Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya ce "Bana son babarku ta zo ta ce ba a kyauta ba" Hajiya ta ce "Ba ƙaninka bane ba? Babu abun da za ta ce" Haka kuwa aka yi, dan sai da suka sake sayen akwati, aka zuba atamfofi da shadda, wanda ake yi wa iyaye, sannan ya gaya masa zai bayar da kuɗin turaren wuta. Gwiwar raihan ba ta yi sanyi ba, dan shi a ganinsa komai zai kashe wa ummi bai faɗi ba. Yadda raihan ɗin ya din ga yi wa salim biyayya, ya sanya da Hajiya ta lallaɓa shi ta ce su tafi tare maidugurin bai yi musu ba. Can Maidugurin ma da ummi ta ce musu raihan zai zo, aka din ga shirye-shiryen tararsa, dan bai gaya mata da Salim zai zo ba ma. Mami ta so hana tafiyar nan, amma Alhaji ya taka mata burki, ya ce babu abun da zai hana raihan zuwa maiduguri, tun da matarsa a can take. Kasancewar ana idar da sallar asuba suka tafi, ƙarfe sha ɗaya na safe suka sauka. Suka bi adress ɗin da ummi ta basu har gidan suka je. Kasancewar sun yi shigar kamala, daga shi har Salim, hakan ya ƙara musu kima a wurin ƴan uwan ummi. Sai rarraba ido kawai yake yi ya ga ummi, aka kawo musu abinci na alfarma. Sun kai a ƙalla awa guda, yaya maryam ta tsare ummi, ta hana ta zuwa, sai daga baya ta shirya cikin lafaya mai kyau, sai ƙamshin turare take yi, hujin hancin da suka yi mata, ta saka barimar azurfa, sai ƙyalli take yi a kan baƙar fuskarta. Da tayi sallama tare suka ɗaga kai suka kalli ummi, babu kunya raihan ya kafe ta da ido. Salim ya jinjina kai a ransa ya ce "Lallai yaron nan akwai tsaurin ido" Ummi ta wani ƙara cika sosai, ga wani irin ƙamshi da ya cika ɗakin. "Oyoyo sweetheart" yayi maganar cikin sanyin murya. Durƙusawa tayi har ƙasa ta gaida Salim, ya amsa mata fuskarsa babu yabo ba fallasa. Ta juya wurin raihan ma ta gaishe shi, ya amsa yana washe baki. Ya ce "Tun da ga yaya salim, akwai kuɗi a jikina, sai a ɗaura yanzu kawai" hararsa tayi ta samu wuri ta zauna. Salim ya mayar da hankali a kan wayarsa, kamar bai san suna wurin ba, raihan kuwa ya rasa control ya din ga zuba a gaban Salim, ummi kuma kunya kamar ta nutse. "Baby me mama take baki ne? Kin ƙara ƙiba, kalli skin ɗinki" "Ni fa bana son ƙibar nan" ta faɗa a hankali. "Ni kuma ina so, baki ga kyan da ki ka ƙara ba, kin ji ƙamshin da ki ke yi kuwa? Anya zan iya jiran lokacin nan, Innalillahi kin ganki kuwa? You look take away, ko dai in yi zamana a nan" Dukan da Salim yayi masa a ƙeyarsa ne, ya sanya shi yin shiru yana sosa kai. Ummi ta yi masa gwalo, ta ce "Bari na je n yi wa mama magana, mu shiga ku gaisa" ta tashi ta fita. Tana fita Salim ya ce "Kai dan ubnka a gidan sirikai fa ka ke? Wannan da bamu zo tare ba me zaka yi?" Raihan ya ce "Bakomai" Yayi ƙasa da murya ya ce "Zaka ƙara da kuɗin gyaran jikin da ake yi mata, kara fa aka yi maka da duk ba ta tambayeka ba, zaka saki bakin aljihu tun da ɗiyar ƴan maiduguri zaka aura" Raihan ya ce "To ai duk ba ta gaya mini ba" Salim ya ce "Ni yanzu na gaya maka, kuma wannan ginin da ka ke yi, ka je ka ce wa Alhaji ya saya ko ka bashi jingina, ka samu gida mai kyau ginanne ka saya" Raihan ya ce "To ai ina son gidan sosai " "To ka ce wa Alhaji ya baka gudunmawar bikin, ka ƙarasa" Raihan ya yi dariya ya ce "Haka za ayi yaya" Ya ɗaga masa gira. Ummi ta ce "Bisimillah ku shigo" Suka tashi suka shiga, suka din ga gaisawa da mutanen gidan, ummi tana gabatar musu da kowa. A ɗakin mama suka yi sallama, suka zazzauna, ta din ga murmushi tana amsa musu gaisuwar. Ta kalli yaya maryam ta ce "Yaya, wannan suwaye?" "Sirikanki ne, wannan ne zai auri ummi" Sai tayi dariya ta rausayar da kai ta ce "Ummin za a yi wa aure yanzu? Ai tayi ƙarama da yawa" Maryam ta ce "Wai ke ummin haryanzu a kan cinyarki take ne tsawon shekaru ba ta girma ba?" Ta kalli raihan ta ce "To kai ba ka ga munin na ta ba? Iya ta ce mummuna ce babu mai aurenta" Raihan ya ce "Haba mama, ummi ba mummuna ba ce ba, kalleta fa ki gani tubarkallah masha Allah" Ta ce "Yauwwa, da ma na faɗa, wani zai ce yana son ummi a haka, amma iya ta din ga yi wa ummi ba'a, har sauran yaran gidan, su yi ta ce mata mummuna ko wasa da yara ba ta yi, kuma duk iya ce ta janyo, da ta tsawatar ai ba za su yi mata ba ko?" Raihan ya ce "Gaskiya ne, amma ummi ai mai kyau ce, ga ilimi da tarbiyya, ta cancanci a so ta" Yaya maryam ta ce "Dan Allah ki daina zancen nan da ya wuce" Salim ya ce "Kamar tana jin daɗin hirar, ki ƙyaleta" Mariya ta sake cewa "Ka san har malaman makarantar su ummi, wai su yi ta ce mata baƙa, na yi ta kuka, ko ace idonta irin na mayu, da ta fita yara su yi ta cin zalinta, shiyasa ni da babanta mu yi ta sonta, ba ka ga yadda yake son ta ba" Raihan ya ce "Allah sarki, mu ma muna son ta sosai" Ta kalli Salim ta ce "Ka ga yadda kakarta ba ta son ta ko? Amma bayan mutuwar baban ummi, matar nan ta ƙwace mini ummi, ba fa iya kula da ita take yi ba, an ce sun azabtar mini da ummi sosai da sosai" tayi maganar tana share hawaye. Salim ya ce "Ki yi haƙuri ki daina kuka dan Allah". Ta kalli raihan ta ce "To ka ga dai yarinya ce, dan Allah ka kula da ita sosai, ka din ga ba ta abinci, idan magariba tayi a saka mata kayan sanyi, cikin dare ma a tashe ta tayi fitsari" Ya ce "Duk za ayi mama, ai ummi yarinya ce kyakkyawa, duk za a din ga kula da ita" "Eh, to amma ban bar maka ita ba fa, zaka dawo mini da ita" Mama ta din ga zuba, suna hira da raihan da Salim, duk rashin sakin jikin salim, suka din ga hira da mama, wani abun idan tana gaya musu, sai tayi kuka, wasu abubuwan ma duk ummi ba ta san sun faru ba. Har da tambayar maryam, wai anya Salim da raihan ba su ne jaririn da suka haifa ba aka ya ce ya mutu. Gashi dai ba ta da cikakken hankali, amma a nutse take, malam kakan ummi, ya din ga yi musu nasiha, tare da gaya musu muhimmancin riƙe addu'a. Salim suka ba su kayan da suka zo da su, Malam ya ce ai ba su suka riƙe ummi ba, dan haka babu buƙatar kawo wannan kayan. Malam akwai kwarjini, ya kasa magana, Salim ne ya tausasa harshe tare da nuna masa cewar ba su takura ba, duk abun da suka yi wa ummi ta cancanta. Kuɗin turaren wuta da na gyaran jiki, suka danƙawa yaya maryam masu kauri. Mama har bakin mota ta raka su, suna cigaba da hira. Ummi ta ji daɗin karamcin da suka nuna wa mama, mama har da tambayar yaushe zasu kuma zuwa? Su faɗi abun da zata dafa musu. Yaya ɗanlami ya ce "Ban da larura ma, yaushe mutum zai zauna ya yi ta zuba da sirikai" Su raihan suka koma kano, cikin farinciki da tausaya wa mama da irin abubuwan da ta din ga faɗa game da rayuwar ummi. Har suka je gida ummi na kiransu na jin yaya suka je gida? Mama sai zancen su raihan take yi, ko sunansu ba ta sani ba, tun da Allah ya sa ta haɗu da ummi, bakinta ya buɗe tayi ta surutu amma da ummi take yi, sai kuma su Salim da suka zo. Da daddare bayan su raihan sun sauka kuwa, ya takurawa ummi da waya, dan duk taka tsantsan ɗin sa sai da ya kusa kauce hanya, sai dai ummi ta yi masa shiru. Kwana biyu da komawar raihan kano,  Salim da kansa ya samu Alhaji ya tsutsiye shi, wai me zai bawa raihan na gudunmuwa. Alhaji ya ji daɗin kulawar da Salim ya bawa raihan a kan aurensa, kuma ya lura raihan ɗin ne bai canza masa daga biyayyar da yake yi masa ba, duk da yana da wani muƙami ba. Alhaji ya ce "Ni za a yi wa solidarity?" Ya ce "A'a ginin da saura ne, kuma saura wata guda biki, za a kai mahaifinta ya ga gida, kuma da kai da hajiya bamu ga gudunmawarku ba" Alhaji ya yi murmushi ya ce "Na tsaya na ga iya gudun ruwan sa ne, kuma yayi ƙoƙari sosai da sosai, kuma babban abun da ya burgeni, duk faɗi tashin da yake yi, bai nemi taimakona ba, bai kuma ci amanar da na bashi ba, ya ɗaukar mini kuɗi babu izinina ba, dan haka za a san abun yi, kar ka damu" Ya ce "Ok, mun gode, dan Allah a bashi da kauri sosai" "Za a duba, Salim na ji daɗin ƙoƙarin da ka ke yi masa, ka yi playing role ɗin ka na babban wa, saura kuma kai ma ka nutsu ka yi naka auren" Salim ya ce "Raihan, duk da wasu abubuwan da mahaifiyarsa take yi, ina kallon yadda yake ɗawainiya da mahaifiyarmu, duk da yadda muke ɓata mata rai wasu lokutan, shi sanyin idaniyarta ne, yana ƙoƙari a kan mahaifiyarmu sosai, amma a cigaba da yi mana addu'a" bai jira me Alhaji zai ce ba, ya fita. Alhaji ya ce "Tabbas raihan babban mutum ne, amma akwai dattaku kam" Da Alhaji ya tashi, a account ɗin Salim ya tura masa kuɗin gudunmuwar auren raihan, kuɗi masu kaurin gaske. Nan da nan aka ƙarasa ginin raihan, suka kai Alhaji tare da Dr. Rana ɗaya suka gani. Jikin dr. Yayi sanyi, gado biyu ya yi wa ummi, da dining da kujeru saiti ɗaya. Sai dai falukan ummi uku, bedroom huɗu, sai kitchen da sauransu. Alhaji ya ja dr. gefe ya ce masa "kar ka damu, ka saka abun da Allah ya yassare maka, zan ƙarasa ba tare da kowa ya sanu ba, ai ana ƙoƙari sai godiyar Allah" Saura sati biyu biki, Raihan ya koma maiduguri ya kai wa ummi katin biki, ya ce ko akwai wanda za ta rabawa a kano ta ce ita ba wanda za ta bawa. Raihan ya tafi da kwana ɗaya, dr. Ya je, ya ɗauki ummi zuwa gagarawa, ta kai musu katin bikin da kanta, in da ta ji daɗi, sai ya tafi da  noor. Kamar kullum, tarbar da ta saba samu ita ta samu, sai dai sai kallon ummi suke yi, ta yi kyau sosai da sosai, a nan dr. Ya gaya wa iya cewar ya gano garin su mariya, kuma ummi tana can, sai da suka yi faɗa sosai da iya a kan hakan. Ummi suna zaune, wata yarinya ta shigo za ta yi sa'ar noor, kallo ɗaya ummi tayi mata ta gane ta, saboda kamar da take yi da hindu matar Idris. Iya ce ta hau zagin yarinyar tana tambayarta daga ina take?. Cikin fitsara yarinyar ta ce "Tasha na bi sajida sayar da shinkafa da wake na tayata ta san mini" "Saboda matsiyaciya ce ke, sai kin tona mana asiri?" "Tun da aka bar ni da yunwa, ba a ƙaunata dole na ciyar da kaina". Ganin da Yarinyar ta yi ummi na kallonta, ya sanya ta ce wa ummi "Ina wuni?" "Lafiya ƙalau ya ki ke?" Ta ce "Lafiya ƙalau" Ummi ta ce "Zo mana" ta ƙarasa gaban ummi ta durƙusa. Ummi ta ciro kuɗi a jakarta ta ce "Ungo, yo cefane sai mu yi girki mu ci, amma ki daina zuwa tasha ba mutuncin ƴa mace bane, kamata yayi ace kina makaranta duk da an yi hutu" Yarinyar ta ce "Ni da bana zuwa makaranta, ko abinci basa bani, sai idan babarmu ce ta bani, kowa ya tsane ni, ni ya zan yi ni na ce a haife ni haka?" Yarinyar tayi maganar tana kuka, duk da ba ta san ummi ba, amma ta ji hankalinta ya nutsu da ita. Ummi ta fuskanci in da zancen ya dosa, ta ce wa noor "Rakata ku yi cefanen, sai ayi girki kowa ya ci" Iya na kallonsu ba ta kula su ba. Kusan mintuna talatin, ummi ta tayar da salla, ta ji sallamar su noor, sun dawo, sai dai suna shigowa ba daɗewa Idris ma yayi sallama, kuma bai yi wata-wata ba, ya hau yarinyar ta sa da duka. Ihu take yi tana neman taimako, ummi ta yanke sallar ta fito da sauri, ya saka itace yana ta jingar yarinyar, har bakinta ya fara kumfa. Ummi ta hankaɗe shi, ta riƙo ta, bai san wacece ba, ya kuma kawo itacen yana ƙoƙarin janye yarinyar, a fusace ummi ta tsinka masa mari, da ya sanya shi ɗaga ido ya ga wacece. "Jahilin ina ne kai? Azzalumi mara imani, ƴar ta ka ma baka ƙyale ba, dabban ina ne kai idris?" Ayshercool 08081012143                            *CUTARWA* *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* 37 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. FOLLOW AND SHARE AYSHERCOOL 08081012143 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. *Alhamdilillah ala kulli halin, ina amfani da wannan damar, wurin isar da ɗimbin godiyata ga ƴan uwana marubuta, tarin masoya makaranta, da sauran al'ummar da suka yi mini ta'aziyyar rashin kakata, ina fatan Ubangiji Allah ya jiƙan magabatanmu baki ɗaya, ya kuma bar zumunci, yayi mana jagora a rayuwa baki daya, Allah ya sanya kaburburan magabatanmu ya zama dausayi daga aljanna, idan tamu ta zo ya sanya mu cika da imani* 37 A razane yake kallon ummi daga sama zuwa ƙasa, iya kuma ta miƙe tsaye da sakakken baki ta kasa magana. Ummi ta durƙusa ta ɗago yarinyar da take zubar da wani irin yawu daga bakinta, saboda wahalar duka. Noor kuwa na gefe tana tsuma, duk da basu saba ba, tare suka yo cefane, har noor ta bata shawarar su sayo taliya sai tafi sauri, tun da ummi ba ta gaya musu me zasu sayo ba. Suna tafe a hanyar ta kalli noor ta ce mata "Ya sunanki?" "Sunana mariyatul kibɗiya, ana ce mini noor" "Masha Allah, sunanki me daɗi" Noor ta ce "To ke ya sunanki?" "Wai hajara, sunan kakata aka saka mini, ni kuwa na ce wallahi bana so, na canza suna ake ce mini Nana" "To meyasa ba kya so, ba kakarku ba ce? Au kamar sunan iya ne ai ko?" Nana ta ce "Eh mana, baki ga yadda ta tsane ni ba, ni ma kuwa na tsaneta, yauwwa idan kuɗin yayi ragowa muka sayi kifi, ba za ta ce komai ba?" Noor ta ce "Ai idan ma kifin ki ka saya da duka kuɗin babu abun da za ta ce miki, yaya ummi fa babu ruwanta" Nana ta ce "Na gani, kin san wani abu, wallahi ta burgeni, ga muryarta mai daɗi, a nutse take komai, sau ɗaya na taɓa ganinta sun zo da kawu yahaya, ƴar sa ce?" Noor ta ce "Ke, ni ma fa ƴar sa ce, iya duk kakarmu ce kenan? To ya aka yi ban sanki ba" Noor ta ce "Ni ba kakata ba ce ba, kakana ta haifa dan haka babu abun da ya yi mini zafi da ita" Wani yaro suka haɗu da shi a hanya ya ce "Nana, ana ta nemanki a gida, wallahi ki je gida baba yana nemanki" "Ba zani ɗin ba, in je a jibgi jaka, gidan iya zan je, tayi baƙi za a dafa abinci, sai na ci na dare zan dawo gida" Mamaki ya kama noor, jin amsar da ta bayar, da aka ce babanta yana nemanta. Sai dai sun shiga sashin iya sun yi sallama babu jimawa, Nana ta fara ɗaukko kwanukan da zasu yi amfani da su su yi girkin, Idris yayi sallama da itacensa a hannu, ya fara jibgar Nana. Marin da ummi ta yi masa ba a kan sa hankalinsa yake ba, face shaiɗan da ya shiga ƙawata masa ummi, hijjabi ne a jikin na roba, dan haka ya kwanta a jikinta, gaba ɗaya tamkar ƙibarta ta koma ƙirjinta, haka da ta juya baya ma, kamar an aunata an dasa mata ƙugunta. "Ke yanzu lalacewar taki har ta kai haka ummi, Idris ɗin ki ka mara?" Duk da jikin ummi tsuma yake da tashin hankali da tsoro, dan ko a mafarki ita kanta ba ta taɓa zaton aikata abu makamancin haka ba. Amma ta ji zuciyarta ta bushe, ta ce "Iya yaushe zaki bari kanmu ya haɗu a matsayin iyalanki ne? Kalli fa dukan da yake yi mata? Mutum ba dabba ba" Cikin ƙwarin gwiwa, da son ɓoye halin da ya faɗa ya aro jarumta ya ce "Ni zaki mara? Kin san abun da ta yi ne?" "Ina ruwana da abun da tayi maka? Barewa za ta yi gudu ɗanta yayi rarrafe ne? Abun mamakin daga haɗuwata da yarinyar yau, har ta fara faɗar irin damuwar da take ciki, look at her, just an innocent kid like me before" Tayi maganar cikin matuƙar rauni, hawaye na zuba daga idonta, tana share wa yarinyar hawayenta da wannan yawun, da daƙalƙallen hijjabin da yake wuyan yarinyar, sautin kukan na ta ma ya kasa fita sai sheshsheƙa, santaleleliyar yarinya kai da ganinta ka san fara ce, azabar datti da rashin kula duk ya dafar da ita. Bilhakki ummi ta rungumeta tana kuka, wanda kukan na ta yana da alaƙa da tuna irin baƙar rayuwar da ta yi a baya. Iya kuwa ba ta taɓa zaton ummi ta yi kilewar da zata iya gaura wa Idiris mari har haka ba. Hashim ne yayi sallama tare da matarsa, ya ji labarin ummi ta zo, ya ce bari ya zo tare da matarsa su gaisa, dan ba su taɓa haɗuwa ba. Amma ya tarar da mutane cirko-cirko, ga Idiris a gefe yana ta huci, ummi a durƙushe da yarinya tana kuka. Ya kalli mutanen ya ce "Lafiya kuwa? Meyafaru ne?" "Ai magaji ba lafiya ba, ƴar daba ta zo mana gida, ashe bayan lalacewa a birnin ina ga ko dai shaye-shaye ko daba ta fara, wai ace ummi ta ɗaga hannu ta zabge Idris da mari" Saroro yayi ya ce "Wane irin mari kuma ana zaune ƙalau?" Iya ta ce"Au to ƙarya zan yi maka, ba gata nan a zaune ba?" Hashim ya ƙarasa gaban su ummi, ya ce "Ummi meyafaru ne?" Ummi ta kasa magana sai kuka. Ya ce "Nana meyafaru?" Cikin kuka yarinyar ta ce "Ƙawata na raka tasha, na tayata sayar da abinci, da ta gama ta bani na ci, shi ne babanmu ya biyoni yana dukana da itace" tayi maganar tana kuka. Magaji ya ce "Tabbas abun da ya baka tausayi, watarana zai iya baka tsoro, Allah ya kyauta, kuma wannan tsayuwar da ku ka yi duk ba mafita ba ce ba, dan Allah kowa ya watse " haka sai hashim ya sallami kowa. Suka gaisa da matarsa da ummi, ummi cikin kuka take yi wa hashim ƙorafin abun da yake faruwa a familynsu, na muzanta wanda wata ƙaddara ta same shi, ko kuma a ɗorawa mutum tsana babu dalili. Ya ce "Ummi, wannan abun da zan iya maganinsa, da tun a kan ki na yi, lamarin yafi ƙarfina, kuma har da sakacin iyayenmu, da son zuciya irin na iyayenmu. Ba irin nasihar da ban yi masa ba a kan kula da yarinyar nan ba, amma yaƙi. Ƙarewa ba ya kula da su da uwarsu, aka korota daga makaranta, uwar ta koma ɗora mata talla, aka tasamma lalata ta, idan ma an lalata tan ban sani ba, duk in da tayi sai tsangwama, na ce ya bani ƴar ya hanani, idan aka ɗora mata tallan sai ta sayar ta kashe kuɗin su yi ta rigima, abubuwan dai duk babu daɗin ji" Ummi ta dafe kai, tare da faɗin "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" muddin ba a takawa wannan lamarin burki ba, ƴaƴa da yawa za su cigaba da shan wahala a gidan, idan har basu zo a yadda ake so ba. Ummi ta bata kuɗi, ta sayo sabulu ta yi wanka, ta bata kuɗin omo ta ce idan ta je gida ta yi wanki, ta ce washegari ma kan su tafi, ta zo ta karɓi kuɗin abinci. Nana ta din ga yi wa ummi godiya, ummi ta roƙi Hashim a kan dan Allah azo mata da Nana kano lokacin bikinta, yayi mata alƙawarin da yardar Allah za a taho da ita. Faranti ɗaya suka ci abinci da ummi, da Nana, nana na ta basu labarin irin azabtarwar da ubanta mahaifi yake yi mata. Ummi a ranta ta ce "Mugunta idan kana yi, ba ka yi wa kanka ba, ai baka iya ba' ta rubuta wa Nana lambar wayarta, ta ce gashi nan ta ɓoye, idan tana buƙatar wani abu, ta saka wani ya kirata. Iya ta din ga bugun cikin ummi, sai ta ji yadda suka haɗu da raihan, da kuma sana'arsa amma ummi ta ƙi gaya mata. Sai dai da dare yayi, Nana ta ce a wurin Ummi za ta kwana, idan ta je gida babansu zai sake zaneta, buɗar bakin Iya sai cewa tayi ba zata kwana da ƙazanta a ɗakinta ba, sai dai ta tafi gidan ubanta ta kwana. Cikin tsiwa Nana ta ce "Sai ka ce wata tsiyar ce a ɗakin, ba dan anty ummi ba nima ba zan ce zan kwana a ɗakin nan ba, kuma in sha Allah sai ɗakin nan yayi gobara, kin ƙone a cikin sa" Iya ta ce "Laaa, ki gani a kan uwarki, tsinanniya" Nana ta ce "Wanda yayi zagi a kasuwa ya san da wanda yake" Ummi kasa magana ta yi, jin mummunan alkaba'in da ƴar ƙaramar yarinyar da ba ta fi sa'ar noor ba, ko sha huɗu ba su cika ba, take ja wa iya. "Oho, idan ma baki ƙone a ciki ba, ko dai ɗakin nan ya zama kabarinki, ko kina ji kina gani zaki barshi tun kina raye" Noor ta ce "Taɓ girma ya faɗi" Ummi ta ce "Shut up noor" "Ai ban ce komai ni" Ummi ta ce "Nana, iyan ki ke gaya wa haka?" "Kina ji fa yadda take tsine mini, ni me na yi mata take ce mini ƙazanta? Ba fa yau ta fara yi mini ba, In sha Allah kina raye sai kin ga ƙazanta a jikinki kuma ba zaki iya gyarata ba" Nana ta yi maganar cikin ɗaga murya tana kuka. Abun duniya ya ishi ummi, ta yi dana sanin zuwa gagarawa. Idris kuwa marin da ummi tayi masa bai yi masa zafin da abun da ya bijiro masa yake damunsa a kanta ba. Yana zuwa gida ya tarar da Hindu a zaune tana tankaɗe, ta saki nono tana shayar da yaro kamar akuya, duk sun zuɓe sun suɗe, ya ja uban tsaki ya shiga ɗaki yana zage-zage. Sai da ya shiga ɗaki ya tsaya ya yi shiru, wai ummi ce ta mare shi a kan ƴar sa, ummin da ya din ga cin ubanta a baya, wai yau ita ce da ƙwarin gwiwar tsinka masa mari. Hindu ba ta kula shi ba, ya hau zage-zage yana ci mata mutunci da ita da Nana. Da abun ya isheta ta ce "Kaga ni fa ban yi maka komai ba, ba zaka din ga zagina ba, Nana kuma ka je can ka nemeta, ni ma ban san gidan uban da ta tafi ba, dan haka ba zaka huce a kaina ba" "Ai koma menene ke ki ka ja, a can gidan Iya na sameta, ta ja mini mari shegiya watsatsiya" Hindu ta ce "kai ne babban watstste da ka kawota duniya, kuma ko waye ya mareka, Allah ya saka masa da alkhairi" suka din ga faɗa, ba ganin mutuncin juna, balle kima. Nana kuwa da ta je gidan, idiris ya kuma yinƙurawa zai daketa, ta fita da gudu, ba ta kwana a gidan ba. Dama dr. Yana garin, cikin gari ya tafi ya samu hotel ya kwana, da niyyar washegari ya mayar da ummi maiduguri

Chapter 38 of 54