Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suke tare da ɗurƙusawa kan gwiwowinta sannan ta janyo su jikinta ta ce. "Ku sani cewa kune komai nawa, kune dangi da kuma iyaye na, ba zan juri naga kuna faɗa a tsakanin ku ba, ku daina kunji ko".


Maida kallonta ta yi kan sauran namun jejin sannan ta ce. "Maza gaba ɗaya ku zo mu yi wasan tsere ko. Idan na riga ku zaku ɗauke ni gaba ɗaya kunji ko. Dan haka ku tawo muje mu yi wasa". Duk abin da take faɗa da yaren dabbobi take yi.

Da gudu ta bar wajan fuskarta ɗauke da annashuwa. ganin hakan ya sa suma namun jejin suka bita da gudu.




************************
"Mai gida ya kamata a ce ka yafe wa ƴarka, ita ɗin fa ƴar mu ce. Yanzu haka ta riga da ta rasu, bai kamata a ce har yanzu kana fushi da ita ba".
Cewar wata dattijuwar mata.

Ɗago da kansa mutumin dake kan wheel chair ya yi sannan ya dube ta ya ce. "Yafiya?, kina nufin na yafe wa Laila cin mutunci da zubar mana da kima da ta yi a shekarun baya?. Abun da ta yi ya daɗe da faruwa amma ina jin shi sabo ne a cikin zuciyata, kin san dai ba bu abin da na fi tsana sama da na ga mutunci na da na ahalina ya zube. Ta ci amanata, samm bata cancanci na yafe mata ba, ni na tsani ma jin sunanta a inda nake, kada ki ƙara kawo min irin wannan maganar na faɗa miki. Kuma abin da ta yi wanda ya sa a yanzu jika na Aliyu yake fama da cutar mantau, yana ɗaya daga cikin dalilin da ya sa ba zan taɓa yafe mata ba, dan haka ki ƙyale ni".


Girgiza kai matar ta yi sannan ta ce. "Shi ke nen, amma ka sani cewa cutar mantau na Aliyu ba laifin Laila bane, tsautsayi ne kawai bada gangan ba, dan Allah a matsayina na uwa nake roƙan ka, dan Allah ka yafe wa Laila ko ruhinta sai samu salama". Ta ƙarashe maganar hawaye na gangaro kan fuskarta.

Nuna ta dattijon dake kan wheel chair ya yi sannan ya ce. "Amina kada ki kuskure ki fusa ta ni nayi miki abin da ba za ki ji daɗin sa ba. Ta ya ya za ki ce ba ita ce silar cutar mantau ɗin Aliyu ba, shi kanshi mijin ta tun da haka kaita magarƙama bai taɓa zuwa ya duba ta, saboda ya san ba mutumiyar kirki bace. Laila ta karya min duk wani yarda ta a kanta, ita ce dalilin zama na a kan wannan wheel chair ɗin. Laila ta ci amanar yardar da nayi mata, ta zalince ni, duk dukiya da companies da take dasu basu ishe ta ba, sai ta haɗa da miyagun laifuka, eh?, na ce duk basu ishe ta ba sai ta haɗa da safaran yaran mutane. ta saka bana iya fita saboda abin kunyar da ta janyo wa wannan ahalin. Har abada ba zan yafe mata abin da ta yi ba".


"Aba mai gida, Allah ma muna yi masa laifi yana yafe mana balle mutum ɗan adam. Ni ina da yaƙinin cewa Laila bata aikata kowane laifi ba, ita ɗin fa mai gaskiya ce da riƙon amana. Amma ba bu damuwa na san dai wata rana gaskiya zata yi halinta, kuma ramin ƙarya ƙurarre ne dole dai wata ran gaskiya zata fito".



***********************
"What!, Umar ka san abin da ka ke faɗa kuwa?, kana nufin a yau zamu je wannan dajin?, yau ɗin nan da ka dawo ku hutawa baka yi ba, ka bari zuwa next week mana, ka ga kafin nan gaba ɗaya engineers da architecture da kayan aiki za su kasance a shirye. Wannan wajan naka ne amma akwai namun jejin dake zaune a cikin dajin, waje ne mai matuƙar hatsarin gaske, ba zai yiwu kaje ba. Kawai kayi zaman ka a gida in ya so idan haka kori namun jejin wajan sai ka zafi filin da ka ke so a wajan".


Ɗago kai Umar ya yi ya kalli mahaifin nasa sannan ya ce. "Saboda me za'a kari dabbobin dake zama a cikin dajin?, su kenen basu da ƴanci na rayuwa ne ko me?, kana ji ba za'a taɓa ɓangaren su ba, za'a gina company ne a wani guri a cikin dajin amma banda ban yarda a taɓa ɓangaren inda dabbobin suke zama ba, kuma a yau nake so na je na ga wajan".


"Amma Umar wajan nan fa gaba ki ɗaya mallakin ka ne, kuma gaba ɗaya wajan ne namun jeji ke zama, ko dai za ka sauya wani jejin da ban muje na Kano?".


Amsa Umar ya ba shi da cewa. "A'a, ni wannan dajin nake so, kuma yanzu nake so na je".

"Shi ke nen Umar, tun da haka ka ke so zan yi wa engineers magana za'a tafi da kayan aiki domin a fara gudanar da aikin company". Cewar mahaifin na shi.


Bayan hawanin biyu da misalin ƙarfen biyar na yamma gaba ɗaya suka shirya tsaff yayin da haka haɗa rukuni na jami'ai da bindigogi suka nufi hanyar dajin.


Tun da suka fara tafiya Umar ke jin gabansa na tsananta faɗuwa, ya rasa me ke masa daɗi, gaba ɗaya ya shiga wani irin yanayi. Lokaci ƙalilan ya yi musu a cikin dajin su Amrah.


Shiga suka fara yi da motoci cikin dajin yayin da suke tattaka itacuwa da ganyayyaki saboda ba bu wata hanya ta mota a wannan jejin. Suna cikin tafiya ƙwatsam suka buge ɗaya daga cikin dabbobin dake bin Amrah a baya. Tsayawa motocin suka yi a tare. Sannan gaba ɗayansu suka fito daga cikin motan banda Umar wanda ke zaune a bayan mota securities sun zagaye motar da yake ciki da bindigogi.


Juyawa Amrah ta yi sakamakon jin ƙaran ɗaya daga cikin namun jejin da ta yi. Zaro idanuwa ta yi waje tare da sakin wani irin ƙara! mai razanarwa.









*TOH FAH YANZU HAKE YINTA, KOYA ZATA KASANCE TSAKANIN AMRAH DA UMAR?. MUJE DAI ZUWA*

KADA KU MANTA DA COMMENTS DA KUMA SHARING PLEASE 🙏 🙏

ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
(Zinariyar Jajirtattu)

Follow the 💖 A'ISHA M.B✍️ HAUSA NOVELS 📚 WORLD 🌎 📚💗💖 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g



*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐.
Daji 🌲
Magarƙama🏢 da kuma
Birni🏙️

WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝♀️Jajirtattu)


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 1️⃣5️⃣▶️1️⃣6️⃣
*_________________________________________________*
Da mugun gudu Amrah ta isa inda dabban yake, sannan ta fara duba shi, ganin cewa ba bu alamun rai a tattare da shi, ya sa ta ɗago da green eyes ɗin ta wanda suka ƙara rinewa saboda ɓacin rai sannan ta ɗora a kansu.


Gurnani Amrah ta fara yi. Da sauri ta miƙe tare da nufar inda suke. Ganin tana nufo inda suke ya sa jami'an suka yi saurin zagaye motar Umar yayin da suka saita bindigun su kanta.


Tsalle ɗaya Amrah ta yi tare da dira kan motan da Umar ke ciki. Zabura gaba ɗayansu suka yi. Nan take suka janyo ta ƙasa ta faɗi, sannan suka fara ririƙe ta.


Ɓangaren Umar kuwa ba abin da yake yi sai aikin kallonta, yayin da ya ji kanshi cikin sabon yanayi da shi kanshi bai san dalilin faruwar akan ba. Fitowa ya yi daga cikin motar tare da ƙura mata idanuwansa. "She is so pretty and cute". Ya faɗa cikin zuciyarsa.


Ɗago da idanuwanta Amrah ta yi tare da sauke su a kan na Umar. A matuƙar fusa ce ta ƙwace kanta daga riƙon da jami'an suka mata, yayin da ta fara dukansu tana ɗaga su sama tare da wurga dasu ƙasa.


Saida ta gama da su sannan ta fara yowa inda Umar yake. Saida ta je har gabansa da zimmar dukansa. Tsayawa ta yi chakk saboda ganin irin ƙwar jinin da ya yi mata.


Gurnani ta fara yi tana mai nuna dabba da suka buge. nan take ta fara hawaye tana dukan motan da ya bude dabban.


Jikin Umar ne ya yi sanyi yayin da ya ji jikinsa ya mutu. Kallon tufafin da ke jikinta ya yi. Ganin gaba ɗaya ganye ne sanye a jikinta akan ya ƙara tabbatar masa da cewa Amrah ƴar daji ce.


Jin kukan Amrah ya sa sauran namun jejin fitowa izuwa harabar wajan. Ganin Amrah durƙushe tana kuka, ya sa suka fara gurnani yayin da suka fara nufar inda Umar yake da zafin nama.


Ganin suna nufo inda yake ya sa Umar ya fara ja da baya-baya.


Ɗago da rinannun green eyes ɗin ta Amrah ta yi tare da sauke su akan namun jejin. ganin suna nufar inda Umar yake da zimmar illata shi ya sa ta sauri miƙe wa, yayin da ta tafi da gudu tare da shan gabansu.

Da sauri jami'an suka miƙe tsaye. Yayin da a dai-dai lokacin yan hukuman row suka ƙaraso wajan.

Dakatar da dabbobin Amrah ta yi da hannunta sannan ta ce da su. "Maza ku ja da baya, kada ku ce zaku cutar da shi, bada sane suka buge ɗaya daga cikin ƴan uwan mu ba, dan aka maza ku koma. In ba aka ba gaba ɗaya rayuwar mu tana cikin hatsari".


Gani suka yi tana yin magana ba tare da fahimtar abin da take cewa ba.


"Sir Umar ka bamu dama domin mu kashe dukanin dabban dake cikin dajin nan, domin nan mallakin ka ne ba ta su ba".

Dakatar da shi Umar ya yi da hannunsa sannan ya ce. "Kada kuyi komai ba tare da izini na ba, gaba ɗaya kuna under control ne don aka be careful. Maza ku tawo mu bar nan sannan yarinyar nan ku saka ta a mota ku tawo da ita".

"Yes Sir". gaba ɗaya suka faɗa, yayin da suka nufi inda Amrah take tsaye tana faɗa wa dabbobi da su koma. Juyawa dabbobin suka yi tareda barin wajan.


Ba zato ta ji sun rirriƙe ta. Da sauri ta dube, sannan ta fara ƙoƙarin ƙwace kanta.

A matuƙar hassale ta gantsara wa ɗaya daga cikin su cizo. Nan take ya saki wata iriyar azababbiyar ƙara. Buga tsalle Amrah ta yi tare da ƙwace kanta daga gare su.

Faɗuwa gaba ɗaya jami'an suka yi. Ganin haka ya sa Amrah ta fara gudu yayin da ta fara aye wa kan manya-manyan bishiyun dake cikin dajin tsalle suka ga ta fara yi tamkar ƴar biri, tana aye wa kan bishiyu ɗaya bayan ɗaya.


Da sauri jami'an suka bi bayan ta. Sannan suka fara sakin harbi.


Ganin sun fara harbi ya sa Umar dube su yana mai cewa. "Don't shoot". Ko saurarensa basu yi ba aka suka ci gaba da harbin bishiyun domin su samu Amrah.




*********************
*Magarƙama*
"Gani nan naji ance wai kuna nema na". Zahra ta faɗa ba bu alamun tsoro a tattare da ita.


Tsayawa ƴan sandan da warders suka yi suna kallonta. Ɗaya daga cikin su ne ya ce. "Zahra wai me ya sa ki ke da wannan jiji da kai ne?".


Kallon wacce ta yi maganar Zahra ta yi sannan ta ce. "Ki tambayi wacce ta haife ni zata baki amsa".


Da kallon mamaki suka fara binta da shi. Ɗaya daga cikin ƴan sandan ne ya ce da ita. "Ta ya ya zata tambayi mamarki bayan bata raye?, koda yake dole ai a tambaye ta tun da uwa ƴar daba ita ma ɗiya ƴar daba. Wannan dai gadon hali ku ka yi".


Danne fusho dake ƙoƙarin ta so mata Zahra ya yi sannan ta ce. "Ɗan sanda ka iya bakin ka, mahaifyata ba abar wasa bace, kada ka tunzurani na aikata abin da raina bai so ba".


Sakin baki ɗan sandan ya yi yana kallonta. "Idan ban iya bakin nawa ba duka na za ki yi?. To ki sani cewa mahafiyar ki babbar sheɗaniya ce, ba bu wanda ya kaita sheɗanci kuma sannan ita ce sanadin mutuwan rayukan mutane a lokacin baya. Don haka ko kina so ko bakya so da kallon ƴar sheɗaniya zamu dinga kallon ki. Ni a duniyar nan akwai wacce ta kai Mrs Laila arha kuwa?, domin ko a gidan karuwai albarka".



Nan take idanuwan Zahra suka kaɗa suka yi jajir. Take ta sak wata iriyar ƙara mai matuƙar razanarwa!.


Shaƙe wuyar ɗan sandan ta yi da dukkanin ƙarfin ta. Tare da ɗaukar hannunta ta ƙwaɗa masa mari. Tare da fara naushin bakin sa da mugun ƙarfi.


Ganin abin da ke faruwa ya sanya sauran jami'an suka ƙaraso wajan, yayin da suka fara ririƙe ta tare da ƙoƙarin ƙwace ɗan sandan daga hannun Zahra. Da sauri suma ƴan magarƙamar suka ƙarasa wajan.

Hajiya Binta dake cutting grass ce ta hango taruwa mutane. Da sauri ta saki gatari da take cutting da shi tare da nufa wajan.


Riƙe shi Zahra ta yi ƙamm a hannunta yayin da ta ci gaba da nausar bakin sa. Cikin huci ta dube shi sannan ta ce.


"Mahaifiyata ce take da arha?, wato mahaifiyata ce ko a gidan karuwai
albarka ko?, yau za ka gane kuranka. Ka sani cewa zagin mahaifiyata da kay shi ne kuskuren da baka taɓa aikatawa ba a rayuwarka domin saina yi maka dukan kawu wuka, saina yi maka dukan da ko ƙauyen ku ka koma da ƙyar yaran ka su gane cewa kai babansu ne". Tana kaiwa nan ta ci gaba da sambaɗansa saida ta yi masa sambaɗe baɗe, sannan ta ci ka shi.


Isa wajan Hajiya Binta ta yi tare da janyo Zahra sannan ta kwashe ta da mari. Dafe ƙuncin ta Zahra ta yi, karo na farko a rayuwarta da hajiya Binta ta taɓa lafiya jikinta.

A matuƙar fusa ce Hajiya Binta ta kalleta sannan ta ce. "Me yake damunki Zahra?, shin kinyi hauka ne?, ɗan sanda da ki ka daka kin san abin da akan zata haifar?, dole ne na ɗau mataki a kan ki in ba aka ba za ki jawo min abin kunya ne".


Ɗaya daga cikin ƴan sandan ne ya ce. "Ba saikin ɗau mataki ba, mu da kanmu zamu ɗauki mataki a kanta. Don haka tun da harta sake ta ɗora hannunta a kan ɗan sanda dole ta fuskanci mummunan hukunci. Jami'ai maza ku kama ta ku wuce da ita offishi sannan ku saka ta a cell yau saita gane cewar Allah ɗaya ne".


Jin haka ya sa Hajiya Binta ta fara basu haƙuri. Ko kallonta basu yi ba haka suka kama Zahra tare da nufar inda motocin ƴan sanda suke. Ba tare da turjiya ba Zahra ta shiga cikin motan.

Shige wa suma suka yi cikin motan yayin da suka cinciɓi ɗan sandan da Zahra ta yi wa duka sannan suka saka shi cikin mota. Fice wa suka yi daga cikin magarƙamar. A sa'in da motar da aka saka ɗan sandan da Zahra ta yi wa duka ta wuce asibiti. Yayin da kuma sauram motocin suka wuce police station.


Suna isa chan suka fito daga cikin motocin yayin da suka kama Zahra sannan suka shigar da ita cikin police station tare da jefa ta cikin cell.




*****************
Ɓangaren Amrah kuwa neman ta suka yi suka rasa a cikin jejin.

Alama Umar ya yi musu da su koma cikin mota. Koma wa suka yi cikin mota gaba ɗaya yayin da suka tada mota tare da barin harabar dajin.


Kai tsaye gida suka koma yayin da suka zayyane wa mahaifin Umar duk abubuwan da suka faru.


************************
*AMERICA*
Cikin harshen turanci ya dubi abokin nasa ya ce. "John ya kamata ka manta da abin da ya faru, Diana bata yi akan da son ranta ba, ya kamata ka manta da komai". Cewar abokin nasa.

Kallonsa John ya yi sannan ya ce. "A kan mene ne zai sa na rabi ita?, a gaban jama'a ta ɗauki hannu sannan ta kwashe ni da mari, ko zan yafe komai ba zan taɓa yafe wannan abin da ta yi min ba. Ya zama dole na ɗauki fansar abin da ta aikata, saina shayar da ita azabar da har abada ba zata manta da ni ba. Ya zama dole na aure ta domin ita ɗin tawa ce ta ni kaɗai, bayan na aure ta zan gana mata azaba, ba dai tana ji da kanta ba, ni nan zan sauke mata jiji da kanta".

Yana kaiwa nan ya fice daga cikin ɗakin wanda ya gauraye da hayakin shisha.


******
Gaba ɗaya Aliyu ya rasa me kai masa dad'i. A duk sa'in da Safeera ta zo ta wuce ta gefen sa sai ya ga tamkar ya santa. Wayarsa ya ji tana ringing. Ɗaukar wayar ya yi ya ga numbern Nigeria ke kiran shi. sunan yallaɓai ne bayyane kan screen ɗin wayar. Ɗaga kiran ya yi tare da karawa a kunnensa. "Hello yallaɓai".


Daga ɗayan ɓangaren ya ce. "Ya batun maganar da muka yi da kai Aliyu?, kace za ka je ka ga MK a magarƙama har yanzu baka dawo bane?".


Cikin rashin fahimtar maganarsa Aliyu ya ce. "Ni kuma?, ni yaushe na ce zan je magarƙama?. Ni fa a halin yanzu ina America kwata-kwata bana ƙasar Nigeria, don aka ka bari idan na dawo Nigeria zamu yi magana". Yana kaiwa nan ya kashe wayar.


Sakin baki mutumin ya yi yana mai kallon wayar dake hannunsa. "Lallai Aliyu ka cika ɗan rainin wayo, za ka gane kuranka ne".


*******
Fitowa Safeera ta yi cikin ƙananun kaya wanda suka karɓi jikin ta tare da fara takawa tana nufar parlour.

Tsayawa Aliyu ya yi da danna waya tare da maida hankalinsa gaba ki ɗaya kan Safeera. Dogon tsaki Safeera ta ja ganin irin mayen kallon da Aliyu ke binta da shi.


Guri ta samu tare da zama. Cikin ɓacin rai Aliyu ya kalle ta sannan ya ce. "ke baki iya gaisuwa bane?".


Kallon shi Safeera ta yi tare da sakin miskilin murmushi sannan ta ce. "Ban iya ba saboda banga mutum a zaune ba".


Mamaki ne ya kama Aliyu ya ce. "Kin san wane ne ni kuwa?, kada ki fusata ni nayi abin da raina bai so ba".

Miƙe wa tsaye Safeera ta yi cike da ɓacin rai ta dube shi ta ce. "Me za ka yi?, kana nufin duka na za ka yi kome?".

Shigowa Daddy ya yi dai-dai lokacin da Safeera ta faɗi kalman "Duka na za ka yi?".


Kallon su biyun Daddy ya yi sannan ya ce. "Me yake faruwa ne?".


*********
*NIGERIA*.

Gaba ɗaya Umar ya rasa me ke masa daɗi. Tun da ya ga Amrah ya kasa zaune ya kasa tsaye. Zama ya yi kan faɗeɗen gadonsa sannan ya ce. "Who is she?, me ya sa take zaune a ciki wannan dajin?, shin bata da iyaye ne?, me ya sa take rayuwa cikin dabbobi?. Dole ita kaɗai ce zata iya bani amsar tambaya ta. Ya zama dole gobe na koma wannan dajin domin yin bincike. Samm ban yarda da wannan yarinyar ba". Ya faɗa yanaai ɗaukar wayarsa tare da shiga contact list sannan ya lalubo numbern ɗaya daga cikin jami'an sa.


Ringing biyu aka ɗaga kiran. "Hello ranka shi daɗe".

Furzar da iska Umar ya yi waje sannan ya ce. "Su waye a kan duty gobe?".

Amsa jami'in ya bashi da cewa. "Mune, shin da wata matsala ne?". Jami'in ya tambaya.

Amsa Umar ya bashi da cewa. "A'a ba bu wata matsala, dama ina so ne ka sanar da sauran jami'an da ke tare da kai cewa gobe zamu koma wannan dajin".


"What!". Jami'in ya faɗa sannan ya ƙara da cewa. "Sir dajin nan yana da matuƙar hatsari, baka ga abin da ya faru bane ɗa zu?, mahaifinka ya sanar da ni cewa kada mu sake mu ƙara zuwa wannan dajin koda ka buƙaci muje, an sorry sir amma ba zan iya bujire wa umarnin mahaifinka ba". Yana kaiwa nan ya kashe wayar.


A matuƙar fusa ce Umar ya wurgar da wayar ta faɗi ƙasa. Dafe kanshi ya yi jin yana mugun sara masa. "What is wrong with me?, me ya sa gaba ɗaya ina neman in fita daga cikin hayyaci na saboda wannan yarinyar ƴar daji, why am I worrying myself because of that forest girl?, what am I suppose to do now?, ya zama dole na koma wannan dajin domin fitar da ita daga cikin wannan jejin, because her life is in risk and i need to rescue her life, if not ba zan yafe wa kaina ba".


**********
Washe gari da safe ƴan sanda suka nufi hanyar kotu da Zahra.


Suna isa suka tarar da ƴan jarida cike a bakin kotu. Ganin motar su Zahra ta ƙaraso ya sa ƴan jarida suka nufi inda motar take da sauri yayin da suka saura cameras ɗin su da speaker.

Fitowa Zahra ta yi ba bu wani alamun tsoro a tattare da ita.

Da sauri ɗaya daga cikin ƴan jaridan ta saita Mic saitin bakin Zahra sannan ta ce. "Shin za ki iya faɗa mana dalilin me ya sa ki ka daki ɗan sanda?".


Murmushi Zahra ta yi sannan ta ce. "Ku saita cameran ku da kyau ta yadda kowa zai ganni".


Saura kamerorin ƴan jaridan suka yi da kyau. Gyara tsayuwar ta Zahra ta yi hannayenta sanye da handcuf sannan ta ce. "Na dake sa ne domin ya zagar min mahaifiya, kuma ni mahaifiyata tamkar zinariya ce a gare ni, bana wasa da ita. Duk wanda ya yi ƙoƙarin zagar min mahaifiya to saina koya masa hankali, gudun karya je ya aikata wa wani bayan ni ya saka nayi masa mugun duka. Ba mahaifiyata ba ko mahaifiyar wani na ga an zaga ba zan ƙyale mutum ba, domin iyaye ba abin wasa bane". Tana kaiwa nan ta shige cikin kotun.


Nan take ƴan jarida suka fara sakawa a news ɗin su yayin da ko ina a garin ya ɗauka. Ba bu abin da ka ke ji da gani a gari sai maganar da Zahra ta yi.



***********
Kunna tv Mom ta yi nan taje ta fara ganin news na yawo a tv. Rass! rass! gaban ta ya faɗi!. Wasu irin zufa ne suka fara ƙeto mata ta ko wane sashe na jikin ta.


Ɗaukar medical glass ɗinta ta yi tare da sanya wa a idonta sannan ta maida kallonta kan tv. "Wannan kamar Safeera".


Miƙe wa ta yi tare da ƙwalla wa duka ƴan gidan kira. Da sauri su Daddy da ke parlour suka nufi ɗakin Mom.


"Shiga cikin ɗakin su Safeera suka yi. Yayin da Daddy ya tambaye ta ."meya faru?". Nuna tv Mom ta yi.


Nan take idanuwan Safeera dasu Daddy ya sauka a kan tv. "Rasss gaban kowanensu ya faɗi! sakamakon ganin abin da basu yi tsammanin gani ba.




@@@@@@@@@@@@



*AM SORRY FOR THE LATE UPDATE PLEASE 🥺 🥺*


ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
(Zinariyar Jajirtattu)

https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g


🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐.
Daji 🌲
Magarƙama🏢 da kuma
Birni🏙️

WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝♀️Jajirtattu)


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 1️⃣7️⃣▶️1️⃣8️⃣
*_________________________________________________*
Abin da ya firgita su ba komai bane illa ganin film na horror wanda ke bayyane kan tv ɗin.


Kallon Mom Daddy ya yi sannan ya ce. "Ke kin san za ki dinga tsorata ki ke kallon film ɗin horror?, wallahi ki ka sake yi mana irin aka sai na ɓata miki rai".


"Film ɗin horror kuma?". A cewar Mom. Maida kallonta ta yi kan tv ɗin. Da mamakin ta ta ga an chanza tashar da ta ga Zahra. Girgiza kai ta yi sannan ta ce.


"A'a ba wannan tashar nake kallo ba, ina kallon news ne, kuma abin da ya tsoratar da ni ba komai bane fa ce ganin mai kama da Safeera da nayi. Babu banbanci tsakanin ita da Safeera. Sai dai wancan eyes ɗin ta ba blue bane brown ne".


"What! gaba ɗaya suka furta. A sa'inda suka kalli juna tare da kwashe wa da dariya. Maida kallonta Safeera ta yi kan Mom sannan ta ce.

"Ni kuma Mom?, how can that be possible?, ta ya ya kuma za'a ga mai kama da ni, hanya Mom kin goge medical glass ɗin ki kafin ki

Please Login or Register in order to submit comment