Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

KUNDIN CINIKAYYA Complete Hausa Novel Document by KUNDIN CINIKAYYA


KUNDIN CINIKAYYA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 101145



KUNDIN CINIKAYYA

Reading Time: 8 Hours

Added On: 08, May 2025

Author: Aisha MB ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 09043687746

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 521.6 kb

File Type: txt

Views: 101+

Download: 182+

Last download: 1 hour ago

Description/Story: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KhkWs8eY42GETnGLk2JC9G


*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Thre siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐.

WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝♀️Jajirtattu)


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
(We stand together)
🤝🤝🤝

*Dedicated this page to you my one and only friends Mom muwadda and Pink darling Ina sonku sosai Allah ya bar mu tare🥰😍🥰*

*Maman ihsan da sauran members na Jajirtattu ina mika gaisuwata gare ku. Na gode da haɗin kai da kuma gudunmawar da ku ka bani Allah ya ƙara haɗa kawunan mu sannan ya bamu zaman lafiya mai ɗore wa🙏*

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*

Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! Aminci ya tabbata ga shugaban fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.
Da sahabbansa da matayensa baki ɗaya.


Yau ma kamar kullum gani tafe da sabon littafi na mai suna.
*KUNDIN CINIKAYYA* wanda yake ɗauke da ilimantar wa,wa'azantar wa, kayatar wa, da kuma nishadantar wa*

Daji
Magarƙama da kuma
Birni.
Three siblings from different part of the world 🌎



*Ban yarda a chanza min littafi ta ko wace tsiga ba Koh kuma s sayar min da littafi na tare da sani na bah Koh kuma s ɗora min littafi a internet bah tareda izins bah toh idan kuwa mutum ya kuskure ya chanza min littafi, yaje na bar shi wa Allah*. *Kuma ba zan yafe masa bah*

Ban yi wannan littafin dan cin zarafin wani koh wata bah, nayi shi ne domin mutanen al'umma su amfana da darusukan dake cikin ta. Idan wannan littafin yayi dai-dai da rayuwar ka toh arashi nee


*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 1️⃣▶️2️⃣*

*________________________* *JIGAWA STATE*
*DUTSE 🪨*
*FEDERAL HIGH COURT*
*DUTSE*

*SHEKARA TA DUBU BIYU DA BIYAR *


__fitowa ta yi daga cikin Motar 'yan sanda yayin da hannayenta ke sanye da handcuf. Nan ƴan sanda suka kalle ta tare da yi mata nuni da ta yi gaba. Tafiya ta fara yi cikin kasala da fauwala wa Allah lamuranta. Ta ke mutanen wajan suka fara tofa albarkacin bakinsu a kanta yayin da suke Allah wadai da halinta. Kare ta police ɗin wajan suka shiga yi gudun kar wani a cikin jama'ar wajan ya yi ƙoƙarin illatata.

shigar da ita cikin kotu suka yi mai matukar girman gaske.

Cikin kotun ya kasance mai matuƙar faɗi gaske benci da wajan tsayawar shaida kake gani tare da kujeru, tebura, kofofi, lectern sai ƙaramin tebur don wakilin kotu kusa da benci na alkali an rufe da magatakarda kotu, sai kuma katako shinge mai raba shari'a daga gallery.



gefe guda jama'a ne da ƴan sanda yayin da lauyoyi suke tsaye tare da alkali.

Kallon su alkalin ya yi tare da basu damar zama. Zama kowanen su ya yi yayin da kotun ta yi shiru tamkar babu wani ɗan adam dake cikin ta.

Mai da kallon sa alkali ya yi kan wanda hake tuhuma yayin da ya bata umarnin da ta fito gaban kotu domin jin hukuncin da haka yanke.

Jiki a sanyaye ta miƙe tsaye tare da nufar gaban kotu tana mai fuskantar jama'an dake cikin wajan.

Magana Alkalin ya fara yi kamar haka, "A bisa hujjoji da muka yi la'akari da su, bisa dogaro da abubuwan da haka bayyana tare da ƙwaƙwarar bincike cewar Mrs Laila Abdullahi tana amfani da kamfanin ta da sunan tana taimakon talakawa bayan kuma safaran yara ta ke tare da aika mata ƙasashen waje domin yin karuwanci suna samar mata da kuɗaɗe sannan tare da miyagun ƙwayoyi da kayan maye wanda duk mun sani cewa doka ta haramta yin hakan".

" Don haka wannan kotun mai albarka ta yanke nan da sati ɗaya za'a mata hukuncin kisa ta hanyar rataya. Yana kaiwa nan. Kwamitin alkali ne suka miƙe tsaye tare faɗin. "Court".

Jin hakan ya sa kowa fita daga cikin kotun yayin da kowa ke farin ciki tare da murnan hukuncin da kotu ta yanke mata.

Fitowa Mrs Laila Abdullahi ta yi hawaye na bin kan ƙuncinta. Gefe guda kuma mutane ne a tsatsaye suna mata tofin Allah tsine.

Shigar da ita jami'ai suka yi cikin motan ƴan sanda yayin da haka nufi can prison da ita. Bayan wasu kwanaki warders suka fito da ita jikinta sanye da kayan magarƙama tare da nufar inda za'a rataye ta. Kuka sosai ta ke tamkar ranta zai fita yayin da ta ke ji ina ma ta samu koda mutum ɗaya wanda zai yarda cewa bata aikata miyagun laifukan da haka tuhume ta dasu bah.

Sai da haka kaita har inda za'a rataye ta. Nan ta ke mai zartarwa ya fito da igiya yayin da haka ɗaure igiyar a sama. Sannan haka ɗauki abin rufe fuska haka rufe mata fuska da baki. Sannan haka saka kanta saitin igiyar tana ihuu tana kururuwa.


A firgice ta farka daga mummunar mafarkin da ta ke, yayin da zufa suka fara ƙeto mata ta ko wane sashi na jikinta yayin da damuwa da tashin hankali suka bi suka tunkushe guri guda a zuciyarta na halin da ta ke ciki na rashin mai taimakon ta. Nan da nan zuciyarta ya shiga bugawa da ƙarfi-ƙarfi.

Dafe cikinta ta yi wanda ya kumburo sosai alamun cewa tana da juna biyu. Sosai taji gaba ɗaya jikinta sunyi mata nauyi yayin da ta kasa motsa koda ɗan yatsarta saboda tsananin azaba da raɗaɗi na ciwon dake tattare da ita.

Jin alamun motsin mutum daga bayanta ya sa ta sauriin waigawa. Nan ta haɗa idanu da gandirebas ɗin da ke tsaye ƙe ƙam a kanta. Ta ke zuciyarta ta ƙara faɗuwa a karo na biyu!. Don ta tabbatar cewa sun zo ne domin tafiya da ita kotu. Kallon su ta yi hawaye na bin ƙuncinta ta ce.

"Dan Allah kuyi min wata alfarma, ina son kafin ku kaini kotu a yanke min hukunci ɗaya daga cikin ku ya hara min waya na kira ƴan uwana dan Allah".

Kallon juna gandirebas ɗin suka yi yayinda ɗaya daga cikin su ya kalle ta ya ce. "Kotu bata bamu damar yin hakan bah. dan haka kada ki ce zaki yi wani yinƙuri a nan wajan idan ba haka bah zamu samu bindiga mu harbe miki kai dan haka obey the law".

Jiki a sanyaye ta miƙe. Jikinta sanye da tufafin ƴan magarƙama. Yayin da ta miƙa hannunta gaba ɗaya a cikin su ya sanya mata handcuf a hannun sannan suka fice daga cikin wajan. Bangare guda kuma sauran matan cikin Magarƙamar suka bita da kallo.

Cikin police van wato motar ƴan sanda ta shiga yayin da suka nufi kotu da ita. Tun da suka fara tafiya ta ke ta istigifari tare da salati har suka isa kotun.

Parking police suka yi. Duk idanuwan jama'a a kansu yayin da suke jiran fitowar Mrs Laila Abdullahi.

Fitowa ta yi daga cikin motar. Ba zato taji saukar dutse a kanta. Dafe kanta ta yi cikin raɗaɗi hawaye na zarya bisa fuskarta. Nan da nan mutane suka fara jifar ta da duwatsu tare da fara Allah wadai da halinta. Ganin hakan ya sa jami'ai suka shiga kare ta. Har haka shigar da ita cikin kotun.



Ƴan jarida da jama'a ne gaba ɗaya suka ƙaraɗe gaban kotun high court yayin da koh ina ƴan sanda da sojoji kake gani hannunsu riƙe da bindigogi don rike mutane a kan madafun iko.

*"Muna buƙatar adalci!muna buƙatar adalci!. Kalmomin da jama'ar wajan ke ta nanata wa kenen.

Daff da wani dattijo wasu ƴan jarida suka nufa, tare da seta mike saitin bakinsa sannan suka ce. "Bawan Allah mene ne sunanka?". Amsa dattijon ya basu da cewa.


"Sunana Namadi". Tambayar sa ƴan jaridan suka yi a karo na biyu da cewa. "Bisa wane laifi ne ku ke tuhumar wannan matar dashi, kuma me yasa kuke jifanta?".

Amsa dattijon ya fara bata kamar haka.

"Muna tuhumar ta da ƙwamushe yaran mu tana safarar su. Dukkanmu muna buƙatar wannan kotu ta yi mana adalci hakan zalunta da yaudarar mu da ta yi. Ta ɓata rayukan ƴaƴan mu mata, ta kashe mana yaran mu yayin da ta ke saka wasu yaranmu suna mata safaran miyagun ƙwayoyi. Muna tunanin ce mun samu walihiya mai share kuka da baƙin cikin mu. ashe muguwa ce shigo-shigo bah zurfi ta yi mana.Ta yi mana alƙawarin cewar zata horar da ƴaƴanmu kuma za ta ba su aiki a kamfaninta ashe ta riƙe ƴaƴan mu ne domin ta kai su wasu kasashen don samar mata da kuɗaɗe ta hanyar karuwanci.Dan haka muna son a bi mana hakkin
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download KUNDIN CINIKAYYA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album