Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saboda kuɗi ba ko mulki".

"Shi ke nen Abba ba bu damuwa, zan dawo ko cikin week ɗin nan ne".

"Okay son Allah ya dawo mana da kai lafiya". Amsa wa Umar ya yi da Amin daga bisani ya kashe wayar.


Miƙe wa tsaye ya yi tare da ɗaukar towel ya shiga toilet. Sai da ya ɗau lokaci sosai kafin ya fito daga cikin toilet ɗin ƙugunsa sanye da towel, sannan ya nufi wajan dressing mirror. Ɗaukar mai ya yi ya fara shafa wa. Sannan ya ɗauki wani oil tare da shafa wa a sumar ƙanshi wanda suka kwanta suka yi luff.
Ɗaukar turarruruka ya yi tare da feffeshe jikinsa da su. Nufar wardrobe ɗin shi ya yi tare da zaƙulo ƙananun kaya brown colour sannan ya sanya su. Nufar inda takalman sa suke ya yi, tare da ɗaukar canvas brown sannan ya sanya su. Bayan ya gama ya nufi inda yake ajiyan hulinanshi sannan ya ɗauki Pcap brown ya sanya. Sannan ya nufi inda yake ajiyan eye glasses ɗin shi sannan ya ɗauki daya daga cikin glasses ɗin shi wanda ke photochronic ya manna a fuskarsa. Nufar inda wrist watch ɗin sa suke ya yi tare da ɗaukar wrist watch rolex ya sanya a hannunshi. Gaba ɗaya abubuwan da sanya diamond 💎 ne.


Masha Allah kawai baki na ya furta lokacin da naga irin haɗaɗɗiyar shigar da ya yi wanda suka yi masa mugun kyau.


Ɗaukar wayarsa ya yi yayin da kai tsaye ya shiga contact list. Nan take naga ya danna kiran sunan officer. Ringing biyu haka ɗauka.


Daga ɗayan ɓangaren haka ce. "Peace be unto you Sir, hope everything is going we'll?".

Amsa ya bashi da cewa. "in sha Allah". Sannan ya ƙara da cewa. "Ina son ku haɗa mun motoci yau zan dawo Nigeria, kuma kada ka sake mahaifina ya san da cewar na dawo, wannan ya zama secret a tsakanin mu, banason maganar da muka yi da kai ya fita".

"In sha Allahu Sir ba bu wanda zai sani, baki na ƙanin ƙafata". Cewar officer ɗin.

Jin hakan ya sa Umar kashe wayar. Sannan ya nufi inda box ɗin sa yake tare da ɗaukar troley ɗinsa sannan ya fice daga cikin ɗakin.



*NIGERIA*
*. INSIDE PRISON*
"Kana tunanin zaka shigo inda nake zaune ka zagar min mahaifiya kuma na barka ka tafi?, a duniyar nan zan iya yin wasa da komai amma banda mahaifyata, tun da har ka riga da kuskura ka ambaci mahafiyata a maganar ka dole yau ka fuskanci uƙuba ta".


Zahra na kaiwa nan ta nufi inda yake.
"Zahra!". Ta ji an ambata da ƙarfi.

Tsayawa chakk zahra ta yi. Nan take kowa ya watse. Juyawa Zahra ta yi tana mai fuskantar ta.
Rass! gabanta ya faɗi.

"Zahra me ki ke shirin aikata wa?, kina shirin dukan ɗan sanda ne?, karki yi tunanin kina zaune cikin magarƙama a matsayin mara laifi kuma kiyi tunanin idan ki ka aikata ba dai-dai ba, ba za'a hukunta ki ba. Maza ki bar wajan nan kafin na ɓata miki rai". Cewar Hajiya Binta.

Ɓata rai Zahra ta yi tare da galla wa Aliyu harara sannan ta bar wajan.

Ganin hakan ya sa Aliyu ɗaukar alwashin sai ya koya wa Zahra hankali.

Juyawa ya yi tare da fice wa daga cikin magarƙamar baki ɗaya. Yana fita bai zarce ko ina ba sai gida, yayin da fuskarta kawai yake masa gizo a idanuwansa.
Yayin da ya ji tsanarta ya ɗarsu cikin zuciyarsa. Wanka ya yi tare da chanza kaya sannan ya saka kayan shi cikin box. Sai da ya ɗauke shi hour biyu yana shirya wa, kafin ya gama. Fitowa ya yi sanann ya ɗauki car key ɗin shi ya nufi parking space. Shiga cikin motan ya yi tare da tada mota sanann ya bar gidan.


Bai zarce ko ina ba sai
airport, yayin da ya karɓi passport ɗin sa tare da visa sannan ya shiga cikin jirgi.

Ɗaukar wayarsa ya yi tare da dialing number wanda ke rubuce da uncle.

Ringing biyu zuwa uku uncle nasa ya ɗaga kiran sannan ya ce. "Hello Aliyu, ka tawo?".

Amsa Aliyu ya ba shi da cewa. "A'a yanzu dai ina cikin jirgi, kuma yanzu zata ta shi. Nan da two to three hour's zamu isa America. Don haka ka kwantar da hankalin ka ina nan zuwa, yanzu dai jirgin zata ta shi zan kashe waya na sai anjima". Yana kaiwa nan ya kashe wayar.


Ajiyan zuciya Daddy ya sauke sannan ya ce. "Zainab kije ki shirya Safeera Aliyu yana nan zuwa nan bada jima wa ba, yanzu haka zanje na jira shi a filin jirgi".

Girgiza kai kawai Mom ta yi sannan ta nufi ɗakin Safeera.


Aliyu na ajiye wayar ya kashe wayar sannan ya saka seat belt. Maida kallonsa ya yi waje. Nan take idanuwansa ya sauka a kan Umar. Zaro ido ya yi waje.

Da sauri ya lalubo wayar shi. Nan take haka sanar da jirgi zai ta shi. Wata daga cikin hottest na jirgi ce ta dube shi sanan ta ce ya kashe wayar.

Ba yadda ya iya haka ya kashe wayar tare da ajiye ta. Yayin da ya ci gaba da kallon Umar wanda officer's suka zagaye shi.

Nan da nan jirgi ya tashi.
Sai da ya ɗauke su lokaci kafin su isa America.

Fitowa ya yi daga cikin jirgi yayin da suma sauran passengers ɗin suka fito.

Daga nesa ya hangi Uncle ɗin sa. Da sauri ya isa gare shi. Rungume Aliyu Daddy ya yi sannan ya ce. "Welcome my son in law".

Kunya ce ta kama Aliyu sanann ya gaishe da shi. Shiga cikin motan gaba dayansu suka yi sanann suka nufi hanyar gida.



********************
Shigar Mom cikin ɗakin Safeera keda wuya, ta tarar da Safeera ta yi kaca-kaca da ɗakin tare da fasa glasses design ɗin da haka ƙawata ɗakin da shi.

Gani Mom ta yi Safeera ta chanza shiga ta shirya tsaff. Sakar baki Mom ta yi tana kallonta.

Murmushi Safeera ta yi sannan ta ce. "Na san za kiyi mamaki Mom, na zauna nayi tunani ne, koba komai shi ɗin mahaifina ne dole nayi masa biyayya.

Murmushi Mom ta yi sannan ta ce. "Shi ya sa nake matuƙar sonki my dear".

Horn suka jiyo daga waje.
Ta shi tsake Safeera ta yi ta ce. "kije Mom zan ƙarasa shirya wa, na san sune suka ƙaraso". Ta faɗa tare da nufar inda wardrobe ɗin ta yake.

Fice wa Mom ta yi daga ɗakin. Ganin Mom ta fita daga ɗakin ya sa fuskar Safeera ya sauya daga walwalah zuwa damuwa.

Nan take ta haɗe rai sannan ta ce. "Ba zan taɓa auransa ba, domin ni ba aure nake so ba".


Shigowa su biyun suka yi ciki, yayin da ya umarci Aliyu da ya zauna. Zama Aliyu ya yi kan kujeran 1seater yayin da ya fara kallon cikin parlourn kamar wani baƙauye.

Kallonsa Daddy ya yi sannan ya ce. "Bara na kira Safeera ta kawo maka abinci".

Fitowa Mom ta yi daga cikin kitchen hannunta riƙe da plate da lemo.

Zuwa ta yi har gaban Aliyu tare da ajiye wa. Gaishe ta Aliyu ta yi yayin da Mom ta amsa sama-sama. Guri ta samu ita ma ta zauna.

Zama Daddy ya yi kan kujera tare da ƙwalla kiran sunan Safeera.


Jin Daddy na kiranta ya sata saurin saka veil a fuskarta tare da rufe gaba ki ɗaya fuskarta, sai iya ƙwayan idanuwanta kawai. Fitowa ta yi daga cikin ɗakin tare da nufar parlour ta tarar da su a zaune.

Binta gaba ki ɗaya suka yi da kallo. Cikin ɓacin rai Daddy ya kalle ta ya ce. "What's the meaning of this?, maza cire mayafin kafin ranki ya ɓace".

Girgiza kai Safeera ta yi ta ce. "Am sorry Daddy i can't".


"What! Daddy ya furta. Ganin kamar ran Daddy ya soma ɓaci ya sata fara cire mayafin a hankali daga ƙarshe ta cire bako ɗaya.


Zaro idanuwa waje Aliyu ya yi tare da miƙe wa tsaye. Cikin kiɗima ya nuna ta da yatsa hannusa da jikinsa gaba ɗaya na kakkarwa ya ce. "Kece, ta ya ya ki ka ƙaraso nan?, meya kawo ki?".


Cikin rashin fahimta gaba ɗaya suke kallonsa yayin da Daddy ya kalle shi ya ce. "Bangane ba Aliyu kayi min bayani, wannan fa ƴata ce ba wata ba". Maida kallonsa Daddy ya yi kan Safeera sannan ya ce. "Shin kin san shi ne?".


Girgiza kai Safeera ta yi baki na rawa ta ce. "ni samm ban ma taɓa ganin shi ba".

Maida kallonsa Daddy ya yi kan Aliyu sannan ya ce. "Ƴata bata taɓa zuwa Nigeria ba koda sau ɗaya, kuma ba aikin jarida take ba ko siyasa balle ka ganta a cikin tv. To a ina kuma ka santa?".


Jiri ne ya fara ɗiban Aliyu ya ce. "Ita ce muka haɗu a magarƙa..... Kafin ya idda maganar ya tafi luuu tare da faɗuwa ƙasa sumamme.






💃💃💃💃💃💃💃💃
*TOH FAH AKWAI RIKICI GABA, KOYA ZATA KAYA A GABA? MUJE DAI ZUWA. KU DAI KU CI-GABA BINA TARE DA SAMBAƊO MIN COMMENTS TA YADDA ZAN DINGA JIN DAƊIN YI MUKU SHI*💃💃💃

*KOYA HAƊUWAR ZAHRA, AMRAH DA SAFEERA ZAI KASANCE?*MUJE DAI ZUWA*

*KADA KU MANTA DA COMMENTS LIKES, AND SHARE FISABILULLAHI 🙏🙏🙏*
*_______________________*
*KUYI HAƘURI DA RASHIN UPDATE KWANA BIYU WALLAHI INA FAMA DA CIWON HANNU NE SHI YA SA*🥺🥹😢.
@@@@@@@@@@@@

ALKALAMIN ✍️
@A'ISHA M.B💞💞💞
(Zinariyar🧝♀️Jajirtattu)


Follow the 💖 A'ISHA M.B✍️ HAUSA NOVELS 📚 WORLD 🌎 📚💗💖 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g


*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐.
Daji 🌲
Magarƙama🏢 da kuma
Birni🏙️

WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝♀️Jajirtattu)


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 1️⃣3️⃣▶️1️⃣4️⃣
*_________________________________________________* Zaro idanuwa waje su Mom suka yi. Nan take suka nufi inda Aliyu ke a yashe. Ɗaukar wayarsa Dad ya yi tare da dialing number ɗan uwansa domin labarta masa abin da ke faruwa.


Ringing biyu haka ɗauki wayar. Kara wayar Dad ya yi a kannensa sannan ya ce. "Hello Yahya, akwai matsala fa, Aliyu ya zo yana ganin ƴata Safeera ya suma, kuma ban san dalilin hakan ba".


Daga ɗayan ɓangaren haka ce. "Kada ka tashi hankalin ka, haka yake da zarar ya ga wani abu ya firgita shi to suma yake kai tsaye. Don haka kada ka tashi hankalinka, zai farfaɗo. Idan ya farfaɗo ka tambaye shi me ya firgitar da shi, za ka ga ya manta domin yana da cutar mantau".



"What!", Dad ya faɗa hankali tashe. Sannan ya ƙara da cewa. "Yahya kana nufin Aliyu yana da cutar mantau?, ta ya ya hakan ta faru?, ni dai na san a yadda na san Aliyu bashi da wata cuta".


Daga dayan ɓangaren haka ce. "Ƙwarai da gaske, cutar tashi bai taɓa tashi bane a gaban ka, amma tabbas Aliyu yana da cuta tun yana yaro. Shi ya sa ma na masa yawo na turo shi domin su gana da ƴarka a ɗaura masa aure ko Allah zai sa cutar ta kau".


Girgiza kai Dad ya yi sannan ya ce. "Shi ke nen Yahya zan kira ka". Yana kaiwa nan ya katse wayan. Kallon Aliyu ya yi tare da maida kallonsa kan Safeera wacce ta yi zuru-zuru tana kallon Aliyu wanda ke a yashe a ƙasa.

Shiga kitchen Mom ta yi tare da nufar inda fridge yake. Buɗe fridge ɗin ta yi tare da ɗaukar ruwan roba mai sanyi sannan ta rufe fridge ɗin ta wuce parlour.


Tana zuwa ta buɗe murfin roban sannan ta watsa wa Aliyu ruwan a jiki. Nan take Aliyu ya buɗe idanuwansa tare da dafa kujera domin ya miƙe tsaye. Taimaka masa Dad ya yo ya miƙe sannan ya zauna a kan kujerar three seater.


Kallon shi Dad ya yo sannan ya ce. "Aliyu me ya tsorata ka game da Safeera?, shin blue eyes ɗin ta ne ya tsoratar da kai ko kuwa?".

Girgiza kai Aliyu ya yi sannan ya fara kalle-kalle. Zumbur ya miƙe tsaye yana mai fuskantar su. "Ta ya ya na zo nan wajan?, wace ce kuma Safeera".

Sakin baki gaba ɗaya suka yi suna kallonsa. Cike da mamaki Dad ya kalle sa ya ce. "Kana nufin baka san yadda ka zo nan ƙasar ba?".


Amsa Aliyu ya ba shi da cewa. "Ƙwarai ban sani ba, ni dai na san zan shiga cikin magarƙama ne amma ban san ta yadda na zo nan wajan ba, ya kamata na tafi domin ina da hayyuka a gaba na".


Jikin Dad ne ya yi sanyi. Ji ya yi kamar ya kurma ihuu saboda takaici. Cikin ransa ya ce. "Tabbas akwai matsala babba, ta ya ya zan aura wa ƴata wanda yake da cutar mantau?, tun da yanzu ya ce bai san ta ba, wata ran idan sun yi aure ma haka zai ce ba matarsa bace. Shi ke nen tun da ya manta ba zan aura masa ita ba, zan barta kawai ta ci gaba da karatun ta a Nigeria".


Dawo wa ya yi daga duniyar zancen zucin da ya shiga, sannan ya dubi Safeera ya ce. "Kada ki damu ƴata, ba zan yi miki aure yanzu ba kunji".


Murmushi Safeera ta yi tare da gyaɗa kai sannan ta shige cikin ɗakin ta.


Maida kallonsa Dad ya yi kan Aliyu sannan ya ce ya shi ke nen Aliyu za ka iya tafiya. Amma me zai hana ka bari zuwa next week muma zamu koma Nigeria da zama saboda anyi min transfer ɗin wajan aiki. Kaga sai mu koma tare, koya ka gani?".


"Shi ke nen". Kawai Aliyu ya furta. Ɗaukar jakar Aliyu Mom ta yi sannan ta yi masa rakiya izuwa ɗakin baƙi.


Safeera na shiga ɗaki kuwa, ta buga tsalle yayin da ta fara murna cewa Daddyn ta ba zai yi mata aure ba. "Shi ke nen yanzu ba bu ni ba bu auren wancan mutumin. Wayyo daɗi kashe ni, zan ci gaba da zuwa makaranta, daga ƙarshe na zama babban Barrister ko lawyer. Sai dai a ji a cikin kotu hana cewa. "Barrister Safeera can you come forward please. Nima daga nan na tashi domin kare wanda haka cuta sannan na tsaya tsayi daka domin ƙwatar wa mutane haƙƙinsu. Wow abin ya burgeni, daga ƙarshe dai zan zama Barrister". Safeera ta faɗa tana mai tiƙan rawa a cikin ɗakin.





*NIGERIA CIKIN MAGARƘAMA*

Zama Zahra ta yi a ɗakin tana mai fuskantar Hajiya Binta. Girgiza kai Hajiya Binta ta yi sannan ta ce.


"Wai me ya sa ki ke da zafin zuciya ne Zahra?, ba daman mutum ya yi miki wasa shi ke nen za ki ɗauki zafi".


Turo baki gaba Zahra ta yi sannan ta ce. "Zan iya wasa da komai amma banda mahaifiyata, a kan me ya sa zai zage ta?, dan yana matsayin ɗan sanda shi ne haka ce ba zai san bambancin dai-dai da kuma ba dai-dai ba?, wallahi da a ce baki zo ba ɗazun nan Allah da saina koya masa hankali. Ni da so samu ne Allah na bar cikin magarƙamar nan domin na gaji da zaman cikin ta, ba bu wani freedom sosai, daga aiki sai wasa sai a zo a bawa mutum abinci wanda ko akuya ta ci ba lallai ta ji daɗinsa ba". Ta ƙarashe maganar tana mai ɗora idonta a kan wani babban littafi.


Ajiyan zuciya hajiya Binta ta sauke sannan ta ce. "Ai idan har na sake na barki ki ka fita daga cikin magarƙamar nan to sai dai ba bu rai a jiki na, domin kuwa rayuwar ki yana cikin hatsari. Ba bu wanda ya san da cewa kina raye, da a ce sun san da cewa kina raye da tunan an sace ki domin ki je ki dangwala hannu a kan wasu dukiyoyi wanda yawan su ba zai misaltu ba. Yanzu dai ba lokacin wannan magana bane, ki tashi ki fita wata warder ta ce tana nemanki".


Tashi tsaye Zahra ta yi sannan ta ce. "Shi ke nen Aunty bara naje". Ta faɗa tare da fice wa daga cikin ɗakin.



******************
"Hello yallaɓai, yanzu nan nake jin labarin cewa ɗan ka Umar ya sauka a Nigeria".

Zumbur mutumin ya miƙe daga kan kujeran da yake, sannan ya ce. What!, kana nufin Umar ya shigo Nigeria?, me ya sa ku ka bari ya sauka a Nigeria bayan na faɗa muku cewa rayuwarsa tana cikin hatsari. Ɗazun nan muka gama waya da shi ya ce min wai sai next week zsi dawo Nigeria. Ta ya ya kuma yanzu za'a ce min wai ya shigo Nigeria?. Yanzu haka gurɓatattun ƴan sanda da ƴan daba neman sa suke ruwa a jallo. Saboda ya kama ɗaya daga cikin babban mai laifi wanda gaba ki ɗaya ƙasa ke nema, kuma sannan ya ƙwace ƴan mata wanda hake ƙoƙarin yin safaransu a ƙasashen waje, sannan ya yi siezing ɗin miyagun ƙwayoyin da hake shigo da su shi da abokin sa wanda yake aikin custom. Yanzu dai abin da nake so da kai shi ne, na san da cewa yana da jami'ai securities wanda ke ba shi kariya. Ina son ka tara jamiai ku dinga binsu a baya har sai sun iso gidan nan lafiya".


"Shi ke ne". Jami'in ya faɗa, daga bisani ya kashe wayar.


Tafiya motar su Umar suke a kan titin layin ɗan masara. Chan na hangi wani katafaren gida mai matuƙar kyau da tsaruwa. Tabbas kuɗaɗen sun yi kuka wajan gina wannan katafaren gidan.



horn jami'an suka yi. A take masu gadi suka fara buɗe gate . wayyo Allah wanan gidan shi hake kira aljannar duniya .


inda hake parking motoci suka nufa tare da yin parking. Kashe motocin suka yi, gba ɗaya motoci ne ya zagaye gidan kai kace wajan saida motoci ne saboda yawa. gaba ɗaya gidan zagaye yake da sojoji, inda gefe ɗaya kuma flag of nigeria ne a sama. dakuma flag na jami'ai. gaba ɗaya jami'an gidan riƙe suke da bidigogi

chan nesa kuma baban gida ne da alama ɗakin karnuka ne wato police dogs

daga gefe kuma swimming pool ne babba mai matuƙar faɗi da girma. chan gefe kuma ɗakin lantarki ne da kuma ɗakin gana wa masu laifi azaba.

cctv cameras ne kewaye a gaba ki ɗaya gidan. gidan babba ne yadda ka san gidan shugaban kasa saboda yadda ya zagaye da sojoji. Idan na ce zan tsaya gaya muku yadda gidan nan ya haɗu sai na gama page ɗin nan ina bayyana irin kyau da gidan yake da shi.

Kai tsaye cikin labari.


wasu maza uku ne sanye da kakin soja suka nufo inda suke, ɗaya daga cikin su ne ya bude side ɗin Umar tare da buɗe masa ƙofar mota sannan ya sara masa.


Ɗaga mai hannu Umar ya yi da ya dakatar da sarawan. Fitowa ya yi daga cikin motan tare da shige wa cikin gidan. Masha Allah baki na ya iya furta wa lokacin da nayi gamo da parlourn gidan. Gaba ɗaya kayan furnitures ɗin gold ne.

Biyo shi securities suka yi da box ɗin shi.


Juyawa ya yi tare da kallonsu sannan ya ce. "Ku ajiye ƴan aiki za su zo su ɗauka". Ajiye wa suka yi tare da fice wa daga parlourn.


Fitowa gaba ki ɗaya family gidan suka yi tare da yi mishi barka da zuwa. Ɗaga musu hannu kawai ya yi daga bisani ya shige part ɗin shi. Baki sake suke binshi da kallo.


Wata budurwa ce sanye da atamfa riga da siket ce ta dubi sauran ƴan uwan nata sannan ta ce. "Wai me ya sa yahya Umar yake haka ne?, kwata-kwata shi bashi da wata farha?, ya kamata a ce Abba ya yi masa magana, mu fa ƙannensa ne ba maƙiya ba". Ta ƙarashe maganar damuwa bayyane a kan fuskarta.


Ɗaya daga cikin su huɗun ne ya dube ta ya ce. "Khairiya kin san dai ba yau ne ya fara ba, tun da mahaifiyarsa ta yi hatsarin mota ts rasu shi ke nen ya chanza a gidan nan, walwala da kuma dariya shi ya guje. Abba ma bai ƙyale shi ba balle mu. Kunga ku tawo mu bar nan kafin ya fito ya tarar da mu".

Kallonsa khairiya ta yi sannan ta ce. "Allah ya bayyana wanda zata sauya Yahya Umar ya dawo yadda yake a da".

"Ameen thumma Ameen". Gaba ɗaya suka furta.


Bayan Umar ya shiga ɗakin ya shiga toilet tare da watsa ruwa. Fitowa ya yi tare da nufar ɗakin Abba, sallama riƙe a bakin shi ya shiga cikin ɗakin.



**************************
*HOSPITAL*.
Zaune take a kan kujera yayin da ta zurfafa cikin tunani, ta rasa me ke mata daɗi. Dafa ta ɗaya daga cikin nurse's ɗin ta yi ta ce. "Nurse Nadiya wai me yake damunki?, tun a kwanakin baya na fahimci cewa kina cikin damuwa, kuma a wasu lokutan idan naga kin idar sallah ina yawan ganin kina kuka kina haɗa hannayen ki guri ɗaya, kuma ni hakan ba ƙaramin kasalar min da jiki yake ba. Ya kamata a ce ki fauwala wa Allah komai Allah shi ne mai jiƙan bayinsa". Cewar nurse ɗin.


Share hawayen dake gangaro mata nurse Nadiya ta yi sannan ta dubi nurse ɗin ta ce. "Ba za ki taɓa fahimta ta ba nurse, koda a ce zan faɗa miki abin da ke ci min tuwo a ƙwarya ba za ki gane ba. Ina cikin halin tsaka mai wuya, na ɗauki alƙawari kuma ban cika ba. Ban san me zan yi ba, gaba ɗaya na ji duniyar ma ta ishe ni, ji nake kamar na mutu na huta". Ta ƙarashe maganar tare da fashe wa da kuka.

Ajiyan zuciya nurse ɗin ta sauke sannan ta ce. "Komai da ki ke gani a duniyar nan muƙaddari ne, ki ci-gaba da kai kukan ki ga ubangiji ko za ki ji sassaucin abin da ke damun ki".


"Shi ke ne". Kawai nurse Nadiya ta faɗa sannan ta ya miƙe tsaye tare da koma wa baki aikin ta.




**************************
*DAJI*
Kwance Amrah take kan jibgegen bishiya, yayin da iska mai ni'ima ke kaɗawa yana shiga kowane sashi na jikinta. Lumshe green eyes ɗinta tare da buɗe su gaba ɗaya. Kallon aku wato parrot dake kusa da ita ta yi sannan ta ce. "Shin bayan wannan duniya tawa akwai wata duniyar da ta kai wannan kyau?".

Girgiza mata kai akun ya yi. Jinjina kai Amrah ta yi sannan ta ce. "Toh indai haka ne zan so in ga ya birni yake, ni dai na san ba za ta kai duniyata kyau ba. Kuma sannan su ya halittar su take?". Ta faɗa tana mai ɗora hannunta kan haɓar ta.


Jin kururuwan dabbobi ya sa ta saurin miƙe wa daga kan bishiyar. Yayin da ta yi tsalle ɗaya ta dira daga kan bishiyan.


Gudu ta fara yi tamkar wata zakanya, yayin da ta fara bin hanyar inda take jiyo kururuwan dabbobin.


Daga chan nesa ta hango kura da dila suna faɗa a tsakaninsu yayin da suke kaiwa juna hari. Ganin hakan da Amrah ta yi ya sa ta ƙara saurin gudun nata. Ganin kura tana ƙoƙarin kaiwa dila cizo ya sa Amrah buga tsalle ɗaya tare da shiga tsakiyar su sannan ta yi musu alamu da hannu da su dakata.

Chakk suka tsaya yayin da sauran. A fusa ce ta dubi su biyun ta ce.


"Mene ne yake damun ku?, shin kun rasa tunanin ku ne?, me ya sa a koda yaushe ku ke yawan faɗa ne?, shin ba zai yu ku zauna lafiya bane?. To daga yau ku saurare ni muddin na ƙara ganin kun ƙara faɗa saina yi muku hukuncin da baku taɓa tsanmani ba sannan daga ranar ba zan ƙara kula ku ba".

Maida kallonta ta yi kan dila sannan ta ce. "Ke kuma kin san da cewa kura ya fi ƙarfin ki amma ki ke ƙoƙarin faɗa da shi, yanzu idan ku ka je ku ka illatar da kanku fa?. to ku sani cews gaba ɗaya zan ɓata muku rai idan baku daina faɗa ba". Tana kaiwa nan ta juya musu baya alamun ta yi fushi da su.


Nan take gaba ɗaya suka sunkuyar da kawunansu tare da nufar inda take. Shafa jikin ta suka fara yi yayin da suka je gaban ta tare da ɗurƙusawa, sannan suka sunkuyar da kai ƙasa alamun suna bata haƙuri.


Ganin sun sunkuyar da kai ƙasa ya sa ta nufar inda

Please Login or Register in order to submit comment