Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce. "Yanzu ba lokacin magana bane, mu fara kaita gida in yaso gobe mu kaita police station ko gidan radio domin bincikar inda iyayenta suke".

Karɓe jaririyar matar ta yi sannan ta ce. "A'a, ba bu inda za'a kaita, zata zauna tare da mu har tsawon ƙarshen rayuwar ta, me ya sa iyayenta zasu watsar da ita su barta a cikin wannan mawuyacin hali. Yanzu da a ce bamu zo ba da wuri da tuni ta rasa rayuwarta saboda rashin iska. Tun da har waɗan da suka haife ta basua sonta ni ina sonta kuma zan riƙe ta tamkar ƴar cikina, ina sonta kuma ina ƙaunar ta. Don haka kamar yadda ka faɗa next week zamu bar ƙasar nan baki ɗaya domin muje mu gina sabuwar rayuwa tare da yarinyar mu". Ta faɗa tana mai rungume jaririyar kan kirjinta.








*BAYAN SHEKARU*.
*GOMA*
Kwance take kan bench na ajin, yayin da ayaniyar yara ya cika ajin baki ɗaya.

Ɗago da rinannun brown eyes ɗinta ta yi, tare da ɗora wa kan yaran dake ta faman wasa a cikin ajin.

A hankali ta ɗago da fuskarta gaba ɗaya. Masha Allah baki na ya iya furta wa lokacin da nayi gamo da cute and pretty face ɗin ta mai matuƙar kyau. Lumshe idanuwanta ta yi wanda suka kunkumbura saboda kuka sannan ta buɗe su baki ɗaya.


Miƙe wa tsaye ta yi tare da nufar inda sauran ɗalibai na ajin suke. Suna ganin ta iso wajan su, gaba ɗaya suka yi saurin barin wajan.

Kallonsu ta yi cikin shesheƙar kuka ta ce. "Wai me ya sa a koda yaushe ku ke gudu na idan ba tunkari inda ku ke?, ban san mena yi muku ba, nima ina son kasancewa tare da ku, ina son na yi wasa sannan muyi karatu tare, bana jin daɗin zama ni kaɗai a cikin wannan makarantar". Ta faɗa tana mai fashe wa da kuka.


Kallonta ɗaya daga cikin yaran ya yi sannan ya ce. "Kinga Zahra Mu ba zamu iya zama da ƴar magarƙama ba, an ce Mamanki sheɗaniya ce tana kashe yara, kuma kema a cikin magarƙama ki ka taso, yayin da ita kanta wacce ta riƙe ki ƴar magarƙama ce. An ce gaba ɗaya ahalin ki rabuwa suka yi dake saboda ba zasu iya riƙe ki ba. muma kuma ba zamu iya zama ko muyi tarayya dake ba, saboda muma kada muje ki kashe mu".

Wata a cikin ɗaliban ce ta ce. "Nima mahaifiyata ta faɗa min cewa kada na kuskure na haɗa ƙawance dake ko na zauna dake. In ba haka ba zata dake ni. Don haka dan Allah ki rabu damu, mu ba zamu zauna da ƴar makashiya ba".

Kallonsu Zahra ta yi sannan ta ce. "Ƙarya ku ke, Mamata ba muguwa bace ba, Idan ku ka ƙara cewa Mamata wai muguwa ce, saina kai ƙarar ku wajan shugaban makaranta.

Ɗaukar jakarta ɗaliban suka yi tare da jefa mata a jiki.


Hana haka malami ya shigo cikin ajin. Nan take kowanensu ya koma wajen zamansa. Banda Zahra wanda ke a tsaye sai faman kuka take.

Kallonta malamin ya yi sannan ya ce. "Zahra me haka yi miki ki ke kuka?".


Kallonsa ta yi cikin shesheƙar kuka ta ce. "Malam zagin Mama ta suke yi, kuma wai suna ce min ƴar magarƙama".


Taɓe baki malamin ya yi sannan ya ce. "To ai da gaskiyar su, in da mahafiyar ki mutumiyar kirki ce bata damfari al'umma ba da ba za'a dinga yi miki wannan kallon banzan ba, don haka duk abin da haka yi miki to ki ƙaddara cewa Mamar ki ce ta jawo miki. Dani ne ma shugaban makarantar nan da ba zan karɓe ki a makarantar nan ba wallahi".

Durƙusawa Zahra ta yi kan gwiwowinta tana mai fashe wa da kuka. Nan take ɗaliban ajin suka fara mata dariya, tare da fara tsokanarta, yayin da suka fara jifarta da littafi.

Miƙe wa ta yi da sauri sannan ta fice daga cikin ajin. Nufar inda warders wanda ke mata rakiya izuwa makarantar ta yi, yayin da ta kalle su sannan ta ce. "Ina son ku maida ni gida yanzu nan". Ta faɗa tare da shige wa cikin mota.

Kamar yadda ta faɗa haka suka ja mota suka bar harabar wajan. Bai fi lokaci ƙalilan ba, suka isa cikin magarƙama.

Fitowa ta yi daga cikin mota tare da rugawa a guje ta nufo inda Hajiya Binta ke da zama.

Binta da kallo mutanen dake cikin magarƙamar suka yi, ganin yadda idanuwanta suka kunkumbura ya sa hankalin kowanensu ya tashi, Da sauri sauran mutanen dake cikin magarƙamar suka nufi inda take.

Shiga cikin ɗakin da Hajiya Binta take ta yi. Tana mai fuskantarta ta ce. "Shin laifi ne dan na kasance ƴar magarƙama?, kowane yaro farin ciki yake, amma ni a koda yaushe ba bu abin da nake fuskanta sai baƙin ciki da ƙyama. Kuma na san duk abubuwan nan na faruwa ne saboda Mamata, da a ce bata tafi ta barni ba, da hakan ba zata faru ba. Na tsane ta, bana sonta, me ya sa da zata tafi bata kashe ni ba?, amma ta barni cikin kaɗai ci". Ta ƙarashe maganar tare da fashe wa da kuka.


Da sauri Hajiya Binta ta isa gare ta tare da rungume ta . "A'a ƴata, mahafiyar ki ba muguwa bace, bada son ranta ta tafi ta barki ba. Mamanki tana sonki sosai, kuma karki damu, nan gaba mutane za su daina tsokanarki kuma su daina gudunki kunji".

"Shi kenen Aunty, kiyi min alƙawarin cewa za su daina tsokana ta".

Murmushi Hajiya Binta ta yi sannan ta ce. "Nayi miki alƙawarin cewa ba bu wanda zai ƙara tsokanarki Zahra".

Murmushi jin daɗi Zahra ta yi sannan ta miƙe tsaye tare da fice wa waje domin yin wasa.




*BAYAN WASU SHEKARU GOMA*

*AMERICA*
Ba bu abin da ke tashi a cikin mashayar nan in banda haka. Yayin da ba bu abin da ka ke gani sai mata da maza, yayin da matan ke sanye da ɗingilallen skirt da shi gwanda ba bu. Chan na hangi wata matashiyar budurwa wacce ba zata wuce shekaru ashirin ba a duniya sai tiƙan rawa take yi. Yayin da gaba ɗaya turawan wajan idanuwansu a kanta.

Ɗaya daga cikin mutanen wajan ne naji ya ce. "Diana".
Juyowa ta yi tare da baje gashin ta, masha Allah na furta lokacin da nayi kicibus da haɗaddiyar fuskantar wanda ke ɗauke da light makeup.

Kallonsa ta yi cikin cool voice ɗinta ta ce da shi. "How are you John?". Ta faɗa da yaren turanci na ƴan ƙasar America.


Amsa wa John ya yi da cewa. "Am good baby". Ya faɗa yana mai ƙoƙarin shafa jikinta. Nan take budurwar ta ɗago da blue eyes ɗin ta tare da ɗaga hannunta ta kwashe shi da mari.


Nan take mai Dj ya kashe waƙar dake tashi, yayin da gaba ɗaya idanuwan jama'ar wajan ya karkata izuwa kansu. Nuna shi ta yi da ɗan yatsarta cikin ɓacin rai ta ce. "How dare you John?, are you mad or something?. Idan har ka ƙara yi min wannan shashanci saina yi maka abin da yafi hakan". Diana ta ƙarashe maganar tare da ɗaukar car key ɗin ta sannan ta fita daga cikin club ɗin.


Da sauri ƙawayenta suka bi bayanta.

Nausar iska John ya yi yayin da ɗayan hannunshi ke dafe da ƙuncin shi.

"Diana! Diana! Diana". Haka ƙawayenta suka shiga ƙwalla kiran sunanta, amma ko juyowa bata yi ba ta saurare su, haka ta shige cikin mota tare da jan motan ta bar harabar wajan.


Girgiza kai ƙawayenta suka yi yayin da suka koma cikin club ɗin.


Tafiya mai nisa ta yi kafin daga bisani ta isa gida. Parking ta yi tare da fitowa daga cikin mota. Ta fara takawa da takalmin ta mai tsini ji ka ke ƙwass! Ƙwas! Ƙwass.


Shiga cikin faɗeɗen palourn su ta yi a tsorace. Cire takalman ƙafarta ta yi sannan ta fara sanɗa tana tafiya. Saida taje daff da zata hau kan upstairs ta ji muryar mahaifiyarta.

Da gudu ta haye kan upstairs tare da shige wa cikin ɗakin ta.



*NIGEIRA*.
"Wannan wane irin shirme ne Aliyu?, sama da yara amsin nasa haka yi safaransu izuwa kasashen waje, amma yanzu sai kace min wai wani ɓoyayyen jami'i ya sake su sun tafi, ta ya ya hakan zata faru?. Nafi sama da shekaru talatin ina wannan aikin nawa a ɓoye, kuma yanzu rana tsaka kace min wai yaran da na aika duk jami'ai sun karɓe su sannan suka mai da su gidajen su. Kasan dai wannan abun zai iya taɓa siyasa ta ko? Gashi zaɓe ya kusa, idan har mutane suka gane abin da nake aikata wa ta ya ya za su yarda su zaɓe ni a matsayin govnor. Ya zama dole kasa a rufe wannan abun, in ba haka ba saina sa an ɓatar min da kai daga cikin wannan duniya.


Ɗago da fararen isanuwansa masu kyau da ɗaukar ido ya yi yayin da ya furzar da iska mai zafi waje cikin jin haushi da takaicin abin da ɗan majalisan yake aikata wa ya dube shi ya ce. "Kada ka damu yallaɓai, ko ta halin ƙaƙa ba zan bari komai ya fita ba, nayi maka alƙawarin hakan. Yanzu zanje na samu Mk ne a magarƙama. Na san yana da cikakken bayani game da wanda ya kunce yaran. Mundin ya faɗa min, in sha Allahu zan zo na sanar da kai". Yana kaiwa nan ya fice daga cikin office ɗin ƴan majalisa yayin da ya nufi inda motarsa take kai tsaye. Shiga cikin motan ya yi tare da jan motan ya nufi hanyar magarƙama.


Isarsa magarƙama keda wuya, ya tarar da wasu mata suna buga ƙwallon ƙafa.

Tafiya ya soma yi yayin da jami'ai suka tare shi. Nan take ya nuna musu ID card ɗin sa. Ganin shima jami'i ne ya sa suka barsa ya shiga.


Sanye matashiyar take da kayan magarƙama yayin da take sarrafa ƙwallon cikin ƙware wa, a yayin da fuskarta ke ɗauke da farin ciki da annashuwa. Buga ball ɗin ta yi da ƙafarta na dama. Cikin rashin sa'a kuwa ball ɗin ya bugi Aliyu.

Zaro idanuwa gaba ɗaya mutanen wajan suka yi tare da bin budurwar da Aliyu da kallo.

Cike da ɓacin rai Aliyu ya ɗaga dara-daran idanuwansa tare da ɗora wa a kan ball ɗin. Cikin ɓacin rai ya ce. "Wace banzar ce ta cilla min ball a jiki?".


Amsa wa budurwar ta yi da cewa. "Nice nan na wurgo ball ɗin". Ta faɗa tana mai juyo da kyakkyawar fuskarta.





💃💃💃💃💃💃💃💃💃
MANAGE PAGE
COMMENTS & SHARE FISABILULLAHI 🥰🙏🥰

ALƘALAMIN ✍️
AISHA M.B💞💞💞
(Zinariyar Jajirtattu)

Follow the 💖 A'ISHA M.B✍️ HAUSA NOVELS 📚 WORLD 🌎 📚💗💖 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g

*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐.
Daji 🌲
Magarƙama🏢 da kuma
Birni🏙️

WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝♀️Jajirtattu)


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 1️⃣1️⃣⏩1️⃣2️⃣
*_________________________________________________*
Sakar baki Aliyu ya yi yana kallonta, yayin da ya rasa me ke mai daɗi.


Ganin kamar ma baya cikin hankalinsa ya sa Zahra faɗin. "Kai malam miƙo min ball ɗin nan".


Kallon kanshi Aliyu ya yi sannan ya mai da kallonsa kan Zahra ya ce. "Kina da hankali kuwa?, kin wurgo min ball maimakon ki bani haƙuri shi ne za ki ce na wani miƙo miki ball. Kin san kuwa ko ni wane ne".


Murmushi Zahra ta yi tare da nufar inda yake a tsaye. Kallon shi ta yi ido cikin ido ba bu tsoro balle fargaba sannan ta ce.


"Ba bu ruwa na da ko kai wane ne, nan yanki na ne kuma gida na, kuma cikin ta ka shigo, sai abin da nace hake yi. Don haka ka ajiye duk izzan da ka ke takama da shi ka watsar a gefe, don ba za ta amfane ka da komai ba a nan wajan".


Ɗaukar ball ɗin Aliyu ya yi sannan ya ce. "Dame ki ke takama?, waya tsaya miki a cikin magarƙamar nan da har ki ka samu ƙwarin gwiwar faɗa wa ɗan sanda maganganun nan?".


Dariya Zahra ta kwashe da shi sannan ta ce. "Dan sanda?, wai kai nan ɗan sanda ne ko?, kuma ka ke tunanin naji tsoron ka?, a kan me ma zan ji tsoron ɗan sanda?. To ka saurare ni kaji ni ƴan sanda su suke min ma bauta ƙarewanta".

Haɗe ransa Aliyu ya yi sannan ya ce. "Kada kiyi tunanin zaki ci mutuncin aiki da kuma kaki na, ƙarya ne ƴan sanda su yi wa mai laifi wacce ke zaune cikin magarƙama bauta. In kuma da gaske ki ke nuna min evidence".


Girgiza kai Zahra ta yi sannan ta ce. "To shi shi ke nen yanzu za ka ga aiki da cikawa". Ta faɗa tare da juya bayanta sannan ta fara ƙwalla kiran jami'an dake cikin magarƙama. Kafin ƙiftawan ido gaba ɗaya suka hallara a wajan.


Maida kallonta Zahra ta yi kan Aliyu sannan ta ce. "Wane evidence ka ke buƙata kuma bayan wannan?. Ka sani cewa waɗan nan da ka ke gani sune suke kaini makaranta, su kaini siyayya, su suturta ni sannan su bani abinci a baki, kuma duk abin da na umarce su suyi nan take za su aiwatar. Domin DPO ɗin ku shi ne ya ɗauki gaba ki ɗaya nauyin karatu na har da ma waɗan nan jami'an. To faɗa min a kan me zanji tsoron ka bayan ni a cikin jami'an ma na taso?".


Girgiza kai Aliyu ya yi sannan ya ce. "Perfect, amma sai dai ni hakan samm bata yi min daɗi ba, domin bai kamata a ce jami'ai suna yiwa mai laifi bauta ba, nayi Allah wadai da ku jami'ai. Irin kune ɓata gari a dinga tunanin cewar haka gaba ɗaya jami'ai suka taru suka zama ɗaya. Sai dai ni nawa aikin ya bambanta domin bana ɗaukar shashanci". Ya faɗa tare da ajiye ball ɗin a ƙasa sannan ya sa ƙafarsa ta dama ya taka ta. Nan take ball ɗin ta fashe.


Ganin ta fashe ya sa shi sakin murmushi sannan ya ce. "Na fasa ball ɗin kiyi duk abin da ki ke ganin za ki iya, maza kije ki kira koma wane, ko uwarki bata isa ta yi min komai ba".


Nan take ran Zahra ya ɓaci yayin da brown eyes ɗin ta suka ƙara rinewa sosai. "Ni zaka fasawa ball?, har kai waye da za ka faɗi magana hakan mahaifiyata?". Ta faɗa yayin da ta juya tare da mai da kallon ta kan jami'an wajan sannan ta yi musu nuni da su rufe ƙofar magarƙamar. Kamar yadda ta buƙata haka suka rufe ƙofar magarƙamar tare da datse wa da kwaɗo.

Juya wa ta yi tare da kallon sa cikin hassala ta ce. "Me ya sa zaka sako uwata a cikin maganar ka?, shin kai baka martaba iyaye ne?, tun ds har ka kuskura kayi magana a kan mahaifiyata sai na yi maka abin da ko da so ɗaya ba zaka kuma ƙoƙarin zuwa magarƙamar nan yin investigation ba".

Maida kallonta ta yi kan matan cikin magarƙamar. Nan take suka fuskanci abin da take nufi. Nan da nan gaba ki ɗaya suka zagaye Aliyu yayinda suka ririƙe hannayensu tare da yin circle.



*. DAJI🌲🌳*
(🦍🦧🐅🐘🐒🐈⬛🐂)
*_______________________*
Gudu take tamkar barewa tana mai aye wa kan manya-manyan bishiyun dake cikin jejin tamkar ƴar biri, yayin da take tsalle gashin kanta na tashi sama, hakan bai bani damar ganin fuskarta sosai ba. Riƙe hannunta yake da wani ɗan ƙaramin biri. Yayin da gefe guda namun jeji ke mara mata baya.

Nan take ta dira a ƙasa tare da baza gashin ta. Masha Allah na iya furta wa lokacin da nayi kicibus da kyakyawar fuskarta wanda ke lulluɓe da farin ciki da annashuwa. Sanye take ciki kaya wanda alamun birrurukan ne suka yi mata, domin gaba ɗaya kayan anyi amfani da ganyayyaki wajan sa ƙashi ne.lumshe green eyes ɗinta ta yi tana mai mai da kallonta kan namun jejin sannan ta musu ciki yaren ko ni kaina ban sani ba".


Nan da nan suka girgiza kai gaba ɗaya tare da watse wa . Yayin da birrurukan suka fara aye wa kan bishiyu suna ɗiban fruits ɗin da ke kai wato kayan marmari.


Ganin gaba ɗaya sun watse ya sata sakin murmushi, sannan ta yi wani irin tsalle. Nan take ta dira a kusa da wani jibgegen dutse wanda ke zaman kansa a cikin dajin.


Ajiyan zuciya ta sauke Tare da nufar katoton ruwan dake cikin dajin. Sannan ta shige ciki. Nan take ta fara wanka. Ganin hakan ya sanya birrirukan suka fara saukowa daga kan bishiyu, sannan suka ɗauki ganyayyaki suka tunkari inda take.


Nan take suka zagaye ta da ganyayyakin tare da kare ta dasu.


Sai da ta gama wankan sannan ta fito daga cikin ruwan. Fitowa ta yi ta ga sun zagaye ta da ganyayyaki sannan sun shirya mata kaya na ganyayyaki wanda zata saka.


Murmushi ta sakar musu wanda ya sanya dimple ɗin ta ƙara lotsawa.
Cikin yaren su na birirruka ta ce. "Na gode sosai ƴan uwana, ina matuƙar alfahari da ku, ina sonku sosai soyayya mara misaltuwa". Ta faɗa tare da janyi kayan ganyen da suka ajiye sannan ta saka.

Fitowa ta yi daga cikin ruwan. Ganin ta sanya kaya ya saka suka ajiye ganyen da suka zagaye ta da shi.


Tafiya ta fara yi tare da nufar inda dutse dake gabanta yake. Sai da ta ƙarasa wajan sannan ta zauna tare da jingina a jikin dutsen. Shafa jikin dutsen ta fara yi tana mai shafa sunan Amrah dake rubuce a jiki.


Nan take fuskanta ya chanza daga walwalah izuwa damuwa. ganin kamar tana ƙoƙarin shiga cikin damuwa ya sa su birrirukan suka tunkaro inda take yayin da suma sauran namun jejin suka nufo inda take. Nan da nan gwagon biri ya ɗauke ta chakk tare da cilla ta sama. Nan take farin ciki ya lulluɓe fuskar Amrah. Nan da nan suka shiga yin wasa abun gwanin burgewa. Ajiye ta gwagon birin ya yi tare da ajiye Amrah a kan wata ƙaramar giwa, nan take giwar ta fara tafiya da ita tare da yawa ta da ita yayin da sauran namun jejin ke mara musu baya.





*AMERICA*
"What is wrong with you Safeera?, wannan ba tarbiyyar da na baki bane ba, me ya sa za ki dinga zuwa club for God sake?, sunanki Safeera amma kin mai da sunanki Diana saboda bakya jin tsoron duk abin da zai je ya dawo ko?". Matar ta ƙarashe maganar ranta a matuƙar ɓace.


Miƙe wa zaune wacce haka kira Safeera ta yi sannan ta dubi mahaifiyartata cikin shagwaɓa ta ce. "Am sorry Mom, wallahi zan daina zuwa club sannan na daina saka waɗan nan matsatsun kayan kinji. Banason ina gani kina shiga damuwa saboda ni , i promise you that I will change, kuma sunan Diana ƙawaye na ne suka saka min a makaranta, amma zan ce kar su ƙara kira na da sunan kinji". Cewar Safeera.

Murmushi Mom ta sakar mata sannan ta ce. "Don't forget that promise is a debt".

Miƙe wa tsaye ta yi tare da nufar inda take sannan ta zaunar da Mom ɗin tata ta ce. "Yes Mom, I promise I will never hurt you again because I love you so much Mom".

Rungume ta matar ta yi sannan ta ce. "That's my baby I love you more than you do".

Jin shigowar mutum ya sa su miƙe wa tsaye tare da maida kallonsu inda suke jin takun mutum.

Washe baki Safeera ta yi yayin da ta tafi da gudu tare da rungume shi.

"Welcome back daddy, I really missed you". Ɓanɓare ta daga jikinsa mutumin ya yi sannan ya dube ta ya ce. "Oh my cute baby, wai yaushe za ki girma ne?, so ki ke ki ɓalla ni, ji fa yadda ki ka tawo ki ka rungume ni".


Murguɗa baki Safeera ta yi sannan ta ce. "idan ka karye ai sai na fi kowa shiga damuwa". Ta faɗa tana mai kwashe wa da dariya.


"Shi ke nen tom naji, wai ina Mom ɗin ki take ne?, ta zo fa na dawo mata da good news". Cewar Daddy.

Daga bayansa yaji ta ce. "Ai gani nan my one, ba saika neme ni ba". Cewar Mom.

Da sauri yaje tare da rungume matar ta shi sanann ya ce. "Na tawo miki da good news, maza ku zauna".

Zama suka yi suna mai fuskantarsa. Kallon su ya yi sannan ya ce. "Akwai ɗan yahya na yau ko gobe zai zo neman auren Safeera, kunga idan haka yi engagement a nan sai mu koma Nigeria da zama tun da anyi min transfer ɗin wajan aiki na koma Nigeria, kuma wanda zai zo neman auren ki shi ɗin police officer ne, kinga zaki kasance koda yaushe kina da tsaro".

Miƙe wa tsaye Safeera ta yi sannan ta ce. "NI banason nayi aure yanzu, kuma ba zan je Nigeria ba. Ni a nan zan ci gaba da zama. Ko da karatu ban gama ba, amma shi ne za'a kawo min maganar aure. Ni dai gaskiya ba zan taɓa auran wanda zaku kawo min ba domin ni banason aure yanzu karatu nake so na ci gaba".


Miƙe wa Daddy ya yi ranshi a matuƙar ɓace ya ce. "Kina nufin ba za ki bi umarni na ba kenan?, ɗan yahya na ne fa zai zo neman auren ki, shi ne za ki ce bakya so, to ki kina so ko bakya so sai anyi engagement ɗin nan, kuma karatu daga yau na dakatar da shi,bake ba ba karatu".

Fashe wa da kuka Safeera ta yi sannan ta ce. "Wallahi ba za'a min aure a wannan shekarun nawa ba". Tana kaiwa nan ta shige ɗakin ta tare da rufe ƙofar ɗakin.


Maida kallonta Mom ta yi kan Daddy sannan ta ce. "Daddyn Safeera ina ganin kamar kada mu tilasta mata, tun da bata so kawai mu rabu da ita ta yi karatun tun da shi take so".


Kallon Mom Daddy ya yi sanann ya ce. "Kiyi min shiru Zainab, dama kece ki ka sangalta yarinyar nan ta zama haka. To ki jini da kyau ko tana so ko bata so wannan engagement ɗin kamar anyi an gama ne, sai dai ba bu numfashi a tattare da ni".





*LONDON*.
Kwance yake a kan faɗeɗen gadonsa mai matuƙar girma, yayin da ya rufu da bargo mai matukar laushin gaske.
Ba bu abin da ke tashi a ɗakin sai ƙamshi da ƙaran Ac. a hankali ya ta shi zaune. Tabbas dukkan yabo da jinjina za su ci gaba da tabbata ga Allah SWA wanda ya yi wannan kyakyawan halittar. Lumshe fararen idanuwansa ya yi masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali.


Wayarshi yaji tana ruri. A hankali ya duba kan table ɗin da ke kusa da shi yayin da ya ga sunan Abba bayyane kan screen ɗin shi.

Ɗaukar wayar ya yi yayin da ya ɗaga kiran tare da karawa a kunnensa sallama riƙe a bakin sa. Daga ɗayan ɓangaren haka amsa sallamar. Sannan naji an ce. "Umar yaushe za ka dawo Nigeria?, na faɗa maka cewar ina so a fara aiki a wannan dajin domin a fara gina wannan company, nayi magana da engineers ɗin da za su je suga yadda girman dajin yake, amma an ce akwai namun jeji a wajan dole sai an kore su. Ya kamata ka dawo Nigeria domin a san abun yi".


Ajiyan zuciya Umar ya sauke, sannan ya ce. "Shi ke ne Abba, in sha Allahu zan dawo nan da next week. Ya maganar zaɓe ko har yanzu ba'a fara ba. Ni a tawa shawarar Abba ya kamata ka ajiye govnor wallahi, kamata ai a ce kana hutawa a gida, ka bari wani ya hau kawai".


Murmushi Abbban na shi ya yi sannan ya ce. "Ai kuma kaga ba zai yiwu ba domin ni buri na shi ne na idimtawa al'umma da ƙasar baki ɗaya. So kaga aikin lada kawai nake bawai

Please Login or Register in order to submit comment