Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

karo na farko ya ga Zahra na hawaye. Dubanta ya yi ya ce.

"Dama akwai abinda zai iya saki kuka ban sani ba?".


Share hawayenta Zahra ta yi ta ce. "Yahya Sooraj ka yafe min, na san na ɗan wahalar da kai kaɗan a gidan ku, amma yanzu na chanza in sha Allahu zan daina tsiwa sannan zan kasance mai haƙuri a kome za'a yi min, kaji idan ma hukunta ni za ka yi a kan rashin kunyar da na dinga yi maka zaka iya ɗauka".


Harara Sooraj ya yi mata ya ce. "Na yafe miki, amma ni na san ba za ki chanza ba, ko duka jikina ƙunne ne ba zan yarda za ki iya chanza wa ba".



"Ka yarda da ni yanzu na chanza, baka gani ba ina kuka ɗazu, ina dana sani ne, idan muka koma gida ma zan je na bawa su Gimbiya Saratu haƙuri, ni yanzu na chanza kuma chanza wa na har aba........ Maganarta ya tsaya chak sakamakon taka ta da wata matashiyar budurwa ta yi.


Nan take Zahra ta zaro idanuwa waje tare da fara kutuntuma ashar. "Kutumeli chan, idan na yarda shegiya nake, har ni zata wuce ta taka kuma taƙi bani haƙuri saboda shegiya ce, zata gane kuranta ". Ta faɗa tare da ƙoƙarin bin bayan budurwar.


Da sauri Sooraj ya dakatar da ita sannan ya ce. "Yanzu fa ki ka ce min za ki chanza, amma kuma kinga abinda ki ke yi".



Girgiza kai Zahra ta yi jikinta na tsuma ta ce. "Na san na faɗi akan. Amma ka bari na fara koya mata hankali kafin nan saina chanza".



Ta faɗa tare da nufar hanyar da budurwar ta yi.


Dafe kansa Sooraj ya yi ya ce. "Wallahi Wannan yarinyar duk wanda ya aure ta zaiga bala'i, domin wannan annoba ce". Ya faɗa tare da bin bayanta.



Ƙara sauri Zahra ta yi yayin da kafafuwanta na harɗe wa dana juna saboda tsananin sauri da kuma bala'in da take.



Ganin budurwar na ƙoƙarin shiga mota ya sanya ta fara gudu harta isa inda budurwar take.



"Ke!". Zahra ta daka mata tsawa.


A razane budurwar ta ɗago idanunta tare da duban Zahra ta ce. "Who are you?, me ki ke nema, kinga kiyi tafiyar ki bani da chanjin da zan baki, dan haka ku baratan nan ku ke da zarar kun ga mai kuɗi ku ke kiɗime wa".



Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Yau akwai ƙura, wato ni ce mabaraciya ko?, kin taka ni kin wuce shi ne ko ki iya bani haƙuri".



Kallon sama da ƙasa budurwar ta bi Zahra da shi sannan ta ce. "Ai na san na taka ki, kuma ina sane nayi hakan, dan aka ki ɓace min daga gani".



Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Idan kinga kin bar wajan nan to bani bace. Kalle ni nan wallahi ni bana ɗaukar raini, kina wani tafiya kamar wata lanƙwasashiyar sanda. Ke daɗin abun ma baki da wani kyau balle kiyi wa mutane iyayi, kalli fa fuskarki yadda ka san wata akuya wacce ta yi shekara ta jin yunwa, ga kunnuwa fala-fala, kamar gwargwaron amarya, kin buɗe ƙwaƙwidon kanki a waje ko gashin ma babu yadda ka san gashin hammatar ɗan iska, kina wani fallewa kamar injin markaɗe. To wallahi ki sani cewa muddin baki bani haƙuri ba saina ci ubanda ya yi tattalin goron auren bikin uwar... Da sauri Sooraj ya rufe mata baki.



Wafce jikinta Zahra ta yi daga nasa sannan ta ce. "Me ya sa za ka dakatar da ni".


Maida kallonsa Sooraj ya yi kan budurwar ya ce. "Zubaida kada ki damu da abinda ta faɗa miki kiyi haƙuri kiyi tafiyarki ".



Kallonsa Zahra ta yi ta ce. "Daman ka san wannan mahaukaciyar?".


Amsa Sooraj ya ba ta da cewa. "Ba mahaukaciya ba ce ita ɗin wacce zan aura ce".


Zaro idanuwa waje Zahra ta yi tana mai cewa. "Akwai ƙura kuma a akwai kallo. Gaskiya babu mai mummunar sa'a a duniyar nan kamar kai, duk rashin sa'an wasu ya biyo bayanka. Kai yanzu me ka gani a jikin wannan mai kama da jaɓar?".



"Ki iya kalaman ki Zahra, auren haɗi za'a yi mana, kuma bana son ki ƙusa baki ciki". Cewar Sooraj.



Kallonsa Zubaida ta yi ta ce. "Abun qauna, me ya sa ka ke yawo da wannan ballagazar, kodai budurwar ka ce?, yanzu kenen cin amana ta ka ke ban sani ba".


A fusa ce Zahra ta ce. "Yaci amanar taki ɗin me za ki yi?, ke zanci bala-balan banki bariki.......


Bata ƙarasa ba taji an kwashe ta da mari. Dafe ƙuncinta Zahra ta yi ta ce. "Yahya Sooraj, mari na kayi, ni ka mara?".


Girgiza kai Zahra ta yi cikin jin aushi ta fita daga asibitin.



Da sauri Sooraj ya koma inda motarsa take tare da tada motan sannan ya fice da sauri daga cikin asibitin tare da bin bayan Zahra.







*********************
Ɓangaren Aliyu kuwa Kano ya nufa da Safira tare da kaita kangon dake cikin daji. Sannan ya yi parking tare da fito da Safira yana mai shigar da ita cikin kangon tare da ɗaure ta. Tana kuka haka ya kammala ɗaure ta sannan ya dube ta ya ce. "Ba za ki san dalilin da ya sa nake miki hakan ba, amma nan bada jimawa ba zaki fahimta".




*****************
Umar kuwa yana cikin tuƙi wasu ƴan daba suka tsayar da motarsa. Nan suka buɗe motar tare da fesa mai hoda wanda ya sanya shi fita daga cikin hayyacin shi. Nan take ya suma. Shiga motan suka yi da shi tare da tada motan suka bar wajan.


Cikin motan kuwa Amrah ce kwance bata cikin hayyacin ta. Chan kangon da Aliyu ya nufa da Amrah aka nufa.


Yayin da aka jefa su a ciki.





***********
"Zahra kiyi haƙuri ki shigo mu tafi". Cewar Sooraj yana mai cigaba da bin bayan Zahra.


Harara Zahra ta galla mai ta ce. "Ba zan shigo ɗin ba, yanzu ka gama mari na kuma kace na shigo, to ba zan shiga ba. Kaje chan da riɓaɓɓiyar motar ka".



Ganin Zahra ba zata bashi haɗin kai ba ya sashi tsaida mota tare da fito wa daga ciki sannan ya nufi inda take, bai bata lokaci wajan ɗaukar chakk ya ɗora a ƙafaɗa. Fusge-fusge Zahra ta fara yi amma samm Sooraj bai ajiye ta ba har saida ya isa motarsa sannan ya direta tare da sakawa motan key. Sannan ya zagaya ya shiga yana mai tada motan suka bar wajan.



Kai tsaye Masarauta suka nufa a sa'inda babu wanda ya ce wa wani ƙala har suka isa. Mamaki ne ya kama Zahra da Sooraj ganin yadda fadawa da dogarai tare da ƴan aiki da mai martaba tare da su Gimbiyoyi suka taru guri ɗaya.


Fitowa Zahra da Sooraj suka yi daga cikin motan.


Fashe wa da kuka Gimbiya Saratu da Samira suka yi. Kallon su Sooraj ya yi ya ce. "Me ke faruwa ne naga mutane sun taru?".


Share hawayenta Samira ta yi ta ce. "An nemi sarƙar zinaren Ammi an rasa, shi ne aka ce kowa ya fito, wasu fadawa ne da dogarai ne suke searching kowane saƙo da lungu na gidan kuma duk wanda aka ganshi a ɗakinsa shi ne ɓarawon".



Mami kuwa babu abinda take in banda addu'ar ganin gold ɗin.


Zahra taɓe baki ta yi dan ta san bata ɗauki wani gold ba.


Saida suka shafe kusan awa guda a tsaye kana daga bisani suka jiyo muryoyin fadawa na faɗin an ganshi.



Ƙarasawa wajan fadawa guda biyar suka yi tare da miƙa wa mai martaba gold.


Kallonsu Sooraj ya yi ya ce. "A ɗakin wa ku ka ga sarƙar gold ɗin?".


Amsa ɗaya daga cikin fadawan ya bada da cewa. "A ɗakin ɗaya daga cikin ma'aikatan masarautar nan wato Zahra".



Zaro idanuwa waje gaba ki ɗaya jama'ar da ke wajan suka yi.


"Zahra kuma!". Mami ta faɗa cikin shiga ruɗani.



Kallonsu Zahra ta yi ta ce. "Wannan ƙarya ne, ni ta ya ya zan ɗauki gold bayan ban san ma da shi s fadar nan ba, wallahi bani bace".


"Ƙarya ki ke, dama ba yau ki ka fara yi mana sata ba, kin daɗe kina yi shi ne yau Allah ya tona asirinki, dama an ce rana dubu ta ɓarawo, rana ɗaya ta mai kaya". Cewar Gimbiya Saratu.


Maida kallonsa Sooraj ya yi kan Zahra ya ce. "Zahra da gaske ke ki ka saci wannan gold ɗin?, me ya sa za ki aikata hakan".


Hawayen da Zahra ke ƙoƙarin riƙe wa ne suka suɓuce mata. Dubansu ta yi ta ce. "Wallahi bani bace ba, sharri kawai suke suyi min saboda a kore ni daga masarautar nan saboda ina muzguna wa rayuwarsu. Amma wallahi sata ba hali na ba ne".



Kallonta Mami ta yi ta ce. "Zahra babu sharri ko ƙarya a nan an ga sarƙa a ɗakin ki, ta ya ya to sarƙar ta shiga ɗakin naki?, ko ita sarƙar ce zata kai kanta ɗakin?".


"Kenen kema Mami baki yarda dani ba?". Cewar Zahra wacce duk ta bi ta rikiɗe.


"Waye ma zai yarda da ke, ɓarauniya, dama aka ku talakawan nan ku ke da zaran kun samu guri, ku ke iskanci yadda ranku ke so". Cewar Gimbiya Talatu.



"Maza zo ki fice daga cikin masarautar nan bamua son sake ganin fuskarki". Cewar Sooraj wanda ranshi ya yi matuƙar ɓaci.



"Dakata!". Suka ji an furta. Juyawa gaba ɗaya suka yi domin ganin wane ne, MK ne tsayem ƙarasowa wajan su ya yi sannan ya dubi kowanne daga cikin su ya ce. "Zahra tafi ƙarfin ta saci gold. Kun san wace ce mahaifiyar ta. Idan da a ce kun san wace ce Zahra da kun dinga yi mata hidima. Mahaifiyar ta na ɗaya daga cikin masu kuɗi na duniya wanda kowa ya san da hakan".


Mamaki ne ya kama kowanensu.


Mamaki ne ya kama Zahra dan ita ta san dai ba ƴar masu kuɗi bace. Kallon Mk ta yi ta ce. "Bana son kayi min ƙarya ni mahaifiya ta ma ban taɓa ganinta ba, kuma ni ɗin ba ƴar masu kuɗi bace asali ma ni ɗin a kurkuku na taso, dan haka karka yi min ƙarya dan ka kare ni".


Murmushi Mk ya yi sannan ya ce. "A wajan ki ke ƴar talakawa ce, amma a zahiri ke ɗin ƴar gidan masu arziƙi ce. Idan da a ce ana siyan masarauta, to tabbas babu tantama a cikin dukiyar ki ƙarami daga ciki zai siyi Masarautar nan har sau biyar".



Jin hakan ya sa kowanensu ya zaro idanuwa waje.





MANAGE PAGE PLEASE 🙏 🙏 🌹. KUN JINI SHIRU KWANA BIYU, WAYATA CE TA LALACE, AMMA YANZU NA GYARA DA YARDA ALLAH ZAN DINGA MUKU UPDATE A KAI A KAI.



ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
(ZINARIYAR JAJIRTATTU)
[12/2, 19:56] Ayeesher MB🥰🥰: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g




https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
(We stand together)
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 5️⃣1️⃣▶️5️⃣2️⃣
*___________________________________________*
"kamar ya ya? mufa ba mu fahimta ba ya kamata ka fahimtar da mu. Kowa a nan wajen kai yake jira kuma sannan bamu san me yake faruwa ba ya kamata ka sanar da mu ko wacece Zahra". cewar mami wacce ta tsaya ta zubawa zahra idanuwa.


ajiyan zuciya mk ya sauke sannan yace. "ko ku yarda ko karku yarda wannan ba damuwa ta bace ba amma tabbas Zahra shahararriyar yar masu kuɗi ce, ba lallai yanzu ku fahimta ba amma nan gaba tabbas zaku sani yanzu dai ku maida ta ciki dan Allah".


girgiza kai Sooraj ya yi sannan ya ce. "Tabbas zamu maida ta ciki amma kuma ina so ka faɗa mana ainihin gaskiya, kazo ne ka tsayar da mu, kuma kana so ka faɗi gaskiya amma ka yi shiru ya kamata ka fito ka bayyana mana duk abinda ke faruwa. Mu yanzu ka saka mu a cikin duhu ya kamata ka fito damu cikin haske, kada ka manta nan cikin masarauta ka shigo ba wai waje ba, ya kamata ka san inda ka ke a halin yanzu".


murmushi Mk ya saki sannan ya ce. "Ya kamata ka saurare ni yarima, na riga na gaya muku cewa nan ba da jimawa ba zaku san ainihin zance yanzu lokacin bayyanar ta bai yi ba shi ya sa ban faɗa muku ba amma insha Allah nan ba da jimawa ba za ku san gaskiya".


Ajiyan zuciya kowa ya sauke jin furucin mk na karshe furzar da iska kowa ya yi waje sannan kowa ya shige cikin fada yayin da bakin ciki da takaici suka bi suka cinkushe guri guda cikin gimbiyoyi da yaransu.


kowa ya shiga ciki yayin da ya rage iya Mk da Zahra kallonsa zara tai sannan ta ce. "Ni fa ban san ka ba, kuma ta yaya za'a ce mahaifiya ta wata ce bayan kuma ni tunda nake ma ban taba ganin mahaifiyar tawa ba, ko da kamshin jikinta ban taba ji ba. Kasan mene ne nifa ba 'yar masu kudi bace ba ka zo nan ka dan bara musu ƙaryar ka, yanzu sai ka san ai yadda zaka wanke kanka dan ni yanzu bansan me zanyi maka ba. Wallahi idan ka saka aka kore ni daga masarautar nan, ba zaka ji da daɗi ba. Ina zaman zama na zaka zo ka tayar min da hankali eh, ni yanzu kawai ka je ka gaya musu cewar duk abinda ka faɗa musu karya ce don wallahi idan gaskiya ta fito duk abinda yazo ya biyo baya babu ruwana kar ma ka nuna ka san ni ko kuma ka taɓa gani na dan ni dai ba abinda ya shafe ni, tunda kaine kazo kayi musu karya ba ni ba '. Dan haka dan Allah dan Annabi ka tawo ka je ka gaya musu gaskiya. Ya kamata ka san da haka wallahi ni ban san kowa ba ma ni a garin nan in banda magarkama ".



"A'a Zahra ba zan iya aikata akan ba domin duk abinda na faɗa babu ƙarya a cikin ta gaskiya nake faɗa miki na san ba lallai ki yarda dani ba amma tabbas wata rana za ki tuna da cewa nazo har gabanki na faɗa miki asalin wace ce ke, sai a lokacin zaki tuna abinda na faɗa miki. Kada kiyi tunanin ko nazo ne saboda wani abu ne domin na taimaka miki amma tunda kin riga kin nuna cewar ba kya son haka ni zanyi tafiya ta nagode". Mk ya faɗa yana Mai ƙoƙarin tafiya.


Da sauri Zahra ta dakatar da shi sannan ta ce da shi. "Tsaya!". tsayawa mk ya yi yana mai fuskantar Zahra. Karasawa inda yake Zahra ta yi sannan ta ce. "Ya kamata ka faɗa min toh inda mahaifiyar tawa take tunda kace kasan ta kuma kasan ita ɗin me kuɗi ce nima kuma yar ta ce kuma in yi ma ina da dukiya, to ya kamata ka kaini wajen ta ina so na ganta domin na tabbatar da abinda ka ke faɗa amma idan baka kaini ba ba zan taɓa yarda da maganar ba. Ya kamata ka san da cewa ni ba komai ne za'a kawo min na yarda ba, ina yarda da wasu abubuwan amma wani abun idan ka faɗa mun ba zan yarda da shi ba. Dan haka ka gaya mun inda mahaifiyata take idan kuwa ƙarya ka ke ba zan ƙyale ka ba dan wallahi sai na muzanta ka a gaban mutane".



Murmushi kawai Mk ya yi dan bai iya ce mata ƙala ba, sannan ya ce. "Hmm Zahra kenan, duk a cikin 'yan uwanki halinki ne kawai ya bambanta da na sauran, bansan ta yadda zan fara fahimtar da ke ainihin gaskiya ba amma ina son daga yau har izuwa sati mai zuwa kada ki kuskure ki fita daga cikin wannan masarautar saboda ana neman rayuwar ke ruwa a jallu sannan kuma da zarar kin fita za'a sace ki ina fada miki hakan ne ba dan wai banason ki fita bane da komai na rayuwarku gaba daya yake akaina dan haka ya kamata ki saurare ni sannan ki fahimci abunda nake fada miki wannan ba wasa nake fada ba gaskiya nake fada miki Zahra duk da cewa nasan ki ba mai daukar komai ba amma ya kamata kyau wannan muna tawa".




kallon sama da ƙasa Zara ta bishi da shi sannan ta ce. "Kamar yaya 'yan uwana? ni fa bani da wasu 'yan uwa sannan da ka ke cewa kada na fita daga cikin masaurartan nan har kai waye da zaka cemin karna fitar ko ina?, ni nake da kaina kuma duk inda nake so zanje da inda bana so bazan je ba ya kamata ka fahimci cewa ni ba kanwanlasa bace babu wanda ya isa taɓa ni ko ya yi yunkurin cutar da rayuwa ta ballantana ma a sace ni. Kana ji na ko, kaje ka koma duk inda ka fito dan ni ba za'a taɓa rinjayata ba, ya kamata ka san wace ce Zara, ni ba kamar sauran mutane bace da za su zo a gaya musu magana su zo su dauka ka gane, idan ba zaka iya ba ka ja baki kan shiru. Sannan ya kamata ka je ka gaya musu cewar ni ba 'yar kowa bace ba ka zo ne kayi mun sharri ban ji ba ban gani ba zaka je ka saka ni a inda Allah bai kaini ba".



Tana kaiwa nan, ta juya masa ƙeya tare da barin inda yake kai tsaye falo ta nufa wato babban falon sarki. Nan ta tarar da su gimbiya talatu da saratu tare da 'ya'yannan su cikin ranta ta ce. "Ba dai ni ku ka je ku ka yi wa sharrin cewar na saci gold ba, to wallahi zaku ga bala'i a gidan nan, dan duk wanda ya ci tuwo da ni miya ya sha, ba zan taɓa ƙyale duk abinda ku ka yi mun ba sai na fanshe duk abinda ku ka aikata mun, kuma wallahi, wallahi ba za ku ci bulus ba tunda har ku kasa nayi kuka da idona, dole kuma sai nasa ku kuka ba zan ƙyale ku ba domin kuma sai kun ɗanɗana kuɗarku".


Tana kaiwa na ta isa inda suke. Ganin tana iso inda suke ya sa ga baki ɗayansu miƙe wa tsaye tare da kwashewa da dariyar mugunta.



girgiza kai Zara ta yi tare da sakin murmushi sannan ta fara yin waƙa da cewa. "kaga ƴan bura'uba, da ni suke bura'uba, ƴan buhum bura'uba, kai ka ga 'yan bura'uba ga wata yar bura'uba, so take in bata bura'uba".


Nan take ran kowa a cikin su ya ɓaci.

Dai-dai lokacin Sooraj ya shigo parlourn tare da zama domin ganin Zahra a wajan. Nan ya shiga kallonta kamar zai cinye ta.



Ganin Sooraj yana ta kallonta ya sa Zara faɗin. "Ni dai na shiga uku wannan wani irin kallo ne haka kamar maye".


Da sauri Zara ta rufe bakinta jin furucinta na ƙarshe tare da saurin jan baya zaro idanuwa ga baki dayansu suka yi jin furucin Zahra na ƙarshe. mike wa tsaye Suraj ya yi a fusa ce sannan ya dube ta ya ce. "Ni ki ke kira maye?, ni ne maye ɗin?, wato lallai yarinyar nan sai yau na ƙara tabbatar da cewa kin gama raina ni, idan har ban koya miki hankali ba, ba za ki daina min duk abinda ki ke min ba. Ai kuwa yanzu za ki gane kuren ki, a yau zan nuna miki halin maitar". Yana kaiwa nan ya ce yi saurin nufar inda take tare da fisgo ta sannan ya kwashe ta da marika har guda biyu. Ihu Zara ta kwalla tare da fara neman taimako, ganin su gimbiya sun ja baya suna ta yi mata dariya ya sa ta fara ƙoƙarin ƙwace kanta daga wajen Suraj, amma ina hakan ya ci tura. Fusgota suraj ya ƙara yi tare da nufar hanyar past ɗin sa da ita.


Yana isa part ɗin sa ya wurga ta ciki tare da nufara kan waydrop dansa sannan ya dauko bulala tare da igiya.


Ganin hakan ya sa Zara ta fara kuka wiwi tare da fara bashi hakuri ta ce mai. "Kayi haƙuri dan Allah, ba zan sake ba, na tuba, dan Allah kayi haƙuri, dan Allah kada ka dake ni na roke ka kada ka ɗaure ni". Tana faɗa hawaye na bin ƙuncinta, amma ina Suraj ya kada sauraran ta. Aka ya janyo ta ya daure ta a jikin gado sannan ya ɗauki bulala bai yi wata wata ba ya ɗaga domin zabga mata sai wani tunanin ya sa ya dakata.



Furzar da iska ya yi waje tare da ƙura mata ido ganin gaba ɗaya hankalinta a tashe duk jikinta ya ji ƙe da zufa ya sa shi kwashe wa da dariya tare da zama a kan gadon yana mai fuskantarta sannan ya ce. "Dama haka ki ke da tsor ai ni ban sani ba sai yau kenan ma dama duk waɗan nan rashin kunyar da ki ke yi kenan duk baki ki ke da shi ba karfi gare ki ba?, ai na dauka ke irin jarumar nan cee ashe- ashe raguwa ce. To ni dai an dai ji kunya". Ya ƙara faɗa yana mai kwashe wa da dariya.


Kallon Suraj ta yi ta ce. "wallahi ƙarya ka ke yi, ni ba raguwa bace ba, ni da ka ke gani na nan sai da na taɓa dukan ɗan sanda kuma na sha ba tare da anyi min komai ba. Kaga tunda ma na iya dukan ɗan sanda ba tare da anyi min komai ba ka ga ni jaruma ce kenan. dan haka ya kamata kayi hakuri ka manta da komai na riga na gaya ma cewar na tuba na koma ga Allah. Na riga dana canza".


Kallon ta Suraj ya yi sannan ya ce. "A hakan ne ki ka canza?, yanzu- yanzun nan naga kina yiwa gimbiyoyi rashin kunya sannan kuma kice min kin canza ba wani canza wanda ki ka yi". Yana kaiwa nan ya kunce ta, sannan ya ce ta miƙe ta zauna.


Miƙe wa tsaye Zahra ta yi tare da galla masa harara sannan ta ce. "Na gode Yahya Sooraj".







***************
*Umar pov.*

Buɗe idanuwansu Umar da Amra suka yi, yayin da suka gansu cikin wani kango da sauri suka miƙe tsaye sannan suka fara wage-wage can suka hango wasu matasan mata cikin ƙunci da bakin ciki suna a ɗaɗɗaure.



Da mamaki Umar ya kalle su sannan ya ce. "Me ku ke yi a nan wajen?, ta ya ya haka ta faru?, me ya same ku haka?, wane ne wannan mutumin ne wai da yake addabar mutane?, mene ne yake nema ga mutane?, me yake so?, me yake da buƙata?, waye shi?". Tambayoyin da ya shiga yi kenan yayin da babu wanda ya ɗago idanuwan sa. Nan suka ji watan budurwa ta kallesu ta ce. "Wani ne governor Musa Muhammad". Nan take gaban umar ya yanke ya faɗi.


Kallonsu ya yi ya ce. "Govnor Musa Muhammad kuma?, kin san wane ne gwamna musa muhammad?, shi ne fa mahaifina, kuma shi din babban mutum ne wanda gaba ɗaya duniya ta san shi, ya za ki zo kiyi mai ƙarya. Sam -sam bashi ba ne ba".


kallon sa budurwar ta yi a karo na biyu sannan ta ce. "Kwarai da gaske mahaifinka shine wannan wanda yake yi mana barazana, yake mana duk abinda yake da bukata yake mana tozarci, ya samu cikin baƙin ciki, da wulakanci duk ya saka mu a cikin ƙunci. Kuma shi ne wanda yake safaran mata, yake safaran miyagun ƙwayoyi yake safarar miyagun laifuka sannan har izuwa halin yanzu babu wanda ya taɓa sanin shi din babban mai laifi bane in ba mu ba. Ya kamata ka fahimce mu ya kamata ka saurare ni sannan kuma ya kamata ka yarda dani bansan wane hujja zan iya baka dangane da hakan ba amma tabbas mahaifinka masheki ne babba kuma criminal ne".


saurin dafe kansa wanda ke ƙoƙarin sara masa Umar ya yi dannan ya ce. " I can't believe this, mahaifi na shi yake duk waɗan nan lefukan kuma ina matsayin ɗanshi jami'in kuma shine ban san da hakan ba, tabbas na aikata babban kuskure, dama na daɗe ina zargin shi da hakan, amma zuciya ta ta kasa aminta da haka sai kuma yanzu na zo na kara ji daga bakin ku, ban taɓa tsammanin cewar mahaifina

Please Login or Register in order to submit comment