Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gano makashin mahaifiyar sa, sai dai har izuwa wannan lokacin bai gano ko wane ne ba kuma bai san irin aikin mahaifin sa ba.

A ɓangare guda kuma shima Musa ya zama ɗan siyasa ba tare da an san ta wace hanya ya bi ya samu wannan takara ba.

*Amma idan ta yi tsami zamu ji ta yadda ya samu takara shiga siyasa*


Haka su Khairiya suma suka taso cike da ƙaunar juna. Yanzu dai Usman ya gama karatun sa yana aiki a office. Sai kuma Ramlat wacce ke University level 300 tana karatun Optometrist. Da kuma Khairiya wacce ke 100 level tana karatun biology.


*Wannan dai shi ne takamaiman tarihin Umar*


___________________
Shigowa da motoci masu tsaron govnor Musa suka yi. Fitowa Gov. Musa ya yi daga cikin mota ganin babu motoci guda biyu a gidan hakan ya nuna masa alamun cewa tabbas Umar ya fita.



Kallon masu tsaron gidan ya yi ya ce. "Where's Umar?".

Amsa ɗaya daga cikin masu gadin ya bashi da cewa. "Yanzu suka fita".


Girgiza kai Gov. Musa ya yi ya ce. "Kun san in da suka je?".


Amsa suka ba shi da cewa. "A'a, amma mun ji kamar suna zancen za su je Kano".



"Kano!". Gov. Musa ya maimaita sunan. "Shi ke nen". Kawai ya ce sannan ya shiga part ɗin shi. Yana shiga ya yi saurin ɗaukar wayarsa sannan ya lalubo number Aliyu tare da danna mai kira.





______
Aliyu da ke zaune sai faman kallon Safira yake yana murmushi ne ya ji wayar sa na ruri. Maida kallonsa ya yi kan wayar. Ganin sunan wanda ke bayyane kan screen ɗin ne ya sa shi miƙe wa sannan ya bar cikin parlour ɗin daba bisani ya ɗaga kiran. Ya ce. "Salamu alaikum".


Daga ɗayan ɓangaren Gov. Musa ya amsa sallamar sannan ya ce. "Aliyu ina da buƙatar taimakon ka yanzu dan Allah, ɗa na da ƙannensa su tafi hanyar Kano, yanzu haka na san sun kusa isa chan, ina son ka bibiyar mun su bana son ya gano gaskiyar ko ni wane ne, sannan kuma bayan nan akwai yarinyar Mrs Laila a Kano ina son ka bincika min duk in da take ka sa a sace ta. Dan Allah ba dan ni ba Please, zan tura maka duk kuɗin da ka ke da buƙata".



Ɗan jimm Aliyu ya yi sannan ya ce. "Shi ke nen naji, million goma shi ne kuɗin aiki na, kuma cash nake so ba transfer ba".


"Shi ke nen Aliyu, ni zan ma ƙara maka ya zama twenty ni dai kawai buri na shi ne ka dakatar da su sannan ka nemo in da yarinyar Lailah take".



"Kada ka samu damuwa wannan abu ne mai sauƙi, nan da sati ɗaya zan nemo duk in da take, kai dai kawai ka shirya min kuɗaɗe na". Cewar Aliyu.



"Angama". Gov. Musa ya faɗa tare da katse wayar yana mai maida numfashi.



Sauke ajiyan zuciya Aliyu ya yi sannan ya shiga ɗakin sa tare da haɗa kayan sa cikin travel box. Bayan ya gama saka kayansa ne ya nufi ɗakin su Grandpa sannan ya sanar da su yana son yin tafiya sainan da sati zai dawo. Addu'a suka yi mai. Daga bisani ya saka kayansa cikin mota. Babu abin da Safira kai ta faman yi sai satar kallonsa.


Babu zato suka haɗa ido da Safira, saurin kawar da kanta Safira ta yi gefe. Murmushi Aliyu ya yi ya ce. "Kodai za ki je ne?".


Taɓe baki Safira ta y ta ce. "Nop, ni kam babu in da zani". Ta faɗa tare da shige wa ciki gidan.



Girgiza kai kawai Aliyu ya yi tare da tada mota sannan suka yi sallama da mutanen gidan gaba ɗaya daga bisani ya fice daga gidan. Bai zarce ko ina ba sai hanyar Kano.



_________________________
Zahra na fita ta hangi kuloli a jere kan dining hakan ya sa ta haɗiye yawu. Da sauri ta je ta zauna kan table ganin zaman kujera ba zai finshe ta ba, ya sa ta kwashe gaba daya kulolin ta jera a ƙasa sannan ta zauna a ƙasa ta fara buɗe kulolin. Take wani irin ƙamshi ya bugi hancin ta hakan ya sa lumshe idanuwanta sannan ta sake buɗe su. Tuwon shinkafa ne miyan taushe ya ji naman turkey yayin da bangare ɗaya kuma fried rice ne ya ji coslow da naman kaza. Sai ɓangare ɗaya kuma kunun aya cikin jug da kuma lemo mai sanyi tare da Fruit salad.


Ganin ba za ta iya ɗauke ido kan wannan abinci ba, ya sa ta cire duka chokulan kan trey ɗin abincin ta zubar a ƙasa. Hakan ya sa ƙaran chokulan suka bada wani irin ƙara.


Jin ƙara daga parlour ya sa su Gimbiya Saratu da Talatu tare da ƴaƴanta fitowa. Yayin da ita ma a dai-dai lokacin Mami ta fito daga cikin ɗakin ta domin ganin meke faruwa. Dai-dai lokacin kuma Junaid ke dawo wa daga fadan mai martaba.


Fitowa Sooraj ya yi daga cikin ɗakin sa. Tare da nufar hanyar parlour. Tsaya wa chakk gaba ɗaya suka yi ganin yadda Zahra ke ɗura wa ciki ta abinci. Cin abinci ta take hankali kwance ba tare da tsoro ko wani tunani ba. Sai loma take ta kwara abincin da lemo tare da kunjn aya. Haka ta cigaba da cin abinta ba tare da ta kula da zuwansu Sooraj wajan ba.


Baki sake gaba ɗaya suke kallonta. Zahra kuwa sai da ta cinye Tuwon shinkafan tass sannan ta koma kan fried rice. Haka ta na ci tana sumbatu. "Wayyo dad'i kashe ni, da wahala gwanda dad'i ka kashe ni, dad'i kashe ni, da wahala gwanda dad'i ka kashe ni"

Sannan ta ƙara da cewa. "Gaskiya kuɗi duniya ne, Allah kayi mu yadda muke so. Yoo ƴan banza ba dole su dinga tumbi ba suna cin abinci mai daɗi da gina jiki. Daɗin ta ma ba za su ci ba, kinga kenen zanci sosai na ƙoshi, naci na ci na bar na bari. Shi ya sa wannan Gimbiya Talatun bakinta yake wangalele kamar na akuya tunda tana cin abinci mai daɗi dole, sai kuma waɗan nan ƙwalaye ukun nan su Samira ko, dole su dinga yadda suka gadama tun da suna cin kayan dad'i. Yanzu ni duk ba wannan ba hanyar da zanbi na koya wa wannan mai ƙaton kai hankali nake Sooraj yake ko, saina koya mai hankali, ba an ce ni ce zan dinga kula da shi ba, kawai idan Mami ta bani abinci shi na cinye sai in kai mai ragowa ya ci". Ta ƙarashe tana mai bushe wa da dariya.


Duk abin da take a gaban idanunsa. A sa'inda ɓangare ɗaya Gimbiya Talatu ta yi mugun ƙulu wa. Jin abin da Zahra ta faɗa game da halittar bakinta. Sooraj kuwa mamaki kawai ya shiga yi ganin yadda take ta sumbatu tana cin abinci duk ba ga san suna tsaye a wajan ba.



Saida ta gama da komai da cikin kulan tass sannan ta kora da kunun aya da fruit salad. Ji ta yi cikin ta ya yi mugum cika. Gatsa ta yi ta ce. "Ya kamata ki kwanta Zahra domin abincin da ki ka ci su zazzage". Ta faɗa tana mai kwanciya a ƙasan wajan tana mai fuskantar saman silin. Gabanta ne ya bada wani rass!, yayin da zuciyarta ya fara dukan uku-uku ganin gaba ki ɗaya ƴan gidan tsaye a kanta.



Zumbur ta miƙe tsaye tare da karkaɗe jikin ta.


Kallonta Sooraj ya yi tare da kallon kulolin da ta cinye abincin ciki sannan ya girgiza kai ya ce. "Sannunki da aiki, yanzu mutum in banda dabba waye zai iya cinye uban abincin nan, to ki sani cewa baki ci a banza ba domin kuwa sai kin koma kasuwa kim siyo duk abin da ki ka ci sannan kin sake dafa irin shi komai da komai".



Rai a ɓace Gimbiya Talatu ta ce. "In banda iskanci ƴar talakawa har ta samu matsayin da za ta ci abinci a kulan da muke cin abinci. Sannan kuma har ta samu damar ta ce wai ni mai wangalellen baki. Lallai kam wuyarki ya isa yanka".



"Madam za ki iya mana shiru a nan". Cewar Sooraj. Tsaki Gimbiya Talatu ta ja tare da wuce wa part ɗin ta ganin hakan ya sa Saratu ta bi bayanta. Sannan sauran ma suka watse ya rage Sooraj, Mami, da kuma Zahra.



Kallonsa Zahra ta yi bakin ta duk maiƙon kaza ta ce. "Yarima wallahi ban iya girki ba, ban taɓa yi ba, ta ya zan iya yin mai daɗin wannan?, kayi haƙuri dan Allah".


Gyara tsayuwar sa Sooraj ya yi ya ce. "My wish is my command, dole ki sake girka irin wannan kuma taste ɗin dole ya zama iri ɗaya.


Zaro idanuwa waje Zahra ta yi jin kalmarsa ta ƙarshe. "Ni na san ma sai dai nayi muku jagwab ɗin abinci don ban iya ba".



Bai ƙara cewa komai ba ya koma part ɗin sa.


Kallonta Mami ta yi ta ce. "Zahra kiyi abin da ya ce karki damu da wajan nan da ki ka ɓata zan sa ƴan aiki su gyara, maza kije ki siyo ingredient ɗin, domin ya ce ba za'a taɓa na gida ba".



"Shi ke nen". Zahra ta faɗa tare da shiga ɗaki ta saka saka hijabi. Fitowa ta yi yayin da Mami ta ba ta isashun kuɗaɗe domin siyan kayan abincin da ta ci. Bayan ta ba ta kuɗin ne fita daga cikin harabar masarautar tare da tarar mai napep ya kaita kasuwa.



Bayan Aliyu ya isa Kano ne ya samu wani guri kusa da kasuwar kwari ya yi parking. Sannan ya fara waige-waige. Chan ya hango mai tallan tsire. Hakan ya sa ya tare shi tare da siyan na dubu ɗaya domin rage yunwar da take damun shi.


Zahra kuwa saida mai napep ɗin ya yi tafiya mai nisa sosai kafin nan ya isa kasuwar kwari. Chan ta hango tsayuwar Aliyu jikin motarsa. Tunani ta shiga yi kamar ta san wannan mutumin. "Wannan kamar wannan ɗan sandan da ya so raina min hankali a magarƙama ne ko?". Ƙara kura masa idanu ta yi. "Laa babu tantama kuwa shi ne". Dakatar da mai napep ɗin ta yi da ya tsaya. Ba tare da ta tsaya biyan mai napep kuɗin sa ba ta tsallaka titi da gudu tare da nufar in da Aliyu yake tana mai faɗin. "Malam ɗan sanda mai ɗagaggen wando kaine a garin Kano?".


Juyawa Aliyu ya yi ganin waye wannan mai furta wannan kalma. Nan take ya haɗa ido da Zahra. Take gabansa ya yi mummunar faɗuwa!. Nuna ta ya yi ya ce. "Safira!".


Kallonsa Zahra ta yi ta ce. "Wace ce kuma haka?, wai Safira, kai ni ce fa baka gane ni ba a magarƙama da ka zagar min uwa na so nayi maka duka ka tuna?. Ba kai ne wannan ɗan sandan mai ɗagaggen wando ba?".


Dafe kansa Aliyu ya yi jin yadda kansa ke ƙoƙarin sara masa. Riƙe kansa sosai ya yi domin yin tunanin a ina ya santa. Ɗaga kansa ya yi ya kalle ta ya ce. "Kenen ba ke ba ce Safira ba?".


Haɗe giran ta Zahra ta yi tare da turnuƙe fuska ta ce. "Wace ce kuma Safira?, ni fa malam sunana Zahra ba Safira ba".



"I am totally confused, what's going on?". Aliyu ya tambayi kansa. Nan take ya fara tuna wan can ta magarƙamar. Rass gabansa ya faɗi. Cikin ransa ya ce. "Tabbas wannan ita ce wanda na gani a magarƙama kwanaki mai brown eyes, sannan Safira ma tana kama da ita, ga kuma ranar nan na ga wata mai kama da Safira mai grey eyes. Kenen hakan yana nufin su uku ne?, idan kuwa hakan ta kasance to tabbas hasashen Mom gaskiya ne, kenen hakan yana nufin yaran Mrs Laila ne?!".







COMMENTS & SHARE FISABILILLAHI 🙏 🙏
ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
(Zinariyar Jajirtattu)




Follow the 🌺🌎A'ISHA M.B🌹 HAUSA NOVELS 📚 WORLD 🌎 📚💗💖 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g


*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part of the world)*🪐🌎🪐.
Daji 🌲
Magarƙama🏢 da kuma
Birni🏙️

WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝♀️Jajirtattu)


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
(We stand together)
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 3️⃣9️⃣▶️4️⃣0️⃣
*___________________________________________*
"Wai tunani me ka ke yi ne malam ɗan sanda?". Cewar Zahra.

Murmushi Aliyu ya saki sannan ya ce. "Babu komai kawai dai ina mamaki ne, masha Allah gaskiya naji daɗin haɗuwa da ke. Idan babu damuwa shin zamu iya zama abokai?".


Harara Zahra ta galla mai sannan ta ce. "Ta ina ka taɓa jin ana aboki tsakani mace da namiji?, ni bana son wanda zamu fara abota ya kawo min zancen soyayya, atohh dai, dan na san yawancin ku daga abota za ku fara sai a zarce soyayya".

Dariya Aliyu ya yi ya ce. "Aba dai karki damu ni ina da ma wacce zan aura, sunanta Safira".


Taɓe baki Zahra ta yi sannan ta ce. "To Allah ya bar soyayya".

Amsa wa Aliyu ya yi da "Ameen".


"Shi ke nen, ni zan tafi, zanje in siyo abu ne a wannan kasuwan kada na daɗe kuma wan can yariman ya zo ya fara balbale ni da masifa, ni bai san ma ɗaga mai ƙafa kawai nake ba".
Zahra ta faɗa tana mai ƙoƙarin tafiya.



Saurin dakatar da ita Aliyu ya yi sannan ya ce. "A'a karki tafi bari nayi miki rakiya, ai yanzu mum zama abokai ko, don haka duk abin da ki ka siya ni nan zan riƙe".


Dariya Zahra ta yi ta ce. "Kai kuwa ka san me zan siyo?, ba za ka iya riƙe wa ba, idan na ce zan baka duk abin da zan siya sai dai ma na saka kuka domin ba za ka iya ba, kawai dai kayi tafiyarka".


Girgiza kai Aliyu ya yi ya ce. "Aba dai, ni fa ba ragon namiji ba ne, ni jarumin jarumai ne, kedai kawai ki bari muje tare zan baki mamaki".


Murmushin mugunta Zahra ta yi ta ce. "Tom shi ke nen malam ɗan sanda muje, ni ba zan ana ka ba".


Ta faɗa tana mai tafiya. Saurin bin bayanta Aliyu ya yi tare da farin cikin ya samu shiga jikin Zahra saura kuma yadda zai yi ya sace ta.


_________________________
Su Umar ba su suka iso Kano ba sai wajan la'asar. Yayin da kai tsaye suka wuce gidan zoo.
Bai ɗauke su lokaci ba suka isa gidan zoo dai-dai lokacin da ake kiran sallah.


Parking gaba ɗaya suka yi yayin da suka fito daga cikin motocin. Kallonsu Ramlat da Usman Umar ya yi ganin hankalin Amrah yana wani wajan da ban, ya sashi faɗin. "Na san ba za'a rasa wasu namun jeji a nan ba, kuje ku kaita ta gansu na san koba komai dai za ta ɗauka ƴan uwanta ne. Kai kuma". Ya faɗa yana mai kallon Usman, "maza biyo ni muje muyi Sallah a masallaci". Ya ƙarashe maganar yana mai yin gaba.


Bin bayansa Usman ya yi suka wuce masjid domin gabatar da Sallah.


Maida kallonsu su Khairiya suka yi kan Amrah sannan suka riƙe hannayenta suka fara shiga ɓangaren dabbobi da ita. Gani suka yi gaba ɗaya dabbobin sun ragu babu wasu dabbobi chan sosai.


Daga nesa Amrah ta hango wasu birurruka cikin zagaye. Da sauri ta wafce hannunta tare da nufar wajan da mugun gudu, a sa'inda jama'ar wajan gaba ɗaya suka bita da kallo.


Da sauri su Khairiya suka bi bayanta a matuƙar tsorace.


Ƙarasa wa wajan Amrah ta yi tana mai aye wa kan ragar birurrukan. Da sauri su Khairiya suka je tare da kokarin saukar da ita. Saukar da ita suka yi. Sannan suka fara kwantar mata da hankali.


Shiru Amrah ta yi sannan ta ƙura wa birurrukan idanuwa. Girgiza kai ta fara yi tana mai ja da baya, tana mai faɗin. "A'a, waɗan nan samm ba su ba ne". Saurin maida kanta ta yi kansu ta ce. "Ina ku ka kai su?, kun kashe su ko?, me ya sa ku ka yi min ƙarya?".
Ta faɗa tana mai fashe wa da kuka.


Kallon juna Ramlat da Khairiya suka yi yayin da bakinsu ya kasa furta komai.


Share hawayenta Amrah ta yi jin kukan yaro ƙarami wanda ya karaɗe wajan. Saurin waiga wa ta yi domin jiyo ta idda wannan kukan ke fitowa. Nan take idanuwanta ya sauka kan wani yaro a ƙasa sai faman kuka yake.


Da sauri Amrah ta isa idda yaron yake sannan ta ɗauke shi tare da sakin murmushi ta ce. "Daina kuka yaro za ka yi wasa?, bara muyi wasa ko". Ta faɗa tana mai cilla yaron sama.

Take mutane suka saki ihuu ganin yadda ta jefa yaro chan sama sosai.


Da sauri su Khairiya suka dube ta suka ce. "Ke Amrah kinyi hauka ne?, maza ki sauke wannan yaron".


Ko kula su Amrah ba ta yi ba, saima cigaba wa da ta yi. Nan ta ci gaba da jefa yaron sama yana ihuu yana kururuwa. A sa'inda jiri ya ɗebi yaron ya suma.


Bayan ya dawo hannunta ne ta ga yaron ya yi shiru. Murmushi ta yi ta ce. "Kun gani ko, yaron ma har ya yi bacci abunsa hankali kwance".


Dafe kanta Ramlat ta yi ta ce. "Mun shiga uku, Amrah me ki ka aikata aka?, kin fa sumar da shi".



Dai-dai lokacin da wata mata take ƙaraso wa wajan hannunta riƙe da leda alamun ita ce mahaifiyar wannan yaron.


"Me yake faruwa ne na ga mutane sun taru a nan wajan?, ina ɗana yake?". Ta faɗa a yayin da idanuwanta suka sauka kan yaronta da ke hannun Amrah.


Ɗora hannayenta ta yi a kai tana mai fasa ihuu!. "Innalilahi wa innahilahir rajihun!, me ku ka aikata wa ɗana, me ya faru da shi. Wallahi idan wani abu ya samu ɗana ba zan ƙyale kowa ba". Ta faɗa tana mai ƙoƙarin wafce ɗanta a hannun Amrah.


Nan take Amrah ta riƙe hannun matar ta ce. "Ba zan baki shi ba har sai ya farfaɗo".

Wafce hannunta matar ta yi daga na Amrah sannan ta ce. "To maza farfaɗo da shi".


Kwantar da shi Amrah ta yi sannan ta hura mai iskar bakinta kan fuskarsa. Cikin ƙanƙanin lokaci yaron ya farfaɗo. Nan take mutane suka fara mamaki. "Dama iskar baki na iya farfaɗo da wanda ya suma?, kodai ita ɗin ba mutum ba ce, don yadda ƙwayar idanunta suke green ma za ka tabbatar da cewa wannan ba mutum bace?". Abin da suka shiga furta wa kenen.


Ɗaukar ɗanta matar ta yi cikin farin ciki sannan ta juya tare da barin wajan ba tare da ta yi wa Amrah godiya ba.



MK da ke zaune cikin mota duk abin da ya faru a gaban idanuwansa. Murmushi wanda ya fi kuka ciwo ya yi ya ce. "Da a ce a wajan iyayenku ku uku ku ka taso da rayuwarku ba ta kasance haka ba, amma haka Allah ya riga ya kaddara cewar ba za ku taso da mahaifiyar ku ba. Ina fatan duk in da mrs Laila take ya kasance tana ƙoshin lafiya, har izuwa yanzu ban sani ba ko tana raye ko kuma ta riga mu zuwa gidan gaskiya. Amma ina fatan duk in da take ya kasance tana cikin rahamar ubangiji".


Ya faɗa yana mai tada mota sannan ya bar harabar wajan.



___________
"Hello your Excellency yanzu haka muna cikin gidan zoo ɗin, umarnin ka kawai muke jira".


Daga ɗayan ɓangaren gov. Musa ya ce. "Perfect, ni na san Aliyu ba zai iya wannan aikin shi ɗaya ba shi ya sa na tura ku chan. Ina son ku sace Amrah kai tsaye ku wuce da ita hanyar Airport ku wuce ƙasar waje domin a sata a kasuwa. Amma fa ku tabbata Umar bai ganku ba sannan ku rufe fuskokin ku kada ku kuskure ku buɗe".


"Shi ke nen yallaɓai kamar yadda ka ce". Mutumin ya faɗa yana mai kashe wayar. Nan take su biyar da ke cikin mota suka kalli juna a yayin da lokaci ɗaya gaba ɗaya suka rufe fuskokinsu da mask. Sannan suka fito daga cikin mota.


Kai tsaye in da Amrah ke tsaye suka nufa wacce ke ta faman kallon dabbobin cikin wajan.


Suna isa wajan suka rirriƙe hannunta tare da ƙoƙarin tafiya da ita. Nan take hankulan mutane da nasu Ramlat ya karkata izuwa kansu.

Dai-dai lokacin da su Umar ke ƙarasowa wajan.


Ganin abin da ke faruwa ya sa Umar ya yi saurin nufar wajan tare da ƙoƙarin ƙwace Amrah daga gare su. Gani Umar na shirin dakatar da su ya sa ɗaya daga cikin su ya kai mishi naushi a ciki. Faɗuwa Umar ya yi a matuƙar zafafe ya miƙe tare da yin kansu sannan ya fara kokawa da su. Nan take mutane suka fara ɗaukar video ganin yadda ɗan gidan govnor musa yake faɗa da ƴan ta'adda.


Cikin rashin sa'a ɗaya daga cikin su ya kai masa naushi cikin sa a karo na biyu. Faɗuwa Umar ya yi yana mai sakin ƙara.


Zaro idanuwa waje su Ramlat suka yi a matuƙar tsora ce suka nufo kan ɗan uwansu.


Ganin abin da suka aikata Umar hakan ya sanya ran Amrah ya fara tafarfasa yayin da ta saki wata iriyar razananniyar ƙara mai matukar firgitarwa.


Ba ta yi wata-wata ba ta shaƙe wuyan mutane biyu daga cikin su tare da ɗaga su sama sannan ta naka su da ƙasa. Ganin hakan ya sa sauran ukun suka yi saurin ja da baya.

Da sauri ɗaya daga cikin ya ɗauki sanda sannan ya buga wa Amrah.



_________________
"Mom!!!!!". Safira ta faɗa da mugun ƙarfi tana mai dafe kanta. Da sauri su Mom da ke zaune a parlour suka fito garden in da Safira ke zaune.


Dubanta Mom ta yi ta ce. "Mene ne ya fara ki ka saki uban wann ƙarar haka?".,


Rintse idanuwanta Safira ta yi ta ce. "Mom ina ji wani iri a jiki na, gaba ɗaya bana jin daɗin jiki na, ina ji kamar wani abu mara kyau na shirin faruwa da ni".


Zama kusada ita Grandma ta yi ta ce. "Kiyi addu'a kinji ƴata, in sha Allahu komai zai zo miki da sauƙi, babu abin da zai faru sai alkhairy".


Girgiza kai Safira ta yi ta ce. "A'a Grandma gaba ɗaya jiki na ciwo yake yi, ba zan iya jure wa ba, jiki na yana min ciwo kamar wacce ta yi dambe da mutane".


"Tashi zo mu shiga ciki na ɗora miki ruwan zafi ki gasa jikin ki". Cewar Grandma. Tashi tsaye Safira ta yi cikin jin ciwo sannan ta bi su Grandma suka shiga cikin gida".



Nan dai Grandma ta ɗora mata ruwan zafi sannan ta fara gasa mata jikin ta. Cikin mamakin su kuwa abun sai ƙara tsamari yake, a maimakon ya ragu saima ƙaruwa da ya yi. Gani hakan ya sa hankulan gaba ɗayansu ya tashi.


"Wai Safira me yake faruwa da ke ne haka?". Cewar Daddy.

Hawaye ne ya fara gangaro wa kan ƙuncin Safira sannan ta bawa Daddy amsa da cewa. "Wallahi ban sani ba, dan Allah kuyi wani abu ina jin raɗaɗi sosai, ina tunanin mutuwa zanyi. Kunga ni na kasa motsa hannayena, na shiga uku, Mom mutuwa zanyi".



Nan take hankalinsu ya sake tashi gani gaba ɗaya Safira ta kasa motsa koda ɗan yatsarta.





_________________________
Rintse idanuwanta Zahra ta yi jin yadda jikin gaba ɗaya ke mata ciwo.
"Wayyo Allah, ya naji lokaci ɗaya jiki na namin ciwo, gaba ɗaya jiki na ya mutu. Ya kamata na samu guri na zauna". Ta faɗa tana mai hango rumfar mai saida kayan miya. Da sauri ta nufi wajan a matuƙar jigata ta isa wajan tare da zama.


Saurin isa wajan Aliyu ya yi ya ce. "Ya ki ka zauna kuma bayan baki siyi abin da za ki siya ba".


Girgiza kai Zahra ta yi a matuƙar jigace ta ce. "Ba zan iya tafiya ba, jiki na ya mutu. Ji nake tamkar nayi dambe saboda a halin yanzu gaba ɗaya gaɓobin jiki na ciwo yake. Tun da yanzu kai aboki na ne ka taimaka min ka siya min duk abin da nake da buƙata".


Mamaki ne ya kama Aliyu ganin yadda gaba ɗaya ta bi ta galabaita. Tamkar wacce aka yi wa duka. "Me ke faruwa?, ba yanzu na ga mum tawo jikin garau ba?, amma a ce yanzu kuma wai jikin ki yana ciwo. Dama dai tun asali baki da lafiya shi ne ki ka tako ki ka zo kasuwa, maimakon kije kina huta wa".



Girgiza kai Zahra ta yi ta ce.

Please Login or Register in order to submit comment