Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Haka ko aka yi na samu Adaidaita zuwa pizzet, daga can akwai ƴan sahun da suke yi lodin samaru har Shika ita na hau, ta cika da wuri, mu uku ma duk shikan za mu je, sauran ne za su tsaya a samaru.   Muna hanya Yallaɓai ya sake kirana na ce masa ina hanya in mun isa zan kira shi. Na sauka Main get na asibitin Shika na duba agogon da ke ɗaure a tsitsiyan hannuna tara da mintina sha biyar, bayan na sallami mai adaidaita na shiga ta babban get ɗin.   Ban kira Yallaɓai ba sai da na kira lambar Dr Fadil kamar yadda muka yi alkwari sai dai bai ɗaga kiran ba, sai na wuce ta can babban falon da ke kusa da main get, na samu waje na zauna asibitin ta cika da zirga zirgan mutane ballatana yau ɗin monday ne, ga marasa lafiya nan birjit ana ciwo Allah dai ya bamu lafiya.   Na sake kiran Yallaɓai na ce masa na sauka ina cikin asibitin amman na kira Dr Fadil bai ɗauka ba, sai ya ce na ƙara kiran shi tun da ma ya ga da sauran lokaci ƙila bai shigo asibitin ba ne.   Mun gama waya da Yallabai kenan Uncle Abba shima ya kirani bayan mun gaisa ya tambayeni ko ina cikin asibitin ne? Sai na amsa masa sannan na gaya masa na kira wayar shi ta shiga amman bai ɗauka ba sai ya ce bari ya kira shi.   Na ɗan yi zaman sama da mintina ashirin, data na buɗe ina duba istergram na wata Hamida makeup , ina following ɗin ta sosai saboda ta iya kwalliya so na ke yi ma na shiga class ɗin ta za ta fara farkon wata gaba anan kano ne na wata ɗaya akan kwalliya, na rage Volume ina ta kallon Videos ɗin kwalliya daman ni duk sune na ke following a wayata,  ina cikin duba dube na sai ga kiran Dr Fadil da sauri na ɗaga kiran gaisawa muka yi sai ya ce yana hanya yanzu zai ƙariso ina ina ne? Sai na gaya masa sai ya ce na jira sa ga shi nan zuwa.   Bayan nan kuma na sake wani zama na tsawon mintina goma sha biyar sai ga kiran shi Again ina ɗauka ya ce" Ga ni a babban falon, ko za ki iya miƙewa ko zan gane ki? Ina jin haka na mike na juya daman a kujerun baya na zauna duk an ma cika na gaba gaba, waige waige nake yi saboda akwai mutane sosai kuma na ga masu waya sama da mutane goma.   "Wani kalan kaya ki ka saka?   Sai na amsa da ina sanye da jan mayafi, sai ya ce kawai ya ganni daga nan ya kashe wayarsa, har ga Allah ni ban gan shi ba sai da na ga wani baki dogo sanye da suit da rigan likitoci a hannunsa tare da briefcase, fuskarsa sanye da wani siririn gilashin, ganin ya na min mirmishi ya sa na fahimci wannan ne Dr Fadil.   "Sadiya Right?   Haka ya faɗa bayan ya tsaya a gabana da sauri na amsa masa sai ya yi gaba yana faɗin"Biyo ni, sunana Dr Fadil. Ni ne Abdulmu'iz ya ce zan taimaka miki.'"   Ina bin sa a baya na ce"Ina kwana" Ya na yar dariya ya ce ai mun gaisa a waya, sai ya dan tsaya har na karoso mu ka jera yana min bayani zan siya domin na buɗe fayel, agogon hannunsa ya duba kafin ya ce"Da fari na so ki ga Dr Nayama ne amman ta ɗauki Annual leave ɗinta last week amman na samo miki appoitment da Dr Fatima Tasiu, ba ki da matsala na ce ke ƙanwata ce saboda haka mu je a siya katin sai na raka ki can in da za ki gan ta."   Muna tafe ina yi masa godiya, Ban sha wahala ba muna zuwa wajen biyan kudin kati bai ma karɓi kuɗina ba ya siya mini sannan muka je ya nuna recip ya karɓo mini kati aka buɗe min fayel, kuma ya ce a bashi Fayel ɗin da ƙaramin katin a hannunsa shi zai kai ma Dr Fatima, daga nan mu ka fara tafiya zuwa bangaren Gyea ɗin ni kuma ina tambayansa nawa ne aka kashe da niyyar na bashi kuɗin sa?   Sai ya kalleni ya na dariya kafin ya ce"Haba, ke ba ƙanwar Abdulmu'iz ba ne? Kallonsa na yi saboda ina so na tuna da sunan da ya ambata. Sai na tuna da Uncle Abba ya ke mgana. Sai na rausayar da kai kafin na ce" E. Amman ina auran yaron Yayarsa ne. Sannan aminaine tare suka tashi da mijina."   Sai ya ɗan juyo yana kallona kafin ya ce"Oh. Nima Babana ɗan Rano ne, amman kaduna muka tashi mun haɗu da Abdulmu'iz a BUK ne kafin na samu scholarship zuwa Singpore."     Sai na jinjina kai alamun gamsuwa, muna tafe yana gaiswa da mutane sannan jefi jefi ana kiransa a waya, mun isa shashen Gyea ɗin akwai likitoci da mutane suna ta layi, amman da ya tambayi Dr Fatima sai a ka ce ba ta riga ta iso ba, sai ya ce na zauna na jirata bayan ya ba ni fayel dina ya ce na riƙe zai mata waya ya faɗa mata in ta iso ni za ta fara gani, na yi ta masa godiya ya ce in akwai wata matsala na kira shi, shima zai wuce bangarensa ne akwai patient na jiran sa.   Aka ce mai nema baya fushi, mun yi zama sama da awa ɗaya, wasu ana ta kiran sunan su suna shiga wasu offices ɗin. Ni dai ina zaune mun yi magana da Yallabai na faɗa masa yadda ake ciki gani dai ina jiranta, ban gaji saboda na saba sama da shekaru bakwai ina zuwa ganin likita zaman bai wani dame ni ba  tun da ga waya a hannuna ina ta latsawa.   Hankalina ya tafi kan waya har ga Allah ban san ta ina likitan nan ta zo ta wuce ba, ni dai kawai na ga wata mace da fararen kaya ta fito tana kiran sunana. "Wacece Sadiya anan? Ina shirin na ce ni ce, sai na ga wajen mutane uku sun ɗaga hannu, sai ta tsaya tana kallonsu kafin ta yi tsam sai kuma ta ce" Wacce Dr Fadil ya kawo?   Sai na yi saurin miƙewa ina faɗin" Yes Ma.". Sai ta kalleni akwai fayels a hannunta, kafin ta ce na biyo ta, da sauri na ɗauki jakata da Fayel ɗina na bi bayanta har zuwa wani office dake gefenta tana gaba ina bin ta a baya.   Likitar na zaune a saman kujeranta, kanta na kasa tana rubuce rubuce akan wata takarda. Wacce ta shigo dani ta bani izinin zama sannan ta fice ba tare da ta yi magana ba, zama na yi a kan kujera na zaman marasa lafiya, Office ɗan daidai akwai wani kato a ciki sai wata kofa ina tunanin kamar Tiolet ne.   "Fayel na ki."   Haka kawai ta ce mini har lokacin ba ta ɗago ba, sai na miƙa ma ta ta saka hannu ta karɓa lokaci ɗaya tana gyara zaman gilashin da ke idanuwanta.   Ta duba sannan ta fara rubutu a jikin Fayel ɗin kafin ta ce"Kin zo da Report ɗin ki na baya? Kaina na gyaɗa kafin na yi saurin buɗe jakata na ɗauko su na tura mata gabanta ta ɗauka ta fara dubawa ɗaya bayan ɗaya sama da mintina goma. "HalimatusSadiya Sulaiman Yashe" Na amsa mata da Yes Mah."   "Ke ƴar Yashe ce?   Sai na amsa da eh kafin na ce"Alhajinmu ɗan can ne." Na faɗa ina kallonta sai a lokacin ta ɗago na ganta da kyau fara ce tar, a shekaru sai dai mu zo tsara ko za ta girmeni da kaɗan ne, tana sanye da rigar likitoci ta yane kanta da mayafi baki sai siririn gilashin da ke saman fuskarta.   Sai na ji gabaɗaya ta burgeni. Har na shagala da kallonta. "Haihuwanki nawa kafin ki yi planning? "Ɗaya." Da hausa take yi mini magana nima ina maida mata da hausa, kanta na ƙasa tana ta rubuce rubuce. "Na how many month kika yi alluran? "Five years" "Amma na 6 months na riƙa yi" Sai ta ɗago ta kalleni kafin ta maida kanta ta cigaba da rubutu a saman fayel ɗina. "Bayan haka, kin sake haihuwa? Na amsa da E. Sai ta ce When, sai na ce bayan first born ɗina ta shekara tara. "Wani symptoms ki ka samu kafin ki sami ciki da kuma bayan kin samu? "Na samu matsalan zubar jini, sannan ga juwwa da ciwom mara, daga baya na fara ramewa sannan bayan nan na daɗe ban samu ciki ba sai bayan shekara tara ga rikicewar al'adata." "Bayan kin samu cikin fa?   "Bayan na samu ciki na wahala, domin har lokacin ban daina zubar jini, sai da na je asibiti aka ɗora a kan mgani. Na sha wahala da ban ma iya haihuwa da kaina ba sai da aka yi min C.S." "Na gani a rubuce an ɗora ki kan magani domin tsaida jinin ko? Sai na gyaɗa mata kai kafin na ce"E. Kuma in na sha jinin na tsayawa gaskiya." Sai ta jinjina min kai, ta ɗan daɗe tana rubutu kafin ta ɗago ta na kiran sunana. "Miss Sadiya." Na amsa mata da Mah. "Da kika fara zuwa ganin likita bayan kin fuskanci canje canje a jikin ki, an faɗa miki kin samu Secondary Infertility ne?   Sai na gyaɗa kaina, ba ta damu ba ta cigaba da faɗin" Daman in kuka zo za ku yi planining, ana yi muku bayanin cewa akwai disadventage da advantage na yin shi ko? Kuma sai da amincewar miji da mata ko? Sai na amsa mata da Yes. Sai ta ƙara kiran sunana. "Miss Sadiya." Sai na amsa mata. "Me ya sa kika zaɓi ki zo wannan asibitin? Na ga a fayel ɗinki ya nuna daga kano kike? Me ya sa ba ki tsaya a asibitin Aminu kano ba? Kai tsaye na ce"E. Daman zaɓi biyu a ka bani ko can ɗin ko nan ɗin. Na ji hankalina ya fi kwanciya da nan ɗin ne."   Sai ta jinjina kai kafin ta ɗago ta na kallona lokaci ɗaya kafin ta ce" Za ki iya jin haka. Amman a matsayina ta likita zan iya ba ki wata ƴar shawara? Sai na gyaɗa mata kai. Ba ta damu ba ta cigaba da faɗin" Zai zame miki wahala a ce duk wata ki rika tasowa daga kano zuwa Zariya ganin likita. Kar mu fara saka maganar kashe kuɗe da walwalahu mu fara duba yanayin tsaron ƙasarmu da ya ke ƙara tabarɓarewa."   Ba ta damu da na yi mgana ba ta sake kallona kafin ta ce" Zan yi transfer ɗin ki zuwa Aminu kano.  Zan haɗa ki da wata consultan Dr Aisha Bukar ita za ki cigaba da gani a kan matsalan ki. Karki damu duk ƙwarewarmu a nan suma acan akwai ƙwararru kuma duk ɗaya ne abin da za mu yi miki a nan a can ma shi ɗin za su yi miki."   Na yi shuru ina tunanin maganarta. Kuma gaskiya ts faɗa. Ban yi tunanin haka ba Yallaɓai kuma bai yi magana ba saboda ya ga nan ɗin na ke son zuwa. "Miss Sadiya ta amince na yi mata Transfer zuwa Aminu kano? Ajiyar zuciya na sauke kafin na ce"Shike nan." Mirmishi ta yi kafin ta ɗauki wayarta da ke kan Tebur ta danna. Zuwa can ta  saka ta a speaker ta ɗora saman tebur ɗin gabanta. Ita kuma sai ta cigaba da rubutu saman wata takardan da ta yaga daga wani littafi da ke gabanta. "Hello. Dr Fatima." Aka faɗa daga cikin wayar cikin harshen Turanci suka gaisa sannan ta ce"Dr Aisha zan yo miki transfer ɗin wata patient ta bangarenki ce gynea. A kano ta ke ta zo ganin likita anan asibitin saboda nisa na ga gwara ta koma tana ganinki a can." "Ohk.." "Zan tura miki bayanan ta in brief ta email ɗin ki. Yaushe za ki ba ta appoitment? "Mu bar shi next week. Gobe zan je semina lagos sai after 3days zan dawo. Mu bar shi coming monday sai ta zo ta same ni a asibiti in sha Allahu." "Thank You Dr. Aisha." "Always Welcome Dr. Fatima. Daga haka suka katse kiran, ni dai ina zaune bayan ta gama rubutun ta miƙa mini takardan da report ɗin na wancan asibitin sai da na karɓa sannan ta ce" Na yi mata mgana Consultan ce. Ranar monday za ki je Aminu kano ki ganta. Ki je mata da wannan takardan" Na rusunar da kai ina yi mata godiya. Jinjina kai ta kafin ta ce"Miss Sadiya mun fito daga Jiha ɗaya nima Granfa ɗina ɗan Yashe ne. Wacce na haɗa ki da ita za ki samu dukkan abin da kike nema daga gare ta. Zan ba ki lambarta ana gobe za ki shiga asibitin ki kira ta, itama zan tura mata lambar ki in sha Allahu matsala. " Sai na ji kamar ma na samu waraka daga matsalolina ina ta yi mata godiya. Ta karanto min lambarta na kwafe a waya na yi saving. Itama ta ce za ta tura mata lambata. Na fito daga office ɗin ina yi mata godiya.   "Thank You Doctor." "My pleasure." Ta faɗa tana mirmishi.   Sai da na fito haraban asibitin sannan na kira Dr. Fadil na faɗa masa Dr Fatima ta sallame ni. Ya tambayeni ko ba matsala na? Sai na sanar dashi ta yi mini Transfer zuwa Aminu kano ta haɗa ni da wata consultan. Shima ya nuna hakan ya yi dai dai saboda zirga zirga can zai fi sauƙi kuma duk ɗaya ne Shika da Aminu kano duk manyan asibitoci ne a afurka. sallama na yi masa tare godiya ya ce bakomai.   Na dawo gidan Yaya Hamza bayan sallar azahar ne, ina ma hanya ne azahar ɗin ta same ni. Itama kanta Khaleesat ɗin ta yi mamakin dawowata da wuri. Ina sauke jakar hannuna ina faɗin" Ke kam don ma na tsaya motar da na hau zuwa pizzet ba ta cika da wuri ba da tun ɗazu ina gida.."   Khaleesat ta sake riƙe baki kafin ta ce"Ikon Allah. " Sai da na kai zaune domin na ji kafafuwana sun gaji, sannan na cire mayafin jikina ina faɗin" Ke kam komai fa yanzu a Nigerian nan in kana da hanya ba ka ba baƙin ciki. Ƙarin abin ma likitan musulma ce kuma yar garin mu ce itama ƴar yashe, sosai ta karɓe ni, ni ta fara gani bayan ta iso da taimakon Dr Fadil." "Ai fa. Na ga alama. Fatan dai an da ce? Ba wata matsala ko?   Ta faɗa lokaci ɗaya ta na zama a gefena. Kora ma jawabin yadda mu ka yi na yi sannan na ƙarishe da faɗin" Ta ce a duka ɗaya ne. Ta yi Transfer ɗina zuwa Aminu kano ta haɗa ni da wata consultan ɗin" "Allah ya sa a dace. Maganarta gaskiya ce. Ko don zirga zirga. Nima kuma sai da na yi tunanin haka ban dai yi mgana ba ne." Na amsa mata ina hammar gajiya da yunwa kafin na ce" Ni idona ne ya rufe, gani na ke yi in na je nesa zan fi dacewa.". Dariya ta yi min kafin ta ce. "Ki yi sallah ga abinci nan na gama tun ɗazu" Da toh na amsa mata sai da na mike sannan na kwashi jakata da mayafina. Ita kuma sai ta juya ta nufi kitchen daman a ciki take lokacin da na shigo gidan. "Ina Amna? Ban ji motsinta ba ne? "Ta yi barci yanzu ba daɗewa ba."   Ina shiga ɗakin da na sauka ina faɗin" Wannan yarinyar kamar kasa? Sai barcin tsiya." Ina jin dariya Khaleesat. Nima dariyan na yi nifa tun da aka haifeta duk lokacin da zan ganta tana barci ne, jiya ma da na zo ana gama bata nono sai barci da safe har na fita tana barci, yanzu ma haka.   Tiolet na shiga na ɗauro alwala na zo na yi sallah. Na idar kenan ina addu'a na ji wayata a cikin jaka na ringing da sauri na miƙa hannu na ɗauko jakar daga saman gado kafin na fito da wayar ta tsinke. Ina dubawa sai na ga Yallaɓai ne kaina na dafe na manta shaf ban kira shi ba, ina dafe da kaina ya sake kirana ina ɗagawa na ce bayan na sassauta murya. "Yallaɓai na."   Daga can bangaren ya ce"Ba wani Yallaɓan ki, ina ta especting kiran ki shuru ni da na damu na kira. Ya ake ciki ne? Ina ta jin hayaniya a wajen da ya ke, ban ma samu zarafin mgana ba na ji ya na sake faɗin" Ga Kawun ki nan ya damu sai cewa ya ke akira ki a ji me ake ciki" Karya wuya na yi kamar ya na ganina kafin na ce"Ayya Afuwan Yallaɓai na. Ina shirin kiranka ne sai ga kiran ka" "Na ji. Yanzu ya ake ciki? Bayani na yi masa duk yadda muka yi da likitan na ƙarishe da faɗin" Ta ma haɗa ni da likitan rana ita yau in sha Allahu zan je na ganta a Aminu kano in sha Allahu. Kai tsaye ya ce" Nima na yi miki wannan tunanin amman ganin kin dage sai can ɗin shi ya sa na ƙyale ki? Ba dai wata matsala ko?na amsa masa da ba matsala. Mun cigaba da tattaunawa har na ce ya ce ma kawu ya yi ma Dr Fadil Godiya ya yi min ƙokari. "Injiniya muna buƙatar ka anan wajen fa" Na ji ana faɗa daga cikin wayar. "Yau ma kana Rano ne? Sai ya amsa min da E. Sallama muka yi tunda ana ta aiki ne, muka rabu akan sai anjuma in mun sake yin waya. ina wayar ma Khaleesat ta yi ta leƙowa, na san maganar abinci ne, ina sauke wayar nan saman gado na zare hijabin jikina na fita falo. Ta na zaune akan kujeran Dinning ta na jirana tare muka ci abinci doya da miya muna ci muna hira bayan mun gama muka dawo falo, ta kunna kallo amman rabin kallon duk hirar duniya ce muke yi da ita.   "Ni fa lamarin ki ya bani tsoro. Kin san Allah ina son nima na yi tsarin iyali na huta ko na shekara uku ne."   Ina ƴar dariya na ce" Zan faɗa in dai magana ta zo akan family planning ba na sauya magana ta. Ba tsarin iyali ne ba a so ba, ba kuma cewa na yi bashi da amfani ba, ammam ki sani bayan amfaninahi akwai rashin amfaninshi, ya na da kyau a yi ɗin tun da malamai ma suna faɗin a yi amman ba zan ba ma kowacce mace shawaran ta yi tsarin iyali ba ta haihu kamar biyar ba, saboda tarin ƙalubalen da ke cikin haka, in kika haihu kamar sau biyar ko da ya ninka adadin shekarunsa sau uku ne ba za ki damu ki ji kina son ƙarin haihuwan ba, sannan wani matsawar dangin miji duk ba za ki fuskanta ba. Ko kafin a farga Ƙila Allah ya ƙara ba ki wata haihuwar shikenan amman a irin yadda na yi nawa, akwai hatsari ba zan goya miki bayan ki yi ba. Ki yi ta haihuwanki zuwa gaba sai ki yi domin ki huta amman in kin aminta da shawarata fa kenan."   Na ƙarishe faɗa ina kallon ta, sai na ga ta yi shuru kamar ta na nazari da sauri na ce" Ban fa hana ki ba. Ki yi in kina da ra'ayi amman ki sani ki shirya karɓan abin da nima na ke karɓa duk da bana yi miki fatan haka sannan kowacce  mace da yanayin yadda abin ya ke karɓanta da kuma illar da ya kan nuna a jikinta. Ba lalle abin da ya faru da ni ya faru da ke ba, watakila ke ki fuskanci ƙalubalen ta wanni fannin dabam. Amman shawaran da zan ba ki shi ne, ki bari ki ƙara haihuwa kamar sau biyu zuwa uku sai ki huta."   Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce"Shikenan bari na bari ko zuwa gaba. Shima fa Yayan na ki cewa ya yi bashi da matsala duk lokacin da na ji ina buƙata zai yi supporting ɗina."   Mirmishi na yi kafin na ce"To wai daman su Maza ina ruwan su? Zai ba ki goyon baya mana. In matsala ta faru yana da zaɓi zai iya ƙara aure ke kuma fa? Kin cutu har abada in kuma danginsa sun matsa ya ce ai tsarin iyali kika yi kamar yadda  Yallaɓai ya yi mini a wajen dangin sa. Da suka damu da rashin haihuwata bayan Jidda shi ya faɗa ma Anty Maimuna wai tsarin iyali na yi ya zo ya ba ni matsala ba shikenan ya gogamin baƙin fenti ba, da sun tashi gwaɓamin mgana sai su ce ai ba Allah ne ya tsaida min haihuwan ba ni na tsaida ma kaina. "   Khaleesat ta yi dariya kafin ta ce" Ke da Yallaɓan na ki kuma? Baki na tura kafin na ce" Yallaɓan fa nawa. Wani lokacin ya cika abin haushi ne." Dariya ta yi mini nima ina tayata. Nan muka lalace muna ta tattaunawa. Sai sallar la'asar muka tashi daga falo ita ta wuce ɗakinta ni kuma na nufi in da na sauka. Bayan na idar da sallah na kira Saude mu ka gaisa. "Saude ya gidan ne? Fata komai lafiya ko? Sai ta amsa mini da lafiya lau kafin ta ce"Anty yaushe za ki dawo? Kai tsaye na ce" Gobe in sha Allahu." Fatan dawowa lafiya ta yi mini ni kuma na ce zan ƙara kiranta in su Jidda sun dawo daga makaranta. Daga nan sai na kunna Data saƙonni na ta shigowa. Maganar Yaya Auwal na fara gani na yi saurin buɗewa. "Zan shigo wannan weekend ɗin fa."   Cikin jin daɗi na rubuta masa Allah ya kawo shi lafiya. "Kai da Laila da yara ne? Yana online amman sanin halin shi da sai ka yi saƙo sai ya ga dama zai buɗe sai na fita, ina duba sauran saƙonnin sunan MA'U da na gani ta yi mini magana ya sa na yi tsaki na wuce ta, na ga an yi mgana a group ɗin gidanmu ban shiga ba domin ban ga an yi tagging ɗina ba kenan mganar ba ta shafe ni ba. Amina ce ta yi min mgana da cewa ta kira waya ta ba ta samu ba na ce mata network ne.   Sai na fita na je bangaren Status ina ta dubawa. Rahilarmu na ga ta saka status har ina rawan jikin dubawa. Ya Muntari na gani ya na riƙe da jaririyar(Zainab Nihad) ba hoton ne ya ba ni dariya ba, sai rubutun da ta yi a ƙasa. "Hubby na. Abu Zainab I love u."   Dariyan da na saka har a sarari, na danna Viocenot ina ƙyaƙyata ma ta dariya kafin na ce"Rahila ma su Hubby, wai Ya Muntarin ne kuma ya koma Hubby? Daga Yaya Muktar ya koma Hubby." Bayan nan na sakin mata VN ɗin. Sannan na riƙa jere mata sticker na shaƙiyanci. A yammacin nan dai status ɗin Rahila ne ya nishaɗantar da ni. Ba ta online, abin mamaki shima Ya Muntarin na ga ya yi sreenshoot ya saka a jikin sunanta My Baby. Haka na ke ta dariya shima sai da na yi tagging ɗin shi. "Su Ya Muntari Hubby manyan ƙasa." Ya na online ya turo mini Emojin dariya kafin ya ce"Ke ko? Sadiya dai ta raina Yayan nan na ta ko? Emojin dariya na tura masa sai na jin kunya sannan na ce"Wace Sadiya ta raina Ya Muntari. Allah ya bar Ƙauna Hubbyn Rahila ta."   Ni kaɗai a ɗaki ina ta dariya ina tuna wani zamani a can baya har gobe ban manta lokacin da Ya Muntari ya zo gidanmu ba. Mama Allah ya jiƙan rai ta ce" Ya sunan ka ɗan samari." "Muntari. Muntari sunana Hajiya." Sai na ji wata dariya ta ƙara kamani har ina buga hannuna a saman cinyata, lokacin da Rahila suka fara soyayya da Ya Muntari ba wanda ya sani, wata rana kawai ya shigo gidan kowa na gaishe shi, da kuma sunan da muke kiran shi kenan  Ya Muntari. "Barka da dawowa Ya Muktar." "Yauwa Sannu Rahilatu." Sake baki na yi ganin yadda Rahila ta wani sunne kai tana dariya, shi ma ya na mata wani kallo. Ba zan manta ranar ba ina bakin famfo ina wanke wanke ita kuma tana bakin madafi ita da Ma'u suna gyaran wake.   Ga mamakin sunan da ta kira shi. Ga wani kallo da suke ma juna. Tun daga ranar fa Rahila, ta daina kiran shi Ya Muntari sai dai Ya Muktar har faɗa mun sha yi da ita, in na ce Ya

Chapter 10 of 31