kanka domin ba za ka taba jin daɗi ba.
Shi ya sa na ji zuciyata ta karye na fara kuka, kenan har a yau ma Ma'u ce za ta sake yin nasara a kaina?
"Kar na kuskura na kara jin kin danganta Ma'u da bare, ita ba bare ba ce. Jinin ki ce domin in aka tsaga jininta za a ga na ki jinin haka itama in aka tsaka na ta jinin za a ga naki, bari na tunasar da ke abin da nasan ba ki manta ba, ni na saki nono mahaifiyar Asma'u ta kama Asiya ƙanwata ce uwa ɗaya uba ɗaya. Me ya sa kike da tunanin banza ne? Me ta yi miki? Tana bin ki amman kina ƙara nuna mata tsana? Ina ce har hakuri Murja ta ce ta yi ta ba ki kika tafi kina ta cin mutumci? Ke sheɗan ce da ba ki jin bari Halima ko so kike ki zama sheɗaniya a cikin mutane?
Kuka kawai na ke yi, wannan karon kukan da na ke yi ya fi na wanda Ma'u ta yi fidda amon sauti, falon ya yi tsit sai tashin faɗan Alhaji kawai ake ji har Gwaggo tana zaune ne amman ba ta iya dakatar da Alhaji ba.
Ma'u ce ta ɗago kanta tana kallon Alhaji kafin ta ce" Alhajinmu har a waya na kira ta bata ɗauka ba sai na yi mata saƙon murya ta WhatApps bari ma ka ji."
Nan da nan ta ɗauko wayarta ta shiga ta duba sai ga shi ta kunna muryanta tarwai ta na fadin"Ki yi hakuri Sadiya da abin da Shema'u ta yi miki. Har ga Allah ban san a ina ji maganar ba. Na nuna mata ban ji daɗi ba na kuma ce sai ta ba ki hakuri saboda haka zan tura mata lambarki sai ta kira ki ta baki hakuri."
Alhajinmu ya girgiza kai kafin ya kalleni ya na faɗin"Ta yi ta ba ki hakuri akan laifin da ba ita ta yi miki ba amman kin kasa hakura. Tabbas na fahimce ke ce sheɗaniya sannan ke ce ke hassada duk abun da ke faruwa."
Ina rawan muryan kuka na kwashi rantsuwa ina faɗin"Wallahi Alhajinmu..."
"Rufe min ba ki, ki kuma tsaya dakyau ki saurareni. Ga uwarki nan ta zama shaida ga mijin ki nan ya zama shaida, daga yau ina mai ba ki umarni a matsayina na mahaifinki, ki ijiye duk abin da ke cikin ranki game da Asma'u ki rumgumi ƴar uwarki. Sannan ki yi zumunci da ita ki je gidanta in abin farinciki ya same ta ki taya ta murna. Sannan ki je a lokacin jaje domin ki ta ya ta jimami. Sannan in ku ka haɗu ke za ki fara yi mata magana, ki bi ta a inda ta ke ku gaisa cikin zumunci da ƙaunar juna. Gargaɗi na ƙarshe a gareki shine ki bi umarnina ya zama wannan shi ne zama na ƙarshe da zan yi a kan wannan mganar, na ƙara faɗa miki ki yarda makaman yaƙin ki ki bi Asma'u sannan ki yi zumunci da ita, in kika saɓa ma ko ɗaya daga cikin umarnina zan yi fushi da ke fushi mai tsananin da ba ki taɓa tsammani ba Halima. Saboda haka in kina so ki rabauta har a ranar gobe ƙiyama ki yi gaggawan bin umarnin da na ba ki."
Alhajinmu na mgana ina jin kamar zuciyata za ta faso ƙirjina ta fito tsabar baƙin ciki tuni kukana ya ɗauke. Saboda ban ga amfanin ina zauna ina kuka saboda Ma'u. Na yarda ta yi nasara a kaina kamar ko yaushe.
Muryanta na rawa na ce"Na ji Alhaji in sha Allahu zan zama mai bin Umarnin ka."
Na faɗa ina sauke numfashi saboda na ji kamar numfashina na shirin kwacewa.
Alhajinmu ya gyaɗa kai kafin ya ce" Kin yi kyan kai. Ki sani ko da rana ɗaya na ji labarin kin bambanta Asma'u da Rahila ki sani kin ɓata mini sannan zan daɗe ban iya kallon ki ba, zan daɗe ina miki kallon wacce ta gagare ni."
Da sauri Gwaggo ta ce" Haka ma ba zai faru ba. Sadiya kara ba ma Alhaji haƙuri."
Kaina na ƙasa na ƙara faɗin" Allah ya huci zuciyarka Alhaji. In sha Allahu hakan ba za ta ƙara faruwa ba."
Na faɗa ina ƙokarin danne abin da ke taso mini daga ƙasan zuciyata.
Sai ya saussauta fushin sa jin har Yusuf ya rankwafa ya na neman min afuwa har da Ma'un da mijinta sai Alhajinmu ya jinjina kai kafin ya ce" Bakomai. Na tsorata ne sabo da halin rayuwa. Ka da na faɗi na mutu na bar baraka daga zuru'a ta, na ji daɗin da kika hangi kuskuranki kika kuma yi aniyar gyarawa. Ki yi ma Asma'u sallama ta amsa miki tare da musabaha yanzu a gabana Dubu."
Ban yi musu ba na juya ina miƙa ma Ma'u hannu lokaci ɗaya ina yi mata sallama. Ta miƙo min hannunta ta na yi min wani irin mirmishin da ni kaɗai nasan ma'anarshi lokaci ɗaya tana amsa sallamata tare da sarƙe hannun juna. Ni ma sai na yi mata mirmishi kwatankwancin mirmishin da ta yi mini, ai ba Ma'u kaɗai ita iya bariki ba nima na iya tunda na fahimci ta na cin nasara a kaina ne ta hanyar amfanin da makirci.
"Ki yi hakuri Ma'u. Ki yafe mini sharrin sheɗan ne."
Haka na faɗa ina mai gayyato mirmishi da rahama a saman fuskata, ko ta yi mamaki ba ta nuna ba sai ta waske, kafin ta ce"Bakomai. Na ji daɗin haka Yar'uwata."
Daga zaunen na matsa na rumgumeta, sai da ta yi wani sansarairai kafin ta rumgume bayana ta na ɗan mirmishi nima mirmishin na ke yi sannna muka saki juna bayan mun kalli juna kowaccenmu ta yi mirmishin da bai kai zuuci ba.
Gwaggo ta yi hamdala Alhajinmu ma haka ya ɗora da cewa" Na ji daɗin haka. Allah na gode maka da korar min sheɗanin da ya shigo cikin zuru'ata. Allah ya yi muku albarka gabaɗaya, ku kuma na ƙara ɗora muku nauyi ku yi musu gyara in sun yi ba dai dai ba. Sannan kuma ku gaya musu su sada zumunci a tsakaninsu saboda samun falala wajen ubangiji irin ta masu sada zumunci."
Suka amsa ma Alhaji da In sha Allahu. Ganin har sha ɗaya ta yi na dare sai ya ce mu ta shi mu ta fi gida mun bar yara su kaɗai a gida.
Dukkanmu a tare muka yi ma Alhajinmu da Gwaggo sallama muka fita, muna gaba ni da Ma'u su kuma mazajen namu suna bin bayan mu.
Ni ce na fara kallon Ma'u dai dai mun fito kofar gida, ƙasa ƙass na ce"Kin iya acting kyan shi ki faɗa harkan film za ki ci kuɗi sosai"
Dariya ta yi kafin ta ce"Ko Sadiya? Ke ma ashe kin san na iya acting sosai."
Sai na gimtse fuska kafin na ce"Kin sha yin nasara a kaina Ma'u kamar baya yau ma kin ci nasara. Amman ina mai ba ki tabbacin daga yau ba za ki ƙara samun nasara a kaina ba har abada."
Cikin reni ta ce"Kai don Allah? Da gaske?
Ban tsaya sauraranta ba na ƙarisa jikin motar Yusuf,ganin sun kariso suma ya sa na ɗaga murya ina faɗin" Sai da safe Ma'u. Alhajin Ma'u mu kwana lafiya a gaida yaran."
Shi ya amsa min cikin sakewa, ita kuma Ma'u sai ta bige da mirmishi kafin ta ce" A gaida min da yarana Sadiya." Kai na jinjina mata a saman leɓena na amsa.
Mu muka fara yin gaba sannan su, a juctiion muka rabu mu muka ɗau hanyar Lodge road, su kuma suka ɗauki hanyar Rijiyar zaki in da gidan Alhaji mustapha ya ke.
Tun da muka ɗau hanya ban yi magana ba. Hawaye na ke yi a ɓoye ina sharewa da gefen jijabina jikina. Yusuf sau ɗaya ya yi min magana na ce ya rabu da ni, sai ya maida hankalinsa kan tuƙi amman rabi da kwatan hankalinshi na kaina ganin yadda hawaye ke kwaramyamin wani na korar wani, ba wanda zai iya fahimtar yanayin baƙin cikin da na ke ciki, Ma'u ta daɗe ta na gigita duniyata ba tare da an sani ba amman komai ya zo ƙarshe. Na fahimci ni nake ba ma Ma'u daman da ta ke cin galaba a kaina to in haka ne zan dakile wannan damar zan toshe mata duk wata hanyar da za ta ƙara kuntatamin.
Sanda muka isa gida ko jiran Yusuf ban yi ba, na yi shigewata cikin ɗaki na barsa yana leƙa ɗakin yara. Bedroom ɗin mu na shiga na faɗa kan gado na saki kukan da na ke ta riƙewa tun dazu har da fitar da sauti.
Ina ji Yusuf ya shigo ganin ina kuka ya sa ya nufeni da sauri ya na faɗin"Haba Sadiyata, ina raye kike kuka? Ko za ki yi kuka ba za ki yi kuka a saman kafaɗata saboda na ji daɗin lallashin ki ba?
Ya faɗa ya na mai hawa gadon ya tarairayoni jikinsa, sai na faɗa masa muka durkushe saman gadon ina wani irin gunjin kuka shi kuma yana ta ɗan tapping ɗin bayana alamun lallashi bai hana ni kuka ba sai da na yi ya isheni sannan ya ɗago fuskata ya saka hannuwansa ya na share min hawaye lokaci ɗaya yana faɗin.
"Ya isa. Ki daina kuka ka da kanki ya fara ciwo. Shii.. is ok kin ji ko?
Haka ya ke faɗa, cikin sanyin murya, buɗe idanuwana da suke rufe ina kallonsa da jajayen idanuwana kafin na ce" Ka yarda da cewa Ma'u makira ce? Ka ga fa ta haɗa ni da mahaifina a gabana na kasa wani abu Yusuf, ta haɗa ni da kowa nawa.'
Sai na ƙara fashewa da kuka ina faɗin" Na rasa me na yi mata ta ke yi min haka? In saboda fasa auranta da Yaya Hamza ne ban yi nadama ba, saboda in da na bari da tuni ta haɗa mana yaƙi a gidanmu. "
Shi dai yana ta faman ba ni, ba ki ya na cewa na yi hakuri na daina kuka tunda Alhaji ya yi min faɗa na bi umarninsa.
Ƙura masa ido na yi kafin na ce"Haka ne zan bi umarninsa. Bakomai."
Daga haka na tashi daga saman jikinsa na sauka daga kan gadon lokaci ɗaya ina cire Hijabin jikina.
Fita na yi zuwa toilet ina wani tunani a cikin raina. Ba haka zan zauna Ma'u ta cigaba da cin galaba a kaina ba, tunda har ta riga ta samu magoya baya, ni kuma daman ba ki na yasa ko ina da gaskiya na ke zama mara gaskiya gwara na yi amfani da fatar bakin nawa domin ka da Alhaji ya sake yin fushi da ni gwara na cigaba da tafiyar da Ma'u kamar yadda nima ta ke tafiyar da ni.
*Janafty*
*TURKEN GIDA.*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY).*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JMpd8nXr7TIDD3ILDXh64z
*🅿️4*
Sanda su Ma'u suka ɗau hanyar gidansu da ke Rijiyar zaki. Zaune ta ke a bangaren mai zaman banza, kamar ba ita ce ta gama kuka wurjajan ba. Wannan karon mirmishi ne da Annuri ke fitowa daga ƙarƙashin zuciyan Ma'u kuma har ya ke iya bayyana a saman fuskarta.
Mijinta Alhaji Mustapha na tuki, sai ya waiwayo da hankalinsa zuwa kanta a tunaninsa har a lokacin ba ta bar kuka ba, amman ga mamakinsa sai ya ganta zaune tana mirmishi. Cikin mamaki ya ce"Har kin huce kenan Hajiyata?
Kallonsa ta yi ta na ɗan mirmishi kafin ta ce"Me ye a ciki? Ba fa komai Alhajina. Farinciki na ke yi yau Sadiya ta kalleni a matsayin ƴar'uwa. Zuciyata na cike da farincikin da ban taɓa tsintar kaina a ciki ba."
Ta ƙarishe faɗa fararan haƙoranta na bayyana a waje. Ma'u Fara ce farinta mai irin ja ja ɗin nan ne, taNa da fadin fuska sannan ba ta da tsawo kuma tana da ɗan jiki, sai kibar ta yi mata kyau sosai.
"Ni fa Sadiya ce ke ba ni mamaki har yanzu. Kina ƴar'uwanta haba. Sai ka ce bare ko bare ce ke ai wannan ƙiyayyar ta yi yawa Asma'u. Ni ko da muke haɗuwa ba ta son yi mini magana ban kawo haka ƙiyayyar nata a kan ki ya yi ƙamari ba, na fi danganta haka da halinta ne tunda ko Anty Bahijja za ki ji ta na complain da Matar Tafida ba ta son mutane, ga shi kuma ta auri ɗan dangi."
Maganarsa ya katse mata tunanin da ta ke yi, kallon shi ta yi mirmishin da ya ke so game da ita. Asma'u ba ta fushi ko an ɓata mata rai yanzu yanzu za ta huce ka ga har tana mirmishi.
"Bakomai Alhajina ai komai ya wuce yanzu. Kuma da man ko lokacin muna gida ni da Rahila mun fi Sadiya son mutane, ita haka take ba ta cika son mutane ba gaskiya."
"Amman ko halinta ba mai kyau ba ne. Ina mamakin yadda Injiniya ke iya zama da ita da wannan murɗewan na ta."
Mirmishi Ma'u ta yi masa ba tare da ta ƙara magana ba. Ta gaji da bashi amsa tana Allah Allah ya yi shuru ya maida hankalinsa kan tuƙinsa amman sai da ya juyo da niyar ƙara yin wata mgana sai kuma wayarsa da ke gaban Aljihunsa ta fara ɗaukan sauti alamun ana kiran shi, shi ya katse masa mganarsa sai ya maida hankalinsa kan wayarsa.
"Alhaji Garzali ne.."
Haka ya faɗa sannan ya ɗaga wayar. Mirmishin gefen kawai ta yi, ya na waya hannunsa ɗaya na saman sitiyari hankalinsa rabi na kan waya rabi na kan tuƙi, shi ya sa ma ya rage gudun motar sai aka ci kuma sa'a dare ya yi sosai ba yalwar giftawan motoci sosai.
Ƙuri Ma'u ta yi masa da ido, tana ƙare masa kallo. Alhaji Mustapha ba zaɓin ta ba ne, ba kuma shi ne muradinta da mafarkinta ba. Ba domin Sadiya ba da ƙila yanzu ita ce a gidan Yaya Hamza kuma ita ce mahaifiyarsu su Afnan ba Khaleesat ba, ba domin Sadiya ta yi mata baƙin ciki ba da yanzu ba ta auri wannan magidajen kanon ba. Shi ya sa har gobe wannan dafin da Sadiya ta bar mata ya kasa ɓacewa daga cikin zuciyarta. So ta ke yi ko da ƙwatanƙwacin irin baƙin cikin da ta ji ne, itama Sadiya ta ɗanɗani irin shi ta ji in da daɗi.
"Ma'u..Ma'u.."
Muryan Alhajin nata ya katse mata tunani, sai ta dawo da ƙwayan idanuwanta a kansa, daman can sunan ta na kallon shi ne amman tunaninta da hankalinta ba su a kansa kwata kwata.
"Tunanin me kike yi haka? Ina ta magana kin yi shuru?
Basarwa ta yi kafin ta yi mirmishin da ta san ya na sace zuciyansa.
"Tunaninka na ke yi mana My Alhaji."
Ta faɗa lokaci ɗaya ta na yi masa fari da wani kallo da shi kaɗai ta san yana kunna shi, aiko sai ga shi ya ke ce da wata dariyan nishaɗi kafin ya buga sitiyari lokaci ɗaya yana faɗin" Ma'u. Ma'u na, ba ki da dama."
Mirmishi ta sake yi tana kara narke masa, dariyan ya sake yi kafin ya ce"Alhaji Ghali na gaishe da Amarya Ma'u."
Cikin yar dariya ta ce"Ina amswa. Ya iyalan nasa? Ya amsa mata da suna lafiya kafin ya ɗora da faɗin" Kin san ko har gobe in na je gidan sai Hajiya Fati ta yi mini tsiyan ba ki zo mata Allah ya sanya alheri ba, lokacin bikin ƴa'ƴanta."
Kai tsaye Ma'u ta ce"Ayya. Ba ka gaya mata bana nan ba ne lokacin? Kuma ai Hajiya ta je ta wakilceni"
Ya na dariya ya ce"Nima haka na ce, da Hajiya da Ma'u duk abu ɗaya ne a waje na."
Taɓe baki ta yi, a farko sannan ta ɗan saki fuska kaɗan. Hira ya cigaba da yi mata, sai faman taɓe baki ta ke yi, in zai juyo sai ta sakar masa lallausan mirmishin da ta san ya na kunna sa har cikin zuciyarsa.
Kanta ta maida jikin window din motar tana kallon hanya har ga Allah ba ta son surutu, surutun ma a wajen Namiji, ba haka ta so mijin auranta ya kasance ba, ta na son namiji mai Aji da kamewa amman mai ake yi da gidahumin namiji, waiwayawa ta yi ta na ƙara kallon Mijin nata wani abu da ya daɗe da tokare mata zuciya duk sanda ta kalleshi a matsayin mijinta ya sake ta so mata. To ta san ba ta san shi me ya sa ta aure shi?
Ba saboda kowa ba ne sai Saboda da BAABA. da kuma KUƊI. Ba domin kuɗin Alhaji Mustpha ba, da ko hanya ba za ta iya haɗawa da shi ba, tunda ya yi yamma da irin zaɓin mijin da ta daɗe tana mafarkin samu. Alhaji Mustpaha irin ƙauyawan kanawan nan ne, shi bai yi boko ba sai arabi, amman fa ya san kan kasuwanci yana kasuwancin Fata sannan kuma ɗan chajin ne, yana da kuɗi sosai. Kuma mahaifinsa ma har ya mutu sana'ar fata ya ke yi, shi ya sa zuru'arsu ke da kuɗi, amman bayan nan mugun bagidajen ƙauye ne, mara lissafi. Sannan ita ba ta taɓa hango kanta a matsayin macen da za ta yi aure ta zo a mace ta biyu, ta tsani zama da kishiya a rayuwarta saboda mahaifiyarta tun auranta na fari ba ta ji daɗin kishiya ba, kafin ta zo ta auri mahaifinta mutuwa ta zo ta raba, sannan a auranta na uku ma gidan kishiyiyon ta je, da har gobe ba ta huta ba. Shi ya sa ta yi fatan samun gidanta ita kaɗai ta gina shi duk yadda ta ga dama ba wai ya kasance ita ce zata shiga gidan da wata ta gina ba.
Amman kaddara ta riga fata, ko da ya ke Sadiya ce ta sauya mata kaddaranta. Domin saura ƙiris ta cika mafarkinta ta yi sanadiyar lalata komai, shi ya sa itama ba ta da wani buri sai na ganin ta lalata ma Sadiya jin daɗin duniyarta ta gigita mata rayuwarta yadda ƙwatankwacin yadda ba ta samu abin da ta ke so ba, itama ba ta fatan Sadiya ta cigaba da samun abin da ta ke so, in ma ta samu to za ta yi sanadiyar lalata shi ya zama baƙinciki a gare ta. Tana da burika da dama akan Sadiya waɗanda ko kwatansu ba ta cika ba. Nasara a kan Sadiya yanzu ta fara yi in a baya ita ta ta yi kuskuren barin Sadiya yin nasara a kanta wannan ƙarnin baya ne da ya shuɗe. Wannan ƙarnin na yanzu ita ce za ta cigaba da samun nasara akan Sadiya daga nan har abadan.
Ba ta ma san sun iso gida ba, sai da ta ji yana hon sannan ta farga da har sun iso gida, gidan Asma'u ƙaton gida ne mai kama da Aljannar duniya, amman duk wannan daular ba ya gabanta matukar ba ta ɗanɗana ma Sadiya irin ɗacin da ta ke ji a cikin zuciyarta ba, ba za ta taɓa samun kwanciyar hankali ba.
Ita ta fara yin gaba zuwa cikin gida. Ta bar Alhajinta na magana da megadi, a falon gidan ta ci karo da ƙanwarta Zainab ƴar kimanin shekaru 16 zuwa 17, da ke hannunta tana zaune ta na kallo, abin sai ya ba ta mamaki ta na ganinta ta yi saurin miƙewa tana sosai ido, wani kallo Ma'u ta yi mata kafin ta ce"Uban me kike yi har yanzu ba ki yi barci ba?
Cikin In ina Zainab ta fara faɗin" Ina. Ina. Kallo ne."
Kafin Ma'u ta samu zarafin magana Alhaji Mustapha ya shigo falon kawai sai ta fasa maganar da za ta yi sai ma ta kalleta tana faɗin" Kin tabbatar da kin saka su Baba ƙarami sun yi fitsari kafin su kwanta ko?
Da sauri ta ɗaga kanta, Alhaji Mustapha na tambayan me ya faru? Ba ta tsaya bashi amsa ba ta kama hanyar ɗakinta lokaci ɗaya ta na faɗin" Ki kashe kallon nan ki je ki kwanta."
Daga haka ta shihe koridon da zai sada ta da ɗakin barcinta a ƙasan ranta ta na ji kamar ta ce Alhaji ya je gidan Hajiya yau ba ta cikin Mood ɗin da za ta iya dauriyan kwana dashi.
Shi ya sa ta na shiga ɗakin barcin na ta ta maida ƙofa ta rufe. Wayarta ta sauke nan saman gadon da mayafinta sannan ta buɗe kofar tiolet ta shiga wanka za ta yi, ta na cikin wankan ta ji Alhajin nata na ƙwanƙwasa mata kofar, tsaki ta ja a fili da ɓoye wani abu na suƙan zuciyarta dagacan ƙasa.
Ta na fitowa ɗaure da Towel, har lokacin bai tafi ba ko ya tafin ma ya sake dawowa.
"Ma'u. Ma'u ta,..'
Tsaki kawai ta ƙara ja a fili sannan ta isa ga kofar ta murza key, ta na buɗewa kawai ta juya ta dawo cikin ɗakin gaban madubin da ke shake da kayan kwalliya ta tsaya shi kuma cikin jallabiya ya shigo yana mai washe baki.
"Au wanka kike yi ne?
Juyowa ta yi sannan ta gyaɗa masa kai tana mirmishi, shi kuma sai ya rumgumota ta baya fuskarsa da nata na bayyana ta cikin madubin, Asma'u ta yi mirmishi, mirmishin da a saman leɓenta kawai ya tsaya, tana kallon Alhaji Mustapha kansa har ya fara furfusa ga uban sauƙo, a fuskarta mirmishi ne, amman a ƙasan zuciyarta ƙuna ne da wani irin turiri da ya ke ta so mata.
Ita ko za ta iya yafe ma Sadiya? Kai ina sai ta gigita rayuwar Sadiya. Sai ta yi sadiyar zama sanadin da farincikin Sadiya zai yanke na har abada. Yadda ita ba ta zauna ita kaɗai ba, itama Sadiya burinta ba zai cika ba, sai ta gayyato mata damuwowi masu tarin yawa a rayuwarta wannan alƙwarin ASMA'U SULAIMAN YASHE ce.
******
*BAYAN KWANA HUƊU*
LODGE ROAD.
JUMMA'A.
Karfe 7:40am na safe Salisu ya zo ya ɗauki su Jidda zuwa makaranta. Suna tafiya ban huta ba na shiga ɗakinsu ina haɗa musu kayansu, na zuwa gidan Anty Maimuna ko jiya sai da ta kirani a waya tana gwaɓa mini magana wai wannan satin ma hala gidanmu za su je? Ban biye mata ba na ce yau in sha Allahu za su zo.
A ƙaramar jakar baya na Jidda na haɗa musu kayansu da duk abin da za su buƙata, tiolet na shiga na ɗauko musu brush na fito kenan sai na ga Yusuf zaune a gefen gadon su Jidda.
Sanye yake da jallabiya. Tun bayan dawowarsa sallar asuba ya kwanta ban ma san ya tashi ba.
Tsayawa na yi sororo ina kallon shi kafin na yi mirmishi na ƙariso ina faɗin"Har ka tashi?
Miƙewa ya yi ya zo gabana ya buɗe min hannuwansa na faɗa ya rumgumeni yana faɗin" Ina kwana Sadiya ta."
Na amsa ina sakin sa kafin na ce"Na ga barcin ka ya yi nisa shi ya sa na ce su Jidda kar su tashe ka, su tafi kawai."
Ya na tsaye ya harɗe hannuwansa a saman kirjinsa ni kuma sai na duka ina saka musu brush ɗin su a cikin jakan da na haɗa musu kaya.
"Kayan me ye wannan?
Ina duƙe na ce" Kayan su Jidda ne.
"Na zuwa ina kuma?
Sai da na ɗago sannan na kallesa kafin na ce"Gidan Anty Maimuna. Wancan satin kasan ba su samu zuwa ba."
Sai a lokacin ya ce"Oh. Na tuna ko jiya da na je gida Nene sai da ta yi min magana. Wai Anty Maimuna na ta faɗa."
Ina kallon idanuwansa na ce"Wai faɗan me?
Taɓe baki ya yi kafin ya ce"Ban sani ba, amman ta tambayeni me ya hanasu zuwa wancan satin na ce ma Nene ban sani ba."
Baki kawai na saki ina kallon shi, wai bai sani ba, Me ya sa Yusuf ya ke yi mini haka ne? Yadda ya ga ina kallonsa ne ya sa ya fara dariya, ya matso ya riƙeni na matsa baya ina haɗe rai kafin na ce"Ba ka sani ba ko? To ai ya yi kyau."
Ina gama faɗin haka na juya na bar masa ɗakin. Wai ni haka maza suke ko nawa mijin ne haka? Sau tari wasu laifuffukan da danginshi ke kallona da shi har da laifin shi, sai a yi abu kuma ya san dalilin faruwan shi amman in suka tare shi da maganar sai ya ce bai sani ba, kuma na
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 31