Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa Umar ya nufa tare da shiga toilet sannan ya kunna wa kansa shawa. Rintse idanuwansa ya yi a sa'inda ruwan ke zuba jikinsa. Tunanin abin da ya wakana ɗazu a shopping mall ne ya faɗo masa. Nan take ya buɗe idanuwansa.






Ɓangaren su Amrah kuwa guri suka samu a parlour suka zauna. Yayin da Ramlat da Khairiya suka shiga kitchen domin su ɗora abincin dinner.


Amrah kuwa kwanciya ta yi kan kujera idanuwanta a kan silin.



Fitowa Gov. Musa ya yi nan take idanunsa suka sauka a kan Amrah.


Murmushi ya saki kana ya nufi in da take. Tare da tsayawa a kanta.



Ganin mutum zololo a kanta ya sa Amrah saurin miƙe wa tsaye tare da ja da baya.



Murmushi Abba ya yi sannan ya ce. "Ke kuwa ya da firgita sai ka ce kinga wani dodo, ina so na faɗa miki gobe ne zagoyowar haihuwar ɗana Umar don haka gobe akwai babban shagali kinji ko, don haka ina so ki shirya kema kike. Ba zan faɗa masa ba sai dai muyi masa ba za ta".



Ya faɗa yana mai shige wa ɗakinsa.


Fitowa Umar ya yi ya tarar da Amrah tsaye gaba ɗaya ta yi wani iri.


Kallonta ya yi sannan ya ce. "Amrah me ya faru?".


Girgiza kai Amrah ta yi alamun babu komai.


Bayan su Khairiya sun gama shirya dinner me suka fito da abinci tare da jera wa kan dining.


Nan suka kira Abba tare da jami'ai sannan suka basu nasu abincin.


Bayan sun gama cin abinci ne kowa ya wuce part ɗin sa. Yayin da ita ma Amrah ta nufi garden tare da awa kan bishiya ta yi kwanciyar ta ba tare da ta bar su Umar sun lura da fitar ta ba.





Washe gari da sassafe Abba ya sa aka ƙawata gidan da kayan al'atu tare da flowers masu kyau. Nan ya sa haka kawo masa cake ɗin da ya kashe makuɗan kuɗaɗe domin a yi shi.



Gaba ɗaya ƴan majalisa tare da govnors daga kowane gari sun cika gidan babu abin da ka ke gani sai shige da ficen mutane. Yayin da harabar gidan ya zagaye da sojoji tare da police men. Motoci kawai ka ke harba da su marasa iyaka.



Bayan su Khairiya sun gama shirya wa ne. Suka tarar da cewa Amrah ba ta ɗakin su. Nan suka fuskanci cewa tana garden ne. Nan suka nufi garden yayin da suka sa ta sauka a kan bishiya nan suka nufi part ɗin su da ita yayin da suka sa ta yi wanka sannan suka shirya tsaff tsaff cikin Arabian gown wanda ya yi matuƙar fito da kyawunta.




Fitowa suka yi gaba ɗaya yayin da Dj ya zo sannan ya fara playing ɗin waka. Ba'ayi aune ba mutane suka cika gidan gaba ɗaya.




Umar kuwa bayan ya tashi daga bacci ne ya nufi toilet tare da taking bath ɗin shi sannan ya shirya domi zuwa wajan aiki.


Bayan ya gama shirya wa ne ya nufi hanyar waje. Yana buɗe ƙofa ya ga mutane a tsatsaye. Nan take Dj ya saki sauti yayin da suka fara yi masa wakar happy birthday.



Murmushi wanda ya fi kuka ciwo Umar ya saki tare da yi musu godiya sannan ya nufi hanyar waje domin ya tafi wajan aiki. Ganin hakan ya sa Abba ya sha gabansa sannan ya ce. "Umar ina kuma za ka je?".



Amsa Umar ya ba shi da cewa. "Zan je wajan aiki ne mana".


"Aba Umar kai baka ga party ɗin da na haɗa maka ba?, duk wannan fa nayi shi ne saboda kai. Ya kamata ka nuna kayi farin ciki ".



Sauke ajiyan zuciya Umar ya yi tare da nufar wajan cake ɗin sannan ya ɗauki ƙaramin wuƙa sannan ya fara yanyanka cake ɗin. Nan take su ministers da sauran govnors tare da jama'ar cikin gidan suka bishi da kallo.



Da sauri Amrah ta nufi in da yake tare da riƙe hannun Umar sannan ta girgiza masa kai. Ƙwace wuƙar ta yi daga hannunsa tare da dungure masa kai.



Shafa in da ta dungure masa Umar ya yi tare da sakin murmushi sannan ya ce. "Mene ne kuma?, kema bakya so na tafi wajan aiki ne?".


Gyaɗa kai ta yi alamun "Eh".


"Shi ke nen tom ba zan je ko ina ba kinji".


Nan take fari ciki ya lulluɓe fuskokin gaba ɗayansu.



Nan haka cigaba da shagali yayin da haka yanka cake kowa ya ci ya sha. Har ƙarfe takwas da rabi na dare suka kai ana shagali a cikin gidan. Harabar gidan suka cigaba da shagali wanda haka ƙawata shi da kayan more rayuwa.



Awa kan hall ɗin da Gov. Musa ya sa haka haɗa musamman saboda Umar. Umar ya hau kana ya gaida kowa na wajan. Sannan ya fara magana kamar haka. "Hello ladies and gentlemen, ina mai godiya da irin wannan ba za ta sa ku ka yi min, naji dad'i sosai Allah ya saka da alheri. Sannan shima mahaifina wato Gov. Musa Muhammad ina mao godiya da irin wannan babban shagalin da ya haɗa musamman saboda ni. Don haka ina godiya. Kuma sannan ina so na gabatar muku da wacce nake so muka nake muradi na aura wato Amrah".



Ya faɗa yana mai waige-waige. Da sauri su Khairiya suka au kan hall ɗin sannan suka sanar da Umar cewa Amrah ba ta cikin gidan.


Nan take Umar ya rikice da sauri ya sauka daga wajan yayin da shiga bin lungu da saƙo na gidan domin neman Amrah.



"Yahya Umarrrrr!!!". Gaba ɗaya suka ji an furta.


Juyowa Umar ya yi yana mai sauke idanunsa kan nata nan take ya yi mutuwar tsaye ganin cewar tabbas Amrah ita ce wacce ta kira sunansa ba wani ba.



Da mugun gudu ta nufo in da Umar yake domin kuwa babban ringlight da ke tsakiyar wajan na shirin faɗo masa.



Da mugun sauri ta nufi wajan sa tare da ture sa. Nan take ringlight na wajan ya faɗo mata a jiki.



Zaro idanuwa waje gaba ki ɗayansu suka yi take gaban Umar ya faɗi.



Faɗuwa Amrah ta yi tare da gangarawa ta faɗa cikin swimming pool ɗin harabar gidan. Umar bai yi wani tunani ba ya faɗa cikin swimming pool ɗin domin ceto Amrah.



💖💖💖❤🔥❤🔥💖💗💗


ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
(ZINARIYAR JAJIRTATTU)


Follow the 🌺🌎A'ISHA M.B🌹 HAUSA NOVELS 📚 WORLD 🌎 📚💗💖 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g




https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 3️⃣5️⃣▶️3️⃣6️⃣
*_________________________________________________*
Mintuna ƙalilan ya ɗauki Umar a cikin ruwan ya fito da Amrah.

Sauke ajiyan zuciya ya shiga yi babu gaggauta wa tare da maida kallonsa kan Amrah.

Da mamakin sa kuwa ya ga ta sakar masa murmushi kamar ba ita ce wacce ya shiga ruwa domin ceta ba.


Miƙe wa tsaye Umar ya yi a fusa ce tare da duban Amrah ya ce. "A kan me ya sa za ki salwantar da rayuwarki saboda ni?, kin san wane irin hali zan shiga idan wani abu ya same ki?, na ga alamun so ki ke sonki ya kashe ni ko?".


Ƙasa da kai Amrah ta yi ta ce. "Kayi haƙuri, ba zan sake ba".



Tsaki Umar ya ja. "Aikin banza kawai". Ya furta tare da barin wajan party ɗin baki ɗaya.


Gaba ɗaya mutanen wajan suka bishi da kallo. Zuwa in da Amrah take su Khairiya suka yi tare da kamo hannun Amrah domin su shiga ciki da ita.


Wafce hannunta Amrah ta yi daga na Khairiya kana ta nufi garden da gudu tare da hawa kan bishiya sannan ta kwanta.


Ganin Amrah ta nufi garden ya sa su Khairiya suka mara mata baya.


Kallon gaba ki ɗaya baƙin nasu Gov. Musa ya yi tare da basu haƙuri sannan ya sa haka rufe party ɗin. Nan take kowa ya watse.


Umar kuwa yana shiga cikin gida bai nufi ko ina ba sai ɗakin sa. Faɗa wa ya yi kan lallausar gadonsa tare da sakin ajiyan zuciya. Lumshe idanuwansa ya yi. Gaba ki ɗaya Amrah ce kawai ke yi masa gizo a cikin idanunsa. Nan take abin da ya faru ya faɗo masa. Zumbur ya miƙe zaune. Kana ya ce. "Ta ya ya ƙwayar idanunta suka iya sauya wa lokaci ɗaya?, am really confused!, ko dai mutum biyu ne". Girgiza kai ya yi ya ce. "No it can't be possible, ba zai yu su kasance su biyu ba, mybe ni ne ban gani ba sosai green ne ba blue ba".





*************************
Shiga cikin ɗakin Safeera Mom ta yi ta tarar da Safeera zaune kan kujera ta yi tagumi kamar wacce haka yi wa mutuwa.



Ƙarasawa in da take Mom ta yi tare da zama kusa da ita. Sannan ta dubeta ta ce. "Safira tunanin me ki ke?".


Ajiyan zuciya Safeera ta sauke sannan ta ce. "Babu komai Mom, kawai dai ni ina son na koma America ne, ina so na ci gaba da karatun lawyer please Mom. Am tired of this country I just want to go back".


Murmushin yaƙe Mom ta yi ta ce. "Ke kuwa Safira ba ana karatun law a Nigeria ba, sai kiyi abunki kawai a nan. Idan ya so ma kafin lokacin anyi engagement ɗin ku keda Aliyu.


Kawar da kanta Safeera ta yi gefe ta ce. "Ni fa ba zan yi aure yanzu ba, ni so nake na yi karatu bana son aure".


Girgiza kai Mom ta yi kana ta ce. "Ki sani cewa shi aure sunnar manzo Allah (SAW) ne. Kamar ta bakin mahaifin ki ko kina so ko bakya so sai an ɗaura miki aure da Aliyu kuma sai kin zauna. Duda cewar auren dole haramun ne amma na san kafin ma lokacin da za'a miki auren za ki fara son Aliyu kuma za ki ce na faɗa miki".



"Allah ya kiyaye, wallahi nafi ƙarfin shi". Safira ta furta tana mai yamutse fuska.


Miƙe wa tsaye Mom ta yi ta ce. "Lokaci zai zo da za ki yarda da maganar da na faɗa miki". Tana kaiwa nan ta fice ta bar mata ɗakin.



Ajiyan zuciya Safira ta sauke!, kana ta ce. "Koma dai mene ne saina koma ƙasar America wallahi". Ta faɗa tana mai shige wa toilet tare da ɗauro alwala sannan ta gabatar da sallah.





**************************
Zahra na fita kai tsaye part ɗin Mami ta nufa. Tana shiga ta tarar da Jakadiya tana yi wa Mami massaging ɗin ƙafarta.


Da sallama ta shige cikin ɗakin kana ta samu guri a ƙasa ta zauna.

Kallon Zahra Mami ta yi cikin farha ta ce. "Zahra kin gama aikin kenen".


Girgiza kai Zahra ta yi kana ta ce. "Eh Mami na gama sai kuma na gobe idan Allah ya kaimu da rai da lafiya".


Kallonta jakadiya ta yi ta ce. "Masha Allah gaskiya kin burge ni, kuma da alama ba za ki ɗauki raini ba. Ni sai nake ganin kina min kama da wata wallahi".


Yaƙe Zahra ta yi ta ce. "Su aba gaskiya ne, masha Allah hakan yy dama an ce kowane ɗan adam yana da mai kama da shi, ina ga mai kama da ni ɗin ne ki ka gani".


"Uhmmm!". Jakadiya ta yi kana ta maida kallonta ƙasa. "Kash". Ta furta sannan ta ce. "Gaba ɗaya na manta ban tawo da nail cutter daga part ɗin su Samira ba. Kuma sabo ne, bara naje na ɗauko".


Kaɗa kai Zahra ta yi ta ce. "Aba dai me ya sa za ki je ki ɗauko bayan ina zaune a nan wajan?, kada ki damu kiyi zaman ki kawai a nan zan je na ɗauko".


"Shi ke nen". Jakadiya ta furta.


Miƙe wa tsaye Zahra ta yi tare da nufae hanyar waje. Saida ta je daff da za ta fita ta ji muryar Mami na faɗin. "Zahra dakata".


Tsayawa chakk Zahra ta yi tare da maida kallonta kan Mami ta ce. "Mene ne Mami?".


Amsa Mami ta ba ta da cewa. "Babu komai, ina so in faɗa miki cewa idan ki ka je chan duk abin da za su yi miki kada ki tanka su dan Allah, bana son a kuma samun wani matsalar please and please".


Girgiza kai zahra ta yi kana ta ce. "In sha Allahu ba zan kula su ba".


Ta faɗa tana mai fice wa daga ɗakin. Kai tsaye in da ta ga su Samira sun nufa ɗazu ta nufa domin ɗauko nail cutter ɗin Mami.

Saida ta zo dai-dai ƙofar part ɗin su kana ta buɗe handle ɗin ƙofan ba ta yi wata-wata ba ta ƙusa kai ciki.


Take ta shaƙi hayakin da ya gauraye ilharin parlourn part ɗin su Samira. Tari Zahra ta fara yi tare da toshe hancin ta. Domin kuwa warin shisha ne kawai ke tashi a ɗakin.


Waige-waige Zahra ta fara yi. Nan take idanuwanta suka sauka a kansu Samira wanda ke faman zuƙan shisha. Dubanta suka yi tare da cewa. "Ya haka yi ne?, me kuma ya kawo ki ɗakin mu?".


Ƙasa da kai Zahra ta yi cikin jin takaicin abin da suke aikata wa.


Ɗaga kanta Zahra ta yi ta dube su ta ce. "Tirr da wannan rayuwa irin taku. Gaba ki ɗaya kun taso babu tsoron Allah a zuƙatan ku, wannan wace iriyar rayuwa ce?, kuna mata kuna shan hayaƙi wanda babu abin da take haifar wa sai cutarwa, Allah ya shirye ku. Ni duk ba wannan ba na zo ne duba nail cutter ɗin Mami yana ina?".



Dariya gaba ɗaya suka kwashe da shi. Yayin da Yusrah ta miƙe tare da zuwa daff da in da Zahra take sannan ta busa mata hayaƙin bakin ta.


Kawar da kanta Zahra ta yi gefe tare da ɗaga hannun da zimmar dirza bakin Yusrah a bango. Nan kawai furucin Mami suka faɗo mata da cewa duk abin da za su mata kada ta kuskure ta tanka musu.



Furzar da iska Zahra ta yi waje sannan ta ce. "Ni banzo wajan nan domin na takale ku ba, na zo ne saboda na nail cutter ɗin Mami".



Ɗaukar nail cutter ɗin da ke kan table Samira ta yi kana ta ce. "Gashi nan ba za'a bayar ba me za ki yi?".


Murmushi Zahra ta yi kana ta ce. "Ni babu abi da zan yi kawai ki bani nayi tafiya ta salin alin".


Miƙe wa tsaye Samira ta yi ta ce. "Na ce ba za'a bayar ba, kina ƴar aiki kina yi mana magana yadda ki ke so, to ki sani cewa ko uwark..........


Maganar Samira ce ta dakata sakamakon tsawar da Zahra ta daƙa mata wanda saida ya ratsa ilahirin ɗakin baki ɗaya.


Take tsoro ya cikashe zuciyoyin su baki ɗaya.


Cikin huci Zahra ta nuna Samira da ɗan yatsarta kana ta ce. "Duk abin da za ki yi to ya tsaya a kaina banda mahaifiyata. Idan kuwa ki ka kuskure ki ka yi sakin baki wajan furta magana mara daɗi kan uwata a ranar za ki san bambancin ƴar sarauta da kuma ƴar magarƙama. Maza miƙo min nail cutter ɗin kafin na ɓa ta muku rai".



Jiki na rawa Samira ta cilla wa Zahra nail cutter ɗin. Chafke wa Zahra ta yi sannan ta bi gaba dayansu da kallo tare da girgiza kai ta ce. "Na fuskanci cewa ba za ku iya zama da mutum cikin lafiya ba tare da wani hayaniya ba. Amma tun da haka ku ke so faɗuwa ta zo dai-dai da zama. Domin ni gyatumar ku ce a fannin rashin son zaman lafiya. Mu zuba mu gani, sai kun ɗanɗana wa aya zaƙin ta".



Tana kaiwa nan ta fice ta bar musu ɗakin.



Suna ganin ta fita suka sauke ajiyan zuciya.
Kallon Samira Fasma da Yusrah suka yi sannan suka ce. "Me ya sa za ki ba ta nail cutter ɗin?".


Amsa Samira ta basu da cewa. "Ta ya ya ba zan ba ta ba, kuna gani lokaci ɗaya yadda fuskarta ya canza kuma ku ce kada na ba ta nail cutter, wannan idan haka bar mu da ita tsaff za ta zane mu, don wallahi yadda nake ganin yanayin ta kamar ƴar daba ko in ce ƴar jagaliya".


Tsaki Fasma ta buga kana ta ce. "An dai ji kunya wallahi, wai a ce wannan ƴar talakawan ta zo har masarautar mu tana razana mu, gaba ɗaya ta ana mutane saƙat dole muyi wani abu domin yin maganin ta. Idan ba haka ba to ba za ta daina ba, dole mu koya mata hankali".


"Ƙwarai kuwa Fasma, maganar ki gaskiya ce dole mu koya mata hankali".






*************************
"Amrah maza ki sauko mu shiga ciki kinji". Cewar Ramlat. Girgiza kai Amrah ta yi kana ta ce. "Babu in da zani, ni kawai ku maida ni wajan ƴan uwa na, su nake son gani".



Dafe kanta Khairiya ta yi ta ce. "Shi ke nen zamu kaiki kinji. To sauko".



Girgiza kai Amrah ta yi alamun A'a.

Babu yadda suka iya haka suka koma ciki suka bar Amrah a kan bishiya.



**********
"Hello yallaɓai, mun samo matar da ka ce mu samu wannan malamar asibitin yanzu haka tana wajan mu a dajin da muka saba haɗuwa wajan yin harƙalla".


Murmushi Gov. Musa ya saki sannan ya ce. "That's great wannan good news ne ku bani nan da mintuna ashirin zan zo".


Yana kaiwa nan ya katse wayar. Yana sauke wayar ya ga kira ta kuma shigowa sai dai na wannan karan da private number haka kira.


Kallon screen ɗin wayar Gov. Musa ya yi cike da mamani yake bin wayar da kallo. Ɗaga wayar ya yi tareda saka wa a handsfree sannan ya ce. "Who's on the line?".


Ji ya yi an saki murmushi sannan ya ce. "Wato baka gane ni ba kenen, to MK ne, naji labarin cewa ka sa an sace nurse Nadiya saboda ta faɗa maka in da Mrs Laila take, sai dai kuma hakan ba zai yi aiki ba domin ita kanta ba ta san Laila na raye ba. Maza ka sa yaranka su sake ta idan kuma ba haka ba zan tona asirinka a wajan ɗanka, na san da cewa babu abin da kafi so a duniyar nan sama da ɗanka bayan ɗanka sai kuɗi ko, to ka sani cewa ni ɗin zan je na tona maka asiri na faɗa masa irin mahaifin da yake da shi".


Ɗan jimm gov. Musa ya yi daga bisani kuma ya babbake da wata mahaukaciyar dariya.


Nan take ya haɗe ransa tamkar bai taɓa dariya ba ya ce. "Ta ina za ka faɗa masa ko ni ɗin wane ne?, wane hujja ka ke da shi a kan hakan?, ka sani cewa ɗana ba zai taɓa yarda da kai ba muddin ba hujja ka nuna masa ba".



Daga ɗayan ɓangaren Mk ya saki murmushi sannan ya ce. "Tabbas kayi gaskiya bani da hujja amma ka sani cewa ina da hujja ta yadda kayi amfani da makircin ka wajan kashe mahaifiyarsa. Ka san dai babu wanda ya fi ƙauna a duniyar nan sama da mahaifiyar sa kuma kai ɗin nan ka kashe ta saboda abun duniya".


Take gaban Gov. Musa ya faɗi!, yayin da zufa ya fara ƙeto wa ta kowane sashe na jikin sa. Duk iskan AC da ke kaɗa wa a ɗakin sa bai ana shi yin gumi da tamkar wanda haka watsa wa ruwan zafi haka gov. Musa ya rikice.



Tattaro nutsuwar sa ya yi kana ya ce. "Ta ya ya ka sani?, wane ne ya faɗa maka?".


Dariya Mk ya kwashe da shi ya ce. "Wato har ka manta da tsohon abokin ka kenen wato Abdullahi mijin Mrs Laila?, Kai da kanka ka sa his Excellency Abdullahi ya gudu daga Nigeria izuwa ƙasar China saboda sharrin da ka maƙala wa matar sa da kuma shi. Kada ka damu gaskiya ta kusan bayyana domin kuwa kundin littafin da ka ke nema na duk asalin abubuwan da ya faru yana nan cikin tsararren guri. Zan ƙara tunatar da kai idan ba ka sa yaranka sun saki Nurse Nadiya ba zan tona maka asiri. Sannan bara na faɗa maka wani abu, ƴar mrs Laila guda ɗaya tana Kano idan ka isa ka gano in da take kuma ka sace ta".



Yana kaiwa nan ya katse wayar. Gaba ɗaya gov. Musa ya rikice da jin furucin Mk hakan ya sa ya yi gaggawan kiran yaran sa masu taya shi aikata miyagun laifuka sannan ya ce dasu su saki nurse Nadiya.


Kamar yadda ya buƙata haka suka saki nurse Nadiya yayin da suka maida ta gidan ta.






*AFTER ONE WEEK*
Ko ina a cikin masarauta ya cika yayin da haka ƙawata ko ina da kayan al'atu tare da na al'adu. Yayin da dakarai suka jeru sai kai kawo suke a masarautar.


Babu abin da ke tashi sai ƙamshi abinci da ƙamshi abubuwan laƙumashe. Yayin da ƴan aiki suka bazama sai girke-girke da share-share suke.


Jin hayaniya ya sa Zahra miƙe wa daga kan gadon ta tare da yin miƙa sannan ta ce. "Wai yau me ke faruwa a masarautar nan ne?, kodai baƙo za su yi ne?".
Ta tambayi kanta.


Takawa ta fara yi tare da nufar hanyar waje sannan ta fice daga ɗakin. Nan taci karo da Mami wacce ta ci kwalliya cikin shigarta na alfarma.


Sakin baki Zahra ta yi tana mai bin Mami da kallo. "Mami irin wannan kyau haka, meke faruwa a ne?".


Murmushi Mami ta yi kana ta ce. "Magajin wannan masarautar ne zai dawo wato gawurtaccen ɗana Sooraj, duk waɗan nan kwalliya da yadda haka ƙawata masarautar nan duk saboda shi ne, s duk sanda zai dawo daga ƙasar waje to ana taruwa ne ayi masa tarba mai kyau".



Jinjina kai Zahra ta yi ta ce. "Gaskiya ne sai kace ɗan gold. Ni har na matsu ma na ga Sooraj ɗin".


Kallonta Mami ta yi ta ce. "Kada ki damu a yau za ki ganshi. Yauwa na ma tuna na ce zan aike ki da wasu daga cikin ƴan aikin masarautar nan zaku je ne kasuwa siyo mai special kayan girki wanda nake yi masa special domin baya cin abinci kowa in ba nawa ba. Sannan kuma yana matuƙar son black tea gashi kuma babu, shi ne nake so ku ɗan je driver ya kaiku ku siyo dan Allah".


"Aba Mami sai kin ma haɗa ni da Allah, kada ki damu in sha Allahu yanzu ma zamu je bara na ɗauko mayafi na". Ta faɗa tana mai shige wa ɗakin ta, lokaci ƙalilan ya ɗauke ta a ɗaki ta fito kanta sanye da mayafi blue colour.


Zuwa inda Mami take ta yi ta ce. "Shi ke nen bani kuɗin muje".


Miƙa mata kuɗaɗe Mami ta yi kusan dubu dari biyu.


Zaro idanuwa waje Zahra ta yi baki na rawa ta ce. "Mami irin wannan kuɗi haka sai kace za'a biya kuɗin sadakin wata. Ina laifin dubu dubu ɗaya ƙarƙari ma mun kashe kuɗi da yawa 1500 amma shi ne za'a zuba uban kuɗi haka. Ni tunda nake ma ban taɓa ganin kuɗaɗe masu yawa haka ba sai yau".


Dariya zahra ta bawa Mami. Girgiza kai kawai Mami ta yi ta ce. "Zahra kenen, kina da abin dariya ke za ki ga kamar sun yi yawa ne amma kuwa babu yawa".


Saka hannu Zahra ta yi ta karɓi kuɗi salati riƙe a bakin ta.

Maida kallonta ta yi kan Mami ta ce. "Amma ni bana so naje da su ƴan aiki".


"To da wa ki ke son ki je?". Mami ta tambayi Zahra.

Amsa Zahra ta ba ta da cewa. "Da su Samira nake son muje".


Zaro ido Mami ta yi waje. "Zahra ki rufa min asiri, ke kin san ba za su je ba wahalar da kai ne kawai".


Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Tabbas ni nan zan sa su suje, bakin ce suna matuƙar tsoron ɗanki ba, to ki jira ki gani".


Ta faɗa tana mai fice wa daga part ɗin Mami. Chan ta hangi su Samira sai sha'anin su suke hankali kwance. Hamdala Zahra ta yi tare da nufar in da suke.


Binta suka yi da kallo ganin yadda ta yi cirko-cirko a kansu.


"Ke mene ne ki ka wani zo ki ka tsaya a kanmu?".



Amsa Zahra ta basu da cewa. "Yahya Sooraj ne ya bamu umarni da muje kasuwa yin siyayya tare". Jin Zahra ta ambaci sunan Sooraj ya suka miƙe tsaye jiki na rawa suka ce. "To ai sai ki faɗa mana tuntuni bawai ki tsaya a kanmu ba".


Nan suka nufi wajan parking space tare da shiga cikin mota. Yayin da driver ya tashi mota suka bar harabar masarautar.



Kai tsaye kasuwa ya nufa. Yana zuwa ya yi parking yayin da suka fita. Nan Zahra ta shiga cikin kasuwa

Please Login or Register in order to submit comment