Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
magana ko?" Ta jinjina masa kai alamar eh. "To ya aka yi?" "Dr. Tun muna waccan ƙasar kamar ban kuma al'ada ba fa" Yayi dariya ya ce "To me ki ke so in ce?" "Koma meye ka ce mana" Dr. Yayi dariya ya ce "Maman ummi rigima, kin fi ni sanin meyake faruwa ai" "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wai ciki ne da ni?" Dr. Ya kashingiɗa yana dariya, gaba ɗaya ta ruɗe "Haba dr. Ummi na jego nima a ganni da ciki, na shige su" "To laifina ne? Ni dai ina so ina murna Allah ya raba lafiya, kowa ya kalle ki fa zai gane kin ƙara haske sosai" gaba ɗaya ta rikice, wai abun kunya ne, shi kuma ya din ga yi mata dariya. Gaba ɗaya ya manta da a gidan farida. Ummi na ɗaki tana ta yi wa noor nasiha, a kan maganar salim, ta ce mata ita tana son sa amma tsoron auren take yi, ummi tana ta lallaɓata, dan sun yi magana da dr. Kuma ta san zai kira noor ɗin ya tambaye ta. Anty Maryam ta shigo ɗakin ta ce "Ummi, kin yi baƙuwa, sai wani harare-harare take yi, ban san me aka yi mata ba, amma da alama ƴar uwar mai gidan ce, suna kama da shi" Ummi ta yi murmushi ta ce "Anty ki ce ta shigo". Mintuna kaɗan sai ga Maryam ta shigo. Ummi ta ce "Sannu da zuwa, yanzu ki ke tafe?" Ta ja tsaki ta zauna. Noor ta ce "To, ikon Allah" "Noor kawo mata ruwa da yaran ta gansu" "Ai fa, an samu abun da ake so, an samu daular da ake kwaɗayi tashin farko an zubo yara biyu, yaran da aka ce babu kalarsu a danginmu" Ummi ta yi dariya ta ce "Ai abun alfaharinku ne, kun samu iri a dangi. Kuma ƴaƴa biyu sai matar so ba kwaɗayayyi ba, abun alfaharinku ne, ƙaninki akwai himma, ko kuma maybe daga ni ce" "Ummi ni ki ke gaya wa haka?" "Ke fa ki ka fara, wai kwaɗayi? Ke in kwaɗayi ne kawai ya kawo ni gidan nan, da ban kai haka a cikinsa ba" Noor tayi sallama, ummi ta amsa, ta miƙawa maryam yaran, maimakon ta karɓa ta ce "Ba shakka, dole mami ta ce akwai lauje cikin naɗi a wannan yaran, ba zata taɓa karɓar su a matsayin jikokinta ba" Ummi ta ce "Noor mayar mini da ƴaƴana wurin Anty"Noor na fita ummi ta ce "Kar Allah ya sa ku karɓe su a matsayin jikokin, ku mayar da su in da suka fito, tun da ubansu ya san nasa ne shikenan. Dama ni ban ce ta ƙaunace ni dole ba, tun da ba ku ku ka halicce ni ba. Ni yanzu a duniyar nan da a so ni da a ƙi ni duk uwar ubansu ɗaya. Babu yadda ban yi ba wurin yi wa mami biyayya, da girmamata amma ba ta gani, a gaban uwata saboda rashin ta ido, take cewa wai yara ba na ɗan ta bane, da yake uwata ba zuciya ce a ƙirjinta ba ko? Maryam da zan baki shawara da kun daina jayayya da ikon Allah, ni da raihan ajiyar Allah ne mutu ka raba. Idan ku ka cigaba da takurawa aurena ko kun raba aurena da raihan, zan cigbaa da rayuwar aure da shi ina haihuwa ko da aure ko babu, dan a yanzu ba wani ƙalubale ko abun kunya da ba zan iya fuskanta ba. Zaman gidan raihan, da zazzago ƴaƴa yanzu na fara, idan kin ga dama daga nan ki je wurin mami ki yi mini wani sharrin ke ta shafa da ke da ita" Maryam ta miƙe ta ce "Ummi, mamin ki ke gaya wa haka?" "Idan tsoho bai ji kunyar hawa jaki ba, jaki ba zai ji kunyar kayar da shi ba. Na yi iya yi na, na gaji, ba zan cigaba da cusa kaina in da ba a ganin kima ta ba. Kuma wallahi idan kuka cigaba da uzzura mini, hakkina zai fara bibiyarku ai ke ma mace ce, kuma a gidan wani ki ke aure, a sannu kema zaki haɗu da dai-dai ke". Ta fice ta bar ta a ɗakin a tsaye. Farida kuwa hankalinta ya tashi, saboda yadda ta je ta tarar da rahama, a asibiti, jikin yarinyar duk ya saɓule, haka na rahama cikinta, fuskarta da ƙafafuwan ta duk sun ƙone ƴan sanda sun kama mijin nata. Ta din ga kuka tamkar za ta zare. Ummi kuwa duk da furucin da Maryam tayi mata, ko a jikinta ta miƙe ƙafa ta cigaba da sabgoginta a gidanta. Hausawa suka ci idan kana da kyau, ka ƙara da wanka, ummi ta san in dai ɓangaren kula da mijinta ne, to tana da kyau ba a magana a ɓangaren kula da raihan. Amma duk da haka, maganar hausawa gaskiya ce, dan haka ba ta yi ƙasa a gwiwa ba, wurin lalubo lambar Amina Gachi, CEO beenad herbal center, mussaman ita da taɓa fama da ciwon sanyi, kuma galibi ciki ya kan tayar da ciwon, dan haka nemi Amina gachi, domin shiryawa koma wa ɗakin mijinta. (Bari na baku bayani, beenad herbal center, ba iya maganin sanyi suka ƙware ba, suna bayar da magunguna daban-daban dai-dai da matsalolin ku, damun kawo daidaito a gidajen auren ku. Suna da kaya kamar haka; Shedaniyar gumba Gumba mai saying Garin mai kabbara Mai dalalan miyau Wayyo dadi Zumar kwakwa Zumar ridi Zumar dabino Zuma mai ma'ul ijaba Farin jini Gumba kalla kalla da dai sauran su A BEENAD HERBAL suna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kuka zaba Ga kuma maganin slimming Gyaran nono Maganin hips Maganin Kara kiba Da dai sauran su. Kayan mu tested and trusted ne Suna maraba da masu siyan Daya ko sari Suna Nan cikin garin kaduna Kuma suna tura Kaya duk inda kike da yardar Allah AMINA GACHI 07034404975 CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE KADUNA Phone no 07034404975. Da labarin abun da ya faru da rahama ya zo kunnen ummi, hankalinta ya yi mummunar tashi, dan sai da ta yi kuka, dan yadda Abdul ya gaya mata abun babu daɗin ji, ummi ta ce raihan ya bar ta je ta dubata, ya ce ba zata fita ba sai tayi arba'in. Yaran raihan kamar ana hura su, dan baya wasa wurin kula da su, ummi na cin abinci mai gina jiki, da zai samar mata da ruwan nono, kunu masu kyau da kayan marmari, su kuma yaran ga isashshiyar madara yana saya, kan su yi arba'in suka cika ɓul-ɓul gwanin sha'awa. Can gagarawa, aka samu wani irin maimakon ruwan sama, kamar da bakin ƙwarya, ga ƙarfi ga kuma iska hakan ya sanya rufin ɗakin iya kwashewa. Dama dr. Ne ya bayar da kuɗi, a gyara mata ɗakin ta saka aka yi rufi ta karɓe sauran kuɗinta ta cinye, sai ledar ɗaki da ta saka. Iska ta yaye kwanon, ruwa ya din ga zuba a kanta, ruwa ya jiƙa tsohuwar ƙasar da aka yi ginin ɗakin da ita, ita ma ta zube wani ya danneta, ban da katakon rufi da ya din ga ƙwalo mata a ka. Gashi itakaɗai take kwana babu kowa a wurinta, dan haka babu wanda ya san abun da ya faru sai washegari. Babu wanda yayi zaton za a ciro iya da rai, haka aka kwashe ta aka yi asibiti da ita, tamkar an jiƙa kaza a ruwa, ga jikinta duk ƙazantar zawon wahala da tayi, kan nan kamar an suɗe ƙwallon giginya, duk ta zama abun tsoro. Su farida kuwa an kai ruwa rana, da su da mijin rahama a wurin ƴan sanda, dan kuwa ƴar kwananta goma sha ɗaya ta mutu, kasancewar uwarsa tana da kuɗi, sai kaiwa ta ke tana komowa a kan lallai sai an sake shi. Ana wannan ƙadamin, su Alhaji Tahir suka kai kuɗin auren noor, aka saka watanni tara watan da za ta kammala karatun sakandare, za a yi bikinta da Salim. Tun da aka saka auren nan, ummi ta dage wa noor da addu'a, tare da yi mata nasiha sosai a kan zamantakewa. "Noor, bani da burin rabaki da anty farida mahaifiyarki ce, kuma komai ta yi miki, mahaifiyar ki ce. Abun da nake so ki sani shi ne, kar ki yadda wani ya ɗauki wani abu na tsafi ya ce miki ki yi wa mijinki. Daga zarar abun ya karye, za ki ji kunya, kuma sai mushen kare ya fi ki daraja a wurinsa. Noor Allah bai halicci namiji dan ya bi mace ba, mace ita ce a ƙarƙashin namiji, gwargwadon biyayyarki, gwargwadon mallakarki. Idan ki ka kwantar da kai, ki ka yi addu'a ki ka miƙa lamarinki ga Allah ki nemi aljannar ki da gaske, zaki juya namiji yadda ki ke so. Wasu abubuwan sai lokacin auren yayi zan gaya miki, babu ruwanki da ɗaukar shirmen ƙawaye su gaya miki abun da ba zai amfane ki ba. Babu ke babu yi wa miji asiri noor, asiri ba ya tasiri, ko yayi na lokaci kaɗan ne. Namiji kullum shi ne a gaba, dan haka ban da ɗaga masa murya, kuma ki fara yi muku addu'a samun zaman lafiya tun yanzu". Noor ta jinjinawa ummi kai. Hajiya kamar ta taka rawa, ganin a wannan karon Salim ya yadda zai yi aure. Kuma ta ji daɗin zaɓar noor da yayi, ko ba komai ta ga misali a kan ummi, ahalin gidan dr. Suna da tarbiyya. Dr. Ya je gagarawa, ya duba Iya, sai dai aka tabattar masa da spinal code ɗin ta ya taɓu, ba zata ƙara takawa ba, komai sai dai ayi mata. Dr. Ya tsorata da yanayin da ya ga Iya a ciki sosai da sosai. Gashi babu wata cikakkiyar kulawa ta a zo a gani. Bayan ya koma gida, ya tarar an dawo da rahama gidansa, a nan za ta yi jinya, da kamar ya ce bai yadda ba, kawai ya ƙyale su. Ummi ta na ta Alla-Alla tayi arba'in, tana son ta je ta duba rahama, kuma ta duba jikin iya. Sai dai shi Yallaɓai MD, lissafinsa kawai tayi ta koma turaka. Da  dr. Ya gaya wa Farida batun karɓar kuɗin noor, bala'i ta hau bala'i taƙi nutsuwa yayi mata bayani balle ta ji waye. Hankalin kausar yayi mummunan tashi, jin an karɓi kuɗin auren noor, ita kuma ba ta ga tsuntsu ba ta ga tarko. Ummi tana jikin raihan, tana ta zuba shagwaɓa, ta kalli fuskar sa tana ƙoƙarin tashi ta ce "Malam cikani na tashi, yarana jarirai ne, ba zaka haɗa ni da ƙajaga ba ban gama warkewa ba, ka sakani konika" Yayi dariya ya ce "Ke matar so ita ce ke konika, ki yi wa duniya proving ɗin ke ɗin matar so ce ga raihan" "Ni zaka yi wa wayo? Ai na riga na gama yi wa duniya proving ni ɗin ɗaya ce a zuciyar mijina" "Wallahi faɗi ki ƙara faɗa, ni kyautar da Alhaji yayi miki ni na so yi miki ita, wata gigitacciyar kyauta nake son yi miki". "Ni ba na son kowace kyauta, wuri nake son ka ƙara gyara mini a zuciyarka na miƙe ƙafata" Raihan ya ce "Kin samu, ba kowa a ciki sai ke Salmana, Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana, ya ƙaro miki lafiya, ki yi ta haifo mini ƴaƴa" Riƙe hannunsa tayi tana dariya ta ce "Ni zaka yi wa wayo, wai ba zuwa ka yi kana cewa ba ka da lafiya ba?" Ya kwashe da dariya ya ce "Duk cikin neman hanyar tsira ne, bani da lafiya idan har ba tare da ke nake tare ba, ni a idona duk wata mace idan ba Salmana ba ba zata taɓa zama ɗaya da ke ba. Ke daban ce a kowane fanni". Kalaman jinjina da girmamawae da yake yi mata, ya sanyata jin kamar ta fi kowace mace sa'a a rayuwarta. *** Idris da sasassafe yana ta shirin fita zuwa karɓar wani kuɗi, sai faɗa suke yi da hindu suna zage-zage kamar ƴan tasha a kan kuɗin cefane. Sallama aka yi a waje ya fita, ya tarar da ƴansanda a tsaye, ba su yi wata-wata ba suka cafke shi suka tafi da shi. Babu wanda ya san in da yake, dan babu wanda ya san kama shi. Sai da aka je wurin ƴan sanda, wai ana tuhumarsa da yi wa wata yarinya fyaɗe, an tsinci yarinyar a hanyar makarantar islamiyyar su, an yi mata fyaɗe an kasheta, wai shi ake zargi saboda hanyar wucewarsa ce, kuma an san halinsa na biye-biye yaran mutane. Farida na tsaka da jinyar rahama, ɗakin da take ƙonuwa sai wari take yi, duk da yadda ake kula da ita sosai. Inteesar ta shigo falon gidan, fuska duk a kumbure, idanunta sun yi jawur. "Ke inteesar lafiya meyafaru?" Ta miƙa wa farida takarda, tana kuka ta ce "Hajiyar sa ta saka ya sakeni, wai sun gaji da ciyar da ni sai dai na yi kashi babu haihuwa, alhalin ɗanta ne silar komai!" *Ina baku haƙuri, na san ina laifi rashin posting, ayyuka da bukukuwa ne suka yi yawa, ayi haƙuri dan Allah ina godiya da kulawa jama'ata ko in ce na ummi😡* Ayshercool 08081012143 CUTARWA! AISHA ADAM (AYSHERCOOL) (BRIGHT PENS) MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g 50 Jikin farida na tsuma, ta karɓi takardar ta duba, ga saki nan rangaɗa-rangaɗa guda biyu. "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wai meyasa duk maza halinsu ɗaya ne? Butulci kawai suka sani? Ita ma uwar ta sa shegiya mummuna mai baƙin hali. Ɗaukko mini wayata maza na kira babanku, na shiga uku ni farida wannan masifa hawa-hawa" ta kira wayar dr. Amma bai ɗaga ba. Ta dungurar da wayar ta ce "Ai na sani, ba zai ɗaga ba yana tare da wannan mahaukaciyar, na shiga uku ni farida". Dr. Kuwa sallama yayi ya dawo daga salla, mariya ta shirya masa abinci, ya lumshe ido ya ce "ƙamshin abincin kawai ya sa na ji na ƙoshi" tayi murmushi ta ce "Ka dai fara ci tukuna" Ta zuba masa faten wake doya, yana ci ya ce "Yauwwa, noor ta dawo ta zo ki fara koya mata irin abincin nan, kar tayi aure ba ta iya girki ba" "Waye ya ce maka ba ta iya girki ba? Idan ta zo gidan nan tana yi ai, noor ɗina ta iya girki sosai ta ce a wurin ummi ta koya" Dr. Ya ce "Ai tun da ummi tayi aure, na yi kewar abinci mai daɗi" "Son kai, saboda ƴar ka ce ko?" Yayi dariya yana kashe mata ido ɗaya. "Yauwwa ga wayarka, an kira ban ɗaga ba" Ba tare da ya karɓa ba ya ce "Ki na tsoron kar ki ɗaga ki ji budurwa ta ce ko?" Tayi dariya ta ce "Haba dai, ko ma budurwar ce na san ba za ta wuce maman ummi ba, maybe ko tana buƙatar wani abun ne, idan ka gama kar ka manta ka kira ta" ya ɗan ƙura mata ido. Ita har cikin zuciyarta tsakani da Allah take son su zauna lafiya da farida, wai ko ba komai ta riƙe mata ummi, daga baya ta haƙura ganin faridan ba haka ne abun a wurinta. Ya gama cin abincin, ta kawar da kwanukan, ta zauna tana matsa masa ƙafa ya lumshe idonsa. Ta ce "Baban ummi, ba ka ce mini komai ba a kan zuwa maiduguri" "A'a" ya faɗa a taƙaice. Ta sunkuyar da kai ta cigaba da abun da take yi masa. Ya ɗago haɓarta ya ce "Kin yi fushi ne?" "A'a, amma in anjima ma zan kuma tambayar ka, dan Allah baban ummi, ka san menene?" Ya ce "A'a sai kin faɗa" "Taron family aka shirya mana, wai an binciko tun farkon asalinmu, an gayyato mutane da dama da muke da alaƙa, ba tare da mun san mu ƴan uwa ba ne, dan Allah baban ummi" Ya ɗan yi murmushi ya ce "Na ji, amma ni kin ga bani da lokacin kai ki, bana son kuma ki hau motar haya, kin ga kina da juna biyu kar ki wahala" "Ai zan gaya wa ummi, idan ya barta sai mu tafi da Abdul da noor, dan Allah kar ka ce a'a" yanayin yadda ta kwantar da kai take lallaɓa shi ya sanya shi jin daɗi a ransa tare da jin kansa eh shi ne maigida. Saɓanin yadda farida ke yi masa magana gatse-gatse, wani lokacin ma sai ta yi abun da take so yake sani. "Shikenan, Allah ya kaimu lokacin, za ki je in sha Allah" Faɗaɗa murmushinta ta yi tana yi masa godiya. Sai magariba ya je gidan farida, dan duba su. Sai dai ta fara da yi masa ƙorafi, da zazzaga masa masifa, sannan ta miƙa masa takardar da inteesar ta zo da ita. Ya karɓa ya karanta, sannan ya kalleta ya ce "Na gani, me zan ce?" "Kamar yaya me zaka ce? Ba zaka kira shi ba a kan abun da ya aikata, ya wulakanta ƴar ka" Dr. Ya ce "Ƴar ki dai, ki nema mata wani uban da zai tsaya mata, ni da ban isheku kallo ba ke da su, ai na yi zaton wani uban ki ka canza musu, kuma ba wani abu da zan kira mijinta na ce masa, tun da ya riga ya saketa, in dai irin halin da ki ke yi, ta je tana yi dole a korota, yayi haƙuri ma. Idan baki riƙe tawa ƴar bazawara karo biyu ba, ga zaurawa biyu nan har da ƙarin budurwa Allah ya haɗa miki, kuma dolenki ki riƙe" ya fice ya bar mata gidan. Inteesar ta ɗora hannu a ka ta din ga rusa kuka, can gefe ma rahama kuka take yi, dan an saki mijinta, ya ƙwace mata sauran yaran, bayan aiko mata da tata takardar sakinta. Farida ta koma kamar mahaukaciya, ta rasa in da zata saka ranta. Kwanan ummi arba'in da biyar, ita da raihan da noor suka tafi yawon arba'in, a motar da Alhaji ya bata. Suka fara da zuwa gidansu raihan, da suka je gwiwa a ƙasa ummi ta durƙusa ta din ga yi wa Alhaji godiyar mota da ya bata. Yara sun cika hannu, sun ƙara kyau sosai, babu yadda za ayi ace yaran hausawa ne a yadda. Alhaji ya ce "Su wannan larabawan ba su fara dariya ba ne? Ko ni ɗin ne ba su gane ba" yayi maganar yana yi musu wasa. Har wurin mami suka je, sai dai Nihal ce kawai ta ɗauki yaran, tana hangen yaran abun ka da jini, zuciyarta na son ɗaukarsu, amma sharrin zuciya da ƙiyayyar ummi ta saka ta share su. Ana ta shirin bikin Nihal, saboda an kusa kawo kayan lefe, da an kawo kuma ba za a saka da yawa ba, za ayi bikin. Daga nan kuma ta ce su tafi can gidan farida, daga nan ma ta duba jikin rahama, tun da an ce a gidan take jinya. Raihan ya ajiye su, ya ce awa uku ya basu, zai dawo ya ɗauke su, su tafi gidan mama. A falo suka tarar da inteesar, kamar aljana ta rame, hasken nan babu shi, duk ta fita hayyacinta. Ummi ta zauna tana faɗin "Anty intee kwana da yawa, ya ki ke ya gida?" "Lafiya lau" ta amsa jiki a sanyaye, tana ƙarewa ummi kallo, da shigowarsu kawai ƙamshin kabbasar kayanta, ta gauraye ɗakin. Wata irin danƙareriyar lafaya ce a jikinta mai tsada, hannunta yatsu uku duk gold ne, haka kunnenta, har da chain na gwal a ƙafarta. Kai ba sai an gaya maka ba ka san ummi a hutu take. Noor ta ce "Anty intee baki da lafiya ne? Duk kin rame" inteesar ta girgiza kai. "Ina su Antyn su ke da rahama?" Da hannu kawai ta nuna musu ɗaki. Ummi ta kwantar da iman, a kan kujera noor ta ajiye aiman suka shiga ɗakin da sallama. Ɗakin sai warin gyambo yake, sai ɗan zani aka yafawa rahama, duk ta ƙone. A gigice ummi ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Anty rahama sannu ya jiki" rahama ta sunkuyar da kai sannan ta amsa. Ta kalli farida ta ce "Anty ina wuni, ya mai jiki?". "Dalla rufe mini baki, kin zo munafunci ki ga a wani hali nake ciki, ko na haukace na fara bin bola kamar babarki, to ina nan daram. Dangin maita bakin da ki ka yi mata ya kama ta. Jiki a sanyaye ta ce "Astagfirullah, ƙaddara ce daga Allah, kuma ke ki ka hasala ni, ɓacin rai ya sanya na yi wannan furucin. Sannu Anty rahama, yadda Allah ya jarabce ki da wuta a duniya, Allah ya haramta mata namanki a lahira, Allah ya baki lafiya da akwai wani abu a raina ba zan zo duba ki ba, Allah ya baki lafiya" Rahama ta riƙo hannun ummi ta ce "Ummi ba zan musa ba, idan aka ce alhakinki ne ya kamani, na san mun azabtar da ke, wallahi tun da na yi aure ko amarci ban gama ci ba, na fara shan wahala har yau ban samu kwanciyar hankali a gidan aure ba. Dan Allah ki yafe mini" Ummi ta shafa hannun rahama ta ce "Na yafe miki wallahi, Allah ya yafe mana baki ɗaya, Allah ya baki lafiya bari na je falon na ji kamar kukan aiman" ta miƙe ta fita. Farida ta kalli noor ta ce "Sannu sallalamammiya, ashe kin canza uwa ko?" Noor ta ce "Idan na yi miki laifi fa ce wa ki ke yi na nemi wata uwar, dama ke ba uwata ba ce, ki yi ta hantarata da zagina, ni kuma bana jin daɗi ni ki ka tsana ban san me na yi miki ba" sai jikin Farida yayi sanyi, ta tuna maganar ummi, ba ta taɓa zaton abun da tayi zai yi tasiri a zuciyar noor ba. Ta basar ta ce "Da uban wa aka saka miki rana ban sani ba?" "Yayan yaya raihan ne, yaya salim" Kausar da ke gefe tana danna waya ta ce "kutt wannan gandamemen mutumin, me yayi miki zafi?" "Ni kar ki yi mini hassada, haka kurum in tsufa a gida, ke da ki ke kyau ma baki yi aure ba, balle ni ba zaki zigani ba" suka hau faɗa kasancewar kwana biyu ba su haɗu ba. Farida ta tsawatar musu, sannan ta koma kan rahama da masifar, uban me suka yi wa ummi da take neman yafiyarta. "Ashsha! Yaya ki farga kema kan lokaci ya ƙure. Kin san mun azabtar da ita, ke ki ka gaya mini halin da Iya take ciki, ni dube ni wallahi hakki ne" "A'a ni ban ɗauki hakkin kowa ba, dan haka ba wata yafiya da zan nema, ta daɗe ba ta yafe ba". Ummi kuwa na komawa falo, ta tarar da inteesar tana zaune ta zuba wa yaran ido, ta saka hannu ta ɗauki aiman da ya tashi ya fara kuka. Tana ɗaga kai ta ga ummi ta ajiye shi, tana basarwa. Ummi ta yi murmushi, ta ƙarasa ta ɗauke shi, ta ajiye mata shi a cinyarta ta ce "Haba ɗan gidan babban mutum, mamanka ce da ba ka santa ba, ka buɗe ido ka kalleta" Inteesar ta saka hannu ta rungume shi, ta fashe da kuka. Ummi ta san kukan me take yi, ta dafa ta ta ce "Haba Anty intee, Allah ya baki rai da lafiya, kar ki yi masa butulci, rashin haihuwa jarabta ce, ki gode masa ki yi addu'a idan ki na da rabo, Allah ya baki naki kema. Zan taya ki Addu'a in sha Allah zaki ga ɗanki, Allah ya baki rabo a satin nan, ni na yi biyu ke ki yi uku, mu tarawa kawu abokan wasa" Cikin kuka ta ce "Aurena ya mutu ummi, uwar mijina ta saka ya sakeni, wai bana haihuwa sai ci da kashi. Sun wulaƙanta ni, sun tozarta ni, Abba ya ce babu ruwansa na ƙarata na nemi wani uban. Zuciyata za ta fashe ummi, gashi tun da na dawo kausar ta mayar da ni kamar maƙiyiyarta sai raini da wulaƙanci ita kanta maama tayi ta hantarata, wallahi ji nake kamar na sha guba na mutu" Da sauri ummi ta toshe mata baki, fuskar ummi ɗauke da hawaye ta ce "Haba anty inteesar, mutuwar aure ba kan ki aka fara ba, ba kuma yana nufin ƙarshen rayuwarki bane ba. Abba kuma kun yi masa laifi yana gaya mini, kun tafka kuskure da kuka daina kula shi, ko gaishe shi ku ka daina yi, dan ya auri mamana. Ku ka manta da duk ɗawainiya da hidima da ya yi mana a rayuwa. Ki kwantar da hankalinki, ki nemi afuwarsa nima zan taya ki roƙonsa, na san zai yafe miki. Abu na gaba kuma, ki yi ta addu'a da miƙa wa Allah lamuranki, idan ki ka gama idda, ki roƙi Abba ya bar ki, ki koma karatu, ko ki fita ki koyi wata sana'ar hakan zai rage miki lokacin da ki ke spending a cikin gida da su Anty farida, amma dan Allah kar ki sake cewa zaki kashe kanki" Inteesar ta kwanta a jikin ummi ta ce "Ba ki san me nake ji ba" "Na ɗanɗani fiye da abun da ki ka ɗanɗana, da ko maƙiyina bana fatan ya ɗanɗana. Sai da ta kai a duniya ina jin

Chapter 53 of 54