Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sir". Ta faɗa tana mai miƙe wa tsaye tsreda fice wa daga ɗakin.


Zama Doctor ɗin ya yi yana mai kallon Amra wanda ke a kan fanka. "Abin mamaki baya ƙare wa, yanzun nan da na fito daga ɗakin ɗayar yarinyar amma kuma yanzu na zo nan, na tarar da mai kama da ita sakk. Wai ko dai na sha maye ne yau?". Ya tambayi kansa.



******
"Shi ya san abin da ya gani hankalin sa ya tashi, koma dai mene ne zan je ɗakin na gani". Cewar nurse Nadiya. Tana isa ƙofar ɗakin ta murɗa handle ɗin ƙofan.


Chan ta hango Safeera a kwance. Riƙe haɓar ta nurse Nadiya ta yi ta ce. "Lahaula, Amrah wato har kin riga ni zuwa nan ɗin ma. Ta ina ki ka bi har ki ka riga ni zuwa?". Dube-dube ta fara yi.



"To wai ina mara lafiyar take ne?, wato dai wannan likitan so yake kawai ya bani wahala shi ya sa ya ce min wai akwai mara lafiya a nan". Ta faɗa tana mai maida kallonta kan safeera wacce ke kwance kan gado idanuwanta a lumshe.


Mamaki ne ya kama nurse Nadiya ganin cewar tufafin da ke jikin Safeera ba irin shi ne a jikin Amrah ba. "Ta ya ya Amrah ta iya sauya kaya cikin ƙanƙanin lokaci aka?". Nurse Nadiya ta tambayi kanta.


Furzar da iska ta yi sannan ta ce. "Mybe ni ce
ban duba ba sosai . Amrah ina zuwa bara naje na faɗa wa Doctor ɗin cewa banga mara lafiyar da ya faɗa ba". Ta faɗa tare da fice wa daga cikin ɗakin.


Nufar ɗakin da Amrah take ta yi. Tana isa ƙofar ɗakin ta buɗe tare da shiga cik. Yayin da idanuwanta suka sauka a kan Amrah. Nan take gabanta ya yi mummunar faɗuwa!, yayin da gabanta ya shiga dukan uku-uku. Babu zato ta ji kanta ya yi mugun sara mata. baki na rawa ta ce.


" Amrah!, kenen ba Amrah na gani a wan can ɗakin ba?, to in dai da gaske ba Amrah bace a wannan ɗakin ita kuma ta cikin ɗakin wace ce?".



💃💃💃🌹🌹💃💃💃

*TASHIN KAI, NURSE NADIYA FA TA SHIGA RUƊANI KOMAI ZAI FARU IDAN TA GANO CEWAR SU BIYU NE A ASIBITIN, SANNAN KUMA YARAN LAILAH ABDULLAHI NE?. MUJE DAI ZUWA*



*WAYYO LOW BATTERY 🔅 🔋, MUNA FAMA DA RASHIN WUTA BANI DA CHARJI🥺, JIYA MA NASO NAYI MUKU AMMA RASHIN WUTA YA HANA. KUYI HAƘURI DA WANNAN PAGE PLEASE 🙏*.


KARKU MANTA DA SHARING, COMMENTS, AND LIKES FISABILULLAH 🙏🙏🙏🙏.


ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
(Zinariyar🧝♀️Jajirtattu)

Follow the 💖 A'ISHA M.B✍️ HAUSA NOVELS 📚 WORLD 🌎 📚💗💖 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g




*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐.
Daji 🌲
Magarƙama🏢 da kuma
Birni🏙️

WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝♀️Jajirtattu)

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 2️⃣3️⃣▶️2️⃣4️⃣
*_________________________________________________*
Nurse Nadiya ta faɗa cikin ruɗu da gigicewa. Kuma maida kallonta ta yi kan Amra sannan ta ce. "Amrah green eyes ne da ita, ita kuma wan can fa?, to in har wan can ta ɗakin blue eyes ce da ita hakan yana nufin ƴaƴan Mrs Laila ne".


Ta faɗa tana kuma koma wa ɗakin da ta ga Safeera. Tana ƙarasawa ƙofar ɗakin ta shiga ciki. Da mamakin ta kuwa sai ta ga babu kowa a ɗakin.


Hakan ba ƙaramin mamaki da tsoro ya sanya ta ba. "Kodai na fara gane-gane ne?, ba'a nan ɗakin ba ɗa zu naga wata mai kama da Amrah?, where is she?". Ta tambayi kanta.


Tuna wa da cewar Umar ya ce kada ta bar Amrah ita kaɗai ya sanya ta saurin barin wajan tare da nufar in da ɗakin da Amrah take.



Safeera kuwa bata je ko ina ba sai bandaƙi domin ɗaura alwala. Bayan ta gama ta fito daga cikin toilet ɗin yayin da ta duba ko ina amma babu hijab sai iya ɗingilallen mayafin ta.

Zama ta yi a bakin gado sannan ta duba arabar wajan. Sai a lokacin ta lura cewar ba'a gida take ba.


Zumbur ta miƙe tsaye tana mai waige-waige. Hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba, ganin cewa tabbas nan ba ɗakin ta ba ne. Kwalla kiran sunan Mom ta fara yi cikin tsoro da fargaba. Su Mom da ke reception jin muryar Safeera hakan ya sa su yin saurin nufar ɗakin da take.


Da sauri suka shiga ɗakin suka tadda ta tsaye gaba ɗaya duk ta bi ta rikice.

Kallonta Mom ta yi ta ce. "Ƴata Safeera kin farka?, Alhamdulillah Allah na gode maka".


Duban Mom Safeera ta yi ta ce. "Mom where am I?, which place is this?, Mom what's going on because I don't understand am confuse, this place doesn't look similar".



Ajiyan zuciya Mom ta sauke sannan ta ce. "Safeera calm yourself down okay?, nan wajan da ki ke gani ba America ba ne, yanzu haka muna Nigeria ne".


Zaro idanuwa waje Safeera ta yi. "What!". Ta furta cikin tashin hankali ta ce. "Why mom why?, me ya sa muka zo Nigeria bayan na faɗa muku cewa bamu kammala second semester ɗin mu ba?, and you know tomorrow am having a paper, so now what do you expect me to do now?". Ta faɗa damuwa bayyane kan fuskarta.


Kallonta Aliyu ya yi baki ya ce. "Sannu Mommy's pet, ke hana ta rai wa yake ta karatu?, idan babu rai za ki iya zuwa ki rubuta paper ɗin?, abin da ya sa muka kawo ki ƙasar nan mun ɗauka kina da aljanu ne shi ya sa kuma cinciɓo ki muka tawo da ke".


Kallonsa ta yi cikin rashin fahimta ta ce. "Aljanu!, mene ne kuma aljanu?".


Kallon baki da hankali Aliyu ya bita da shi ya ce. "Kije kiyi searching a google zai baki amsa. Aikin banza wai mene ne aljanu".


Ran Safeera ne ya ɓaci ta dube shi ta ce. "Kai mind your word's, I can't tolerate any stinking shit from you okay, apart from that ma, i dislike Nigeria, the country it so disgusting I prefer America, Mom please let's go back, there is too much heat here and dirty environment".


Sakin baki Aliyu ya yi yana kallonta sannan ya ce. "Sannu ƴar America, to iyayen ki ƴan Nigeria ne, kuma nan ƙasar mu ce ta gado, ko kina so ko bakya so sai kin zauna, sannan tun da kakannin ki da iyayen ki suka zauna wajibi ne kema saikin zauna".


Kallon Aliyu Daddy ya yi ya ce. "Ka ga ka rabu da ƴata, idan ta ce bata so fine sai mu koma, ba wani abun tayar da hankali ba ne. Yanzu dai bara naje na samu Doctor ya zo ya duba ki, idan ya ce kun samun sauƙi zamu iya tafiya da ke sai mu wuce gidan mu, na san Baba zai yi farin ciki sosai".


Yana kaiwa nan ya fita daga cikin ɗakin.


Ɓangaren Nurse Nadiya kuwa tana zuwa ta tarar Amrah bata ciki ɗakin. Bincika ko ina ta yi na ɗakin ta ga ba ta ciki. "Innalilahi wa innahilahir rajihun!". Kalmar da ta fito daga bakin ta kenen.


Cikin tashin hankali ta ce. "Na shiga uku ni Nadiya!, ina kuma Amrah ta shiga?, yanzu me zan faɗa wa mijin ta idan ya zo". Tana cikin magana taji sallamar Umar.


Amsa sallamar sa ta yi tana mai maida kallonta kansa. Dubanta Umar ya yi ya ce. "Nurse lafiya naga kamar hankalin ki a tashe?".



Ajiyan zuciya Nurse Nadiya ta sauke!, sannan ta ce. "Ina da lafiya, naje domin duba wata a wan can ɗakin, kafin naje na dawo sai naga matar ka Amrah ba ta cikin wannan ɗakin.


"What!". Umar ya furta. "Kamar ya ba ta cikin ɗakin?, saida na faɗa miki fa cewa kada ki barta kije ko ina saboda ita ɗin ba kamar mu take ba daga daji take. And besides Amrah ba matata ba ce ba, nayi helping ɗinta ne kawai. Ni yanzu ina ki ke so naje na nemo ta fisabilullah?". Ya faɗa tare da fice wa daga cikin ɗakin.


Fita ya yi daga harabar wajan baki ɗaya. yayin da ya saka securities suka bincika masa asibitin baki ɗaya.
Duba ko ina na harabar asibitin suka yi amma babu alamun Amrah.


Gaba ɗaya hankalin Omar ba ƙaramin tashi ya yi ba. Da sauri ya shiga cikin mota tare da tada motan sannan ya bar harabar wajan.

Tuƙi ya fara yi yayin da yake buga styring motan da ƙarfi. Cije leɓensa wanda suke jajir ya yi. Tare da shafa sumar kansa.


Kamar an ce masa ya juya. Juya wa ya yi ɗayan ɓangaren. Zaro idanuwa ya yi waje ganin Amrah daga ɗayan side ɗin titi kan bishiyar mangwaro.


"Alhamdulillah". ya furta tare da samun guri a hanyar titin ya yi parking.

Fitowa ya yi tare da tsallaka wa izuwa ɗayan ɓangaren da Amrah take.



******************
Su DPO kuwa sunyi neman duniya basu ga Zahra ba hakan ya sa ba yacce suka iya suka kama hanyar Jigawa.

******

Zahra kuwa da ta ga zaman bakin titi ba zai finshe ta hakan ya sa ta miƙe wa tsaye sannan ta fara tafiya. A matuƙar gajiye take tafiya ba tare da ta san in da take nufa ba.


Tafiya ta yi mai nisan gaske kafi daga bisani ta tsagaita da tafiya. Tsayawa ta yi ta kalli gabas da arewa ta ce. "To wai nan ina ne?, yanzu ta ya ya zan koma Jigawa?, idan na ci gaba da tsaya wa aka yunwa ce za ta kashe ni. Ya zama dole na nemi mafita". Chan ta hango wani shago na kayan cosmetics.
Ba ta yi ƙasa a gwiwa ba ta ƙarasa cikin shagon.


Sallama ta yi mai shagon ya amsa yana mai kallon kayan dake sanye a jikinta.


Ganin yana binta da kallo hakan ya sa ran Zahra ya soma ɓaci dubansa ta yi ta ce. "Malam ya dai ka ke kallo na?, kona yi maka kama da wacce ta yi gudun hijira ne?".


Kawar da kansa mutumin ya yi yana mai ci-gaba da karkaɗe kayansa sannan ya ce. "Ai naga kina sanye da kayan ƴan magarƙama ne dole naji tsoro kuma na kalle ki, haka kurin hana zaune ƙalau ki ƙundume min kaya".


Hangame baki Zahra ta yi ta ce. "Ni nayi maka kala da ɓarauniya?, to idan baka sani ba ni ce ƴar gatan magarƙama, wanda a kaff magarƙaman jigawa babu wacce ake ji da ita sama da ni. Karka sake ce min ɓarauniya". Ta faɗa tana mai gyara tsayuwar ta sannan ta ce. "Dama na zo nan ne na tambaye ka cewa nan wajan ina ne?".


Dubanta mai shagon ya yi ya ce. "Nan zoo road ne kin gane".


Jinjina kai Zahra ta yi ta ce. "Tom naji idan babu damuwa dan Allah ka ɗauke ni aiki saboda na tara kuɗi na koma jigawa".



Girgiza kai mutumin ya yi ya ce. "Ni?, chab ɗi jam, A'a kam kiyi haƙuri amma ba zan iya ɗaukar ƴar magarƙama aiki ba gaskiya, ba zan ɗauki wannan kasadar ba".


Kallon shi Zahra ta yi ta ce. "To su ƴan magarƙamar ba mutane ba ne?, kenen basu da damar neman aiki?, ni zan yi aiki ne kawai saboda na tara kuɗaɗe na koma in da na fito, domin ni naga alamun ma zaman magarƙama ya fi nan wajan ƴanci".



Kallonta mai shagon ya yi ya ce. "Yafi nan ƴanci me ya sa to ki ka gudo daga cikin magarƙamar?, kamata ai a ce ki zauna a chan tun da yafi nan ɗin ƴanci. Ni dai ba zan baki aiki ba sai dai zan baku shawara guda ɗaya wacce za ta yi miki amfani. Shawarar ita ce. Ki samu kwano ki zauna a bakin titi kiyi bara na san za'a taimaka miki. Ina ganin kamar hakan zai fi".



Murmushin takaici Zahra ta yi ta ce. "Naje bakin titi inda kowa ke wuce wa nayi bara ko?, kuma kai ɗin mutum ne da gaske mai zuciyar imani?, ta ya ya za ka ce naje nayi bara?, da a ce ni ƙanwar ka ce ko ƴarka haka za ka ce naje nayi bara?, tirr da halinka. Ni dai da nayi bara na gwammace na dauwama a wannan garin banje ko ina ba, haramunne yin roƙo idan baka sani ba yau ka sani. Shashashan banza kawai alade". Tana kaiwa nan ta ja tsaki tare da barin shagon.



Jikin mutumin ne ya yi sanyi. basar wa ya yi ya ci-gaba da aikin da ke gabansa.



*****************
*MASARAUTA*
"Kayi haƙuri mai martaba hakan ba zata sake faruwa ba". Prince Junaid ya faɗa yana mai duƙar da kai.


Kallonsa mai martaba ya yi ya ce. "Na san iya Sooraj ne kaɗai zai yi maganin ka". Barin wajan mai martaba ya yi ya bar Junaid a tsaye.

Ajiyan zuciya Junaid ya sauke tare da faɗin. "Allah na gode maka da bai ce zai faɗa wa yahya Sooraj ba da na shiga uku". Yana kaiwa nan ya fita harabar fadan.


Masha Allah baki na ya iya furta wa ganin yadda masarautar take da matuƙar girma da kyau.


Grand entrance na hango daga nesa ƙofa mai matuƙar ban sha'awa yayinda bangare guda ƙofofi ne masu ado na gida je cikin masarautar.

Yayin da katangar wajen masarautar anyi sa ne da dutse mai sheƙi tamkar lu'ulu'u tare da sassakaƙƙun sassaƙa na tagogi mai ƙyalli.


Chan gefe kuma baranda ce wacce tsayin ta baki ba zai gama faɗi ba.

Chan gefe turret ne da husumiya spiers mai tafiya da imanin mutum.


Ɓangare ɗaya kuma manyan fadoji ne tare da kyawawan kayan ado wanda aka haɗa da chandeliers na kristal masu kyau gaba ɗaya kayan kwalliya ne ya cikashe su tare da kayan al'atu da kayan more rayuwa. An ƙawata fadojijin da sassakaƙƙun sassaƙa wanda ke nuna fasaha na musamman.

Bangare ɗaya kuma manyan zaure ne da ɗakunan karaga masu kyau an tsara su don dalilai na biki dana hukuma.

tare da ɗakunan ma'aikata da na fadawa harda na bayin masarautar.


Chan ɓangaren kuma kyawawan lambuna ne wanda ya ƙawata masarautar ta kuma bada wata iriyar kyau mara misaltuwa.



Ɓangare ɗaya kuma ɗakunan kayan tarihi ne da kayan al'adun mu na gargajiya sai gwala-gwalai da lu'ulu'u masu matuƙar sheƙi da kyau.

Tsayawa misalta yadda masarautar nan take da kyau ɓata lokaci ne ku dai kawai ku fasalta a ranku.


Kai tsaye cikin labari.


Direct garden Junaid ya nufa yayin da ya samu karƙashi bishiya ya zauna. Ganin fitowar sa ya sa ma'aikata da fada wa suka ƙaraso wajan sa suka fara kwasar gaisuwa suna mai yi masa ƙirari.


Dakatar da su Junaid ya yi ya ce. "Ku tafi ya isa". Jin hakan ya sa suka bar wajan suka ci gaba da harkar gabansu.


Dafe kansa Junaid ya yi ya ce. "Ni yanzu a ina zan samo maƙullin nan, kuma ina da tabbacin cewa yana wajan wannan ƴar dabar nan ta ɗazu, to a ina ma zan ganta?, kuma muƙullin nan yana da mahimmanci sosai, gashi mai martaba ba zai barni na fita daga masarautar nan ba. Yanzu ya zan yi kenen?". Ya tambayi kansa.





********
Ɓangaren Umar kuwa yana tsallaka wa ya sauko da Amrah daga kan bishiya yayin da ya ga fuskarta shaɓe-shaɓe da hawaye babu abin da take yi sai kuka.



Damuwa ne ya lulluɓe fuskar Umar. Kallonta ya yi ya ce. "Amrah me ya faru?, kina son ki koma wajan ƴan uwan kine?".


Babu tsanmani ya ga ta girgiza masa kai. Mamaki ne ya kama shi. Cike da farin ciki ya ce. "Kina iya fahimtar abin da nake cewa?".


Gyaɗa kai ta kuma yi a karo na biyu.

Hamdala Umar ya yi ya ce. "Shi ke nen naji dad'i tun da kina iya fahimtar abin da nake cewa. Yanzu dai kina so ne na kaiki wajan ƴan uwan ki ko".


Gyaɗa masa kai ta yi. Tare da fara kalle-kalle. Nan ta hango ruwa wanda ya zuba a ƙasa.


Murmushi ta yi tare da wafce hannunta ta nufi in da ruwan yake.

Ganin hakan ya sa Umar bai yi ƙasa a gwiwa wajan bin bayanta ba.

Tana isa bakin ruwan datti da ya zuba a ƙasa ta tsugunna kan gwiwowinta tare da kokarin kai hannunta kan ruwan domin ta sha.


Ganin hakan ya sa Umar saurin dakatar da ita. Mikar da ita ya yi ya ce. "A'a Amrah karki damu in dai ƙishin ruwa ki ke ji zan siya miki ruwa ba saiki sha na datti ba, maza tawo mu je".


Ya faɗa tare da jan hannunta. Ba musu Amrah ta bi bayanshi yayin da babu abin da take ta faman yi illa kallon jama'ar da ke wajan tare da tufafin da ke sanye jikin su. Kallon jikinta ta yi ta ga dai ita nata tufafin da nasu da iri ɗaya ba ne domin naya na ganye ne.


Binta jama'ar wajan kawai suke da kallo.

Wani ƙaramin super market Umar ya samu ya shiga da Amrah yayin da ya yi order ruwa. Cikin lokaci ƙalilan aka kawo masa ruwan roba. Karɓan ruwan Umar ya yi tare da buɗe murfin roban ruwan sannan ya miƙa wa Amrah.


Bin roban da kallo kawai Amrah ta yi tare da kawar da kanta.


Sauke ajiyan zuciya Umar ya yi sannan ya ce. "Ki karɓa ki sha ruwa ne fa, maza karɓi ki sha idan ya so muje na kaiki gidan mu ina da ƙanne za su kula da ke kinji".


Karɓar roban ruwan Amrah ta yi tana mai jujjuyawa a hannunta. Taɓe baki ta yi sannan ta fara kwararar da ruwan a ƙasa.


"Ya Salam". Umar ya furta yana mai dafe kansa. Karɓar ruwan ya yi sannan ya fara bata da kansa. Take ta shanye ruwan tasss.



Mamaki ne ya kama Umar ganin lokaci ƙalilan ta shanye ruwan roba ɗaya. Girgiza kai Umar ya yi sannan ya ce. Tashi mu tafi ko.



Gaba ɗaya mutanen super market ɗin sai binsu Umar suke da kallo most especially Amrah wanda suka ga shigar ta sakk irin na ƴan jeji.


Lura da Umar ya yi cewa mutanen wajan su suke kallo hakan ya sa shi miƙe wa tsaye sannan ya je ya bada kuɗin ruwan roban da ya siya. Tare da jan hannun Amrah suka fice daga wajan.


Tafiya suka fara yi yayin da Umar yake ta faman kallon Amrah. Wai shi ne yau tare da mace yana lallaɓa ta kamar ƙwai. Abun ba ƙaramin mamaki yake ba shi ba.



Ba zato ya ga Amrah ta ƙwace hannunta daga nasa ta fara gudu. Zaro ido Umar ya yi tare da saurin bin bayan ta.


"Amrah ina za ki je?, ki dakata, oh my God hanya ban ɗaura ruwan dafa kaina ba kuwa ni Umar?".


Abin da ya sa Amrah gudu kuwa bakomai ba ne fa ce gani da ta yi wata mai ciki za ta tsallaka titi ga mota ya tawo sai faman sharara gudu yake.


Hakan ya ja hankulan mutane yayin da suka fara ihuuu taimako.


Kaɗan ya rage mota ya buge matar da sauri Amrah ta sha gaban matan tare da matsar da ita gefe.


Nan take motan ya buge Amrah. Zaro ido jama'ar wajan da Umar suka yi.


Ga mamakin su kuwa sai gani suka yi ta tashi sama tare da sauka ƙasa ta tsaya chakk tamkar ba ita mota ya buge ba.


Sakin baki mutane suka yi ganin abun mamaki da ya faru a dai-dai lokacin.


Ɓangaren Umar kuwa abin ba ƙaramin mamaki ya bashi ba ganin yadda mota ta kaɗe ta amma bata faɗi ba.


Saurin zuwa bakin titin Umar ya yi tare da jan hannun Amrah. Janyo ta ya yi har izuwa in da motar sa yake sannan ya tsaya ya dube ta ya ce. "Kina da hankali kuwa?, chan fa tsakiyar titi ne ba kamar dajin ku ba ne wanda za ki dinga tsalle kina shiga da fice yadda ranki yake so, yanzu da a ce wani abu ya same ki fa, kin san wane hali zan shiga". Ya ƙarasa maganar yana mai kallonta.


Lura da ya yi cewar gaba ɗaya hankalin ta ba'a kansa yake ba yana wani wajan da ban ya sa shi faɗin. "To wai wannan ina take kallo?".


Ya faɗa yana mai bin in da take kallo da kallo. Mai mangwaro ya hango zaune a bakin junction.


Kallonta ya yi ya ce. "Shima mangwaron sha za ki yi?".

Gyaɗa masa kai ta yi.

Takaici ne ya kama shi ya ce. "Ke yanzu komai ki ka gani za ki sha?, to ai yanzu dai bamua kusa da wajan saiki tawo mu tafi".


Ya faɗa tare da juyawa sannan ya buɗe mata ƙofar ƴan zaman banza. "Zo ki shiga". Ya faɗa hin shiru bata shiga ba ya sa shi juyawa.


Zaro idanuwa ya yi waje ya ce. "Ina kuma ta shiga?". Daga chan tsallake ya hango ta wajan mai mangwaro babu abin da take ta faman yi sai gwawuyan mangwaro kamar ta samu goruba.


Ɗora hannunsa biyu Umar ya yi a kai ya ce. "Ya Allah!". Tafiya ya fara yi tare da tsallaka wa bakin titin ganin ta sha mangwaro sun kai biyar hakan ya sa ya ciri kuɗi a aljihun shi ya biya mai mangwaron. Maida kallonsa ya yi kanta tareda fara janta. janta ya fara yi ya ga dai taƙi jawuwa. Ganin hakan ba zai finshe shi ba ya sa shi ɗaukarta chakk sannan ya nufi in da motar sa take.


Tafiya ya yi sosai kafin daga baya ya isa in da motar sa take sannan ya saka ta a cikin motan tare da saka wa ƙofar lock.

Koma wa ya yi mazaunin driver sannan ya tada motar suka bar harabar wajan.


A takure ta zauna a cikin motan yayin da iskan AC ya addabe ta. Hannu ta saka tana mai ƙoƙarin fasa glass ɗin motan domin ta shaƙi iskar waje.



Ganin tana ƙoƙarin fasa glass ya sa Umar saurin kashe Ac ɗin.



**********
"Yanzu dai munyi magana da Doctor ya ce kin samu sauƙi sosai zamu iya tafiya da ke".



Murmushi Safeera ta yi ta ce. "Na gode Daddy amma yanzu Airport zamu wuce ko?".


Amsa Daddy ya bata da cewa. "A'a dole sai mun je mun fara ganin su grandma da grandpa ɗin ki tukun".


Taɓe baki Safeera ta yi ta ce. "Shi ke nen, amma muna zuwa zamu koma America, saboda i can't stay here".

Fita suka yi gaba ɗaya tare da shiga cikin motan taxin da ya ɗauko su daga airport sannan suka fice daga harabar asibitin. Kai tsaye hanyar gidan Grandpa suka nufa.


Dai-dai junction suka tsaya sakamakon goslow da ya cike wajan.



Daga nesa Safeera ta hango mai mangwaro. Murmushi ta yi ta ce. "Laa Mom dama akwai Mango a Nigeria?, ina so zan sha please Mom".



Kallonta Mom ta yi ta ce. "A'a Safeera nan titi ne ki bari Aliyu zai zo ya siya miki daga baya".


"No Mom gaskiya ni ba zan iya jira ba". Tana kaiwa nan ta fice daga cikin motan tare da tsallaka wa ɗayan ɓangaren.


Ganin hakan ya sa Mom fita daga cikin motan sannan ta bita a baya.


Safeera na zuwa ta kalli mai mangwaron ta ce. "Hey you, I need one mango how much dollar is it?".


Ƙura mata idanu mai mangwaron ya yi yayin da mamaki ya bayyana kan fuskar shi.


Kallonta ya yi ya ce. "Bake ba ce yanzu ki ka sha mangwaro guda biyar da tufafin ƴan daji?".


Ƙarasawa wajan Mom ta yi ta kalli Safeera ta ce. "Ki tawo mu tafi babu Nigeria money yanzu a waje na, they don't deal with dollar okay let's go".



Miƙa mai dollar ɗaya Safeera ta yi ta ce. "Take it I need one mango".


Kallon kuɗin mai mangwaro ya yi ya ce. "Ni za ki kawo wa kuɗi bogi. yanzu-yanzu da ki ka sha mangwaro kusan biyar amma a ce har kin dawo za ki ƙara".


Kallon mai mangwaron Mom ta yi cikin rashin fahimta ta ce. "Ƴata kuma?, hanya kuwa?, yanzu fa ta zo nan wajan".


Girgiza kai mai mangwaron ya yi ya ce. "A'a Hajiya, ɗa zu ƴarki ta zo sai dai ba wannan shigar ba ne a jikinta, ita ne da wani ya zo ya ɗauke ta a nan suka tafi. Nayi mamaki ne ganin lokaci ƙalilan harta chanza kaya ta kuma dawo wa sannan kuma idanuwanta naga ba kalar da ɗa su ba ne na ɗazu kamar kore ne idanuwanta".



Sai a lokacin Mom ta tuna da mai kama da Safeera da ta gani a Tv.


Kallon Safeera Mom ta yi ta ce. "Babu shakka magana ta gaskiya ce, kenen da gaske ne akwai mai kama da

Please Login or Register in order to submit comment