Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ke fita daga kan wannan Samira kamar mutacce alade. Chabb ashe duk gayun da iyayin na banza ne tun da ba'a iya tsaftace jiki".


Node Kai su ukun suka yi kana suka ce. "Za ki san mu ki ka taɓa wallahi yau kin taɓo wa kanki bala'i, kuma za ki gani". Suka faɗa tare da fita daga cikin ɗakin.



Duban su Zahra ta yi ta ce. "Zan ga alkhairy ba tsiyar ku ba, shegun yara kawai".


Su Samira na fita kuwa suka je suka sanar da su Gimbiya Saratu da Talatu duk abubuwan da Zahra ta yi musu. Nan take gaba ɗaya suka miƙe tsaye yayin da suka nufi kitchen daga mai ɗaukar wuƙa saime ɗaukar chokali. Yayin da su Yusrah kuma suka ɗauki wayar chaza suka nufi ɗakin Mami.




"Ke Zahra, nan fa ba kamar gidan ku ba ne, za su ya cutar da lafiyar ki ni kuma ba zan bari hakan ta faru ba, tun da ki ka ji sun ce za ki gani to sun tafi ne su haɗa dabar su za su iya cutar da ke, ya kamata ki bar masarautar nan yanzu".
Cewar Mami.


Murmushi Zahra ta yi kana ta ce. "Mami ki barsu su zo dai-dai nake da kowaccen su, nayi da wanda yafi su ma balle su ƙananun tantirai. Jira nake su ƙaraso a nan za su tabbatar da cewa Allah ɗaya ne, domin duk saina koya musu hankali".


Ta faɗa tana mai hango dorina a ajiye kan table. Da sauri ta nufi in da dorinan take tare da ɗauka ta riƙe a hannunta tana mai jiran shigowar su Samira.



********************
💃💃💃💃💃💃💃💃
*KAI ZAHRA KINA ƘAMSHI MUNA BINKI DA UMRAH, INA YINKI OVER😂, MA ZA KIYI MANA MAGANIN SU. SU SAMIRA JIKIN KU ZAI FAƊA MUKU DOMIN ZAHRA BA ABAR RAINA WA BACE. ALIYU DA KUMA UMAR FA SUN RIKICE, SUN KASA GANE SAFEERA DA AMRAH. KOYA ZA TA KASANCE MUJE DAI ZUWA💃💃💃.*


*KADA KU MANTA DA LIKING, SHARING DA KUMA COMMENTS FISABILILLAH🌹🫠🫠🥰💞*


ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝♀️Jajirtattu)


Follow the 🌺🌎A'ISHA M.B🌹 HAUSA NOVELS 📚 WORLD 🌎 📚💗💖 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g










https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 3️⃣3️⃣▶️3️⃣4️⃣
*_________________________________________________*
Saida su Gimbiya Saratu suka zo dai-dai lokacin da za su shiga part ɗin Mami ne suka ci karo da Junaid.

Shan gabansu Junaid ya yi sannan ya dube su ya ce. "Mene ne ku ke shirin yi haka?". Maida kallonsa ya yi kan Gimbiya Saratu sannan ya ce. "Ammi what's going on?, kar dai wajan Mami za ku je?".


Kallonsa Gimbiya Saratu ta yi ta ce. "Koma wajan ta zamu je ina ruwan ka?, maza ka bamu hanya mu shiga. Har ma ta kai da har za ta kawo wata ƴar aiki cikin fadan nan kuma ta saka ƴar aikinta ta ɗaga hannu ta mari Samira saboda ta cika tangararriyar ƴar iska".


Fashe wa da kuka Samira ta yi ta ce. "Wallahi yahya kome za ka yi ba zan rabu da ita ba, ɗaga hannu da ta yi ta mare ni kawai ka bamu hanya mu shiga don wallahi saina yi mata tsinannen duka".


Sauke ajiyan zuciya Junaid ya yi sannan ya ce. "Kun san dai mai martaba yana nan. Kuma idan har ya ji abin da ku ke shirin aikata wa to ran mu ne gaba ɗaya zai ɓaci. Hanyar zaman lafiya a bita da shekara. Yanzu me ku ke so ita ƴar aikin ta yi muku?".


Amsa Gimbiya Talatu ta bashi da cewa. "In dai tana so mu rabu da ita to dole ne ta zo ta durƙusawa har ƙasan gwiwowinta ta bawa Samira haƙuri kuma bayan nan za ta wanke musu kayan su. Wannan shi ne". Ta ƙarashe maganar hannunta riƙe da ƙugunta



Furzar da iska Junaid ya yi waje, sannan ya dube su ya ce. "Shi ke nen kuje ku zauna a parlour zan kira ta za ta zo ta baku haƙuri gaba ɗaya har da ma ita Samiran".


Ya faɗa yana mai shige wa part ɗin Mami sallama riƙe a bakin sa.


Su Gimbiya Saratu kuwa jin abin da Junaid ya faɗa ya sanya suka koma parlour tare da zaman jiran fitowar Zahra.


Ƙarasawa ciki Junaid ya yo yayin da Zahra ta bishi da kallo. Murmushi Mami ta yi ta ce. "Junaid kaine a wannan lokacin".


Cikin jim kunya ya ce. "Eh Mami ni ne". Ya faɗa yana mai maida kallonsa kan Zahra.


Mamaki ne ya kama shi ganin dorina kan hannun Zahra.


Baki sake ya bita da kallo sannan ya ce. "ke kuma me ki ke da dorina?, me za ki yi da shi?".


Kallonsa Zahra ta yi sannan ta bashi amsa da cewa. "Zan daki ƙannen ka da shi ne, ko za ka rama musu?".


Kawar da kai Junaid ya yi gefe cikin jin haushin furucinta ya ce. "Ki fito babban parlour yanzu nan ko kuma ranki ya ɓaci". Yana kaiwa nan ya fice ya bar musu ɗakin.



Dogon tsaki Zahra ta ja sannan ta ce. "Aikin banza, ni gaba ɗaya ma zaman magarƙamar ma ya fi ƴanci a kan nan wajan".


Binta da kallo Mami ta yi ta ce. "Kije Zahra zai iya yiwu wa sun kai ƙarar ki wajan mai martaba".


Zama Zahra ta yi kan kujera ta ce. "Ni babu in da zani ina nan tare da ke".


Girgiza kai Mami ta yi ta ce. "Zahra kiyi haƙuri ki tashi ki je ko kuma mu je tare kinji ni".


"Shi ke nen Mami zanje ne kawai saboda ke, amma da ba dan haka ba babu abin da zai sa na ɗau ƴan matan ƙafafuwa na naje wajan su".


Ta faɗa tana mai miƙe wa tsaye sannan ta fita daga cikin ɗakin. Ganin hakan ya sa ita ma Mami ta bin bayan Zahra.






***********************
Cikin rashin fahimta Safeera ta dubi Umar ta ce. "I don't understand what you are talking about, wace ce kuma mai green eyes?, ni a ina na sanka ma da za ka ce wai ni mai green eyes?. Kodai kana imagination ne?, ya kamata ka je asibiti a duba ka".


Ta faɗa tare da juya wa ta yi tafiyar ta.


Baki sake Umar ya bita da kallo sannan ya ji zuciyar shi nayi masa zugi. Baiyi aune ba ya ga Safeera ta ɓa ce masa daga gani.


Ɓangaren Aliyu kuwa gaba ɗaya ya rasa me ke masa daɗi yayin da ya rasa me zai yi domin tabbatar da cewa wannan Safeera ce ko ba ita ba ce. Yana tsaka da tunani ne kwatsam ya ji wayarsa ta fara ringing.


Nan hankalin sa ya ɗauke daga kan Amrah izuwa wayarsa. Ɗaukar wayar sa ya yi ganin sunan wanda ke bayyane kan screen ɗin wayar ya sa shi saurin ɗaga wayar.



Juya wa Amrah ta yi tare da barin wajan sannan ta nufi ɗayan sashen da Umar yake. Dai-dai lokacin da Safeera ke yowa wajan. Kai tsaye in da Aliyu yake ta nufa ba tare da sun haɗu da Amrah ba.




"Hello your excellence fatan komai lafiya".
Cewar Aliyu wanda waya ke maƙale kan kunnensa alamun yana waya.


Daga ɗayan ɓangaren Gov. Musa Muhammad ya ce. "Aliyu ina so kayi min wani aiki".


"Okay". Aliyu ya ce yana mai jiran mai Gov. Musa zai fada masa.


Magana Gov. Musa ya fara yi kamar haka. "Ina son ka bincika min wane ne ya kuɓutar da Lailah harta gudu daga asibiti a wannan lokacin".


Cikin rashin fahimta Aliyu ya ce. "Ban fahimci me ka ke faɗa ba yallaɓai, kamar ya na bincika waye ya taimaka mata. Ita ɗin fa ta riga da ta bar wannan duniya, kuma ko ba komai ita ɗin kamar ƴar uwa take a waje na ko kuma na ce tamkar uwa take a waje na a kan me ya sa za ka ce na bincika waye ya taimaka mata. Gaskiya ba zan iya yin wannan aikin ba sai dai ka saka wani ya yi maka". Yana kaiwa nan ya katse wayar.



Ɓangaren Gov. Musa Muhammad kuwa idan ranshi ya kai dubu to ya ɓaci!, cikin hassala ya ce. "Lallai ma aliyu, mun daɗe cikin harkar nan tare da kai shi ne kuma yanzu ka ke ƙoƙarin juya min baya na san ta yadda zan ɓullo maka".


Kiran wasu daga cikin body guards ɗinsa ya yi tare da faɗa musu cewa su binciko wacce ta taimaka wa Laila ta gudu a asibiti.



Kamar yadda ya umarce su haka suka fice suka fara yawo a gari domin neman wace ce ta taimaka wa mrs Laila Abdullahi.



***************
Bayan Aliyu ya sauke wayan ne ya ci karo da Safeera a tsaye sai binshi da idanuwa take.


Binta ya yi da kallo sannan ya ce. "Wato yanzu ma kin kuma sauya shiga kenen kuma ƙwayar idanunki kin mayar da su yadda suke da sannu da ƙokari kinji".


Cikin rashin fahimta Safira ta dube shi ta ce. "Ni fa ban gane abin da ka ke magana a kai ba".


"Koma dai mene ne ke ki ka sani, maza tawo mu tafi idan kuma baki gama ba ni na tafi na barki a nan". Ya ƙarashe maganar yana mai fice wa daga wajan. Ganin yana ƙoƙarin ya tafi ya barta ne ya sa ta yi saurin bin bayansa.


Suna isa waje suka tadda jami'ai zagaye ta ko ina. Mamaki ne ya kama su. Simi-simi Aliyu ya nufi in da ya ajiye motar sa tare da shiga ciki nan ita ma Safeera ta shiga cikin mota. Tada mota Aliyu ya yi sannan suka bar harabar wajan.




Ɓangaren Amrah kuwa kai tsaye wajan Umar ta nufa. Nan Umar ya shiga binta da kallo yayin da ya rasa a mafarki yake ko zahiri. Ya shiga cikin ruɗani. Su Khairiya kuwa bayan sun gama siyayya ne suka nufi wajan su Umar.


Kallon Umar suka yi ganin gaba ki ɗaya yanayin shi ya chanza ya sa Ramlat faɗin. "Yahya meya faru?". Ta faɗa da alamar tambaya.


Girgiza kai kawai Umar ya yi sannan ya ce. "Babu komai mu tafi". Ya faɗa yana mai jan hannun Amrah suka fice daga cikin wajan.

Nan ya ga jami'an da ya kira har sun iso harabar wajan. Sara masa jami'an suka shiga yi a sa'inda suka buɗe musu kofofin mota suka shiga. Gaba ɗaya yanayin Umar ya sauya ba kamar yadda suka sanshi ba. Binsa da kallo kawai Amrah ke yi ganin dan murmushin nan da yake mata baya yi hakan ya sa ta cikin wani irin yanayi na damuwa.


Tada mota jami'ai suka yi tare da barin wajan baji ɗaya.





*****************
Zahra da Mami na fita kuwa suka tarar da ƴan aiki tare da su Gimbiya Saratu da Talatu tare da su Samira a zazzau ne gaba ɗaya sun ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya.


Ƙarasawa wajan su Zahra ta yi sannan ta ce. "Gani na zo me ya faru?". Ta faɗa idanunta a kan Junaid.

Sauke ajiyan zuciya Junaid ya sauke!, kana ya ce. "Maza ki durƙusa ki bawa Samira haƙuri tare da sauran domin yin hakan ne kaɗai zai sa ki zauna lafiya a cikin masarautar nan".


Jin maganar Zahra ta yi tamkar saukar aradu. Ƙasa da kai ta yi yayin da ta ji wani zuciyan ya ce mata kawai ta bawa Gimbiya Saratu da Talatu haƙuri domin a haifa sun haife ta.


Dubansu ta yi kana ta ce. "Shi ke nen tun da abin da ku ke buƙata kenen zan yi. Amma Gimbiya Saratu da Talatu kawai zan bawa haƙuri Samira kuwa laifi ta yi don haka ba zan iya ba ta haƙuri ba".


Miƙe wa tsaye Gimbiya Talatu ta yi sannan ta ce. "To idan ba za ki iya ba ta haƙuri ba muma bamua da buƙatar haƙurin ki, in dai kina son mu yafe miki kuma keda wannan matsiyaciyar Mamin ku zauna lafiya cikin fadan nan to dole sai Mami ta durƙusa har ƙasa ta bawa Samira haƙuri".


Nan take jinin Zahra ya fara tafarfasa yayin da ta ji wani irin ɓacin rai ya ziyarce ta. Nan take ta dubi Gimbiya Talatu ta ce. "A kan me ya sa za ta ba ta haƙuri?, ni ce da laifi ba ita ba, kuma ita ta kawo ni masarauta nan ba ku ba, ya kamata ku san irin furucin da za ku dinga furta wa domin ita ɗin ba sa'ar ku ba ce ba".



Duban Zahra Mami ta yi sannan ta ce. "Aba ke kuwa Zahra wannan ba shi ba ne karo na farko da zan fara basu haƙuri ba wannan abu mai sauki ne. Ki bari kawai na ba ta haƙuri ". Ta faɗa hawaye na gangaro wa kan fuskarta yayin da ta fara yinƙurin durƙusa wa kan gwiwowinta.



Da sauri Zahra ta riƙe ta sannan ta ce. "Aba Mami, sai dai idan bani da rai shi ne kawai zan barki ki durƙusa a wajan nan amma muddin da numfashi na to babu abin da zai sa ki durƙusa mata".


Maida kallonta ta yi kansu sannan ta ce. "Na san Mai martaba bai san duk abin da ku ke yiwa Mami ba to a yau duk zan tona muku asiri domin saina faɗa masa komai". Ta faɗa tana mai yinƙurin fita.


Take suka ci karo da mai martaba a hanyar ta na fita. Hamdala Zahra ta yi kana ta ce. "Mai martaba dama ina so na faɗa maka abu ne sai kuma gashi Allah ya kawo ka, dama.......


Zahra ba ya kai ga ta idda maganarta ba suka ji Gimbiya Saratu da Talatu sun fashe da kuka.


Maida kallonsa Mai martaba ya yi kansu Gimbiya Saratu sannan ya ce. "Me ya faru?".


Cikin kuka Gimbiya Talatu ta ce. "Mai martaba uwar gidan ka ce ta kawo sabuwar ƴar aiki take yi mana rashin kunya harda zagin uwata. Sannan kuma uwar gidan ka ta saka ƴar aiki ta mari Samira sannan kuma ta zage mu".


Zaro idanuwa waje Zahra ta yi tana mai faɗin. "Innalilahi wa innahilahir rajihun, wannan wane irin sharri ne, ku sani cewa ramin ƙarya ƙurarre ne".


Kallon Mami Kai martaba ya yi sannan ya ce. "A'isha maganar su Talatu gaskiya ne?".


Sunkuyar da kai Mami ta yi hawaye na sauka kan fuskar ta. Kallonta mai martaba ya sake yi a karo na biyu sannan ya ce. "A'isha da ke nake fa, na ce maganar su Talatu gaskiya ne ko ƙarya?".


Girgiza kai Mami ta yi tare da share hawayenta sannan ta ce. "Eh gaskiya ne".


Kallon juna Gimbiya Saratu da Talatu suka yi tare da sakin murmushin mugunta.


Kallon Mami Zahra ta yi kana ta ce. "Aba Mami me ya sa za ki ɗora laifin da ba naki ba a kanki?, me ya sa za ki amsa abin da ki ka san baki yi ba? ta ya ya za ki ce da gaske ne bayan kuma sam ba haka ba ne ba".



"Yi min shiru!!". Mai martaba ya faɗa a matuƙar tsawa ce.


Shiru Zahra ta yi tana mai maida kanta gefe tare da dunƙule hannunta na dama kana ta cije leɓenta cikin tsananin ɓacin rai da zafin zuciya.


Kallon kowanensu mai martaba ya yi sannan ya maida kallonsa kan Mami ya ce. "Na yarda da ke A'isha na san ba za ki iya aikata abin da suka faɗa ba, don haka ki koma part ɗin ki".


Nan take farin ciki ya ziyarci zuciyar Zahra. Jiki a sanyaye Mami ta koma part ɗin ta.



Maida kallonsa mai martaba ya yi kan Zahra sannan ya ce. "Ke kuma, tun da ki ka iya ɗora hannunki kan Samira kuma ki ka iya zagin gimbiyoyi dole ki fuskanci hukunci. Don haka hukuncin shi ne dole ki dinga share gaba ki ɗaya masarautar nan har na tsawon sati ɗaya".


Zaro idanuwa waje Zahra ta yi jin abin da Mai martaba ya faɗa.

Nan take Zahra ta durƙusa kan gwiwowinta sannan ta sunkuyar da kanta ƙasa ta ce. "Ranka shi daɗe ka gafarce ni, dan Allah na yarda ayi min wani hukuncin amma banda wannan, na san kai ɗin mai tausayi ne kuma mai fahimta. Don Allah a sassauta min".


Jin hakan ya sa Mai martaba kallonta sannan ya ce. "Shi ke nen zan sassauta miki. Sassaucin kuwa shi ne dole idan ɗana na fari wato Sooraj ya dawo daga ƙasar da ya je to ya zama wajibi ki dinga masa aiki, kama da share-share, aiki da dai sauransu duk ke ce za ki dinga yi masa har na tsawon lokacin da ki ka ga za ki bar wannan masarauta".


Jin hakan ya sa Zahra ta yi wa mai martaba godiya da irin wannan hukuncin da ya yanke.


Kallonta mai martaba ya kuma yi a karo na biyu sannan ya ce. "Akwai wani ajiyayyen ɗakin sa daga yau nake so ki fara aikin maƙullin yana hannun Junaid shi zai baki". Yana kaiwa nan ya fice daga wajan.



Tashi tsaye Zahra ta yi tare da karkaɗe jikinta sannan ta ce. "To me kuma ya rage ko duka na za ku yi?".


Ta faɗa tana mai kallon su Gimbiya Saratu.


Idan ransu Gimbiya Saratu ya kai dubu to ya ɓaci. Miƙe wa tsaye suka yi sannan suka bar cikin babban parlourn.


Kallon Junaid Zahra ta yi sannan ta ce. "Malam Junaidu ina muƙullin yake?".


Galla mata harara Junaid ya yi sannan ya ba ta amsa da cewa. "Muƙullin ba yana hannun ki ba, shi ne ai ki ka ɗauke a cikin aljihu na".


"Ohh to ai ban sani ba, shi ke nen sai a nuna min ɗakin ko, na je na fara aiki na tun yanzu".


Nuna mata hanyar ɗakin Junaid ya yi sannan ya ce. "Wan can shi ne ɗakin". Ya faɗa yana mai wuce wa part ɗin sa.



Taɓe baki Zahra ta yi ta ce. "Duk saina koya muku hankali, ƴan iskan yara kawai, gaba ɗaya yaran gidan nan an lalata su da sangarci". Ta faɗa tana mai nufar in da Junaid ya nuna mata.



Tana zuwa ƙofar ɗakin ta ɗauki muƙullin sannan ta saka a bakin ƙofan. Nan take ta ga ƙofar ya fara ƙoƙarin buɗe wa. Ba ta yi aune ba ta ga ƙofar ya fito da thumbprint wanda dole mamallakin shi ne kawai zai iya saka hannu ya buɗe wajan.


Sauke ajiyan zuciya Zahra ta yi sannan ta ce. "Ikon Allah sai ka ce ɗakin sirri da har za'a saka masa password, to ni kam mene ne password ɗin ƙofar nan?, ko na ce hannun waye za'a saka kuma ya buɗe". Haka ta shiga yin magana ita ɗaya ba tare da ta san mene ne abun yi ba.



Nan take tunanin mahaifiyarta ya faɗo mata. "Allah sarki Allah ya jiƙan ki Mamata duda ban taɓa ganinki ba amma ina jin sonki a cikin zuciyata Mrs Laila".


Ta faɗa tana mai rubuta Mrs Laila a jikin in da haka saka enter password. Da mamakin ta kuwa ta ga ƙofar ya buɗe.


Zaro idanuwa waje Zahra ta yi ta ce. "Laaaa!, lallai na yarda babu in da Allah baya ikon sa. Daga rubuta sunan uwata gaskiya nayi farin ciki sosai ashe soyayyar da nake wa uwata na gaskiya ne ba ƙarya ba".

Nan take ta ƙarajin son mahaifiyar ta yana ƙara ninkuwa cikin zuciyarta. Ba tare da dogon tunani ba ta ƙusa kai cikin ɗakin.


Gaba ki ɗaya ɗakin cike yake da ƙura tare da datti, sai ajiyayyun takaddu tare da akwatina tare da hotuna.


Sakin baki kawai Zahra ta yi tana mai cigaba da bin ɗakin da kallo.


Ɗaya daga cikin ajiyayyun hotunan Zahra ta ɗauka tare da goge wa da mayafin jikin ta. Rass! gabanta ya faɗi!, nan take ta saki hoton ya faɗi ƙasa yayin da glass da ke jikinshi suka tarwatse suka fashe. Saurin ja da baya Zahra ta yi tareda nuna hoton ta ce. "Wannan ba ita ce wannan mahaukaciyar da na gani a asibiti ba?, me kuma hoton ta yake yi a cikin wajan nan?, shin ita ɗin wace ce?. Kodai ita ma tana da halaƙa da wannan masarautar?".


Haka ta cigaba da magana ita ɗaya kamar wata zautacciya.


Ba ta yi aune ba ta ji an banko ƙofar ɗakin da take.


Zumbur Zahra ta miƙe tana mai maida kallonta kan ƙofa don ganin wane ne.




**************************
Su Aliyu kuwa suna isa gida suka shiga parlour nan suka tarar da su Grandpa tare da su Daddy a zazzau ne.


Gaishe su suka yi a yayin da Safeera ta samu guri ta zauna kusa da Mom.


Kallonsu Aliyu ya yi sannan ya ce. "Grandpa ya hanya?, me haka ce yake damun Safeera?".


Amsa Grandpa ya bawa Aliyu da cewa. "Babu abin da ke damun Safeera lafiyarta ƙalau bawai shafar aljanu ba ne".


Sauke ajiyan zuciya Aliyu ya yi sannan ya ce. "To alhamdulillah haka ake so".


Maida kallonsa Grandpa ya yi kan Safeera sannan ya ce. "Jikata ki kwantar da hankalin ki komai lafiya, baki da wani aljanu kinji ko".


Girgiza kai kawai Safeera ta yi tare da miƙe wa tsaye ta shigar da kayan da suka siyo cikin ɗaki.





*************************
Ganin babu kowa a wajan ƙofa ya sa Zahra sauke ajiyan zuciya. Nan take ta miƙe tsaye tareda ɗaukar mayafinta ta yi ɗaurin ture ka ga tsiya, sannan ta ɗauki tsintsiya da ta gani a ƙasa ta fara share ɗakin.



Saida ta kwashe fiye da awa biyu tana abu ɗaya. Ganin ɗakin ya fara dawo wa yadda yake ya sanya ya kwanciya tana sauke ajiyan zuciya!,




Ganin ba ta ga ta kwanciya ba ya sanya ta miƙe wa sannan ta ɗora daga in da ta tsaya. Saida ta gama tsaff tare da jera hotunan cikin ɗakin kan bango sannan ya fito daga ɗakin kana ta rufe ɗakin.


Nan suka ci karo da Junaid a tsaye sai faman kallonta yake.


Turnuƙe fuska Zahra ta yi ta ce. "kai ya dai na ga kana kallo na kamar wani tsohon maye?".



Girgiza kai Junaid ya yi sannan ya ce. "Ni ba ke nake kallo ba, mamaki nake ta yadda ki ka iya buɗe ɗakin nan ba tare da taimakon kowa ba. Mutum ɗaya ne kacal a gidan nan ya san sirrin buɗe wannan ɗakin kuma shi ne yahya Sooraj bayan shi babu wani. Muƙullin nan ma ba buɗe shi duka yake yi ba dole sai yahya Sooraj ne kawai yake buɗe ɗakin nan, amma nayi mamaki ta yadda ki ka iya sanin sirrin buɗe wannan ɗakin".


Murmushi Zahra ta yi kana ta ce. "Kai ba ka san ni ɗin ƴar baiwa bace ba?, lallai mutumin nan kana wasa, to in faɗa maka ni ɗin ƴar baiwa ce shi ya sa na iya buɗe wa. Kuma Ni fa kun dame Ni da maganar wani yahya Sooraj, wai shi ɗin wane ne haka?, na ga gaba ki ɗaya masarautar nan suna matuƙar ji da shi hatta mai martaba da Mami, yaushe ne zai zo na ganshi. Ina son na ganshi kafin na bar fadar nan".


Murmushi Junaid ya yi sannan ya ce. "nan ba da daɗe wa ba zai dawo. Amma fa me iya zama da shi saita shirya, duk wannan rawan kai da jiji da kai da ki ke takama da shi duk saiya sauke su. Na san baki san ko shi ɗin wane ne ba amma lokaci zai yi da za ki ga ko wane ne shi".


Yana kaiwa nan ya bar wajan.


Tsaki Zahra ta ja sannan ta ce. "Aikin banza to ya zo ɗin mana, wa yake tsoronsa, ai ba haifi wanda Zahra za ta ji tsoronsa ba. Kuma ni dai-dai nake da koma wane ne". Ta faɗa tana mai wuce wa part ɗin Mami.









********************
"Hello sir, mun samo wacce ta taimaka wa Mrs Laila Abdullahi ta gudu daga asibiti, sunan matar Nadiya ita ɗin nurse ce a cikin asibitin da haka kai mrs Laila".



Murmushi gov. Musa ya yi sannan ya ce. "Maza ku sace ta ku kaita gidan gona ta. Zuwa gobe zan sa a sace Amrah a wajan birthday ɗin Umar. idan Nurse Nadiya ba ta faɗi gaskiya ba sai a haɗa da ita da Amrah muyi safarar su izuwa ƙasar waje. Ku kasance a hankare saboda shima Umar jami'i ne idan ya gane gaskiya gaba ɗaya ba zamu tsira ba".


"Shi ke nen yallaɓai". Mutumin ya faɗa yana mai kashe waya. Nan ya ɗauki wani perfume tare da fesa wa Nurse Nadiya. Nan take jiri ya fara ɗiban Mrs Laila faɗuwa ta yi a ƙasa sumammiya. Nan take suka rufe fuskokinsu da mask. Tare da cinciɓar Nurse Nadiya sannan suka saka ta a mota. Tada mota suka yi tare da barin harabar gidan nurse Nadiya.


Su Umar kuwa na isa gida. Kai tsaye ɗakin

Please Login or Register in order to submit comment