Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Safeera?, to wai ta ya ya hakan ta kasance?, kodai Safeera ƴan biyu ne, kenen hakan yana nufin ajiya biyu ne su ɗin?".






💃💃💃💃💃💃💃💃




*LIKE SHARE & COMMENTS FISABILULLAH 🤌🙏*


*YANZU WASAN YA SOMA. MOM BA AJIYA BIYU BA NE, AJIYA UKU NE😂, KI SHAFA WA ZUCIYAR KI RUWAN SANYI. KAI KAM UMAR KAGA TA KANKA DOLE KA SHIRYA DOMIN ZAMA DA AMRAH BA WASA BA NE🤣*



ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
(Zinariyar Jajirtattu)




Follow the 💖 A'ISHA M.B✍️ HAUSA NOVELS 📚 WORLD 🌎 📚💗💖 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g



*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐.
Daji 🌲
Magarƙama🏢 da kuma
Birni🏙️

WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝♀️Jajirtattu)

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 2️⃣5️⃣▶️2️⃣6️⃣
*_________________________________________________*
Kallon Mom Safeera ta yi ta ce. "Aba Mom kema kin yarda da wannan tatsuniyar, ta ya ya ma za'a ce akwai wata mai kama da ni, ai abin da ba zai taɓa yiwu wa ba kenan. Ya kamata mu tafi daga nan nama fasa siyan mango ɗin duk ƙudade sai bi suke its looks disgusting".


Jan hannun Mom Safeera ta yi suka koma cikin taxi ɗin. Nan goslow ɗin ya ragu har suka samu hanya suka wuce.


*******
Umar kuwa bai zarce ko ina ba sai gidansu.


Horn ya yi jami'ai suka buɗe masa ƙofa. Direct parking space ya nufa tare da yin parking.


Ajiyan zuciya ya sauke tare da maida kallonsa kan Amrah wacce ta takure guri guda.


Fitowa ya yi tare da zuwa side ɗin Amrah ya buɗe mata ƙofa.


Fito da ita ya yi. Kallon fuskarta ya yi nan yake ya ga hawaye kan kwance a kai. Hankalinsa ba ƙaramin tashi ya yi ba . "Mene ne ya sa ki ke kuka Amrah?, ko gidan namu baiyi miki ba ne?, kina son na maida ki wajan ƴan uwanki".


Da sauri ya ga ta girgiza masa kai. Murmushi ya yi ya ce. "Karki damu zan maida ki chan wajan su yanzu haka na saka jami'ai suyi treating ɗinsu wasu sun mutu wasu kuma suna raye don haka kiyi murmushi kinji, domin zan maida ki bayan komai da komai ya kammalu".


Yana kaiwa nan ya ja hannunta tare da shigar da ita cikin gidan.


*******
A matuƙar gajiye take takawa yayin da mutane ke binta da kallo.


Daga nesa ta hangi wata mai ƙosai a baki jection. Da sauri ta nufi in da mai kosan take sallama riƙe a bakin ta.

Amsa sallamar mai ƙosan ta yi ta ce. "Na nawa za'a baki?".


Sosa ƙeya Zahra ta yi ta ce. "A gaskiya bani da kuɗi sai dai idan za ki taimaka min da shi ina matuƙar jin yunwa ne".



Kallon sama da ƙasa mai ƙosan ta bita da shi sannan ta ce. "Ke a wa zan baki kyauta?, ke baki ga kowa garin ya yi masa zafi ba ne?, kin san yadda wake yake tsada kuwa, to ko na goma wanda na san ma babu sai dai ashirin ba zan iya baki ba. Maza ki bar nan wajan. Ke ana ganin ki ma an ga wacce ta gudo daga magarƙama, to ki bar nan kafin nayi miki ihuun ɓarauniya".


Nan take ran Zahra ya ɓaci ta dubi matar ta ce. "ke wace iriyar gajarabul asaratun donkey ce?, shin na ce miki ki bani ƙosai ne ko an gaya miki cewa ni mabaraciya ce?, na zo na taimaka miki shi ne za ki wani yaɓa min magana da wannan hangamammen bakin naki".


Tashi mai ƙosan ta yi daga kan kujerar da take sannan ta ce. "Ni ce mai hangamammen bakin?, ke dama kallo ɗaya za'a miki a san ƴar fashi da makami ne domin kuwa shi ne gadon ahalin ku. Gaskiya uwar ki bata iya haihuwa ba".


Ba zato ta ji saukar mari kan fuskarta. Nan take hankulan jama'a ya garzayo wajan yayin da mutane suka taru.


Nuna mai ƙosan Zahra ta yi ta ce. "Zan iya tolerating komai amma banda zagin mahaifiyata, idan har bakya son ki ganki kwance a gadon asibiti to ki kiyaye harshen ki. Wannan marin da nayi miki ba mari ba ne shafa miki fuska kawai nayi wanda zanyi miki next sai dai aga tiririn hayaki yana fita daga kunnuwanki. Shashashan banza ƴar kutumur kitabi dangin gajeru kawai". Tana kaiwa nan ta bar wajan. Yayin da mutane suka bita da kallo.

Ganin yadda mutane suke binta da kallo ya sa ta dube su ta ce. "ku kuma ya aka yi ne?, sa'idinawa kawai". Ta faɗa tana mai barin wajan baki ɗaya.


Barin wajan mutane suka yi .


Dafa kumatun ta mai ƙosai ta yi yayin da take jin fuskanta nayi mata zugi dan ba ƙaramin shigar ta marin ya yi ba. Simi-simi ta koma kan aikin ta.



Ci-gaba da tafiya Zahra ta yi. Nan take hadari ya taso yayin da aka fara iska mai ƙarfi.



"Wayyo Allah kodai ruwa za'a yi ne?, ni yanzu ina zanje na zauna". Bata yi aune ba ta ga an fara yayyafi. Ganin hakan ya sa ta ƙara sauri chan ta hango wani kango ba ta yi wani tunani ba ta yi saurin nufar in da kangon yake sannan ta shige ciki. Tana shiga aka zuge da ruwa.


Hamdala ta yi tana mai juya wa. Nan take gabanta ya faɗi!, ganin rukunin ƴan daba a cikin wajan babu abin da suka yi sai shaye-shaye. Yayin da gefe guda kuma mata biyu ne zaune sai sharɓan kuka suke.


"Barka da ƙarasowa kyakkyawar budurwa. Kaga wata tsuleliyar budurwa wannan kam ta yi". Cewar ɗaya daga cikin ƴan shaye-shayen.

Tashi suka yi gaba ɗaya suka fara tunkarar in da Zahra take.



******
Taxi ɗin su bai tsaya ko ina ba sai gaban family House ɗin su Aliyu.


Sauko wa suka yi daga cikin motan yayin da suka biya mai taxi ɗin. Kallon ƙofar gidan Daddy ya yi cike da kewa ya ce. "Gaskiya nayi kewan wannan gidan, yanzu shekaru ashirin kenen rabon da na ɗora ƙafata kan wannan gidan".


Taɓe baki Safeera ta yi ta ce. "Daddy this place is so annoying let's just go back to America please".


Maida kallonsa Daddy ya yi kanta ya ce. "Nan shi ne asalin gidan mu Safeera ba America ba, ya kamata ki gane hakan".


Murmushi Aliyu ya yi ya ce. "Rabu da ita kawu, idan ta ci tuwo za ta san cewar ba rayuwa take yi ba a America nan shi ne in da jin daɗi yake".



Yana kaiwa nan ya fara ƙwanƙwasa ƙofa. Nan take mai gadi ya buɗe. Ganin wanda ke bakin ƙofar ya sa shi wangale musu gate tare da yi musu barka da zuwa.


Washe baki Daddy ya yi ganin har izuwa yanzu Baba Sule ne yake yi musu aiki.


"Baba sule har yanzu kana nan dama?".


Amsa Baba Sule ya bashi da cewa. "Ina nan ɗana ya ka ke?, kaje ƙasar ƴan gayu ka ƙi ka dawo ko?, wannan ita ce ƴarka?".


Amsa Daddy ya bashi da cewa ƙwarai kuwa ita ce ƴa ɗaya tilo da Allah ya bani".


"Masha Allah gata kuma kyakkyawa tabarakalla. Ku shigo na san su Alhaji za su yi fari cikin ganin ku".


Shiga ciki suka yayin da suka tarar babu kowa a compound ɗin. Sai yara wanda ke wasa, babu abin da ka ke ji sai ayaniyar yara. Tsayawa yaran suka yi suna mai kallonsu.

Da gudun su suka tawo tare da zuwa suka rungume Aliyu.

"Welcome back, brother Aliyu where have you been?, we missed very much".


Murmushi Aliyu ya yi ya ce. "Yanzu dai ai na dawo kuma na tawo muku da chocolate masu dad'i. Ina su grandma da grandpa suke?".


"Suna cikin gida". Yaran suka faɗa


Jin yara suna ta ihuu na farin ciki ya sa mutanen gidan fitowa baki ɗaya.


Mamaki ne ya kama kowanensu ganin su Daddy a wannan lokaci.

Kallon Daddy Grandpa ya yi cikin ɓacin rai ya ce. "Lallai sannu Ibrahim, wato tun bayan shekaru ashirin da ka saka ƙafa kaida matar ka ku ka fice daga gidan nan baka sake garzayo wa ba sai yanzu ko, me ka zo yi to maza ka koma domin kuwa bamua da buƙatar ku".


Kallon Grandpa Grandma ta yi ta ce. "Aba mai gida, bai kamata ka faɗi haka ba, koba koma shi ɗin ɗan ka ne kuma ya zo ne tare da matarsa da kuma ƴarsa".


"Yi min shiru Amina, ɗana ne kuma ni nafi ki iko a kansa. In dai har yana son zama a cikin wannan gidan to ya zama dole ya tattara ina shi ina shi ya dawo nan da zama na har abada ba tare da ya koma chan ƙasar kafirai ba, sannan kuma dole ƴarsa ta auri Aliyu ko tana so ko bata so".


Zaro idanuwa waje Safeera ta yi jin cewar ba za su koma America ba.


Murmushi Daddy ya yi ya ce. "Shi ke nen Abba in dai abin da ka ke so kenen na amince zan zauna tare da matata da kuma ƴata, sannan kuma batun auren Safeera wannan a zaune take dole Aliyu ya aure ta tun da abin da ka ke so kenan".


A zabure Safeera ta ce. "No Daddy, ta ya ya zamu dawo nan da zama na har abada, how do you expect me to marry this guy that has a mental issues?. No it can never be possible I can't".


"Will you keep that your dirty mouth shut. Are you out of your senses?, what's wrong with you Safeera?, he is your grandpa, he knows what is bad and good for you okay". Mom ta faɗa cike da ɓacin rai.


Fashe wa da kuka Safeera ta yi ta ce. "Wallahi ba zan zauna a nan ba, i rither die than to stay in this environment".


Tasss ta ji saukar mari kan fuskarta. Dafe ƙuncinta ta yi cike da mamaki yau karo na farko da a aka taɓa sanya hannu kan fuskarta. Ɗago da rinannun idanuwanta Mom ta yi ta ce. "Waɗan nan families ɗin ki ne karki kuskure ki faɗi magana mara daɗi a kansu".


Murmushi Grandma ta yi tare da janyo Safeera jikinta ta ce. "Aba Zainab me ya sa za ki mare ta?, yi haƙuri jinki jikata, zamu yi maganin ta. Maza ku tawo mu shiga daga ciki.


Shiga ciki suka yi yayin da suka samu guri a parlour kowa ya zauna. Nan suka shiga yin labarai na yaushe rabo. Suna yi suna dariya abun gwanin burgewa. Dubansu mahaifin Aliyu ya yi ya ce. "Me ku ke so a kawo muku?, zansa su Zuwaira su kawo muku".


Nan take wasu kyawawan ƴan mata guda uku suka fito daga cikin kitchen hannun kowannensu riƙe da abinci. Nan take suka ajiye abincin da lemukan hannayensu tare da fara serving ɗin su Daddy.

"Zuwaira ki miƙa wa Safeera nata ta ci". Cewar Abba wato mahaifin Aliyu.



"Tom Abba bara na zuba mata". Zuwaira ta faɗa tana mai ƙoƙarin zuba abinci a plate.

Kawar da kai gefe Safeera ta yi ta ce. "Bana son, ba zanci wannan ƙazamin abincin naku ba".


Kallon ta kowa ya yi cike da mamaki ganin irin hali na Safeera. Abba ne ya ce. "Ke kuwa ki ɗanɗana ki ci za ki ji daɗin sa fa, shi iyayen ki suke ci kafin su tafi ƙasar America, tuwo da miyan taushe gashi ya ji kayan haɗi maza ki sauko m muci".


"Bana so kuci kayan ku". Ta faɗa tare da kwanta kan kafaɗar grandma ta ce. "Grandma ɗita ce kawai mai mutunci a cikin ku gaba ɗaya baku da mutunci, ita ce kawai ta yi min maraba da zuwa. Ku kuma kamar baku san da halitta ba , karo na farko kunga yarinyar ɗan ahalin nan maimakon kuyi farin ciki da hakan sai ku wani yi kamar baku ga mutum ba, hakan me zanci abinci".



Dafe kansa Abba da sauran mutanen parlourn suka yi sannan Grandpa ya ce. "Kiyi haƙuri shalele mun san mun aikata kuskure a gafarce mu ko".


Ƙura mata ido Abba ya yi ya ga suna matuƙar kama da ƙanwar sa Laila.


"Laaa Baba ka ga abin mamaki, ƴar Ibrahim tana matuƙar kama da Laila sosai ku duba ku gani".


Nan take gaba ɗaya suka maida idanuwansu kan Safeera yayin da Safeera ta yi baki tana kallonsu a ranta tana cewa. "Wace ce kuma Laila?".


Zumbur Grandpa ya ɗago idanuwansa tare da gyara zamansa a kan wheel chair ɗin sa sannan ya ce. "Kada ku sake kawo min maganar Laila a in da nake na ga muku, ita ce silar faɗa wa ta cikin wannan yanayin, na tsane ta" .


Shiru Grandma ta yi damuwa ɗauke kan fuskarta ta ce. "Allah muna yi masa laifi ya yafe mana ballantana mu ƴan adam, ya kamata a ce komai ya riga ya wuce mai gida".





******
Da gudu su Khairiya suka fito tare da su Ramlat da Usman. Tsayawa suka yi chakk ganin Umar da yarinyar jeji.


Kallon Amrah Khairiya ta yi ta ce. "Yahya wannan fa daga ina?".


Kallonsu Umar ya yi gaba ɗaya ya ce. "She is your new sister, ina son ku ɗauke ta matsayin ƴar uwarku, bana son naji abu wanda ya saɓa wa hakan ba. Ku kaita part ɗinku ku chanza mata kaya sannan kusa ta yi wanka tare da yi mata kwalliya kunji ni ko. Ita ma daga yanzu a nan zata dinga zama".


"Wow yahya she is so amazing she looks pretty and cute, oh m God green even ne da ita". Ramlat ta faɗa tana mai jan hannun Amrah suka shigar da ita part ɗin ta.



**************
"Kai ku dakata me ku ke shirin aikata wa?". Zahra ta faɗa tana mai ja da baya.


Dariya ƴan daban suka kwashe da shi sannan ɗaya daga cikin su ya ce. "Za ki iya dakatar da mu ne?, muna so ne mu haɗa da ke, ƴar cika kamar ki kice ba zamu yi miki komai ba". Ya faɗa yana mai babbakewa da dariya.


Cikin ɓacin rai Zahra ta ce. "Kuna da hankali kuwa?, ku samm bakua daraja mace ne?, idan baku saki ƴan matan nan kun basu haƙuri ba saina yi maganin ku baki ɗaya".


Dubanta ƴan daban suka yi suka ce. "Sarkin yawa yafi ƙarfin sarki, ta kanki zamu fara". Suna kaiwa nan suka sa hannu tare da jan Zahra.


Nan take Zahra ta kurma ihuu!, yayin da ta yi nasarar ƙwace kanta. Daga nesa ta hangi wata ajajjiyar bulala. Da sauri ta nufi in da bulalar take tareda ɗauka sannan ta nufi in da suke. Bata yi wata-wata ba ta fara zuba musu bulala a jiki.



Ihuuu ƴan shaye-shayen suka fara yi suna mai ƙoƙarin guduwa.


"Ina za ku je?, baku tsageru ba, nafi ku tsageranci, shashashu ƴan iska kawai marasa ɗa'a. Saina yi maganin ku, idan gomnati bata ɗauki mataki a kan mutane ire-iren ku ba mu zamu ɗauka". Da sauri ta yi wa matan alama da su fita daga cikin wajan.



Da sauri matan suka tashi tsaye tare da fita daga cikin kangon suka bar Zahra da ƴan shaye-shayen.


Cikin rashin sa'a ta ji saukar naushi kan cikin ta. Nan take ta kurma wani azababbiyar ƙara!.



Su Daddy da ke zaune babu zato suka ji Safeera ta kurma wani irin razananniyar ƙara! Mai matuƙar firgitarwa.



Ɓangaren Amrah ma haka ƙara ta saki tare da fusge hannunta daga na Ramlat. Nan take jami'an gidan suka nufo in da suka jiyo ƙaran yayin da shima Umar ya sauko daga kan upstairs da sauri.


"Me ku ka yi mata?".


Girgiza kai kowanensu ya yi ya ce. "Wallahi babu abin da muka yi mata kawai muna cikin tafiya muka ga ta kurma ihuu".




*****
Safeera what's going on?, me ya faru?". Daddy ya tambaye ta.



Kuka Safeera ta fara yi hannunta dafe da cikinta ta ce. "My stomach, ciki na wayyo ciki na!".



🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*NI FA ƳAN UKUN NAN LAMARIN KU SAI AN HANKALI🧐😏😏. DA ZARAR ABU YA SAMI ƊAYA SAI SAURAN SUNJI A JIKIN SU🧐. MUJE DAI ZUWA*.

KADA KU MANTA DA LIKING DA KUMA SHARE TARE DA COMMENTS PLEASE DOMIN ALLAH 🙏🙏🙏

ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
(Zinariyar Jajirtattu)


*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐.
Daji 🌲
Magarƙama🏢 da kuma
Birni🏙️

WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝♀️Jajirtattu)

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 2️⃣7️⃣▶️2️⃣8️⃣
*_________________________________________________*
Hankalinsu ba ƙaramin tashi ya yi ba ganin yadda Safeera ke birgima s ƙasa tana ihuun cikin ta.


Da sauri Aliyu ya ɗauki waya tare da kiran family Doctor ɗin su.

Ɗaukar Safeera Aliyu ya yi tsreda shigar da ita cikin ɗaki sannan ya kwantar da ita a kan gado.


Cikin lokaci ƙalilan likitan su ya zo tare da fara duba Safeera. Yayin da gaba ɗaya family ɗin suka kasa zaune sai kai kawo suke a cikin gidan.



*****
Ɓangaren Amrah kuwa. Ɗaukarta Umar ya yi sannan ya nufi part ɗin sa da ita yayin da su Khairiya da Usman suka bi bayan shi.


Yana zuwa ɗakin shi ya kwantar da ita kan gado yayin da ya sa su Khairiya suje su haɗa mata shayi mai kauri. Fita suka yi suka bar Umar da Amrah a cikin ɗakin. Tashi Umar ya yi tare da fita domi ya je pharmacy domin siyo maganin ciwon ciki.




****
Kwashe wa da dariya ƴan shaye-shayen suka yi yayin da suka dubi Zahra wacce ke kwance cikin mawuyacin hali sannan suka ce. "Ke ba ƴar ranin wayo ba, yanzu zamu yi duk abin da muke sonyi da ke ba tare da wani ya dakatar da mu ba". Suna kaiwa nan suka nufi kanta.


Nan take suka ji karan motocin ƴan sanda. Da mugun gudu suka fice daga cikin kangon yayin da suka bar Zahra ita m ɗaya a cikin wajan.


Shiga cikin kangon suka yi tare da matan da suka fita daga cikin kangon ɗazu.


Nan suka tarar da Zahra kwance cikin mawuyacin hali.


Kallon ƴan sandan matan suka yi sannan suka ce. "Yauwa ita ce ta cece mu daga wajan ƴan daban dan Allah ku taimaka ku kaita asibiti".


"Shi ke nen". Ɗaya daga cikin ƴan sandan ya faɗa. Kana ya saka mata ƴan sanda suka cinciɓi Zahra, basu zarce ko ina ba sai asibiti.


Shigar da ita ciki asibitin suka yi. Nan take nurse's suka fito da gado tare da karɓar ta sannan suka shige da ita cikin asibitin.


Nan take suka fara ba ta taimakon gaggawa.



*********
Bayan su DPO sun isa garin Jigawa ya sa suka wuce magarƙama kai tsaye.


Suna zuwa ya fito yayin ya tarar da Hajiya Binta ta yi tagumi.


Zuwa ya yi daff da ita. Ganin su ya sa Hajiya Binta saurin miƙe wa sannan ta ce. "DPO ina Zahra take?".


Kallonta DPO ya yi tare da ba ta amsa da cewa. "Ƴarki ta gudu daga sjaan mu, yanzu haka tana Kano bamu san in da take".


Gaban Hajiya Binta ne ya yanke ya faɗi!, cikin tashin hankali ta dubi DPO ta ce. "Kamar ya baku ganta ba?, aba DPO kaima fa ka san Zahra amanarta aka damƙa min, mene ya sa baku nemo ta, na dai san aikin ku ne yin hakan. Kuma kai da kanka ka san babu in da ta sani a wannan garin balle a ce garin Kano wanda ba ta ma taɓa zuwa ba sai a wannan karan. Ni dai gaskiya ka sa a nemo ta in ba haka ba zan sa a kai ƙarar ku wajan shugaban ƴan sanda".


Ajiyan zuciya Dpo ya sauke!, sannan ya ce. "Ki kwantar da hankalinki Binta, ina da tabbacin cewa Zahra za ta iya kula da kanta domin kuwa ba shiru-shiru bace, kai kanki kin san fitinanniya ce ba ta jin magana, ita ce ta gudu daga hannun mu. Karki damu zan saka a nemo ta duk in da take kuma za ta dawo da izinin Allah".



*************
*ƘASAR CHINA*
"Hello MK, da gaske ne cewar matata tana raye tare da ƴaƴanta?".


Daga ɗayan ɓangaren Mk ya bashi amsa da cewa. "ƙwarai da gaske yaranka tare da matarka Laila gaba ɗaya suna raye".


Ajiyan zuciya dattijon ya sauke!, tare da yin hamdala sannan ya ce. "Alhamdulillah Allah na gode da ya kasance matata tare da yarana suna raye. Dan Allah ka tabbatar da kana kula da shige da ficen su, bana son su kasance cikin kaɗaici kowanen ka shiga cikin rayuwarta domin kare ta, kai ɗin jami'i na ne kuma na yarda da kai ɗari bisa ɗari, ina so kayi min wannan alfarman dan Allah".


Daga ɗayan ɓangaren Mk ya ce. "Kai ɗin kamar walihi ka ke a gare ni Sir Bashir, a kan me ya sa ba zan yi abin da zai faranta maka ba, bayan kuma kai ka faranta mu tare da iyalaina, ka fito da ni daga cikin magarƙama kuma ka sa an maida ni kan aiki na, dole nayi maka duk abin da ka ke so. In sha Allah zan shiga rayuwar kowacce a cikin su domin kare su. Ba zan taɓa barin Gov.Musa Muhammad ya ci galaba ba". Yana kaiwa nan ya katse wayar.


Ajiyan zuciya Sir Bashir ya sauke!, sannan ya kwanta kan lallausar gadon sa ya ce. "Tabbas na aikata babban kuskure, na san ba za ki yafe min ba Laila, duk abin da ya faru ba laifi na ba ne, ban zo nan ba domin na sa a cutar da ke, na zo ne kawai saboda mahaifin ki ya bani umarnin yin hakan. Ina matuƙar ƙaunar ki matata".





**********************
*NIGERIA*
Safeera kuwa, bayan likita ya duba ta ya ba ta magani ta sha. Cikin ƙankanin lokaci bacci ya yi hawon gaba da ita. Yayinda Grandma ta saka su Zuwaira da Salma su yi mata farfesun kaji".


Fita suka yi suka bar iya Aliyu da kuma Safeera a ciki ɗakin.


Tsaya wa Aliyu ya yi yana kallon kyakkyawar fuskar Safeera. Tagumi ya yi cikin ransa ya ce. "Yarinyar nan ba dai kyau ba, duk wanda ya same ki gaskiya ya yi sa'ar mata". Ya faɗa cikin ransa yayin da ya ci gaba da kallo yadda take fitar da numfashi cikin kwanciyar hankali.



******
Bayan Umar ya dawo ya tarar da su Khairiya su haɗa wa Amrah shayin. Shiga cikin ɗakin suka yi a tare. Cikin mamaki kuwa suka tarar ba ta cikin ɗakin.



Zaro idanuwa waje gaba ɗaya suka yi yayin da Ramlat ta ce. "Ina kuma ta je?".


Dafe kansa Umar ya yi sannan ya ce da su. "Maza ku bincika cikin gidan nan gaba ɗaya, na san ba za ta wuce cikin nan ba".


Haka gaba ɗaya suka bazu cikin gidan suna nemanta, yayin da Umar ya saka jami'ai suma suka shiga bincika wa.


Neman duniya sunyi amma basu ganta ba.

Nan take wani tunani ya faɗo wa Umar. Da sauri ya nufi garden yayin da suma su Usman suka bishi a baya. Dube-dube suka fara yi.


Tsayawa Umar ya yi chakk jin musharin mutum. Ganin ya tsaya ya sa suma suka tsaya. Shiru kowanensu ya yi.


Kasa kunne Umar ya yi domin jin ta ina musharin yake fitowa.


Babu zato ya ji Khairiya da Ramlat sun fasa ihuu!.


Da sauri ya dube su sannan ya ce. "Mene ne ya faru?".


Baki na rawa suka haɗa baki wajan faɗin. "Ka duba sama kan bishiya".


Kamar yadda suka ce babu musu Umar ya duba sama. Abin da ya gani ne ya bashi mamaki. Ganin Amrah ya yi kwance kan bishiya sai sharɓan baccin ta take.


Dafe kansa Umar ya yi ya ce. "Ya salam!, wannan yarinyar ta riga da ta saba da zaman jeji, idan ba nan na maida da ta ba ba za ta taɓa iya zama damu ba".


"Ko ta ya ya ma ta iya hawa kan bishiyar nan". Usman ya faɗa.


Duban jami'an gidan Umar ya yi sannan ya saka su su ɗauko masa igiya. Kamar yadda ya umarta haka suka je suka ɗauko igiya mai matuƙar kauri sannan suka ɗaure cikin bishiya da shi tare da riƙe shi gamm a hannun su.



Kama igiyar Umar ya yi tare da fara hawa kan bishiyar. Yayin da jami'an suka ƙara riƙe igiyar sosai a hannunsu.


Jan igiyar Umar ya fara yi yana mai hawa kan bishiyar har ya isa in da Amrah take sannan ya janyo ta.


Zumbur ta miƙe tsaye. Nan take Umar ya ja da baya. Cikin

Please Login or Register in order to submit comment