sannan ta ɗora da cewa "Ke ma ki ji idan da daɗi abun da ki ke yi wa taki sirikar, saura maryam dan ubanta, zan iya wanke ƙafa na je har fatakol ɗin, ba a barikin soja ba, idan a cikin bindiga take na je na ci ubanta a kan matar raihan. Raihan ɗin sai ka ce wani ɗan gwal da ake ta wannan tsiyar a kansa, ita ba uwa ce tayi naƙuda ta haifeta ba? Da ki ke mata iƙrarin munin ke halitta ki ke yi, da hancinki kamar pipe ɗin ruwa. Mu danginmu bamu sabawa yi wa sirikai rashin daraja ba, dan haka ba zaki fara ba. Tun wuri ki samu rakiyar ki yi mata bayani, idan kuma ki ka bari na yi mata abun ba zai yi muku daɗi ba".
Duk da haka sai da suka yi faɗa da Alhaji, yayi mata ƙorafin za ta mayar da su ƙanan mutane.
Bayan su hajiya sun tafi ta ce masa "Yarinyar nake yi wa gata, na lura matar raihan irin matan nan ne da ba kowace irin mace za ta iya gogayya da su ba a kishi, ai ko ba ƙarara ba yana faɗa, kai ka sani, idan aka yi masa auren dole matar wahala kawai za ta sha, shi wannan dai da ake yi wa kallon mummuna ita ce tayi masa, da azo ya auri ƴar mutane ta wahala a banza ai gara ba ayi ba".
Ya ce "Na nuna wa bilkin haka, amma taƙi ganewa, kuma uwar yarinyar ce take zigata, amma tun da ke tana tsoranki, ƙila ta ji.
***
Dr. Kuwa kwanansu uku a uganda, dama akwai abokinsa da yake zaune a can yake lecturing, kasancewar babban gida ne sosai da gwamnatin ƙasar ta bashi, a wani sashe na gidan dr. Yake zaune.
Kamar wanda ya auri yarinya ƙarama, haka yake jin kansa, ya tuna abun da farida ta ce na ba uwar da za ta tsinana masa, amma ya ga abun da bai yi tsammani ba.
Tun ranar da suka je, take mugun jin kunyarsa, ko kallonsa ba ta iya yi, da safe idan ta gaishe shi, komai zai ce mata sai dai ta bashi amsa da ka, amma ba zata yi magana ba, kamar ya auri budurwar ƙauye.
Shi gaba ɗaya ma dariya take bashi, jin sa yake hankalinsa a kwance ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali, saɓanin idan yana tare da farida, da wani lokacin rashin mutuncinta ba ya motsawa, sai yana buƙatar ta, sai ta tsiro da na ta buƙatun, sai ya yadda zai yi, koma ya yi mata sannan ta yadda da shi, kamar masu zaman dadiro ba aure ba.
Ya zuba mata ido, ta koma gefen kujera tana ta sinne kai, ya ɗaukko wayarsa ya duba ummi na online, ya kirata voice call.
Mariya na jin muryar ummi, ta tattara hankalinta a kansa.
Suka gaisa da dr., Yake tambayar ta ko sun je duba Iya, ta ce masa a'a sai cikin satin.
Mariya ta ƙura masa ido, ya ce "Ko in baki ku gaisa?" Ta jinjina masa kai da sauri.
Ta matsa kusa da shi ta karɓi wayar, ta saka a kunnenta ta ce "Ƴar baƙa kyakykyawa"
Ummi ta yi dariya ta ce "Mama Amarya"
Ta ɗan tsuke fuska ta ce "Zan ci gidanku"
Ummi ta yi murmushi ta ce "To ya ugandan? Kin fara jin yaren su"
Ta ce "A'a ni ban taɓa fita ba ma, amma daga nan gidanki ba nisa ko? Ai zan iya zuwa"
Ummi ta ce "Haba mama, ba fa Nigeria ba ce ba, ba ki ga sai da ku ka hau jirgi ba"
Ta ce "Eh to haka ne, to ya cikin naki ashe kin kusa haihuwa"
Ummi ta yi sauri ta kashe wayar dan kunya, tun da mama tazo manyan riguna take sakawa da hijjabi, dan kar ta ga cikin, kuma har ta gama kwanakinta ba ta nuna mata ta ga cikin ba sai yanzu.
Ta kalli dr. Ta ce "Ka ga na daina jin ta, ɗan dubo mini ita"
Yayi dariya ya ce "Kunya ki ka bata ta kashe wayar, ina ruwanki da cikinta" yayi maganar yana matsawa daf da ita.
"Ni mamaki ma nake yi, har ummi ce da ciki, ohh kwanci tashi asarar mai rai. Aka yi ta cewa ba zata yi aure ba, gashi ma har za ta haihu"
Dr. Ya ce "Eh haka lamarin Allah yake, amma dai dan Allah ki daina guduna, ni ba dodo bane ba, yanzu saboda maganar ummi ce shi ne ki ka kula ni, bayan tun safe kin ƙi kulani"
Ta sunkuyar da kai kamar ta yi layar zana ta ɓace.
Ya ɗago haɓarta, amma ta ƙi kallonsa.
Yayi murmushi ya ce "Zo mu tattaka, mu je kasuwa ki ga garin" ya riƙe hannunta ta tashi tsaye, suka nufi bedroom.
Kusan kwana huɗu, da Abdul ya tura kuɗi, kawu Ilyasu ya kira Abdul yana tambayar sa, wai shiru fa ba su ga kuɗi ba, jikin Iya yana tsamari, za a sallame su ma saboda rashin kuɗin.
Abdul ya ce "Ai tun a ranar na tura dubu tamanin, dr. Bai hau jirgi ba sai da ya tura mini kuɗin, ni kuma na ƙara na tura".
"To ya haka? Idris ya ce ba su shigo ba".
Abdul ya ce "A'a dai, ya sake bincikawa, dan ta application na tura kuɗin"
Ya din ga mamaki, ya duba wayarsa har da receipt kuɗi sun fita.
Washegari tun da safe suka shirya, raihan ya je Abuja, noor da Abdul sai ummi suka tafi Jigawa duba Iya.
Sai dai da suka je asibitin, sai da ummu ta ɗan tsorata, Iyan duk ta zama abun tsoro, fatarta ta yamushe, gashi an aske gashi, duk an liƙe kan da bandeji, hannunta da ƙafrta ma haka, idonta yayi ja saboda azabar ciwon kai, ba ayi hoton ƙwaƙwalwa ba, balle a san menene yake faruwa.
Noor ta ce "Kai na ga iya ta koma kamar simigul"
Abdul ya galla mata harara, ummi ta ce "Sannu iya ya jiki?" Iya ba baki sai kallon ummi da take yi.
Ta kalli amaryar kawu Ilyasu ta ce "Ga abinci mun zo da shi a bata, amma kunu ai ba zai riƙe ta ba".
Suna nan zaune su kawu Sagir suka zo, aka gaggaisa, ake sake mayar da yadda aka yi, kuma ummi ta yi musu kwarjinin da suka kasa yi mata zancen auren dr., Sai magana suke yi mata da girmamawa.
Ummi ta ce "To shi Auwwalun an kama shi an hukunta shi, ko kuwa?"
Amarya ta ce "A'a ya gudu"
Ummi ta ce "Kodayeke ba hurumina bane ba, tun da dauɗar gora ciki ka sha ta, da na saka an nemo shi, wannan dauɗar yakamata iya ta shanye ta, a rufa masa asiri ai ɗan so ne "
Aka rasa wanda zai yi magana, Idris yayi sallama, suka amsa, sai dai hankalinsa ya tashi ganin su ummi.
Ummi ma zaune har da ciki, kayan jikinta ya isa ya saye nasu gaba ɗaya har da canji.
Sai gashi ya risuna yana gaida ummi.
Abdul ya ce "Malam Idris, na turo kuɗi aka ce ba ka gani ba"
Cikin kame-kame ya ce "Eh wallahi, ba su shigo ba"
Abdul ya ce "Kawo wayar ta ka in duba balance" ga waya a hannunsa babu damar yin ƙarya, ya miƙawa Abdul.
Yana duba messages, ya ga alerts, yadda Idris ya din ga cire kuɗi, ga tsohuwa a kwance a asibiti ciwo zai kashe ta!!!
Ayshercool
08081012143
Masu neman daga farko, dan Allah ku yi haƙuri ku duba a watpad, ko ku tambaya a groups whats app ɗina ne yayi expire, bani da shi a what's app 🙏
Masu son a tallata musu hajar su a what's app channel ɗina, should contact me, ina godiya sosai da jimirin bibiyata.
*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*
CUTARWA!
AYSHERCOOL
(BRIGHT PENS)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
48
Cikin tsananin takaici, Abdul yake kallon Idris da yake ta rarraba ido, kamar an kwashe wa karya ƴaƴa.
"Amma ga alert ɗin da banki suka yi maka, na kuɗin, kuma sannan ga wanda suka yo maka kana ta cirar kuɗi, ga sunana da komai da sunan bankina".
Nan ƴan ɗakin suka hau salati da salallami, iya ta ɗago idanunta da suka yi ja, saboda azabar ciwo da wahala, ta kalli Idris kawai ta sunkuyar da kai.
Wata ƙanwar iya ta fara masifa ta ce "Amma Idris an yi mutumin banza, kana kallon yadda matar nan take kwana tana wayyo ciwo, an rasa kuɗin yi mata abun da yakamata, saboda kai azzalumi ne ka cinye kuɗi ka ce ba a turo maka ba, yanzu duk soyayyar da iya take nuna maka wannan ne sakamakon abun da zaka yi mata?"
Yaya magaji ne yayi sallama, suka amsa masa, ya kalli yadda suka yi jugun-jugun ga dai iya a zaune, balle ya ce mutuwa ta yi suka jimami.
Suka gaisa da kowa, suka gaisa da ummi cikin girmamawa, sai dai bai ko kalli in da Idris yake ba, dan tuni ya daina yi masa magana ba ya shiga harkarsa.
"Wai lafiya na ga kowa ya yi shiru?"
Kawu Ilyasu ya ce "Ɗan uwanka ne ya cinye kuɗin da aka turo masa ayi wa Iya magani, yayi magana ma ya ƙi yayi shiru"
Hashim ya ɗan kwaɓe baki ko a jikinsa, dan gaba ɗaya yana danasanin kasancewarsa a tsatson iya. Da ƙyar matarsa take tursasa shi ya zo dubata.
Ya ce "To Allah ya kyauta, ai da sauƙi tun da shi ya ci ba wani ba, balle a tsine masa na hannun daman ta ne"
Kawu sagir ha haɗe fuska ya ce "Wane irin iskanci ne wannan? Uwarmu na kwance ba lafiya kuna faɗar abun da ku ka ga dama"
Ummi ta ce "A'a kawu, Allah ne ya kawo wa iya lokacin shan dauɗar gora, dan duk wanda zai sha barinta ne, ita da take yawan faɗa, kuma da sauƙi tun da shi ya ci ba wani ba, sai ta fi jin daɗin shanyewa"
Abdul ya kalli ummi yana girgiza mata kai, amma tayi burus da shi, dan lokaci yayi da yakamata ta amayar da damuwarta, ayi mata fyaɗe amma iya ta ce a rufa dauɗar gora ciki ka sha ta. Duk wani abu in dai a kan Idris ne ko son zuciyarta, sai ta ce dauɗar gora ciki ka sha ta. Ita ma gashi Allah ya kawo nata lokacin.
Kowa ya din ga tofa albarkacin bakinsa a kan Idris, yayi shiru ya kasa magana.
Wata maƙwabciyar su idris, mai suna ɗahara ta zo duba iya, sai dai matar kamar ba ta da saiti, kamar wadda ta taɓa hauka, saboda yadda take magana take sakinta yadda ta ga dama.
Cikin tsantsar ƙauyanci da rashin iya magana ta ce "Kai Innalillahi wa... me ye ma ƙarashen na manta, Iya haka ki ka koma? Wannan naɗai da aka yi miki a ka, kamar shugabar bokayen gagarawa? Rayuwa kenan, ai baban Nana, gidanka da na higa kan na taho, na ce wa Shindatu ta zo ta rakoni na duba gyatumar nan Iya, amma ta ce mini wallahi ba za ta zo duba tsohuwar banza da ba ƙaunarta take yi ba.
Nana ta ce Allah ya sa daga Asibitin nan ba za a maidota gida ba, na ce ke Shindu ki ji tsoron Allah, da gyatumar ki ce a ba kya ce haka ba". Ta yi maganar tana dariya, kamar abun da ta faɗa ɗin ba wani abu bane a wurinta.
Ta sake cewa "To dai jin abun da suka faɗa, ya sa jikina yin sanyi na taho, to Allah dai ya bata lafiya, ni dai idan ta warke to, idan ba ta warke ba dai dan Allah ina bin ta jaka ɗaya da muttala biyu kuɗin surfe na, gara a fara sauke mata nauyi tun tana raye".
Hashim ya saka hannu a aljihunsa, ya ɗaukko ɗari biyar ya bata ya sallameta.
"Amma dai ka kyauta, wallahi gara ku bincika, Iya akwai shegen cin bashi, kuma ba ta biya, sai dai wani ka yi mata Allah ya isa ka ga hakan kuma ai bai yi ba"
Kawu Ilyasu ya ce "Ke dan Allah ki tafi ki bawa mutane wuri, mahaukaciya kawai"
Ta soke ɗari biyar ɗin ta, ta fita tana dariya.
Babansu ya kalli Idris ya ce "Ka ga illar bujirewa iyaye ko? Matar da aka aura maka, ka wulaƙanta ta bayan ka yi abun kunya, ga wadda ka ke so ɗin abun da take faɗa a kan kakarka, mun gode amma in Allah ya yarda zaka gani, kuɗin nan da ka cinye sai sun hanaka kwanciyar hankali " aka din ga bashi haƙuri, a kan kar ya yi wa Idris baki.
Ummi ta ƙara tsorata da lamarin rayuwa, da yadda take tsoron Iya da Idris, abun ba a cewa komai, amma kallesu yanzu abun tausayi, da gari banza ne da iya tana nan tana ta zagin jikokinta tana tsine musu da sun motsa, ga tsinuwar nan tana ta tasiri a tsakanin su yanzu.
Ummi ta tashi ta fita tana amsa wayar raihan, a ƙalla ta kai mintuna arba'in, sai ga ta dawo da receipts a hannunta.
Ta miƙawa ƙanwar iya ta ce "Gasu nan, na biya duk abun da yakamata ayi mata, za su yi mata".
Ta waiwaya ta kalli Idris ta ce "Kai kuma, daga nan zan je in kai ƙararka wurin ƴan sanda, duk in da kuɗin nan suke ka dawo da su, dan ba wanda za a ƙara tursasawa shan wata dauɗar gora, da ake shanye ta wasu a ƙi shan ta wasu, shi ma auwwalun duk in da yake sai an nemo shi"
Kamar su shige cikin ummi, suka din ga zambaɗa mata godiya, Iya kuwa ta ƙure ummi da ido.
Ummi ta zauna a kusa da ita, ta ciro kuɗi, ta saka mata a cikin hannunta ta ce "Na san da magana a bakinki iya, amma ki sani ban yi miki wannan abun, dan na burgeki ba, ko ki so ni, bana fatan ko da ƙiftawar ido na yi abun da zai saka ki so ni ko na burgeki, tun da wanda na yi a baya ma babu riba.
Na yi miki ne kawai saboda zatin Allah, kuma saboda kin haifi mahafina, mutumin da ki ka azabtar kamar ba ke ki ka haife shi ba, saboda abun duniya, saboda waɗan nan" tayi maganar tana nunawa Iya kuɗin hannunta.
"Yanzu dai ba ya duniyar, mummunar ƴar sa da baki tabattar ko daga tsatsonki take ba, cikin hukuncin Allah ya rufa mata asiri. In sha Allah ba zan bari ki yi wulaƙantcciyar jinya ba, saboda babana bai wulaƙanta mini uwa ba, ke ma ba zan wulaƙanta ki ba, amma ki sani hakkin zuriyarki da ki ka raba kansu da kanki ne, ki ka gama tsine musu yake bibiyar ki.
Allah ya baki lafiya, duk abun da Allah ya yassare mini, zan din ga turawa yaya magaji"
Kamar munafukai haka duk suka duƙar da kai, ta gama maganganun ta, ta tashi ta ce wa su Abdul su tafi.
Idiris hankalinsa ya tashi da ya ji ta ce ƴan sanda, dan ya tsorata da lamarin ummi, tun da ta saye gidansu na gado.
Abdul suna tafe a hanya, suna tattaunawa a kan yadda familynsu yake ƙara rushewa, saboda jahilci da rashin background mai kyau.
Can uganda dr. Ya cigba da karatunsa, idan baya nan yaran abokinsa suna shiga su taya mariya zama. Duniyarsa kawai yake ci da tsinke, yana samun duk abun da yake so daga gareta, ba tare da fargabar tashin hankali ko abun da za a buƙata daga gare shi ba.
Sai dai ƙasan zuciyarsa babu daɗi, yadda kausar da inteesar suka haɗe kai da babarsu, suka daina shiga sabgarsa, ko gaishe shi da suke yi a waya suka daina, daga noor sai Abdul sune suke ta tasa, sai kuma ummi.
Dan ƙarewa ma farida blocking ɗin sa ta yi a what's app.
Tun abun yana damunsa har ya watsar, ya cigaba da addu'a tare da rungumar amaryarsa hannu bibbiyu, ya ji hakam kamar samun salama ne daga rashin mutuncin farida.
Ga mariya da tsantsar ladabi, dan haryanzu wasu lokutan abubuwan ta irin na da take yin su.
Bayan tafiyar ummi, a ka yi wa Iya hoton ƙwaƙwalwa, cikin kanta lafiya ƙalau, sai dai tsananin damuwar abubuwan suke faruwa ya sanya jininta yin mummunan hawa.
Likitoci suka yi iya bakin ƙoƙarin su, aka sallamota a kan magunguna.
Bayan sun koma gida, aka kwantar da ita aka shiga jinya, saboda ba ta iya yi wa kanta komai, ita ma jinyar tun da aka yi mata ta marmari, aka fara ƙosawa.
Idris kuwa ya din ga bin ƙannen babansa yana roƙonsu a kira ummi, a bata haƙuri kar ta kai shi wurin ƴan sanda.
A ranar da ya koma gida daga asibiti, ya samu hindu ya din ga zaginta da ci mata mutunci, a kan maganganun da ɗahara ta ce ta faɗa a kan Iya.
Hindu ta ce "Duk tsohon dai bai ji kunyar hawa jaki ba, jaki ba zai ji kunyar kayar da shi ba, tun da ba uwata ba ce ta je ta mutu ba abun da yayi mini zafi, matar da ba ta da mutunci. Wai kai har ka na da bakin magana ma, tun kan ka dawo har gida aka zo aka bani labarin ka cinye kuɗin maganinta, kai ba ka ga laifinta ba sai nawa, sai ka fara yi wa kan ka masifar ai"
Kamar yadda suka saba, haka suka yi ta faɗa su na cece ku ce.
***
Anty rakiya kuwa, ta samu mami ta din ga surfa mata bala'i, ta in da ta shiga ba ta nan take fita ba, wai ta biyewa tsoron dangin miji, za a raba musu zumunci.
Ta ɗauki gaba da ita, gaba ɗaya ta rasa abun da yake yi mata daɗi, ta na ji tana gani raihan yanzu ya koma mata kamar wani baƙo, sam ba ya sakewa da ita, saboda kar ta yi wata magana a kan ummi, kusan abun da take gudu shi yake shirin faruwa, ummi ta mallake mata ɗa.
Dan labari yana isheta cewar, kullum raihan status ɗin sa, yabon ummi ne tare da koɗata, dan ita ya riga ya rufeta daga gani.
Ta fuskanci sam fushinta da shi ba ya tasiri a kan sa yanzu, dan ya fi zuwa wurin hajiya ma yayi al'amuransa, ga wata irin muguwar shaƙuwa tsakaninsa da Salim yanzu har ma da Sagir.
Hakan ya ƙara mata tsananin tsanar ummi, da duk da abun da take yi wa ummin, ta kan kira waya ta gaisheta, tayi girki ko ta bayar da abu ta ce a bata, ta wulaƙanta amma tun da abun nan ya faru, ummi ba ta ƙara shishshigin raɓar in da take ba.
Aka gama gyaran gidan dr. Da idan sun dawo za su tare da mariya, daga can ƙasar ya turowa ummi kuɗi, a kan ta yi mata sayayya ta haɗa da kuɗaɗen hannunta, ta din ga yi mata sayayya.
Dan ba ƙarya hannun raihan a sake yake, kuma yana sakar mata yadda yakamata, kuma ita ma na ta hannun a sake yake.
Tun da aka yi scanic aka tabattar wa su ummi, yara biyu ne a cikinta, raihan yake murna, kuma ya gargaɗe ta a kan kar ta kuskura ta gaya wa kowa.
Suka yi ta shiri, tare da sayen kayan jarirai.
Sai dai cikin yana wata bakwai, kamar ummi za ta durƙusa ta haihu, saboda girma, kullum cikin lissafin kwanakin da suka rage take yi, saboda yadda nauyin cikin yake damunta, idan ta zauna sai an ɗagota saboda girman cikin.
Gefe guda kamar yadda ta yi alƙawari, tana tura wa yaya magaji kuɗi lokaci zuwa lokaci, saboda kula da Iya.
Farida ba ta haƙura ba, wurin bin bokaye da malamai, a kan lallai sai an raba auren dr. Da mariya, kuma a sake mallake mata shi ta juya shi fiye da yadda take yi a baya.
Sai dai abun da ba ta sani ba shi ne, duk da kallon mahaukaciya tuburan take yi wa mariya, a hakan ba ta wasa da addu'a, mace mai son addini sosai da sosai, dan yana ɗaya daga abun da ya sanya ta ƙara shiga ran dr. Sosai da sosai.
Hajiya ita ta maye wa ummi gurbin sirika, dan kusan har role ɗin uwa take yi mata playing, kusan kullum tana tafe zuwa duba ummi, ko yi mata aike take, tana tausayin ummi sosai da sosai, saboda abu ne na fari ba ta san ya yake ba, tana yawan cewa ummi "Anya ummi ba zaki likitoci su ƙara caje cikin nan ba, girmansa yayi yawa tubarkallah" sai dai tayi murmushi, ba tare da gaya mata haƙiƙanin abun da yake cikin ba.
Ummi ta daina fita ko ina, gashi ta ƙara zama mafaɗaciya, saboda damuwar ciki. Kasancewar Hajiya na gaya wa raihan sai yayi haƙuri da ummi, a wannan stage ɗin mata masu ciki na fuskantar saurin fushi, dan haka sam baya damunsa, shi tausayi ma take bashi.
Duk tsaftar ummi, sai da zamana dogon gashin nan sai ya kwana uku babu taza, kusan kullum sai dai ta saka kaya masu sauƙin nauyi yadda iska za ta wadace ta, takalmi kuma idan ba over size ba duk haushin takalman take ji.
Da safe ta fito, tana ta mita noor ba ta ɗumamata shinkafa ba, wai ita ba ta cin abun da ta dafa.
Noor ta ce "Ke fa ki ka ce ba kya son warin shinkafa"
Kamar tayi kuka ta ce "Haba noor, amma tun jiya na ce miki zan ci, yunwa nake ji, ina magana kina kallo kin yi mini banza"
Noor ta ce "Ai Yaya ummi ban san yaya zan yi miki na burgeki ba, MD ne kawai yake iya miki, ni ba ni na ɗora miki nauyin cikin nan ba, amma ki yi ta yi mini faɗa. Kuma sai na koma gida tun da faɗa ki ke yi mini"
Ummi ta marairaice ta ce "Haba noor, to ki yi haƙuri dan Allah kar ki tafi, wai ni ya ku ke so in yi?"
Raihan da yake bayanta ba ta sani ba, ya kama dariya, ba wuya ta bayar da haƙuri, ba wuya kuma ta fara kuka.
Ciki duk ya mayar da ita wata iri, sai dai bai sanya ta daina kyau a idonsa ba.
Yayi gyaran murya ya ce "Ya aka yi ne yau ke da noor ɗin taki ku ke faɗa"
A shagwaɓe ta ce "Wai tafiya za ta yi"
Ya ce "Haba nooriya, uwa guda ki tafi ki bar ƴar ta ki?"
Noor ta tura baki ta ce "Faɗa take yi mini, kai ma fa shaida ne ta ce ba ta son shinkafa, wai yau kuma shinkafa za ta ci, wai ta gaya mini jiya da daddare, ni ina na ganta jiya da daddaren?"
Ummi ta ce "Ni duk kun tsane ni, baku san me nake ji ba, ko tausayina ba kwa ji"
Raihan ya ce "Mu mun isa, mu kuwa muke ƙaunar ki, jeki ki yi wanka ki shirya, har noor tare zamu tafi office yau, kya ji daɗin jikinki"
Ta juya tana hararar noor, noor ta kama dariya ta ce "Na fasa tafiyar yaya ummi"
"Ki yi ta tafiyar ma, ina ruwana" suna lallaɓata suna yi mata dariya.
Aka ba ta ɗunamen shinkafa ta ci hankalinta ya kwanta.
Tare suka tafi wurin aiki, fitowar ta yi mata daɗi tana kallon titi.
A can wurin aikin, suna zuwa a parking space noor ta ga motar Salim.
Sun shiga take tuna masa wulaƙancin da ya yi mata, ta zo ganinsa.
Yau bai biye mata ba, ya ce "Allah ya baki haƙuri, kar na tanka cibi ya zama ƙari"
Ma'aikata na ta gaishe shi, yana amsa musu cikin mutuntawa.
Wani mutum ya taso, ya tare su ya durƙusa a gaban raihan yana dan Allah maigida ka taimaka mini da aikin sharar nan ko masinja, nafi wata ina zuwa an hana ni ganinka, ina cikin mummunan yanayi na babu da fama da rayuwa, dan Allah ka taimaka mini.
Ummi ta zubawa mutumin ido, raihan ya kalli ummi ya ce "ya dai? Kin san shi ne?"
"Ishaq Abdulkarim magashi" ta faɗa jiki a sanyaye, mutumin ya ɗaga kai yana kallonta.
A rikice cikin tashin hankali mutumin ya ce "Salma Muhammad Bashir, ke ce
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 51 Chapter of 54