kawai ta fita, ta kama hanyar makaranta, lokacin kusan tara da kwata, tana tafe iska na kaɗata, ga azabar sanyi jikinta babu rigar sanyi, sannan babu mai a jikinta, dan haka tayi busu-busu da ita.
"Ke daga ina?" Malamar da take ajin su ta tambaye ta.
"Gida" ta faɗa a taƙaice.
"Yanzu ne lokacin zuwa makaranta?"
Tuni hawaye ya cika wa ummi ido, saboda tana tsoron duka ta ce "Mama ce bata nan, ba ta dawo ba"
"To kuma gidanku babu wanda zai ce ki taho makaranta da wuri? Kalli jikinki fa ko mai baki shafa ba, kamar wadda zata aikatau ba makaranta ba" ƴan ajin suka kwashe da dariya.
"Silent" malamar ta tsawatar tana kallon ƙafar ummi, da kamar an ciro ta daga haƙa rami, ummi kuwa gwanar kuka, ta kama ƙasan farin hijjabinta, tana goge hawaye.
"Wuce ki je ki zauna"
Ta nufi wurin zamanta, can wuri ɗaya, ta cigaba da sheshsheƙar kuka, tana jin muryar wani yaro, cikin murya ƙasa² yana cewa "Baƙar tukunya, yau an shafeta da toka"
Iya sam bata san makaranta ummi ta tafi ba, kawai sai nemanta ta yi ta rasa, hankalinta ya tashi, ta fito tana zagawa tana nemanta.
Ummi kuwa da ƙyar ta koma gida, saboda azabar yunwa, har wani jiri take yi, tana ta Addu'a Allah ya sa tana zuwa ga mama, sai dai kash, tsakar gidan nan fayau, ko shara bai gani ba, ta kalli wurin murhu da maman ke ɗora girki, shi ma babu komai a wurin, ta kalli ƙofar ɗakin su, ɗakin dai a rufe.
Ɗakin iya ta shiga, ta nemi wuri ta kwanta, ta fara kuka tana share hawaye, tana kiran sunan mama da baba.
Bacci ya ɗauke ta, sai dai hayaniyar iya ta tashe ta, "Dan ubanki ina ki ka je, ki ka tayar mini da hankali, nake ta yawon nemanki, lungu-lungu kamar akuya.
"Makaranta na je"
"Uwar makarantar, kin gaya mini zaki je?" Ummi ta girgiza kai.
"Kawai dan ki tayar mini da hankali, to ubanki ma bai ɗaga mini hankali ba, balle ke" ummi dai tayi shiru ba ta ce komai ba.
Iya ta gama zaginta tsaf, sannan ta bata abincin rana, sai dai ba dan zai isheta ba, haka ta ci.
Da yamma yarinyar da take tafiya da ita makarantar allo, na'ima, ta zo tafiya da ita, Naima ƴar ɗakin mariya ce, dan tana son ummi sosai, ita take tafiya da ita makarantar allo, kuma ta ji labarin mariya ta tafi, iya ta ƙwace ummi. Ta tarar da ummi a zaune tayi shiru, idonta duk hawaye.
"Iya na zo tafiya da ummi makaranta"
"Gata nan, sai kun dawo" iya tayi maganar tana nuna ummi a wulaƙance.
Naima ta tambayi iya kayan ummi, ta gaya mata in da suke, ta ga jiƙaƙƙun kaya a ciki.
Ta ce "Ummi, na ji kayan ki a jiƙe?"
"Fitsarin kwance na yi ban sani ba"
"To ki daina haɗa su da kayanki masu kyau, idan mun dawo daga makaranta, zan wanke musu"
Ummi ta saka mata kuka ta ce "Yaushe mama zata dawo?"
"Ki yi haƙuri, nima ban sani ba, amma za ta dawo" ta shirya ummi ta sakata a gaba suka tafi makaranta, tausayin ummi ya kama ta.
Kwana ɗaya kawai, mariya ji take yi tamkar ta taka da ƙafa, ta koma gagarawa, ta ɗaukko ƴar ta, duk sallar da tayi, bata iya addu'ar komai, sai roƙon Allah ya kula mata da ummi, Allah ya dawo mata da umminta.
A kwana a tashi mariya ta gama takaba, sai da tun bai fi watanni biyu da daowarta gida ba, ta fuskanci tana ɗauke da juna biyu, kuma ta ja bakinta ta yi shiru, ta din ga rashin lafiya, ba cin abinci, duk ta rame ta fita daga hayyacinta, maryam ta rakata asibiti, sai a lokacin da likita yake yi mata tambayoyi ta tabbatar musu da tana da ciki.
Da suka koma gida, aka din ga yi mata faɗa, saboda ya zama dole a sanar da dangin su bashir maganar juna biyun nan.
Watanni huɗu da barin ummi a hannun iya, Ummi ta gane shayi ruwa ne, dan duk da ba girma ne da ita ba, amma tafi samun sauƙi da sassauci, a lokacin da mariya tana nan.
Gashi son makaranta ya shiga ranta sosai da sosai, idan ta yi wa iya laifi, sai iya ta hanata abinci, da ƙyar take iya zuwa makaranta, sai dai da ka ganta a cikin uniform ɗin nan, ka san babu kulawa, da babu wanda ya kai ummi tsafta a makarantar, amma wataran idan ka ganta, kamar ta shekara babu wanka, a wannan shekarun, ita take wanka da kanta, idan gari babu sanyi sosai tayi wanka da ruwan buta, idan da sanyi taƙi yi, dan wataran ruwan kawai take zubawa a jikinta.
Man shafawa sai iya ta ga dama zata bata ta shafa, shi ma ba iya shafawar tayi ba, iya ta daina bata, wai tana yi mata ɓarnar mai.
Wanki kuwa, sai idan na'ima za ta yi nata, sannan ya ta haɗa da na ummin, tayi ta goge mata, idan ba haka ba kuwa, sai dai tayi ta yawo cikin dauɗa.
A wata ukun nan, ummi ta koma kamar rainon mahaukaciya, wannan uban gashin babu mai kula mata da shi, ga cin zali da yara suka cigaba da yi mata, tun ummi na saka ran dawowar mama, har ta haƙura.
Saboda sabo, da sassafe idan ta tashi, sai ta ɗauki tsintsiya ta share sashin, ko da kuwa ba zai fita ba, saboda haka mama take yi, ta wanke bakinta da gawayi, ta jiƙa jikinta da ruwa buta ɗaya.
Idan ba makaranta ta tafi ba, mutanen gidan wannan ya ja ya aika, wancan ya ja ya aika, kamar baiwa, masu aiken nata, wani lokacin idan sun yi abinci su bata, domin kuwa bata ƙoshi da wanda iya take bata.
Duk ranar da tayi kuskuren yi wa iya fitsarin kwance kuwa, ko wani laifin, sai ta kira idris, ta bashi bulala, ta tuɓe ummi, ta ce ya zane mata ita.
Ga shi ya cigaba da kawo mata farmaki, gashi ta yi girman da ba zai yiwu ya ɗauke ta ba, sai ya tsiro da salon aike, ya ce idan ta sayo ta kai masa ɗakin su.
Yau idris ya kasa jurewa, ya aiketa sayen omo, ta dawo ta tsaya tana raɓe-raɓe, cikin ikon Allah sai ga naima, suka yi kiciɓis da ummi a soro ta ce "Ummi, tun ɗazu nake jiranki, ina kallon yadda malam babba ya zane ki, saboda makara, amma shi ne baki taho ba".
"Yaya idris ne ya aike ni sayen omo, ya ce na kai masa ɗakin su".
"Ɗakin su kuma? Ina laifin ya ce ki kai wa babarsa, kuma ina sauran yaran gidan? To wallahi ko da wasa, kar ki kuskura wani a mazan gidan nan, ya aike ki ya ce ki kai masa ɗakinsa, ko wani wuri da mutane ko da kuwa zasu dake ki" ta waiwaya ta ga awwalu zai shiga sashin mazan ta karɓi omon ta ce "Kai auwwalu, ka kai wa idiris aiken da ya yi wa ummi, wuce muje ke kuma"
Suka tafi makaranta, ta saya wa ummi awara a hanya, da suka je ta zaunar da ita a makaranta ta bata ta ci.
Suna tafe a hanya naima na sake jaddadawa ummi, kar ta kuskura wani ya aiketa, ya ce ta kai masa ɗakinsa a samarin gidan.
Ta raka ummi har cikin gidan, tana shirin tafiya, Idris ya shigo yana yi wa naima bala'i.
"Wacece ke a wurinta, da har zan aiketa ki hana ta kai mini aike?"
Naima ta ce "kamar yaya, makaranta zamu tafi mun makara"
"Dole tare zaku tafi makarantar? Har in aike ta ki hanata kawo mini saƙona?"
"Amma dai da alama baka da gaskiya, ba dai an kai maka aiken ba, ya zaka din ga aiken yarinya ka ce ta kai maka ɗakin ka" nan da nan bala'i ya kaure abunka da gidan gandu, nan da nan aka taru, ya din ga kurarin zai yi mata dukan tsiya.
Iya ta hau naima da masifa, har da cewa kar ta sake shigowa, tun da sharri za ta yi wa idris.
Ita duk wannan abun ba shi ne damuwar ta ba, tausayin ummi take ji, ta kalli yadda ummin ta rakuɓe tana kuka.
Naima ta ce "Ba abun da zai sake shigo da ni in sha Allah, amma dai wallahi idris ka canza hali, mutumin banza kawai" iya ce ta hana shi, da cewa yayi sai ya zane naima.
Iya ta ce kowa ya watse, har ya nufi hanyar fita, ya dawo ya shaƙo ummi tare da luƙa mata wata irin ashar. Ƙara tayi tana kakari.
"Dan ubanki, daga yau idan na sake aikenki, ki ka biya wani wurin, ko kuma na sake ganinki da wannan yarinyar, sai na kashe ki" ya jefar da ita a wurin, ta riƙe wuya tana tari, wani irin yawu mai kauri na wahala, na zubowa daga bakinta, ta cire hijjabin makarantar ta tana gogewa, gashin kanta kuwa, kalba biyu ce tafi wata, ita ma naima ce tayi mata.
Mariya kuwa sallar magariba ake yi, kawai suka ga ta fito daga ɗaki, tana ƙoƙarin fita, mama wadda take matar babansu, ta riƙe ta, ta ce "Mariya lafiya ina zaki?"
"Mama kukan ummi nake ji, kamar tana ƙofar gida fa"
"Mariya ummi na jigawa, kina Maiduguri ta ina ki ka ji kukan nata?"
"Iya wai ba kya ji ne? Ni kukan ummi nake ji"
Mama ta ce "Iya kuma, nice fa mariya"
Mariya ta yi ƙuri da ido, tana kallon mama, sai yanzu ma ta dawo hayyacinta, gaba ɗaya ta kasa gane menene yake faruwa, bacci take ko idonta biyu, ita dai kamar kukan ummi kunnunwata suke jiye mata.
Ayshercool
08081012143
*CUTARWA*
BRIGHT PENS
(FREE BATCH)
Shiru mariya ta yi, tana bin mama da kallo, jiki a sanyaye ta ce "Ki yi haƙuri, na zata gaske ne, magungunan da na sha ne, bacci ya ɗauke ni na ga ummi"
Mama ta ce "Mariya ki sassauta wa kanki a kan yarinyar nan, kar ki je ki haukace a banza fa"
Mariya ta amsa da "To"
"Ki din ga yi mata addu'a, Allah zai tsare miki ita" gyaɗa mata kai kawai ta yi, ta koma ɗaki.
Ummi kuwa ta ci kuka kamar babu gobe, saboda zafin shaƙar da ta sha.
Iya ta ritsuta a ɗaki tana tambayarta, ko wani abun take gayawa na'ima, ummi cikin kuka ta din ga girgiza mata kai, tana tsoron kar ta dake ta.
Har gari ya waye, tana jin wuyanta babu daɗi, ta yi wanka, ta sanya cukurkuɗaɗɗun uniform ɗin ta, dan ma an yi sa'a a wanke suke, dama na'ima da yamma ta ce zata yi musu guga, aka yi uwar watsi.
Iya bata kulata ba, dan haka ta yi sharar tsakar gida, ta ɗau kofinta, ta je sashin sa'adatu, da niyyar a bata kunu, sai dai ta tarar ta gama rabawa yaranta, suna sha zasu tafi makaranta.
Ta juyo da kofin a hannunta, tayi karo da magaji.
"Baki tafi makarantar ba ne?" Ta jinjina masa kai.
Ya kalli kofin hannunta, babu komai a ciki.
"Kunun ma baki samu ba? Iya bata baki ba?" Ta jinjina masa kai.
Ya karɓi kofin, ya shiga sashin su na maza, ya fito ya miƙa mata kunun cikin kofi.
Har ƙasa ta tsuguna ta karɓa, ta zauna a kan wani kututture, ta kafa kai ta din ga sha, saboda uwar yunwar da take ji.
Ta shanye ya karɓi kofin, ya bata naira ashirin, ta karɓa ta ce "An gode"
"Kiyi sauri ki tafi makaranta, kar su dake ki" ta ce "To"
Ta kamar hanya ta tafi, jin ta a ƙoshe da kunu ya sanya ta tafiya cikin nishaɗi.
Sai dai yau ma ta makara, a bakin gate discipline mistress ta fara zane ta, tare da ci mata mutunci saboda ƙazanta, jikinta bususu fuskarta duk busasshshen koko, ga sauran kwantsa a idonta.
Ta tafi aji tana kuka, saboda zafin bulala.
Ta je ta tarar ana yi musu darasi, ta buɗe jakarta da yanzu a baƙar leda take zuba su, duk sun zama shara da tarkace, fensirinta kuwa dama tsintar sa tayi, ya zama ɗan mitsitsi da ƙyar take iya riƙe shi ta yi rubutu.
Head master ya shigo ajin, duk suka tashi suka gaishe shi, yayi musu umarnin su zauna.
Ya dubi malamarsu ya ce "Malama, yara biyar zaki zaɓo mini masu ƙoƙari, zamu tafi da su gidan talabijin, za ayi wani shiri da su, a haska su"
Malamar ta ce "Ok sir, yanzu kuwa"
Ta tashi ta kira yara uku, ta huɗu ta kira sunan Salma Muhammad Bashir.
Wani irin farinciki ya kama ummi, saboda malamarsu ta zaɓeta a cikin wanda za a tafi da su gidan talabijin na jigawa, tana ta murna za ta ganta a talabijin, dan duk da rashin kulawar nan, ummi tana da matuƙar ƙoƙari, in dai aka yi darasi a gabanta, to ta ɗauke.
"Ke!ke tsaya" headmaster ya dakatar da ita a tsakiyar aji.
"Wannan kuma ina zata?"
Malama ta ce "Sir, yarinyar na da ƙoƙari fa, ita ce take first position"
"A hakan, wannan yarinyar da ya take karatun,? Ba ita ake kora ba ba ta biyan kuɗin PTA, da yaya take iya karatun"
Ta ce "A haka, ita take ta ɗaya?"
"Kai canza wata dan Allah, haba wannan tayi muni da yawa, wannan ko an saka mata camera ai ba za a ganeta ba, baƙi ƙirin da ita haka, ji uniform ɗin ta fa, tubarkallah ni wannan tayi baƙi samo wata mai ɗan kyan gani, ke koma ki zauna ba za a tafi da ke ba, ji kayan jikinta kamar ƴar ci rani"
Tuntsirewa da dariya da yaran suka yi,hakan ya bawa hawayen idonta ƙwarin gwiwar zubowa, ta tafi lungun aji ta zauna, tana share hawayen.
Tana gani aka zaɓi wata daban, bayan malamar ta fita, suka ɗora da yi mata dariya da tsokanar ta, har da masu ja mata hijjabi, suna ƙazama ba ta wanka ba ta wanki, waƙar da aka saba yi mata a assembly idan an zo duban tsabta, har misali ake yi da ita, na ƙazamai.
Ana tashi ta fita daga aji, ta nufi gida har da gudunta, dan kar ma ƴan ajinsu su taso, su tireta a hanya, ta ƙarasa tana ta numfarfashi.
Sai da ta ɗan huta sannan ta shiga sashin su da sallama, muryar iya ta fara jiyo wa tana hayaniya, da muryar baba saminu, ba ta san dai faɗan me suke yi ba, ta kutsa kai ta shiga.
Wan mahaifiyarta ta gani, a zaune suna ta jayayya da su iya.
Hayaniyar da suke yi, ba ita ce ta dame ta ba, murnar ta Allah ya sa da mama suka dawo.
Bai lura da ummi ba, sai da ta riƙe hannunsa, ya waiwayo ya kalleta ta ce "Ina maman take?" Yayi ƙuri da ido yana kallon ummi, sai ka ce ba ƴar mutane ba.
Yadda mariya ke ƙalƙaleta, take kula da ita, amma ya ganta kamar an janyota daga ramin ƙasa.
Ya ce "Baki gaishe ni ba" ta tsuguna ƙasa ta ce "Ina kwana"
"Lafiya ƙalau, ya makarantar?"
Ta ce "Lafiya lau, to ina maman take?"
"Mama tana lafiya, ta ce; a gaishe ki"
Ummi ta sake kallonsa ta ce "To zaka kai ni wurinta?"
"Ke wuce ki je ki cire uniform, ki yi salla" Iya tayi mata tsawa. Yayi shiru ransa a matuƙar ɓace, bai taɓa tunanin ganin ummi a cikin wannan mummunan yanayin ba.
Ta fito kanta babu ɗan kwali, gashin nan a cukurkuɗe, sai soshe-soshe take yi, saboda yadda ya addaba mata da ƙaiƙayi.
Ya dubi iya ya ce "Shikenan, tun da kun ce cikin ba naku bane ba, baku san da shi ba, ni ba dan wani abun hannunku ya sanya muka zo muka sanar da akwai cikin ba, saboda a cika umarnin Ubangiji, amma tun da abun haka ne, Allah ya kyauta, mu mun ji mun gani, mun karɓa. Amma dan Allah ku bani ƴar ta in kai mata, mariya ta kasa zaune ta kasa tsaye, hankalinta yaƙi kwanciya, ku bata ƴar ta dan Allah"
"Ba rashin ummi ne ya hanata nutsuwa ba, mugun abun ta ne yake koma mata kanta, hakkina da na ɗa na ba zai taɓa barinta ba, ya din ga bibiyar ta kenan"
Ganin idan ya cigaba da zama, wannan jayayyar zata kai su ga maganar banza, ya sanya ya tashi tsam, ya ce "Shikenan babu laifi, Allah ya kyauta"
Jin ya ce zai tafi, ya sanya ummi fitowa da gudu daga ɗaki, ta ce "Ba zaka tafi da ni, ka kai ni wurin maman ba?"
Ya durƙusa ya shafa kanta ya ce "Ki yi haƙuri, in sha Allah nan gaba kaɗan, zaki koma wurin mamanki, Allah ya yi miki albarka" ya ciro kuɗi dubu biyar, ya bawa iya ya ce "Dan Allah a canza mata uniform, a saya mata wasu ƴan kayan buƙata"
Ba kunya iya ta amshe, tana harare-harare.
Ummi ta tsaya tabi bayansa da kallo har ya fice.
Dukan da aka yi mata a kanta ne, ya sanya ta dawowa hayyacinta, ta firgita ta kalli Iya.
"Duk wanda ya sake zuwa gidan nan, ki ka ce ya kai ki wurin uwarki, sai na saka idris ya zane miki jikinki, wato salon ace ba a kula da ke, saboda ƙwarewa a munafunci kin tsotsa a nono ko?" Tayi shiru ta sunkuyar da kanta ƙasa.
"Munafuka, ga muni ga kinibibi, tashi ki wanke kwanukan nan na safe" sumi-sumi ta nufi wurin tara kwanukan wanke wanke, ta haɗa ta fara wankewa.
***
Bayan sallar magariba, yaya garba ya je ya samu mahaifinsu ya sanar da shi cewa iya ta ce ba su san da ciki ba, dan haka a nemi ubansa.
Malam yayi shiru, lamarin ya girmame shi ya ce "Haka suka ce?"
"Wallahi, matar nan ba ta da mutunci ba ta da imani ko kaɗan, ba ka ga Yarinyar nan a halin da na baro bata ba, kamar ƴar jari bola saboda azabar datti da ƙazanta"
"Ƙyalesu, yarinya kullum muna yi mata addu'a, in sha Allah babu wanda zai sake bi ta kansu, ita kuma Allah ya raba ta da ciki lafiya"
Ya amsa masa da "Amin"
***
Na'ima kuwa ummi na ranta, amma babarta ta ce mata ba ita ba ummi, dan kakarta ba mutunci ne da ita ba, kar ta yi mata wani sharrin.
Sai dai ta kan ƙulle abinci wasu lokutan, ta tafi da shi makaranta ta bawa ummi.
Yanzu babu mai yi wa ummi wanki balle guga, dan haka dauɗa kamar ka kankarota a jikinta.
Ummi na iya ƙoƙarin ta wurin kaucewa haɗuwa da idiris, ga bala'in tsoronsa da take ji, saboda dukan da yake yi mata idan tayi laifi babu tausayi babu imani.
Allah ya taimake ta, wasu lokutan magaji na taka masa burki a kan wasu abubuwan.
Tsabar rashin gyara, ya sanya kwarkwata cika wa ummi gashi, kayan ta duk suka cukurkuɗe suka yi mata kaɗan, tana zaune har sakkowa kwarkwata suke yi daga kanta, suna bin ta, sai dai ta ɓuya tayi ta kashewa, ba ta son a gani.
Ga wasu irin manyan ƙuraje da suka din ga fitowa a cikin gashin kan nata, suna ɗurar ruwa, suka ƙara bawa kwarkwatar nan damar hayayyafa babu ji babu gani.
Banda zarnin fitsari da warin datti, babu abun da take yi, dan kuwa da kanta take yi wa kanta wankin kayanta, wando sai ya fi kwana uku a jikinta, ba ruwan iya balle ta ce cire ki wanke.
Sa'adatu ce babar auwwalu, ta fara lura da wannan ƙurajen na kan ummi, ta kamata ta buɗe kan, ta ga ƙazantar da take cikin gashin.
Ta nuna wa iya, Iya ta yamutse fuska ta ce "Taɓ gaskiya ba zan iya taɓa wannan kan ba, to gashi ne ba kaɗan ba, gaba ɗaya ba irin namu ba, kalar na mutanen ƙetare, shiyasa nake cewa anya ma kuwa tamun ce, duk zuriyar mu, babu irin wannan gashin, yanzu meye abun yi kar kan ya ruɓe ace ni ce ina kallonta, na bari ya ruɓe ji yadda wani mugun ruwa yake tsatstsafowa da ƙwayayen kwarkwata a ciki".
"Aikuwa sai dai a aske kan nan, dan ban ga yadda za ayi maganin abun nan ba"
Cikin ƙyanƙyami, sa'adatu ta sauke wa ummi gashin nan tsaf, ta koma sai ka ce namiji, ga hudar kunnenta ma, tana ruwa saboda tsufan ɗan kunne a kunnenta, ba a taɓa cirewa ba.
Iya ta saka aka haɗa kanwa da gishiri, da omo aka wanke kan nan, ummi ta din ga wani irin masifaffen kuka, saboda azabar raɗaɗi, da bal'in zafi haka nan da ruwan sanyi aka tuɓe ta, aka wanketa a tsakar gidan, iya har tana cewa wannan baƙar fatar ba da dutsen goge faso za a wanketa ba kuwa?. Wata irin annakiyar dauɗa ta din ga zuba daga jikin yarinyar. Yara suka cika sashin danƙam suna kallon ummi, da tana ta ƙoƙarin rufe jikinta, amma azabar wahala da zafi ya sanya ta manta da tsiraicinta.
Ummi na ji na gani, aka ɗaure gashinta a leda kaya guda da shi aka zubar, iya ta ce a sakawa kan ummi fiya-fiya, idan ba haka ba, sauran ƙwan zai ƙyanƙyashe kansa.
Ba tare da tunanin wane hali zata shiga ba, suka shafe ƙwallon kan da suka saukewa sumarta da fiya-fiya, hakan ya sa ta din ga tari da atishawa, gaba ɗaya kanta ya juye, ta din ga jiri, kan dare zazzaɓi ya rufe ta da ciwon kai.
Ba wanda ya kula ya saya mata magani, haka ta kwana tana rawar sanyi, da ta yinƙura ta tashi, sai ta tafi luuu zata faɗi.
Da safe gwaggo ta bata, koko da ƙosai, sai dai ta kasa ci, ta cigaba da kwanciya tana burgima a ƙasa, kanta yana ciwo, ga tari da take ta faman yi.
Cikin barccin wahala, ummi ta ji wani ƙamshin turare mai daɗi, ta ji magana sama-sama kamar muryar babanta.
Da sauri ta buɗe ido, ta yi ƙuri da ido tana kallonsa, ga iya a gefe suna magana da shi.
Yayi murmushi ya ce "Uwata ta kaina, kin tashi? Ƙaraso mu gaisa" sai yanzu ta lura ba baba bane ba, mutumin nan ne mai kama da shi.
Tasowa ta yi da sauri, sai dai ta faɗi, saboda jirin da take ji.
Da sauri ya tashi, ya ce "Iya ba ta da lafiya ne?" Iya ta taɓe baki, mussaman jin ya kirata da uwassa ta kansa ta ce "Eh zazzaɓi take".
"Subhanallah, kuma ba a kaita asibiti ba?"
Ya zaunar da ummi, ya sinsuna kanta ya ce "Ya na ji kamar kina warin fiya-fiya? Ya cire hular kanta, sai ga kai sol ba gashi, ga dagwalon gyambo a kan, ciwon duk yayi baƙi saboda fiya-fiya.
A razane ya ce "Meye wannan? Iya meya sameta a kanta?"
"Kwarkwata ce, da wasu ƙuraje, shi ne aka aske kan aka shafa mata fiya-fiya"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, iya wannan ai ganganci ne, ina laifin a kaita asibiti, wannan ƙaramar yarinyar a saka mata fiya-fiya a ka, ai shi ya sanya mata zazzaɓi".
"To ban da kai yahaya, ana ta abun da za a ci, waye yake ta wani asibiti, wa zai bayar da kuɗin kai ta wani asibiti?"
Miƙewa yayi ya ce "Wannan abun kunya da yawa yake"
Cak ya saɓa ummi a kafaɗarsa, yayi waje da ita, iya ta biyo shi tana tambayar ina zai kai ta?.
"Asibiti zan kai ta, idan ta mutu ba makawa ku ne ku ka kasheta" yayi waje da ita.
A mota ya kwantar da ita, ya ja suka tafi.
Sosai likitoci suka din ga faɗa, dan ma asibitin kuɗi ne, aka sake wanke kan ummi, da magunguna, aka saka mata ruwa saboda zazzaɓin da ya rufeta, take ta rawar sanyi.
Ya fita ya sayo kayan marmari, da ta farfaɗo zazzaɓin ya sauka, ya din ga bata da kansa.
"Kana kama da baba" ta faɗa a lokacin da zaƙin kankana ya ratsa kwanyarta, wanda rabon da ta sha har ta manta.
Yayi mata murmushi ya ce "Ai nima baba ne"
"Ai an ce baba ba zai dawo ba, ya mutu yana cikin kabari".
"Haka ne mamana, kina yi masa addu'a ko?" Ta gyaɗa kai alamar eh.
"Yanzu me ki ke son na saya miki?"
"Littafi" ta bashi amsa.
"Littafin makaranta?" Ta jinjina masa kai alamar eh.
Ya ce "To shikenan, zan sai miki in sayo miki kifi ko nama, wanne zaki ci?"
"Nama" ta faɗa tana murmushi.
Yayi mata murmushi shi ma, ya ce "To bari su sallame mu, sai na saya miki mu tafi gida"
Har ummi ta ɗan murmuro, ya saya mata tsire a hanya, da babbar robar youghurt, ya sai mata litattafai, da sabuwar jakar makaranta. Babban abun da ya burgeta da shi, shi ne yadda take ta ce masa ta gode, a yanayin tattaunawar da yayi da ita, ya san baƙar azaba kawai take sha, bai ga dalilin da ya sanya iya riƙe ummi ba, kuma shi ma idan ya ce zai tafi da ita can
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 54