Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

so daga nan sai a wuce da ita ƙasar waje".



Godiya ɗaya daga cikin kidnapper's ɗin ya yi. Sannan ya kashe wayar. Sakawa ya yi haka kunce.


Miƙe wa tsaye Amrah ta yi tana mai kalle-kalle ta ce. "Ina ne nan wajan?, me ya sa ku ka kawo ni nan?, su waye ku?". Tambayoyin da ta shiga yi musu kenan.


Shiru kowanensu ya yi mata ba tare da ya sanar da ita komai ba.



Basu yi aune ba suka ji tsayuwar mota a wajan. Da sauri gaba ɗaya suka juya. Umar ne tare da su Ramlat suna mai nufo wa wajan.



Murmushi su kidnapper's ɗin suka yi. Take gaba ɗaya suka sara masa. Ƙarasowa wajan Umar ya yi yana mai sakin murmushi ya ce. "Nice job guy's". Ya faɗa yana mai maida kallonsa kan Amrah.


Su Ramlat kuwa da sauri suka nufi kan Amrah tare da rungume ta suna mai fashe wa da kuka.



Kallon jami'an nasa Umar ya yi ya ce. "Kun gano wane ne ya sa aka sace Amrah?".


Shiru jami'an suka yi yayin da ɗaya daga cikin su ya ce. "A'a yallaɓai".


Girgiza kai Umar ya yi ya ce. "Ƙarya ne, kada ku ji tsoro, kawai ku gaya min gaskiya".


Cire jikinta Amrah ta yi daga na su Ramlat sannan ta nufi inda Umar yake ta ce. "Me ya sa ka zo nan?, me ya sa ka saka aka sace ni?".


Furzar da iska Umar ya yi waje sannan ya ce. "Amrah zan yi miki bayani daga baya, yanzu bamu da wannan lokacin".

Girgiza kai Amrah ta yi ta ce. "A'a ni yanzu za ka faɗa min".


Shiru Umar ya yi na ɗan wasu lokaci sannan daga bisani ya ce. "Na sa an sace ki ne saboda na gano cewar akwai wani wanda ke ƙoƙarin ya sace ki, tun a gidan zoo na fahimci hakan, hakan ya sa na sa jami'ai na suka bibiyi bayan wanda suka zo gidan zoo, a nan muka kama ɗaya daga cikin su ya faɗa mana cewa wani ne ya ce su sace ki amma kuma basu faɗa mana ko wane ne ba, jin hakan ya sa a ranar da kika zubar da abinci na mare ki saboda kiji aushi ki fita idan ya so su kuma jami'ai na su sace ki domin ki kasance cikin tsaro. Amma ina mai baki haƙuri bisa ga marin da nayi miki kinji".


Shiru Amrah ta yi dan ita ba ta wani fahimce shi ba sosai. Waige-waige ta fara yi. Chan ta hango manya manyan bishiyu masu ɗaukar ido. Washe baki ta yi tare da sakin murmushi da sauri ta nufi inda bishiyun suke ta fara ɗane su tamkar ƴar biri, aka ta fara aye wa kan bishiyu ɗaya bayan ɗaya tana mai yin tsalle a kansu.


Gaba ɗaya babu abin da suke faman yi in banda binta da idanuwa.


Juyawa Umar ya yi ya maida kallonsa kan ɗaya daga cikin jami'ansa ya ce. "Ku gaya min wane ne wanda ya sa a sace Amrah, kada ka damu kawai faɗa min".


Kallonsa jami'in ya yi ya ce. "Maganar gaskiya ainiyin wanda ya sa a sace Amrah shi ne mahaifin ka wato Gov. Musa Muhammad, mun gano shi ɗin yana aikata miyagun laifuka, yana safaran mata tare da shigo da ƙwayoyi ba tare da izinin kowa ba, am sorry to say sir but your Father is a big terrorist kuma bai cancanci zama Govnor ba".


Jin maganganun jami'in Umar ya yi tamkar saukar aradu. "Mahaifi na, safaran miyagun kwayoyi da kuma mata!". ya faɗa yana mai cigaba da nanata maganar.


"I can't believe this, ni fa jami'i ne, ban yarda Baba na zai aikata hakan ba".


"Gaskiya nake faɗa maka yallaɓai, amma idan baka yarda ba shi ke nen". Cewar jami'in.


Nan take ran Umar ya ɓaci yayin da yaji tsanar mahaifin na shi ya shiga cikin ranshi. Duban kowanensu ya yi ya ce. "Ku kulan mun da su zanje Kano yanzu wajan mahaifi na, sannan na kama da na damƙa sa wajan ƴan sanda".


Ya faɗa yana mai barin wajan kai tsaye inda motar sa take ya nufa tare da tada motan sannan ya bar harabar wajan.




*******************
*JIGAWA*
Shiga cikin dajin Aliyu ya yi yana mai faka motarsa. Fitowa ya yi daga cikin motan. Chan ya hango Safira zaune kan dutse gaba ɗaya idanuwanta sun kumbura saboda kuka.


Ƙarasa wa inda take ya yi. Ganin Aliyu ya sa Safira saurin miƙe wa tsaye tana mai ja da baya ta ce. "Don't you dare!, karka kuskure ka zo inda nake. Nayi maka kallon mutumin kirki, ashe kai ɗin mugu ne, mena yi maka da zaka sa a sace ni?, wai kuma a hakan ni za ka aura?, i have never knew that you are a criminal until now. Na tsane ka Aliyu, wallahi ba zan yafe maka ba, idan kashe ni zaku yi kada ku mata lokaci wajan zaryar da hakan kawai ku aiwatar da abinda ku ke da niyar yi".


Shiru kawai Aliyu ya yi ba tare da ya ce da ita ƙala ba.





********
*KANO*

"Wallahi Gimbiya ba zamu rabu da ita haka ba, dole mu koya mata hankali har ita ta kai ta saka mu wanki muyi". Cewar Gimbiya Saratu.


Shiru kawai Gimbiya Talatu ta yi ta ce. "Ni dai ina ganin kamar mu rabu da wannan yarinyar, dan gaskiya idan muka ce zamu biye mata mune zamu cigaba da jin kunya sannan mu cigaba da shan wahala, yarinyar tamkar mai aljanu duk abinda muke yi mata gaba ɗaya yana tashi a banza ne. Ni dai gaskiya na zubar da makamai na".



Tashi tsaye Samira ta yi ta ce. "Wallahi ba zamu zubda makaman mu ba, kenen mu barta taci banza?, sai na ganar da ita cewa ruwa ba sa'an kwando ba ne, idan ta san wata ba ta san wata ba".


Suna cikin haka suka ji an banƙo ƙofar part ɗin su. Da sauri gaba ɗaya suka miƙe tsaye.


Sooraj da Zahra suka gani a tsaye a yayin da hannun Sooraj ke riƙe da ballet.


Dubansu ya yi ya ce. "Idan kin san kin taɓa sa Mami na aiki ki matso nan wajan kafin na ƙaraso da kaina".


Nan take cikin kowanensu ya ɗuri ruwa, kallon juna suka yi cikin tashin hankali. Da sauri gaba ɗaya suka ja da baya.


Saurin shan gabansa Zahra ta yi sannan ta saki murmushi ta ce. "Kai baka san wasa ba, babu abinda suka yi wa Mami kaji, kawai dai na faɗi hakan ne saboda na kare kaina, ka tafi kawai".


Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Wato raina min hankali ki ke so kiyi ko?, za ki gane kuranki". Ya faɗa yana mai damƙe hannun Zahra sannan ya fitar da ita daga cikin wajan.


Suna fita gaba ɗaya suka shiga sauke ajiyan zuciya. Yayin da suka yi mamakin yadda Zahra ta rufa musu asiri.



Sooraj bai nufi ko ina da Zahra ba sai part ɗin sa. Wani irin daddaɗar ƙamshi ne ya bugi hancin ta. "Wow!". Zahra ta furta ganin yadda part ɗin Sooraj ya yi maƙurar haɗuwa, gaba ɗaya ko ina a tsaftace gaba ɗaya abubuwan da ke ciki Royals ne.


Wurgar da ita ya yi ta faɗi a ƙasa. Miƙe wa tsaye Zahra ta yi ta ce. "Malam ya dai?, mena yi maka, ka kiyaye ni fa, ka san dai ni ba sa'ar ka bace ba, ka san ni ɗin ƴar ina ce?, to ni ɗin ƴar gidan yari ce, kuma wallahi kayi min wani shirme, zan danne ka nayi maka tsinannen duka".


Ta faɗa a tsorace dan ita kanta ta san ba zata iya ba, domin tana matuƙar tsoron Sooraj sai dai bata taɓa nuna masa hakan.



Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Wato ni za ki yi wa tsinannen duka ba?" .ya faɗa yana mai ɗaukar ballet ɗin sa.


Girgiza kai Zahra ta yi ta ce tare da ja da baya ta ce. "Lahaula!, ni asuwa kare da gudun layya, aba yahya Sooraj kana ƙamshi muna binka da umrah, afuwa ɗan sarki mai jiran gado, ka san ba zamu yi hakan da kai ba".



Sooraj bai san sanda murmushi ya suɓuce masa ba. Da sauri ya haɗe ransa sannan ya dube ta ya ce. "Dama ina son kiyi min wani ɗan ƙaramin taimako ne".



Kallonsa Zahra ta yi cike da mamaki ta ce. "Taimako kuma daga wajen nawa?".


Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Ke dalla bana son shirme, shadda nake son na siya kuma an tura min hotunan su, to bana son naje na zaɓi ishirinka ne saboda ban san yadda yake ba, genzna nake so. Kuma bana gane yanayin su, dan ni ban cika siya ba gaskiya, shi ne za ki zaɓar min genzna ba ishirinka ba, na san ku talakawa za ku gane bambancin sosai. Saboda ina son naje wani guri mai mahimmanci ne".



Girgiza kai Zahra ta yi. "Lallai ma wannan Sooraj ɗin, wato talakawa ko, za ka gane kuranka, harda cewa wai wani guri zai je ina ga ma wajan budurwa zai je". Ta faɗa cikin ranta sannan daga bisani ta ce. "Kai yanzu kana namiji baka san yadin ishirinka ba da na genzna, an dai ji kunya, to shi ke nen nuna min hotunan shaddodin".



Ɗaukar system ɗin sa Sooraj ya yi yana mai nuna mata shaddodin.


Duba wa Zahra ta fara yi ɗaya bayan ɗaya. Take idanuwanta ya sauka a kan yadin ishirinka murmushin ta saki sannan ta ce. "Yauwa ga genzna nan gata blue sai sheƙi take za ka yi kyau a ciki sosai".


Kallonta Sooraj ya yi ya ce. "Kin tabbata dai ba ishirinka ba ne ba ko?".


Kallonsa Zahra ta yi ta ce. "Zan yi maka ƙarya ne, gashi nan kana gani genzna ce fa".


"Tom shi ke nen naji". Ya faɗa tare da tura hoton yadin izuwa ga toilor ɗin sa sannan ya ce ya nemo masa irin wannan yadin.


Sosai mamaki ya kama toilor ganin Yarima guda zai saka ishirinka.


Kamar yadda Sooraj ya faɗa haka toilor ɗin sa ya sa aka nemo irinsa sannan ya ɗinka masa a ranar.


Zahra kuwa tashi ta yi ta bar masa part ɗin sa tana mai dariya. Yayin da ta ƙosa ta ga yarima cikin ishirinka ta yadda za ta tsokane shi.



***********
"Safira zan yi miki bayani daga baya, koda na gaya miki gaskiya ba za ki fahimta ba". Ya faɗa yana mai barin wajan.



*************
"Tun jiya fa nake kiran number Safira baya shiga, gaskiya ina cikin damuwa, ina tunanin wani abu na shirin faruwa da ƴata". Cewar Mom.


Kallonta Grandpa ya yi ya ce. "Babu abin da zai faru da Safira sai alkhairy, kada ki damu zamu je office ɗin ƴan sanda tunda shima Aliyu ɗan sanda ne zai taimaka mana wajan neman inda Safira take, in sha Allahu ma tana cikin ƙoshin lafiya". Da tunanin Safira gaba ɗaya suka kwanta.





*****************
*Sooraj pov*.
Da sassafe ya shirya tsaff cikin ishirinkan sa ba tare da ya san cewa ba genzna Zahra ta zaɓar masa ba.

Fesa turare ya yi tare da kallon kansa cikin madubi. Sannan ya taje summar kansa.


Bayan ya kammala ya ɗauki maƙullin motarsa ya fita. Tun daga takunsa har izuwa suturar jikinsa abun kallo ne. Gaba ɗaya ƴan aiki tare da fadawa suka bisa da kallo ganin karo na farko Yarima ya saka yadi, kuma yadin ma na ishirinka.


Ganin suna binsa da kallo ya sa shi ya yi tunanin cewa ko genznar sace ta yi musu kyau.


Shiga cikin mota ya yi tare da tada mota sannan ya bar harabar gidan.


Tun yana kan hanyar tafiyar sa Sooraj yake ta tantama a kan kayan da ya sa. Amma hakan bai sa ya chanza ƙudirin sa na zuwa inda yake son zuwa ba.


Wata zuciyar ce ta ce masa ya tsaya da tafiya ya gwada fita. Hakan ya yi, parking ya yi sannan ya fito daga cikin motan.


Nan take ya fara jin jama'a na cewa "Dama Yarima yana saka ishirinka?".


Nan take ransa ya yi mugun ɓaci. "Kenen dai wannan banzar yarinyar ishirinka ta je ta zaɓar min ba genzna ba, lallai yau saina koya mata hankali". Ya faɗa yana mai shiga cikin mota sannan ya tada motan ya juya ya koma gida.



Da mugun gudu yake jan motan a kan titi har ya isa izuwa fada. Ko parking bai yi ba sosai ya fito ya nufi cikin gida.



Chan ya hango Zahra zaune kan kujera ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. Daga nesa ta hango Sooraj, da sauri ta miƙe tsaye, ganin yadda yadin yake ƙyalle ido sai maiƙo yake ya sa ta nufar in da yake sannan ta saka hannu ta taɓa ishirinkan.


Nan take ta bushe da dariya. Tana mai faɗin. "Daga nesa kamar genzna, saina matso na ga shadda ce, da na taɓa naji shegen ne, ashe ishirinka maraya ne". Ta ƙarashe maganar tana mai kwashe wa da wata dariyar.


Baƙin ciki da takaici ne suka bi suka cunkushe cikin zuciyar Sooraj. Kallonta Sooraj ya yi ya ce. "Kenen kina sane ki ka zaɓar min yadin ishirinka a maimakon genzna?".


Sosa ƙeya Zahra ta yi ta ce. "Kaine fa kace mu talakawa ne dama muke iya gane ishirinka kuma kace genzna ka ke so, kuma ni duk na duba genzna babu wacce ta fi kyau sai wannan ishirinkan, shi ya sa na zaɓar maka ita, kai baka ga yadda kayi kyau a cikin wannan yadin ba, yadda ka san wani basarake".



Baƙin ciki ya ana Sooraj ya furta komai, illa girgiza kai da ya yi sannan ya aura sama domin chanzo wani kayan.



Taɓe baki Zahra ta yi ta ce. "Yaran masu kuɗin nan basu san komai ba, uhmm ai ishirinka maraya duniya ne. Na san zuwa zai yi ya saka wani kayan, ai wallahi ba zan bari ya fita daga gidan nan ba, duk kayan da zai je ya saka saina kushe su gaba ɗaya".



Ɓangaren Sooraj kuwa, shiga ɗakin sa ya yi ya cire yadin ishirinkan ya watsar da su gefe. Sannan ya saka ƙananun kaya t-shirt da trouser white colour tare da facing cap sannan ya fito daga cikin ɗakin.


Kai tsaye downstairs ya nufa.


Zahra na hango shi ta miƙe tsaye tana mai hangame baki ta ce. "To wannan kuma wane irin shiga ce kamar ɗan gudun hijira, ka wani ɗamɓara hula sai kace ɗan vigilante. Ko kyau ma baka yi ba, yadda ka san kamar wani ɗan almajiri". Ta faɗa tana mai bushe wa da dariya.


Baƙin ciki Sooraj yaji ya cika zuciyarsa. Koma ya yi cikin ɗakinsa. Haka yana ji yana gani, ba yacce ya iya sai illa ya ɗauki jallabiya ya zumbula".



Fitowa ya yi inda Zahra take domin yaji ko zata sake kushe kayan.


Sai ya ji ta ce. "Yauwa ko kaifa, yanzu ka fito a musulmi, amma ka wani saka matsantsun kaya sai kace wanda zai je ya burge mata".




LIKE, COMMENTS AND SHARE FISABILILLAHI 🙏🌹🌺💗


ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
(ZINARIYAR JAJIRTATTU)


[11/30, 12:58] null: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g




https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
(We stand together)
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 4️⃣9️⃣▶️5️⃣0️⃣
*___________________________________________*
Girgiza kai Sooraj ya yi tare da zama kan Three seater yana mai fuskantar Zahra ya ce.


"Me ya sa bakya jin tsoro na Zahra?".

Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Hakan me zan dinga jin tsoron ka kaida ba maye ba, aini babu wanda nake tsoro sai Ubangiji na".

Shiru Sooraj ya yi ya ce. "Kin san ina zanje ne kika zaɓar min Ishirinka a maimakon genzna?".


Taɓe baki Zahra ta yi ta ce. "Ina za ka je kuwa in banda wajan ƴan matan ka, dan yadda na ga ranka ya yi mugun ɓacin nan nasan cewa akwai wata a ƙasa. Koma dai mene ne, ni ban ana ka zuwa wajanta ba zaka iya tashi ka tafi".


Girgiza kai Sooraj ya yi sannan ya ce. "Samm ni bana da ƴan mata balle budurwa, zanje wajan mahaifiyata ne".


Jin maganar sa ya sa Zahra shiga cikin ruɗani. Dubansa ta yi ta ce. "Wace mahaifiyar kuma bayan Mami?".


Amsa ya bata da cewa. "Ƙwarai Mami ita ce asalin mahaifiyata, kuma ita ma waccan tamkar mahaifiyata na ɗauke ta, yanzu haka na san tana asibiti tana jira na".


Shiru Zahra ta yi ta ce. "To ita bata ɗa ko ƴa ne?".


Murmushi Sooraj ya yi ya ce. "Zomu je chan zan baki amsa".


Ya faɗa yana mai miƙe wa tsaye tare da fice wa daga gidan. Babu gardama ta bisa a baya.


Motar da ta ga ya shiga ta shiga, a sa'inda ya tada mota tare da fita da su daga cikin masarautar, kai tsaye asibitin da Mrs Laila take suka nufa.






************
Umar kuwa hawanni ƙalilan ne ya ɗauke shi ya isa Jigawa kai tsaye gidan su ya nufa, bai gama parking ba ya fito daga cikin mota tare da shiga cikin babban parlour.


Nan ya tarar da mahaifin shi zaune kan kujera yana shan juice.


Furzar da iska mai zafi Umar ya yi waje sannan ya dubi mahaifin na shi ya ce. "Abba".


Sai a lokacin Gov. Musa ya lura da zuwan Umar wajan. Saurin miƙe wa tsaye ya yi sannan ya ce. "Son yaushe ka shigo?, ina su Khairiya suke?".



"Abba ban taɓa tunanin zaka iya aikata abinda aka faɗa min saboda kuɗi ba". Umar ya faɗa a yayin da idanuwansa suka yi ja tamkar an zuba garwashi.



Rass! Gaban Gov. Musa ya faɗi. Cikin ransa ya ce. "Kodai Umar ya gano munanan hayyukana ne?".

Kallon Umar ya yi ya ce masa. "Umar ban fahimci inda ka dosa ba, me kake nufi da hakan?, ka fahimtar da ni".



Girgiza kai Umar ya yi ya ce. "Really?, wato baka san me nake nufi ba, wai tukun nama shin kai mahaifi na ne ko maƙiyi na?, me ya sa za ka sa a sace Amrah?, wato kenen aikin ka shi ne safaran mata ko. Karka manta ni jami'i ne mai gaskiya, kuma duk wanda yake yin laifi burina shi ne a hukunta shi, koda kuwa ƙanne na ne balle kuma kai. Ba zan yi duba da cewa ko kai mahaifi na ba ne, dole na miƙa ka domin a hukunta ka".


Koma wa gov. Musa ya yi kan kujerar da ya tashi tare da zama yana mai fuskantar Umar ya ce . "Wato harma wani zai zo ya faɗa maka mummunar magana a kaina kuma ka yarda?, banyi tunanin hakan daga gare ka ba, kai ɗin ɗana ne mafi soyuwa s gare ni, ni ne nan na ɗora ka a matsayin da ka ke a halin yanzu".



"A'a, samm ba kai ba ne ba, jajircewa ta da kuma ƙwazo na ne ya kaini wannan matsayin ba kai ba, ka faɗa min gaskiya shin kana aikata abinda ake tuhumar ka da shi?". Cewar Umar.



Shiru Gov. Musa ya yi na ɗan wasu lokaci kana daga bisani ya ce. "Kenen dai baka yarda da ni ba?, well shi ke nen, tunda yanzu babu yarda tsakanin mahaifi da ɗa me ya rage, kawai ka zo ka saka min handcuf ka kaini kotu a yanke min hukunci. Ba aka ka ke so kaji na ce ba. So ka ke na faɗi abinda banyi ba na ce nayi".



Girgiza kai Umar ya yi sannan ya ce. "Shi ke nan Abba, bama sai ka faɗa min ba, ni da kaina zan gano. Kuma ka sani cewa muddin da gaske ne abinda aka faɗa a kanka ba zan bari ka tsira ba, domin saina sa an yanke maka hukuncin da zaka gwammace baka haife ni ba, dole a bi wa mtane haƙƙin su domin suma mutane ne kamar kowa, kuma suma suna da madu sonsu bawai babu. Kuma ka sani cewa muddin wani abu ya sami Amrah, ba zan rabu da kai ba". Ya ƙarashe maganar tare da fice wa daga cikin parlourn.



Murmushin mugunta Gov. Musa ya yi ya ce. "Umar kenen, ba zaka taɓa samu wata hujja a kaina ba".




*********************
"Safira ina son ki bani haɗin kai, bana son kiyi min gardama, maza yanzu ki biyo ni". Aliyu ya faɗa yana mai kallon Safira.



Banzan kallo Safira ta watsa masa sannan ta ce. "Idan kai ka isa da ni to ka sa na bika"


Ajiyan zuciya Aliyu ya sauke ya ce. "Okay tom idan baki je ta lallami ba za ki je ta dole". Ya faɗa tare da jan hannunta.


Wafce hannunta daga nasa Safira ke shirin yi amman akan ya cutura. Nan take ta fashe da kuka tana mai dukan bayansa tare da cizon hannunsa, amma hakan bai sa ya sake ta ba. Jefa ta ya yi a cikin mota sannan ya ɗaure ta a jikin mota kana ya tada mota ya bar wajan.






*****************

Parking Sooraj ya yi tare da fitowa daga cikin mota. Nan ita ma Zahra ta fito daga cikin motan. Yayin da ta fara bin asibitin da kallo. "Kamar na taɓa zama a asibitin nan". Zahra ta faɗa cikin ranta.


Zaro idanuwa waje Zahra ta yi sakamakon riƙe mata hannu da Sooraj ya yi. Nan take ta ji gabanta ya tsananta faɗuwa.


Murmushi Sooraj ya saki kana suka shiga daga ciki. Nan likitocin asibitin suka shiga kwasar gaisuwa.


Kai tsaye inda ɗakin Mrs Laila yake suka je. Tare da shiga ciki.



Nan take Zahra ta haɗa ido da Mrs Laila. Take gabanta ya ƙara faduwa ƙarasa wa ciki ta yi tare da bin Mrs Laila da kallo.

Gaishe ta Zahra ta yi ta amsa yayin da suka shiga kallon juna.


Zahra kuwa tunani take a ina ta taɓa ganin matar nan. Sai a wannan lokaci ta tuna cewa tabbas a wannan asibitin ta taɓa ganin ta.


Kallon Zahra Sooraj ya yi ganin yadda ta nutsu ya sa shi sakin murmushi sannan ya ce. "Zahra kenen, to wannan ita ce mahaifiyar tawa da nake baki labari".


Shiru Zahra ta yi sannan daga baya ta ce. "Ina asali ƴarki ko ɗanki yake?".


Ta faɗa tana mai kallon mrs Laila . Murmushi Mrs Laila ta yi ta ce. "Ni ba wai ƴa ɗaya gare ni ba, yara uku ne, amma sai dai na rabu da su saboda na ceci rayuwarsu da tawa. A halin yanzu dai ban san ko suna raye ko sun mutu ba, amma ni yanzu fata na shi ne na gansu ko a karo na biyu ne kafin na bar duniyar nan ".

"Amma shin baki bawa kowa riƙo ba?". Cewar Zahra.

Amsa mrs Laila ta bata da cewa. "Mutane biyu na bawa riko, ɗaya kuma na ajiye ta a daji sakamakon lokacin ƴan sanda suna ta bibiyata, ban samu na tafi da ita ba, amma na saka mata suna Amrah, sannan ɗuk ƴaƴan nawa uku suna matuƙar kama da juna, sai dai kowanne da irin kalar ƙwayar idanuwansa. Amma kinga maƙiya na duk sun sa na rabu da su, duk dan saboda abin duniya ". Ta ƙarashe maganar hawaye na sauka kan ƙuncinta.



Tausayin matar ne ya kama Zahra. Sai a lokacin ita ma ta tuna da cewa bata da uwa. Share wa Mrs Laila hawayenta ta yi sannan ta ce.

"Kinga kamar yadda kika rasa ƴaƴan ki, aka nima bani da uwa, ban sani ba ko ta mutu ko kuma tafiya ta yi ta barni, amma a kullum a jikina sai ina jin cewa wata rana zan ganta. Ina son ki ɗauke ni a matsayin ƴar da ki ka haifa dan Allah".



Murmushi Mrs Laila ta yi ta ce. "Shi ke nen ƴata". Ta faɗa tana mai rungume Zahra jikinta. Lokaci ɗaya zuciyar ta ya buga da ƙarfi.


Kallon su Sooraj ya yi tare da taɓe baki sannan ya ce. "Ni kuma shi ne aka ware ni a gefe ko?, yanzu Mama shi ne kika share ni ko?".


Murmushi Mrs Laila ta yi ta ce. "Aba my son, to kaima tawo nan kaji ɗan Mommy".


Murmushi Sooraj ya yi ya ce. "A'a ba saina zo ba".


Saida suka taɓa hira kafin daga nan suka shirya domin su tafi.


Tashi tsaye Zahra ta yi sannan ta dubi Mrs Laila ta ce. "Tunda yanzu ke mamata ce, zan taimaka miki wajan neman sauran ƴaƴanki saboda nima yanzu ƴan uwa na ne".



Ta faɗa tana mai fice wa daga ɗakin. Kallon Mrs Laila Sooraj ya yi ya ce. "To mu dai zamu tafi, karki damu an kusan sallamar ki daga cikin wannan asibitin, sannan kuma zan cigaba da neman yaranki har sai inda ƙarfi na ya ƙare". Yana kaiwa nan ya fita daga cikin ɗakin.


Nan ya tarar da Zahra a gefen motarsa ta tsaya tana share hawaye".


Mamaki ne ya kama Sooraj ganin

Please Login or Register in order to submit comment