Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 3️⃣1️⃣▶️3️⃣2️⃣
*_________________________________________________*
Ƙaraso wa mai martaba sarki ya yi wajan su kana ya dube su ya ce. "Me ya ke faruwa ne nake jiyo hayaniyar ku?".


Amsa Junaid ya ba shi da cewa. "Mai martaba babu komai".


Kallon mai martaba zahra ta yi kana ta ce. "Mai martaba ƙarya yake da akwai komai, aka ya ce min wai ɓarauniya, ranka shi daɗe ɗan nan naka yana da matsala ya kamata a kai shi asibitin dawanau domin duba ƙwaƙwalwar sa".


Murmushi mai martaba ya yi kana ya ce. "Gaskiya ki ka faɗa ƴar nan dole ne ma na saka a kai shi chan ɗin. Ku shiga daga ciki ko. Kai kuma ka zo ka same ni ni a fada yanzu". Ya faɗa yana mai kallon Junaid kana daga bisani ya bar wajan.


Sallamar mutanen wajan dogarai da fada wa suka yi suka fita daga cikin masarautar".


Bin bayan mai martaba Junaid ya yi yayin da Mami ta yi murmushi kana ta ja hannun Zahra suka shiga cikin fada.


Kai tsaye cikin parlour suka shiga. Yayin da Zahra ta saki baki tana kallon yadda cikin fadan da parlourn ya yi matuƙar tsaruwa.

"Wayyo Allah na, wannan gida aka ko a mafarki ban taɓa ganin irin wannan gida ba".
Zahra ta faɗa cikin ranta.


Suna tsaka da tafiya kawai suka ga an sha gabansu.


Dakata wa suka yi da tafiya kana suka dubi matan da suka tsaya a gaban su. Motsa leɓenta Mami ta yi ta ce. "Saratu, Talatu mene ne kuma?".

Kallon juna waɗan da Mami ta kira Saratu da Talatu suka kana suka kwashe da dariya.


Dungure wa Mami Kai Talatu ta yi kana ta ja dogon tsaki ta ce. "wato har kin samu damar ɗauko ƴar aiki ki kawo cikin fadan nan?, uban waye ya baki izinin yin hakan?".


"Rabu da ita Talatu, ai naji duk abin da ya faru a waje, har ƴar talakawan nan ta samu bakin da za ta iya furta wa ta faɗa wa ɗana Junaid magana, lallai dole na koya miki hankali A'isha. Dama yanzu ɗanki Sooraj baya nan balle ya ƙi barin kowa cikin sukuni a gidan nan, saimun ta galla za wa rayuwar ki. Idan ɗan naki ya dawo daga ƙasar da yaje sai ki faɗa masa. Ke kuma".

Gimbiya Saratu ta faɗa tana mai maida kallonta kan Zahra ta ce. "Ke kuma ƴar talakawa, wato kenen kina tunanin kin zo gidan masu arziki ko za ki iya shoshale kuɗin mu ko, to maza ki fice daga cikin masarautar nan kafin na saka yara mata su zo suyi min waje da ke".


Murmushi Zahra ta yi kana ta fara ƙoƙarin gaya wa Gimbiya Saratu maganar da za ta tsufa tana jimamin shi. Ji ta yi Mami ta riƙe mata hannu tare da girigza mata kai . Nan hawaye ya fara sauka kan ƙuncin Mami ta ce. "A'a Zahra kada ki furta komai ke ɗin ƴar aiki na ce, kada kiyi magana dan Allah".


Wafce hannunta Zahra ta yi kana ta ce. "A kan me ya sa ba zan yi magana ba?, baki ji yadda suke gaya miki maganganu marasa dad'i ba ne. Chabb Gaskiya wannan masarautar tana da buƙatar gyara sosai. Kuma ni nan zan gyara mutanen cikin ta".


Da sauri Mami ta ja hannun Zahra kana ta nufi part ɗin ta da ita.



***********
"Wow Amrah wallahi kinyi kyau sosai. Maza muje ki nuna wa yaya Umar kwalliyar ki". Ramlat ta faɗa tare da jan hannun Amrah wacce ta yi zuru zuru da idanuwa tana kallon su. Kai tsaye parlour suka nufa da ita yayin da suka nufi in da Umar yake wanda ke zaune kan kujera.

Kamar an ce ya ɗago kansa. Ɗaga kansa ya yi tare da ɗora wa kan Amrah. Bai sanda bakinsa ya furta kalmar masha Allah tabarakalla ba.

Ajiye system ɗin da yake yin aiki ya yi kana ya miƙe tsaye ya ce. "Muje yanzu nayi muku siyayya tare gaba ɗaya".

"Laa yau yaya da kanka za ka kai mu shopping, wannan abu kamar a mafarki". Khairiya ta furta suna mai haɗa ido da Ramlat.


Dubansu Umar ya yi ya ce. "Mene ne a ciki dan na kaiku shopping da kaina?, na ga dai ba wani abu ba ne".


Sosa ƙeya Ramlat ta yi ta ce. "A'a yaya ba saika wahalar da kanka ba, mun riga mun faɗa wa yaya Usman ya ce zai kai mu da kansa, kuma sannan koda ma bai kaimu na ga dai akwai jami'ai a gidan nan za su kai mu, amma a ce da kanka ka kaimu ai abun ya yi wani iri".


Kallonsu ya yi kana ya ce. "Ni nayi ra'ayi bawai ku ka sani ba kun fahimta, don haka ni zan kai ku , karku ɗauka wa saboda ku ne kun gane".


Girgiza kai Ramlat da khairat suka yayin da suka girgiza kai suka haɗa baki wajan faɗin. "Mun fahimta".


Dai-dai lokacin Usman ke sauko wa daga kan bene.

Ƙaraso wa in da suke ya yi ya ce. "Muje ko". Cewar Usman.


"A'a Usman kai kayi hayyukan ka, ni zan kai su, saboda bana son wani abu ya same su domin idan wani abu ya same su ba zan ji daɗin hakan ba, ana neman rayukan mu ruwa a jallo. Bayan kariyar Allah muma ya kamata mu kare kanmu. Don haka ni zan kai su kai ka koma kawai".


Girgiza kai Usman ya yi kana ya ce. "Tom yaya nima kuma akwai in da zan je Ramlat ta na ce wai saina kai su shopping. Yanzu kuma tun da ka ce za ka kai su shi ke nen, ni zan tafi in da zanje".

Ya faɗa tareda fita daga cikin parlourn.



Nan ya ci karo da Gov. Musa Muhammad wato Abban su. Gaishe shi Usman ya yi, yayin da Abba ya amsa kana ya shiga ciki.


Nan take idanuwan Gov. Musa Muhammad ya sauka a kan idanuwan Amrah. Nan take gaban shi ya faɗi!, yayin da ya ji kamar an buga masa ƙararrawa a kai. Salati ya saka sannan ya ce. "Who is this fine beb?". Ya tambaya.


Kawar da kai Umar ya yi kana ya ce. "Am sorry to say Sir, but this is none of your business, please mind your self, banzan ji dad'i nayi maka rashin kunya ba. Wannan da ka ke gani rayuwata ce kuma a kanta babu wanda ba zan iya faɗa da shi ba muddin wani ya ce zai yi ƙoƙarin taɓa ta to lallai ya janyo wa kansa bala'in da babu wanda zai iya cetar sa daga ciki".


Ya faɗa tare da jan hannun Amrah kana suka bi ta gefen Abba suka wuce.


Baki sake gaba ɗaya suka bisu da kallo.


Maida kallonsa Gov. Musa Muhammad ya yi kan su Ramlat kana ya ce. "Ita ɗin wace ce?".


Amsa Khairiya ta ba shi da cewa. "Ita ɗin ƴar daji ce yaya ne ya kawo ta ya ce mana a nan za ta dinga zama har sai ya gano in da ainiyin iyayen ta suke. Bayan nan bamu san komai ba".


Girgiza kai Gov. Musa ya yi ya ce. "Shi ke nen kuna iya tafiya". Kamar jira suke ya ce su tafi m nan suka ruga a guje tare da fice wa daga cikin parlourn.


Samun waje Gov. Musa ya yi ya zauna kan kujera tare da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya sannan ya furzar da iska mai zafi tare da sakin murmushi ya ce. "Umar kenen mai zuciyar ƙarfe. Amma fa ba laifi yarinyar nan ba dai kyau ba, ga green eyes masu tafiya da hankali. Tabbas idan nayi safarar wannan ba ƙaramin kuɗaɗe ƴan ƙasar waje za su bayar ba, za su bada fiye da millions ma, ya zama dole na san yadda zan yi na sace ta. The girl is so beautiful and sexy". Haka Gov. Musa ya shiga yin magana shi ɗaya kamar wani zautacce.


Bayan su Umar sun shiga cikin mota ne Umar ya tada mota yayin da Amrah ta zauna a mazaunin gaba. Nan Umar ya tuƙa motar suka bar harabar gidan baki ɗaya.

Kai tsaye hanyar shopping mall suka nufa



**********************
*KAUYEN GUJINGU*

"Malam wallahi abin da ke faruwa da ƴata ya wuce a kaita asibiti sai dai wajan malamai shi ya sa muka zo gare ka. A da chan ba ta yin hakan. Amma kwanan nan kawai sai mu ga tana faɗi ƙasa ita ɗaya ba tare da anyi mata wani abu ba". Daddy ya ƙarashe maganar damuwa ɗauke kan fuskarsa.



"Ƙwarai da gaske Malam, saboda wannan abun da ke damunta ne ya sa muka baro America mu ka zo Nigeria domin neman mafita. Dan Allah ka taimaka mana".
Cewar Mom.


Murmushi dattijon ya yi wanda ke zaune kan wata katifa wanda aka zagaye shi da kara. Yayin da ɗakin gaba ɗaya rubutun Qur'ani ka ke gani tare da magunguna kala-kala na cututtuka da na aljanu.


Kallonsu malamin ya yi kana ya ce. "Shin ku kuka haife ta?".


Nan take gaban Mom da Daddy ya faɗi!, kallon juna suka yi yayin da suka haɗa baki wajan faɗin "Eh mu muka haife ta".


Sauke ajiyan zuciya Malamin ya yi kana ya ce. "kuma kuna da tabbacin cewa ita ɗaya ce ba ta da wasu ƴan uwan wanda basua tare da ita?".


Amsa Daddy ya ba shi da cewa. "Eh babu ita kaɗai kawai muka mallaka a duniyar nan".


Girgiza kai Malamin ya yi kana ya ce. "To ƴar ku ba ta da wani aljanu, samm babu aljanu ko sihiri ko kuma maita a tattare da ita. Wannan abun da ke faruwa da ita ba wai haka kawai ba ne dole dai akwai dalilin faruwar hakan. Amma batun cewa ko aljanu ke damunta, samm ba gaskiya ba ne".


"To Malam idan ba aljanu ba ne mene ne?, Sannan kuma mene ne abin da zamu yi ya daina?". Cewar Grandpa.


Amsa Malamin ya ba shi da cewa. "Babu abin da zamu iya yi ya daina domin da wannan abun haka haife ta, sannan alamu ya nuna cewa wannan ahali naku sun aikata wani babban kuskure a baya wanda a yanzu ba za ku iya gyara wannan kuskuren ba domin kuwa lokaci ya riga ya ƙure. Dole a chan baya kun cutar da wata wanda ba ta ji ba, bata gani ba, sannan kuma kunyi shedar zurr hakan abin da ba ta aikata ba, to ku sani cewa ƴaƴanta su ne za su ɗaukar mata fansar abin da haka aikata mata".



Cikin rashin fahimta gaba ɗaya suka dubi malamin kana suka haɗa baki wajan faɗin. "Bamu fahimci abin da ka ke magana a kai ba".


Murmushi Malamin ya yi kana ya ce. "Baku da wata ƴa a ahalinku ku ka kore ta ba tare da tabbatar bincike da kuma ƙwaƙwarar hujja hakan abin da ba ta aikata ba".


Nan take jikin kowanensu ya yi sanyi.
Ajiyan zuciya Grandpa ya sauke!, kana ya ce. "Babu wacce muka kora sai Laila, kuma ita ma ɗin na kore ta saboda zubar min da mutunci da ta yi a idanun duniya kana kuma ta lalata sunan ahalin mu, ita ce dalilin kasance wa ta kan wheel chair yanzu. Ta chanza sunan ahalin mu daga masu mutunci izuwa marasa mutunci. Ita ce kawai nake tunanin na kore ta na damka ta a hannun ƴan sanda. Sannan har yau har gobe ba zan manta irin cin mutunci da jama'a suka yi mana ba duk ta dalilin ta. Kuma bayan nan ma ta dalilin ta ne jikana yanzu haka yake da cutar mantau. Don haka ba zan taɓa yafe mata ba, koda zan yafe wa kowa a duniyar nan to banda Lailah".


Share hawayen da ke shirin zubo mata Grandma ta yi kana ta ce. "Kuma ita ɗin a halin yanzu ba ta raye ta riga da ta je gidanta na gaskiya, kuma ina fatan tana cikin rahamar Ubangiji".



Sauke ajiyan zuciya Malamin ya yi kana ya ce. "Tabbas kun aikata babban kuskure a rayuwar ku, ya zama dole ku nemi gafarar wannan ƴar taku idan kuwa ba haka ba, rayuwar ku za ta taɓe. Zato zunubi ne koda ya kasance gaskiya. Baku gani ba sannan baku sheda ba ku ka yanke wannan mummunar hukuncin a kanta, idan ma baku samu kun nemi gafarta ba to ku nemi gafarar ƴaƴan ta domin kada fushin Ubangiji ya dauwama a kanku. Ni na gama magana ta za ku iya tafiya".


Ya ƙarashe maganar yana mai kwanciya kan katifar sa.


Kallonsa Mom ta yi ta ce. "Malam batun maganar ƴata fa?". Jin shiru babu amsa ya sa gaba ɗayansu miƙe wa sannan suka fice daga ɗakin Malamin.


Kai tsaye wajan motocin su suka nufa sannan suka shiga ciki yayin da drivers da ke tsaye suka shiga cikin motan tare da tada motocin sannan suka bar harabar wajan. Kai tsaye suka nufo hanyar Dutse. Tun da suka fara tafiya kowanensu ke ta saƙe-saƙe a cikin zuciyarsa yayin da gaba ɗayansu suka kasa samun sukuni.






***********************
Zumbur Safeera ta miƙe tsaye tqreda nuna Aliyu da yatsarta sannan ta fara kokarin magana. Nan wata zuciyar ta ce da ita ta rabi da shi kawai. Waje ta samu ta zauna sannan ta kawar da kai gefe ta ce. "Ina neman wata alfarma".


Murmushi Aliyu ya yi kana ya ce. "To fa, alfarma a waje na kuma, me ya sa sai a waje na?".


Amsa Safeera ta bashi da cewa. "Saboda na ga kafi cancanta na nema a wajan ka ne. Ina da buƙatar sabulu da man shafa wa sannan da kayan sawa. Duka kaya na suna chan America. Ina da wasu ƴan kuɗaɗe a acc ɗina, shi ne na ce idan babu damuwa ka taimaka ka kaini in da ake shopping domin na yi siyayya".



Kallon baki da hankali Aliyu ya bita da shi kana ya ce. "Wato ma ke ɗin nan kin cika ƴar rainin hankali, yanzu-yanzun nan ki ka gama yi min rashin kunya, and you are expectimg me to take you to shoppin mall, hope dai kina lafiya ba wai giyan wake ki ka sha ba".



Turnuƙe fuska Safeera ta yi ta ce. "Tun da na zo fa banyi wanka ba, am irritating myself, I feel so disgusted I can't take it anymore shi ya sa na nemi alfarma, amma idan ka ga ba za ka kaini ba it fine, i know what to do".


Sauke ajiyan zuciya Aliyu ya yi kana ya ce. "Shi ke nen je ki saka hijabi na kaiki".


Murmushin jin daɗi Safeera ta yi kana ta ce. "Amma ba zan iya zuwa haka ba ne, na ga dai akwai sutura a jiki na ga kuma veil na yafa".


Binta Aliyu ya yi da kallo tare da kallon matsatsun kayan da ke jikin ta. Kawar da kai ya yi gefe sannan ya ce. "In dai da wannan kayan za ki bini to babu in da zan je wallahi kinji na faɗa miki".


Taɓe baki Safeera ta yi ta ce. "Shi ke nen bari na ɗauko hijabi. Ta faɗa tareda shiga cikin ɗakin su Zuwaira ta ɗauko maroon hijab ta sanya. Sosai hijabin ya yi mata kyau.


Fitowa ta yi kana ta ce. "Muje ko".

Kallonta Aliyu ya yi cikin zuciyarsa ya furta kalmar. "Masha Allah Alhamdulillah, tabbas su Mom sun zaɓa min mace kyakyawa, gaskiya nayi dace".


Taɓe baki ya yi a fili ya ce. "Ko kyau, abu kamar a hura ta faɗi".


Taɓe baki Safeera ta yi ta ce. "Koma dai mene ne kai ka sani".


Fita suka yi a tare da shiga cikin mota a tare. Tada mota Aliyu ya yi kana suka fice daga cikin gidan yayin da ma'aikatan gidan suka bisu da kallo.



Saida suka yi tafiya mai nisan gaske kafin su isa ga shopping mall ɗin.


Ɓangaren su Amrah kuwa sosai su khairiya ke yi wa Amrah siyayya, kama daga abayoyi atamfa, Arabian gowns, hijabbai da mayafai tare da set na kayan makeup da dai sauransu.



Jan hannun Amrah Umar ya yi kana ya fara zagaya da ita cikin mall ɗin domin ya zaɓo mata wasu abubuwan.



Bayan shigar su Aliyu ne suka nufi ɓangare da za su samu abin da Safeera ke buƙata.



Sakin hannun Amrah Umar ya yi kana ya fara dube-duben wasu abubuwan.



Safeera ganin hankalin Aliyu ya tafi wani wajan ya sa ta yi saurin barin wajan tareda nufar wani part na ciki wajan


Amrah kuwa barin in da Umar yake ta yi tare da nufa ɗayan sashin da ba ta san ko ina ba ne.


Juyawar Umar keda wuya kawai ya ga Amrah ba ta nan.


Waige-waige ya fara yi ya ga dai still bai ganta ba. Hankalin sa ba ƙaramin tashi ya yi ba domin kuwa a tunanin sa waɗan da suke bibiyar rayuwarsa sune suka sace Amrah nan take ya kira jami'ansa.


A ɓangaren Aliyu dai shima haka domin ya yi neman duniya bai ga Safeera ba.


Chan Aliyu ya hango Amrah a tsaye. Mamaki ne a ya kama shi domin duk a tunanin shi Safeera ce. "To ikon Allah wato Safeera harta chanza shiga izuwa pink abaya". Ƙarasa wa in da Amrah yake ya yi kana ya ja hannunta ya ce. "Ke safeera ina ki ka je ki ka sa nake ta neman ki?".

Juyo wa Amrah ta yi. Nan take idanuwan kowannensu ya sauka a juna.


Take gaban Aliyu ya yi mummunar faɗuwa!, sauri sakin hannunta ya yi tare da ja da baya. Baki na rawa ya ce. "Safeera garin ya ya idanuwanki suka chanxa kala?".


Ɓangaren Umar kuwa ganin Safeera ya yi tana ta tsince abubuwan da take so. Murmushi ya yi ba tare da sanin ba Amrah ba ce ba ya ja hannun ta ya ce. "Ke Amrah kin fiye yqwo maza mu tafi.


Mamaki ne karara ya bayyana kan fuskar Safeera. Saurin wafce hannunta Safeera ta yi ta ce. "Hey wane ne kai kuma?, wace ce kuma Amrah?".


Juyo wa Umar ya yi domin kuwa ya yi matuƙar mamki a karo na farko Amrah ta yi magana. Juyawar sa keda wuya idanuwansa ya sauka a na idanuwan Safeera. Gabansa ne ya bada wani irin ƙara tare da wani irin bugu. Da sauri ya saki hannunta yayin da ya nuna ta cikin zallar mamaki ya ce. "Gari ya ya idanuwan ki suka sauya izuwa blue kuma?, dama kin iya magana ne?".







************************
"Wai Mami su wane ne waɗan chan matan ne?, na san a girma za ki girme su amma shi ne suke miki rashin kunya, ni fa idan da abin da nafi tsana bai wuce zagar min uwa da raini ba. Shin ke ƴar aiki ce a gidan nan ne suke yi miki irin wannan cin fuskar?".


Murmushi Mami ta yi kana ta ce. "A'a ni ɗin ba ƴar aiki bace ba, su ɗin kishiyoyi na ne ni kuma ni ce Uwar gidan su".


Zaro idanuwa waje Zahra ta yi ta ce.
"Kuttmelesin chan dumadu, chabb ɗi jamm kenen dama wai kishiyoyin ki ne?, kai Mami, gaskiya kinyi sanyi da yawa, chabb na yarda da kaina. Wayyo ni Zahra, dama ni ce nake zaune da waɗan nan kishiyoyin guda biyu da tuni na saita wa kowanensu zama duk gaba ɗaya na ga ɗuwawunsu rawa yake duk da saina saita musu shi. Gaskiya Mami kinyi sanyi da yawa. Ai kuwa dole ne na gyara wa kowa zama a gidan nan kafin na bar wannan masarautar. Domin samm ba zan juri ire-iren waɗan nan abubuwan ba, me yafi wannan raini. Na ga ma kamar sun raina ki, wata a cikin su mai haƙora kamar na akuya mai gatso ɗin nan Talatu na ji kin ce ɗazu ko, ita harda wani dungure miki kai tsabagen ta raina ki".


Murmushi Mami ta yi kana ta ce. "To ya zanyi Zahra?, ni sam bana san tashin hankali da hayaniya, shi ya sa kawai nake zaune da su a hakan banason rigima. Shiru- ba tsoro ba ne gudun magana ne, a lokacin da ɗana Sooraj yana nan babu wanda ya isa ya yi min abin da suke yanzu. Domin kuwa kowa tsoronsa yake a gidan nan. In dai baya nan ne suke mim waɗan nan abubuwa, idan kuma ya dawo kowa shan jinin jikinsa yake. Ni kuma ban taɓa buɗar baki na faɗa wa mai martaba ko ɗana Sooraj ba. Saboda bana son tashin hankali".



Girgiza kai Zahra ta yi kana ta ce. "Tabbas ni ce zan kawo sauyi cikin wannan masarautar saina tabbatar da na saita musu zama kafin na bar gidan nan, ba zan iya zuba ido na ga ire-iren waɗan nan abubuwan na faruwa ba, ya zama dole na koya musu hankali".



Babu zato suka ji an banko ƙofar cikin ɗakin. A zabure gaba ɗaya suka juya tareds sauke idanuwansu a kan matan da ke tsaye bakin ƙofa babu abin da suke ta faman yi sai tauna chewgum yayin da suka ɗora hannuwansu kan ƙugu. Sanye kansu yake da gashin ƙari wanda ya sauko musu har gadon baya yayinda ko ina na jikin su ke sanye da azurfa masu kyau da sheƙi. Kallo ɗaya za ka musu ka tabbatar da cewa su ma ƴaƴan wannan masarauta ne.


Ƙaraso wa ciki mata ukun suka yi sannan suka buga tsaki. Daya daga cikin su ce ta ce. "Ke Mami me ya sa har yanzu baki je kin wanke min panties ɗina ba?".


Kallon Mami Zahra ta yi kana ta ce. "Mami su waye kuma waɗan nan almajiran?".


Kallonta Mami ta yi kana ta ce. "Su ɗin ba almajirai ba ne, ƴaƴan kishiyoyi na ne, Samira, Yusra, da Fasma".


A matuƙar fusa ce ƙaramar cikin su ta dubi Zahra ta ce. "Su wane ne almajiran, nan ɗin gidan ubanki ne. Tsaya ma tukun nan ke ɗin wace ce daga wane duniyar ki ka zo nan". Cewar Fasma.


Yusra ce ta dubi Fasma ta ce. "Dalla ƙyale ta Fasma zamu ji da ita daga baya. Yanzu wajan wannan banzar matar muka zo, ta zo ta wanke mana kayan mu, domin ni yau bana sha'awar saka kaya a cikin washing machine da hannu nake so a wanke mu".


Idan ran Zahra ya kai dubu to ya ɓaci. Cikin ɓacin rai ta ce. "Kuna da hankali kuwa?, ku san da cewa wannan matar ba sa'ar iyayen ku mata ba ce, amma shi ne ku ke cewa ta zo ta wanke muku panties da kaya, lallai kamm banga ta zama ba a gidan nan domin daga yanzu ya kamata na soma aiki na".


Rai a ɓace su ukun suka tunkari in da Zahra take kana suka ce. "Eh mun aike ta ɗin wace ce ke da za ki dakatar da mu?".


Nuna su gaba ɗaya Zahra ta yi kana ta ce. "Zai iya kasance wa kun daɗe kuna yi mata abin da ranku ya gada ma, like mothers like daughters ko, to tun da na riga da sanya ƙafafu na cikin wannan masarautar komai ya zo ƙarshe domin kuwa ba zan bar koda iyayen ku mata su ƙara ci mata mutunci ba balle ku ƙananun ƙwari".


Nan take Samira ta saka ƙafarta wanda ke sanye da takalmi mai tsini ta taka ƙafar Mami da shi. Nan take Mami ta saki wani irin azababbiyar ƙara!.



Nan take ran Zahra ya ɓaci yayin da ta kai hannu tare da fizge gashin dokin da ke kan Samira sannan ta kama ƙwaƙwidon kan Samira kana ta kwashe ta da lafiyayyun maruka har guda biyu. Nan take su Yusra suka ja da baya.



Shafa kan Samira Zahra ta yi ta ce. "Wai dama ba gashin ku ba ne, ashe gashin doki ne, ji gashi kamar ammatar ɗan iska". Ta faɗa tana mai kwashe wa da dariya sannan ta maida kallon ta kan Mami ta ce. "Mami kada ki damu za ki riɓanya hakan abinda ta yi miki kiyi mata times 2".


Girgiza kai Mami ta yi kana ta ce. "Ki rabu da ita Zahra, bana son matsala".


"A'a Mami ba zai yu ba, me ya sa koda yaushe waɗan da suke da shiru-shiru su haka fi raina wa ne?, ke sa'ar su ce da za su wai ki wani wanke musu kaya da panties, idan ba rashin tarbiya ba wa ye zai faɗi hakan?". Cewar Zahra.



Kallonta Mami ta yi ta ce. "Zahra umarni nake baki ba shawara ba maza ki sake ta".


Jin hakan ya sa Zahra sakin gashin Samira tare da shinshina hannunta. Nan take ta ji wani mugun wari ya bugi hancin ta.


"Ya subha'anallahi!". Zahra ta furta kana ta ce. "Wannan kai ne ko kashin akuya?, ji wani wari da

Please Login or Register in order to submit comment