Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

ka kaini gida Please".

Kallonta Aliyu ya yi ya ce. "Karki damu zan nemo mana abinci, yanzu idan na fita za su ganmu kuma su kashe mu".

Cikin rashin fahimtar maganarsa Safira ta dube sa ta ce. "Su waye kuma za su ganmu kuma su kashe mu?".

Amsa Aliyu ya bata da cewa. "Mutanen da suke neman rayuwar mahaifiyar ki da kuma taki rayuwar tare da na ƴan uwanki, sannan duk wanda ya yi nasaran kashe ki ko mahaifiyar ki da ƴan uwanki, za su samu dubbannin kuɗaɗen da ba za su misaltu ba".

"What!". Safira ta faɗa cikin rashin maganarsa ta ce. "I don't understand, me Mom ta yi musu za su kashe ta?, sannan kuma wane ƴan uwa ka ke magana a kai?".

Amsa Aliyu ya bata da cewa. "Bawai ina nufin Mom ba, domin Mom ba ita ce mahaifiyar ki ba".

Rass! Zuciyar Safira ta buga yayin da ta zaro idanuwa waje. Rai a ɓace ta ce. "Kamar ya Mom ba ita ce mahaifiyata ba?, wannan wane irin shirme ka ke faɗa aka?, idan Mom ba ita bace ta haife ni wace ts haife ni to?".

Amsa Aliyu ya bata da cewa. "Mrs Lailah Abdullahi, tana ɗaya daga cikin richest women in the world, ita ɗin Aunty ta ce, kamar uwa take a waje na".

"Hanya ba wani abun ka sha ba kuwa?, ni bani da wata uwa in ba Mom ba, ka daina faɗa min waɗan nan tatsuniyoyin domin ba yarda zanyi ba".

*************
"Gashi yallaɓai Hajiya Binta ce ta ce na baka wannan littafin, ka bawa Zahra shi idan ka ganta".
Cewar warder.

Kallon littafin hannunta DPO ya yi ya ce. "Littafin mene ne kuma wannan?. Shikenen naji labarin cewar Zahra na Kano har yanzu sannan tana masarautar chan, zan je na tabbatar idan tana chan sannan na dawo da ita". Ya faɗa tare da miƙa hannu ya karɓi littafin sannan ya ajiye a gefe.

*******
Sooraj kuwa chan ya hango mai saida ruwa. Parking ya yi tare da sauka sannan ya je ya siyo ruwa guda ɗaya. Saida ya ɗau lokaci Sosai Kana ya dawo cikin motan. Zuwan shi keda wuya ya ga bata cikin motan.

Mamaki ne ya kama Sooraj . "Lallai ma yarinyar nan, yanzu kuma ina ta shiga". Waige-waige ya soma yi, chan idanuwansa ya sauka a kanta. Tsaye take da wasu samari guda uku suna sanye da baƙaken suit. Yayin da Zahra ke surfa musu bala'i ta inda take shiga bata nan take fita ba.

Dafa kansa Sooraj ya yi. "Wayyo Allah, wannan wace iriyar masifa ce, wai ko ina taje saita nuna halin ta".

Ya faɗa yana mai ƙarasa wa inda take. Zuwa wajan keda wuya Zahra ta ganshi. Girgiza kai Zahra ta yi ta ce . "Yauwa masha Allah kazo a dai-dai, zo ka jini da wata masifa, ina zaman-zama na waɗan nan kajin dake sanye cikin wannan abun da suka kira suit suka zo inda nake, na tambaye su me suke so suka ce wai ai zuwa suka yi su sace ni, shi ne na ce idan za su iya su sace ni".

Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Kema in banda abunki ai wasa suke miki".

"A'a wallahi waɗan nan ba wasa suke ba, kana ganinsu yadda ka san wasu ƙasurguman masheƙa, ni kuma dai-dai nake da su". Cewar Zahra wacce ta faɗa hannunta riƙe a ƙugu tana karkaɗa su tare da karka ƙafarta yadda kasan wacce zata yi dambe.

"Shi ke nen to mu tafi ko". Sooraj ya faɗa yana mai kama hannun Zahra.

Nan take maza ukun da ke sanye cikin suit suka kalli juna, nan suka fito da wani abu kamar perfume tare da fesa musu.

Duk abinda ke faruwa a gaban idanuwan Mk.

Nan take jiri ya ɗebe su suka faɗi a ƙasa.

Kwashe su mutanen suka yi tare da saka su a mota.

Ganin hakan ya sa jama'a suka saki ihuu yayin da suka jifar motan kidnappers ɗin da dutsina. Da sauri kidnappers ɗin suka tada mota tare da fara ƙoƙarin barin wajan. Nan jama'a suka dinga binsu a baya har suka ɓace wa ganinsu.

Da sauri Mk ya nufi inda motar Sooraj yake domin ganin idan akwai inhaler a motar domin ya san perfume da aka fesa musu zai iya affecting ɗin shi, domin kuwa ya san Sooraj yana da asma. Nan ya fara dube-dube a motar. Cikin sa'a kuwa ya ga inhaler ɗin saman kujera. Da sauri ya ɗauka sannan ya nufi motarsa da sauri tare da tada wa ya bi bayansu Zahra.

Gudu suke falfalawa kamar za su tashi sama.

Buɗe idanuwanta Zahra ta yi ta gansu cikin mota. Ihuuu ta buga yayin da ta fara dukan wanda ke bayan seat ɗin kusa da Sooraj.

Nan take ɗaya a cikin su ya kwaɗe ta da mari. Jin marin Zahra ta yi har cikin ƙwaƙwalwarta. Nan take ta fusa ta yayin da ta kama kunnen wanda ke kusa da ita tare da fara gantsara masa cizo.

Ihuuu saurayin ya buga yayin da ya fara ƙoƙarin ƙwace kanshi amma hakan ya cutura. Kuma hakan bai sa sun dakatar da tuƙin ba.

Nan saurayin ya taki sa'a ta sake shi. Ganin ta saki kunnensa ya sa shi dafa kunnensa wanda ya yi jajir. Gurnani ya fara yi. Nan ya shaƙe mata wuya tare da ƙoƙarin yi mata allura kan jijiyar wuyanta.

Duk abinda ke faruwa Sooraj bai sani ba, domin har izuwa wannan lokaci bai farfaɗo ba.

Babu zato suka fara jiyo Sooraj yana nishi sama-sama alamun asma ɗinsa ya tashi.

Ganin hakan ya sa Zahra ta sa dukannin ƙarfinta ta ture wannan saurayin.

Hankali tashe ta ɗaga Sooraj tare da girgiza shi. "Yahya Sooraj me ya sa me ka?, dan Allah kada ka mutu ka barni".

Cikin fitar hayyaci Sooraj ya dube ta ya ce. "Asma ɗina ya tashi kuma inhaler ɗina yana cikin motata".

Zaro idanuwa waje Zahra ta yi nan take tausayin Sooraj ya kama ta. Kallon kidnappers ɗin ta yi ta ce . "Dan Allah ku mayar da mu, idan ba haka ba zai mutu, ko baku ga yana cikin mawuyacin hali ba ne".

Ko kallon Zahra basu yi ba saima ƙara wa motar gudu da suka yi.

Rungume Sooraj Zahra ta yi tare da ɗaukar ruwan da ya siyo ta bashi yasha.

Chan cikin dajin suka isa. Tsayar da motar suka yi tare da fitowa. Sannan suka fito da Zahra da Sooraj kana suka ɗaɗɗaure su jikin bishiya sannan suka nufi inda su Amrah suke domin fito da su.

Dai-dai lokacin shima Mk ya ƙaraso wajan. Da sauri ya nufi inda su Sooraj suke sannan ya bashi inhaler ya shaƙa.

Dubansa Zahra ta yi ta ce. "Dan Allah ka kunce mu".

"Shiiiiii!". Mk ya yi mata alama da hannu da ta yi shiru.

A hankali Mk ya fara kunce su yana mai waige-waige.

******************
"Wai ni kamm Yahya Usman ina su Amrah da Yahya Umar suke?, har yanzu shiru basu dawo gida ba, ni fa ina tsoron kada wani abu na cutarwa ya cutar ds su.
Cewar Khairiya.

Kallonta Usman wanda ke zaune kan 3seater ya yi ya ce. "Babu abinda zai same su, insha Allah suna cikin ƙoshin lafiya, ni na matsu su dawo mu koma jigawa".

Kallon su Ramlat ta yi ta ce. Ni fa ina ganin kamar akwai abinda ke tafiya ba dai-dai ba, tabbas akwai wani abu da Yahya ke ɓoye mana, kuma baya son mu sani".

Kallonta Usman ya yi ya ce. "Mene ne to Yahya zai ɓoye mana?".

Amsa Ramlat ta bashi da cewa. "Jiya na kira Abbah, munyi waya to a lokaci da muka gama wayar ya manta bai kashe wayar ba, naji yana yin magana da wani bansani ba ko mace ce ko namiji, naji yana cewa ya tabbatar su Yahya basu tsira daga gare shi ba, sannan a tabbatar an tafi da Amrah Lagos daga nan a wuce da ita ƙasar waje. Na kasa gane me ke faruwa".

Kallonta Usman ya yi ya ce.
"Kina nufin Abba ya sace su Amrah?".

Amsa Ramlat ta bashi da cewa. "Ƙwarai kuwa tabbas ya sace su. Kenen dama Abba ba mutumin kirki bane?"

*********

Ɓangaren su Umar kuwa su kidnappers ɗin na zuwa suka ga babu kowa a wajan in banda Amrah da kuma Umar. Ɗaga bindigar su suka yi kan Umar sannan suka ce. "Ina sauran mutanen suke".

Kallon su Amrah ta yi ta ce. "Mun kunce su, sun gudu".

"Zaku ga abinda za mu yi muku maza ku fita".
Cewar ɗaya daga cikin kidnappers ɗin.

Da sauri Umar ya riƙe hannun Amrah sa'anan suka fita waje.

Bayan Mk ya gama kunce su Zahra. Sooraj ya riƙe hannun Zahra suka fara gudu suna nufar inda kangon yake.

Dai-dai lokacin da su Amrah ke fitowa daga wajan.

Take Amrah ta buge Zahra cikin rashin sani. Da sauri Zahra ta juya domin ganin waye.

Dai-dai lokacin suka haɗa ido da Amrah.

Chakkk Zahra ta dakata yayin da gaban kowanensu ya buga da mugun ƙarfi. Zaro idanuwa waje Umar da Sooraj suka yi.

Sakin baki Zahra ta yi tare da shafa fuskantar. Kallonta Amrah ta yi domin ganin mai kama da ita sakkk.

"Me nake gani haka?, wayyo Allah babu maraba dani da ita". Cewar Zahra wacce ta ƙura wa Amrah kallo. Yayin da itama Amrah abinda take yi kenen.

"I can't believe this". Cewar Sooraj.

"Wayyo Allah shin gamo nayi ko kuwa". Amrah ta faɗa cikin zuciyarta.

"Babu maraba tsakaninsu, abinda ya bambanta su shi ne ƙwayar idanuwa". Cewar Umar wanda ya saki baki yana kallo.

******
Riƙe hannun Safira Aliyu ya yi sannan ya fita da ita.

Zagayawa suka yi daidai inda su Zahra suke.

Cikin rashin sa'a ƙafar Safira ya buge itace. Hakan ya sa ta sakin ƙara!.

Waigawa gaba ɗaya suka yi nan take idanuwansu ya sauka kan Safira. Yayin da ita ma Safira nats idanuwa suka sauka kan su Zahra.

Nan take gabanta ya faɗi!, yayin da wata iriyar razananniyar ƙara! .

Ɗora hannu Zahra ta yi a kai ya ce. "Na shiga uku wai masu kama dani ɗin har guda nawa ne?, shin mafarki nake yi ko kuwa".

Nan Zahra, Safira da Amrah suka haɗa baki wajan faɗin.

"muɗin su waye?".

Jiri ne ya fara ɗiban su ukun. Nan take kowacce a cikin su ta faɗi ƙasa sumammiya.

Ba tsammani su Umar suka ga an fara wani irin iska mai haɗe da guguwa wacce karaɗe ilahirin dajin baki ɗaya.

WASA FARIN GIRKI🤸♀️💃💃💃🤸♀️🤸♀️🤸♀️

ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTUhttps://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
(We stand together)
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 5️⃣5️⃣▶️5️⃣6️⃣
_______________________
A matuƙar tsora ce Sooraj ya nufi inda Zahra ta faɗi da mugun sauri tare da ɗago ta ya fara jijjiga ta a razane da firgici yana mai faɗin Zahra me kika aikata haka? ya za ki sha wannan abunda kika san guba ce a ciki kina da hankali kuwa".

Hankalin Mami da sauran ƴan cikin falon ba ƙaramin tashi ya yi ba ganin yadda Zahra ta fara fita daga cikin hayyacin ta. fusge jikin ta zahra ta yi daga jikin na Sooraj sannan ta miƙe tsaye a hankali nan take jiri ya ɗebe ta, ta faɗi a ƙasa . Da sauri Sooraj ya nufi inda take sannan ya dauke ta ya nufi waje da ita da mugun gudu saboda sauri ko ganin gabansa ba ya yi.

Kai tsaye inda motarsa yake ya nufa tare da nufar side ɗin ƴan zaman banza tare da buɗe ƙofar motar sannan ya saka Zahra a cikin mota sannan ya rufe ya juya tare da shiga mazaunin driver ya sa car key ya ta da motar tare da jan motan da gudu ya fita daga cikin masarautar. tafiya yake yi ba gaggautawa tare da wani irin gudun tuki tamkar ana tseren mota.

Maida kallonsa ya yi kan Zahra hankali a tashe ya ce. "Kada ki damu Zahra babu abinda zai same ki zan ceci rayuwar ki duk rantsi duku ya bazan taba bar ki ba, saboda dalilin mu bazan so a ce kin rasa rayuwar ki ba, ban sani ba ko gaskiya ne abunda su Samira suka faɗa amma tabbas na san da cewar ba zaki iya aikata abinda suka ce kin yi ba, amma ke ma me ya sa za ki sha wannan guba tunda kin san da cewa cutar dake zai yi bai kamata a ce kin sha ba, ya kamata ace anyi bincike kafin nan a gano gaskiyar lamari amma kuma kika ɗauki gubar ki ka sha gashi nan za ki mutu a banza. Ya kamata a ce kin fahimce ni ban so a ce kin sha wannan guban ba, idan kika mutu ban san wani hali zan iya shiga ba".

Zahra dake kwance ta yi luff jin maganganun Sooraj ya sa ta sakin murmushi cikin zuciyarta ta ce. "Dama haka ya damu da ni shi ne kuma zai mare ni wato dai ya san ba nice na saka wannan guban ba amma kuma shi ne yake yi kamar bai sani ba, lallai dole in koya masa hankali".

Buɗe idon ta guda ɗaya ta yi tare da kallon sa da gefen ido da sauri. A hankali ta buɗe idonta gaba ɗaya tare da kallon sa. A matukar tsora ce Sooraj ya dube ta sannan ya ce. "Kina lafiya?, babu abinda ya same ki?".

Harara Zahra ta galla masa sannan ta saukar da glass ɗin motan tare da tofar da poison din bakinta.

Mamaki ne ya kama Suraj ganin cewar bata haɗiye poison din ba. "Wai dama ashe ba haɗiye poison din nan kika yi ba ki kai kamar kin haɗiye?".

Kallon baka da hankali Zahra ta bishi da shi sannan ta ce. "jaka ce ta mun gula da zan haɗiye guba?, an gaya maka bana son rayuwata ne eh?, na ce an gaya maka bana son rayuwata ne?. To in faɗa maka kawai na sha ne saboda na kawar da tunanin ku a kaina amma me zai kaini shan guba bayan ba gajiya nayi da rayuwar ba".

girgiza kai Suraj ya yi sannan ya ce. "lallai yarinyar nan kin cika tantiriya kuma a hatsabibiya, wato dama baki sha wannan gubar ba shi ne kuma kika tayar mana da hankali lallai yarinyar nan sai na koya miki hankali wannan wani irin shashanci da akuyanci ne wannan ai ba daidai ba ne, me kike tunanin zai faru by mistake kika haɗiye guban?".

Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Eh ba matsala Allah ya yi lokaci na ne ya yi. Sannan ma da ka ke wani min magana ina ruwanka da ni?, ɗazun nan ka gama mari na yanzu kuma kana nuna wa kamar ka damu da ni. Ni ka bani ruwa na kuskure bakina guban yana min wani iri a baki".

"Bani da ruwa, ko kinga frigde ne a cikin motan?". Cewar Sooraj wanda ya tsaya faman kallonta yayin da yake driving.

Amsa Zahra ta bashi da cewa. "Na sani abu a duhu a bak'ar leda, na sani ko Kanada fridge a motarka?, ni ka kalli gaban ka kada kasa muyi hatsari, idan kaga mai shagon saida ruwa saika tsaya kaje ka siyo min".

Kallon baki da hankali Sooraj ya bita da shi ya ce. "Karki samu damuwa shi kanshi mai shagon da shagon gaba ɗaya zan haɗa na kawo miki".

******************
Shiru kawai Safira ta yi yayin da taji cikin ta nayi mata ciwo alamun tana jin yunwa. Kallon Aliyu ta yi da rinannin idanuwanta cikin raunatacciyar murya ta ce. "Ina jin yunwa, ciki na yana min ciwo dan Allah ka kaini gida Please".

Kallonta Aliyu ya yi ya ce. "Karki damu zan nemo mana abinci, yanzu idan na fita za su ganmu kuma su kashe mu".

Cikin rashin fahimtar maganarsa Safira ta dube sa ta ce. "Su waye kuma za su ganmu kuma su kashe mu?".

Amsa Aliyu ya bata da cewa. "Mutanen da suke neman rayuwar mahaifiyar ki da kuma taki rayuwar tare da na ƴan uwanki, sannan duk wanda ya yi nasaran kashe ki ko mahaifiyar ki da ƴan uwanki, za su samu dubbannin kuɗaɗen da ba za su misaltu ba".

"What!". Safira ta faɗa cikin rashin maganarsa ta ce. "I don't understand, me Mom ta yi musu za su kashe ta?, sannan kuma wane ƴan uwa ka ke magana a kai?".

Amsa Aliyu ya bata da cewa. "Bawai ina nufin Mom ba, domin Mom ba ita ce mahaifiyar ki ba".

Rass! Zuciyar Safira ta buga yayin da ta zaro idanuwa waje. Rai a ɓace ta ce. "Kamar ya Mom ba ita ce mahaifiyata ba?, wannan wane irin shirme ka ke faɗa aka?, idan Mom ba ita bace ta haife ni wace ts haife ni to?".

Amsa Aliyu ya bata da cewa. "Mrs Lailah Abdullahi, tana ɗaya daga cikin richest women in the world, ita ɗin Aunty ta ce, kamar uwa take a waje na".

"Hanya ba wani abun ka sha ba kuwa?, ni bani da wata uwa in ba Mom ba, ka daina faɗa min waɗan nan tatsuniyoyin domin ba yarda zanyi ba".

*************
"Gashi yallaɓai Hajiya Binta ce ta ce na baka wannan littafin, ka bawa Zahra shi idan ka ganta".
Cewar warder.

Kallon littafin hannunta DPO ya yi ya ce. "Littafin mene ne kuma wannan?. Shikenen naji labarin cewar Zahra na Kano har yanzu sannan tana masarautar chan, zan je na tabbatar idan tana chan sannan na dawo da ita". Ya faɗa tare da miƙa hannu ya karɓi littafin sannan ya ajiye a gefe.

*******
Sooraj kuwa chan ya hango mai saida ruwa. Parking ya yi tare da sauka sannan ya je ya siyo ruwa guda ɗaya. Saida ya ɗau lokaci Sosai Kana ya dawo cikin motan. Zuwan shi keda wuya ya ga bata cikin motan.

Mamaki ne ya kama Sooraj . "Lallai ma yarinyar nan, yanzu kuma ina ta shiga". Waige-waige ya soma yi, chan idanuwansa ya sauka a kanta. Tsaye take da wasu samari guda uku suna sanye da baƙaken suit. Yayin da Zahra ke surfa musu bala'i ta inda take shiga bata nan take fita ba.

Dafa kansa Sooraj ya yi. "Wayyo Allah, wannan wace iriyar masifa ce, wai ko ina taje saita nuna halin ta".

Ya faɗa yana mai ƙarasa wa inda take. Zuwa wajan keda wuya Zahra ta ganshi. Girgiza kai Zahra ta yi ta ce . "Yauwa masha Allah kazo a dai-dai, zo ka jini da wata masifa, ina zaman-zama na waɗan nan kajin dake sanye cikin wannan abun da suka kira suit suka zo inda nake, na tambaye su me suke so suka ce wai ai zuwa suka yi su sace ni, shi ne na ce idan za su iya su sace ni".

Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Kema in banda abunki ai wasa suke miki".

"A'a wallahi waɗan nan ba wasa suke ba, kana ganinsu yadda ka san wasu ƙasurguman masheƙa, ni kuma dai-dai nake da su". Cewar Zahra wacce ta faɗa hannunta riƙe a ƙugu tana karkaɗa su tare da karka ƙafarta yadda kasan wacce zata yi dambe.

"Shi ke nen to mu tafi ko". Sooraj ya faɗa yana mai kama hannun Zahra.

Nan take maza ukun da ke sanye cikin suit suka kalli juna, nan suka fito da wani abu kamar perfume tare da fesa musu.

Duk abinda ke faruwa a gaban idanuwan Mk.

Nan take jiri ya ɗebe su suka faɗi a ƙasa.

Kwashe su mutanen suka yi tare da saka su a mota.

Ganin hakan ya sa jama'a suka saki ihuu yayin da suka jifar motan kidnappers ɗin da dutsina. Da sauri kidnappers ɗin suka tada mota tare da fara ƙoƙarin barin wajan. Nan jama'a suka dinga binsu a baya har suka ɓace wa ganinsu.

Da sauri Mk ya nufi inda motar Sooraj yake domin ganin idan akwai inhaler a motar domin ya san perfume da aka fesa musu zai iya affecting ɗin shi, domin kuwa ya san Sooraj yana da asma. Nan ya fara dube-dube a motar. Cikin sa'a kuwa ya ga inhaler ɗin saman kujera. Da sauri ya ɗauka sannan ya nufi motarsa da sauri tare da tada wa ya bi bayansu Zahra.

Gudu suke falfalawa kamar za su tashi sama.

Buɗe idanuwanta Zahra ta yi ta gansu cikin mota. Ihuuu ta buga yayin da ta fara dukan wanda ke bayan seat ɗin kusa da Sooraj.

Nan take ɗaya a cikin su ya kwaɗe ta da mari. Jin marin Zahra ta yi har cikin ƙwaƙwalwarta. Nan take ta fusa ta yayin da ta kama kunnen wanda ke kusa da ita tare da fara gantsara masa cizo.

Ihuuu saurayin ya buga yayin da ya fara ƙoƙarin ƙwace kanshi amma hakan ya cutura. Kuma hakan bai sa sun dakatar da tuƙin ba.

Nan saurayin ya taki sa'a ta sake shi. Ganin ta saki kunnensa ya sa shi dafa kunnensa wanda ya yi jajir. Gurnani ya fara yi. Nan ya shaƙe mata wuya tare da ƙoƙarin yi mata allura kan jijiyar wuyanta.

Duk abinda ke faruwa Sooraj bai sani ba, domin har izuwa wannan lokaci bai farfaɗo ba.

Babu zato suka fara jiyo Sooraj yana nishi sama-sama alamun asma ɗinsa ya tashi.

Ganin hakan ya sa Zahra ta sa dukannin ƙarfinta ta ture wannan saurayin.

Hankali tashe ta ɗaga Sooraj tare da girgiza shi. "Yahya Sooraj me ya sa me ka?, dan Allah kada ka mutu ka barni".

Cikin fitar hayyaci Sooraj ya dube ta ya ce. "Asma ɗina ya tashi kuma inhaler ɗina yana cikin motata".

Zaro idanuwa waje Zahra ta yi nan take tausayin Sooraj ya kama ta. Kallon kidnappers ɗin ta yi ta ce . "Dan Allah ku mayar da mu, idan ba haka ba zai mutu, ko baku ga yana cikin mawuyacin hali ba ne".

Ko kallon Zahra basu yi ba saima ƙara wa motar gudu da suka yi.

Rungume Sooraj Zahra ta yi tare da ɗaukar ruwan da ya siyo ta bashi yasha.

Chan cikin dajin suka isa. Tsayar da motar suka yi tare da fitowa. Sannan suka fito da Zahra da Sooraj kana suka ɗaɗɗaure su jikin bishiya sannan suka nufi inda su Amrah suke domin fito da su.

Dai-dai lokacin shima Mk ya ƙaraso wajan. Da sauri ya nufi inda su Sooraj suke sannan ya bashi inhaler ya shaƙa.

Dubansa Zahra ta yi ta ce. "Dan Allah ka kunce mu".

"Shiiiiii!". Mk ya yi mata alama da hannu da ta yi shiru.

A hankali Mk ya fara kunce su yana mai waige-waige.

******************
"Wai ni kamm Yahya Usman ina su Amrah da Yahya Umar suke?, har yanzu shiru basu dawo gida ba, ni fa ina tsoron kada wani abu na cutarwa ya cutar ds su.
Cewar Khairiya.

Kallonta Usman wanda ke zaune kan 3seater ya yi ya ce. "Babu abinda zai same su, insha Allah suna cikin ƙoshin lafiya, ni na matsu su dawo mu koma jigawa".

Kallon su Ramlat ta yi ta ce. Ni fa ina ganin kamar akwai abinda ke tafiya ba dai-dai ba, tabbas akwai wani abu da Yahya ke ɓoye mana, kuma baya son mu sani".

Kallonta Usman ya yi ya ce. "Mene ne to Yahya zai ɓoye mana?".

Amsa Ramlat ta bashi da cewa. "Jiya na kira Abbah, munyi waya to a lokaci da muka gama wayar ya manta bai kashe wayar ba, naji yana yin magana da wani bansani ba ko mace ce ko namiji, naji yana cewa ya tabbatar su Yahya basu tsira daga gare shi ba, sannan a tabbatar an tafi da Amrah Lagos daga nan a wuce da ita ƙasar waje. Na kasa gane me ke faruwa".

Kallonta Usman ya yi ya ce.
"Kina nufin Abba ya sace su Amrah?".

Amsa Ramlat ta bashi da cewa. "Ƙwarai kuwa tabbas ya sace su. Kenen dama Abba ba mutumin kirki bane?"

*********

Ɓangaren su Umar kuwa su kidnappers ɗin na zuwa suka ga babu kowa a wajan in banda Amrah da kuma Umar. Ɗaga bindigar su suka yi kan Umar sannan suka ce. "Ina sauran mutanen suke".

Kallon su Amrah ta yi ta ce. "Mun kunce su, sun gudu".

"Zaku ga abinda za mu yi muku maza ku fita".
Cewar ɗaya daga cikin kidnappers ɗin.

Da sauri Umar ya riƙe hannun Amrah sa'anan suka fita waje.

Bayan Mk ya gama kunce su Zahra. Sooraj ya riƙe hannun Zahra suka fara gudu suna nufar inda kangon yake.

Dai-dai lokacin da su Amrah ke fitowa daga wajan.

Take Amrah ta buge Zahra cikin rashin sani. Da sauri Zahra ta juya domin ganin waye.

Dai-dai lokacin suka haɗa ido da Amrah.

Chakkk Zahra ta dakata yayin da gaban kowanensu ya buga da mugun ƙarfi. Zaro idanuwa waje Umar da Sooraj suka yi.

Sakin baki

Please Login or Register in order to submit comment