Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"A'a ni samm ba haka ba, lafiya ta ƙalau babu abin da ya same ni. Ni kaina mamaki nake sannan na shiga cikin ruɗu ta yadda lokaci ɗaya na tsinci kaina da ciwon jiki. Amma na san zuwa wani lokaci zai daina, ina ga saboda abincin da na dinga ɗurƙa wa ciki na ne ya sa jiki na ya mutu".




_______________________
Faɗuwa ƙasa Amrah ta yi yayin da ta saki wata ƙara sannan ta buga tsalle ɗaya ta dira kan ɗaya daga cikin su ukun. Nan take ta fara buga mai hannu a kai tare da gantsara masa cizo a kunne.


Nan take ya saki ihuu. Sauka ta yi kansa tare da yin kan sauran. Ganin ta nufo in da suka ya sa suka saka gudu domin tsere wa. Ganin suna ƙoƙarin tserewa ya sa Amrah ita ma ta bi su da gudu.


Miƙe wa tsaye Umar ya yi a ɗingishe sannan ya fara ƙwallah kiran sunan Amrah. Amma ina Amrah ta yi nisan da ba za ta jiyo kira ba.









*😨😨😨😨😨😨😨*
*MANAGE PAGE 📄 📃 PLEASE 🥺*


ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B 💞💞💞
(ZINARIYAR JAJIRTATTU)

Follow the 🌺🌎A'ISHA M.B🌹 HAUSA NOVELS 📚 WORLD 🌎 📚💗💖 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g


*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part of the world)*🪐🌎🪐.
Daji 🌲
Magarƙama🏢 da kuma
Birni🏙️

WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝♀️Jajirtattu)


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
(We stand together)
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 4️⃣1️⃣▶️4️⃣2️⃣
*___________________________________________*
Da mugun gudu suka nufi wajan motocin su domin tsere wa daga wajan Amrah, kafin suyi aune suka ji an chafko rigar su tare da ɗaga su sama sannan ta fara ajijiya da su kamar dabba.


Ganin hakan ya sa mutane zaro ido waje a sa'inda suke cewa Amrah ba murum bace.

Da sauri Umar da su Ramlat suka isa wajan tare da fara ƙoƙarin dakatar da Amrah, amma ina samm hakan ya cutura.


Chakk Amrah ta dakatar da abinda take yi sakamakon tsawar da Umar ya daƙa mata. Sauke su ta yi yayin da mutanen Gov. Musa suka shiga mota tare da barin wajan.


Zuwa daff da ita Umar ya yi ya ce. "Mene ne hakan?, me ya sa ki ke so ki zubar mana da mutunci?, ko dan kinga ina sonki ne?. Ba dai wajan ƴan uwanki ki ka ce na maida ki ba, shi ke nen zan maida ki". Ya faɗa yana mai juya wa sannan ya bar wajan.


Ƙasa da kai Amrah ta yi. Jiki a muce su Khairiya suka riƙe hannunta tare da ƙoƙarin tafiya.


Cire hannunta Amrah ta yi daga na su sannan ta girgiza kanta ta ce. "Ku tafi kawai ku barni a nan".


Kallonta Usman ya yi ya ce. "Aba Amrah kiyi haƙuri, kada ki damu da maganar yaya Umar wasa yake miki".


Girgiza kai Amrah ta yi s karo na biyu tana mai faɗin. "Ai ni abin da ya faɗa shi nake so, shi ne ya maida ni wajan ƴan uwa na, ni samm ban san yadda zan iya irin taku ba, kuma idan na cigaba da zama da ku zan dinga jawo muku abun kunya ne gwara ku neman mu ƴan uwana".



"Tom shi ke nen karki damu za mu neme su kinji". Cewar Umar. Jin hakan ya sa ta bi su suka tafi. Shiga motan gaba ɗaya suka yi, a sa'inda Umar kuwa ko ɗaga kai bai yi ya kalli Amrah ba saboda har izuwa wannan lokacin ranshi a ɓace yake.


Tada motocin nasu suka yi yayin da suka wuce babban gidan Umar wanda ke a layin Darmanawa.


______________________
Girgiza kai Aliyu ya yi jin furucinta ya sa shi kwashe wa da dariya sannan ya ce. "Ikon Allah, wato kina da ci kenen irin kune masu ci amma ba'a ƙiba".


Miƙe wa tsaye Zahra ta yi rai a ɓace ta ce. "Malam karfa ka raina mim hankali, ban san shashanci, ka iya bakin ka banƙi yanzu na kutuntuma maka ashariya ba, India ka san wannan ne abota to zamu yanke ta gaskiya".


Murmushi Aliyu ya yi ya ce. "Ayi haƙuri hajiya babba, na tuba. Ni kin ma tuna min har yanzu da ban san sunanki ba, ina son ki faɗa min mene sunanki?".


Kallon rainin wayo Zahra ta yi masa sannan ta ce. "Kana nufin baka san sunana ba kuma kace za ka yi abota da ni?, to ni sunana suna da yawa, ba lallai ka iya riƙe su ba".


Murmushi kawai Aliyu ya yi ya ce. "Ina jinki faɗa min su, ni kuma na miki alƙawari duk zan riƙe".

Murmushin mugunta Zahra ta yi sannan ta ce. Sunana oho".


Girgiza kai Aliyu ya yi ya ce. "Allah ya shirye ki, dan Allah ki faɗa min".


Taɓe baki Zahra ta yi. "Toh me ya sa ka damu lallai saika san sunana?, kodai akwai abin da ka ke ƙulla min ne?, haka aka ce ka karɓo sunana ka kaiwa boka ya yi maka magani?".


Dariya Aliyu ya kwashe da shi sannan ya ce. "Aba dai Allah ma ya tsare, ina ni ina wajan boka, rufa min asiri".


Jinjina kai Zahra ta yi sannan ta ce. "Tom shi ke nen ni dai sunana Fatima kai kuma fa mene naka sunan?".


"Wow! nice name". Aliyu ya faɗa sannan ya ce. "Ni dai sunana Aliyu".


"Masha Allah". Zahra ta furta. Karɓar kuɗin da ta ba shi ta yi sannan ta fara siyayyar abin da ya kawo ta. Saida ta gama tass sannan Aliyu ya ɗauke ta ya kaita har gaban masarauta.


Fitowa Zahra ta yi daga cikin motan yayin da Aliyu ya bita da kallo. "Zahra". Ya faɗa cikin maƙe murya.


Hangame baki Zahra ta yi ta ce. "Mene haka kuma sai kace kana kiran budurwar ka, idan za ka fa Zahra ka faɗa da muryar ka ta garda wa ba saika maƙe ta ba. Don haka ina jin ka me ya faru?".


Murmushi kawai Aliyu ya yi sannan ya ce. "Babu komai, dama ina mamaki ne da na ganki a nan masarautar, dama ke ƴar sarauta ce?".


Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "A'a ko ɗaya, ni ɗin ƴar aiki ce". Ta faɗa tana mai shige wa ciki.


Ganin ta shiga ciki ne ya sa shi sakin murmushin mugunta kana ya ce. "My mission will soon be complete, ya zama dole na yi taka tsantsan idan ba haka ba za ta iya gano shiri na".


Ya faɗa yana mai tada motan sannan ya bar harabar masarautar.


Ɓangaren Zahra kuwa ta shiga cikin masarautar ta ci karo da Sooraj a tsaye ya rungume hannuwansa a ƙriji.


Ƙasa da kai Zahra ta yi cikin ranta ta ce. "Na ga alamun wannan mutumin da gaske yake na cewa dole sai ya azabtar da ni, ni kuma wallahi dai-dai nake da kai".


"Ke!". Zahra ta ji ya faɗa a matuƙar tsawa ce. Ko kallonsa ba ta yi ba ta ci gaba da tafiya.


Ganin ta share shi ne ya sa ran shi ya ƙara ɓaci ya ce. "Ke ba da ke nake ba?".

Sai a lokacin Zahra ta tsaya tare da juya wa tana mai fuskantar shi. Binsa ta yi da kallo sannan ta ce. "Kayi haƙuri ranka shi daɗe, ni sunana ba ke ba, naji kana ta ke, ni kuma ba da ke aka yanka min ragon suna ba, Zahra ne sunana".


Girgiza kai Yairma Sooraj ya yi rai a ɓace ya ce. "Kenen bani da hankali kenen ko?, kenen ba a kan dai-dai nake ba?".


Kawar da kai Zahra ta yi ta ce. "Na sani, abu a duhu a baƙar leda".


Furzar da iska mai zafi ya yi waje sannan ya ce. "Wane ne wanda ya kawo ki a mota yanzu?, wane ɗan wahalan ne?".


Riƙe aɓar ta Zahra ta yi ta ce. "Toh!, ikon Allah mutum da duniyarsa, kenen ban isa a kawo ni gida a mota ba ne ko me?, to saurayi na ne kuma shi zan aura sai kuma me ya faru?".


Girgiza kai Sooraj ya yi sannan ya ce. "Wato kenen mai saurayi ko?, wane ɗan wahalan ne ma ya ce yana sonki, ya rasa wacce zai so zai ballagaza mara kamun kai irin ki".


Murmushin takaici Zahra ta yi sannan ya ce. "A hakan ya ganni ya ce yana so, sannan kuma kada ka manta so babu ruwanshi da ballagazanci ko rashin kamun kai ko kuma kuɗi ko iko, ka gane Yarima, sannan kuma koma dai mene ne ina ruwan ka?, meya shafe ka da hakan?, wallahi karka kaini bango na faɗa maka maganar da za ka kwana ka tashi ba za ka manta ba, kada ka sa na faɗa maka maganar da za ta sanya ka rashin lafiya harta kai ga an kaila ƙasar waje operation ɗin zuciya, na gaya maka domin kuwa idan na gaya maka magana sai zuciyar ka ta fito ta bugi ƙasa sannan ta koma".


Jinjina kai Sooraj ta yi sannan ta ce. "Kin san kuwa da wa ki ke magana?, ni Sooraj ki ke gaya wa aka?. Shi ke nen kije ki girka duk abin da ki ka ci yanzu nan kuma za ki yi".


Harara Zahra ta galla masa ba tare da ya sani ba sannan ta ce. "Naji".


Ta faɗa tana mai shige wa ciki. Girgiza kai Sooraj ya yi yana mai ayyana irin ƙuntata wa Zahra da zai yi, zai nuna mata banbamcin ɗan sarauta da kuma ƴar aiki". Haka ya cigaba da ayyana maganganu sa kana daga bisani ya shiga ciki.




Zahra kuwa ba ta zarce ko ina ba sai cikin kitchen ajiye kayayyakin ta yi kan table sannan ta yi jugum tare da bin kayan da kallo.


"Zahra kin taro wa kanki match, yanzu ta ina za ki iya girka abin da ki ka ci". Su Samrah suka faɗa suna mai kwashe wa da dariya.

Binsu da kallo Zahra ta yi rai ɓace ta ce. "Zan yi kuma za ku gani, an gaya muku ban iya girki ba ne, to zan yi ma wanda yafi wannan dad'i, maza ku ɓace min daga gani".
Ta ƙarashe maganar tana mai maida kallonta kan ingredients ɗin.


Fice wa su Samrah suka yi suka barta a kitchen ɗin.


Zama Zahra ta yi tana mai ɗora hannayenta guda biyu a kai sannan ta ce. "Na shiga uku!, yanzu ta ina zan fara?, ni da ko girki ban taɓa yi ba ta ina zan iya wannan abincin, gashi ba'a taɓa girki a gaba na ba balle na iya, yanzu ya zan yi. Kuma idan ban yi ba hukunci wannan Sooraj ɗin zai yanke min, ya kamata nayi abu. To me ma zan yi?". Ta tambayi kanta.


Ɗaukar babban tukunya ta yi tare da ɗora wa kan gas cooker. Dafe kanta ta yi tana mai nazarin mene ne abu na gaba da za ta yi. Nan ta ɗauki man gyaɗa tare da zuba wa cikin tukunyar sannan ta zuba kayan haɗi da wanda ta san mene ne da wanda ba ta san mene ne ba duk ta zuba tare da zuba yaji mai matuƙar yawan gaske, sannan ta yanka albasa ta zuba a ciki tare da kwara wa man gyaɗa ɗin ruwa. Take tukunyar ta kama ci da wuta mai matuƙar ƙarfi.


Zaro idanuwa waje Zahra ta yi tana mai ƙoƙarin rage gas ɗin amma ina wutan ba zai ba ta damar kai hannunta wajan gas cooker domin ta rage ba.


"Yanzu ya zan yi na rage wutan nan?, ko na zuba masa ruwa ne?". Ta tambayi kanta.

Girgiza kai kawai ta yi tare da cewa. "Kawai bara na rage da kai na". Ta faɗa tana mai kai hannunta wajan gas ɗin. Haka ta naji tana gani ta ƙusa hannunta wajan wutan tare da rage gas ɗin. Da mamakin ta kuwa ta ga samm wutan bai yi mata komai ba. Basar wa ta yi kana ta cigaba da yin hayyukan. Ta fara shirye-shiryen kunun aya da coslow saidai duk ba ta iya ba. Gashi kitchen ɗin duk ya yi kaca-kaca ruwan da ta ɗora ya tafasa har ya fara zuba a ƙasa.



Zama ta yi cikin gajiya ta ce. "Gaskiya ba zan iya ba, ina ga guduwa kawai zan yi, shi ne zai fi min sauƙi. Haka kurum za'a bunne ni da raina, chabb ina naga ta zama".


Ta faɗa tana mai waige-waige. Leƙo da kanta ta yi wajen kitchen ɗin ganin ƴan aiki da su Samrah basua nan ya sa ta sakin ajiyan zuciya sannan ta cire takalman ƙafarta ta riƙe su a hannu kana ta fara tafiya cikin sanɗa tare da saurin bin hanyar backyard.


Saida ta tabbatar da ta fita daga ciki sannan hankalinta ya kwanta. Nan ta fara nufar wajan garden domin kada wani ya ganta.


Haka ta cigaba da tafiya da tafiya ba tare da kowa ya lura da ita ba.

Ganin babu kowa a wajan ya sa ta fara gudu saida ta je daff da za ta fita daga garden ɗin taci karo da Sooraj tare da Junaid.


Nan take ta yi saurin jan burki. Ba ta yi aune ba ta ji zufa ya fara ƙeto mata ta kowane sashe na jikinta.



"Ina kuma za ki je?, ko dai ba za ki iya ba ne shi ne ki ka yi tunanin guduwa?". Cewar Sooraj.


Nuna kanta Zahra ta yi ta ce. "Ni!, nayi maka kala da wacce za ta gudu?, ka san kuwa wace ce Zahra?, zahra ba ta taɓa guduwa sai dai a gudan mata, ba guduwa zan yi ba naga baku da albasa ne a kitchen shi ne na fito tsinka". Ta faɗa tare da kawar da kanta gefe sannan zuciyarta ya shiga dukan uku-uku!.


"Junaid dama muna da shukar albasa a masarautar nan?". Cewar Sooraj.


Dariya Junaid ya yo ya ce. "A'a yaya, ina ga ita ce ta shuka shi ne ta zo tsinka. Don mu dai bamu da wani shukan albasa a nan wajan".


Maida kallonsa Sooraj ya yi kanta sannan ya ce. "Kinji dai ko, babu albasa nan gwara ki lallaɓa ki koma ki cigaba da abin da ki ke yi".


Sunkuyar da kai Zahra ta yi sannan ta girgiza kai ta ce. "Shi ke nen".


Ta faɗa tana mai koma wa ciki.


_______________________
"Safira yanzu kin ji dai-dai?". Cewar Mom.


Girgiza kai ta yi ta ce. "Eh Mom naji dai-dai, Mom dan Allah ku barni na koma America, mun kusan fara exam ɗin mu na Law, kuma shi ne exam na tantance wa, ya kamata ku barni na tafi".


Murmushi Mom ta yi sannan ta ce. "Amma na tambaye ki wani abu?".

Girgiza kai Safira ta yi alamun eh.

Kallonta Mom ta yi ta ce. "Me ya sa ki ke son zama lawyer bayan akwai wasu courses ɗin da yawa bayan shi?, sannan so ki ke kiyi ne don kuɗi ko don kare al'ummar da aka zalunta?".


Murmushi Safira ta yi sannan ta miƙe tsaye tare da juya wa mahaifiyartata baya ta ce. "Ina son na zama lawyer ne domin kare haƙƙin al'umma sannan duk wanda aka zalunta nayi ƙoƙarin tsaya masa har saina ga an ƙwatar masa haƙƙin sa, ina son nayi law ne domi bayar da adalci tare da gaskiya, ban taɓa jin ina son yin aikin Law saboda kuɗi ba, ina son ne nayi domin tsaya wa tsayin daka domin kare haƙƙin ɗan adam. Idan tsanani ya kai maƙurar tsananta to adalci ne kaɗai yake iya maganinta. Sannan ina ji a jiki na kamar an taɓa zalunta ta a baya, shi ya sa nake son nayi wannan aikin. Dan Allah Mom karki ce A'a".



Ɗan jimm Mom ta yi sannan ta ce. "yanzu misali na tambaye ki, idan wani talaka ya zo domin ki tsaya masa a shari'a saboda na cuce shi, sai wanda ya cuce shi ɗin ya kawo miki maƙudan kuɗaɗe da kiyi shari'ar ƙarya kan wanda ya nemi taimakon ki idan ba haka ba zai kashe ki. To a wannan lokacin mene ne za ki yi?".



Murmushi Safira ta yi sannan ta ce. "Farko zan amince masa sannan na karɓi kuɗin, a yayin da muka je kotu zan tsaya wa wanda aka cuta naga an ba shi gaskiya sannan kuma shi wancan a yanke masa hukuncin kuma baya sannan a gaban idanuwan shi zan ɗauki ƙuɗaɗen da ya bani sannan na bawa wannan talakan, yayin da shi kuma kotu ta yanke masa hukunci".


Girgiza kai Mom ta yi sannan ta ce. "Kinga kenan maganganun da aka faɗa kan lauyoyi na cewa suna da baki biyu gaskiya ce. Farko kin gaya wa mugun cewa kin amince sannan bayan kinje kotu kuma ki ka faɗi wani abun da ban ba wanda ku ka shirya da shi ba, kinga hakan yana nufin kinci amanarsa kenen. Ke za ki iya gani cewa ta hanya mara kyau hakan iya samar da gaskiya da adalci. Amma asalin hanya ita ce ka bi ta hanya madaidaiciya domin samar da adalci wannan shi ne. Kinga kenen ba za ki iya aikin Law ba".

Saukar da ajiyan zuciya Safira ta yi sannan ta ce. "No Mom, I can do it. Ina da tabbacin cewa zan iya wannan aikin kuma ki zuba ido ki gani. Nan gaba za ki yi alfahari da ni".





________________________
"Wannan wane irin shashanci ne?, ta ya ya za ku ce Amrah ta gagare ku kun kasa kamata?, yanzu kenen duk plans ɗina za su tafi a banza?. To wallahi na baku 24hours ku sace ta, idan kuma ba haka ba zan sa a gama mun da ku". Ya ƙarashe maganar tare da jan tsaki sannan ya kashe wayar.



Wurgar da wayar ya yi sannan ya ce. "I have to make another plan, in ba haka ba, duk wahala na za su tafi a banza".




********
Zama Nurse Nadiya ta yi kan gadon kwanciyar ta sannan ta ce. "Na kasa gane me yake faruwa, me ya sa waɗan can mutane suka sace ni?, me ya sa suke tambaya ta mrs Laila, ko dai Mrs Laila har yanzu tana raye ne?, ya kamata na fara bincike kan wannan lamarin, idan ina son sanin gaskiya dole naje prison ɗin da take domin sanin asalin labari".




*********
"Hajiya Binta ki daina kuka, Zahra fa ba yarinya bace, ba za ta ɓata ba, ita ɗin ma ƴar iskar kanta ce, kin ga za ta iya kare kanta ba tare da taimakon kowa ba".


Share hawayenta Hajiya Binta ta yi tana mak maida kallonta kan Dpo sannan ta ce. "Ai don saboda ba ƴar ka bace shi ya sa ka ke faɗin hakan, akwai kundin littafin da mrs Laila ta bani kafin ta tafi, ta ce idan Zahra ta kai lokacin da ta mallaki hankalin kanta na ba ta wannan littafin. Kuma gashi Zahra ta kai minzalin da zan ba ta wannan littafin gashi kuma an rasa in da ta shiga. Banason wani abu ya faru da ita saboda idan wani abu ya same ta ba zan yafe wa kaina ba". Ta faɗa tare da miƙe wa tsaye ta shige ciki.


Shiru Dpo ya yi a sa'inda gaba ɗaya jikinsa suka yi sanyi.




______________________
Ganin Zahra ta shiga ciki ya sanya Sooraj maida kallonsa kan Junaid sannan ya ce. "Junaid ka sa ido kan wannan yarinyar ni sam ban yarda da ita ba, ina son zan fita naje wani wuri ne".


Girgiza kai Junaid ya yi ya ce. "Tom yaya in sha Allah, amma dai dakarai ne za su kai ka ko?".


Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "A'a ni kaɗai nake son zuwa bana son kowa ya bini".


Ya faɗa yana mai wuce wa wajan parking space, nan take ƴan aiki suka fara kwasar gaisuwa, yayin da dakarai suka nufo in da yake.


Dakatar da su ya yi da hannunsa sannan ya ce. "Kuyi zaman ku bana da buƙatar ku".


Ya faɗa yana mai buɗe mota ƙirar ferari tare da shiga. Nan take ya zura maƙulli sannan ya tada motar yana mai barin harabar masarautar sannan ya fice daga masarautar baki ɗaya.


Bai zarce ko ina ba sai asibiti.


Lokaci ƙalilan ya ɗauke shi ya isa asibiti.


Ganin motar wanda ya yi parking ya sa likitoci suka fara nufar in da yake.


Suna mai gaida shi. Fito wa ya yi daga motan yana mai amsa gaisuwar sannan ya dube su ya ce. "Where is she?".

Nuni ɗaya daga likitocin ya yi masa da cewa tana cikin room.


Nufar wajan ya yi bai tsaya ba har saida ya isa bakin ɗakin sannan ya kai hannunsa kan handle tare da murɗa handle ɗin ƙofan sannan ya ƙusa kai ciki.



Yana shiga ya tarar da ita kan kujerar mara sa lafiya ta yi ruff da ciki sai kuka take.


Nan take idanuwansa suka kaɗa suka yi jajir, zuwa ya yi daff da ita sannan ya zauna kusada ita ya ce. "Me ya sa ki ke kuka eh mrs Laila?".


Ɗago da rinannun idanuwanta Mrs Laila ta yi tare da ɗora wa kan Sooraj. cikin dashashiyar muryar ta tace. "Me ya sa ba zan yi kuka ba Sooraj?, yarana duk na rasa su ban sani ba ko suna raye ko Allah ya amshe kayansa. Na rabu da ƴaƴa na tun kafin su san ciwon kansu, yanzu ban sani ba ko suna raye ko A'a, sannan miji na bai damu ta nemi in da suke ba, ƴan uwana basu neme su ba, ni haka tawa kaddarar take". Ta ƙarashe maganar tare da fashe wa da kuka.


Furzar da iska mai zafi Sooraj ya yi sannan ya ce. "Kada ki damu na dawo Nigeria ne duk saboda na nemo in da suke, kuma naje chan ne domin neman maganin ki. Zan ƙoƙarta wajan ganin kin samu lafiya sannan anbi miki haƙƙin ki da na yaranki".







ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B
(ZINARIYAR JAJIRTATTU)



*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part of the world)*🪐🌎🪐.
Daji 🌲
Magarƙama🏢 da kuma
Birni🏙️

WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝♀️Jajirtattu)


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
(We stand together)
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 4️⃣ 3️⃣➡️4️⃣4️⃣
*___________________________________________*
Sooraj ya faɗa yana mai miƙe wa tsaye. Sannan ya juya da zimmar tafiya.


Saurin riƙe hannunsa Mrs Laila ta yi sannan ta ce. "Na gode sosai Sooraj, ban san da mai zan iya saka maka ba, da a ce ƴaƴana suna nan da na aura maka ɗaya daga cikin su tunda baka da aure".


Murmushi Sooraj ya yi ya ce. "Aba ke kuwa suma ai kamar ƴan uwa na suke, sannan na sha gaya miki cewa ki daina min wannan godiyar kinji. Ni yanzu zan tafi, zan sa likitocin su cigaba da kula da ke, sannan kuma na manta ban faɗa miki ba, akwai wani abun mamaki da ta faru a dawowar nan nawa. Na dawo na ga an shiga wannan ɗakin ajiyar sannan kuma sunanki ne password ɗin wannan ɗakin, amma abin da ya bani mamaki wata ƴar aiki a cikin masarautar mu ta iya gano password ɗin sannan kuma ta buɗe bayan kuma babu wanda ya san wannan password ɗin daga ni sai mahallici na".


Girgiza kai kawau Mrs Laila ta yi ta ce. "Zai iya kasancewa kawai canka ta yi bawai ta sani ba, ko kuma wani ne ya faɗa mata. Yanzu dai ya kamata ka tafi, saboda bana son maƙiyana su san cewa ina raye ".


Girgiza kai Sooraj ya yi sannan ya ce. "Shi ke nen, zan tafi yanzu kamar yadda ki ka buƙata". Ya faɗa yana mai kiran likitoci. Cikin mintuna ƙalilan suka bayyana a wajan. Nan ya faɗa musu cewa su cigaba da kula da ita sannan duk abin da take da buƙata su bata ba tare da sun tambayi umarnin sa ba.


Bayan ya gama yi musu bayani, ya miƙe tsaye tare da barin room ɗin sannan ya nufi wajan parking space. Bai yi aune ba ya ga ya taka ƙafar mutum. Da sauri ya ɗago da idanuwansa tare da ɗora wa kan wanda ya taka.




*******
Ɓangaren su Amrah kuwa, basu zarce ko ina ba sai wani babban gida wanda ke cikin layin darmanawa, fitowa Usman ya yi daga cikin mota sannan ya buɗe gate ɗin domin kuwa babu kowa a cikin wannan gida.


Shiga ciki gaba ɗaya suka yi yayin da Usman ya koma tare da rufe gate ɗin.


Fitowa Amrah ta yi daga cikin mota, kallo ɗaya za ka mata kasan cewa samm

Please Login or Register in order to submit comment