Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saka?".


"What nonsense are you saying?, I am not blind I can see clearly without even my glasses, not wearing my glasses doesn't mean I can't see clearly, I know what am talking about, you guy's should believe me".


Ajiyan zuciya Daddy ya sauke sannan ya ce. "Ko za ki kai gobe kina faɗin abu ɗaya babu wanda zai yarda da ke. Bana son ki sake cewa kinga mai kama da Safeera na dai gaya miki". Yana kaiwa nan ya fice daga cikin ɗakin.


Zuwa daff da ita Safeera ta yi sannan ta ce. "Mom please take a rest, yanzu lokacin shan maganin ki ya yi, ya kamata ki sha maganin ki kinji, yanzu zan je nayi karatu ne gobe muna da exam a makaranta and i have to prepare well to pass this exam. For now am leaving okay Mom have your rest". Tana kaiwa nan ta miƙe tsaye tare da fice wa daga ɗakin.


Dafe kanta Mom ta yi a sa'inda ta fara magana ita kaɗai. "Ko dai da gaske gizau idona yake min ba mai kama da Safeera bace?, amma kuma fa na ganta sosai fa sanye da kayan magarƙama, tabbas babu tantama akwai mai kama da Safeera kuma saina tabbatar musu da hakan".


Tsayawa Aliyu ya yi yana mai nazarin kalamanta. Ƙarasawa in da take ya yi tare da ɗurƙusawa kan gwiwowinsa sannan ya dube ta ya ce. "Da gaske ne kinga mai kama da Safeera Mom?".


Kallonsa Mom ta yi sannan ta ce. "Au kenen kaima baka yarda da cewar na ga mai kama da Safeera ba a tv?".


Girgiza kai Aliyu ya yi sannan ya ce. "Me zai ana?, na yarda mana ɗari bisa ɗari, amma kuma ba kowa ne zai yarda da hakan ba. Domin nima kaina har yanzu ina tantamar cewa ba mai kama da Safeera ki ka gani ba. Amma shi ke nen babu komai na san abin da zan yi, domin sanin gaskiya dangane da abin da ki ka faɗa. Zan ɗauki photon Safeera sannan na tura wa jami'an da ke Nigeria muddin akwai mai kama da ita da gaske za su binciko ta. Don aka ki shafa wa zuciyarki ruwan sanyi".


Sai a lokacin Mom ta ji wani nutsuwa ya ziyarce ta. Kallon Aliyu ta yi sannan ta ce. "Na gode sosai Aliyu, tabbas babu wanda ya da ce ya auri Safeera sama da kai. Don aka zan faɗa wa Daddyn Safeera cewa mu koma Nigeria da zama, daga nan sai ayi auran ka da Safeera a chan".


Murmushi Aliyu ya yi sannan ya ce. "Shi ke nen, duda cewar ban iya tuna mai ya kawo ni nan ba amma gaskiya yarinyar ku ta burge ni sosai kuma ahalina za su yi farin cikin samu sirika irin Safeera".




*NIGERIA🇳🇬*
Government House.

Kunsan mutane goma na hango kan kujera a cikin parlourn wanda ke ƙunshe da kayan al'atu da kayan more rayuwa.

Zaune mahafin Umar wato Gov. Musa Muhammad yake kan kujerar three seater wanda aka yi amfani da royal furnitures wajan ƙera wa. Kallon engineers da architectures ɗin da ke zaune ya yi sannan ya ce.


"Me da me ake buƙata domin fara wannan aikin na company da za'a gina?, ka lissafo duk abin da ya kamata za'a yi".


Ɗaya daga cikin engineers ɗin ne ya dube shi ya ce. "Farko dai za'a bawa surveyors engineers domin duba kwalitin ƙasa ko fili ta yadda za'a san ginin zai zauna ko A'a, sannan za'a ɗebo ƙasar wajan a je a duba a laboratory domin sanin ginin zai zauna ko A'a".

"Bayan aka zamu fara auna tsare-tsaren gefen ta gine-gine ta ƙasa ko ta fili. Sannan architecture ya riga ya yi zanen yadda ginin company zai kasance.
Yanzu dai zamu ɗebo laburori su fara tonan tushen ginin, sannan a zo s fara tsarin ƙirar injiniya da tsarin lantarki. Sai ƙirƙirar sandar ƙarfe da ginshiƙai. Bayan nan sai mu zo muyi order na yashi mai kaifi, yashi mai laushi, yashin tsaƙuwa da siminti. Sannan ayi amfani da kankare ko rodi a cikin tushe. Bayan order wannan sai a zo a fitar da kewaye bango na gine-gine da rushewar sassan. bayan aka idan ya kai matakin doc za'a jefa dukkanin gishinƙai tare da kankare".

"Bayan nan zamu koma baya mu cika da latarite. Don za'a yi compactor don ƙaddamar da latarite. Bayan shi dpm ne ledder sa'an nan mu shirya hardcore saboda ya kwanta da wayar raga. Na ƙarshe kuma shi ne jefa gadon kankaren 6inch (dpc). Bayan hakan shi ke nen".


Ajiyan zuciya Gov. Musa Muhammad ya sauke!, sannan ya dube su ya ce. "Wannan bayanin sai ku engineers don ban fahimta ba sosai. Yanzu dai duka kuɗin da kuka yi calculating zaku faɗa min zan saka a ciki cashbook ɗina ko kuma ku faɗa nayi muku transfer, saboda ina so ne a fara aikin yau. Sannan kuma bana son Umar ya san da wannan batun. Wannan maganar ta tsaya a iya tsakanin mu kawai. Muddin na ji labarin cewa Umar ya san da za'a je dajin nan domin fara aiki saina ɓata muku rai, saboda gaba ɗaya mun san da cewa ba zai taɓa bari a je wannan dajin domin fara wannan aikin na company ba. Don aka You guy's should keep this as secret. Apart from you guy's I don't want you here that somebody heard our conversation".


Amsa wa gaba ɗaya suka yi da cewa. "Yes Sir. In sha Allahu wannan maganar ba zai fita ba. Bakin mu ƙanin ƙarfar mu. Yanzu dai ka sako mana jami'ai mu tafi tare domin koran waɗan nan namun jejin, ko a ɗebe su gaba ɗaya a wuce da su gidan zoo ko kuma idan ka bamu dama mu saka su kashe kowacce dabba ta cikin jejin kawai".


"Shi ke ne, kuyi dai abin da ku ka ga zai da ce. Kuje ku fara aune-aunen yau, idan ya so gobe zan saka a kawo yashi da blocks sannan zan tura laburori wajan ko kuma nayi muku transfer ɗin kuɗin komai da komai idan ya so sai kuyi aikin. Yanzu dai idan kun tafi ɗaya daga cikin ku ya yi calculating kuɗin everything da ake buƙata na aikin wannan company, in ya so saina yi muku transfer. Yau dai zan sama jami'ai su kori namun jejin gaba ɗaya. Idan ya so gobe kawai sai ku fara aikin". Cewar Gov.Musa Muhammad.


Miƙe wa gaba ɗaya engineers ɗin suka yi tare da yiwa Gov. Musa Muhammad godiya daga bisani suka fice daga cikin parlourn.




**************************
Ɓangaren Zahra kuwa tana shiga cikin kotun ta tarar da ƴan sanda tare da alkali a zazzau ne. Chan ta hango dan sandan da ya yi wa sambaɗe-baɗe daga nesa. Taɓe baki ta yi tare da bin kotun da kallo sannan ta ce. "Su ashe na harda shi a zuwa kotun, da an barni da kai da jikin ka ya faɗa maka". Maida kallonta ta yi cikin kotun ta ce. Dama aka kotun take?, ji fuskar alƙalin ma kamar tsohon biri, fuska tamkar kashi". Tsayawa ta yi in da masu laifi ke tsaya wa.


Tashi lawyer da ke kare ɗan sandan ya yi sannan ya ce. "Ina miƙo gaisuwata ga alƙali tare da mutanen da ke cikin kotun baki ɗaya. Muna nan ne gaba ɗaya domin maganar case na wannan budurwar da ta ɗauki hannu ta daki ɗan sanda wanda hakan a dokance bai kamata ba. A cewar sashe na 356 na dokar aikata laifuka, kai hari ga ɗan sanda babban laifi ne, kuma duk abubuwan da za'a bayyana domin kare ta zai ci-gaba da zama babban laifi ne. Don aka ina neman wannan kotu mai alfarma ta dubi halin da dan sandan nan ya shiga, ta hukunta wannan budurwar ta hanyar hukunta ta dai-dai da laifin da ta aikata".
Yana kaiwa nan lawyer ya zauna.


Maida kallonsa alƙalin kotun ya yi kan Zahra sannan ya ce. "A kan wane dalili ne ki ka ɗaga hannu ki ka daki ɗan sanda?".


Murmushi Zahra ta yi sannan ta ce. "Na dake shi ne domin ya zagar min mahaifiya, abin da kuma bana taɓa bari kenen".

Kallonta alƙalin ya yi sannan ya ce. "saboda ya zagar miki mahafiya shi ya sa za ki yi masa irin wannan dukan?".


Murmushi Zahra ta yi tana mai kallon ɗan sandan wanda ya cunkushe guri ɗaya yayin da fuskar sa ke zagaye da bandage. Maida kallonta ta yi kan alƙalin sannan ta ce. "Ƙwarai da gaske da a ce ma ba su zo sun kawo masa agaji ba a dai-dai wannan lokacin da saina yi masa dukan da har ya mutu sai ya dinga tuna wa dani".


"Wannan kuskure ne ki ka aikata, dukan ɗan sanda yayin da yake sanye cikin kayansa na ƴan sanda kuskure ne, ɗan sanda yana da damar dukan koma waye muddin ya yi masa laifi amma ke baki da damar yin akan, don aka abin da ki ka aikata kuskure ne".


Murmushi wanda ya fi kuka ciwo Zahra ta saki sannan ta ce. "Kuskure?, kenen kuskure ne don na tsaya domin kada a ci zarafin mahafiyata?, kuskure ne dukan ɗan sandan da bai san daraja da kima uwa ba?, kuskure ne dukan ɗan sandan da bai san aikin shi ba?. Wai shin tukun nan ma ka san wace ce uwa kuwa?, uwa ita ce ɗaukar ciki wata tara, shayar da yaro, ita ce malamar mu ta fark a duniya, sannan cinyarta shi ne wajan ɓatawan mu idan muka yi fitsri ko kashi. Ta raine mu, ta tarbiyartar damu, ta bamu kulawa wanda babu wanda zai iya mana. To a kan me zai sa ba zamu daraja ta ba?, idan abin da na aikata wa wannan ɗan sandan kuskure ne to shi ma abin da ya aikata kuskure ne. Don aka ni da shi masu laifi ne gaba ɗaya dole a hukunta mu ni da shi".


"Don ya kasance ɗan sanda akan bai bashi damar ya ci zarafin mace ba, ba uwa ta kaɗai ba, koda wata uwar ya sake zaga to saina tabbatar da na fasa masa baki".


Buɗe littafi Alƙali ya yi tare da yin rubuce rubucen sa a ciki. Ɗago da kansa alƙalin ya yi sannan ya ce. "Duba da yanayin abin da ki ka aikata sannan duba da kotu ta yi na cewa ke mace ce. Kotu za ta sassauta miki hukunci. Hukunci da wannan kotun ta yanke ita ce. Za'a kai wannan budurwar izuwa gidan gyaran hali da ke garin Kano zata zauna a chan na kimanin tsawon shekara guda tare da aiki babu sassauta. Wannan shi ne".


Zaro idanuwa waje Zahra ta yi sannan ta ce. "Shi kuma ɗan sandan fa?, ba za'a masa hukuncin ba kenan?". Kamata jami'ai mata suka yi tare da fitar da ita daga cikin kotun sannan suka sanya ta a cikin motan ƴan sanda tare da rufe motan. Shiga cikin motan DPO ya yi tare da kare wa Zahra kallo sannan ya ja dogon tsaki. Tayar da mota jami'ai suka yi tare da barin harabar kotun. Yayin da ƴan jarida da mutanen wajan suka bi motocin ƴan sandan da kallo.

Kai tsaye hanyar garin Kano suka nufa.

**************************
*Ɓangaren Daji kuwa*.


Bayan da jami'an Gov. Musa Muhammad sun shiga cikin jejin suka fara harbe duk wani dabban da suka yi kicibus da shi. Suna saka wa a cikin mota. Sosai suka fara kashe dabbobin cikin jejin yayin da babu abin da ke tashi a ciki daji sai ƙarar bindig. A sa'inda ɓangare guda dabbobin suka fara yi ta kansu.


Amrah da ke kwance kusa da dutsen da sunanta ke rubuce ta jiyo ƙaran bindiga da sauri ta miƙe tsaye, sannan ta fara gudu tana nufar in da suke jiyo ƙarar bindigu.



Zuwanta keda wuya ta ga an kashe gaba ki ɗaya namun jejin da ke cikin wannan dajin. Chakk ta tsaya yayin da hawaye suka fara zarya kan ƙuncin ta. Wani irin razananniyar ƙara ta saki! tare da buga tsalle ɗaya ta dira kan ɗaya daga cikin jami'an. Nan take ta fara kokawa da su . Yayin da ta sa hannayenta wanda ke ɗauke da zara-zaran farcina ta fara yagar su da shi.


Aka ta cigaba da yagar fatar jikin su babu gaggauta. Kururuwa ta yi tare da yin yin tsalle ta aye kan bishiya. Nan take ta janyo sandan dake jikin bishiyar mangwaron dake tsakiyar wajan.


Ɗaukar sandan ta yi wanda da matuƙar girma sannan ta dira ƙasa. A zafafe ta fara buga musu wannan sandan ɗaya bayan ɗaya tare da dukan su da shi. Nan take wasu daga cikin jami'an suka ja da baya ganin cewar tabbas idan suka ci gaba da tsayuwa zata hallakar da su.


Ɗaukar bindiga ɗaya daga cikin jami'an ya yi tare da saita saitin kafarta sannan ya harbe ta. Nan take ta faɗi ƙasa tare da sakin wata iriyar azababbiyar ƙara!.




*************************
"Hhhhhhh!, suka ji Zahra ta kurma wata iriyar ƙara mai matuƙar firgitarwa a cikin motan. Jikinta ne ya soma kakkarwa yayin da haƙoranta na sama ya fara dukan na ƙasa. Nan take zazzaɓi ya rufe ta yayin da jikinta ya soma rawan ɗari. Nan take ta faɗi a cikin motan sumammiya.


Mamaki ne ya kama jami'ai da DPO da ke cikin motan ganin lokaci ɗaya ta kurma ihuu tamkar mai aljanu.


*******
Ɓangaren Safeera kuwa suna zaune a parlour suka ga ta faɗi tare da sakin azababbiyar ƙara!.

Zumbur gaba ɗaya suka miƙe tare da nufar kanta da sauri. Nan take suka ga ta dafa kanta yayin da zazzaɓi ya rufe ta shure-shure ta fara yi hannunta dafe da cikin ta. Nan take suka ga ta daina yin shure-shuren.


Zuwa kusa da ita Aliyu ya yi tare da saka hannunsa saitin hancin ta. Ganin bata numfashi ya da shi saurin ɗago da kansa sannan ya ce. "Safeera fa ta suma".


"Suma kuma?". Cewar Mom. Sannan ta ƙara da cewa. "Wai me yake faruwa ne?".







*TOH FAN'S 💃💃NI MA DAI ZANCE ME YAKE FARUWA NE🤔?, DAGA HARBIN AMRAH GABA ƊAYA SAURAN BIYUN SUN FITA A HAYYACIN SU, KODAI AKWAI ABIN DA KE FARUWA NE🤔?, MUJE DAI ZUWA*.

*KUYI MANAGE NA PAGE ƊIN NAN BANI DA CHARGE NE SANNAN KUMA BANA JIN DAƊI SOSAI. NA SO NAYI MUKU FIYE DA AKA AMMA KUYI MANAGE*

LIKE, SHARE, AND COMMENTS PLEASE 🙏🙏🙏


ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar Jajirtattu)


🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐.
Daji 🌲
Magarƙama🏢 da kuma
Birni🏙️

WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝♀️Jajirtattu)

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 1️⃣9️⃣▶️2️⃣0️⃣
*_________________________________________________*
Mom ta faɗa damuwa bayyane kan fuskarta yayin da ta riƙe Safeera ƙamm jikinta.

"Wallahi Allah masani, hanya yarinyar nan ba ta da aljanu kuwa?". Aliyu ya faɗa.

Kallonsa Daddy ya yi ya ce. "Gaskiya bana tunanin tana da aljanu saboda a wannan ƙasar babu aljanu balle maye, kuma ba ta taɓa zuwa Nigeria ba balle na ce a chan ta ɗebo aljanu".

Kallon baka da hankali Aliyu ya bishi da shi sannan ya ce. "Okay wato a iya Nigeria ne kaɗai ake samun aljanu ko?, gaskiya Daddy ya kamata ka koma islamiyya ko ka dinga shiga YouTube ko chrome kana koyan abubuwan da ya daganci addinin musulunci, don naga kamar har yanzu da sauran ka".

Kallonsa Daddy ya yi sannan ya ce. "Na je islamiyya mana kuma har ma nayi sauka sai dai ba'a ƙasar Nigeria na ta so ba a wannan ƙasar America na ta so".

Kallonsu gaba ɗaya Mom ta yi ta ce. "Yanzu ba irin wannan magana ya kamata kuyi ba yanzu, ya kamata a ce ku san abin yi domin ta farfaɗo, tun ɗazu nake jijjigata har yanzu ba ta numfashi. Dan Allah ku taimaka bana son na rasa ƴata ɗaya tilo".

Kallonta Aliyu ya yi cikin tausayawa ya ce. "Na fahimci yadda ki ke ji Mom, yanzu mafita ɗaya muke da shi, dole ne muje Nigeria domin yi mata maganin gargajiya. Idan muka ce zamu yi a nan sanadin hakan ƴan sanda za su iya kama mu, domin za su ɗauka cutar da ita zamu yi hakan na iya sawa su kai mu magarƙama ma. Yanzu mafita ɗaya ce shi ne muje Nigeria domin wannan maganin gargajiya ne kawai zai yi aiki.

Kallonsa Daddy ya yi ya ce. "maganin gargajiya kuma?, gaskiya ba za'a bawa ƴata irin wannan ƙazaman maganin ba, saboda ni duk ban yarda da ire-iren waɗan nan magungunan ba".

Girgiza kai Aliyu ya yi sannan ya ce. "Ko ka yarda ko karka yarda dole ne muje Nigeria domin yi mata maganin, in ba aka ba za ku rasa ta".

Jin an ambato batun za'a rasa ta, ya sanya Mom ta miƙe zumbur tare da nufa part ɗin ta. Saida ta ɗau lokaci kafin ta fito daga cikin ɗakin ta. Fitowa ta yi sanye da hijabi yayin da hijabi ɗaya na hannunta. Ƙarasowa wajan ta yi tare da ɗurƙusawa ta sanya wa Safeera hijabin a jikin ta".

Miƙe wa ta yi tsaye sannan ta ce. "Yanzu me ya rage, maza ku shirya mu tafi".

Kallonta Aliyu ya yi ya ce. "Ai kuma bamu haɗa kayayyakin da zamu tafi Nigeria da su ba".

Kallonsa Daddy ya yi ya ce. "Kada ka damu da wannan zan saka ƴan aiki na su aiko mana su".

"Amma ka san da cewa bamu da visa, kuma kuɗaɗe basua aiki a wannan ƙasar domin idan ka ce za ka basu kuɗi za su kama mutum ne, sannan kuma ta ya ya zamu je filin jirgi da ita a haka?, domin fa kwata-kwata ba ta numfashi, ba kayi tunanin cewa ƴan sanda za su yi zargin cewa ko sace ta muka yi. Yanzu dai dole ne muna iya ba da shaida takardun aure, takaddun Haihuwar Ma'aurata da masu dogara, hotunan da ke nuna kyakkyawar alaƙa da dangi da abokai". Cewar Aliyu.

Kallon Daddy Mom ta yi sannan ta ce. "Yanzu mene ne abin yi?". Ta tambayi Daddy.

Amsa Daddy ya ba ta da cewa. "Ina da aboki ɗan sanda a chan airport sannan kuma ina da wani ma wanda na san idan na roƙe shi zai bamu visa tun da gaba ɗaya muna da password. Yanzu kawai abin da zamu yi muje chan ɗin, na san da cewa idan suka ganta za su gane ta domin sun san ta sosai ko a cikin office ɗina suna zuwa su ga photon ta a ajiye kan table, so za su gane
cewar ƴata ce".

"Tom shi ke nen, yanzu waye zai ɗauke ta?". Mom ta tambaya.

Amsa Aliyu ya bata da cewa. "Kada ki damu, ni zan ɗauke ta". Yana kaiwa nan ya shiga cikin room ɗin sa. Saida ya ɗau kusan rabin hour bai fito ba, sannan daga bisani ya fito cikin ƙananun kaya wanda suka yi matuƙar karɓar jikin sa. Nufar in da suke ya yi sannan ya sa hannu tare da ɗaukar Safeera sannan ya yi hanyar waje da ita.

Ganin hakan ya sa su Daddy suka mara masa baya bayan sun ɗauki muƙulli.

Kai tsaye in da motocin gidan suke Aliyu ya nufa. Danna muƙullin motan Daddy ya yi. Nan take motar ta buɗe da kanta.

Ganin hakan ya sa Aliyu saka Safeera cikin motan yayin da gaba ɗaya su Daddy suma suka shiga cikin motar. Tada motar Aliyu ya yi. Yayin da gate man ya buɗe musi ƙofa daga bisani suka fice daga cikin gidan baki ɗaya.

Basu nufi ko ina ba sai hanyar airport.

************************
*Nigeria*

"Mene ne ka aikata haka officer?, me ya sa za ka harbi yarinyar nan bayan da cewa Gov. Musa Muhammad ya ce baya son ɗansa ya san da cewa munzo mun kori dabbobin da ke cikin daji nan".

Officer da haka faɗa wa hakan ya ce. "To baka ga yadda take tsalle kan bishiyoyi ba kamar biri, na san ba zamu iya kamata ba idan muka ce zamu kamata za ta illatar da mu ne. Bani da wani zaɓin ne shi ya sa na harbe ta a ƙafa".

"Wannan laifin ka ne, yanzu idan Sir Umar ya sani na san tamu ta ƙare".

Wayarsa ya ji tana ringing. Ɗauko wayar ya yi daga cikin aljihun sa sannan ya ɗaga kiran tare da karawa a kunnen sa ya ce. "Hello".

Daga ɗayan ɓangaren haka ce. "Maza-maza ka ce da sauran jami'an wajan nan su bar wajan, domin kuwa Sir Umar ya nufo hanyar wajan yanzu".

Zari ido jami'in ya yi tare da katse wayar sannan ya kalli sauran jami'an ya ce. "An kira yanzu an ce mu bar nan domin sir Umar yana tawo wa nan".

Da sauri suka matsar da Amrah wanda ke yashe kafarta sai fidda jini yake gefe. Sannan cikin ƙware wa suka fara shiga cikin motocin. Tare da tada mota suka bar harabar wajan.

Bai ɗauki Umar lokaci ba ya ƙaraso wajan. Guri ya samu a cikin dajin sannan ya yi parking.

Fitowa ya yi ciki cikin izza. Sannan ya rufe ƙofar motan. Dafe zuciyarsa ya yi ciki ranshi ya ce. "ban san dalilin da ya sa zuciyata take ta buga wa da ƙarfi-ƙarfi ba, amma yanzu tun da na zo , na san hankali na zai kwanta". Ya faɗa tare da fara tafiya.

Sai da ya yi tafiya mai nisan gaske kafin ya isa wajan kogin dake cikin dajin. Tsayawa ya yi jin yadda dajin ya ɗauki shiru. Mamaki ne ya kama shi jin babu ko da kururwan wani dabba a cikin dajin sai dai tsuntsaye wanda suke ta kai kawo a sama.

Ƙatasawa in da kogin yake ya yi. Take idanuwansa ya sauka a kan dutsen da ke kusa da kogin. Daff da dutsen ya je ganin kamar abi rubuce a jiki.

Durƙusawa ya yi tare da shafa sunan dake jikin dutsen ya yi. Murmushi ya yi sannan ya ce. "Kenen sunanta Amrah, nice name".

Miƙe wa ya yi tsaye sannan ya bar wajan.

Tafiya ya soma yi yayin da ya fara arangama da dabbobin da ke yashe a ƙasa.

Mamaki ne ya kama shi ganin dabbobin da ke daji yashe a ƙasa cikin jini.

Daga nesa ya hangi Amrah dake kwance kusa da jikin bishiya. Zaro idanuwa ya yi waje yayin da ya tafi da gudu tare isa in da take.

Yana zuwa ya durƙusawa tare da aza kanta a kan cinyarsa. Tattaɓa fuskar ta ya soma yi. "Amrah me ya sa me ki?, wane ne ya yi miki haka?". Ɗaukar ta ya yi chakk tare da nufar in da motar shi yake da ita.

Saka ta ya yi cikin mota sannan shima ya shiga tare da tuƙa motan sannan ya bar harabar wajan.
Kai tsaye asibiti ya nufa da Amrah.

****************
Ɓangaren su Zahra kuwa suna isa Kano basu nufi ko ina ba sai asibiti suka nufa. Nan take nurse's suka saka ta a gadon marasa lafiya tare da shigar da ita cikin ɗaki. Nan take suka fara mata aiki ta yadda numfashinta zai dawo. Saka mata oxygen suka yi tare da bata allura.

Cikin ƙanƙanin lokaci numfashinta ya dawo.
Allurar bacci suka bata tasha ta yi bacci.

Fita likitocin suka yi suka bar Zahra kaɗai a ɗakin.
Miƙe wa DPO ya yi sannan ya dubi ɗaya daga cikin likitocin ya ce. "Me yake faruwa ne?, ya jikin nata?".

Amsa likitan ya ba shi da cewa. "Lafiya ƙalau munyi nasaran cetan ta domin kuwa yanzu harta samu bacci. Hamdala DPO ya yi sannan ya ce. "Yanzu zamu iya shiga mu ganta?".

"Eh za ku iya, amma dan Allah banda hayaniya". Yana kaiwa nan ya bar wajan.

Shiga ciki gaba ki ɗaya suka yi, yayin da suka tarar ba ta kan gadon. Zaro ido gaba ɗaya suka yi ganin ba ta kan gadon. Kallon jami'an DPO ya yi ya ce. "Me ya sa muka yi sakaci har ta fece daga nan".

Daga sana suka ji muryarta na cewa. "Yallaɓai DPO gani fa a ta nan". Zahra ta faɗa tana mai sakin murmushi.

Kallon ko ina suka yi basu ganta ba. Nan take suka maida kansu kan gado.

Kallonta DPO ya yi ya ce. "Ta ya ya kuma ki ka dawo kan gado bayan bakya nan?".

Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Ta ya kuma, kune dai baku duba ba da kyau amma ni dai ina nan banje ko ina ba".

Ajiyan zuciya DPO ya sauke sannan ya ce.

Please Login or Register in order to submit comment