Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da shigar da ita labour room tare da shirya ƙwararrun likitoci domin karɓar haihuwa.

Nan likitoci suka shiga cikin labour room ɗin da haka ajiye ta sannan suka fara gudanar da aikinsu. Yayin da suka canza mata kayan dake jikinta suka saka mata na marasa lafiya. Sannan suka saka mata ƙarin ruwa. Su kuma suka saka hand glove da facemark tare da wular kai. Ganin sai naƙuda ta ke ta kasa haihuwa ya sa suka yi scanning ɗin cikin ta. Nan suka gano cewar ba guda ɗaya bane ke cikin ta yara biyu ne.

Ganin hakan ya sa ɗaya daga cikin doctor's ɗin faɗin ba za ta iya haihuwa da kanta bah dole ne a yi mata operation idan har muna son ceton ranta da kuma ƴaƴan dake cikin cikinta. a halin yanzu jininta ya zuba sosai dole muna buƙatar wanda zai yi donating ɗin jini domin a ƙara mata don kada ta rasa rayuwarta. Dan haka dole mu muyi mata operation to save her life.
Cewar wannan likitan.

Jin hakan ya sa suka kwaso kayan aiki yayin da haka canza mata position tare da direction na haihuwan. Sannan suka yi mata allurar kashe zafi da raɗaɗi. Sannan daga bisani suka yi mata allurar bacci.

Ganin bacci ya ɗebe ta ya sa suka fara gudanar da aikinsu. cikin ƙware wa suka tsaga cikin ta tare da fiddo yaran ciki.







🌎🪐🌎🌎🪐🌎🪐🪐
*mafarin kenen. Koh ya zata kasance gaba? Ta ya ya kowanen suka kasance a ɓangare daban-daban? Shin kuma da gaske Mrs Lailah Abdullahi safaran yara ta ke tare da miyagun laifuka? Domin jin amsoshin tambayoyin ku, ku kasance tare da ni domin jin yadda zata kaya*💃💃💃


*Yawan comments yawan post ina son na ga ruwan comments*🥳👌 🥳

*kuma wannan littafin zai dinga zuwar muku ne da zarar ina ganin comments 💃🥳da likes*

DON'T FORGET TO COMMENT AND SHARE PLEASE 🙏 🙏 🙏

ALKALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
(Zinariyar🧝♀️Jajirtattu)


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KhkWs8eY42GETnGLk2JC9G


*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Thre siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐.
Daji 🌲
Magarƙama🏢 da kuma
Birni🏙️

WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝♀️Jajirtattu)


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
(We stand together)
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 3️⃣➡️4️⃣
*___________________________________________* kukan jariran ne ya kauraye gaba ki ɗaya cikin room ɗin. Hamdala likitocin suka yi ganin sun yi nasaran ceton yaran da kuma mahaifiyar su.

Nan ta ke daya daga cikin likitocin ya ɗauki ɗaya daga cikin jariran, yayin da bayan hannunsa ya kasance a kan bangon mahaifa wato ji ga gefen mahaifa. Sa'an nan kuma tare da yatsun hannunsa sannan ya miƙa hannunsa baya da gaba don raba mahaifa ya fara yi a hankali daga bangon mahaifa kadan-kadan, bai dakata bah har sai da ya ga mahaifar ta cire.

Ajiye jaririyar ya yi sannan ya ɗauki ɗayar jaririyar ya cire mata mahaifa kamar yacce ya yi wa ta farko.

Ɗaukar towel suka yi sannan suka saka su a ciki yayin da suka ajiye su a kusa da Mrs Lailah. Kallon jariran likitocin suka shiga yi ganin yadda Ubangiji ya yi musu baiwa ta halitta, juyawa suka yi tare da ficewa daga cikin room ɗin suka bar iya Mrs Lailah Abdullahi da jariran.

A hankali ta fara buɗe idanuwanta tana lumshe su yayin da ta ji dukkan gaɓoɓin jikinta nayi mata ciwo. Miƙe wa ta yi zaune tare da maida kallonta kan jariran. Murmushi wanda ya fi kuka ciwo ta yi tare da rintse idanuwanta jin yadda maranta ke yi mata mugun ciwo.

Ɗaukar jariran ta yi tareda ƙura musu ido. Zaro idanuwa waje ta yi ganin kowacce da kalar idanuwanta ɗaya blue eyes, sannan kuma ɗaya green eyes. Hakan ba ƙaramin mamaki ya bata bah.

Rungume su ta yi a kirjinta ganin yadda suke ta faman kuka. Waige-waige ta fara yi ganin ba bu kowa a ɗakin ya sa ta ajiye jariran sannan ta miƙe tsaye a hankali. Tafiya ta fara yi a daddafe harta isa gaban ƙofar ɗakin.

Leƙawa waje ta yi ta jikin ƙofar. Nan ta ga jami'ai a tsatsaye tare da warders gaba ɗaya sun zagaye wajan. Wasu irin zafafan hawaye ne suka fara zarya bisa ƙuncin ta.

Koma wa ta yi ta zauna tare da ci-gaba da rusa kuka cikin shesheƙar kuka ta ce. "Mene ne na aikata dana cancanci irin wannan sakayyar? shin wane zunubi ne na aikata? me ya sa haka zata kasance dani?".

"Mutanen da na taimaka da hannuna na ciyar da su sannan na basu abubuwa na more rayuwa. Ina tunanin koda na shiga wata matsala nsn gaba zasu tsaya mun saboda abubuwam alkhairy dana dinga aikata musu. Sai kuma gashi yau da kansu suka juya min baya saboda abin duniya suka butulce yayin da idanuwansu ya rufe suka kasa gane gaskiya. Wannan wace iriyar zamani ce wanda ba bu yarda kwata-kwata s cikinta saima cin amana da yaudara".

"Ban yi tunanin zasu iya cin amana ta har haka bah, amma ba komai Allah shi ne abun dogaro sannan shi ne mai warware kowace matsala, ina da yaƙinin cewa nan gaba sai gaskiya ta yi halinta".

Ta faɗa tare da maida kallonta jikinta ta ga faba ɗaya ta ɓata gadon saboda ba ƙaramin bleeding take yi bah.


*"Yauwa Nurse Nadiya ina son ki ɗauki ruwan zafi ki kai room 8 akwai patient ɗin mu a ciki sannan kuma kiyi wa yaran wanka. Ga tea nan mai zafi a flask wanda haka kawo mata ki kai mata tasha, sannan kuma ki bata maganin relief tasha". Cewar Doctor ɗin.

"Shi kenen sir in sha Allahu zan yi kamar yadda ka faɗa". Ta faɗa tare da kwashe kayan ta zuba su a troley sannan ta ɗauki towel mai kyau tare da tissue da allura sai maternity pad da kuma bedsheet. Tana gama haɗa wa waje ɗaya ta nufi room ɗin da su.

Sai da taje har gaban room ɗin zata shiga. Nan ta ke ɗaya daga cikin jami'an mata ta dakatar da ita yayin da ta yi amfani da portable scanner ta fara scanning ɗin jikin nurse ɗin gudun kada ta kasance tana tare da abun cutarwa.

Ganin dai ba bu komai ya sa ta bata hanya nurse Nadiya ta shiga cikin room ɗin. Ajiye troley ɗin ta yi a gefe sannan ta shiga toilet tare da haɗa ruwan zafi a cikin babban baff. Fitowa ta yi tare da nufa wajan mrs Laila wanda ke zaune kan patient bed. kallon Mrs Lailah nurse Nadiya ta yi ta ce.

"Na gama haɗa ruwan ki zo ki ɗan gasa jikin ki sannan ki saka maternity pad don naga kina bleeding so sai, sannan kuma zan baki magani wanda bleeding ɗin zai tsagaita amma sai kin fara cin abinci tukun". Ta faɗa tare da cire zanin gadon dake kai wanda ya yi chaɓa-chaɓa da jini sannan ta ɗauki zanin gadon dake kan troley ta shimfiɗa a kai. Maida kallonta ta yi kan jariran sannan ta chanza musu position na kwanciya.

Shiru Mrs Lailah ta yi ma nurse ɗin tare da sakin murmushi wanda ya fi kuka ciwo. Maida kallonta nurse Nadiya ta yi kan Mrs Lailah sannan ta ce. "Madam kiyi haƙuri ki daure ki tashi kiyi wanka. Hana hakan ne duk saboda lafiyar ki sannan kuma gashi kina ta yin bleeding ya ƙi tsaya wa. Ya kamata ki tashi na taimaka miki ki shiga toilet ki gasa jikin ki. Ga jariran ki suna ta kuka da alama yunwa suke ji kuma kin ƙi ki shayar da su ga ruwan nono ya nata zuba a jikin ki. Nurse Nadiya ta faɗa tana mai zuba ma Mrs Laila idanuwanta.

Shiru Mrs Lailah ta yi mata a karo na biyu. Ajiyan zuciya ta sauke cikin dashashiyar murya ta ce. "Shin za ki iya yi min wani taimako?".

Cikin rashim fahimta nurse Nadiya ta ce. "Taimako kuma? wace iriyar taimako zan yi muku?".

Amsa Mrs Lailah ta bata da cewa, "Ina son ki taimaka min na fita daga cikin wannan asibitin".

Zaro idanuwa waje nurse Nadiya ta yi sannan ta ce. "Na taimaka miki ki futa kuma, ke ɗin fah babban mai laifi ce, ta ya ya zan taimaka miki ki gudu bayan kuma kina gama samun lafiya za'a mayar dake cikin prison. Gaskiya ba zan taɓa iya taimakawa makashiya bah".

Saurin share ƙwallan dake shirin zubo mata Mrs Laila ta yi tare da miƙe wa tsaye daka kan gadon sannan ta durƙusa kan gwiwowinta tare da haɗe hannayenta guri ɗaya tana mai fuskantar nurse ɗin ta ce.

"Na roƙe ki da girman fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) ki taimake na fita daga wajan nan na samu na tseratar da rayukan yarana sannan na ceci tawa rayuwar. Bana son na mutu ba tare da gaskiya ta yi halinta bah, ina so koda nan gaba yarana na su kasance sune waɗan da za su bayyana gaskiya sannan jama'a suyi alfahari da su, su kasance ababen faɗa na alkhairy a wajan jama'a. Ki tamaika min dan Allah". Ta ƙarashe maganar tare da fashe wa da matsanancin kuka.

Tausayin ta ne ya kama nurse Nadiya. Saurin ɗaga Mrs Laila ta yi tsaye sannan ta ce, "Na dahimce ki kuma na tausaya miki matuƙa amma matsalar ba daga nan take bah, matsalar ita ce yanzu koda na barki ta ina za ki fita bayan ko ina a asibitin nan karaɗe yake da jami'ai tare da CCTV camera. Ya kamata kiyi ƙara nazari a kai saboda kin san yin hakan babban hatsari ne dole sai mutum ya shirya don koh a ƙofar gate ma akwai jami'ai Da ƴan jarida jira kawai suke ki fito su fara karɓar bayanai. Kuma sannan jariran ta ya ya za ki fita da su?".

Kallon nurse Nadiya Mrs Laila ta yi sannan ta ce. "Guda ɗaya zan ɗauka na bar ɗaya". What!" Nurse Nadiya ta furta. Cike da da mamaki ta ce, "saboda me za ki ɗauki ɗaya ki bar ɗaya bayan kuma duka yaran ki ne? baya sannan ma naji an ce kin haifi guda ɗaya a cikin magarƙama ga kuma biyu a nan. Idan ki ka tafi da guda ɗaya sauran biyun ya zaki yi da su? saboda me za ki aikata hakan?".

Haka nurse Nadiya ta shiga jera mata tambayoyi. Murmushi Mrs Laila ta yi tare da nufar inda jariran suke tana mai shafa fuskarsu ta ce.

"Ina so ne gaba ki ɗayansu su taso a gurare daban-daban a cikin wannan duniyar. Bawai zan raba su bane saboda wani kuduri nawa. Zan yi hakan ne kawai saboda tseratar da rayukan su sannan kuma su san mahimmanci da rayuwa take dashi. Ina da dukiya wanda yawanta ba zai misaltu bah kuma wannan dukiyan tun kafin na haife su na mallaka musu. Kuma hakan wannan property ɗin makiya na za su iya kashe koh nawa ne domin yarana su saka hannu hakan wannan property ɗin daga baya kuma su kashe su domin shi ne burinsu. Ni kuma ba zan bar hakan ta faru bah. Shi ya sa zan raba su, su rayu a gurare daban-daban yayin da kowaccen su za su kasance da uwa daban-daban. Daga baya idan sun girma su binciki tarihin su, tohh dole ne a dawo da shari'a sannan a bayyana gaskiya ta hanyar bayar da gamsassun bayanai".

Nannauyan ajiyan zuciya nurse Nadiya ta sauke sa'anan ta ce. "Shi kenen baki da wata matsala. Na miki alƙawari idan ki ka ɗauki ɗaya zan riƙe ɗaya koh kuma ba bawa duk wanda ya zo yana neman haihuwa zan bashi, idan kuma bansamu bah zan damƙa ta gidan marayu. Kuma sannan na miki alƙawarin ba zan taɓa cin amanar ki koh na yaudare ki bah. Amma kuma ina da wata tambaya, shin ta ya ya yaran gaba ki ɗaya za su haɗu bayan kuma duk a gurare daban-daban suke? kuma sannan ta ya ya za su san koh su ɗin su wane ne bayan kuma ba bu wani hujja da za'a fahimtar da su cewar iyayen da suke tare da su ba iyayensu ba asalin iyayensu ba ne? kuma wane ne zai basu property ɗin su?".

Murmushi Mrs Laila ta yi sannan ta ce. "Wannan ba abun damuwa bane gaba ɗaya bayanai da hujjoji suna tare da hajiya Binta a magarƙama. Ban faɗa mata komai ba saboda gudun cin amana, amma na san ba zata ci amana ta ba kamar yadda na saka ran cewa kema ba za ki ci amana ta bah. Kuma sannan haɗuwa da sanin asalin su za su fahimta domin Hajiya Binta zata sanar dasu ko mai".

Kallon ta nurse Nadiya ta yi ta ce. "Wace ce kuma hajiya Binta?". Amsa Mrs Laila ta bata da cewa, "hajiya Binta ita ce na zauna da ita a magarƙama kuma komai yana wajan ta hatta ta ukun su tana wajan ta".

"Shi kenen toh na fahimta yanzu dai abin da zamu yi domin fita daga cikin wajan nan shi ne dole na baki kayan nursing scrubs wato kayan mu na Nurse's ƙi saka saboda kada a gane ki sannan na baki face mark. Ita kuma jaririyar da za ki ɗauka ki saka ta a cikin troley na ƙasa amma dole sai na bata maganin bacci gudun kada ta yi kuka a gane. Bauan kin fita ni sai nayi ihuu na ce kin fasa min habu sannan kin gudu".

"Eh hakan ya yi shi kenen sai mu fara koh". Cewar mrs Laila. Nan da nan suka shirya kamar yadda suka tsara yayin da Mrs Laila ta saka kayan Nurse's ɗin wanda suka kwanta suka ƙarɓi jikinta sannan kuma ta bawa nurse ɗin kayan patient ta saka a toilet. Sai da suka gama shiryawa tsaff.

Sannan mrs Laila ta saka facemark tare da nufar inda jariran suke wanda gaba ɗaya sun lulaya duniyar bacci saboda wanka da gasa musu cibi da nurse ta yi tare da maganin bacci. Kallon su ta yi hawaye na bi bisa ƙuncinta ta ce. "Kuyi haƙuri ku yafe min, banso haka ta kasance ba, banida niyar raba ku amma dole ce ta sani zan raba ku. Kaddarar mu ce a haka kuma wannan jarabawar da zaku shiga, in sha Allahu sai kun tsallake ta". Ta faɗa tare da ɗaukar ɗaya daga cikin jariran mai green eyes sannan ta yi rolling ɗinta a cikin towel daga bisani ta saka ta a ƙasan troley ɗin wanda samansa ke rufe da kaya magunguna a kai. Maida kallonta ta yi kan nurse Nadiya sannan ta nufe ta tare da rungume ta ta ce.

"Insha Allahu ba zan taɓa manta irin wannan habun alkhairin da ki ka aikata a gare ni bah na gode sosai Nurse". Tausayinta da kuma yaran ne ya ƙara shiga zuciyar Nurse Nadiya ta ce. "Kada ki damu da wannan ɗan ƙaramin taimakon, idan da ina da halin yin fiye da haka ma zan yi. Kuma karki ƙara ce min Nurse suna na Nadiya ki ɗauke ni tamkar ƴar uwa kamar yadda ki ka ɗauki Hajiya Binta. Dan haka yanzu ki hanzarta ki fita kafin wani yazo ya ganki". Ta faɗa tare da cire ID card ɗin ta sannan ta sawa Mrs Laila a wuya.

"Kinga yadda ki ka yi kyau kuwa a cikin uniform ɗin nan, yacce ki ka san real Nurse, ba but wanda zai gane ki kinyi ɓadda kama sosai. Murmushi wanda bata yi tsamani shi ba ne ya suɓuce wa Mrs Laila sannan ta ce. "Na gode sosai Nadiya, Allah ubangiji ya baki damar sauke nauyin da ki ka ɗauka".

"Ameen". Nurse Nadiya ta furta. Mrs Laila na kaiwa nan ta riƙe troley ɗin sannan ta fara ja harta isa bakin ƙofa. Tsayawa ta yi tare da maida kallonta kan jaririyar dake kan gado sannan ta ce. "Nadiya duk wanda ya yi adopting ɗin ƴata kice mai ya kula min da ita sosai saboda ba dan banason ta na ajiye ta bah". Tana kaiwa nan ta murɗa hannun handle ɗin ƙofar tare da ƙoƙarin fita daga cikin ɗakin.

"Dakata!". Ta ji nurse Nadiya ta furta. Tsaya wa ta yi chakk ba tare da ta motsa koda ɗan ƴatsarta ba. Ta kowa nurse Nadiya ta fara yi tana nufo inda Mrs Laila take. Nan ta ke gaban Mrs Laila ya shiga faɗuwa! Saida tazo kusada ita sannan ta miƙa hannunta tare da riƙe na Mrs Laila sannan ta saka mata kuɗaɗe. Nan ta ke Mrs Laila ta sauke nannauyan ajiyan zuciya.

Murmushi Nurse Nadiya ta yi ta ce. "Na baki tsoro ne? ga kuɗi nan ba bu yawa na san zaki buƙaci kuɗin hawan mota da kuma kuɗin da za ki ɗan ci wani habu idan kina jin yunwa kuma sannan number na yana jikin Id card ɗina idan kina da buƙatar wani taimako ki kirani kinji".

Nan ta ke Mrs Laila ta ji ina ma a ce dukiyoyin ta na kusa da ta mallaka wa nurse Nadiya ɗaya daga ciki. Share hawayen da ke zarya kan ƙuncinta ta yi sannan ta ce. "Nagode sosai Nadiya haƙiƙa ke ɗin mace ce ta ƙwarai kuma in sha Allahu saina saka miki da alkhairy".

Girgiza kai nurse Nadiya ta yi sannan ta ce. "Ni banyi miki hakan ba domin ki saka min nayi ne domin Allah dan haka ki hanzarta ki tafi kada su shigo su tarar damu".

"Shi kenen". Mrs Laila ta furta Daga bisani ta fice daga cikin ɗakin. Kallon ta jami'an suka yi yayin da suka ga kamar yanayin nurse da ta shiga da kuma wacce ta fito ya bambanta domin tafiyar da take yi tamkar mara lafiya.

Fargaba da tsoro ne ya cunkushe guri ɗaya a zuciyar Mrs Laila. Tafiya ta ci-gaba da yi a karkace da troley yayin da hannayenta da ƙafafuwanta ke kakkarwa saboda tsoro, gashi maranta bai daina yi mata ciwo bah duda cewar ta sha maganin relief. Saida taje har gaban gate zata fita taga an dakatar da ita.

Tsayawa ta yi tana mai kallon masu gadi. Daga gefe kuma police ne da sojoji sai ƴan jarida zagaye a wajan. Ɗaya daga cikin police ɗin ne ya kalle ta ya ce. "Nurse ina kuma za ki je da troley bayan kuma ba'a fita da shi?".

Wani irin zufa ne ya fara ƙeto daga kowane sashe na jikin ta. Cikin ƙasa da murya ta ce, "Eh dama zan zubar da magunguna ne a shara zan dawo da troley ɗin".

Kare mata kallo police ɗin ya yi sannan ya ce. "Shara kuma? bayan dustbin ɗin asibiti ina kuma za ki je da wannan. Kuma yana ga kina magana kamar wata mara gaskiya, hanya ke nurse ce kuwa?".

Rass! Gaban Mrs Laila ya faɗi. Cike da tsoro ta kalle shi ta ce, "ni nurse ce kuma Doctor ne ya umarce ni dana zubar da waɗan nan dattin a waje. Saboda wari yana affecting ɗin patient ɗin mu na asibiti kuma yana iya tada musu da rashin lafiyar su".

Jinjina kai police ɗin ya yi sannan ya saka a ɗauko masa portable scanner domin ayi scanning ɗin troley dake hannunta.

Ganin hakan ya sa gaban Mrs Laila ya tsananta faɗuwa. Karɓar scanner police ɗin ya yi wajan ɗaya daga cikin jami'an sannan ya fara scanning troley ɗin. Rintse idanuwanta Mrs Laila ta yi yayin da take karanto duk wani addu'oin da ya zo cikin zuciyarta.

Saida ya zo daff da inda jaririyar take sannan ya ɗauke scanner ɗin tare da bata damar fita. Hamdala Mrs Laila ta yi sannan ta fara jan troley ɗin harta je daff da bakin ƙofa.

Daga sama ta ji muryar police ɗin ya ce. "Dakata". Chak Mrs Laila ta tsaya Tare Dmda jiran furucin da zai ƙara fitowa daga bakinsa.

Zuwa police ɗin ya yi daff da ita sannan ya ce. "Ina son kafin ki fita ki cire facemark ɗin fuskarki na ganki". Ta ke zuciyar Mrs Laila ya buga da mugun ƙarfi. Cikin zuciyarta kuwa ta ce. "Na shiga uku yanzu na san shi kenan asirina zai tonu. Ya zama dole na ƙara yi masa wata ƙaryar domin fita daga wajan nan".

Juyawa ta yi tana mai fuskantar sa sannan ta ce. "Kayi haƙuri ni ɗin matar aure ce miji na ne ya bani umarnin yin hakan, kuma ya ce kada na kuskure na buɗe fuskana saboda baya son haga matarsa. Kuma kaga dole na bi umarnin sa saboda igiya uku ce a kaina ba zan so na rasa su ba kuma aljannata tana ƙarƙashin kafar mijina dole nayi masa biyayya. Ko kaima ba zaka so matar ka ta bijire maka bah". Ta faɗa tana mai kauda kai gefe.

"Shi kenen na fahimce ki. Tabbas ke ɗin mata ce ta gari har ki iya jure zafin rufe fuskarki saboda kiyi wa mijinki biyayya toh tabbas ba bu makawa ke ɗin ta gari ce, ba bu komai za ki iya tafiya".

Godiya Mrs Laila ta yi masa daga bisani ta fice daga cikin asibitin.

Bayan ficewar Mrs Laila daga cikin room 8 nurse Nadiya ta ɗauki ɗayar jaririyar sannan ta ɓoye ta a ƙarƙashin gado. Maida kallonta kan CCTV camera dake cikin ɗakin ta yi sannan ta ɗauki ƙarfe tare da fasa cameran. Yayin da ta samu kanta ta dinga bugawa a jikin gini har saida taga yafara jini.

Nan ta ke ta faɗi ƙasa sannan ta ƙwalla wani irin razananniyar ƙara!. Nan ta ke ƴan sanda da warders suka fara nufo hanyar ɗakin yayin da likitoci suka nufo wajan. Buɗe ƙofar suka yi yayin da suka tarar da nurse Nadiya a kwance rai a hannun Allah.

Ɗaya daga cikin jami'an ne ya isa gare ta tare da tambayar ta me ya faru?. Cikin ciwo ta ce.
"Ta gudu mai laifin ta gudu ita ce ta ji min rauni saboda kada na tona mata asiri".

Shitttttt! Ɗaya daga cikin jami'an ya faɗa yayin da ya ɗauki field telephone na ƴan sanda tare da sanar da sauran jami'ai. Nan ta ke labari ya karaɗe cikin asibitin cewar Mrs Laila ta gudu.

Ta ke ƴan sanda da warders suka shiga zagaye cikin asibitin suna neman Mrs Laila.
Police ɗin da ya bar Mrs Laila ta fita ne ya yi nazari yayin da yaga cewar tabbas shi ɗin babban maloho ne har bai iya gane cewar ita ta fita bah. Nan ta ke suka fita tare da fito da police dog's da makamai na tsaro.

Nan ta ke ƴan jarida suka fara ɗaukar rahoto na labarai cewar Mrs Laila ta gudu daga asibiti.

Fita jami'an suka yi daga cikin asibiti sannan suka saki karnuƙa suka fara bin ƙarnin jinin dake jikin Mrs Laila.



TOH FANS KOYA ZATA KASANCE DA MRS LAILA DA KUMA JAMI'AI? SHIN ZA SUYI NASARAN KAMA TA KO KUWA TA TAFI KENEN? SHIN NURSE NADIYA MAI AMANA CE KOH KUWA MAI BUTULCI CE? SHIN YARANTA ZA SU TASO SU GURARE DABAN DABAN SU SAN JUNA DAGA BAYA? WAI WACE CE MA MRS LAILA? DOMIN JIN AMSOSHIN TAMBAYOYINKU KU CI-GABA DA BIBIYA DON JIN YACCE ZATA KAYA.

*KADA KU MANTA INA SON NAGA RUWAN COMMENTS. YAWAN COMMENTS YAWAN POST😍😘💕💕😍. COMMENTS ƊIN KU SHI NE ZAI NUNA KUNA MARABA DA WANNAN LITTAFIN SANNAN KUNA JIN DAƊIN SA*.

COMMENTS & SHARE PLEASE 🙏 🙏
ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B
(Zinariyar Jajirtattu)





[7/24, 11:15] Ayeesher M.B🥰🥰: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KhkWs8eY42GETnGLk2JC9G

https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g
Ku shiga channel ɗina domin samun sauran littatafai na👆👆👆👆👆

*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Thre siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐.
Daji 🌲
Magarƙama🏢 da kuma
Birni🏙️

WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝♀️Jajirtattu)


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
(We stand together)
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 5️⃣▶️6️⃣
*__________________________________________*
"Sir Mrs Lailah Abdullahi fah ta gudu daga asibiti amma yanzu mun bazama nemanta".

"What! Kamar ya ta gudu? ina ku ke da harta samu damar fita daga cikin wannan asibitin? wannan wane irin shashanci ne?". Cewar DPO

"Kayi haƙuri sir ɓadda kama ta yi hakan ya sa bamu gane ta ba.

Please Login or Register in order to submit comment