Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Amma yanzu zamu je mu binciki ccctv camera domin ganin komai". Cewar police officer ɗin

"Shi kenen ba bu damuwa. Amma yanzu me zamu ce wa mutanen gari da kotu kenen? wai waya ce muku ma ku fito da ita daga magarƙama?. Yanzu dai shi kenen best solution shi ne kuje gidan radio da gidajen jarida ku buga news paper da photon ta ku saka wanted duk wanda ya ganta yana da kyauta mai tsoka. Kuma baya sannan ku sanar da masu motoci da adaidaita cewar yau ba bu aiki kada wanda ya fito hatta masu motar tasha karsu fito domin banason ta fita daga cikin garin nan kajini Koh?".

"Shi kenen sir yadda kace haka za'a yi". Yana kaiwa nan ya kashe wayar yayin da suka nufi cikin inda ccctv cameran yake.

Miƙarda Nurse Nadiya ɗaya daga cikin police ɗin ta yi. Yayin da Doctor ya saka mata bandage tare da bata magani rage zafi tasha.

"Wai mene ne ya faru?". Ɗaya daga cikin warders ɗin ta tambayi Nurse Nadiya.

Share hawayen ta Nurse Nadiya ta yi sannan ta ce. "Na shigo zan bata magani sai ta ce min na taimaka mata na fitar da ita ni kuma naƙi amince mata harna yi iƙirarin cewar zan tona mata asiri, kawai sai ji nayi ta buga min ƙarfe a kaina sannan ta cire min kayan Nurse's ta saka. Bayan ta buga min ban sake sanin inda kaina yake bah sai yanzu".

Ajiyan zuciya police ɗin suka sauke sannan suka ce. "Amma shin ina yaran da ta haifa suke?".

Nan ta ke zufa ya fara ƙeto ma nurse Nadiya ta kowane sashi na jikinta.

Cikin daƙewa ta ce. "Iya jaririya ɗaya na gani a wajan ta kuma ta fita da ita".

"Shi kenen Kada ki damu zaki bamu number ki da address ɗin ki domin mu ci-gaba da investigation hakan wannan lamarin because this is an criminal offense ba zai yu a rufe bah. Kuma sannan zamu bincika gaba ki ɗaya ccctv camera dake cikin asibitin nan".

Yana kaiwa nan ya yi musu alamun da su fita. Fice wa suka yi gaba ki ɗaya yayin da suka bar iya nurse Nadiya da doctor a ciki.

Gaban nurse Nadiya ne ya tsananta faɗuwa jin cewar za'a je a duba ccctv camera.

Ta ke kukan jaririyar dake ƙasan gado ya karade ɗakin. Rass! gabanta ya faɗi.


____ Yauwa Doctor ina ccctv csmersn cikin room 8 naga kowane ɗaki ccctv camera yana yi amma banda na room 8. Muna so ne mu ɗau recording duk abin da ya faru a ɗakin". Cewar ɗaya daga cikin ƴan sandan.

"Kuyi haƙuri na manta ban faɗa muku bah ccctv cameran ɗakin nan ya daɗe da de nayi kuma mun kira mai fixing ɗinshi ya ce zai zo ya gyara".
Cewar likitan.

Miƙe wa ɗan sandan ya yi a fusa ce sannan ya ce. "Wannan wane irin shashanci ne? ya za'a ce ccctv camera na room 8 bayayi bayan kuma duk sauran suna yi? kin san mahimmanci cctv camera kuwa?".

Cctv hana sanyawa a cikin ɗakunan majiyyata, da sassan kulawa masu mahimmanci. Wannan na iya taimakawa wajen lura da yanayin marasa lafiya da faɗakar da ma'aikatan kiwon lafiya idan akwai gaggawa. Cctv kuma na iya taimakawa wajen lura da hulɗar marasa lafiya tare da masu ba da lafiya don saka idanu hakan ingancin kulawa da bin ka'idoji. Amma shi ne zaku je wannan room 8 ɗin ba bu, a shi ma ya kamata a bar cctv domin babban makashiya ce a ciki dole a dinga ganin take-taken ta. Yanzu da a ce cctv na ɗakin nan nayi da binciken sai ya fi mana sauƙi. Rubbish kawai". Police ɗin ya faɗa tare da ficewa daga wajan. Ganin hakan ya sa sauran jami'an suka mara masa baya.

Haka jami'an suka bazu cokin gari wajan neman mrs Laila Abdullahi. Yayin da bangare guda kuma Jami'ai waɗan da ke tare da police dog's wajan bin ƙarnin jinin Mrs Laila sun gaza samo ta. Ba yacce suka iya haka suka koma police station.

Ɓangare guda kuma ƴan sandan sun buga photon Mrs Laila a jarida wanda haka saka wanted a jiki. Sannan suka fara kafawa a titinuwa. Yayin da gefe guda kuma suka je gidan radio tare da sanar da jama'ar garin. Nan da nan garin ya karaɗe da maganar Mrs Laila Abdullahi babbar yar ta adda mai safaran miyagun ƙwayoyi wanda gaba ki ɗaya garin ya amsa da hakan.





**Ɓangaren Mrs Lailah Abdullahi kuwa tun da ta fara tafiya gabanta ke tsananta faɗuwa. Gefe guda kuma jaririyar dake hannunta sai kuka take. Hawayenta mrs Laila ta share yayin da ta fara waige-waige koh Allah zai sa ta ga mai napep ya kaita tasha. Cikin sa'a kuwa ta hango tawowar mai napep. Ganin hakan ya sa ta yi saurin gyara zaman face mark ɗin da ke kwance kan fuskarta. saida ta rufe fuskarta gaba ɗaya ba'a ganin komai banda idanuwanta.


Tare shi ta soma yi.
Ganinta ya sa mai napep ɗin ya tsagaita da tafiya. Tsayawa mai napep ɗin ya yi daff da ita sannan ya ce mata. "Madam ina zaki je?".


Amsa ta bashi da cewa, "Ina son ka kaini sabon tasha zan hau mitar kano".


Girgiza kai mai napep ɗin ya yi sannan ya ce. "Amma naji jami'ai suna cewa wai wata criminal ta gudu daga asibiti kuma ance kada masu motocin tafiya su yi aiki yau saboda yau za'a rufe kowace hanya ta shige da fice domin kama wannan criminal ɗin. Na faɗi hakan ne badan ina zargin ki ba na faɗi hakan ne kawai saboda kada ki je ki ɓata kuɗin motar ki kiga yau basu yi aiki bah. Kuma ba iya su kaɗai ba harda masu napep nima na fito ne kawai saboda zan siyi abin da zanci".


Ɗan jimm Mrs Laila ta yi yayin da ta gyara kwanciyar jaririyar dake hannunta. Maida kallonta ta yi kan mai napep ɗin sannan ta ce.


"Naji dukkanin abin da ka ce amma ina son nayi wannsn tafiyar ne ba dan komai ba saboda wani abu wanda ke da mahimmanci a rayuwata, dan Allah ka kaini koh nawa ne zan biya ka mundin zaka kaini sabon tasha kuma nayi maka alƙawari ba bi wanda zai tuhume ka da cewar me ya sa ka fito aiki. Kayi wa Allah da annabi ka kaini kaji?".

Ajiyan zuciya mai napep ɗin ya sauke tare da maida kallonsa kanta ya ce. "Ni wallahi har kin fara ban tsoro ma karna je ma ko ke ce wanda ƴan sanda suke nema ni nazo na shiga uku. Amma ba bu matsala zan kaiki kamar yadda ki ka buƙata saboda duba da nayi cewa kina tare da jaririya kuma keda ita kuna matuƙar buƙatar kulawa. Ba bu damuwa kiyi sauri ki shigo cikin motan kada wani ya ganmu zan bi one way ne inda na san ƴan sanda da ƴan road safety da karota basua wajan".


"Shi kenen na gode sosai". Mrs Laila ta faɗa hawaye na ƙoƙari zubo wa kan ƙuncinta sannan daga bisani ta shiga cikin motan.

Tada napep ɗin mai sahu ya yi sannan ya fara tafiya. Kamar yadda mai sahun ya faɗa one way ya bi inda ba bu jami'ai ko ɗaya a wajan. Tun da suka fara tafiya ƙarnin jinin jikin Mrs Laila ya karaɗe cikin adaidaitar. Tunani mai sahun ya fara na kodai ya shigo da wani abu ne wanda ke ƙarnin shi bai sani bah.

Kawar da kai ya yi sannan ya ci-gaba da tafiya. Mintuna ashirin ne ya yi musu suka isa tashar.

Parking mai napep ɗin ya yi tare da fara dube-dube.
"Dama na faɗa miki ba bu wanda zai yi aiki yau domin ƴan sanda sun yi annoucing kada wanda ya fito aiki yau duba ki gani".

Waigawa Mrs Laila ta yi yayin da taga ba bu koda ƙuda a wajan gaba ɗaya sun rufe motocin da kayan mota wajan gaba ki ɗaya ya ɗauki shiru.

Kuka mai ƙarfi ne ya kufce mata sosai Mrs Laila ke kuka tamkar za'a zari ranta. "Wannan wace iriyar ƙaddarar rayuwa ce? shin mena aikata haka? ni da nake ƙoƙari wajan faranta wa mutane marasa shi harda waɗan da suka da hali sai kuma yau ni ce na ƙare ina yawon kan titi domin tseratar da kaina. Ya hayyu ya ƙayyun Allah ka kawo min agaji".

Shiru mai napep ɗin ya yi yayin da ya zuba ido ya kallonta. Bai san dalilin ta nayin kuka ba kuma bai san wace ce ba saidai yaji tausayinta ya shiga cikin ranshi. Tantama ya soma yi cikin zuciyarshi. "Ko dai ita ce Mrs Laila Abdullahi wanda ya gudu daga asibiti?". Tambayar da ya yi wa kansa kenen.

Maida kallonsa ya yi kanta sannan ya ce. "Shin na tambaye ki wani abu?".

Girgiza kai Mrs Laila ta yi alamun eh. Juyowa ya yi gaba ɗaya yana mai fuskantar ta sannan ya ce. "Shin kece Mrs Laila Abdullahi wanda ta gudu daga asibiti har ƴan sanda suka ce duk wanda ya yi ƙoƙarin gano ta yana da kyauta mai tsoka?".

Saurin kauda kanta Mrs Laila ta yi sannan ta ce. "A'a bani bace ba ni ban ma san wace ce Mrs Laila bah". Ta faɗa bakin ta na rawa yayin da ta kasa nutsuwa.

Murmushi mai napep ɗin ya yi sannan ya ce. "Alamu ya nuna cewa kina jin tsoro a san wani abu game da ke dan gashi ma muryar ki rawa yake. Kada kiji tsoro ni ɗin mutum ne mai tausayi kuma mai fahimta. A wannan duniyar yana da wuya ka yarda da mutum bai ci amanar ka bah, shi yasa ma ba zan ga laifin ki ba koda baki gaya min ba saboda mutanen yanzu ba abin yarda ba ne. Dan haka ki yarda dani 100% ba zan ci amanar ki ba. Ki faɗa min wace ce ke?".


Shiru Mrs Laila ta yi masa daga bisani kuma ta cire face mark ɗin kan fuskarta. Zaro idanuwa waje mai napep ɗin ya yi sannan ya ce. "Tabbas ke ce Mrs Laila wannan fuskar ta yi kama sakk da wanda na gani a jikin jarida".


Murmsh Mrs Laila ta yi sannan ta ce. "Ƙwarai kuwa nice Mrs Laila Abdullahi kuma ni ban aikata wani laifi ba haka kaini magarƙama hakasari ma ni ɗin mai taimakon wanda haka zalunta ce sai kuma yau ya kasance ni hake zalunta yayin da na kasa aiwatar da komai domin wanke kaina. Tabbas mutane sun raunata rayuwata gaba ɗaya sun yi amfani da rauni na wajan cin galaba a kaina sai dai kuma wannan ba ƙarshe bane wannan mafari ne domin kuwa ba zaka taɓa koma wa ga ubangijinka ba tare da ka gurbi abin da ka shuka tun a nan duniya bah. Ƴan uwa na iyaye na, ƙawaye na da kuma mijina ba bu wanda ya taɓa zuwa magarƙama duba lafiya ta bah. Dai-dai da rana ɗaya kacal ba bu wanda ya zo koh ya tambaye ni mai na aikata bah kowa dai abin da yake gani ni ɗin makashiya ce mai safaran yara yin karuwanci tare da safarar miyagun ƙwayoyi. Kuma wai duk ni ce ke aikata waɗan nan munanan ayyukan. Wallahi ba zan taɓa yafe ma abin da suka aikata a gare ni bah". Ta ƙarashe maganar tare da fashe wa da matsanancin kuka.


Shiru mai napep ɗin ya mata yayin da yaji tausayinta ya kama shi sosai. Cikin jimami da tunanin rashin kyautata wa da haka yi mata ya ce. "Shin idan na faɗa miki wani abu zaki yarda?".


Share hawayenta ta yi sannan ta ce. "Eh zan yarda".

"Ni ɗin jami'in ɗan sanda ne wanda haka bawa aiki nayi ɓadda kama kamar yadda ki ka yi na kama ki". Mai napep ɗin ya faɗa tare da nuna mata police warrant ID card.


Zaro idanuwa waje Mrs Laila ta yi ta ce. "Shi kenen yanzu komai ya ƙare.






*ASIBITI*
"Wannan ba kukan jariri nake ji ba a ƙarƙashin gado?". Cewar Doctor.

Miƙe wa tsaye nurse Nadiya ta yi tare da ɗauko jaririyar dake kwance a ƙasa ta ce. "Ƙwarai kuwa kukan jaririya ce kuma jaririyar ma yarinyar Mrs Laila ce".

"What! Doctor ya furta sannan ya ce. Kin san abin da ki ke faɗa kuwa? dama akwai jaririya a ɗakin nan kuma ki ka ce da su jami'ai ba bu".

Shiru nurse Nadiya ta yi sannan ta ce. "Nayi ma mahaifiyarta alƙawarin cewa ba zan taɓa bari wani abu ya samu ƴarta ba kuma nayi mata alƙawarin zan damƙa ta a hannun mutanen ƙwarai koh kuma ni na riƙe ta, shi ya sa ban fito na faɗa cewar akwai yarinya a nan ba dan Allah ka rufa min asiri banason wani abu ya samu wannan yarinya saboda mundin maƙiyan Mrs Laila suka gano tana da ƴa a nan sai sun san yadda suka yi suka ɗauke ta domin cimma wani kudirin nasu".

Ɗan jimm Doctor ɗin ya yi sannan ya ce. "Shi kenen ba bu damuwa zan rufa miki asiri kuma sannan zan taimaka miki. Yanzu dai ki kai yarinyar gida kada ki bawa kowa ke ki riƙe ta s matsayin ƴarki idan mijinki ya aminta da hakan idan kuma bai amince ba sai a kaita gidan marayu Koh kuma duk wanda suka zo suna son adopting ɗin ƴa sai a basu".

Godiya sosai Nurse Nadiya ta yi mishi sannan daga bisani ta fice daga cikin ɗakin.




Ɓangaren magarƙama kuwa bayan binciken da ƴan sanda suka yi sun gano inda asalin mahaifan Mrs Laila ke zaune hakan ya sa suka yanke shawarar cewa su kai musu yarinyar dake hannun Hajiya Binta tun da ita ma jaririyar ƴar gidan ce. Ba bu yacce Hajiya Binta bata yi dasu ba wajan ganin basu tafi da jaririyar ba amma koh sauraranta basu yi ba. Ba yacce ta iya haka ta haƙura ta barsu suka ɗauki jaririyar.

Kamar yadda suka shawarta a tsakaninsu haka suka ɗibi jami'ai da lauyoyi tare da warders suka nufi gidan ahalin Mrs Laila Abdullahi da jaririyar.

Mintuna talatin ya yi musu a cikin estate ɗin Wanda ke kusads Abubakar rimi houses estate.

Wani katafaren gida na hango wanda koh ina zagaye yake da jami'ai kallo ɗaya zaka yi kasan gidan babban mutane ne masu jini a jiƙa. Tsayawa faɗa muku yadda gidan nan ya tsaru ɓata lokaci ne domin sai mu gaba page ɗin ba'a gama ba saboda irin kyau na gidan tabbas kuɗaɗe ba ƙaramin kuka suka yi ba wajan gina wannan gidan.


Horn jami'an suka yi. Nan ta ke masu gadi na gidan suka fara buɗe gidan.


Shiga cikin gidan suka fara yi ɗaya bayan ɗaya har na daina ganin motocin nasu. Kai tsaye wajan parking space suka nufa tare da yin parking daga bisani kuma suka fara fitowa daga cikin motan.

Ganin hakan ya sa ahali gaba ɗaya fitowa daga cikin gida. Wani dattijo na hango a zaune kan wheel chair da alamu shi ne mai gidan sai kuma wata mata kusa da shi alamu sun nuna cewar ita ce matar gidan gefe guda kuma mature guy's ne tsatsaye a gefensu su biyu ɗayan barin kuma mata ne kyawawa guda biyu.

Magana dattijon ya fara yi kamar haka. "Me kuke nema kuma bayan Kun kama mai laifin da ku ke buƙata mai ya rage?".

Ɗaya daga cikin police ɗin ne ya nuna warrant ID card ɗin da sannan ya fara magana da cewa. "Mun zo gidan nan ne ba dan komai ba sai dan mu baku jaririyar da ƴarku ta haifa a magarƙama sannan kuma zamu yi bincike a cikin gidan ku da nata don sanin koh nan ta zo bayan ta gudu daga asibiti".

"What! Kamar ya ban fahimta ba? shin an gaya muku cewar bayan ta gudu nan ta tawo? koda nan ta tawo ba zamu taɓa karɓar ta ba domin ta zubar mana da mutunci da kimar mu. Mun daɗe muna rwyuwa cikin farin ciki ba tare da wani tseko ba amma Laila haka taja mutuncin mu ya zube a kan titi. Wannan wheel chair ɗin da nake zaune a kai yanzu ita ce sanadiyar hakan. Kuma yanzu ku kawo min ƴarta ku ce na karɓa ai ba'a wannan gidan ba don ba zan taɓa karɓar wannan yarinyar bah. Ni kimar gidana ta fiye mun komai a rayuwa. Ba zan karɓi wannan jaririyar ba domin yanzu mahaifiyarta bata da halaƙa da wannan ahalin dan haka ku fice min daga gida".

Ɗaya daga cikin lauyoyin ne ya yi magana cikin girmama wa. "We due respect sir, yarinyar nan jikar ka ce kuma ba ta yadda za'a yi ka ƙi karɓar gudan jininka koda kuwa laifin da Laila ta aikata ya kai girman ruwan ƙorama. Idan kace ba zaka karɓe ta ba yarinyar zata sha wahala ne sannan zata tashi bata da kowa, bai kamata laifin uwa ya shafi ƴa bah. Dan Allah kayi nazari kayi haƙuri ka karɓe ta koba komai dai jikarka ce".

Dafa shi matar dake kusa da shi ta yi sannan ta ce. "Mai gida ya kamata mu yafe ma Laila. Ina da tabbacin cewar abin da haka ce Laila na aikatawa ƙarya ne bai kamata laifin ta kuma ya shafi yarinyar ta ba dan Allah kaji".

Shiru dattijon ya yi sannan ya ce. Shi mijin Laila Yana ina? me ya sa baku kai masa yarinyar ba sai ni zaku kawo wa. Kafin na irga uku idan har baku fita daga gidan nan ba sai na lahira ya fiku jin daɗi, zan sa jami'ai na su zo su yi waje daku saidai muyi shari'a a kotu wallahi. Maza ku fice".

Jin hakan ya sa manyan yaransa maza suma suka fara nasu zuben suna koran jami'an.

Ganin hakan ya sa jami'an suka shiga cikin motocin su tare da barin gidan.



LOW BATTERY🪫 🪫
NASO NAYI MUKU WANDA YAFI HAKA YAWA AMMA BA BU CHARJI KUYI MANAGE.


TOH FAH MRS LAILA DS YARANTA SUNA GANIN RAYUWA KOYA MRS LAILA ZATA YI DA RAYUWARTA? GASHI MSI NAPEP YA BAYYANA MATA CEWAR SHI ƊIN JAMI'I NE. GA KUMA MAHAIFINTA YAƘI KARƁAR ƳARTA SO SAD 😢 😭 😢💔. ALLAH YA KUƁUTAR DAKE MRS LAILA ALLAH YA BAKI NASARAN CINYE WANNAN LARABAWAN🙏🙏



COMMENT & SHARE FISABILULLAH🙏🙏🙏
ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
(Zinariyar🧝♀️Jajirtattu)
[7/28, 14:43] Ayeesher M.B🥰🥰: Follow the 💖 A'ISHA M.B✍️ HAUSA NOVELS 📚 WORLD 🌎 📚💗💖 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g


https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KhkWs8eY42GETnGLk2JC9G

https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g
Ku shiga channel ɗina domin samun sauran littatafai na👆👆👆👆👆

*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐.
Daji 🌲
Magarƙama🏢 da kuma
Birni🏙️

WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝♀️Jajirtattu)


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 7️⃣▶️8️⃣
*__________________________________________*
"Kenen dama kai ɗin ɗan sanda ne ba mai napep ba?, me ya sa saida na gama faɗa maka dukkanin sirri na tukun zaka fito ka gaya min cewar kai ɗin ɗan sanda ne?".

Ajiyan zuciya ɗan sandan ya sauke sannan ya ce. "Ki kwantar da hankalin ki Mrs Laila ni ɗin bana ɗaya daga cikin ƴan sandan da haka ce su ɓadda kama wajan kama ki. Ƙwarai da gaske ni ɗin jami'i ne amma banzo nan dan na kama ki ba, hasali ma nazo ne don na taimaka miki".


"Ƙarya ka ke yi, duk bakin ku ɗaya. Wato so ka ke na ƙara yarda da kai a karo na biyu domin cutar da rayuwata ko?, to ni bana buƙatar taimakon naka, idan kamani zaka yi ka kamani ka daina kwane-kwane". Mrs Laila ta ƙarashe maganar kamar zata yi kuka saboda baƙin ciki.


"Mijin ki ne ya ce nazo na taimaka miki ba wani ba, ni ɗin ɗaya daga cikin jami'an mijin ki ne, shi ya aiko ni gare ki. Dan haka ki kwantar da hankalin ki, ni zan taimaka miki". Cewar ɗan sandan.


Cikin rashin fahimta Mrs Laila ta ce. "Mijina?, mijina shi ne wanda ya aiko ka?, me ya sa zai yi hakan bayan lokacin da nake buƙatar taimakon sa bai taimake ni ba, ba bu ɗaya daga cikin ahalina ko mijina da yazo ya tsaya min a kotu, haka na zama tamkar marainiya. Dai-dai da rana ɗaya mijina bai zo ya duba ni a magarƙama ba. Sai yanzu kuma da nake shirin samun ƴanci zai wani turo min da kai. To bana buƙata, lokacin da nake buƙatar tsimakonsa bai taimake ni ba sai yanzu da nake shirin samun ƴancin kaina na gudo daga asibiti domin gaskiya ta wanzu a gaban idanuwa na. Ni ba zan bi ka ba".
Mrs Laila ta faɗa tare da fito wa daga cikin napep ɗin.

Gyara kwanciyar jaririyar dake hannunta ta yi hawaye na sauka kan ƙuncinta ta ce. "A gaban idanuwan mijina ƴan sanda suka zo suka kama ni ba tare da ya dakatar da su ba. Ba bu abin da yafi bani mamaki kamar yadda naga mijina ya haɗa hannu da maƙiya na, koda zan iya yafe wa kowa a duniyar nan to banda mijina". Mrs Laila ta faɗa tana mai barin wajan.


Saurin fitowa ɗan sandan ya yi yana mai binta a baya.

Ɓangaren Nurse Nadiya kuwa, kamar yadda Doctor ya faɗa mata, haka ta ɗauki jaririyar dake hannunta ta nufi gidan ta da ita.

Cikin sa'a kuwa ta tadda mijinta na gida. Sai da ta yi addu'ar shiga gida kafin daga bisani ta shige cikin gidan.

Kwance ta ganshi kan wani makeken kujera 3seater, yayin da remote ke riƙe a hannun shi da alama kallo yake yi a tv.

Sallama nurse Nadiya ta yi. Juyowa ya yi ya kalle ta sannan ya ci gaba da kallon shirin da hake haskowa a tv.

Nannauyan ajiyan zuciya nurse Nadiya ta sauke, sanin yadda halinshi yake ya sa bata ko tanka masa ba ta ƙara riƙe jaririyar dake hannunta ƙamm tare da nufar ƙofar ɗakin ta.

Daga sama taji muryar shi na faɗin. "Daga ina ki ke?".

Juyowa ta yi, ciki rashin fahimta ta ce. "Ban gane daga ina nake ba?, ina zanje in banda gurin aikina?". Ta faɗa tana mai haɗe rai.

Murmushi ya sakar mata sannan ya dubi jaririyar dake hannunta ya ce. "Wannan jaririyar fa daga ina ki ka ɗauko ta?".

Jin hakan ya sa nurse Nadiya ta saki ranta tare da sakin murmushi, ta fara nufar inda yake a zaune. Saida ta ƙarasa har inda yake tare da zama kusa da shi ta ce.


"Ba ka san wace ce ba ko?, kayi haƙuri na karɓi yarinya ba tare da na nemi izinin yin hakan daga gare ka ba. Maganar gaskiya dama wannan yarinyar ita ɗin ƴar babbar mai laifin da ƴan sanda suke nema ce, wato Mrs Laila Abdullahi, kuma nayi mata alƙawarin cewar zan kula mata da ƴarta har izuwa girmanta, sannan kuma nice na taimaka mata wajan guduwa daga asibiti. Ina fatan dai ba zaka ƙi yarinyar nan ba mai gida". Ta faɗa kanta a sunkuye.


Zaro idanuwa waje mijin nata ya yi tare da miƙe wa tsaye, cikin fusata ya ce da ita. "Shin kin yi hauka ne?, ta ya ya zaki kawo min ƴar babbar mai laifi gidana sannan kuma kiyi tunanin zan barta a ciki?, wato so ki ke kija wo min bala'i nima ƴan sanda su fara nema na ko?. Lallai wuyanki ya isa yanka. Toh bara kiji, ki ɗan yadda zaki yi ki fitar da yarinyar nan daga gidan nan, mundin baki fitar da ita daga gidan nan ba kin kaita wani gurin daban toh wallahi a bakin auren ki, don ba zan zauna ina zaman zamana ki jawo min masifa har gida ba".
Ya faɗa ranshi a matuƙar ɓace.


Baki sake nurse Nadiya ta bishi da kallo yayin da hawaye suka fara zarya kan fuskarta. Maida kallonta ta yi kan jaririyar. Nan take taji tausayin jaririyar ya kamata.a yayin da ba bu abin da jaririyar keyi in banda kuka domin ba ƙaramin yunwa take ji na, gashi kuma bata da ruwan nonon da zata bata.

Cikin tausayawa ta ce. "Allah sarki yara, daga zuwan ku duniya har kun fara fuskantar ƙalubale, wannan wace iriyar rayuwa ce, a ce ba bu wanda ya dube ku da idon rahama ya taimaka muku. Ya Allah na roƙe ka, ka sa wannan wahalar ta tsaya a iya yarintar su kaɗai kada ya kasance har izuwa

Please Login or Register in order to submit comment