Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba ta farin ciki. Maida kallonta ta yi kan Umar wanda ko inda take bai kalla ba saima fitowa da ya yi daga cikin mota sannan ya shiga cikin gidan.


Jan hannun Amrah su Khairiya suka yi tare da shigar da ita ciki gidan.


Suna shiga suka tadda ƙawataccen parlour mai matuƙar kyau. Zama suka yi a matuƙar gajiye. Yayin da suka miƙe suka bar Amrah a zaune tare da shiga ɗaki suka ɗauro alwala domin gabatar da sallah da ake binsu.


Bayan su gama alwalan ne suka fito daga cikin ɗakin tare da nufar inda Amrah take suka ce ta tashi ta yi alwala. Binsu kawai take sannan daga bisani ta kawar da kai daga kallonsu.


Kallon juna Khairiya da Ramlat suka yi mamaki bayyane kan fuskokin su sannan suka ƙara cewa. "Amrah ki tashi kiyi alwala mu haɗa jam'i tare. Jin shiru kamar ma bata san suna magana ba ya sanya su jan hannun ta tare da yi yi mata alwala ba dan tana so ba ta tsaya suka fara nuna mata yadda za ta yi alwala bayan sun gama ne, suka sanya mata hijabi sannan suka ɗauko sallaya daga cikin wardrobe suka shimfiɗa a ƙasa. Sannan suka tada sallah. Kamar yadda ta ga suna yi haka ita ma Amrah ta yi. Sannan ta bi bakinsu da kallo ganin bakin nasu na motsi ba tare da sanin me suke cewa ba.


Haka dai suka yi har suka idar da sallah.

Azkhar suka yi sannan Ramlat ta miƙe tsaye nufi hanyar kitchen domin dafa indomie da ƙwai.


Mintuna ƙalilan ya ɗauketa ta gama girka indomie sannan ta soya ƙwai tare da zuba su a kan indomie.


Chan kan dining ta nufa da abincin a sa'inda ta ƙwalla wa su Umar da su Khairiya kira.



Cikin ƙanƙanuwar lokaci gaba ɗaya suka bayyana a wajan. Zama Umar ya yi kan kujera dining table sannan ya ɗibi abinci sannan ya yi bissmillah ya fara ci.


Daidai wannan lokacin su Amrah da Khairiya ke fitowa. Zaunar da Amrah Khairiya ta yi kan kujera dining sannan ta zuba mata indomie ɗin tare da saka mata chokali a ciki. Maida kallonta Khairiya ta yi kan Amrah sannan ta ce. "Amrah kici wannan indomie, tunda ki ka zo gidan mu kayan marmari kawai kike sha. Bakya cin abinci, kuma ya kamata ki dinga cin abinci wanda za su ƙara miki lafiya".


Kallon abincin Amrah ta yi sannan ta kawar da idanuwanta tare da cewa. "Ni bana ci wannan ƙazamin abun"

Maida kallonsu gaba ɗaya suka yi kanta. A sa'inda Ramlat ta ce. "ke kuwa Amrah ki ɗauka kici mana".

Kallon indomie ɗin Amrah ta yi tare da buge shi gefe harta kai ga ya zube a ƙasa. Yayin da kwanon da aka zuba indomie a ciki ya fashe.


A matuƙar fusa ce Umar ya miƙe tsaye sannan ya ɗaga hannu tare da wanka mata mari.


Dafe ƙuncinta Amrah ta yi da zallar mamaki.


Mamaki ne ya kama kowanne a cikin su.


"Kinyi hauka ne?, tayaya za ki zubar da abinci bayan wasu suna chan basu samu ba?, ke naga alamun idan mutum ya biki ta lallami kike yi masa iskanci. To ki tsaya ki saurare ni ba zaki yi wannan shashanci da ni ba. Idan nace ina sonki bawai hakan yana nufin kiyi abinda kika gadama ba, dan kawai kinga ana rarrashin ki shi ne za ki dinga yi wa mutane hauka tsewwn!" ya faɗa yana mai jan tsaki sannan ya bar dining ɗin gaba ɗaya.


Ja da baya Amrah ta yi yayin da jikinta suka fara kakkarwa. Kallonta su Ramlat suka yi sannan suka shiga bata haƙuri. Da sauri Amrah ta nufi hanyar waje tare da ƙoƙarin fita daga gidan. Ganin hakan ya sa suka bi bayanta nan suka shiga dakatar da ita, amma ko sauraransu ba ta yi ba.


Da sauri Usman ya koma ciki domin sanar da Umar halin da ake ciki.


******
"Grandma wai wace ce wannan matar da nake gani a photon da Grandpa ya ce a ƙona?".


Ajiyan zuciya Grandma ta sauke sannan ta ce. "Wane hoto kenen?".


Amsa Safira ta ba ta da cewa. "Wani photo kwanaki da na taɓa gani a parlour".

Sauke ajiyan zuciya Grandma ta yi a karo na biyu. Sannan ta ce. "Kina nufin ƴata Lailah?".,


Girgiza kai Safira ta yi alamun eh sannan ta ƙara da cewa. "Tana ina ne?, ita ɗin bata da ƴaƴane ko kuwa bata nan ne?".


Amsa Grandma ta ba ta da cewa. "Lailah ko ta na raye ko ta mutu Allah ne masani, sannan maganar ƴa tabbas a shekarun baya an kawo ƴar da ta haifa a gidan yari aka kawo ta mahaifin Lailah ya yi rejecting ɗin yarinyar. A yanzu haka bamu sani ba ko tana raye ko kuma ta mutu, amma fatana shi ne idan suna raye gaba ɗaya Allah ya cigaba da kare su sannan kuma Allah ya dawo da su wannan family ɗin mu koma yadda muke a da, mu cigaba da rayuwa cikin farin ciki, shi ne kawai fatana".


Girgiza kai Safira ta yi ta ce. "Amma mene ne ta yi da har Grandpa yaƙi karɓar yarinyar ta sannan kuma ita mene ne ta aikata da har aka kaita gidan yari?".


Murmushi Grandma ta yi sannan ta ce. "Labari ne mai dogon zango ko ni kaina ban san tushen labari ba, amma ni na san da cewa Lailah ba zata taɓa aikata abinda haka ce tana yi ba domin na yarda da ita ɗari bisa ɗari, Lailah tana da kyakyawar zuciya. Tana gudanar da aikin Company tana taimaka wa talakawa marasa ƙarfi, sannan ta saka yaransu a makaranta yayin da ta buɗe gidan marayu na marasa iyaye. Duk don ta taimaka wa al'umma amma shi ne haka ƙaƙala mata sharri haka ce duk tana hakan ne saboda kuɗi".
Ta ƙarasge maganar tana mai fashe wa da kuka.


Tausayin Lailah ne ya kama Safira hakan ya sa ta ƙudiri aniyar cewa duk sanda ta zama lawyer saita wanke Lailah.








*******
"Ya ƙuri na taka ka bada sani na ba". Cewar Sooraj.


Murmushi MK ya yi sannan ya ce. "Ƙwarai na san ba da sanin ka kayi hakan ba domin hakasari ma ni ne nan wanda na sa ƙafata a wajan da zaka wuce".


Nan take fuskar Sooraj ya sauya daga walwalah zuwa ɓacin rai. "A kan me ya sa za ka saka min ƙafa a wajan tafiyata?, so ka ke na faɗi ko me?".
Cewar Sooraj


Girgiza kai MK ya yi ya ce. "A'a ko ɗaya, nayi hakan ne domin janyo hankalin ka izuwa gare ni. Shin mene ne alaƙar ka da Mrs Laila Abdullahi?".


Shiru Sooraj ya yi jin tambayar da bai san amsarta ba. Kallon mk ya yi ya ce. "Me ya sa ka ke son sanin alaqa ta da Mrs Laila, tukunan ma wane ne kai?, me ya sa ka ke bibiyar rayuwar mrs Laila da tawa?, ka faɗa min waya turo ka?".


Tashi tsaye mk ya yi daga kan kujerar da yake kai sannan ya ce. "Ni ne wannan ɗan sandan da ya taimaka wa Mrs Laila Abdullahi a shekarun baya. Na ɗauka Laila ta mutu, sai kuma daga baya na gane cewar taba raye bata mutu ba, hakan ya sani yin farin ciki, yanzu dai ina da good news da zan baka. A cikin yaran mrs Laila akwai guda ɗaya a cikin masarautar ku".


Zaro ido waje Sooraj ya yi ya ce. "Da gaske ka ke?, wace ce?".

Murmushi MK ya yi ya ce. "Ba zan faɗa maka ba kai ka gano ta da kanka, ita ma ɗaya daga cikin ma'aikatan masarautar ce. Abinda kawai zan faɗa maka kenan, na barka lafiya". Ya faɗa yana mai barin wajan.


Ruɗani Sooraj ya shiga tare da ƙoƙarin gano ko wace ce amma hakan ya cutura. Shiga cikin matarsa ya yi tare da tada wa yana mai barin harabar wajan.







*****
"Yahya Amrah na ƙoƙarin fita daga gida". Cewar Usman.

"What!". Cewar Umar, sannan ya ƙara da cewa . "Amrah kuwa, saboda me, muje na gani". Ya faɗa yana mai miƙe wa tsaye sannan suka fita suna zuwa suka tarar ta fice daga gidan.


Tarar da su Ramlat suka yi a zaune a jugun, ganin Umar ya fito ya sanya su faɗin. "Yahya Amrah ta tafi, mun bi bayanta amma bamu ganta ba".


Jin hakan ya sa hankalin Umar ya tashi, "Kamar ya baku ganta ba, muje mu nemo ta domin ba zan yafe wa kaina ba idan wani abu ya same ta". Ya faɗa suna mai shiga mota tare da barin gidan domin neman Amrah.



******
Zama Zahra ta yi tana mai bin komai na kitchen ɗin da ido nan ta shiga tunanin ta ya ya zata fara girkin. Tunani ta yi ta duba google sai kuma ta yi duba da cewa ita ɗin bata da waya.


Jungum ta yi tana mai cigaba da bin kitchen da kallo.


Daidai lokacin Gimbiya Saratu da Talatu suka shigo cikin kitchen ɗin tare da kwashe wa da dariya.


Riƙe ƙugu Gimbiya Saratu ta yi sannan ta ce. "Ya dai?, kin kasa girkin ne?, an dai ji kunya".


Kallonta Gimbiya Talatu ta yi ta ce. "Ke Zahra ko mene sunanki, kin san ba za ki iya girka ba me ya sa ki ka cinye abincin?, gashi kuma shi Sooraj ba zai barki abinda ki ka yi ya tafi a banza ba dole ne ki yi girkin nan ko kin iya ko baki iya ba".


Murmushin takaici kawai Zahra ta yi tare da girigza kai ta ce. "Ban san me ya sa mutane suke shiga abin da babu ruwansu ba, sai kutsen jaraba kamar tinkiyoyi, mutane baka shiga harkar su ba amma dole su shiga harkar ka, sun shigo da wasu ƴan matan ƙafafuwansu sun zo suna min aushi".


Kallon ta Gimbiya Saratu ta yi rai ɓace ta ce. "Da wa ki ke?, abaici ki ke ko me?, wallahi ki shiga taitayinki domin ni ba sa'ar uwar.......
Maganarta ce ta tsaya chakk sakamakon tsawar da Zahra ta daka mata. Nan take suka sha jinin jikinsu.


Kallonsu Zahra ta yi ta ce. "Kada ki kuskure ki ƙarasa wannan kalmar, da a ce kin ƙara da yau za ki san bambancin jinin sarauta da kuma jinin talaka. Ban tanka muku ba dan haka ku barni, ni zan yi kayana da kai na".


Ba tare da sun so ba haka suka fice daga cikin kitchen ɗin. Shigowa ƴan aiki suka yi domin su taya Zahra girka abincin, amma Zahra taƙi amincewa da su tayata. Ba yacce suka iya haka suka fice suka bar mata kitchen ɗin.



Ganin zama ba zai finshe ta ba, ya sanya ta miƙe wa tsaye sannan ta fara shirye-shiryen girkin.

Haka ta cigaba da girki cikin tunani, yayin da duk abin da ta gani zuba wa kawai take ba tare da sanin mene ne shi ba. Bayan nan ta yi blending ɗin kunun aya a blender sannan ta tace garin nan ta saka mai su flavour da dai sauran kayan da ba za'a rasa ba.


Haka ta cigaba da yin girkin ba tare da ta huta ba. Ba ita ta gama girkin ba sai bayan insha'i.


Zama ta yi tana mai yarfe zufan da ke ƙeto mata. "Tunda nake ban taɓa shan wahala irin ta yau ba, ba gaira ba dalili wan can banzan mutumin ya sani girkin dole, na san ma ba zai yi dad'i ba".

Ta faɗa tana mai jera abinci sannan ta fita daga cikin kitchen ɗin. Tare da nufar hanyar dining sannan ta ajiye abincin tare da fara ƙwalla wa gaba ɗayansu kira.

Cikin kankanin lokaci gaba ɗaya suka hallara daidai lokacin shima Sooraj ke fitowa daga part ɗin shi


Zama suka yi a kan dining ɗin sannan Zahra ta zuba wa Sooraj abinci domin ya ji ɗanɗanon. Ɗaukar spoon Sooraj ya yi sannan ya ci chokali ɗaya, ji ya yi abincin ya yi daɗi, amma dan kada ya nuna cewa yayi dad'i hakan ya sa ya haɗe rai. "Wannan wane irin abinci ne haka mara daɗi?, ko taste babu. Maza ku kwashe abincin nan ku kaiwa karnuka su ci".


"Ƙwarai kuwa domin mu ba zamu ci wannan ƙazamin abincin ba". Cewar su Gimbiya Saratu da su Samira.


Murmushin gefen baki Zahra ta yi, sannan ta cire ɗan kwalin kanta tare da ɗaura wa a ƙugu sannan ta rungume hannayenta a ƙirji, ta maida kallonta kan Sooraj ta ce. "Me ma kace?, a kaiwa karnuka abincin da na ɓata lokaci na wajan yinsa, kunsan hawanni nawa nayi ina girka abincin nan tare da haɗa su fruit salad da kuma kunun aya shi ne za ku ce ba za ku ci ba. Ai wallahi tallahi baku isa ba, na rantse da Allah sai kunci wannan abincin tass".


Ta faɗa tana mai nufar hanyar ƙofar parlour tare da saka wa ƙofar parlourn maƙulli sannan ta saka maƙullin a cikin aljihunta.


"Mene ne ki ke ƙoƙarin aikata wa?, wato muci wannan abincin, to ba za mu ci ba, kiyi abin da ki ka ga za ki iya". Cewar su Fasma.


Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Ashe yau za'ayi tashin balagan tsuntsaye a masarautar nan, chabb wallahi yau akwai tashin hankali a masarautar nan muddin baku zauna kun cinye abincin nan ba. Wato na gama shan ɓakar wahala shi ne za ku ce za ku kaiwa karnuka dan ma kun raina wa mutane wayo, to ku sani idan kuna yiwa kowa iskancin ku ba zaku yi min ba. Maza-maza ku fara ci dama ai kuna da hannu maza ku zuba da kanku kuci salin ali abunku ɗanoinoi".


"Ba za mu ci ba me za ki yi?". Cewar Sooraj.


Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Ohh nufin ku ba za ku ci wannan abincin ba?, haka ku ka ce ba za ku ci ba ko?, uhmm shi ke nen. Idan baku ci ta lallami ba za ku ci da ƙarfi da yaji". Ta faɗa tana mai shiga ɗakinta.


Tsayawa gaba ɗaya suka yi domin ganin me ta shiga ɗauko wa. Gani suka yi ta fito hannunta riƙe da igiya tare da turare.


Bata yi wata-wata ba ta fesa musu turaren a fuska tana mai rufe hancin ta. Nan da nan jiri ya fara ɗiban kowanensu, ganin sunyi laushi ya sa Zahra ta fara ɗaɗaure kowanensu da igiya tana mai faɗin. "Ƴan kutumur kitabi dangin gajeru kawai, wai nayi girki suce ba za su ci ba, kun ma isa, chabb da Zahra ku ke zancen wallahi da kaina zan ɗurka muku abincin har sai kun cinye tass".


Haka ta cigaba da ɗaɗɗaure su ba tare da gajiya ba. Duk abinda ake yi Mami ba ta sani ba domin kuwa tana chan part ɗin sarki.


Zahra kuwa ɗauri ta yi musu kamar ta samu akuyoyi. Bayan ta gama ta miƙe tare da ɗaukar abincin ta sauko da su ƙasa.


Zuba mai mugun yawa ta yi cikin plate sannan ta kai dubanta kan gaba ɗayansu ta ce. "Ni kuma ta kanwa zan fara ɗura wa wannan abincin?, yauwa Samiran nan zan fara tura wa dan naga tafi dogon baki a cikin su". Ta faɗa tana mai zuwa inda Samira take sannan ta lanƙwasar da kan Samira tamkar za ta ɗura wa yaro magani haka Zahra ta shiga ɗura wa Samira abincin nan ba tare da gaggauta wa ba.


Dariya Zahra ta fashe da shi ganin yadda gaba ɗayansu suka ƙwalalo da idanuwa waje. "Shashanci banza kawai, aka ce bakua ji ashe gani ne bakua yi. Wallahi duk saina saita muku zama a gidan nan, marasa mutunci kawai. Su Sooraj kuwa suna ganin komai saidai jikinsu ba zai yi motsi ba balle su dakatar da ita domin kuwa turaren da Zahra ta ɗauko ba normal turare ba ne.


Haka ta shiga ɗura musu abincin da shi da su kunun aya tare da tuwon shinkafa. Tana ɗura musu abincin tana raira waƙa. "Hayya ra'iye alagidibo, yara sai dai kallo amma ba'a isa aiwatar da komai ba".

Ɓangaren Sooraj kuwa hayyana wa yake irin rashin mutuncin da zai yi wa Zahra idan ya dawo cikin hankalinsa.








ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
(Zinariyar Jajirtattu)
.
*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part of the world)*🪐🌎🪐.
Daji 🌲
Magarƙama🏢 da kuma
Birni🏙️

WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝♀️Jajirtattu)


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
(We stand together)
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 4️⃣5️⃣▶️4️⃣6️⃣
*___________________________________________*
Haka Zahra ta shiga ɗura wa kowanensu abinci har saita da ta kai kan Sooraj.


Tsayawa ta yi tare da zuba masa idanuwa sannan ta ce. "Kaine babba ko?, harda wani cewa, kiyi maza-maza ki kije ki girka abincin nan, sannan na gama ka ce wani a kaiwa karnuka saboda ka raina min hankali, to kai ma saikaci domin naka ma yafi yawa ka ganshi ko, ta faɗa tana mai nuna ƙaton kula wanda ya cika da abinci. Maida kallonta ta yi kansa ta ce. "To sai ka cinye abincin nan tass in faɗa maka gaskiya". Ta faɗa tana mai ɗaukar chokali sannan ta ɗibi abincin ta kai bakin sa. Ganin ya matse bakinsa yaƙi buɗe wa ya sanya ta kama fuskarsa tare da buɗe bakin nasa da ƙarfi sannan ta cusa chokalin ciki. Haka ta shiga ɗura mai abinci har na kulan ya ƙare.



Tashi tsaye Zahra ta yi tare da karkaɗe jikinta ta ce. "Ƴan banza kawai wato ku nan ƴan sarauta ko?, ko banza dai kunci abincin". Ta faɗa daidai lokacin da Mami ke fitowa daga ɗakin ta.


"Ya subha'anallahi!". Kalmar da ta fara zuwa bakin Mami kenen.


Kallon Zahra Mami ta yi ta ce. "Zahra wane ne ya yi musu haka?, ji fa yadda aka ɗaɗɗaure su kamar wasu akuyoyi, mene ne abin da ya faru?".


Kallon Mami Zahra ta yi ta ce. "Yauwa Mami barka da ƙarasowa". Ta faɗa tana mai zuwa kusa da Mami sannan ta kalleta ta ce. "Kin san mene ne suka aikata?".


Girgiza kai Mami ta yi alamun A'a.


Maida kallonta Zahra ta yi kan su sannan ta ce. "Kina ji ba, Yarima Sooraj ba ya ce saina ƙara girka wannan abincin da na cinye ba, to wai bayan na gama ɓata lokaci na nasha wahala sannan na kawo musu, wai da suka zo wai yarima Sooraj ya ce wai a kaiwa karnuka su cinye. Ni kuma na ce idan na yarda mai tatsine ya dawo duniya, na ce suci suka ce ba za su ci ba. Ni kuma da naga aka na je na ɗauko wani turare na kashe jiki a ɗaki nima ban san turaren na mene ne ba, na fesa musu sannan na ɗaɗɗaure su kana na basu abincin da kaina, shi ke nen fa".


Salati Mami ta rafta tana mai faɗin. "Zahra kin kashe ni, Sooraj fa yana da cutar Asma kuma chronic ne, bai kamata a ce kinyi musu haka ba, domin kuwa ke ƴar aiki ce kawai, ya kamata a ce kina iya sarrafa fushin ki a wasu lokuta".



Ƙunce su Mami ta fara yi yayin da ita ma Zahra ta saka hannu suka kunce su tare.


Saida suka shafe kusan hawa guda ba tare da wani a cikin su ya dawo cikin hayyacin sa ba. Bayan wasu mintuna suka fara dawo wa cikin hayyacin su , yayin da suka shiga amai.


Gaba ɗaya babu wanda bai farfaɗo ba sai dai Sooraj wanda har izuwa wannan lokacin bai farfaɗo ba.


Hankalin Mami ba ƙaramin tashi ya yi ba ganin Sooraj bai farfaɗo ba. Ɓangaren Zahra ma gaba ɗaya hankalinta ya tashi yayin da take tsoron kada ta je ta kashe ɗan mutane.





******
Bayan Umar yaji labarin cewa Amrah ta tafi ya sa hankalin shi ya tashi. Yayin da suka bazama nemanta amma hakan ya cutura.


A sa'inda Umar ya kira jami'ansa domin su zagaye gaba ɗaya garin Kano dan a nemo ta.




Ɓangaren Amrah kuwa, bayan fitar ta daga ciki gidan ta fara tafiya ba tare da ta san inda take sanya kafafuwanta ba. Babu zato ta ga wasu motoci sun zagaye ta. Nan wasu mutane suka fito fuskokin su rufe da mask. Ba ta yi aune ba ta ji sun shaƙa mata wani abu. Take jiri ya ɗibe ta yayin da bacci mai nauyi ya kwashe ta.


Shigar da ita suka yi cikin motan sannan suka bar harabar wajan da ita.








*******
Tun ana ɓoye wa har labari ya garzayo kunnen sarki. Nan haka wuce da Sooraj asibiti yayin da aka shiga bashi taimakon gaggawa.


Gaba ki ɗaya hankalin Sarki da na Mami ya tashi. Yayin da ɓangaren Zahra take ta faman addu'a Allah ya sa bai mutu ba.


Nan dai likitoci suka yi nasarar dawo da numfashin sa, saida Sooraj ya kwashe kwana biyu a asibiti ana duban lafiyar sa. Kafin daga bisani aka sallamo shi daga asibiti.


Gaba ki ɗaya jikin ƴan gidan ya mutu yayin da suka kasa furta komai, tare da ganin duk laifin Zahra ne da a ce ba ta yi abin da ta yi ba da hakan ba ta faru da shi ba.


Zama gaba ɗaya suka yi a parlour, yayin da Zahra durƙushe gwiwowinta a ƙasa ta duƙar da kai ƙasa.


Kallonta Gimbiya Talatu ta yi ta ce. "Kinga abin da ki ka aikata ko?, yanzu da a ce daga nan ya mutu mene ne za ki ce?, kin san da a ce ya mutu kema rataye ki za'a yi?, wannan wane irin shashanci ne da almubazarancu".



Kallon Sooraj Zahra ta yi nan take taji nadamar abinda ta aikata. Duƙar da kai ƙasa ta yi ta ce. "Ina mai baku haƙuri gaba ɗaya, banyi hakan ba dan wata manufa a zuciyata ba, nayi hakan ne dan kawai na saku kuci wannan abincin amma bawai nayi hakan ba da nufi cutarwa. Idan duk na ɓata muku rai kuyi haƙuri ba zan sake ba".


"Babu wani ba za ki sake ba, kawai mafita shi ne ki tattara komai naki ki bar wannan masarautar". Cewar Gimbiya Saratu.


Ɗaga musu hannu Sooraj ya yi ya ce. "A'a, ba zata je ko ina ba, bazan bari ta tafi haka nan ba, dole ita ma ta ɗanɗana kuɗarta, tunda harta iys ɗora hannayenta a kanmu to ba zata tafi kuma a ƙyale ta ba".



Kallonsa Mami ta yi ta ce. "Amma Sooraj ya kamata kayi nazari, ta riga ta baku haƙuri, ni kawai zan sallame ta tafi".


Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "A'a Mami, da a ce na mutu haka za ki ce a rabu da ita?, bazan bar abinda ta aikata ba, wallahi saina gana mata azaba a masarautar nan, saina sa ta gwammaci mutuwa da rayuwa". Ya ƙarashe maganar tare miƙe wa tsaye sannan ya nufi part ɗin sa.



Maida kallonta Mami ta yi kan Zahra ta ce. "Zahra tashi ki shiga ɗaki kinji".



Girgiza kai kawai Zahra ta yi sannan ta miƙe tsaye tare da nufar ɗakinta. Binta kawai su Samira suka yi da kallo, yayin da suke hayyana irin muguntar da za su yi mata.


Zahra na shiga ɗaki kuwa ta faɗa kan gadonta tana mai sauke ajiyan zuciya sannan ta miƙe zaune ta ce. "Wai me yake nufi?, yana nufin zai azabtar da ni?, dan ma ya samu na bashi haƙuri shi ne zai dinga fadar waɗan nan maganganun, to wallahi daidai da kai aikin banza kawai". Ta faɗa tana mai buga tsaki.




*****
"Hello Please am I talking to Safira Ibrahim?".


Girgiza kai Safira ta yi kamar tana gaban mai maganar a waya sannan ta ce. "Yes of course, please how may I help you?".

Daga ɗayan ɓangaren aka ce."The law school you applied to has accepted you, now you just need to start, but before that, today we need you to come in for signing so that we can verify your details. They will come to pick you up at home, and don't worry about receiving a visa or passport because everything has been completed. We are just waiting for you."


Miƙe wa zumbur Safira ta yi cike da farin ciki ta ce". Wow!, thank you so much, I can't even describe how happy I am. Very soon, I'll be heading to America." Ta faɗa tana mai katse wayar.



Da sauri ta fita parlour ciki sa'a ta tarar da su Mom a parlour, nan ta sanar musu abin da ya faru. Babu wanda bai yi farin ciki ba amma Mom samm ba ta so hakan ba domin ba ta som ta yi nisa da ƴarta.


A gurguje Safira ta koma ɗaki kana ta shirya kanta da kayanta. Bayan ta gama shirya kayanta a travelling box.

Please Login or Register in order to submit comment