Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kamar nikaɗai aka tsana, na sha jin nima kamar na kashe kaina, a lokacin da bani da kafaɗar kashingiɗa na yi kuka, noor ce kawai take tayani kuka, sai zuwan Baban su iman rayuwata, ya nuna mini ita rayuwa yadda ka ɗauke ta, haka take zuwar maka. Dan Allah ki daina wannan kukan". Ummi ta yi ta rarrashin inteesar, Farida ta fito tana faɗin "Ke Inteesar kukan me ki ka yi mata?" Inteesar ta share hawayen ta, ta ce "Babu abun da tayi mini, miƙo mini macen na ganta" Ummi ta miƙa wa inteesar iman, ta haɗa su ta rungume, tana cigaba da zubar da hawaye. Duk yadda farida ta bugi cikin noor, a kan ta gaya mata shirye-shiryen da ake ciki a kan aurenta, amma tayi mursisi tayi shiru. Sai da suka yi faɗa, ta ce noor ba za ta bi ummi su tafi ba. Sai ga inteesar ta sake da ummi, tana ta bata labarin irin zaman da ta yi a gidan aurenta. Ummi ta ce "Babu auren da ba shi da ƙalubale" nan ita ma ta din ga ba ta labarin irin ƙalubalen da take fuskanta. Ummi ta din ga jaddada mata, ta nemi yafiyar dr. Raihan ya kira wayar ummi ya ce yana waje. Noor ta kwashi takalmanta da gudu, ta yi waje saboda farida ta ce ba zata bar gidan ba. Ummi ta je ta ajiye wa rahama kuɗi, suka yi waje. Inteesar ta raka ummi da jariran nan, kamar kar ta bawa ummi su, har ta yi wa ummi alƙawarin zuwa har gida ta yi mata barka. Daga nan suka wuce gidan mariya, tayi murna sosai da sosai da zuwansu, aka yi sa'a dr. Yana nan, ummi ta yi masa maganar inteesar. Ya ce "Inteesar tsakanina da su ai sai ido, ni da ban ishe su kallo ba" Ummi ta ce "Mun yi magana da ita kawu, dan Allah ka yi haƙuri, za ta baka haƙuri ma. Ta fara iƙirarin shan guba ta kashe kanta, dan Allah ka yi haƙuri ka ja ta a jiki dan Allah. Mun yi hira da ita sosai, ta fuskanci ƙalubale sosai a gidan aure, sai dai anty farida ba ta din ga ba ta shawara ta kirki ba" Ummi ta cigbaa da lallaɓa shi, har ya amince. Noor tun da aka saka ranar aure, take wani irin jin nauyin Salim, idan ya zo duk surutun ba ta iya yi masa. Kausar kuma hankalinta ya tashi, noor za ta yi aure ta bar ta, duk samarin nata babu na aure sai ƴan sharholiya. Mariya kuwa, Abdul ne zai kai ta maiduguri, ummi kuma da ita da noor, raihan ya tafi da su bauchi, daga can idan suka kwana biyu su tafi maiduguri. Hajiya Aisha ta din ga murna, dan dama raihan bai taɓa kai mata ummi ba. Ranar da suka sauka da magariba, Hajiya Aisha ta kira wata a waya, ta ce ta shigo yau ga matar raihan su gaisa. Ummi na zaune a kan sallaya tana lazumi, ta ji muryar da ko a mafarki ba zata manta mai ita ba. "Ina amaryar tamu, yau Allah ya yi zamu haɗu, na ji kunya ni ban je ba su gasu a garinmu" Raihan da yake bawa yaransa madara ya ce "Aikuwa dai kin ji kunya yasin, kuma na daina uwar ɗakin da ke" "Amma dai ka san uzurina, bama gari amma tuba nake, dolena na je Kano, Mummy ki taya ni bayar da haƙuri" Hajiya Aisha ta ce "Kun fi kusa ni babu ruwana". "Anty Na'ima" ummi ta yi maganar cikin rawar murya. Na'ima ta waro ido ta ce "Ummi, ummi ke ce" da gudu ummi ta ƙarasa jikin na'ima suka rungume juna, ummi na kuka" Na'ima ta ɗago ta ce "Ummi, dama zan sake ganinki? Kan rasuwar mama duk lokacin da na je gagarawa sai na tambayeki, ace mini ki na kano, bayan rasuwar mama na daina zuwa, ummi me ki ka zo yi nan, zan sake ganinki dama". Mummy ta ce "Ikon Allah, ai ita ce matar babban mutum" Na'ima ta waro ido ta ce "Alhamdilillah ala kulli halin, Allah kai ne abun godiya, ummi na san ba zaki wulaƙanta ba a rayuwa, raihan ummi ƙanwata ce, dan Allah ka ƙara riƙe mini ita da kyau, ta sha wahala a rayuwa" Raihan dai ya din ga bin su da ido, da ƙyar suka bar kukan. Na'ima yaron mijin Hajiya Aisha take aure, shi ne, shi ne babban yaronsa, dan shi ne babban manager, kuma lokacin da raihan ya zauna a bauchi, gidanta yake zuwa yawon cin ɗan wake, suna zaman mutunci sosai. Ummi ta fara basu labarin, gudunmawar da take iya tunawa, da Na'ima ta yi mata a gagarawa. Raihan ya ce "Salma, ku daina tuna abun da ya wuce, anty na'ima in dai ummi ce, ba zan sake barin tayi kukan wahalar rayuwa ba". Na'ima ta ce "Ummi ina Anty mariya?" Nan ummi ta bata labarin suna tare, da yadda gagarawa ta koma. Ai har kusan sha biyun dare, Naima suna tare da ummi, kuma ta yi wa ummi alƙawarin zuwa kano. Kwanansu biyu a bauchi, suka tafi Maiduguri. Mariya sai ɓoye-ɓoye take yi, dan kar a ga cikinta, ita kuwa ummi tuni ta gano ta. Gagarumin taron family aka shirya, ƙaton hall na gaske, da ya haɗa da manyan mutane daga sassan ƙasar nan, wanda suke duk ƴan uwa ne, ba tare da sun san ƴan uwa bane ba. Riahan ma yana wurin, noor ta ce "Yaya ummi, kin ga har da larabawa a ƴan uwanku". Aka rarraba musu sovenir, wanda a ciki yake ɗauke da littafi da ya bayar da asalin su. Asalin mahaifin kakan su mariya ta ɓangaren uba, balaraben ƙasar tunus ne. A yawon fatauci ya auri wata ƴar somalia, ya taho da ita Nigeria, yawon fatauci, jin daɗin zamansa a Nigeria, ya sanya ya cigaba da zamansa a Nigeria, ya auri wasu matan ya hayayyafa. Bayan rasuwarsa, galibi duk suka kama gabansu, ita ta somalia ta koma ƙasarsu, manyan ƴaƴanta da suka riga suka girma a Nigeria, basu bi ta ba suka yi auratayya a Nigeria, duk suna jin turanci, larabci da wasu yarukan na Nigeria. A taron har da ire-iren dangin su na tunusiyya, da wasu daga cikin dangin matar nan ta somalia. Kuma ɓangaren su ummi, suka faɗo a ɓangaren matar nan ta somalia. Ta ƙaton allon majigin da yake ɗakin taron, aka din ga nuna hotunansu, wanda da ka kalla ka san na da ne, sai dai da aka zo kan matar nan ta somalia, duk da tsohon hoto ne mai black and white, sai da na kusa da ummi suka juyo suna kallonta. Kamarta ɗaya da matar, sai dai shi mutumin, brown ɗin gashi ne da shi, haka zalika yaron hannun raihan aiman kamarsa ɗaya sak da mutumin. Raihan ya ce "Allahu Akbar, sweetheart ashe can ki ka tafi ƙarshen dangi, ki ka kwaso mana kamannin larabawa. Su Aiman ma haka" Ummi na zaune ta ga an fara zagayeta ana kallonta, sai larabci ake yi mata a ka. Aka kamo hannun ummi, aka fita da ita kan stage, tare da sake nuna hoton matar nan, a ƙalla kakarta ta huɗu kamanninta ta ɗaukko. Sai da mariya ta yi kukan daɗi, mussman idan ta tuna yadda aka din ga wulaƙanta mata ƴa, da iƙirarin cewa ba ƴar su ba ce ba. Galibin wanda suka zo taron daga somalia, duk brown eyes ne da su, irin na ummi. Sai taro da kallo ya koma kan ummi, aka din ga ɗaukar hotunanta, duk yadda raihan yake kaffa-kaffa da yaran nan da matarsa, haka ya zuba ido yau, dan sosai yaran suke kama da wannan mutumin na tunusiyya. Gaba ɗaya taro ya koma kan ummi, aka din ga basu kyaututtuka da ita da yaran, aka ce har gidanta za a bayar da wakilci, aje a ga in da take zaune, kuma za a bata muƙami a shugabancin jagorancin haɗa kai da tattaro kan sauran iyalan. Ba ummi ba har raihan da mariya sai da aka gabatar da su a wurin, aka gabatar da shi a matsayin MD na Tahir and son's. Ummi ta ga manyan mutanen da ba ta taɓa tunanin ganinsu ba. A matuƙar gajiye ummi suka koma gida, da a ranar raihan ya ce su koma kano, amma gajiyar da suka yi sai da suka bari su kwana. Labari har a gidajen jaridu da radiyo, aka haɗa hotunan ummi da na matar mai suna Alina, da kuma su Aiman da balaraben tunus, yadda yara suka ɗaukko kamanin kakansu na biyar. Kuɗi kuwa ummi ta same su, Alhaji Tahir suna kano ya kira raihan, yana gaya masa suna gida suka ga taron su ummi. Ummi dai a satin sai da ta zama cele, ko ina zancenta ake yi. Kamar yadda ummi ta buƙata, dr. Ya yafewa inteesar kuma ya ce ta cire tunanin tsohon mijinta daga ranta, ta gama idda, zai yi ƙoƙarin ganin ta koma makaranta. Raihan da kansa ya je gidan su, ya samu mami ya ce "Mami, ina fatan zuciyarki ta wanke daga zargin da ki ke yi, na cewar su aiman ba yarana bane ba" "Na ji, ni matarka ce ba na ƙauna, kuma ba zan taɓa ƙaunarta ba" Ya ce "Na sani, ita ma ta gaya mini na daina wahalar da kaina ba zaki taɓa ƙaunarta ba, amma ina roƙon kar hakan ya shafi yarana". Tayi masa banza ba ta kula shi ba. Na'ima sai da ta zo Kano, gidan ummi, har wurin mama suka je. Mariya ta ji daɗin haɗuwa da Na'ima sosai da sosai. An kawo lefen nihal, sai dai wasu abubuwan duk babu, tun da kuɗi ya bata ta haɗa abun ta da kanta, ya zo ya ɗauka ya kai gidansu aka kawo. Sai dai babarsa da yayyensa duk suka ciccire wasu abubuwan, ita kuwa ta ce masa ko dai a dawo da abubuwan da aka cire, ko kuma ta fasa. Ya je gida yana masifa, uwar sa ta ce idan ba sa so, ya je ya karɓo kayan, tun da ba ƴar gold ba ce ba. Aka din ga kai ruwa rana, Mami ta ce su zo su kwashi tsiyarsu. Alhaji ya ce ba za a mayar da shi ƙaramin mutum ba, neman auren ƴar sa a hannunsa yake ba hannunta ba, dan haka ba za a mayar da lefen ba, shi zai sayi abun da babu a saka. Hajiya kuwa suna ta shirin bikin Salim, ɓangaren ummi ma, ita da mariya ke ta shirin bikin noor, farida ta zama ƴar kallo. Rahama ta warke, sai dai ga zawarci, ga inteesar ga kausar duk a gabanta. Ummi da ta je ta ga Iya, ta tsorata. Gaba ɗaya kamaninta sun sauya, jikinta har saɓa yake yi saboda tsabar kwanciya, ba a ɗaga ta a gyara mata jikinta. Ga ɗakinta duk ya rushe, ga kuma abun da aka ce Idris yayi, ƴar sa nana ma ta gudu, babu wanda ya san in da take. Watan ƴan biyu shida, mariya ta haifi ɗanta namiji, murna a wurin dr. Ba a magana, aka saka masa sunan baban ummi. Ummi na ta shirin auren ƙanwa, kuma ƴar da ta raina, sai haɗeta ta take yi da kayan gyaran jiki kala-kala, tare da yi mata nasiha da addu'a. Noor da sassafe bayan raihan ya fita, ta samu ummi ta ce "Yaya ummi, kin san meyafaru?" "A'a" "Muna waya da shi da asubar nan, yake gaya mini wai yayar raihan, jiya da daddare ta dawo gida" Ummi ta ce "Maybe zuwa ta yi ganin gida" Noor ta ce "Akwai magana, gaya mini ne ba zai yi ba, ba ganin gida ta zo ba, ban tambaye shi ba ya fara gaya mini, bai kai ƙarshen labarin ba ya wani maze ya canza labarin. Ni ya fara bani tsoro ma" Ummi ta ce "Tafi can, ba wani tsoro kar ki yadda mijinki ya baki tsoro, abokin rayuwa ne, kuma aure tausasawa ce a ciki. Nima fa kan na yi aure sai da ya fara bani tsoro, yadda ya canza mini, amma daga baya komai normal" Sai dai da azahar bayan raihan ya dawo, yake gaya wa ummi cewar, Maryam ta kama mijinta da wata a gidanta, tayi magana ya kamata yayi mata dukan tsiya, jikinta duk jini ta ɗaukko mota ta taho gida. Ummi kuwa ta jajanta ta ce Allah ya kyauta. An kai ruwa rana sosai da sosai, maryam ta ce ba zata koma gidansa ba, ta daɗe tana zarginsa ba ta tabattar ba, sai da ta kama shi red handed. Ana tsaka da case ɗin maryam, aka yi auren nihal, sai dai a yanayin yadda aka yi bikin, zaka san iyayen mijin ba su da kirki. Aka jinkirta buɗe kamfanin su raihan na Abuja, sai an yi auren Salim. Alhaji ya yanke raihan ya koma Abuja, Salim ya riƙe Kano. Raihan ya ji daɗin hakan, saboda Ummi ta samu chance na reapplying aikin gidan jaridar, da suka taɓa gayyatar ta ya hana. Lokaci-lokaci inteesar na zuwa gidan ummi, ummi kamar babu abun da ya faru, haka za su yi hira su ci abinci, ta kawo alkhairi ta yi mata. Ta kan yi amfani da damar, wurin nemawa farida afuwar ummi. Ba yadda ƴan gagarawa ba su yi da ummi ba, da dr. Akan su taimakawa Idris, a fitar da shi sharri aka yi masa, ummi ta ce babu ruwanta. Dr. Ya ce kar wanda ya sake kiran ummi, ya ce tayi masa wani abu, ba zaman kanta take yi ba, a ƙarƙashin wani take. Tun ana ƙoƙari a kan case ɗin nasa, har aka ɓatar da file ɗin shari'arsa. Ummi da za ta bar kano, gaba ɗaya furniture's ɗinta, raihan ya canza mata. Ta ɗauki nata ta bawa mama, na mariya kuma masu kyau, ta bawa matar yaya magaji. Bikin noor ne kawai ya zaunar da ita, aka yi gagarumin biki, aka din ga taya Hajiya murna, an samu Salim yayi aure. Duk irin tarin miskilancinsa, da rashin son wargi, sai da yaba wa noor, dan ummi ba ƙaramin ƙoƙari ta yi a kanta ba. Farida tana ji tana gani, ga ta amma Abdul, inteesar, ko noor idan suka tashi neman shawara sai dai su nema a wurin ummi. Kuma su ka koma suna girmama mahaifiyarta, dan har gidanta suke zuwa. A danginsu da aka yi taron family, sai da suka cika alƙawarin zuwa gidan ummi, bayan ta koma Abuja. Ta samu aiki, a sashen hausa da turanci na gidan talabijin na Chinese da yake Abuja. Iya ta sha baƙar wahalar jinya, kafin Allah ya karɓi rayuwarta. Duk girman kan farida, sai da ta koma ta kwantar da kai, tana bin ummi, saboda rufin asiri da arziki da Allah ya yi wa ummin. Dan sai da Mariya ta je aikin Hajji ta kai dr. ta kai farida umara. Ta saka raihan ya mayar da Abdul Abuja, yayi aure a can. Maryam ta samu ta sake aure na biyu, babu kwanciyar hankali. Nihal ma haka ta din ga fama da nata dangin mijin. Barin ummi kano, har mantawa take yi da matsalar mami. Noor kuwa lafiya ta zauna da salim, ya nutsu kamar bashi ba,hajiya ma ta riƙi noor kamar ƴa. Ummi ta cigaba da hayyafa da raihan, shima kuɗi ya zauna. Mariya ma yara maza uku ta haifa wa dr. Ummi ta cigaba da rayuwarta hankali kwance, kamar babu wani abu mara daɗi da ya taɓa faruwa a rayuwar ta. Tammat bi hamdillah *DUKKAN YABO DA GODIYA, DA JINJINA DA KIRARI SU TABATTA GAREKA TSARKAKKEN SARKI, UBANGIJIN TALIKAI* *INA MIƘA TARIN GODIYA, DA JIMIRIN BIBIYATA DA KU KA YI A WANNAN TAFIYAR, INA FATAN DARUSSAN DA KE CIKI, ZA AYI AMFANI DA SU, AKASIN HAKA KUMA UBANGIJI ALLAH YA YAFE MANA BAKI ƊAYA, KUMA INA FATAN ZAKU YI WATSI DA SHI* *JAMA'AR DA SUKA BANI TALLACE-TALLACE INA GODIYA, MASU ADDU'A DA FATAN ALKHAIRI, KUMA INA GODIYA* *A MADADIN BRIGHT PENS, INA SAKE MIƘA GODIYATA GA AL'UMMAR DA SUKA BIBIYE MU, A LITATTAFAN CUTARWA! MUNAFUKIN MIJI DA KUMA YI WA KAI. INA FATAN ZAKU BIBIYE MU A SECOND BATCH, DOMIN JIN, ME ZAMU ZO MUKU DA SHI* *Ƙofata a buɗe take, dan jin darussan da ku ka ɗauka, in da littafin ya samu naƙasu da sauransu ina godiya sosai, taku har kullum Aishatu Adam (Ayshercool)* Ayshercool 08081012143 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 54 of 54