Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ta saka kaya masu kyau riga da wando sannan ta saka ɗan ƙaramin veil sannan ta ɗora kimono a kan riga da wandon.


Fitowa ta yi da box ɗin sannan ta nufi hanyar waje. Bakwana suka yi da kowa na gidan yayin da Daddy ya shiga saka mata albarka. Mom kuwa shiru ta yi domin gaba ɗaya hankalinta ba'a kwance yake ba, ji take kamar wani abu na shirin faruwa da ƴarta.


Kallon Safira ta yi ta ce. "Safira, ni da za ki ji ta baki na kiyi zamanki kawai, idan ya so idan za mu koma America sai kiyi komai, wallahi hankali na ya kasa kwanciya, tsoro na shi ne kada wani abu ya same ki".


Murmushi Safira ta yi ta ce. "Kada ki damu Mom babu abin da zai same ni da izinin Allah".


Daidai lokacin suka jiyo horn ɗin mota a waje. Bye-bye tayi musu kana daga bisani ta fice daga gidan. Fitowa driver ɗin motan ya yi sannan ya karɓi box ɗin kayanta tare da saka su a bayan mota. Shiga cikin motan ta yi kana daga bisani driver ya ja mota suka bar wajan.



Sosai Safira ke farin ciki yayin da take gani kamar cewa ta riga ta zama lawyer.


Kallon driver ɗin ta yi ta ce. "Yanzu hanyar airport zamu wuce ko?".


Shiru driver ɗin ya yi mata bai ko tanka mata ba.

Mamaki ne ya kamata ganin bai amsa ba, hakan ya sa ta yi tunanin ko bai ji ba ne.


Hankalinta bai tashi ba sai sanda ta ga anyi wani kwana da ita ana shiga cikin dajin.


Nan take gabanta ya tsananta faɗuwa. Kallon driver ɗin ta yi ta ce. "Kai driver ina ka ke ƙoƙarin kai ni?, ba airport ka ce zamu je ba, ni ka ga just take me back home please".


Ganin ko kulata bai yi ba ya sa hankalinta ya ƙara tashi.


Addu'a ta shiga yi tana mai neman kariyar Ubangiji. Yayin da hawaye ya fara sauka kan ƙuncinta tana mai nadama kan me ya sa ta biyo wanda ba ta sani ba, kuma saida Mom ta faɗa mata cewa kada taje ta bari idan za su koma America.


Saida suka je chan cikin tsakiyar daji. Sannan driver ɗin ya tsagaita da tafiya. Parking ya yi kusa da sauran kidnapper's ɗin sannan ya fito daga mota. Buɗe mata ƙofa ya yi kana ya dube ta ya ce. "Duk abinda haka faɗa miki a waya to ƙarya ne. A halin yanzu dai kina ƙarƙashin mu ne, kuma idan muka gadama za mu kashe ki har lahira, ina son ki bamu haɗin kai idan ba haka ba ki mutu".


Faɗuwa gaban Safira ta yi sannan ta ce. "Dan Allah ku faɗa min mene ne na aikata muku?, sannan wane ne ya turo ku sace ni?".



Murmushi mutumin ya saki sannan ya ce. "Kina son sanin wane ne?".


Girgiza kai Safira ta yi alamun eh.

Amsa mutumin ya bata da cewa. "To Aliyu ne".


Rass! gabanta ya buga da mugun ƙarfi. Kallon mutumin ta yi ta ce. Wane Aliyu?, Aliyu wanda zan aura?".


Amsa suka bata da cewa. "Ƙwarai kuwa da gaske".


Kallon su Safira ta yi cikin rashin yarda ta ce. "Ƙarya ku ke, samm Aliyu ba zai sa a sace ni ba, saboda me zai yi hakan?, ni ce fa wacce zai aura. Kunga ku faɗa min gaskiyar cewa ba Aliyu ba ne, domin na yarda da shi ba zai taɓa sace ni ba, kuma mene ne ribarsa ma idan ya sace ni?, me zai samu?".



Dariya gaba ɗaya suka kwashe da shi sannan suka ce. "Kina son sanin me zai samu?. To ki baza kunnuwanki kiji, zai samu kuɗaɗe ne, dubbunan kuɗaɗe, Aliyu samm ba sanki yake ba illa dukiyar ki, kuma dai Aliyu shi ne ba wani ba. Idan baki yarda ba duba nan ki gani".


Mutumin ya faɗa yana mai nuna mata wayarsa. Nan ta ga Aliyu tare da mutanen wajan suna raba kuɗi a tsakanin su, yayin da suke maganar yadda suka sace Amrah, gashi za su sace Safira.




Jikin Safira ne ya mutu, yayin da takaici ya ana ta kasa cewa ƙala. Hawaye ne ya fara gangaro wa bisa ƙuncinta. Ta ce. "Ban taɓa tunanin haka daga gare ka ba Aliyu, me ya sa zai aikata min haka?, da na yanke cewa zan amince na aure sa domin ya nuna min cewa yana so na sannan kuma yana da nutsuwa da sanin ya kamata, ashe duk ƙarya ne". Ta ƙarashe maganar tana mai fashe wa da kuka.









**********
Zahra na zaune ta ga ƴar aiki ta shigo sallama riƙe a bakin ta. Amsa sallamar Zahra ta yi ta ce. "Mene ne ya faru?".


Amsa ƴar aiki ta bata da cewa. "Yarima Sooraj ne ya ce na kira wo masa ke, kuma ya ce ki zo cikin gaggawa".


Taɓe baki Zahra ta yi ta ce. "Allah ko?". Sannan ya ƙara da cewa. "To ki koma ki gaya masa cewa ba zan zo ɗin ba, idan zai iya zuwa ya tafi da ni chan ya zo ya ɗauke ni, sannan kice mai tunda shi ne yake buƙata ya zo da ƙafarsa amma ba dai ni na je ba, ni Mami kawai nake yi wa aiki bawai shi ba, ita kaɗai ce za ta sani aiki nayi ki gaya masa hakan". Ta faɗa tana mai koma wa tare da kwanciya.



Fita ƴar aikin ta yi sannan ta nufi part ɗin Sooraj ta zayyane masa duk abin da Zahra ta faɗa. Nan take ran Sooraj ya ƙara ɓaci. "Ni ce zan kira ta tace wai ba zata zo ba sai dai ni da kaina naje?, za ta gane kuranta". Maida kallonsa ya yi kan ƴar aikin ya ce. "Jeki na san yadda zan yi da ita".

Jin hakan ya sa ƴar aikin ta bar masa part ɗin sa.




******
Zahra na kwance taji an banƙo mata ƙofa. A matuƙar razane ta miƙe tsaye. Su Gimbiya Saratu ne tare da su Fasma.


Rufe ɗakin suka yi sannan suka saka maƙulli suka rufe.


Murɗa hannayensu suka yi a ƙirji sannan Gimbiya Talatu da su Samira suka fara karkaɗa ɗuwawu.


Kallonta Yusra ta yi ta ce. "Wati ke kin cika ƴar iska da har za ki iya sa mu ci wannan ƙazamin abincin naki".



Murmushi Zahra ta yi sannan ta ce. "Naji ƙazami ne, amma dai koba komai kunci abincin. Tukun na ma me ya kawo ku ɗaki na?".


Amsa Gimbiya Saratu ta bata da cewa. "Munzo mu nakaɗa miki na jaki ne, duka zamu yi miki".




Babu zato Zahra ta kwashe da dariya. Kallon juna su Gimbiya Saratu suka yi ganin tana dariya ya sa abin ya basu mamaki.


Saida Zahra ta yi mai isarta sannan ta ce. "Wai da gaske duka na ku ka zo yi?. To masha Allah maraba da zuwa, me ku ke so na kawo muku, tuwo ko shinkafa?, kun san ana son mutun kafin ya fara dambe ya fara cin abinci mai lafiya ta yadda zai samu ƙarfin yin duka sosai".


Kallon juna suka yi gaba ɗaya suka yi ganin tana neman shashantar da su ya sasu cewa. "Da gaske fa muke ba wasa ba".


Jin hakan ya sa Zahra ta haɗe ranta sannan ta ce. "Zan baku shawara kyauta ba tare da ko sisin ku ba, kuyi wa kanku faɗa ku koma, domin idan na fara dukan ku karku zo kuna bani haƙuri naƙi hakura, ku yanke shawara a tsakanin ku tun kafin a fara".

Kallonta Samira ta yi ta ce. "Kin ɗauka za ki iya dukan mu ne?, ko kin manta cewa sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi?, to ba za mu fita ɗin ba kiyi abin da ki ke ganin za ki yi" .


Jin hakan ya sa Zahra miƙe wa sannan ta nufi hanyar waje ta ƙara rufe ƙofar sosai sannan ta cire ki ɗin tare da saka wa a ciki kayanta wanda yake doguwar riga atamfa mai aljihu.



Koma wa ta yi ta zauna kan gado ta ce. "Ta kan wa za'a fara?, ku gimbiyoyi ku koma ku zauna ku ga idan yaranku suna da ƙarfi ko basu da shi".


Kamar yadda ta faɗa aka gimbiya Saratu da Talatu suka koma suka zauna, yayin da suke jiran kawai suka yaran nasu sun fara jibgar Zahra.



Take Samira ta kaiwa Zahra naushi a fuska. Da sauri Zahra ta kawar da kai sannan ta kama kan Samira da Fasma ta gwara su guri ɗaya.



Nan take suka saki wata iriyar azababbiyar ƙara!. Ƙaran da suka saki ya janyo hankulan su Junaid da na so Sooraj ɗakin. Da sauri suka nufi hanyar ɗakin Zahra tare da bubbuga ƙofan.


Ɓangare Zahra kuwa ɗaukar dorina ta yi ta fata shauɗa musu babu gaggauta wa. Ihuu suke suna neman a kawo musu agaji . Ganin ba za su iya cigaba da jure wa ganin Zahra na dukan musu yara ba ya sa su miƙe wa suka fara rirriƙe hannun Zahra.


Ɗaga hannu Zahra ta yi zata zuba wa wanda ya riƙe ta dorina. Chak da dakata ganin su Gimbiya Saratu ne. Wafce jikinta ta yi daga nasu ta ce. "Ba zan iya dukan ku ba, domin kuwa kuma a matsayin iyaye na ku ke, dan haka ba zan taɓa iya ɗora hannu na a kanku ba". Ta faɗa tare da koma wa ta zauna.



Miƙe wa su Samira suka yi suna hawaye, yayin da su Gimbiya Saratu suka shiga rarrashin su gani yadda jikinsu ya yi jajir yayin da satin bulalan Zahra duk ya fito jikinsu.



Kallon Zahra Gimbiya Talatu ta yi ta ce. "Ki bamu maƙulli mu fita".


Kallonsu Zahra ta yi mamaki bayyane kan fuskarta ta ce. "Ku fa ku ka ce ba za ku taɓa fita daga ɗakin nan ba har sai kun dake ni, to a kan me ya sa za ku fita bayan baku dake ni ba?, to ku sani cewa muddin baku dake ni ba bazan baku maƙullin ɗakin nan domin ku fita ba".


Roƙan Zahra gaba ɗaya suka fara yi. Yayin da suka ce ba za su sake irin wannan gangancin ba.


Saidai Zahra ko sauraren su ba ta yi ba illa ca da ta yi cewa. "Wallahi ba zan bari ku fita ba muddin baku dake ni, maza-maza ku tawo ɗaya bayan ɗaya ku dake ni kunji ko, kunce za ku dake ni kafin ku fita kuma baku dake ni ba. To ku sani cewa ko wane ne zai zo bai isa ya sani na baku maƙulli domin ku fita ba har sai kun dake ni kamar yadda ku ka furta, ba saida na faɗa muku kuyi wa kanku faɗa ba?, na baku shawara na ce ku tafi amma ku ka yi kunnen ƙashi, kuma na riga na faɗa muku idan na fara jibgar mutum idan wani ya roƙe ni na buɗe ƙofa ba zan buɗe ba, dan aka a yanzu mun sa ƙafar wando ɗaya da ku, sai dai ku dauwama a cikin ɗakin nan muddin baku zo kun taɓa ni ba".







*KAI ZAHRA AKWAI ƘARFIN HALI😹😹😹, KI ƘYALE SU AJEBUTTERS SU FITA😂🤣*




ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
(ZINARIYAR JAJIRTATTU).







https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g





*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part of the world)*🪐🌎🪐.
Daji 🌲
Magarƙama🏢 da kuma
Birni🏙️

WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝♀️Jajirtattu)


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
(We stand together)
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 4️⃣7️⃣▶️4️⃣8️⃣
*___________________________________________*
Shiru gaba ɗaya suka yi jin furucin Zahra. Takaici ne ya kama kowanne a cikin su. A matuƙar fusa ce Gimbiya Saratu ta ce.

"Karki manta kefa ƴar aiki ce kawai a masarautar nan, kinga kenen muna da iko a kanki, dan haka a matsayina na Gimbiya mai faɗa a ji, ina mai baki umarmin ki buɗe wannan ƙofan yanzu".


Dariya Zahra ta kwashe da shi sannan ta ce. "Sannu Gimbiya mai faɗa a ji, wato kina mai bani umarni na buɗe ƙofa ko, tun farko mena faɗa muku muddin na fara ba zan buɗe muku ba, amma ku ka yi kunne uwar shegu ku ka ƙi tafiya, shi ne yanzu kuma za ku ce na buɗe muku ƙofa, chab kuna ruwa wallahi".


Shiru gaba ɗaya suka yi, yayin da suka ji cewa dama tun farko basu shiga ɗakin ba.


Ƙarasa wa inda Zahra take Gimbiya Talatu ta yi tare da zama kusa da ita ta ce. "Zahra na san ke yarinyar kirki ce, kuma na san kina daraja manya sai dai idan manyan basu kama girman su ba kamar dai yadda muma bamu kama ta mu girman ba, a madadin kowa da ke nen, ni zan bada haƙuri bisa ga abinda muka aikata. Dan Allah kiyi haƙuri".


Shiru Zahra ta yi tana mai sauke ajiyan zuciya ta ce. "Shi ke nen zan barku ku fita amma da sharaɗi".


Washe baki gaba ɗaya suka yi jin cewa zata barsu su fita. Nan suka haɗa baki wajan faɗin. "Mene ne sharaɗin?".


Murmushi Zahra ta yi kana ta gyara zamanta a kan gado sannan ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ta ce. "Na san da zarar na barku kun tafi za ku je ku sake wani ƙulla-ƙullan, hakan ya sa na ce da sharaɗi kafi ku tafi, sharaɗin shi ne". Ta faɗa tana mai maida kallonta kan Fasma ta ce. "Ku biyun nan za ku wanke min banɗaki na wato toilet, ku gyara shi tsaff saiya fita. Sannan ke kuma". Ta faɗa tana mai maida kallonta kan Samira ta ce. "Za ki gyara min ɗaki na har saiya fita fess. Bayan nan Samira da ke da Yusra za ku wanke min kayana gasu chan basu da yawa. Ku kuma su Gimbiyoyi masu faɗa a ji, za ku yi musu jagora kusa ido a kan abin da za su yi, bayan nan ku zo kuyi min tausa a ƙafafuwana naji suna min ciwo, yanzu kuje ku fara kafin nan ni zan ɗanyi baccin rabin lokaci ".


Jin maganganunta suka yi tamkar saukar aradu, mamaki ma ya sa kowanensu ya kasa buɗe baki ya yi mata magana.


A take ɓaccin rai da baƙin ciki ya ziyarci kowanensu. Dubanta Samira ta yi ta ce. "Har ke wace ce za ki saka mu muyi miki wanki, sharan ɗaki da kuma wankin toilet?".


Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Dan ma kunci sa'a ban haɗa muku da panties ɗina ba, wato kenen har ni wace ce ko?, ita Mami da ku ke sata ta yi muku wanki shara ta wanke muku panties ba ta isa haifar ku ba?, har kuna da ma bakin magana?, to wallahi idan baku yi abinda na ce ba, ba zaku fita ba".



"Wallahi ba za mu yi ba sai dai karki buɗe mana ƙofa". Cewar Gimbiya Saratu sannan ta ƙara da cewa. "Kina matsayin ƴar aiki za ki ce muyi miki wanki da shara, mu kuma mu zo muyi miki tausa ko?, ina tunanin kin sha giyan wake, wallahi sai dai mu dauwama a nan ɗin da na zuba ido naga yara na suna yiwa ƴar aiki shara da wanki".



Murmushi Zahra ta yi sannan ta ce. "Toh shi ke nen mu zuba mu gani, kun san dai nafi ku taurin kai ko, to karku yi, ni kuma ban baku mamaki".



Ta faɗa tare da kwanciya cikin ƙankanin lokaci baccin ɓarawo ya yi hawon gaba da ita. Takaici ne ya kama kowanensu ganin yadda Zahra ke bacci harda minshari hankalinta kwance.


Baƙin ciki ne ya bi ya cunkushe guri ɗaya a zuciyoyin su yayin da suka ji kamar su sa pillow su danne ta har lahira.



Aka suka cigaba da zama ba tare da wani a cikin su ya yi abin da Zahra ta ce ba. Ganin dai an fi hour ɗaya ana zaune gashi kuma Zahra ba ta da niyar buɗe musu ƙofa ya sa suka fara shawara a tsakanin su.


Kallonsu Gimbiya Saratu ta yi ta ce. "Kun san me?". Amsa suka bata da cewa. "A'a.


Gyara muryarta ta yi ta ce. "Kawai ku zo muje muyi abin da ta ce, ina ga hakan zai fi mana sauƙi ko".


Yamutse fuska kowanensu ya yi a sa'inda Samira ta ce. "Aba Ammi wallahi ni gaskiya ba zan yi ba, ita ɗin fa ƴar aiki ce, kuma shi ne za ta zo ta saka mu wai muyi mata wanki shara da gyaran toilet, lallai ma".


Girgiza kai Gimbiya Saratu ta yi ta ce. "Kunga ku zo mu rufa wa kanmu asiri muje muyi kafin ta tashi, kinga idan ta tashi bamu yi ba kuma ta ganmu a zaune za ta iya zuwa ta faɗa wa ƴan cikin masarautar nan cewa mun shigo ɗakinta".


"Kunga ni ku tashi". Cewar Gimbiya Saratu. Miƙe wa kowanensu ya yi yayin da Fasma da Yusrah suka nufi toilet, Kai tsaye ba ɓata lokaci suka fara wanke wa. suna yi suna hawayen baƙin ciki, wai yau gasu suna wanke banɗakin ƴar aiki.


Ɓangaren Samira ma kuwa, haka ta ɗauki tsintsiya ta fara share ɗakin yayin da baƙim ciki ya bi ya cunkushe guri guda a zuciyarta. Kukan da take haɗiye wa ne ya suɓuce mata. Take ta fashe da kuka, tana mai yi wa Zahra Allah ya isa. Haka ta cigaba da share wa ba tare da taso hakan ba. Su kuwa gimbiyoyi kamar yadda Zahra ta faɗa haka suka fara yi wa Zahra Tausa. Yayin da suke ji kamar su hallaka ta saboda takaici.


Bayan sun gama ne Samira da Yusrah suka kwashe kayan Zahra wanda basu da wani yawa, suka shiga da shi toilet suka sa a bokiti tare da balbala omo suka fara wanke wa. Haka su cigaba wanke wa suna kuka da hawaye. Karo na farko a rayuwarsu da suka fara yin wanki.



Bayan sun gama ne suka shanya su a igiyar toilet ɗin.


Zama suka yi suna mai sauke ajiyan zuciya dan gaba ɗaya su ba ƙaramin gajiya suka yi ba.


Dai-dai lokacin Zahra ta farka daga bacci. Ganin ta farka ya sa gaba ɗaya suka washe baki suna mai faɗin. "Mun gama komai da komai Hajiya Zahra, yanzu dai a bamu maƙullin mu fita".


Sosa ƙeyar ta Zahra ta yi tare da miƙe wa tsaye ta ce. "Saina ga aikin ku sosai, in dai na ga akwai wani kuskure to sai kun sake shi daga farko".


Ta faɗa tana mai girgiza kai duban ɗakin gaba ɗaya ta yi sannan ta ce. "Wai ke Samira sharar ma baki iya ba?, ya za ki yi to idan ki ka je gidan mijin ki?. To ni fa sharar nan ba ta yi ba dole ki sake wata gaskiya".


Samira ji ta yi kamar ta shaƙe Zahra ta mutu kowa ma ya huta.


Shiga banɗakin Zahra ta yi ta girgiza kai sannan ta maida kallonta kan wankin da su Samira suka yi ta ce. "Ya salam!, wannan wane irin wanki ne?, sai ka ce wasan yara?, idan ku ka sa Mami wanki haka take wanke muku kaya a jagwalgwale?, to fa baku isa ba sai kun sake wanke kayan nan".



Fashe wa gaba ɗaya suka yi da kuka suna mai nadamar shigowa ɗakin Zahra. Kuka suka cigaba da rusa wa kamar yara suna mai faɗin. "Wannan wace iriyar masifa da bala'i ce?, dama mun sani bamu shigo wannan ɗakin ba, dan Allah kiyi haƙuri ki rabu da mu haka, wallahi ba zamu sake ba, mun tuba mun koma ga Allah, a iya hakan ma ai kin koya mana hankali, dan Allah ki buɗe".



Duk abin da ke faruwa a kunnen Sooraj wanda ke tsaye a bakin ƙofa har izuwa wannan lokaci.



Furzar da iska Zahra ta yi waje ta ce. "Zan barku ku tafi ne kawai saboda kun haɗa ni da Allah, amma da ba dan haka ba da saikun sake duk abinda ku ka yi".


Kallonta suka yi a gajiye suka ce. "Mun gode Aunty Zahra".


Taɓe baki Zahra ta yi ta ce. "Tohh!, yau an kira ni da sunaye kala-kala, wai yau ni na zama Aunty Zahra, harda su Hajiya Zahra, kwa ji da shi chan ta matse muku".


Ta faɗa tana mai nufar hanyar waje domin ta buɗe ƙofan. Ganin hakan ya sa suka tawo a guje.


Tsayawa Zahra ta yi tana mai kallonsu ta ce. "Kada ku fusata ni fa na fasa buɗe ɗakin".


Da sauri kowanensu ya ja da baya.

Ƙarasawa bakin ƙofan ta yi kana ta saka maƙullin a jiki sannan ta buɗe musu ƙofan. Take suka haɗa ido da Sooraj wanda ke tsaye ƙeƙam ya harɗe hannuwansa a ƙirji.


Da sauri su Gimbiya Saratu suka zo fita. Nan suka ci karo da Sooraj. Kallonsu Sooraj ya yi yana mai yi musu kallon ƙurilla. Ya ce. "Mene ne wannan yarinyar ta aikata muku?".

Shiru kowanensu ya yi yayin da suka ji kunyar furta cewa Zahra ta sa su aiki. Washe haƙora Gimbiya Talatu ta yi ta ce. "Bakomai kawai dai muna ciki muna hira ne, gaskiya Zahra yarinyar kirki ce, domin ta yi mana tarba mai kyau". Ta faɗa suna mai kallon junansu.


Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Ya naga jikin kowannenku ya yi datti?".

Murmushi Samira ta yi ta ce. "Yahya fa bakomai wasa kawai fa muka yi, kasan muɗin ne har yanzu muna ji da yarinta".


Ganin hankalin shi ya karkata izuwa kan Zahra ya sa su saurin barin wajan.


Ƙarasawa inda Zahra ke tsaye Sooraj ya yi, yayin da yaje daff da ita har numfashin kowanensu na bugan na wani.


Take ta ga fuskarsa ta chanza izuwa maƙurar ɓaccin rai. Da sauri Zahra ta ja da baya, ganin cewa zai iya aikata mata komai ya sa ta juya da zimmar shige wa ciki.


Da sauri ya janyo hannunta. Take ta faɗa kan ƙirjinsa. Saurin ɗaga ta yi daga jikinsa sannan ya kwashe ta da lafiyayyun maruka har guda biyu.


Dafe ƙuncinta Zahra ta yi yayin da idanunta suka kaɗa suka yi ja.


Shigar da ita yayi ɗakin nata sannan ya shaƙe mata wuya cikin lion voice ɗin sa ya ce. "Wato abinda ki ka yi mana na abinci ma bai ishe ki ba, sai kin ja su ɗakin ki kin sa su abin da basu yi niya ba ko, to wallahi a yau zan koya miki hankali, harma na sa a kira ki, kice min ba za ki zo ba, lallai na yarda wuyanki ya isa yanka, na niyar rabuwa da ke amma ganin abin da ki ka aikata wa ƴan uwana da gimbiyoyi ya sa saina huƙunta ki". Ya faɗa yana mai ƙara shaƙe wa Zahra wuya.


Kakari Zahra ta fara yi, da sauri ta cire hannunsa daga wuyanta. Tari ta fara yi. Kallonsa ta yi ta ce. "Me ya sa za ka tambaye ni?, kafin ka tambaye ni kaje ka fara tambayar su mene ne suka zo aikata min, zuwa suka yi suka ce za su dake ni, kenen ni naje na same su na jawo su nan?, nayi ƙoƙarin ganar da su cewa suyi wa kansu faɗa su koma amma suka yi kunnen uwar shegu suka ƙi tafiya, kenen sai kace laifi na ne?".


Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Me ya sa to za ki saka su wanki shara harda wankin toilet sannan ki sa su Gimbiya Saratu suyi miki tausa bayan kuma ke ƴar aiki ce.


Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Su da ma ba iyayenka ba kaji haushin abinda nayi musu, kai ka san abinda su biyar ɗin nan suke aikata wa Mami da baka nan?, haka za su saka ta shara da aiki susa ta wanki".


Ɗago da idanuwansa Sooraj ya yi wanda suka kaɗa suka yi jajir ya ce. "Mahaifiyar tawa suke yi wa hakan?, me ya sa ki ka barsu suka fita?".



Amsa Zahra ta bashi da cewa. "Saboda sun roƙe ni ne shi ya sa".

Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Tabbas yau sai sun ɗanɗana kuɗarsu". Ya faɗa yana mai fice wa daga cikin ɗakin Zahra. Ganin hakan ya sa Zahra ta yi saurin bin bayansa".









*********************
Amrah kuwa kidnapper's ɗin da suka sace ta basu nufi ko ina da ita ba sai wani ƙatoton gidan kango wanda ke tsakiyar jeji. Chan na hango ta an ɗaɗɗaure ta da igiya. Ƙoƙarin kunce kanta take amma hakan ya cutura. Kallonsu ta yi da rinannun idanuwanta cikin ƙaramin muryarta ta ce. "Ku kunce ni". Ta faɗa cikin jin raɗaɗi.



Ɗaya daga cikin su ne ya kira gov. Musa yana mai zayyane masa cewa aiki ya kammala. Murmushi gov. Musa ya yi ya ce. "Ku wuce da ita Lagos idan ya

Please Login or Register in order to submit comment