Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KhkWs8eY42GETnGLk2JC9G


*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Thre siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐.

WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝♀️Jajirtattu)


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
(We stand together)
🤝🤝🤝

*Dedicated this page to you my one and only friends Mom muwadda and Pink darling Ina sonku sosai Allah ya bar mu tare🥰😍🥰*

*Maman ihsan da sauran members na Jajirtattu ina mika gaisuwata gare ku. Na gode da haɗin kai da kuma gudunmawar da ku ka bani Allah ya ƙara haɗa kawunan mu sannan ya bamu zaman lafiya mai ɗore wa🙏*

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*

Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! Aminci ya tabbata ga shugaban fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.
Da sahabbansa da matayensa baki ɗaya.


Yau ma kamar kullum gani tafe da sabon littafi na mai suna.
*KUNDIN CINIKAYYA* wanda yake ɗauke da ilimantar wa,wa'azantar wa, kayatar wa, da kuma nishadantar wa*

Daji
Magarƙama da kuma
Birni.
Three siblings from different part of the world 🌎



*Ban yarda a chanza min littafi ta ko wace tsiga ba Koh kuma s sayar min da littafi na tare da sani na bah Koh kuma s ɗora min littafi a internet bah tareda izins bah toh idan kuwa mutum ya kuskure ya chanza min littafi, yaje na bar shi wa Allah*. *Kuma ba zan yafe masa bah*

Ban yi wannan littafin dan cin zarafin wani koh wata bah, nayi shi ne domin mutanen al'umma su amfana da darusukan dake cikin ta. Idan wannan littafin yayi dai-dai da rayuwar ka toh arashi nee


*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 1️⃣▶️2️⃣*

*________________________* *JIGAWA STATE*
*DUTSE 🪨*
*FEDERAL HIGH COURT*
*DUTSE*

*SHEKARA TA DUBU BIYU DA BIYAR *


__fitowa ta yi daga cikin Motar 'yan sanda yayin da hannayenta ke sanye da handcuf. Nan ƴan sanda suka kalle ta tare da yi mata nuni da ta yi gaba. Tafiya ta fara yi cikin kasala da fauwala wa Allah lamuranta. Ta ke mutanen wajan suka fara tofa albarkacin bakinsu a kanta yayin da suke Allah wadai da halinta. Kare ta police ɗin wajan suka shiga yi gudun kar wani a cikin jama'ar wajan ya yi ƙoƙarin illatata.

shigar da ita cikin kotu suka yi mai matukar girman gaske.

Cikin kotun ya kasance mai matuƙar faɗi gaske benci da wajan tsayawar shaida kake gani tare da kujeru, tebura, kofofi, lectern sai ƙaramin tebur don wakilin kotu kusa da benci na alkali an rufe da magatakarda kotu, sai kuma katako shinge mai raba shari'a daga gallery.



gefe guda jama'a ne da ƴan sanda yayin da lauyoyi suke tsaye tare da alkali.

Kallon su alkalin ya yi tare da basu damar zama. Zama kowanen su ya yi yayin da kotun ta yi shiru tamkar babu wani ɗan adam dake cikin ta.

Mai da kallon sa alkali ya yi kan wanda hake tuhuma yayin da ya bata umarnin da ta fito gaban kotu domin jin hukuncin da haka yanke.

Jiki a sanyaye ta miƙe tsaye tare da nufar gaban kotu tana mai fuskantar jama'an dake cikin wajan.

Magana Alkalin ya fara yi kamar haka, "A bisa hujjoji da muka yi la'akari da su, bisa dogaro da abubuwan da haka bayyana tare da ƙwaƙwarar bincike cewar Mrs Laila Abdullahi tana amfani da kamfanin ta da sunan tana taimakon talakawa bayan kuma safaran yara ta ke tare da aika mata ƙasashen waje domin yin karuwanci suna samar mata da kuɗaɗe sannan tare da miyagun ƙwayoyi da kayan maye wanda duk mun sani cewa doka ta haramta yin hakan".

" Don haka wannan kotun mai albarka ta yanke nan da sati ɗaya za'a mata hukuncin kisa ta hanyar rataya. Yana kaiwa nan. Kwamitin alkali ne suka miƙe tsaye tare faɗin. "Court".

Jin hakan ya sa kowa fita daga cikin kotun yayin da kowa ke farin ciki tare da murnan hukuncin da kotu ta yanke mata.

Fitowa Mrs Laila Abdullahi ta yi hawaye na bin kan ƙuncinta. Gefe guda kuma mutane ne a tsatsaye suna mata tofin Allah tsine.

Shigar da ita jami'ai suka yi cikin motan ƴan sanda yayin da haka nufi can prison da ita. Bayan wasu kwanaki warders suka fito da ita jikinta sanye da kayan magarƙama tare da nufar inda za'a rataye ta. Kuka sosai ta ke tamkar ranta zai fita yayin da ta ke ji ina ma ta samu koda mutum ɗaya wanda zai yarda cewa bata aikata miyagun laifukan da haka tuhume ta dasu bah.

Sai da haka kaita har inda za'a rataye ta. Nan ta ke mai zartarwa ya fito da igiya yayin da haka ɗaure igiyar a sama. Sannan haka ɗauki abin rufe fuska haka rufe mata fuska da baki. Sannan haka saka kanta saitin igiyar tana ihuu tana kururuwa.


A firgice ta farka daga mummunar mafarkin da ta ke, yayin da zufa suka fara ƙeto mata ta ko wane sashi na jikinta yayin da damuwa da tashin hankali suka bi suka tunkushe guri guda a zuciyarta na halin da ta ke ciki na rashin mai taimakon ta. Nan da nan zuciyarta ya shiga bugawa da ƙarfi-ƙarfi.

Dafe cikinta ta yi wanda ya kumburo sosai alamun cewa tana da juna biyu. Sosai taji gaba ɗaya jikinta sunyi mata nauyi yayin da ta kasa motsa koda ɗan yatsarta saboda tsananin azaba da raɗaɗi na ciwon dake tattare da ita.

Jin alamun motsin mutum daga bayanta ya sa ta sauriin waigawa. Nan ta haɗa idanu da gandirebas ɗin da ke tsaye ƙe ƙam a kanta. Ta ke zuciyarta ta ƙara faɗuwa a karo na biyu!. Don ta tabbatar cewa sun zo ne domin tafiya da ita kotu. Kallon su ta yi hawaye na bin ƙuncinta ta ce.

"Dan Allah kuyi min wata alfarma, ina son kafin ku kaini kotu a yanke min hukunci ɗaya daga cikin ku ya hara min waya na kira ƴan uwana dan Allah".

Kallon juna gandirebas ɗin suka yi yayinda ɗaya daga cikin su ya kalle ta ya ce. "Kotu bata bamu damar yin hakan bah. dan haka kada ki ce zaki yi wani yinƙuri a nan wajan idan ba haka bah zamu samu bindiga mu harbe miki kai dan haka obey the law".

Jiki a sanyaye ta miƙe. Jikinta sanye da tufafin ƴan magarƙama. Yayin da ta miƙa hannunta gaba ɗaya a cikin su ya sanya mata handcuf a hannun sannan suka fice daga cikin wajan. Bangare guda kuma sauran matan cikin Magarƙamar suka bita da kallo.

Cikin police van wato motar ƴan sanda ta shiga yayin da suka nufi kotu da ita. Tun da suka fara tafiya ta ke ta istigifari tare da salati har suka isa kotun.

Parking police suka yi. Duk idanuwan jama'a a kansu yayin da suke jiran fitowar Mrs Laila Abdullahi.

Fitowa ta yi daga cikin motar. Ba zato taji saukar dutse a kanta. Dafe kanta ta yi cikin raɗaɗi hawaye na zarya bisa fuskarta. Nan da nan mutane suka fara jifar ta da duwatsu tare da fara Allah wadai da halinta. Ganin hakan ya sa jami'ai suka shiga kare ta. Har haka shigar da ita cikin kotun.



Ƴan jarida da jama'a ne gaba ɗaya suka ƙaraɗe gaban kotun high court yayin da koh ina ƴan sanda da sojoji kake gani hannunsu riƙe da bindigogi don rike mutane a kan madafun iko.

*"Muna buƙatar adalci!muna buƙatar adalci!. Kalmomin da jama'ar wajan ke ta nanata wa kenen.

Daff da wani dattijo wasu ƴan jarida suka nufa, tare da seta mike saitin bakinsa sannan suka ce. "Bawan Allah mene ne sunanka?". Amsa dattijon ya basu da cewa.


"Sunana Namadi". Tambayar sa ƴan jaridan suka yi a karo na biyu da cewa. "Bisa wane laifi ne ku ke tuhumar wannan matar dashi, kuma me yasa kuke jifanta?".

Amsa dattijon ya fara bata kamar haka.

"Muna tuhumar ta da ƙwamushe yaran mu tana safarar su. Dukkanmu muna buƙatar wannan kotu ta yi mana adalci hakan zalunta da yaudarar mu da ta yi. Ta ɓata rayukan ƴaƴan mu mata, ta kashe mana yaran mu yayin da ta ke saka wasu yaranmu suna mata safaran miyagun ƙwayoyi. Muna tunanin ce mun samu walihiya mai share kuka da baƙin cikin mu. ashe muguwa ce shigo-shigo bah zurfi ta yi mana.Ta yi mana alƙawarin cewar zata horar da ƴaƴanmu kuma za ta ba su aiki a kamfaninta ashe ta riƙe ƴaƴan mu ne domin ta kai su wasu kasashen don samar mata da kuɗaɗe ta hanyar karuwanci.Dan haka muna son a bi mana hakkin mu a kan abin da haka aikata mana". Ya faɗa yana mai fashe wa da kuka. Sannan ya ƙara da cewa. "Ta cuce mu ta zalunce mu, mu ɗora mata yardar mu ta hanyar bata amanar ƴaƴan mu. Indai har kotu bata yanke mata hukunci bah toh tabbas sai mum kashe ta".


Mai da kallon ta ɗaya daga cikin ƴan jaridar ta yi kan camera sannan ta ce. "Jama'a fatan kunji abin da wannan dattijon ya faɗa kan cewar suna zargin Mrs Laila Abdullahi da aikata laifin safaran yara da safaran miyagun ƙwayoyi. Neman gaskiya da amfanin jama'a, Bayyana zalunci, yi rahoto da gaskiya da daidaito. Kare yancin jama'a da mutuncin dan Adam duk a wannan kotu mai alfarma muke samunsa. Dan haka mu jira hukunci".


*Shigar su cikin kotu keda wuya Alkali shigo shi ma ciki Ma'aikacin ma'aikacin kotu yana sanar da lokacin da alkali ya bada umarnin da kowa ya zauna.

Umarni Alkali ya bada da Mrs Abdullahi Muhammad ta fito gaban kotu. Fitowa ta yi har inda masu laifi ke tsayuwa. Yayin da police suka tsaya daga bayanta.



Buɗe littafi Alkali ya yi tare yin rubuce rubucen shi a ciki tare da bawa mgatakadda damar ya tashi.

Miƙe wa magatakadda ya yi tsaye sannan ya ce. "Assalamu alaikum Barka da safiya fatan kowa yana cikin ƙoshin lafiya". Ɗaukar takarda da alƙali ya miƙa mai ya yi sannan ya ce. "A wannan rana ta Litinin ɗaya ga watan february, a wannan kotun tamu mai dumbin albarka zamu ci gaba da sauraran ƙaran da wasu suka kawo bisa zargin aikata wannan laifi. Kuma a wannan rana za'a yi zama na ƙarshe na sauraron shari'ar Mrs Laila Abdullahi wanda hake tuhuma da safarar yara da salwantar dasu".

"Shin koh lawyer Mrs Lailah Abdullahi yana nan? da kuma lauya da ke kare wanda suke tuhumar Mrs Lailah Abdullahi yana nan? Idan gaba ɗaya kuna kusa muna bukatar ku Miƙe tsaye. Miƙe wa lawyer dake kare Mrs Lailah Abdullahi ya yi tare da bashi amsa da cewa, "Eh ina nan". Yayin da ɗaya tsagin shima ya miƙe tsaye.


Magana magatakadda ya fara yi kamar haka.
"Bayan hujjoji da haka gabatar a gaban kotu cikin zama da ya gabata na ɗaya na biyu dana uku kotu zata bayyana matsayinta hakan wannan shari'ar". Yana kaiwa nan ya zauna.


Kallon lauyoyin dake kare kowane ɓari yayi sannan ya ce. "Shin akwai wata hujja da zaku gabatar koh A'a?".

Amsa wa suka yi da "babu".

Ɗaukar littafin dake kan tebur ɗinsa alƙali ya yi sannan ya ce. "Bisa la'akari da hujjoji da suka bayyana a gaban kotu waɗan da hujjojin duk suna nuna cewa abin da hake tuhuman Mrs Lailah Abdullahi, laifin ta ruga ta aikata kuma ba bu wata da lauyarta ya bayar ƙwaƙwara da zata gamsar da kotu cewa bah ita ta aikata wannan laifin bah. Don haka wannan kotun mai alfarma ta zata yanke mata hukunci kamar haka".

"Bisa dogaro da duba da haka yi da halin yana yin da ki ke ciki na juna biyu. Wannan kotun ta bada umarnin cewa ba za'a rataye ta ba har sai ta haifa abin ke cikinta, sannan wannan kotu mai alfarma ta bada umarnin cewa Mrs Lailah Abdullahi ta samu kulawa daga likitoci da kuma cikin magarƙama tare da bata abinci masu kyau har lokacin da za ta haifi abin da ke cikin ta, sannan nan da shekaru biyar masu zuwa za'a rataye ta. Wannan shi ne".
Kwamitin alkali ne suka tashi tare da cewa. "COURT".

Miƙe wa jama'a suka yi. Yayin da babu wanda yaji daɗin hukuncin da Alkali ya yanke sunso nan ta ke zai bada order da a rataye ta sai kuma suka ji hakasarin hakan sakamakon cikin dake cikinta.

Fita jama'a suka yi daga cikin kotun, yayin da jami'ai suka fito da Mrs Lailah Abdullahi tare da nufar inda motar police ke a fa ke.

Bah zato ta ji saukar mari kan fuskarta. Saurin dafa ƙuncinta Mrs Lailah Abdullahi ta yi sannan ta kalli matar hawaye ni bin kan ƙuncin ta.

"Allah ya tsine miki albarka, muna fuka maciya amanar ƙasa, dole ki gurbi abin da kika shuka". Cewar wata dattijuwa.

Ganin suna tunkaran inda Mrs Lailah Abdullahi ta ke ya sa jami'ai suka fara kare ta yayin da suka shigar da ita cikin mota. Nan ta ke suka ji saukar talkalma kan jikinsu yayin da suka fara bubbuga jikin motar da Mrs Lailah Abdullahi ke ciki. Ruff da ciki Mrs Lailah ta yi tare da fara rusa kuka. Kukan da ta ke yi ba saboda cin mutuncin da jama'a suka yi mata bah. Tana kuka ne bisa ga nadama da kuma takaicin abin da ya sa ta yarda da mutum. Haƙika yardar da ta baiwa mutane shi ne ya yi silar tarwatse war rayuwarta, shi ne mafarin kuma ƙarshe na rugujewar rayuwarta, tabbas ta aikata babbar dana sani a rayuwarta.

Tun da suka fara tafiya ba abin da ta ke sai kuka har suka isa harabar magarƙamar da ita.

Parking daya daga cikin police ɗin ya yi kafin daga bisani gaba daya suka fito daga cikin motar yayin da warders mata suka nufo motar tare da buɗe wa suka fito da Mrs Lailah Abdullahi waje tare da shigar da ita cikin magarƙamar mata wato ɓangaren mata sannan suka shigar da ita cikin kurkuku tare da ƙulle ƙofar wajan.

Guri Mrs Lailah Abdullahi ta samu ta zauna yayin da ta shiga yin tunanin koh a wane hali ƴan uwa ta suke ciki a yanzu. Motsi tajiyo daga bayanta. Saurin waigawa ta yi tareda zuba idanuwanta hakan matar da ba za ta wuce shekaru arba'in zuwa sama bah a duniya.

Murmushi matar dake gefenta ta yi sannan ta ce. "Kada ki ji tsoro sunana Hajiya Binta nima kamar ke haka lokacin da haka kawo ni magarƙama na dinga kuka bah tare da aika ta wani laifi bah sa'anan ina ji ina gani na kasa aiwatar da komai saboda fito da gaskiya lamari. Kuma abin takaicin ma kina da juna biyu. Karki damu zan kula da ke tamkar ƴar uwa har ki sauka lafiya kinji?".

Murmushi wanda ya fi kuka ciwo Mrs Lailah Abdullahi ta yi sannan ta ce. "Nagode sosai ƴar uwa". Ta faɗa tare da zaro wani babban littafi a cikin jakarda haka kama ta dashi. Sannan ta miƙa ma hajiya Binta littafin ta ce. "A gaba ɗaya magarƙamar nan ke kaɗai ce wacce na gani naji hankalina ya kwanta da ita, dan haka Ina son ki hadana min wannan littafin saboda yardar da miki domin na san duk abin da ya yi ƙarshe akwai mafarin faruwar sa, ina son ki hadana min shi".

Miƙa hannun Hajiya Binta ta yi tare da karɓar littafin wanda ya ke da matukar girman gaske. Juya littafin Hajiya Binta ta yi a hannunta sannan ta ce. "Wannan littafin fah mene ne a ciki?".

Murmushi Mrs Lailah Abdullahi ta yi sannan ta bata amsa da cewa. "Tarihi na da mafarin lamarin duk abin da ya shafi rayuwata da kuma abubuwa da dama wanda baki ba zai gama faɗar su bah duk sune a ciki. Ina son ki hadana min shi koh bayan raina idan ina da rabon haihuwa a duniya ki bawa ɗan da na haifa wannan littafin domin ya san wane ne shi, idan ma mace ce ki bata domin sanin wace ce mahafiyarta da kuma ita kanta".


"Kai maza ku taso kuyi aiki". Cewar wata warder a cikin magarƙamar.

Miƙe wa suka yi yayin da Hajiya Binta ta ɓoye littafin a ƙarƙashin pillow ɗinta. Tana saka wa suka fice daga cikin ɗakin da suke.

*BAYAN WATANNI UKU*
kwance ta ke yayin da ta ke jin bayan ta nayi mata ciwo ga wata iriyar azababbiyar ciwon mara da ta bi ta addabe ta. Yayin da cikin wanda ya yi tartsotso a gaba yake ta faman motsi.


Nan ta ke ta saki wata iriyar razananniyar ƙara!. A firgice matan dake cikin magarƙamar suka nufi inda ta ke yayin da suka shiga bata taimakon gaggawa. ta ke suka haɗa rufi da tsumma tare da zagaye wajan. Nan da nan mutane suka cunkushe guri ɗaya.

Cikin tsananin azaba na naƙuda take nishi tare da furzar da iska mai zafi yayin da numfashinta ya ke ƙoƙarin sarƙewa.

Ganin hakan ya sa Hajiya binta ta fara danna mata cikin tana ihuu yayin da saura matan suka shiga yi mata addu'ar sauka lafiya.


Ganin tana ƙoƙarin rufe idanuwanta ya sa hajiya binta ta yayyafa mata ruwa tare da tattaɓa fuskarta. Gani ta yi gaba ɗaya ƙarfin ta ya ƙare yayin da ɗan dake cikin ya kasa fitowa.

Ba zato suka ji kukan jaririya ta fito. Nan ta ke farin ciki ya lulluɓe fuskokin su yayin da suka shiga yi wa Allah godiya. Ɗaukar jaririyar Hajiya Binta ta yi sannan ta ce. "Masha Allah, ubangiji ya albarkaci rayuwarki". Ta faɗa tare da miƙa wa ɗaya daga cikin matan magarkama suka sanya jaririyar a cikin tsumma tare da rufe ta. Sannan hajiya Binta ta ɗauki placentar yarinyar wanda haka yanke ta haƙa rami a can bayan magarƙamar ta bunne.



Mai da kallon ta kan Mrs Lailah Hajiya Binta ta yi. Nan ta ke Lailah ta kuma fashe wa da wani irin azababbiyar ƙara mai matuƙar razanarwa.

Cikin kiɗima da firgici kowanennsu ya mai da kallon sa kanta. Yayin da suka ga Lailah ta ci-gaba da naƙuɗa.

Zaro idanuwa waje Hajiya Binta ta yi cikin farin ciki ta ce. "Kenen ba guda ɗaya bace bah akwai wata a ciki. Allah mun gode maka da ka albarkaci wannan baiwar taka da ƴaƴa waɗan da sune za su zamo gata da kuma abun alfaharin ta.

Ganin ɗan dake cikin ta kasa yin nishin da zai fito ya sa ta shiga cikin tunani.

Wani dabara ne ya faɗo mata. Miƙe wa ta yi yayin da sauran mata da warders suka bita da kallo.

Wani babban bokiti ta ɗauka mai matuƙar faɗi da girma yayin da ta cika she bokitin tsaff da ruwa. Tare da ƙoƙarin jan bokitin ta nufi inda Laila ta ke. Ganin ta kasa ya sa warders suka taimaka mata ta ɗauki ruwan yayin da suka kai har gaban lailah.

Ajiye wa suka yi yayin da suka cinciɓe ta tare da saka ta cikin ruwan.

Nan ta ci gaba da naƙuɗa yayin da jariri ya ƙi fitowa. Sai da ta ɗau hawanni biyu tana abi ɗaya bah tare da anji labari mai daɗi bah.

Zama hajiya Binta ta yi tare da girgiza kanta ta ce. "Ba za ta iya haihuwa da kanta bah saboda bata samu kulawar da ta ke buƙata bah, wannan aikin ba mune zamu yi bah dole likitoci ne zasu yi kuma wannan bah maganar kawo likitoci magarƙama bane tana buƙatar a kaita asibiti yanzu nan kafin lokaci ya ƙure.

Ɗaya daga cikin warders ɗin ne ta kalli Hajiya Binta ta ce. "Asibiti kuma? Ta ya ya zamu fita da ita cikin magarƙama bayan ita ɗin babbar mai laifi ce kuma kotu bata bamu damar aiwatar da hakan bah.kafin hakan ta faru dole sai da sa hannun kotu tukun nan".

Cikin ɓacin rai Hajiya Binta ta kalleta ta ce. "Wato ta mutu a gaban idanuwan mu kenen koh? kotun banza kotun wofi na bi kotu da gudu ba wando. Idan ta rasa rayuwarta ba tare da haifar abin da ke cikin ta bah shin kun san da cewa babban laifi ne? Saboda kuna ji kuna gani tana buƙatar agaji ku ka ƙi agaza mata sannan kuma wallahi idan ta mutu sai kin fuskanci mummunar uƙuba tare da hukunci dan haka kuje a haɗa jami'ai a tafi da ita asibiti. Maza-maza yanzun nan".

Cikin ƙanƙanin lokaci warders suka tara jami'ai yayin da haka ɗauki Mrs Lailah Abdullahi haka shigar da ita cikin mota. Riƙe hannun Hajiya Binta Lailah ta yi sannan ta ce. "Ga amanar ƴata na baki ki kularmin da ita tamkar ƴar cikin ki sannan kada ki taɓa faɗa mata cewar ke ɗin bah mahafiyarta bace, har sai ta kai munzalin sanin hakan. ina son ki nemi ta gano inda mahaifinta ta ke. Tana kaiwa nan ta saki hannunta alamun ta suma.

Jikin Hajiya Binta ne ya yi sanyi yayin da ta kalli jaririyar dake hannunta cikin tausayawa.

Tada mota jami'ai suka yi yayin da suka fita da ita daga cikin magarƙamar tare da nufa da ita babban asibiti.

Tun da suka shiga cikin asibitin mutane ke binsu da kallo yayin da suke ganin kamar Mrs Lailah ce a cikin motar. Nan da nan labari ya zagaye gari cewar Mrs Lailah Abdullahi tana cikin international hospital zata haihu yayin da ƴan jarida suka cika wajan domin ɗaukar rahoto da bayanai.

Bangare guda kuma Jami'ai sun zagaye asibitin hannunsu riƙe da bindigogi.

Fitowa Nurse's suka yi da gadon ɗaukar mara lafiya sannan suka ɗora ta a kai tare

Please Login or Register in order to submit comment