Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tareda fara siyayyar abubuwan da Mami ta gaya mata. A sa'inda su Samira suka samu guri suka zauna a bunsu.


Saida Zahra ta gama siyayya tsaff sannan ta saka hannu domin ciro kuɗi a jikin ta. Wayam ta ga babu kuɗi ba alamar su. Zaro idanuwa waje ta yi tare da sakin salati.


"Yau akwai tashin balagan tsuntsaye. Wane ɓarawon ne ya sace min kuɗi, tabbas yau babi wanda zai fita daga kasuwan nan muddin ba'a fito da kuɗin nan ba".




*******
Jere fararen motoci ke tafiya kan titin wanbai. Tare da dokuna wanda suka mara musu baya da kuma fadawa wanda suka zagaye motocin yayin da jama'a suka shiga miƙa gaisuwa.


Cikin motan kuwa wani mature guy ne zaune cikin mota a ƙalla zai kai kimanin shekaru 35 zuwa 38 ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. Yayin da news paper ke riƙe a hannunsa. Dukkan yabo da jinjina su tabbata ga ubangiji wanda ya yi wannan kyakyawar halittar.


Sanye idanuwansa suke da broline glass yayin da hannayensa suke sanye da rolex wrist watch. Lumshe idanuwansa ya yi masu kama da madara. Yayin da suman kansa suka kwanta suka yi luff. Sajen fuskarsa masu taushi da laushi suka ƙara masa kyau.



Sanye yake cikin labcoart duban driver ya yi cikin cool voice ɗin sa ya ce. "Ka wuce da ni kasuwa zan siya black tea".


Murmushi Driver ɗin ya yi ya ce. "Aba ranka shi daɗe, mene ne amfanin mu?, yau ɗin nan ka dawi Nigeria bai kamata ka shiga kasuwa ba idan muka isa fada ƴan aiki za su zo su siya".


Girgiza kai mutumin ya yi ya ce. "Kaine shugaba ko ni ne shugaba?, maza kayi yadda na ce".


"A gafarce ni ranka shi daɗe in sha Allahu zamu je. Amma me ya sa ba zamu wuce shopping mall ba sai cikin kasuwa?, ina ganin kamar hayaniya ta yi yawa a chan".


Shiru Yarima ya yi sannan ya ce. "Shi na gadaman zuwa kai mene naka?".


"Bakomai ranka shi daɗe ". Driver ɗin ya faɗa.


Kai tsaye kasuwa ya nufa da su. Yayin da ya tarar da taru jama'a sun yi zagaye da alama wani abu ne ke faruwa.



Ɓangaren Zahra kuwa babu abin da take sai surfa bala'i yayin da ta rikita kasuwar a lallai sai an fito da wannan kuɗi.


Babu abin da mutane ke yi sai kallo.



Fitowa Yarima Sooraj ya yi daga cikin mota. Daga nesa su Samira suka hango shi. Nan take cikin su ya ɗuri ruwa. A hankali suka silale daga wajan.



Ƙarasawa wajan Sooraj ya yi. Nan idanuwan shi ya sauka a kan Zahra wanda sai faman masifa take ta inda take shiga ba ta nan take fita ba. Takaici ne ya kama Sooraj, dubanta ya yi ya ce. "Ke baki da hankali ne za ki zo ki tada wa mutane hayaniya a wajan nan". Ya faɗa cikin ɓacin rai.



Dubansa Zahra ta yi nan suka haɗa ido a tare. take gaban kowanensu ya faɗi!, yayin da suka fara jin wani irin yanayi na da ban.


Galla masa harara Zahra ta yi ta ce. "Kai malam waya gayyace ka nan?, shin ka zo ka biya kuɗin da haka sace ne?, to maza ware daga nan".


Nan take ran Yarima Sooraj ya ƙara ɓaci. Take ya ji tsanarta ya shiga cikin ransa ya tsani mace mara kamun kai da rashin sanin darajar kai.



Juya wa Yarima Sooraj ya yi tare da barin wajan. Shiga cikin mota ya yi yayin da driver suka tada mota suka bar wajan.

Kai tsaye masarauta suka nufa.


Bayan tafiyar Sooraj ne Zahra ta ga kuɗin a dunƙule s ƙasa. Hamdala ta yi tare da bawa mutanen gurin haƙuri. Miƙa wa mai kayan kuɗin ta yi tare da karɓar abubuwan da ta siya.


Waige-waige ta fara yi domin gani su Samira amma ba ta gansu. Haka ta ci gaba da cigiyar tmds ta ga ba zata iya ba ta shiga cikin mota yayin da driver ya ja ta suka bar kasuwan.




Shiga ciki motocin su Sooraj ya yi cikin masarauta. Nan take dakarai da fadawa suka shiga durƙusawa suna kwasar gaisuwa tare da yi masa ƙirari.



Fitowa Yarima Sooraj ya yi tare da amsa gaisuwar tasu.


Yayin da su Gimbiya Talatu suka sha jinin jikinsu. Gaishe da mai martaba Yarima Sooraj ya yi cikin girmama wa tare da gaidar da su Gimbiya Saratu. Sama-sama su Gimbiya Saratu suka amsa.


Part ɗin sa ya nufa tare da nufar ɗakin ajiyar sa sannan ya saka thumbprint ɗin sa. Nan take ƙofar ta wangale gani ya yi an tsaftace ɗakin an gyara shi ba kamar yadda yake ba. Mamaki ne ya bayyana kan fuskarsa. Da sauri ya fita daga cikin ɗakin tare da fitowa harabar fada yana mai ƙwalla kiran kowa na wannan masarautar. Kan ka ce me mutane sun taru a fada.


Kallon kowanensu ya yi sannan ya ce. "Wane ne wanda ya shiga ɗakin ajiya ta?". Shiru gaba ɗaya suka yi babu mai bakin magana. Dai-dai lokacin da Mami da su Samira ke ƙarasowa wajan.



Daka musu tsawa ya yi yana mai faɗin. "Na ce wane ne ya shiga ɗakin ajiya ta?". Ya faɗa rai a matuƙar ɓace. Sannan ya ce. "Tabbas ko wace ce wannan ƴar leƙen asiri ce kuma ba zan rabi da koma wane ne ba. babu wanda ya san password ɗin wannan ɗakin sai ni kaɗai, ta ya ya haka iya buɗe wa bayan ni kaɗai ne na san password ɗin?".


Kallonsa Mami ta yi ta ce. "Eh wata sabuwar ƴar aikin mu ce sunanta Zahra. Laifi ta yi shi ne mai martaba ya ce za ta dinga share wannan ɗakin kuma babu ranar da za ta tashi ta faɗi ba ta share ba".


"Where is she?". Yarima Sooraj ya tambaya cikin tsananin ɓacin rai.



Dai-dai lokacin da motar su Zahra ke shigowa. Parking motan ya yi yayin da ta fito tare da kayayyakin da ta je siya.


Maida kallonsu suka yi baki ɗaya kanta. "Yauwa ka ga ƴar halak ita ce wannan". Mami ta faɗa tana mai nuna Zahra.



Take rab Yarima Sooraj ya ƙara ɓaci ganin yarinyar da ya gani a kasuwa. Ƙarasawa wajan Zahra ta yi ganin yadda gaba ɗaya suke binta da ido ya sa ta kawar da kanta gefe.



Nan take ta haɗa ido da Sooraj. Take gabanta ya faɗi!. Sakin kayan da ta riƙo ta yi gaba ɗaya suka faɗi ƙasa. Sannan ta fara tafa hannunta tare da riƙe haɓarta ta ce. "Iyyeeh!, wato har gida ka biyo ni kenen, ƙara ta ka kawo ko me?, dama ina ganin fuskar ka na san kai ba na Allah ba ne. To maza zo ka fice daga cikin masarautar nan kada ka bari Yarima Sooraj ya shigo ya tarar da kai a nan domin ba za ka ji da dad'i ba".


Murmushi Yarima Sooraj ya yi ya ce. "Au aba da da gaske?".


Amsa Zahra ta bashi da cewa. "Ƙwarai da gaske nake ko zaci ƙarya nake?. Idan ka bari Yarima Sooraj ya zo ya ganka a nan ba za ka ji da dad'i ba".


Kallonta Mami ta yi ta ce. "Wane Yarima Sooraj kuma bayan gashi nan a gaban ki".



Nan take gaban Zahra ya bada wani irin sauti. "Kambala'i, da gaske shi ne?".


Amsa Mami ta ba ta da cewa. "Ƙwarai da gaske shi ne".


Haɗiye tsoron da ke ƙoƙarin bayyana Zahra ta yi ta ce. "Shi ke nen tawa ta ƙare!".











*KUYI HAƘURI DA RASHIN UPDATE DA WURI DAN ALLAH*.





LIKE, COMMENT AND SHARE FISABILILLAHI 🙏 🥺 🥺 🙏

ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
(ZINARIYAR JAJIRTATTU)


*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Thre siblings from different part of the world)*🪐🌎🪐.
Daji 🌲
Magarƙama🏢 da kuma
Birni🏙️

WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝♀️Jajirtattu)


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
(We stand together)
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 3️⃣7️⃣▶️3️⃣8️⃣
*___________________________________________*
Jiki a muce Zahra ta ɗauki kayan da ta zube a ƙasa sannan ta fara ƙoƙarin wuce wa ta gefen Sooraj, a sa'inda zuciyarta ke dukan uku-uku!.


Daga sama ta ji muryarsa. "Dakata!". Ta ji Sooraj ya furta.


Tsaya wa chak Zahra ta yi yayin da ta kasa motsa ko da ɗan yatsarta ne saboda tsananin tsoron da ta shiga.


Zagayowa Yarima Sooraj ya yi har gabanta sannan ya tsaya yana mai fuskantar ta. Yayin da ɓangaren guda idanuwan jama'a a kansu.


Ƙura mata idanuwansa ya yi masu matuƙar ɗaukar hankali sannan ya ce. "wace ce ke?".


Jin tambayar da ya yi mata, hakan ya sa Zahra ta bashi amsa da cewa. "Ni mutum ce mana".

Kallonta ya yi cike da mamaki ganin yadda babu wata alama na nuna jin tsoronsa a tattare da ita, hakan ya ƙara bashi aushi. "Ke haka na ce wace ce ke, me ya kawo ki wannan masarautar?, sannan daga ina ki ka fito?, da me ki ke takama?, sannan tambaya ta ƙarshen ta ya ya ki ka iya buɗe ɗakin ajiyana bayan ni kaɗai ne na san maƙullin sirrin buɗe wannan ɗakin?".


Zololo Zahra ta yi tana kallon shi. "Kai kuwa Yarima irin wannan tambayoyi haka sai ka ce google ake tambaya, ai sai kayi min tambayar ɗaya bayan ɗaya. To farko dai ni sunana Fatima ana kira na da Zahra, na rasa mahaifiya ta ne tun kafin na san ciwon kaina, yanzu haka bani da kowa sai iya Aunty Binta wacce ke kula da ni. Sannan batun me ya kawo ni masarautar nan babu ita domin ba ni ce na kawo kaina ba Mami ce ta buƙaci na zo nayi aiki domin tara kuɗin motan da zan koma garin mu Jigawa. Sannan ka ce da me nake takama, to ni dai babu wanda nake takama da shi sai mahallici na bayan shi kuma babu, sannan sanin ta yadda na iya buɗe wannan ɗakin abu mai sauƙi ne domin wani suna kawai na danna ya buɗe, shi ke nen".


Ajiyan zuciya Sooraj ya sauke!, sannan ya ce. "Har yanzu baki bani amsa gamsashiya ba. zan ƙara tambayar ki a karo na uku ko. Wace ce ke?".


Furzar da iska mai zafi Zahra ta yi kana ta ce. "Kamar yadda na faɗa maka tun fari, sunana Zahra, ni ɗin na taso ni cikin magarƙama tsakiyar masu laifi, hatta daga yin wayo na har izuwa girma na a magarƙama nayi".


Zaro idanuwa waje gaba ki ɗaya al'ummar masarautar suka yi.
Murmushi Sooraj ya yi sannan ya ce. "Kenen dai ke ɗin babbar mai laifi ce ko?".


Sauke ajiyan zuciya Zahra ta yi!, sannan ta ce. "A'a, mahaifiyata ce haka yi mata sharri shi ne aka kaita magarƙama bayan ta haife ni ne ta rasu, kuma ƴan uwanta suka ƙi ƙarɓa ta shi ne Hajiya Binta ta raine ni". Ta ƙarashe maganar zuciyarta nayi mata zafi da ƙuna.



Murmushin mugunta Sooraj ya saki kana ya ce. "Kenen dai mamarki ita ce muguwa ko?, ita ce babbar mai laifi har aka kaita magarƙama. Ai dole ma ƴan uwanta su yi rejecting ɗin ki saboda kar su zo suna dana sanin karɓar ki, sai kuma gashi kema kin yo halin uwar taki".



Danne fushin da ke ƙoƙarin bayyana kan fuskar ta Zahra ta yi tare da kawar da kanta gefe sannan ta ce. "Yarima ka san me za ka faɗa dan Allah, ka iya sarrafa harshen ka".


"Ba zan sarrafa harshen nawa ba". Sooraj ya faɗa a matuƙar tsawa ce.


Nuna Zahra ta yi da yatsarsa sannan ya ce. "Na tabbatar da cewa ke ƴar leƙen asiri ce, kuma idan ki ka kuskure na gano ko asalin wace ce ke to ba za ki sha ba". Yana kaiwa nan ya shige cikin fada sannan ya nufi part ɗin ta.



Sallamar kowa Junaid ya yi, yayin da jama'a suka watse saura mutanen cikin masarautar.


Kallon Zahra Mami ta yi sannan ta ce. "Zahra tawo mu shiga daga ciki".


Murmushi wanda ya fi kuka ciwo Zahra ta yi ta ce. "Wallahi Mami nayi duba da irin mutunci da kuma kima da ki ke da shi ne a waje na. Hakan ya sa na rabu da yarima Sooraj, amma da ba dan haka ba wallahi sai ya san cewa Allah ɗaya ne, ba zan ji daɗin a zagar wa wani mahaifiyarsa ba, haka zalika nima ba zan ji daɗin a zagar min tawa mahaifiyar ba, da ka zagin uwa ta na gwammace ka kwana kana zagi na".


Tana kaiwa nan ta shige cikin fadan sannan ta shiga ɗakin kwanan ta wanda haka ware mata a matsayin ƴar aiki.


Kallon Juna Gimbiya Saratu da Talatu suka yi tare da bushe wa da dariya yayin da suka riƙe hannun juna sannan suka shige part ɗin su.

Girgiza kai kawai Mami ta yi sannan ta ce. "Allah ya ganar da ku gaskiya". Ta faɗa tare da shige wa part ɗin ta.


Rakiya Junaid ya yi wa mai martaba izuwa fadar sa. Gaba ɗaya gidan ya koma kaman gidan makoki. Babu wani hayaniya ko surutu. Abincin ma da aka jera kan dining babu wanda ya bi ta kansu.



Zahra na shiga ɗaki kuwa ta kwanta kan gado. Yayin da fuskar Sooraj ya fara yi mata gizo. Lokaci ɗaya ta ji tsanar sa ya mamaye zuciyar ta. "Aikin banza kawai, dan kawai yana matsayin ɗan gidan sarauta shi ne zai zo ya dinga raina wa mutane hankali, ni Allah ya bani kuɗi ma ni na haɗa kuɗin mota na tafi, na san kuɗin motan ba za ta wuce dubu biyu zuwa dubu uku ba". Dafa cikinta ta yi jin yadda yake murɗa mata alamun yunwa take ji.



"Kambala'i, ashe fa ban ci abincin safe ba na fita, chab Zahra me ki ke jira maza-maza tashi kije ki cika cikin ki". Ta faɗa tana mai miƙe wa tsaye sannan ta nufo hanyar ƙofar ɗakinta ta murɗa handle ɗin ƙofar ta fita.






_________________________
"Dan Allah Amrah ki nutsu, ko daina kuka kinji, munyi miki alƙawarin duk in da ƴan uwanki suke zamu kai ki wajan su". Ramlat ta faɗa damuwa bayyane kan fuskarta.


Girgiza kai Amrah ta yi cikin ƙaramin muryarta ta ce. "Ni A'a, ku maida ni inda ku ka ɗauko ni, ina son ganin ƴan uwana". Ta ƙarashe maganar tana mai rushe wa da kuka.



Dai-dai lokacin Umar ke ƙaraso wa wajan. Su Khairiya kuwa, ganin Umar ya ƙaraso ya sa su sakin ajiyan zuciya sannan suka ce. "Yauwa yahya barka da dawo wa, ka ga Amrah tun ɗazu take kuka wai ita a mayar da ita in da aka ɗauko ta".



Furzar da iska Umar ya yi waje sannan ya nufi in da Amrah take zaune karƙashin bishiya ta yi ruff da ciki. Ƙarasawa ya yi wajan da take sannan ya dube ta ya ce. "Amrah, me ki ke so?".


Ɗago da rinannun idanuwanta Amrah ta yi ta ce. "Ina son ganin ƴan uwa na".


Kallonta Umar ya yi a karo na biyu ya ce. "Shi ke nen, idan ki ka ga ƴan uwan naki komai zai dawo dai-dai?".


Girgiza kai Amrah ta yi alamun eh.

Miƙe wa tsaye Umar ya yi ya ce. "Shi ke nen, zamu kaiki wajan na su".


Kallon Umar Usman ya yi ya ce. "Yahya me ka ke cewa haka?, ta ina zamu samo su?, basun riga sun mut......


"Shshiiiiiii!". Umar ya yi alama da hannu da ya yi shiru.


Shiru Usman ya yi yana mai jiran furucin da zai fito da baki yayan nasa.


Kallon Umar Khairiya ta yi ta ce. "To yahya a ina za'a samo su?".


Amsa Umar ya ba ta da cewa. "Wallahi nima ban sani ba, lokacin da Abba ya je ya saka mutanen sa suka je suna kashe dabbobin dajin ban sani ba sai daga baya naje na tarar da sun kashe duk dabbobin dajin. Ni yanzu ban san ya zan yi ba".




Kallon su Ramlat ta yi ta ce. "Yahya ina da shawara".



"Mene ne?". Suka furta a tare.


"Ku matso ku ji". Ramlat ta faɗa. Matso wa suka yi kusa da ita tare da kasa kunnen su in da take.


Shiru ta yi kana daga bisani ta ce. "Me zai ana muje gidan Zoo na san dai akwai dabbobi a chan, mybe idan muka kaita ta ga dabbobin cikin wajan za ta yi farin ciki. Amma ya ku ka gani?".


Murmushi Khairiya ta yi ta ce. "Wow wannan shawara ce mai matuƙar kyau".


Shiru Umar ya yi na ɗan wasu lokaci sannan ya ce. "Kuma ganin wannan shawarar za ta yi aiki kuwa?".


"Me zai ana?, zai yi aiki mana, suma ai dabbobi ne a chan na san idan ta gansu za ta yi farin ciki".
Cewar Usman. Sannan ya ƙara da cewa. "Amma kamar babu gidan zoo a nan dutse ko?, ni dai ban sani ba ko akwai ko babu".


Kallonsa Umar ya yi ya ce. "Ko akwai ma, ba na wannan zamu je ba, ina son muje Kano daga nan zan yi bincike na a kan wanda nake nema mai safaran miyagun hayyuka".



"Shi ke nen bara muje mu haɗa wasu kayan mu da wanda Amrah za ta saka". Khairiya ta faɗa suna mai shige wa ciki. Lokaci ƙalilan ya ɗauke su suka gama shirya wa sannan Umar ya kalli Amrah ya ce .


"Tashi muje zamu kaiki in da ƴan uwanki suke". Jin abin da Umar ya faɗa, hakan ya sa Amrah saurin miƙe wa tare da sakin murmushi. Juyawa suka yi gaba ɗaya suka nufi wajan parking space, ganin hakan ya sa Amrah ta yi saurin bin bayansu. Shiga cikin motan ɗaya Usman da su Khairiya yayin da Usman ya tada mota, tare da fice wa daga gidan. Buɗe wa Amrah ƙofa Umar ya yi ta shiga sannan ya sauke mata glass ɗin motan ƙasa. Sannan ya tada motan tare da barin harabar gidan.


Daga bisani suka nufi hanyar garin Kano.


*To kafin mu cigaba dai muna son sani wane ne asalin Umar? sanann wane ne asalin gov. Musa Muhammad*.

Alhaji Muhammad shi ne asalin mahaifin Musa Muhammad. Alhaji Muhammad ya kasance mutum tawakali da kuma sanin ya kamata, ya kasance mutum bai bin ƙa'ida. Matar sa Halima ta rasu ne a lokacin da take naƙudan ƴar su ta biyu wacce ta ci suna A'isha. Musa ya kasance ɗa na fari a wajan mahaifin sa sai kuma A'isha. Musa ya taso tun yana ƙarami da burin zama ɗan siyasa domin shi gaba ɗaya a tunanin shi babu komai a cikin yin harkar siyasa sai kuɗi. Hakan ya sa ya ƙudiri niyar zama ɗan siyasa. Alhaji Muhammad ya tura musa karatu domin ya yi karatun Engineering, sai dai kuma abin da bai sani ba shi ne Musa ya chanza course ɗin da mahaifin nasa ya zaɓa masa izuwa Political science. Musa ya gama diploma sa ne yana da shekaru talatin shif. A wannan lokacin A'isha ta kammala HND ɗin ta. yayin da ta fito da wanda take so wato ɗan sarkin garin Kano. Bayan an ɗaura musu aure shima Musa ya auri matarsa Khadija wanda suka haɗu da ita a University ɗin da ya yi.

Haka ya cigaba da sha'awar zama ɗan siyasa ba tare da mahaifin ko matar sa ta sani ba.

Khadija ta kasance mace mai riƙo da addini, tana ƙoƙarin gujewa duk abin da zai ɓata wa mijin ta rai. Bayan shekara ɗaya ta haifo santalelen ɗanta wanda ya ci suna Umar.


Farin ciki wajan waɗan nan ma'auratan ba zai misaltu ba.


Ana tsaka da aka, Musa ya je ya bayyana wa mahaifin sa abin da ya karanta a jami'a. Hakan ya sa ran mahaifin sa ya yi matuƙar ɓaci. Yayin da mahaifin sa ya ƙudiri niyar cewa muddin yana da rai ba zai bari ya zama ɗan siyasa ba. Jin furucin da ya fito daga bakin mahaifin nasa ya sa Musa ya tunzura sannan ya yi tafiyarsa sai bayan wasu lokaci ya dawo wajan mahaifin sa, sai dai a wannan karan bai dawo domin neman yafiyar mahaifin sa ba, ya dawi ne domin ya ɗauki ran mahaifin sa.


Bayan isarsa chan ne ya tara ƴan daba suka zagaye gidan a yayin da ya sa a ɗaukar masa video ta yadda zai kashe mahaifin na shi. Alhaji Muhammad na kwance cikin jinya da tsananin ciwo Musa ya shiga ɗakin nasa. Ganin yana kwance ya sa shi sakin murmushi ba tare da imani ko tausayawa ba ya samu pillow ya danne fuskar mahaifin nasa da shi. Haka Alhaji Muhammad ya dinga kuruwa har rai ya fita daga jikin shi. Musa bai sake shi ba saida ya tabbatar da baya da sauran numfashi. Hakan ya sa shi farin ciki a sa'inda ya dinga ganin kansa matsayin govnor domin kuwa tunda mahaifin nasa ya mutu babu wanda zai ana shi zama govnor.

Jama'a sun yi kuka na rashin Alhaji Muhammad da suka yi, yayin da ita ma Khadija ta ci kukan ta har ta gode wa Allah.

Musa ya fara neman takara shida babban Abokin sa wato Abdullahi wanda suka taso tun suna ƙanana har izuwa girmansu tare suke. Hakan ya sa kowanensu yake da burin zama ɗan siyasa. amma sai dai shi musa bai yi nasara ba domin babu wanda ya karɓe sa hannu biyu. A yayin da Abdullahi ya zama babban ɗan siyasa ya yi alƙawarin gyara ƙasar sa da mutanen cikin ta. Musa ya ji aushi sosai ganin abokin saya samu takara shi bai samu ba, hakan ya sa ya ɗora tsanar duniya a kan abokin nasa, a yayin da yake zuwa wajan Abdullahi da fuska biyu na kirki da kuma na mugunta.

Umar yana da shekaru biyar a duniya Khadija ta kuma haifo santalelen ɗanta saidai yaron bai zo da rai ba. Bayan wasu shekaru Khadija ta sake haifo namiji wanda ya ci suna Usman, Sannan Ramlat sai kuma ta ƙarshe Khairiya wanda su ukun gaba ɗaya shekara ɗaɗɗaya ne a tsakani.


Haka rayuwa ta cigaba wataran da dad'i wataran kuma godiyar Allah. Ana tsaka da haka wata rana Khadija na gyara ɗakin Mijin ta, nan ta tarar da wani caset. Ɗaukar caset ɗin ta yi sannan zuciyar ta tace da ita ta saka caset ɗin a tv ta ga ko film ne. Bayan ta saka caset ɗin ne a tv ta ga abin da ya yi matuƙar firgita tunaninta. Mijinta ta gani ya kashe mahaifin sa da hannunsa . Hakan ya sa ta ji dana sanin auran sa. A dai-dai wannan lokacin kuma Musa ya shigo ya tarar da ita a ɗakin tana kuka. Nan dai ya gano cewa ta gano shi ne wanda ya kashe mahaifin sa. Ganin hakan ya sa Musa ya fara roƙon matar sa da ta rufa masa asiri. Amma ita kuma Khadija taƙi amincewa sannan ta ce dole ta sanar da ƴan sanda ko wane ne mijinta domin ba za ta iya take gaskiya ba. Ganin dai taƙi bashi haɗin kai ne ya sa ya ɗauki glass cup sannan ya rotsa wa kanta. Nan take kanta ya fara fidda jini yayin da ta faɗi ƙasa mutacciya. A dai-dai wannan lokacin Umar ya dawo daga makaranta sannan ya shiga cikin ɗakin nan ya tarar da gawar mahaifiyarsa a kwance. Hakan ya sashi sakin ƙara yayin da ya faɗi ƙasa sumamme.

Ganin hakan ya sa Musa ya goge kowane sheda da ƴan sanda za su bi domin gano makashin.


Bayan nan ne ƴan sanda suka zo suka yi ƙaraci binciken su basu samu komai ba. Hakan ya sa haka rufe case ɗin.


Bayan wasu kwanaki ne Umar ya dawo cikin hayyacinsa a yayin da yake mafarkin mahaifiyar sa sannan ya ƙudiri niyar dole ya zamo jami'i, domin ya san wanda ya kashe mahaifiyar sa sannan kuma ya kare ƙasar sa daga sheɗanun mutane irin mahaifinsa. Umar ya fara jin tsanar mahaifinsa ne tun lokacin ya ga mahaifin sa da wasu karuwai a gidan su. Daga wannan rana Umar ya tsani mahaifin sa.


Bayan Umar ya yi karatun sa na boko da na addini ne ya shiga training school na jami'ai. Hakan ya sa ya fara gudanar da al'amuran sa shi ɗaya. A sa'inda duk abin da ƙanensa suke da buƙata shi yake musu. Kan kace me Umar ya zama babban jami'i wanda gaba ɗaya ƙasa ke magana kan ƙwarewarsa domin kuwa duk wani mai laifi idan ya yi musu wahalan kama wa Umar shi ne wanda ake bawa wannan aikin kuma duk in da wannan mai laifi yake zai nemo shi sannan ya tabbatar da an hukunta shi. Aka ya cigaba da bincike domin

Please Login or Register in order to submit comment