Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rashin sa'a kuwa igiyar ta tsinƙe. Nan take su Ramlat suka saki ihuu domin kuwa Umar yana shirin faɗo wa ne daga saman bishiyan.


Ganin yana ƙoƙarin faɗi ƙasa ya sa Amrah saurin riƙe masa hannu yayin da ta fara jan shi kan bishiyar. Hawa da shi ta yi kan bishiyar yayin da Umar ya shiga sauke ajiyan zuciya.


Kallonta ya yi sannan ta ce. "Maza zo mu sauka ƙasa, bana son wani abu ya same ki, za ki iya faɗo wa ki karye".


Girgiza kai Amrah ta yi. Babu zato ya ga ta dira ƙasa ba tare da tsoro ba.

Zaro idanuwa waje gaba ɗaya suka yi ganin yadda ta dira ba tare da wani tsoro ba.


Furzar da iska mai zafi Umar ya yi ciki ransa ta ce. "To ta ina zan fara sauka daga kan bishiyar nan?, hanya ban jawo ka kaina ba kuwa?".


Kallon saman bishiyar Amrah ta yi sannan ta yi mai nuni da ya sauko.


Ba tare da wani tsoro ba Umar ya fara bi ta jikin bishiyar yana sauko wa a hankali.

Kai hannunsa Umar ya yi domin riƙe bishiyar sosai. Cikin rashin sa'a hannun sa ya suɓuce ya tafi ƙasa daga kan bishiyar.



"Yahya Umar!". Gaba ɗaya suka furta.


Ganin ya kusan faɗo wa ya sa Amrah ta buga tsalle tamkar ƴar biri tare da chafko Umar sannan ta ajiye shi ƙasa".


Sauke ajiyan zuciya suka shiga yi tare da yin hamdala.



Kallon Amrah su Khairiya suka tsaya yi sannan suka ce. "Wannan ita ce ma mace mai kamar maza, irin wannan ƙarfi haka, daga gani ƴar daji ce".




************
"Ta ya ya hakan za ta kasance?, farko na shiga room 8 na ga Amrah q ciki, bayan na kuma koma wa cikin room ɗin da na baro Amrah na kuma ganinta a ciki. Tabbas babu ta yacce hakan zai yiwu dole dai mutum biyu na gani. Amrah green eyes ne da ita, sannan kuma ƴaƴan Mrs Laila da na sani mai green eyes ne sai blue eyes, dole dai ta room 8 blue eyes ne da ita. Idan kuwa har da gaske ne blue eyes ne da ita to babu tantama ƴaƴan Mrs Laila ne".


Aka Nurse Nadiya ta shiga yin magana ita ɗaya kamar zautacciya.




**********
*Daji*.
Babu abin da ka ke gani a wajan sai mata wanda aka ɗaɗɗaure musu hannu da baki. Kallo ɗaya za ka yi musu ka tabbatar da cewa ba ƙaramin jigata suka yi ba. Yayinda ɓangare guda allurori ne a ƙasa wanda aka yi musu domin a kawar musu da tunani. Kuka sosai suke yi. Ɓangare daya kuma maza ne hannunsu riƙe da bindigogi yayin da fuskokinsu gaba ɗaya yake a rufe.

Baka iya ganin komai na fuskarsu sai iya ƙwayar idanuwansu.



"Your excellence, matan da muka yi kidnapping yanzu za su kai kumanin 250. Yanzu muna jiran cewar ka ne domin a je a siyar da su a kasuwa, za'a mu yi safarar su ne zuwa ƙasashen waje yayin da kai kuma kuɗaɗe ne kawai za su dinga shigo maka".


Murmushi mahaifin Umar ya yi sannan ya ce. "Well done guy's, aikin ku na kyau yadda ya kamata. Maza ku sa su a Bus, zan saka a ƙaro muku bus domin Bus ɗaya ba zai isa ba. Sannan kuma kamar yadda muke yi abun nan cikin sirri bana son ɗana da kuma ƴan sanda su sani, domin idan suka sani abun ba zai yi min daɗi ba".


"Yes Sir". Mutumi ya faɗa.


Ɗaya daga cikin matan wajan ne ta yi nasarar kunce kanta da kuma kunce bakin ta. Zumbur ta miƙe tsaye tare da kallon Gov. Musa Muhammad sannan ya ce.


"Kai mugu azzalumi, ka sani cewa ƙarshen ka ba zai yi kyau ba, kana ɗaukar mu da ƴaƴan mu wanda muka damƙa maka su a matsayin amana kana safarar su izuwa ƙasashen waje". Duban kanta dattijuwar ta yi tare da tsugunna kan gwiwowinta ta ce. "Da wannan hannun nawa na ɗauki dutse na bugi Mrs Laila da shi. Tabbas na aikata kuskure, nayi zaton Mrs Laila ita ce muguwa ashe kaine asalin tantiri, ka ɓata mata suna a idanun duniya, ka sani cewa koda mun barka Allah ba zai barka ba. Kuma ka sani cewa Allah saiya tona maka asiri".



Kallonta Gov. Musa Muhammad ya yi tare da kwashe wa da dariya.




***********
Ɓangaren Zahra kuwa bayan anyi mata treatment ta samu bacci ya ɗebe ta. Saida ta ɗau hawanni biyu tana bacci kana daga bisani ta buɗe idanuwanta.


Nan take idanuwanta suka sauka a kan mahaukaciyar da ta gani kwanaki.


Miƙe wa ta yi zaune tana mai kallon matar da ke zaune kusa da ita.

Shafa fuskarta mahaukaciyar ta yi murmushi ɗauke kan fuskar ta.


Lokaci ɗaya Zahra ta ji ƙaunar matar ya shiga ranta ba tare da sani dalilin hakan ba.


Murmushi Zahra ta yi sannan ta ce. "Wace ce ke?, me ya sa a koda yaushe ki ka ƙoƙarin zuwa in da nake?, shin kin san ni ne?".


Girgiza kai kawai mahaukaciyar ta yi.


Shigowa likitoci suka yi yayin da suka kama hannun mahaukaciyar domi fitar da ita. Fuffuzgewa mahaukaciyar ta fara yi.

Kallonsu Zahra ta yi sannan ta ce. "ku ƙyale ta mana ya za ku wani kamata kamar yarinya za ku fita da ita, wannan sam ba adalci ba ne".


Kallonta ɗaya daga cikin likitocin ya yi sannan ya ce. "Ita ɗin fa mahaukaciya ce, yanzu shekaru ashirin kenen tana cikin wannan asibitin. Kuma yanzu aka ma magani zamu je mu ba ta bawai cutar da ita zamu yi ba".


Kallonsu Zahra ta yi ta ce. "To kuyi mata mana a hankali bawai sai kun dinga janta ba, yanzu da wannan mahaifiyar wani a cikin ku ne za ku ji dad'i ku ga wani yana janta a ƙasa kamar kayan wanki?. Maza ku cika ta kafin na ɓata muku rai". Ta faɗa ranta a matuƙar ɓace.



💃💃💃💃💃💃💃💃

COMMENTS, LIKE, AND SHARE FISABILILLAHI 🙏 🙏 🙏



ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B
(Zinariyar Jajirtattu)

https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g




*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐.
Daji 🌲
Magarƙama🏢 da kuma
Birni🏙️

WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝♀️Jajirtattu)

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 2️⃣9️⃣▶️3️⃣0️⃣
*_________________________________________________*
"Kinga malama muna kan aikin mu ne, ita ɗin mara lafiya ce kuma nauyin kula da lafiyarta yana rataye a wayar mu ne , don aka Please ki bar mu muyi aikin mu. Ke mene ne ma naki a cikin tun da ita ɗin ba ɗaya daga cikin dangin ki ba ce ko ko kuma ince ita ɗin ba mahaifiyar ki bace don aka ki ƙyale mu". Ɗaya daga cikin su ya faɗa yayin da suka fitar da ita daga ɗakin.


Ajiyan zuciya Zahra ta sauke!, sannan ta ce. "Kuma fa maganar sa aka ne, me ya sa nake nuna damuwa ta sosai a kan matar?, sa'anan kuma me ya sa naji ta shiga raina sosai?". Basar wa ta yi sannan ta ce. "Ki basar kawai, naji ta shiga raina ne kawai". Aka ta cigaba da magana ita ɗaya.


Miƙe wa tsaye ta yi tare da fizge drip ɗin da aka saka mata. Ya mutse fuska ta yi ganin yadda jini ke fita a saitin in da ta fizge drip ɗin. Sannan ta ɗauki cotton wool da ke ajiye kan table ta saka a wajan. Kallon taga ta yi ta waje ta ga mutane na fice da shige.


"Ya kamata na tafi daga nan". Ta faɗa tana mai dafa cikin ta da sauri jin yadda yake murɗa mata.


"Wayyo ni Fatima Zahra, yanzu me zan ci?, gashi ko biyar bana magani, ya kamata na tafi daga nan wajan". Ta faɗa tana mai fice wa daga cikin ɗakin.



***************
Cikin masarauta kuwa, ko ina ka kalla tarin jama'a ne, tare da fadawa a tsatsaye. Yayin da kowa ke riƙe da kwanon abincin. Junaid ne zaune gefe ɗaya yayin da gefensa kuwa tarin buhun shinkafa. Babu abin da yake sai faman miƙa wa jama'a kayan abinci. Al'adar masarautar kenen a duk wata ana sadakar avinci tare da kuɗaɗe ga talakawa marasa ƙarfi.


Fitowa mai martaba ya yi. Nan take mutane suka fara kwasar gaisuwa tare da yi masa kirari. Zama ya yi kan kujera kusa da Junaid yayin da ya cigaba da zuba ido ga abin da Junaid yake yi don ya sanshi da albazaranci.




***********
Kallonta Gov. Musa Muhammad ya yi sannan ya ce. "Au aba da gaske?, sune za su kawo ƙarshen nawa?, gaskiya kina da abin dariya. To ki sani kafin ma su san cewa ni ne na wargaza su nayi sanadin rabuwarsu izuwa gurare daban-daban zan gama da su. Don aka ba zan kashe ku ba yanzu, domin idanuwan ku ya gane muku abin da zan aikata, zan sa ne a fitar min da ku daga wannan ƙasar gaba ɗaya". Ya ƙarashe maganar yana mai kallon ɗaya daga cikin yaran nasa sannan ya ce. "Maza ku saka su a mota ku tafi da su, ni yanzu zan wuce gida".


"Done". Suka furta gaba ɗaya.



Shiga cikin motarsa Gov. Musa Muhammad ya yi yayin da jami'an sa suka ja mota tare da barin cikin dajin baki ɗaya.



********
"Habib wai me yake damun yarinyar ka Safeera ne?". Cewar Grandpa.


Amsa Daddy ya ba shi da cewa. "Wallahi Abba nima ban sani ba, na rasa me yake damunta, aka ma lokacin da muke a America ta faɗi kasa saida muka zo nan Nigeria sannan ta buɗe idanuwanta. Aliyu ya ce min ko Aljanu ne da ita, amma ni samm ban yarda ƴata tana da aljanu ba, ban san mene ne abin yi ba".


Sauke ajiyan zuciya gaba ki ɗaya suka yi sannan suka ce. "Dole dai akwai wani abu a ƙasa, babu ta yadda za ta dinga faɗuwa aka kurun ba tare da wani ya yi mata abu ba". Cewar Grandma.


Gyara zamansa Grandpa ya yi kan wheel chair sannan ya ce. "Maza ku zo muje wajan wani tsohon aboki na a chan wani ƙauye, shi ɗin babban malamin ruƙiya ne, aljanu, mayu da sheɗanu tsoronsa suke dole muje mu kawo sa da kannu domin ya duba ta. na san shi zai san koma mene ne yake damunta". Grandpa ya faɗa tare da ƙwalla wa Aliyu kira. Nan Aliyu ya fito daga ɗakin.


Kallon Aliyu Grandpa ya yi sannan ya ce. "Aliyu zamu fita yanzu, zamu je mu ɗauko maganin ruƙiya mu kawo domin sanin meke damun Safeera. Don aka ka zauna ka kula da Safeera mu zamu je mu dawo, su Zuwaira basua nan sun tafi makaranta don aka na baka amanar Safeera idan ka ɓata mata rai sai nayi maganinka".


Girgiza kai Aliyu kawai ya yi sannan ya ce. "Tom shi ke nen Kaka sai kun dawo". Ya faɗa yana mai koma wa ɗaki da Safeera take.



Fita su grandma suka yi tare da shirya wa suka shiga cikin motocin gidan sannan suka fice daga gidan. Kai tsaye suka nufi hanyar Gujingu.

********
Koma wa Aliyu ya yi kan kujerar da ke fuskantar Safeera sannan ya cigaba da zuba mata idanuwansa.


A hankali Safeera ta fara buɗe idanuwanta a yayin da a ƙarshe ta yi nasarar buɗe su bako ɗaya tare da sauke su kan Aliyu wanda ya zuba mata idanuwa sai kallonta yake kamar wani maye.


Zumbur ta miƙe zaune sannan ta ce. "Ya dai mene ne ka ke yi tare da ni?, where is my Mom?".


Furzar da iska Aliyu ya yi ya ce. "Sun tafi wajan malamin ruƙiya domin a kawo shi ya yi miki ruƙiya aljanun da ke jikin ki su fita".


Nan take ran Safeera ya ɓaci ta ce. "Kamar ya Aljanu?, ni ce mai aljanu?, koda yake ba laifin ku ba ne ba".


Taɓe baki Aliyu ya yi ya ce. "Ke Safra ki ke da suna ko me, ki dinga sarrafa harshen ki domin ni hannu na rawa yake zan iya bugar bakin ki da shi".


Cikin jin haushi Safeera ta miƙe tsaye sannan ta ce. "Ka ga malam sunana Safeera ne ba Safra ba idan ba za ka iya cewa Safeera ba ka kira ni da nickname ɗina wato Diana. Sannan kuma da ka ke cewa za ka buge baki na kai a waye za ka ce za ka buge baki na?, wallahi ka fita daga cikin harka ta na gaya maka. Kuma wallahi su Mom na dawo wa zamu tattara komai namu mu bar gidan nan, dan ni gaskiya ba zan iya rayuwar wannan ƙasar ba".


Ta faɗa tana mai ƙoƙarin fita daga cikin. Da sauri Aliyu ya fizgo ta jikinsa tare da matse ta ya ce. "Kada ki manta ni da ke ne kaɗai a gidan nan, idan ki ka yi min rashin kunya zan zane ki kuma na zane banzam sannan shi wannan ƙasar da ki ka ce bakya so na ga dai iyayen ki ƴan nan ne ba'a ƴan chan ƙasar ba, don aka makntain your word's okay".

Cire jikinta ta yi daga na shi sannan ta ce. "Kada ka sake ɗora hannun ka a jiki na, domin kai ɗin ba miji na ba ne okay, you don't have the right to touch a responsible lady like me okay, please don't add to my anger this afternoon".


Murmushi Aliyu ya yi tare da janyo ta sannan ya samu bakinta tare da kama wa ya fara murɗawa. Nan take ta saki ɗan ƙaramin ƙara na raɗaɗi!.

"Leave me alone". Ta faɗa hawaye na bin ƙuncinta.


Murmushi Aliyu ya yi ya ce. "In fa ki ka ce za ki yi jayayya da ni sai dai kici wuya, kuma da ki ke wani ikirarin cewa ni ba mijin ki ba ne, na san da hakan ai amma kuma an your future husband so ya kamata tun yanzu na fara saita ki kafin ki shiga gida na". Ya faɗa tare da sakin leɓenta wanda suka ƙara rinewa suka yi jajir saboda jan da Aliyu ya yi musu.



Riƙe leɓenta Safeera ta yi sannan ta ce. "Wallahi Allah ya kiyaye na zamo matar ka, kuma in dai suka dawo saina faɗa wa Grandma abin da kayo min kuma wallahi bashi ka ɗauka domi saina rama". Ta faɗa tare da fice wa daga ciki ɗakin.


Chan ta samu guri a parlour ta zauna tare da kunna tashar Bollywood ta fara kallo. Saida ta ɗau lokaci sosai tana kallonta cikin nishaɗi hankalinta kwance take kallon abinta.
Fitowa Aliyu ya yi tare da samun guri ya zauna a parlourn sannan ya ɗauki remote tare da chanza tashar izuwa tashar Ball.


Nan take ran Safeera ya ɓaci dubansa ta yi ta ce. "A kan mene ne za ka zo ka wani chanza min channel ɗin da nake kallo?, maza ka maida min abuna. Kai na fahimci cewa baka son zaman lafiya kuma ni ma zan nuna maka cewa nafi ka rashin son zaman lafiya, maza ka mayar min".


Murmushi Aliyu ya yi ya ce. "To Mama ɗanki zai yi kamar yadda ki ka ce". Ya faɗa tare da sakin wani killer smile sannan ya ce. "Nan ɗin ba gidan ku ba ne balle ki saka wani doka ko order okay, nan ɗin gidan mu ne, don aka be careful".




**************
Jan kumatun Amrah Khairiya ta yi sannan ta ja hannunta suka shigar da su part ɗin su. Nan suka cire mata grasses ɗin jikin ta tare da ɗaura mata towel sannan suka nufi toilet da ita. Nan suka shiga wanke mata gashin kanta wanda suka kwanta har gadon bayanta. da hair oils masu ƙamshi.

Bayan sun gama wanke mata tass ya fita sai sheƙi yake. Ne suka fara nunnu na mata yadda za ta yi amfani da toilet ɗin ɗakin.


Ita ko Amrah kawai kallonsu take domin kuwa ita ba ta san ta ian za ta fara amfani da irin wannan toilet ɗin ba.


Fita suka yi suka barta tsaye a cikin toilet ɗin. Bin ko ina ta yi da kallo.

Sannan ta fara tattaɓa socket ɗin toilet. Nan hannunta ya kaiga water heater ɗin toilet ɗin. Ba tare ta san mene ne ba ta danna. Nan ruwa ya fara zubo wa kanta. Zaro idanuwa ta yi waje jin ruwa mai matuƙar zafin gaske. Da sauri ta fita daga cikin bandaƙi tana mai sauke ajiyan zuciya.

Zumbur su Khairiya da Ramlat suka miƙe ganin yadda ta fito daga cikin toilet a guje.


"Mene ne ya faru kuma Amrah?". Ramlat ta tambaya.


Kawar da kai gefe Amrah ta yi sannan ta nuna toilet. Maida kallonsu suka yi cikin toilet sannan suka ce "Shin baki gane bayanin da muka yi miki ba ne?".


Girgiza musu kai ta yi da alamun "Eh".


Nan suka koma toilet ɗin tare da sake nunnuna mata yadda za ta yi amfani da shi. Bayan sun gama suka fita suka barta cikin toilet ɗin.


Nan dai wuya da ƙyar Amrah ta yi wanka.

Ko 1minute ba ta yi ba ta fito daga cikin toilet ɗin. Mamaki ne ya kama su ganin cikin ƙanƙanin lokaci har ta gama wankan.


Nan Khairiya ta ɗauko mata ɗaya daga cikin abayoyinta wanda ke dark blue gaba ɗayansa storn ne. Saka mata su suka yi tare da yi mata kwalliya ta fito ta yi kyau kamar ba ita ba.


Kallon ta suka yi yayin da su biyun suka haɗa baki wajan faɗin. "Wow you look awesome and gorgeous, you are so beautiful. Kin ganki kuwa kamar ƴar Arab".


Jinsu kawai take yi domin kuwa ba su ne a gabanta ba so take ta ga ƴan uwanta namun jeji.





***********
Zahra na fita daga cikin asibitin ta fara tafiya ba tare da ta san in da take cilla ƙafafunta ba.


"Ni wallahi rayuwar magarƙamar ma yafi dad'i, ya zama dole na tara kuɗi na koma Jigawa, mutum ai sai yunwa ta kashe shi ma bai sani ba". Ta ƙarashe maganar tare da tsaya wa. Nan ta tuna da abin da ya faru ɗazu tsakaninta da ƴan daba.


"Da a ce zan sake haɗuwa da ku ko da sai kun shinshina takashin ku". Ta faɗa tana mai waige-waige kan titi. Chan ta hangi wata dattijuwa.


Tana ƙoƙarin saka kaya cikin mota amma hakan ya cutura.


Tausayin matar ne ya kamata hakan ya sa ta nufi in da matar take da sauri sannan ta taimaka wa matar ta saka kayan nata a cikin boot ɗin motar.


Kallonta matar ta yi sannan ta ce. "Gaskiya naji dad'i da irin wannan taimakon da ki ka yi min, don aka bara na baki kuɗi".


Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "A'a ni bana taimaka miki ba ne domin ki biyan, nayi ne saboda Allah don aka kawai ki riƙe kuɗin ki". Ta ƙarashe maganar tana mai dafa cikin ta wanda har izuwa wannan lokacin bai daina murɗa mata ba.


Kallonta matar ta yi sannan ta ce. "Amma na ga kamar kuɗin zai yi miki amfani, ya kamata ki karɓa".


Kuma girgiza mata kai Zahra ta yi ta ce. "A'a ki barshi wallahi, ni kawai abin da za ki bani ki burge ni a halin yanzu dai shi ne abinci, domin tun ɗazu ƴaƴan ciki na suke ta faman kuka, ina son na saka su dariya ta hanyar cin abinci".


Dariya dattijuwar ta yi sannan ta ce. "Gaskiya ne, karki damu wannan ba mataala ba ne, muje fada akwai abinci kala-kala iri-iri da ban da ban duk wanda ki ke so shi za'a baki, kuma in dai kina buƙatar aiki ma ni zan baki".


Washe baki Zahra ta yi sannan ta ce. "Wallahi kamar kin san ina neman kuɗin da zan koma garin mu. Kin ga saina dinga yi mini aiki ki dinga biya na har na tara ƙuɗaɗe na koma".


Murmushi matar ta yi sannan ta ce. "Mene ne sunanki?".


Amsa Zahra ta ba ya da cewa. "Sunana Fatima amma ana kira na da Zahra".


Kuma kallonta matar ta yi ta ce. "Nice name, faɗa min nawa ki ke buƙata ni zan baki sai ki koma gida da shi".


Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "A'a wallahi, nafi son nayi aiki da gumi na na samu kuɗi na tafi saina fi jin daɗi domin kuwa nima zan dinga tuna wa cewa nayi abun kirki".


Murmushi matar ta yi ta ce. "To shiga mota muje ko".

Ba tare da jayayya ba Zahra ta shiga mota.

Nan matar ta shiga motar tare da jan motan suka bar harabar wajan.

Kallon matar Zahra ta yi ta ce. "Shin baki da ɗana ne wanda zai dinga tuƙa ki?, naga kamar girma ya kama ki, idan ma babu ya kamata ki nemi driver".


Kallonta matar ta yi ta ce. "Ina da ɗa kuma ina da driver, shi drivern nawa bashi da lafiya ne ya koma ƙauyen su. Shi kuma ɗana ƙwalli ɗaya baya ƙasar nan yana ƙasar India shi ɗin babban likita ne sunansa Sooraj ina matuƙar alfahari da shi".


"Sooraj!". Zahra ta maimaita sunan cikin ranta. Taɓe baki ta yi sannan ta ce. "Shin ba zai dawo ba ne a chan zai zauna?".


Amsa matar ta ba ta da cewa. "Zai dawo ƙarshen month ɗin nan in sha Allahu".


Sosai suka dinga hira da Zahra kamar sun san juna a baya. Nan matar ta ji Zahra ta shiga ranta sosai.


Saida suka ɗau lokaci kafin daga bisani suka isa cikin masarauta.


Parking matar ta yi tare da fita daga cikin motan. Nan take fadawa da jama'a suka fara kwasar gaisuwa.


Mamaki ne ya kama Zahra ganin tarin jama'a a wajan. Zololo ta yi tana kallon masarautar.


"Wayyo ai wannan shi ake kira aljannar duniya, shi kuma nan ɗin ina ne?". Zahra ta tambayi kanta tare da fita daga cikin motan.


Junaid kuwa tashi ya yi ya bar fadawan su xigaba da sadakan sannan ya nufi hanyar parking space.



Nufo in da su Zahra suke ya yi. Nan take suka haɗa ido a tare.


Take gaban Junaid ya faɗi!, ganin Zahra a wannan lokacin. Da sauri ya nufi in da su Zahra suke sannan ya gaidar da dattijuwar. Amsa wa ta yi ta ce. "Junaid ga sabuwar ƴar aikin da muka samu a masarautar mu, fatan dai ta yi maka ko".


Kallon sani Zahra ta yi masa sannan ta cem "Ba kaine wannan yariman ba mai jiji da kai?, tabbas dai kaine, wai dama Aunty wannan ɗanki ne?".


Murmushi natar ta yi ta ce. "A'a step son ɗina ne amma shima kamar ɗa yake a guri na".


Kallonta Junaid ya yi ciki ɓacin rai sannan ya maida kallonsa kan matar ya ce. "Mami bamua da buƙatar ƴar aiki, wanda muke da su sun isa. Ke kuma". Ya faɗa yana mai maida kallonsa kan Zahra ya ce. "Bani maƙullin da ki ka ɗauka a aljihu na, sam ba za ki yi mana aiki a wannan masarautar ba".


Kallonsa Mami ta yi ta ce. "Dama kun san juna ne Junaid?, me ya sa ba za ta yi mana aiki ba?".


Amsa Junaid ya ba ta da cewa. "saboda ita ɗin ɓarauniya ce, ta sace min maƙullin ɗaki tare da kuɗaɗen aljihu na, dama kana ganin ta ka san gadon sata ta yi, ɓarauniyar banza kawai maza ki dawo min da maƙulli na ni na bar miki kuɗaɗen".


Nan take fuskar Zahra ya chanza daga walwalah izuwa ɓacin rai yayin da idanuwanta suka kaɗa suka yi ja. Matsar da Mami ta yi gefe sannan ta fara tunkarar Junaid a matuƙar fusa ce ta ce. "Wace ce ɓarauniyar?, ni ɗin?, wallahi kayi sa'ar cewa nan ɗin gidan ku ne, da ba dan aka ba uhmmm, da yau saika san da cewa Allah ɗaya ne, kuma maƙullin ƙarfi ya cinye idan za ka iya ƙwata ka zo ka ƙwata, kuma gidan nan na shigo ta kenen ba zan fita ba har saina gadamar fita don aka ka shirya zama da tantiriya domin kuwa zama da ni sai wanda ya shirya".



Nan hankulan jama'a da na sarki ya karkata izuwa kansu Zahra.






*JUNAID KA BI A HANKALI FA, ZAHRA BA KANWALLASA BACE BA😂. BA TA ƊAUKAR RAINI, IDAN BA KIYAYE BA ZA TA YI MAGANIN KA*.💃💃💃



MANAGE PAGE PLEASE.
COMMENTS, LIKE & SHARE FISABILILLAHI 🙏 🙏 🙏


ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞💞
(Zinariyar Jajirtattu).

Follow the 🌺🌎A'ISHA M.B🌹 HAUSA NOVELS 📚 WORLD 🌎 📚💗💖 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g




*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐.
Daji 🌲
Magarƙama🏢 da kuma
Birni🏙️

WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝♀️Jajirtattu)

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma

Please Login or Register in order to submit comment