu Yashe bayan sallar nan akwai bikin autar su Ya Muntari wato ɗiyar Baba Aminu kenan Yaya Aina ce ke mganar haɗa guddumuwa daman haka muke in sha'ani ya tashi sai mu haɗa kanmu kowa ta kawo abin da ta ke dashi mu haɗa mu ba ma Gwaggo ita kuma sai ta nuna ma Alhajinmu ya yi ta godiya kuma in sha'anin ya tashi ko ba dukkanmu. Yaya Murja da Yaya Balki suna zuwa ni ce ma ban cika zuwa ba sosai Rahila daman can ne tushen Mijinta tana yawan zuwa amma wannan karon tunda na ji bikin na ce sai na je Yashe na yi sati in sha Allahu tun da na daɗe ban je ba tun ina da cikin Baby da babbar ɗiyar Baba Sani ta rasu muka je gaisuwa kuma a ranar muka dawo ba mu kwana ba.
Bikin bayan salla da sati uku ne. Yaya Aina ta ce ana jibi biki za mu tafi saboda Matar Baba Aminu magajiya mai yi ce ba ta wuce duk wani sha'anin mu ko ba ta zo ba ƙannen Yaya Muntari za su zo gaskiya tana da ƙoƙari daga ita har Baba Aminun suna da riƙo kan zumunci.
Muna cikin hiran ne Marwa ta shigo sai dai ta ce sannanun ku gabaɗaya a ka amsa mata in da na ke zaune ta nufa tana faɗin" Umma Baby ta jiƙa kayanta da ruwa."
(Daman Umma ta ke ce mini kamar yadda su Jidda ke kirana.)
Kai na jinjina kafin na ce" To ai sai ta zauna dashi. Domin ban zo mata da wasu kayan ba."
Da sauri ta ce" Gwaggo ta ce a cire rigar a shanya kar zazzaɓi ya kamata."
Kafin in yi mgana Rahila ta karɓe da cewa" To ba wasu kayan? In sanyi ya kamata fa"
Yaya Balki ce ta yi mgana wannan karon da cewa" Sadiya ce fa da tsiyarta. Ba za a rasa wasu kayan su Baby a gidan nan ba."
Yaya Murja na gefe ta ce" Ko ba na ta ba. Ba za a rasa kayan da za ta saka kafin na ta ya sha iska ba."
Muna cikin mganar Marwa ta fita sai ga Gwaggo ta leƙo ta na faɗin ita ta ce a cire mata rigar a shanya ta samu wata riga ta ba ma Marwa ta saka mata na amsa mata da to Gwaggo.
Yaya Balki ce ke mganar ta ga Marwa ta yi mata girma ne a ido ina mirmishi na ce" Ai na kusa yin suruki in sha Allahu."
Yaya Balki ta amsa da Allah ya sa.
"Aina can Marwa ta yi salla gidan Sadiya ne?
Ya Murja ta faɗa ta na mai kallon Ya Aina wacce ta amsa da mata da cewa" E. Tun kafin ta dawo daga makaranta ta dame ni da ni Mama a gidan Umma Sadiya zan yi salla na ce to. Ta na dawowa ta gaya ma Baban shima yana dariya ya ce to yar gidan Umma Sadiya a dawo lafiya."
Ina mirmishin jin daɗi na ce" Ai wallahi na ji daɗin haka. Ni da za ku bar mini ita a wajena Ya Aina."
Yaya Balki na dariya ta ce" Topha ƴan mata ba su ishe ki ba ne Sadiya?
"Ina fa suka ishe ni. Ban ƙi dozin ba Yaya Balki."
Muka saka dariya gabaɗayanmu Rahila ce ta ce" Sai Ya Aina ta baki. Ki haɗa da Jidda ki riƙe gabaɗaya."
Ma'u na gefe ba ta ce komai ba ta na latsa wayarta. Ya Murja na sauraran mu amma ba ta yi mgana ba Ya Aina ke faɗin Marwa za ta fara pratical a asibti kuma babanta ba zai bari ba amma don ta riƙa zuwa miki hutu lokaci bayan lokaci ba zai ce komai ba.
na marairacewa na ce" Haba Ya Aina. In kika saka baki zai bari mana."
Dariya kawai ta yi ba tare da ta yi mgana ba Yaya Balki ce ke faɗin" Topha! Lalle lamarin Sadiya azimin ne.
"Da gaske take yi."
In ji Rahila ni kuma na juya ina rantse musu da gaske nake yi.
"To ke in kina son ɗauka shi Yallaɓan na ki na so ne?
Ya Murja ta faɗa tana kallona da sauri na ce" Haba Ya Murja na ɗauka ke mai shaidar Yallaɓai na ne. Ba Marwa ba ko wacce bai sani ba ne na kawo na ce ina so zan riƙe wallahi ba zai ce komai ba. Ballatana ma Marwa shi ya fara cewa ko za mu karɓo Marwa ne ta dawo wajen mu da zama Sadiya? Shi ya sa ma kika ji na yi mgana."
"Oh."
Kawai ta ce ba ta ƙara mgana ba. Yaya Balki ce ta karɓe mganar da cewa" Kuma fa hakane. Yallaɓan na ki ba shi da matsala gaskiya."
Rahila ma ta amsa da cewa" Shi da ke son yara. Allah ne dai bai bashi da yawa ba."
Ita dai Yaa Aina ba ta ce komai ba sai dai ta na ta mirmishi daga karshe ta kashe mganar da cewa babanta ba zai bari ba ni kuma na ce zan sako Yallaɓai a gaba mu zo tambaya Rahila na dariya ta ce" Shike nan ma an kashe boss ɗin."
Muna ta dariyan mu cikin nishaɗi. Daman fa ko haɗuwa aka yi waje ɗaya Ma'u da Ya Murja sun fi tsame kansu gefe ana hira sai jifa jifa suke saka baki tun ballatana ma in ina wajen. Ni kuma ban damu da su ba in suka sako ni na yi da su in ba su sako ni ba na juya na yi da waɗanda ke yi da ni. Zaitunan Yaya Abubakar tana ɗakin Gwaggo tun da ta zo sai barci kamar wata kasa Yaya Balki ta ce Allah ya sa ba ciki ne da ita ba Ma'u ta kwashe da dariya ta na faɗin" Kuma kamar kin san ta yi yaye ba."
Ya Aina ta ce" Kai wannan mata ta Abubakar. Allah ya sauwaƙe."
Ni kuma sai na kada baki na ce" Ku barta ta haihu. Iya rabon ta a duniya fa za ta haifa. "
Sai Rahila ta ce kuma gaskiya ne. Gwaggo ce ta leƙo ta ce an kira salla ga ƴayanmu can har sun yi alwala mu ma sai mu tashi jin haka yasa muka firfito domin yin alwala ni ban samu buta ba sai na zauna ina jira Anti ta gama da na ta butan ta bani sai da ta idar da alwalan sannan ta kawo min na amsa ina faɗin" Su Anti an zama yan mata."
Ta na dariya ta rufe fuska kafin ta ce" Anty Sadiya ina goron sallah na."
Kai tsaye na ce" Gorom sallah kike so?
Sai ta gyaɗa min kai. Ni kuma sai na rausayar da kai kafin na ce"
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 29 Chapter of 31