Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da kin guara masa mari, gaba ba zai ƙara ba ai" Ta girgiza kai ta ce "Ni ban kula shi ba, muna level 3 ma aka kore shi daga makaranta ya yi satar amsa, duk abun da zan yi mutane ba za su daina ce mini mummuna ba" tayi maganar a raunane. "Sun gano weak point ɗin ki ne, shiyasa suke amfani da hakan suna yaƙarki. Ki kwantar da hankalinki na san kawu ba zai taɓa bari ki koma ƙauye ba, and ki ƙara tuntuɓawa ko zaki samu wani information a kan in da mama take, zan yi iya ƙoƙarina na gano miki ita". Ummi ta zabura ta ce "Dan Allah raihan da gaske?" "I promise you salma, wannan kukan nake son na daina gani sai farinciki a fuskar ki" "Nifa abubuwan da suke sakani kuka da yawa, ka san alfarmar da nake so ka yi mini?" "Sai kin faɗa". "Dan Allah ka manta na taɓa baka labarin nan, ban taɓa yin irin wannan hirar da wani ba, kai ne mutum na farko da na ji na nutsu da kai, na yi maka kuka, na rage abun da nake ji a raina, dan Allah kawai ka manta da labarin babu wani abu mai daɗi na tunawa a rayuwata, amma for now ka manta da shi, na gaya maka ne saboda na yi maka alƙawarin gaya maka abun da ya sani kuka" Idanuwanta yake bi da kallo, ya kasa amsa mata maganar, muninta kawai yake so ya gani, amma har ga Allah ya kasa, kawai dai baƙa ce, kuma baƙi dai ba muni bane ba. "Kayi magana mana" tayi maganar a ɗan shagwaɓe. "Zan yi, amma ba yanzu ba, mu karya ko, zuwa azahar mu yi salla sai mu je siyayyarmu ko?" Ummi ta ɗan ɓata fuska ta ce "Ko kawai mu canza rana, kaga yau duk sai godiyar Allah". Ya jingina da jikin tebur, ya ce "Kin sani kuka ba, marainiyar Allah, Allah ya ƙara kulawa da ke". "Amin amma ba na ce ka manta ba". Ya shafa sumar sa ya ce "Kema dai kin faɗa ne kawai, tashi in nuna miki aikin da zan kai wa Alhaji na gama" Ta miƙe suka koma kan kujera, yadda ya rarraba bayar da zakka, da kujerun umara da na hajji da zasu bayar, da ƙarin da za a yi a ɗan bawa ma'aikatan na riba da sauransu. Ummi a ranta ta jinjina dukiya tana nan a in da take, kuma yadda raihan ke gudanar da lamarinsa, ba zaka ce ɗan mai kuɗi ne haka ba, Maryam ce ma dai uwar jin kai, da jin ita wata ce. Sai da suka yi sallar azahar, sannan suka nufi tafiya, a mota take tambayarsa ina za su je, ya ce mata zata gani. Ya ja ɗan guntun tsaki ya ce haƙarƙarinsa a riƙe yake, zai fara koya mata mota, ya gaji da aikin direba ba a biyansa. "Ai ba ni na ɗauke ka aikin ba, kai ka ɗauki kanka, amma ba faɗuwa ka yi ba ka ke ciwon haƙarƙari?" "Ina fa, coach ɗina ne na gym, ya sakani ɗaga wani ƙarfe, haƙarƙarina ya amsa". Ta kalleshi ta ce "Wai sai ka ji wa kanka ciwo tukuna, meye na zuwa gym kai ba ƙiba ba?" Ya rausyar da kai ya ce "Waye ya ce dan a rame ake motsa jiki, bari na nuna miki ƙarfen da na ɗaga a Instagram" ya buɗe mata wayarsa ya bata. Suna tafe tana mitar ƙarfen yayi girma, daga bisani ta cigaba da yi masa taɓe-taɓe a wayar. Suka shiga go slow, yana jiran a basu hannu, ya ɗan leƙa wayar, ya ga ta nutsu, kallon dogwayen riguna kawai take yi tana liking ɗin su, da takalma da jakunkuna. Ya ɗan yi murmushi, aka basu hannu suka tafi. Katafaren kantin saye da sayarwa, suka shiga, ummi kamar ƴar ƙauye, sai kalle-kalle take yi. "Ta ina zamu fara?" Ummi ta ce "Ko ta ina ne ma". Sannu a hankali suke zagayawa, suka fara zuwa wurin turarruka, ya saka hannu ya ɗauki wani, ya jefa a cikin trolley. Ummi ta waro ido ta ce "Raihan, dubu sha takwas fa aka rubuta, ka manta kuɗin dubu sha biyar ne?" Ya kashe mata ido ɗaya ya cigaba da ɗaukar kaya. Tayi ta magana, amma yayi mata shiru, suka je wurin kayan kwalliya ya kalleta ya ce "Me ki ke so a nan?" "To ai kuɗin sun ƙare" "Ke ina ruwanki ne, ɗauki abun da ki ke so kawai" Comb ta ɗauka sai ribbon da coacoa butter, dan man yana burgeta ta ce sun isa. "Wai ke ba kya kwalliya ne, ga su hoda da kayan mata" "Ni bana wata kwalliya" ta bashi amsa tana ɗan kalle-kalle. Ya ɗaukko ɗaya wayar ta sa, yana dube-dube, ya ɗaukko wasu mayuka ya koma kan mayukan gyaran gashi, suma ya ɗauka. "Wannan me zaka yi da su?". "Budurwata zan saiwa lefe zan fara tarawa". Ummi ta yi dariya ta ce "Riga malam masallaci, za ta kwashi kayan shiririta" "Ni ne ma shiriritar ko? Son kowa ƙin wanda ya rasa da ni ɗin nan, ɗan kyakkyawan matashi mai gemu, kin san maza masu gemu muna da tsada". "Ai mami ta ce mai ka shafa ya fito" "Wallahi ban shafa mai ba, girma na yi gemu ya fito" "Muyi sauri kar na makara komawa gida" Ita dai ummi ta zuba wa sarautar Allah ido, ta san dai abubuwan da raihan ya ɗauka, sun fi ƙarfin kuɗinta nesa ba kusa ba. A wurin biyan kuɗi aka yi billing ɗin sa kuɗi masu yawa, ya basu ATM suka cire. Gaba ɗaya ummi ta manta da damuwar da ta baro a gida, jin zuciyarta take fes, yau ta faɗi abun da yake ci mata zuciya tsawon shekaru, kuma ta samu ta yi kuka, an saurareta. "Raihan" ya ɗago ya kalleta "Na gode sosai da lokacinka, Allah ya saka da alkhairi, ya ja kwanan Alhaji da mami" Ya ce "Da kuma Hajiya" tayi murmushi ta ce "Amin, kuma dan Allah da ka je gida, ka yi haƙuri ka danne zuciyarka, ka bawa yaya Sagir haƙuri dan Allah" "Zan yi in sha Allah" "Allah ya yi maka albarka" Kasa amsa mata yayi sai murmushi, ƙasan zuciyarsa na hango masa ita tana kuka ɗazu. Suka isa bayan layin su ummi, ta buɗe motar ta sauka har ta fara tafiya ya ce "Ke wannan alkunyar taki tayi yawa, maimakon ki ce "Malam bani kayana, ko kin bar mini  dubu sha biyar ɗin taki?" Ta waiwayo ta jinjina masa kai alamar eh. Ya fito daga motar, ya ɗaukko kayan yabi bayanta, ta tsaya cak ta waiwayo ta ce "Ina zaka ne?" "Gidan zan biki na kai miki kayan" A rikice ta ce "A'a dan Allah" "To karɓi kayanki" "To ya zan yi da su, idan aka tambayeni.... "Ki ce da salarynki ki ka saya, ba wasu kaya ne masu yawa ba fa, ya kamo hannunta ya danƙa mata ledar ya ce "Zan je gida na cika alƙawarin da na yi miki" ya juya ya koma motarsa ya tafi. Cikin mamki ummi take kallon kayan, wai duk wannan nata ne? Amma uban kuɗin da raihan ya kashe, dubu ɗari da sha takwas, kayan mai turare da ciye-ciye. Cikin matsananciyar fargaba ta shiga gidan, kasancewar ɗakinta ne a farko, ba ya cikin main safe contain na gidan, shiyasa ba sa sanin shige da ficenta. Ta kalli agogo ta san noor tana makarantar islamiyya, da ta kirata ta gani. Tayi alwala ta yi sallar la'asar, ta zauna ta din ga kallon kayan, wannan mayuka masu uban tsada, ita za ta shafa a fatarta. Wai har da hoda, to ita mai za ta shafawa hoda ma? Ta ɗau turaren tana shaƙar ƙamshinsa mai sanyi da daɗin gaske. Ga roll on, kusan kala huɗu, wanda kullum cikin dabaru take na haɗa alumun, ko ta jiƙa gishiri bayan yi wanka ta shafe jikinta, saboda kar ta yi wari. Wata envelope ta gani a cikin kayan, wadda ba ta san da ita ba, ta ɗauka ta buɗe taga kuɗi a ciki sai takarda. "Assalamu alaikum, brown eyes, this is your first salary, given to you 15th April, spend it well, ga additional na 15k making 30k, ki lallaɓa na ji daɗi na kuma gode da shopping, Allah ya ƙara arziki ummita. Raihan" galala take bin takardar da kallo, Raihan ya mayar da ita sakarya ma. Wurin Alhaji ya fara zuwa, ya tarar da mami, da kuma Hajiya tare da Alhajin. Cikin damuwa mami ta ce "Raihan sannu da zuwa, ba abun da ya sameka dai ko?" Ya ce "A ina?" "An ce mini Sagir yaje har office, ya yi yinƙurin dukanka, na kira wayarka baka ɗauka ba, na zo in ji ba'asi". Raihan ya haɗe rai ya ce "In ji wani munafukin ne ya faɗa?". Alhaji ya ce "Bai yi maka komai ba dai ko?" "To aini Alhaji ban gane yayi mini wani abu ba?" Sagir yayi sallama, suka amsa banda mami da take sababi tana faɗin "Wallahi dole ka ɗau mataki Alhaji, kar a kassara mini ɗa a cuceni" Cikin dakiya Hajiya ta miƙe ta ce "Sagir, uban meye ya kai ka wurin raihan, ka yi yinƙurin dukansa?" Yayi shiru yana kallon Hajiyan. Alhaji ya ce "Yi masa a hankali, ni na tura shi wurinsa, ban san kuma haka zata faru ba, zo ka yi mini bayanin meyafaru?" Cikin fusata hajiya ta riƙo rigar Sagir ta ce "Ba magana nake yi maka ba? Zuwa ka yi kayi rashin mutunci a gaban mutane ko sagir? Idan baku yi abun da za a ce baku kyauta ba ba kwa jin daɗi ko?" Raihan ya cire hannun Hajiya daga jikin Sagir ya ce "Duk fa baku fuskanta ba, ya zaku ɗauki zafi a kan abun da ba a gabanku aka yi ba? Ni ne mai laifi abun da na yi wa yaya Sagir yana gaba da ni ban kyauta ba, kuma da niyyar ba shi haƙuri na dawo, bai kamata ba yadda na yi treating ɗin sa, dan Allah ka yi haƙuri yaya Sagir" wani irin mugun kallo Sagir yayi masa, tare da tunanin wata shiryayyiyar ce Raihan da babarsa suka shirya, kawai ya juya zai tafi, Hajiya ta bishi a zafafe, Raihan ya riƙeta ya girgiza mata kai, kawai ta fashe da kuka zuciyarta na yi mata zafi. "Jarrabawa ce mai buƙatar juriya Hajiya, ki daina yi masa kuka" raihan ya faɗa da sigar rarrashi. Mami kuma sai rashin mutunci take yi, tana yaɓawa Hajiya magana, Raihan ya dafa kafaɗarta ya ja ta suka bar falon yana rarrashinta. "Gaskiya Alhaji ka saka baki, yaranta ba za su lalace kuma ta din ga nema ta ƙwace mini ɗa ba, alhalin yaranta na barazana ga rayuwar Raihan ba. Ummi ta yi ta kiran raihan a waya, amma sai ta ji busy, bama ta shiga gaba ɗaya, haka ta haƙura ta ajiye ta tafi kitchen dan yin sanwar dare. Farida ta daka mata tsawa, ta ce kar ta kuskura ta shigar mata kitchen, ba ta buƙata, domin kuwa barin gidan za ta yi. A karo na farko da ummi ta ji ko a jikinta, yau ta samu hutu. Alhaji Tahir ya kira meeting na gaggawa na iyalansa, da manyan manajojinsa da lawyoyinsa gidansa, bayan sallar isha'i. Suka din ga mamakin hakan, dan kuwa ba su san dalilin hakan ba, dan bai taɓa yi ba. Raihan yana maƙale da Hajiya, dan tun ɗazu da suka bar falon, sashinta ya koma ya tare yana rarrashinta. "Bakomai ne ya sanya na taraku a halin yanzu ba, sai dan gabatar da wani hukunci da na yanke, wanda na daɗe ina nazarinsa kafin yanke shi. Daga yanzu Raihan zai riƙe office ɗina, na tsawon shekara guda, ni kuma zan koma gefe ina monitoring ɗin ayyukan sa, duk hukuncin da ya zartar kamar ni na yi ne, duk mai buƙatar wani abu, zai yi a rubuce ya kai masa, yana da damar sallama ko ɗaukar ma'aikata, kar wanda ya zo ya sameni ya sani in yi masa wani abu, wurinsa za aje. Aikinka tuƙuru shi zai tabattar da kai a kan wannan kujera mai nauyi, Allah ya tayaka riƙo Muhammad Raihan sabon MD na Tahir and Son's Limited. Wata irin razana raihan yayi yana kallon mahaifinsu, yayin da Mami ta rangaɗa guɗa tana faɗin "Ƙaraminsu babbansu, ka ga ɗan ƙaramin sauro mai hana giwa bacci" Hajiya da yake zaune kusa da ita ta yi murmushi ta shafa sumar Raihan ta ce "Allah ya tayaka riƙo babana, Allah ya tsare mana kai" Raihan kuwa miƙewa yayi ya bar falon, zuciyarsa babu daɗi ko kaɗan Allah ya gani baya so, kuma ya ƙudirci a watse ya samu Alhaji. Ayshercool 0808012143 What's app only please 🙏                       *CUTARWA!* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* P27 FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK. https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu Abduljalal Wata kissar sai mata Wuta a masaƙa Cutarwa Ƙanwar maza Gaba da gabanta Aƙidata Ruɗin ƙuruciya Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata. 08081012143. And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link. https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Ayshercool. PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI. 27 Mami har ta yinƙura za ta bi bayansa, amma Alhaji ya hanata, mami tamkar ta taka rawa, tana kallon fuskar Hajiya, ko zata ga damuwa ko ɓacin rai a fuskarta. Amma sam bata ga hakan ba, sai ma fatan alkhairi da take ta yi wa raihan ɗin, su kansu su Salim ko a jikinsu, sai dai Salim ya ɓata fuska ya kalli Alhaji ya ce "Yanzu idan muna buƙatar wani abun sai mun je wannan yaron ƙanin bayanmu ya yarje mana, ni bani da matsala da koma me ka bashi, amma wallahi ba zan je wurinsa neman abu ba, a nemi wani abun kawai" Sagir ya ce "Balle kuma ni, da yayi niyyar dukana, sai dai ace na daina morar komai a gidan nan, da dai ace in je in sake neman wani abu a wurinsa wallahi" "Sagir.... "Shhhh" ita ma Alhaji ya hanata yi masa magana, duk ya ce su rabu da su. Raihan wuri ya samu yayi zamansa, gaba ɗaya ransa babu daɗi, saboda sam bai yi farinciki da wannan al'amarin ba. Har kusan sha ɗayan dare, babu wanda ya san in da raihan ya yi, Alhaji kuma yana falo yana jiransa, dan ya san a daren dole zai dawo ya neme shi. Aikuwa sai ga shi yayi sallama ya dawo, da ya tabattar kowa ya watse. Alhaji bai ɗago ya kalli raihan ba, har ya zo gabansa ya zauna, a hankali ya ce "Alhaji" "Ka dawo ka ce mini ba zaka yi aikin bane ko? Ba ka so na nemi wani, kaima da nake jin daɗinka zaka fara bujure mini" Jiki a sanyaye raihan ya girgiza kai ya ce "Ba haka bane ba Alhaji, yayi mini nauyi da yawa, ba zan iya ba wallaahi kaima ka san na yi ƙanƙanta da wannan al'amarin, kuma nine ƙarami kar yayyena su ji babu daɗi a kan hakan" "Raihan" "Na'am". "Ba lokaci ɗaya kuma kai tsaye na yi assigning ɗin ka a kan wannan matsayin ba, na yi addu'a, kuma na jarrabaka ta kowane ɓangare, kai ɗin ne dai zaka iya, yara nawa Allah yake ɗaukakawa wanda suka kai ka, da wanda basu kai ka ba ma? Wani a waje bare ka ke so na ɗaukko na danƙa masa ragamar dukiyata da kula mini da ku? Ko kuma wannan yayyen naka da ba su san ciwon kansu ba? Ka sani ko takaicin abun da na yi musun, ya sanya su shiryu? Hajiya ce ta bani wannan shawarar, kuma na ga hakan ne ya dace" Raihan ya kalleshi da sauri, ya ce "Hajiya ce ta ce ka bani ragamar kula da harkokinka?" Alhaji ya jinjina masa kai, raihan ya yi shiru yana tunani, ya san da mami ce sai dai ayi mutuwar kasko kowa ya rasa, da dai ta yarda ko ta bayar da irin wannan shawarar. Maganar Alhaji ce ta dawo da shi daga tunanin da ya tafi "Babban mutum, kar ina yabonka salla ka kasa alwala mana, kar ka watsa mini ƙasa a ido, i will always be by your side, duk abun da ba ka gane ba, ko abun da ka ke buƙata i will assist you like a ghost" yayi maganar yana dariya, wanda raihan ma yayi murmushi. "Alhaji ka ɗaureni da jijiyoyin jikina, kana faɗar maganar nan na ji kamar ka sakani a kurkuku". Yayi dariya ya ce "Ba wata kurkuku, ka san babban abun da ya burgeni? Da ka yi offending ɗan uwanka, ka dawo ka bashi haƙuri, ka hana abun da ya faru yin tasiri a cikin gidan nan, da kuma tsakanin iyayenku mata". Raihan ya jinjina kai ya ce "Ummi ce ta bani shawarar yin hakan ai, ba idea ta ba ce". Alhaji ya sake dubansa ya ce "Wace ummi kuma?" "Baka santa ba, ƙawata ce bari ne je na kwanta Alhaji, idan na yi bacci wataƙila kaina ya daina ciwon". "To Allah ya bamu alkhairi, zan saka ranar yi maka walima tare da abokan hulɗarmu da ma'aikata, da gabatar da kai a matsayin sabon MD". "Alhaji riƙon ƙwarya fa ka ce, ko dai wayo ka yi mini?" "Tashi ka tafi sai da safe" kamar soko raihan ya tashi ya bar ɗakin ya nufi ɗakinsa. Wayarsa ce ta fara ringing, ya tsaya ya ɗaga. "Ƙaraso sashina ina son ganinka" ya sauke hannunsa shi ko son yin wata maganar baya yi. Ya koma ya nufi sashin mami, tana falo tana jiransa, "Mami, baki yi bacci ba?" "Ya za ayi na yi bacci, zaka yi mana sagegeduwa, ai bacci bai kama ni ba, dole na din ga bacci da ido ɗaya. Uban me ka je ka cewa Alhaji?". Kai tsaye raihan ya ce "Ce masa na yi ya taimaka ya saukeni daga muƙamin nan". "Saboda ba ka da hankali ko? Allah ya ƙwaci abun ya baka, sai ka ce ba ka so saboda shashasha ne kai raihan?" Bin mami kawai yake yi da kallo, ta haƙiƙance ta din ga yi masa faɗa, shi dai yayi shiru bai ce mata komai ba, babban abun da ya bashi mamaki, irin huɗubar tsiyar da ta din ga yi masa, har ta yi ta gama bai ce mata komai ba, ya tashi ya tafi, yana mamakin halin mami da tunanin yaushe zata sauya. Ta kafa wa Hajiya ƙahon zuƙa, gashi dai hajiya ta tarar a gidan, amma tun tasowarsu mami ta kanainaye komai, gashi kishi take da hajiya kamar abokiyar gabarta, ta haɗe kai da yaranta mata duk sun saka Hajiya a gaba, dan ma duk an yi musu aure saura Nihal da ke karatu a ABU zariya, ba ta fiye zama a gidan ba, shikaɗai ne a ƴan ɗakinsu suke shiri da hajiya, dan shi har ga Allah bai ga aibun matar ba. Ummi kuwa daga ita sai noor suka san da kayan nan, ummi ta ɓoye su a cikin kayanta, tuni ta yi wanka ta fara shafawa, sai dai fa kayan kwalliyar ne ba sa gabanta, ita turarukan da mayukan sun fi ɗaukar hankalinta. Tayi ta kiran Raihan, daga baya tana ta shiga amma baya ɗagawa, tayi wankanta ta shafa mayukanta da turare, tana sake kiran wayarsa farida ta shigo ɗakin. Gabanta ne ya ɗan faɗi, ummin na zaune a kan katifa, babu hijjabin nata na gado, ta saka skirt kawai da vest ga hijjabin a gefe, fatarta tana ta ƙyallin man da ta shafa, ga ƙamshi da ɗakin yake yi, ta saki gashin kanta ta sunkuyar da kai tana danna waya. "Ke!" Ta daka mata tsawa, ummi ta ɗago da sauri, ta ja hijjabi ta saka. "Dalla ki tashi ki wuce ki ɗora mana abincin dare" kallonta ummi take da mamaki, ɗazu taje tayi girkin ta koreta ta ce ba ta buƙata, yanzu kuma ta ce wai sai ta taso ta yi. Da "To" ta amsa, ta tashi ta tafi kitchen. Ga alamar an yi girki, amma duk an jibgeshi an ƙi ci, ta duba tukunya wata jallof aka yi ta shinkafa ta yi jagab kamar da shinkafar tuwo aka yi ta, ta kai bakinta ta ɗanɗana, da sauri ta fuzar an zabga uban gishiri da attaruhu, ga mai male-male a kai. Hakan ba aikin kowa bane sai kausar, dan farida ta ce ummi ba zata sake shigar mata kitchen ba, ta ƙuduri aniyar ƙuntata mata, kausar ta yi girki ya ƙi ciyuwa. A daren ta tuƙa tuwon semovita, ta sallami kowa sannan ta koma ɗaki. Missed calls ɗin raihan ta tarar, da message "Call me when you are available" Ba ɓata lokaci ta kira shi, ya ɗaga da sallama, ta amsa masa sannan ta ce "Ka kyauta raihan". "Da na yi me?" "Ka fi kowa sanin me ka yi mini ai, sannan ka kashe wayarka, daga baya ka ƙi ɗaga wayata, mun yi da kai muje mu yi sayayya, in saya maka abu sai ka sai abun da ya fi ƙarfin kuɗina, kuma ka dawo mini da kuɗina har da ƙari, kafi ƙarfin abun hannuna ko?" "A'a ba haka bane ba, dan Allah kar ki yi mini wata fassara daban". "Haka ne mana, ni bani da abun da zan baka ko? To ka zo ka karɓi kuɗin nan and am serious" Ya gyara kwanciyarsa ya ce "Ni fa a cikin damuwa nake, kaina har ciwo yake yi, zaki ƙara mini damuwa" Sai kuma ta nutsu "Wace irin damuwa kuma?" "Ba maganar waya bace ummi, zan zo in sameki" Ummi ta ce "Amma dai komai lafiya ko? Kar ka sa hankalina ya tashi fa, ka fara gaya mini" "A'a ba abun tashin hankali bane ba, ki kwantar da hankalinki gobe in sha Allah zan zo" "To Allah ya kawo ka lafiya, ko menene ka fawwala wa Allah ka ji?". "In sha Allah, sai da safe" suka yi sallama, ta gyara shimfiɗarta, ta kwanta tana jin ta kamar wata ta daban, ƙamshin da yake tashi a jikinta sai nishaɗi take yi. *** "Anty Rakiya, ai in gaya miki da ƙyar na yi barci daren jiya, tun da Alhaji ya faɗi wannan sanarwar da ƙyar na yi barci saboda murna, shi ɗan naki da yake ba kan gado ya cika ba, ya je ya samu uban wai ba ya so" Rakiya ta ce "Kin ga raihan da rigima, Allah ya kawo dama yayi fatali da ita, kar ki kuskura ki yarda, ai ke lalacewar ƴaƴan can gaba ta kai ki Bilki". Mami ta ce "Can gaba ma, kuma ƙoƙari zan yi duk mai yiwuwa in saka masa ido, dan tun a jiyan na kirawo shi na ƙare masa ta tas, yanzu abun da ya rage zan yi, dole in jajirce kar ruɗin kuɗi ya sanya shima ya fara biye-biye in yi biyu babu, shima ya lalace aure zan yi masa yaya, ai zai iya riƙewa" Yaya rakiya ta ce "Ke bilki" "Wallahi yaya rakiya, kar in je ya lalace mini in shiga uku, idan na yi masa aure, sai ma yafi mayar da hankali a kan kasuwancin uban, ya san yana da nauyi a kansa, duk da ba ma'abocin kula mata bane ba, amma kin san kuɗi, yadda ya samu wannan babban matsayin yakamata ace yana da cikar kamala ta aure kuma" "Wannan gaskiya ne, to da mai zai hana ki haɗa shi da Safiyya, ayi ƴar gida kawai" Mami ta ce "Wallahi kuwa, tuwona naina sai dai kin san shi, ba a iya masa, zan tuntuɓe shi da zancen idan har ya amince bani da matsala, amma dolensa yayi aure, hakan zai ƙara sanya ma'aikatan su girmama shi" Suka cigaba da hira, Anty rakiya na ƙara ziga mami, da yadda za ta ɓullowa lamarin hajiya, ta kankane komai, da kuma muhimmancin aurar da raihan, mussman idan suka haɗa shi

Chapter 26 of 54