Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi yake aikata duk laifukan da nake kokarin gano wane ne ainihin criminal ɗin ba ashe ma asalin criminal ɗin yana zaune a gida na ban sani ba. To wallahi ba zan bar shi ba ba zan duba ko shi ɗin mahaifina bane dole sai na kama shi na damka shi wa hukuma sannan an bi muku hakkin ku kum........


Maganarsa ce ta tsaya sakamakon ƙarar da Amrah ta ƙwalla wanda ya cikashe ilahirin gidan kangon baki ɗaya.



Nan take suka ga ta fara laulayi tana mai dafe kanta.




Ɓangaren su Aliyu, bai yi aune ba ya ga Safira ta buɗe ƙofar mota tare da faɗa wa cikin jeji. Nan take ta fara gangara wa cikin daji ba tare da ta tsaya ba. Da sauri Aliyu ya bi bayanta yayin da suka haɗu su biyu suna gangarawa cikin daji.


*********
Ɓangaren Sooraj kuwa, da mamakin sa ya ga jikin Zahra ya fara ƙaƙƙarwa.



A matuƙar tsora ce Sooraj ya miƙe tsaye tare da karanto duk wata addu'a da ta zo bakinsa.


Bai yi aune ba yaga Zahra ta tafi zata faɗi da sauri ya isa gare ta tare da kare ta daga faɗuwa. Nan ta faɗa a jikinsa.


MANAGE PAGE PLS.


SHARE FISABILILLAH 🙏



ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTU



[12/7, 16:26] Ayeesher MB🥰🥰: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g






https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
(We stand together)
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 5️⃣3️⃣▶️5️⃣4️⃣
_______________________
a tsora ce Suraj ya dube ta ya ce. "Zara me ke faruwa dake haka? me ya sa me ki haka?, ya kamata ki sanar dani me yake faruwa dan Allah ". Ya faɗa a matuƙar razane.


A hankali Zahra ta buɗe idanuwanta sannan ta cire jikinta daga na shi tare da ƙwalolo idanuwa waje tana mai yin gurnani.


Ganin hakan ya sa Sooraj razana sannan ya ja da baya, yana mai karanto duk wata addu'a da ta zo bakinsa.


"Zahra lafiyar ki ƙalau kuwa?, ya kamata ki dawo yadda ki ke".



Girgiza kai Zahra ta yi sannan ta zauna a ƙasa tare da sunkuyar da kanta.


Kallonta ya yi yana mai ƙura mata ido.


Nan take ya ga ta ɗago idanunta tare da kwashe da dariya. Firgita Sooraj ya yi ganin yadda Zahra ta ƙyalƙyale da dariya.


Takawa ya fara yi tare da isa inda take ya ce. "Zahra kina lafiya kuwa?".



Fashe wa da dariya Zahra ta ƙara yi a karo na biyu tana mai faɗin. "Dama kana da tsoro aka?, ai ban san aka ka ke da tsoro ba sai yau. Dama nayi hakan ne saboda na tsoratar da kai kamar yadda nima ka tsoratar dani".


Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Kenen kina sane ki ka kurma ihuun nan?, tare da kakkarwar nan?".


Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "A'a, wannan bana sane naji kamar an buga min guduma a kaina shi ya sa na kurma ihuu, amma ka yarda dani iya wannan ne ba da sane nayi ba".


Shiru kawai Sooraj ya yi ya ce. "Fitar min daga ɗaki".


Taɓe baki Zahra ta yi tare da shagwaɓa fuska sannan ta ce. "Saboda za ka kore ni?".



Tashi tsaye Sooraj ya yi ya ce. "Idan baki fita ba zan miki dukan babban bargo yanzu nan".



Ba musu Zahra ta miƙe tsaye tare da fice wa daga ɗakin. Ganin ta fita ya sa shi jan dogon tsaki, kana ya koma kan gado.







*******************
Chan cikin jeji Safira da Aliyu suka tsinci kansu.



Ganin kan Safira na fidda jini ya sa hankalin Aliyu ya tashi. Da sauri ya miƙe a hankali saboda shima yaji rauni sannan ya yi saurin isa gare ta.


Saurin ɗaga masa hannu ta yi ta ce. "Kada ka kuskure ka matso kusa da ni, bana ƙaunar wani abu da zai haɗa ni da kai, dan Allah kayi tafiyar ka".


Aliyu bai ko saurare ta ba ya ƙarasa inda take, sannan ya samu ya yagi ɗan ƙarami daga jikin mayafin ta, tare ɗaure mata inda jinin yake fita.
Kana ya shafa kan fuskarta. Saurin ture shi ta yi daga inda take sannan ta ce . "Wai bana ce ka rabu da ni ba, me ne ne na ƙulle min ciwo?, dama ba so ka ke ka kashe ni ba, to ka barni na mutu ɗin mana. Wai kai jami'i ne ko?, kai sam baka cancanci zama jami'i ba ko kaɗan, tunda har ka iya tauye haƙƙin wasu saboda son abin duniya, sannan ka iya manta da irin halin da iyayenka za su shiga samm baka cancanci kasance wa jami'i ba, Allah wadaran mutum irin k.........


Maganarta ne ya tsaya sakamakon tsawar da Aliyu ya daka mata.




******
Ɓangaren su Umar kuwa, waɗan da suka yi kidnapping ɗin su ne suka jiyo ƙara da Aliyu ya daka. Da sauri suka fita daga wajan tare da bindigogin su domin ganin wane ne.


Umar kuwa da sauri ya nufi inda Amrah take yana mai rungume ta a kirji tare da shafan lallausan gashin kanta.


A hankali Amrah ta buɗe idanuwanta tana mai rungume Umar sannan ta ce. "Ina son zan faɗa maka wani abu".


Ɗaga ta Umar ya yi daga jikinta ya ce. "Mene ne?".


Furzar da iska waje Amrah ta yi ta ce. "Shin idan na faɗa maka wani abu za ka yarda da ni?".


Girgiza kai Umar ya yi ya ce. "In sha Allah, ai na san bakya ƙarya, ki faɗa min ko mene ne zan yarda".


Shiru Amrah ta yi na ɗan wasu lokaci, murya a raunace ta ce. "Mahaifin ka shi ne wanda ya kashe mahaifiyar ka".


Rass gaban Umar ya faɗi!, yayin da mutanen wajan gaba ɗaya suka zaro idanuwa waje.


"Ban fahimta ba, ki fahimtar da ni, ta ya ya ki ka san da cewar mahaifi na ne ya kashe mahaifiyata?, samm hakan ba zai yu ba, duk rashin imani mahaifina ba zai iya kashe rai ba".



"Tabbas idan mahaifinka ne abinda ya fi hakan ma zai aikata". Umar ya ji wata ta faɗa. Da sauri ya juya domin ganin wace ce.



Chan ya hango Nurse Nadiya a ɗaure kusada wani benching wanda mutanen gov. Musa ke zama a kai.


Mamaki ne ya kama Umar ganin nurse ɗin kwanaki da ya taɓa kai Amrah wajanta lokacin da ta suma.
"Kamar ke ce wannan Nurse ɗin ko wanda na baki amanar Amrah a asibiti lokacin muna Jigawa?". Umar ya tambaya.


Amsa nurse Nadiya ta bashi da cewa. "Ƙwarai da gaske ni ce nan ba wata ba, Mahaifin ka ya yi sanadiyar tarwatsa rayukan mutane babu adadi, shi ya yi sanadiyar rabuwar uwa da yaranta duk dan saboda abin duniya. Mahaifin ka ya kasance ya na aikata laifuka ne tun kafin ya zama Govnor, shi ɗin babban mara imani ne, ya ƙala wa baiwar Allah sharri wacce bata ji ba bata gani ba, ya sa kuma iyayen ta sun tsane ta dangint mijinta duk sun ƙi ta, sannan kuma duk da hakan bai rabu da ita ba, yana neman dukiyarta wanda ke a ɓoyayyen, wanda babu mai zuwa sai ita ko yaranta, gashi ya kashe ta, yaran ma bamu san inda suke ba. Shin mahaifinka baya tunanin shima wata rana zai koma ga ubangijin sa?, baya tunanin ta yadda zai fara sauke nauyin haƙƙin mutane da ya ci bayan ya mutu?".



Shiru Umar ya yi yayin da ya rasa ta cewa. Ji yake dama ba ta hanyar mahaifin shi ya zo duniya ba, nan take ya ji tsanar mahaifin na shi ya cikashe zuciyarsa baki ɗaya.





*********
"Safira ya ishe ki aka, kina ta tsawatar min ina yin shiru, na riga na gaya miki cewa zan faɗa miki komai daga baya amma kin ƙi saurare na, me ki ke so nayi miki. Kin san dai ina sonki kuma ina ƙaunar ki, ta ya ya zan iya cutar da wanda nake so har cikin raina?, ya kamata ki fahimce ni, duk abinda ki ka ga ina yi, to ina yi ne ba dan komai ba sai dan saboda ke, ina san na bayyana miki wata gaskiya, kuma bana don na bayyana miki wannan gaskiyar ta baki na fison na bayyana miki ki gani da kanki".



Tashi tsaye Safira ta yi ta ce. "Bana da buƙata, ni kawai ka mayar da ni gida. Kai ɗin macuci ne, da a ganka a ga maciji, gwanda a fara kashe ka kafin a kashe wannan macijin, domin kai kafi maciji cutarwa".



Jin takum takalman mutane ya sanya Aliyu saurin riƙe hannun Safira sannan ya fara gudu da ita. Ƙoƙarin wafce hannunta take amma hakan ya cutura.



Kuka Safira ta fara yi ganin yadda Aliyu ya matse mata hannu yana gudu da ita.



Aliyu bai tsaya ba saida ya isa bayan kangon babban gidan da su Umar suke sannan ya dakata yayin da ya ja hannunta tare da shigar da su domin su ɓuya.



****
Mutanen Gov. Musa kuwa suna zuwa wajan, suka tarar ba kowa, hakan ya sanya su koma wa inda suke.



Ajiyan zuciya Safira ta shiga jera wa tana mai kallon hannunta da Aliyu ya riƙe. Gani ta yi guri ya kaɗa ya yi jajir. Nan da nan hawaye suka fara bin ƙuncinta.


"Yi haƙuri Safira duk abinda ki ka ga ina yi duk saboda ke ne". Aliyu ya faɗa murya a ƙasa.





*************
Ɗaki mai num105 na hango hajiya Binta ta yi tagumi idanuwanta a kan littafin da mrs Lailah ta bata, yayin da take tunano maganar da Mrs Lailah ta faɗa mata kafin su rabu. "Ga amanar ƴata na baki ki kularmin da ita tamkar ƴar cikin ki sannan kada ki taɓa faɗa mata cewar ke ɗin bah mahafiyarta bace, har sai ta kai munzalin sanin hakan. ina son ki nemi ta gano inda mahaifinta ya ke".


Share hawayen da ke shirin zubo mata Hajiya Binta ta yi sannan ta ce. "Yanzu Zahra ta kai minzalin sanin wace ce ita tare da sanin inda mahaifinta yake, na san dai ba iya ita ɗaya Lailah ta haifa ba. Ina son na bawa Zahra wannan littafin amma ban san ta ya ya zan bata ba".



Daga nesa ta hango wata warder. Nan ta miƙe tsaye kana ta fara takawa izuwa inda wannan warder ɗin take.

Kallonta warder ɗin ta yi ta ce. "Ya aka yi?, me ya sa baki ke kinyi cutting grass ɗin da aka sanya ki ba".


Shiru Hajiya Binta ta yi ta ce. "Taimako nake so kiyi min, maganar cutting grass, zanyi shi, dan Allah wannan littafin nake son ki bawa DPO, kice idan ya ga MK ya ba shi wannan littafin, na san Mk zai iya sanin inda Zahra take. Ya bata littafin, gaba ɗaya tarihin mahaifiyar su yana ciki".




Turnuƙe fuska warder ɗin ta yi ta ce. "Ba zan kaiba maxa kije kiyi aikin ki".


"Dan Allah kiyi haƙuri ki karɓa, dan Allah". Ta faɗa hawaye kan fuskarta.


Ganin hakan ya sa warder ɗin karɓar littafin sannan ta jaddada mata cewa zata bawa DPO. Jin hakan ya sanya Hajiya Binta yin farin ciki sannan ta koma inda take.







***********************
Bayan fitar Zahra ne ta saki murmushi yayin da ta fara jin son Sooraj ya fara shiga zuciyarta.


Chan ta hango Mami zaune tana shan lemo a parlour.


Da sauri Zahra ta yi fuska tare da ƙoƙarin wuce wa dan kada Mami ta ganta.


Cikin rashin sa'a ta ji Mami ta ce. "Zahra zo nan".


A kunya ce Zahra ta ƙarasa inda take tare da gaishe ta.


Amsa wa Mami ta yi murmushi kan fuskarta ta ce. "Zahra kenen, da fuska za ki yi ki wuce ko?".


Sosa kai Zahra ta yi ta ce. "A'a Mami, ai ban isa ba".


Girgiza kai Mami ta yi ta ce. "Wai me ke tsakanin ki keda Sooraj, naga yanzu kuna shiri ba kamar da ba, sannan naga har fita kunyi tare, yanzu ma naga kin fito daga ɗakin sa, faɗa min meke faruwa, kodai akwai wata a ƙasa" .


A kunya ce Zahra ta sa hijabin ta tana mai rufe fuska sannan ta girgiza.



Murmushi Mami ta yi ta ce. "Mene kuma na jin kunya, ki faɗa min gaskiya, nimai sa sarki ne ya je a neman miki auren ki wajan iyayen ki".


Ɗago kai Zahra ta yi sannan ta ce. "Ni bani uwa ko uba, amma ina da Hajiya Binta wacce ta maye min gurbin uwa".


"Ohh Allah sarki, ban san baki da iyaye ba, Allah y a jiƙan su ya yi musu rahama".


Amsa wa Zahra ta yi da "Ameen". Sannan ta ƙara da cewa. "Ni bani nake nani ƙewa yahya Sooraj ba, shi yake naniƙe min kinga kuwa shine yake sona, kuma nima na san yana sona kawai ɓoye min yake, bai san na sani ba". Ta faɗa tana mai yin dariya.



Girgiza kai Mami ta yi tare da miƙe wa sannan ta ce. "Na manta ban baki kyautar da na siyo miki ba, bara naje na dauko min, ki jire min lemo na".



Gyaɗa kai Zahra ta yi ta ce. "Tom zan jire miki".


Jin hakan ya sa Mami barin parlourn tare da shiga part ɗin ta.



Duk abinda suke yi a gaban idanuwansu Gimbiya saratu da yaransu.

Tashi Zahra ta yi jin wani ƙishin ruwa ya dame ta ya sata nufar hanyar kitchen domin samo ruwa.





Miƙa wa Samira ƙullin magani Gimbiya saratu ta yi ta ce. "Kije ki zuba wannan garin maganin a cikin lemon nan kafin wan can sheɗaniyar yarinyar ta dawo daga kitchen, maza-maza, ina son A'isha ta mutu idan ta sha maganin nan.



Da sauri Samira ta karɓa tare da zuwa inda lemon Mami yake sannan ta fara zazzaga maganin a ciki.


Dai-dai lokacin Junaid ya shigo da sauri ya ɓuya sakamakon harba da ya yi da Samira. Bai yi dogon tunani ba, ya fara yin video sannan ya yi saurin juyawa.




Dai-dai lokacin Zahra ta shigo cikin parlourn yayin da idanuwanta ya sauka kan abinda Samira ke aikata wa.



"Kuttmelesi!, me nake gani haka, guba za ki saka wa Mami a lemo".



A razane Samira ta dube ta kana ta karkaɗe hannunta ta ce. "Toh ina ruwan ki?, waya gaya miki guba nake saka mata, na ɗanɗana lemon ne naji ba zagi shi ne na saka mata siga saboda ya yi daɗi".




"Ƙarya ki ke munafuka". Cewar Zahra sannan ta ƙara da cewa. "Lemon haɗi ne da zai buqaci siga?, wannan lemon roba ne, ki faɗa min gaskiya me ki ka saka a ciki, ko na danne ki a nan wajan nayi miki duka".



Dai-dai lokacin Mami ta shigo parlourn. Ganin Mami na zuwa ya sa Samira ta yi saurin wurga wa Zahra ƙullin maganin tare da fasa ihuu.


Nan da nan mutane suka cika cikin parlourn. Kallonta Mami ta yi ta ce. "Samira me ya sa za ki kurma ihu aka?".


Amsa Samira ta bata da cewa. "Zahra na gani tana saka miki guba a cikin lemo".


Take gaban Zahra ya faɗi. "Ni kuma?, hakan me ya sa za ki yi min sharri?, ba ke na kama ba kina saka mata guba".



Dai-dai lokacin Sooraj ke fitowa daga part ɗin shi.


Nan ya yi kicubus da su Mami tare da su Gimbiya saratu a tsatsaye. Mamaki ne ya kama shi.



Ƙarasa wa inda suke ya yi ya ce. "Me yake faruwa?".


Amsa Samira ta bashi da cewa. "Zahra muka gani tana zuba wa Mami guba a cikin lemo".




"What!, no wannan ƙarya ne, saboda me za ta aikata hakan".



Maida kallonta Mami ta yi kan Zahra ta ce. "Zahra da gaske ne abinda Samira ta faɗa?".



Girgiza kai Zahra ta yi ƙwallah fal idanuwanta ta ce. "Wallahi bani bace ba, ita na gani tana saka wa Mami guba shi ne ita kuma ta ƙala min sharri".

"Ƙarya kike muma mun ganki lokacin da ki ke saka wa". Cewar Gimbiya Talatu.


Zuciya a rauna ce Mami ta ce. "Zahra ki rasa da me za ki saka min da shi sai sanya min guba cikin abin sha na?, Why Zahra why?, ga kyautar sarƙar da na siya miki nake shirin baki amma ki ka ɓata wayon ki ta hanyar wannan hanyar da ki ka biyo".



Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Wallahi Mami bani bace. Yahya Sooraj tunda Mami bata yarda da ni ba kai ka yarda da ni, samm ba zan iya aikata hakan ba".

"Tunda kin ce ƙarya muke miki ki ɗauki lemon ki sha, a nan ne zamu tabbatar baki saka guba ba". Cewar Gimbiya Saratu.


Furzar da iska waje Sooraj ya yi. Take idanuwansa ya sauka kan hannun Zahra wanda ke riƙe da ƙullin magani. Da sauri ya ƙarasa inda take tare da sa hannu ya karɓi ƙullin maganin ya shinshina. Da sauri ya kauda kai jin cewar tabbas wannan poison ne.



Ɗago da idanuwansa ya yi tare da ɗora su kan Zahra ya ce. "Tabbas Zahra kece nen ki ka zuba wa mahaifiyata guba a lemo, idan ba ke bace ta ya ya ƙullin magani ya zo hannunki?".



Nan su Gimbiya Talatu da yaransu suka saki murmushin mugunta.


Hawaye ne suka fara bin ƙuncij Zahra ta ce. "Ban san ta ya ya zan fara yi muku bayani ba, ni bani da sheda sai Allah. Allah shi ne sheda na, shi ne ya san wanda ya sa wannan guban. Wallahi bani ni ce..... Bata ƙarasa maganar ba Sooraj ya kwashe da marika har guda biyu wanda ya yi sanadiyar faɗuwa Zahra ƙasa.


"Mahaifiyar tawa za ki kashe?, wacce ta ɗauki ki tamkar ƴar cikinta?, a da ina tunanin ke ɗin mutuniyar kirki ce ashe ke ɗin mutuniyar banza ce. Na tsane ki, na tsani duk wanda yake ƙoƙarin cutar da lafiyar mahaifiyata. Wallahi da a ce mahaifiyata ta sha wannan poison ɗin, da saina tabbatar da kinsha baƙat azaba a rayuwarki, zan sa a kama ki a zartar miki hukunci. Yanzu aka ma baki tsira ba, domin yanzu zan kira ƴan sanda su kama ki".


Babu abinda Zahra ke yi sai kuka. take ta ji kewar iyayen ta da na danginta. Da a ce suna raye ba za'a dinga yi mata hakan ba.



Dakatar da Sooraj Mami ta yi ta ce. "A'a kada ka kira ƴan sanda, bana son wannan abun ya isa kunnen mai martaba domin hukuncin zai fi haka, kawai ta tashi ta fice daga masarautar nan kuma kada mi sake ganin koda inuwarta a nan fadan".



Miƙe wa tsaye Zahra ta yi tana mai share hawayenta.



Kallonta Sooraj ya yi ya ce. "Maza zo ki fice, bana son na sake ganin wannan fuskar taki" Ya faɗa yana mai yi mata nuni ga hanyar ƙofa".


Murmushi wanda ya fi kuka ciwo Zahra ta yi ta ce. "Zan tafi amma kafin nan, zan sha wannan lemon idan ya so ni zan mutu a maimakon Mami".



Ta ƙarashe maganar tana mai nufar inda lemon yake. Da sauri Sooraj ya tafi domin dakatar da ita. Amma ina kafin ya isa, Zahra ta ɗauki kofin lemon tare da shanye lemon ciki kana ta wurgar da glass cup ɗin".



Zaro idanuwa gaba ki ɗayansu suka yi.

Take gaban kowanensu ya faɗi!.


Nan take Zahra ta faɗi a ƙasa.







ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
(ZINARIYAR JAJIRTATTU)
[12/14, 18:40] Ayeesher MB🥰🥰: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g




https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
(We stand together)
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 5️⃣5️⃣▶️5️⃣6️⃣
_______________________
A matuƙar tsora ce Sooraj ya nufi inda Zahra ta faɗi da mugun sauri tare da ɗago ta ya fara jijjiga ta a razane da firgici yana mai faɗin Zahra me kika aikata haka? ya za ki sha wannan abunda kika san guba ce a ciki kina da hankali kuwa".



Hankalin Mami da sauran ƴan cikin falon ba ƙaramin tashi ya yi ba ganin yadda Zahra ta fara fita daga cikin hayyacin ta. fusge jikin ta zahra ta yi daga jikin na Sooraj sannan ta miƙe tsaye a hankali nan take jiri ya ɗebe ta, ta faɗi a ƙasa . Da sauri Sooraj ya nufi inda take sannan ya dauke ta ya nufi waje da ita da mugun gudu saboda sauri ko ganin gabansa ba ya yi.


Kai tsaye inda motarsa yake ya nufa tare da nufar side ɗin ƴan zaman banza tare da buɗe ƙofar motar sannan ya saka Zahra a cikin mota sannan ya rufe ya juya tare da shiga mazaunin driver ya sa car key ya ta da motar tare da jan motan da gudu ya fita daga cikin masarautar. tafiya yake yi ba gaggautawa tare da wani irin gudun tuki tamkar ana tseren mota.



Maida kallonsa ya yi kan Zahra hankali a tashe ya ce. "Kada ki damu Zahra babu abinda zai same ki zan ceci rayuwar ki duk rantsi duku ya bazan taba bar ki ba, saboda dalilin mu bazan so a ce kin rasa rayuwar ki ba, ban sani ba ko gaskiya ne abunda su Samira suka faɗa amma tabbas na san da cewar ba zaki iya aikata abinda suka ce kin yi ba, amma ke ma me ya sa za ki sha wannan guba tunda kin san da cewa cutar dake zai yi bai kamata a ce kin sha ba, ya kamata ace anyi bincike kafin nan a gano gaskiyar lamari amma kuma kika ɗauki gubar ki ka sha gashi nan za ki mutu a banza. Ya kamata a ce kin fahimce ni ban so a ce kin sha wannan guban ba, idan kika mutu ban san wani hali zan iya shiga ba".



Zahra dake kwance ta yi luff jin maganganun Sooraj ya sa ta sakin murmushi cikin zuciyarta ta ce. "Dama haka ya damu da ni shi ne kuma zai mare ni wato dai ya san ba nice na saka wannan guban ba amma kuma shi ne yake yi kamar bai sani ba, lallai dole in koya masa hankali".


Buɗe idon ta guda ɗaya ta yi tare da kallon sa da gefen ido da sauri. A hankali ta buɗe idonta gaba ɗaya tare da kallon sa. A matukar tsora ce Sooraj ya dube ta sannan ya ce. "Kina lafiya?, babu abinda ya same ki?".

Harara Zahra ta galla masa sannan ta saukar da glass ɗin motan tare da tofar da poison din bakinta.


Mamaki ne ya kama Suraj ganin cewar bata haɗiye poison din ba. "Wai dama ashe ba haɗiye poison din nan kika yi ba ki kai kamar kin haɗiye?".


Kallon baka da hankali Zahra ta bishi da shi sannan ta ce. "jaka ce ta mun gula da zan haɗiye guba?, an gaya maka bana son rayuwata ne eh?, na ce an gaya maka bana son rayuwata ne?. To in faɗa maka kawai na sha ne saboda na kawar da tunanin ku a kaina amma me zai kaini shan guba bayan ba gajiya nayi da rayuwar ba".


girgiza kai Suraj ya yi sannan ya ce. "lallai yarinyar nan kin cika tantiriya kuma a hatsabibiya, wato dama baki sha wannan gubar ba shi ne kuma kika tayar mana da hankali lallai yarinyar nan sai na koya miki hankali wannan wani irin shashanci da akuyanci ne wannan ai ba daidai ba ne, me kike tunanin zai faru by mistake kika haɗiye guban?".


Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Eh ba matsala Allah ya yi lokaci na ne ya yi. Sannan ma da ka ke wani min magana ina ruwanka da ni?, ɗazun nan ka gama mari na yanzu kuma kana nuna wa kamar ka damu da ni. Ni ka bani ruwa na kuskure bakina guban yana min wani iri a baki".



"Bani da ruwa, ko kinga frigde ne a cikin motan?". Cewar Sooraj wanda ya tsaya faman kallonta yayin da yake driving.



Amsa Zahra ta bashi da cewa. "Na sani abu a duhu a bak'ar leda, na sani ko Kanada fridge a motarka?, ni ka kalli gaban ka kada kasa muyi hatsari, idan kaga mai shagon saida ruwa saika tsaya kaje ka siyo min".



Kallon baki da hankali Sooraj ya bita da shi ya ce. "Karki samu damuwa shi kanshi mai shagon da shagon gaba ɗaya zan haɗa na kawo miki".





******************
Shiru kawai Safira ta yi yayin da taji cikin ta nayi mata ciwo alamun tana jin yunwa. Kallon Aliyu ta yi da rinannin idanuwanta cikin raunatacciyar murya ta ce. "Ina jin yunwa, ciki na yana min ciwo dan Allah

Please Login or Register in order to submit comment