Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mahaifiyar Ummi, yakamata a sanar musu. Iya ta ce "Rabu da su, gayyar tsiya ko an gaya musu uwar mai za su tsinana, talakawan banza, ba su ajiye komai ba sai buzu da tawwada sai allo, ai a haka aka tsaface mini ɗa, aka shanye shi ba ya moruwa sai abun da take so, yanzu idan suka sani tsaf za su yi wata ƙulla-ƙullar, a bari sai komai ya lafa, an kwana biyu sai a aika musu da goro da alewa ace na aurar da jikata, shikenan" Saminu ya ce "Amma Iya za su ga kamar ba a kyauta musu ba fa" "Ita abubuwan da tayi mini kyautawar ta yi? Can su ƙarata yarinya ce dai na aurar da ita" Saminu ya jinjina kai, amma dai ya san abun da aka yi ba a kyauta ba, ko ba komai suna da hakki a kan ummi, tun da ƴar su ce ta haifeta. Ummi haka ta sake kwana a gidan nan, ita kaɗai babu idris babu alamarsa, haka ta sake yin kwanan tsoro da tashin hankali. Sai dai wayewar garin Allah, babu wanda ya tuna da ita balle ya aiko mata da abinci. Babar idiris ta fara ƙorafin, tun da aka kai ummi, Idiris bai zo ya ko gaishe su ba, har maganar ta je kunnen iya, ita ma tayi maganar a ranta, amma kasancewar sai a ranar baƙi suka gama watsewa, abun ya dawo kanta. Rai a ɓace ta aika Alhassan, ta ce ya je gidan ummi, ya ce Idris ya zo tana nemansa. A hanyar ƙofar fita, ya tarar da ita a zaune, tana kallon masu wucewa. "Ke ummi, kina amarya kina zama a hanyar ƙofar gida kina leƙe?" Duk da ba shiri suke yi ba, ummi ta ce "Tsoro nake ji, nikaɗai ce a gidan" Ya ce "Taɓ, ina yaya idiris, Iya ta ce yaje tana nemansa" Ummi ta ce "To ai bai taɓa zuwa gidan nan ba, ni tun da aka kawo ni ban ganshi ba" Ya waro ido ya ce "Ke da gaske!? Ke kaɗai ki ke kwana a gidan nan?" Ta ɗaga masa kai alamar eh. Ya ce "Sannu da ƙoƙari, kuma ki ka zauna? Kodayeke idan ma ki ka ƙi zama kin san sauran, bari na je na gaya wa Iyan" Hankalin iya ba ƙaramin tashi yayi ba, da jin cewar wai tun da aka kai ummi bai taɓa kwana a gida ba. Ta ɗau mayafi ta tafi gidan ummi, a nan tsakar gida suka tarar da ita a zaune. "Ke ummi, ashe tun da aka kawo ki, Idiris bai kwana a gidan nan ba?" Ummi ta ɗaga mata kai alamar eh. "Kuma dan ubanki ki ka ja baki ki ka yi shiru baki faɗa ba? Har sai da na aiko, ke da na nemeki na rasa haka na yi miki, ba yawon nemanki na tafi ba? Wato baki damu da shi ba ko?" Ummi dai ta yi shiru ba ta ce komai ba. Iya ta yi ta mata masifa, sannan ta fita, daga gidan, ta saka aka tafi kasuwa aka kirawo babansa, da sagir aka ce musu, ba a ga idiris ba. Iya ba ta damu da tsawon kwanakin nan, ya ummi take ba, ta ci abinci ko ba ta ci ba, bata bi ta kan hakan ba. Aka din ga yawon nemansa, wurin abokansa da sauransu, da ƙyar aka gano shi, can wurin wani abokinsa ya koma, a can yake kwana. Iya ta same shi ta din ga zaginsa, ta in da ta shiga ba ta nan take fita ba, mahaifinsu ma kamar zai kai masa duka, saboda takaici da ɓacin rai. Hashim kallon su Iya yake yi, yana tausaya musu ranar da hakkin ummi zai kama su baki ɗayan su, babban abun da yake ƙara bashi mamaki, irin yadda ba wanda yake iya yi wa musu a kan duk wani son zuciyarta. Ummi ba ta san me yake faruwa ba, sai ma tunanin Allah ya sa Idris yana lafiya, tun da an ce tun ranar ɗaurin aure ba a sake ganinsa ba. Da ƙyar tayi sallar la'asar, saboda yunwar da take ji, cikinta sai ƙugi yake yi, har wani jiri take ji idan ta tashi, ban da ruwa ba abun da ta sha, tana son fita nemawa kanta mafita, amma an ce idan ta fita ba da izinin Idris ba, Allah zai ƙonata, gashi kuma tana son komawa makaranta, amma ba ta ganshi ba balle ta tambaye shi. Sallamar yaro ta ji, tayi sauri ta fito daga ɗakin, wani yaro ta gani da kwano, ya ce mata "Gashi in ji mamanmu" saboda ƙuruciya da yarinta, ummi ba ta tambayi daga ina ba, ta karɓa ta ce ta gode. Dafaffen rogo ne, da ƙuli-ƙuli, ko wanke hannu ba ta yi ba, ta hau rogon nan da ci, saboda yunwar da take ji. Ta gode wa Allah bayan ta kammala, duk da ba ƙoshi tayi ba, saboda ɗan kaɗan ne aka zubo shi a kwano. Ta fito da kwanon tsakar gida, ta saka ruwa tana girgijewa, dan ba ta da ko omo. Kamar wanda aka cillo, ta ga idiris ya shigo, babu ko sallama, hannunsa riƙe da jakar kayansa, wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta yi, saboda faɗuwar gaba da tsorata. Babansa da yake bayan sa yayi sallama, ummi ta amsa ta tsuguna ƙasa ta ce "Baba ina wuni?" "Lafiya ƙalau, ya gidan?" Kai a ƙasa ta amsa masa da "Lafiya lau". "Gashi nan, duk ranar da bai kwana a gidan nan ba, da safe ki je gida ki sanar da ni, zaka ga yadda zan yi da kai, mutumin banza wanda bai san abun da yake yi masa ciwo ba, an lallaɓa abun nan a rufawa juna asiri, ka daina ɗaukko mana magana, amma kana ƙoƙarin tona mana asiri" mahaifinsa yayi masa kaca-kaca, sannan ya tafi. Ummi ji ta yi kamar tabi bayan sa, dan ta wani fannin zamanta ita kaɗai babu Idris shi ne rufin asirin ta. Ta ajiye kwanon da take ɗaurayewa, ta nemi wuri can a tsakar gida ta zauna, tana ta addu'a a zuciyarta. Idris kuwa ya cika yayi fam! Kamar ya fashe saboda tsabar baƙin ciki da takaici, fuskar ummi kawai idan ya kalla, ji yake kamar ya shaƙeta ta mutu, me zai yi da wata ummi, mummuna kamar ba bil'adama ba, aba kamar bayan garwa. Tsaki yayi ya fito zai sake fita, aikuwa ta sake razana, kai tsaye inda take ya nufa, ta fara ƙoƙarin miƙewa tsaye, ya sanya ƙafarsa ya tankaɗata ta faɗi ƙasa. "Shine ki ke je ki ka gaya musu bana kwana a gidan nan ko? Idan na kwana a gidan uwar me zan yi miki?" Da sauri ta girgiza kai ta ce "A..aA'a iya ce ya aiko nemanka, wallahi ba faɗa na yi ba" tayi maganar cikin rawar murya. "Rufe mini baki"  yayi maganar yana dukanta a ka da hannunsa. Ta saka hannu bibbiyu ta dafe kanta, saboda jin zafin dukan da tayi, dan ma Allah ya taimaketa, tudun gashinta bai bari ta ji zafin sosai ba. "Idan ki ka kuskura ko da wasa, ki kai ƙarata, sai na yanka ki, kuma azabar da zan gana miki, sai kin gudu da ƙafarki, ke baki san yadda na tsaneki ba ko? Zaki gani yanzu ai, banza mai kama da dabbobi" Kame jikinta take sake yi, saboda gudun kar ya kuma dukanta, aikuwa sai da ya sake takata da ƙafarsa, sannan ya fita. Sai da ta tabattar ya fita, sannan ta iya ɗagowa a hankali, ta bi hanyar da ya fita da kallo. Ta kalli jikinta, da ya ɓata mata da ƙasar takalminsa, tun da tazo gidan sau ɗaya tayi wanka, shi ma ba soso babu sabulu. Kayan jikinta tun wanda ta zo da su ranar da aka kawota, Iya ta ce za a aiko mata da kaya, amma shiru. A hankali ta saka hannu ta karkaɗe ƙasar, tana takaicin yadda ya ƙasƙantar da ita ta hanyar takata da takalminsa mai datti da taɓo. Tayi shiru tana ta saƙe-saƙe a zuciyarta, ta haɗe gwiwoyinta, ta kifa kanta, ta nemi hawayen ma ta rasa, sai zafi da ƙunar zuciya. Yaya Hashim bai zo ya ganta ba, maman na'ima ba ta zo ba, tayi ta lissafin mutanen da take sanya ran su zo su ganta, amma basu zo ba. *** A ɓangaren mariya kuwa, tuburan depression ya zame mata hauka, ga ta dai a nutse, sai dai babu cikekken hankali, wasu lokutan sai hankalin ya dawo, ta yi ta harkokinta, amma da abun ya juyo, sai daina cin abinci, ta daina magana. Duk wanda ya shigo da ƙaramin ɗa gidan, sai ta ce sai an bata umminta, ko ta ɗauki fulo tana yi masa wasa, ta ce ummi ce. Idan ƴan yara mata suka shigo gidan, suma sai tayi ta kiransu da sunan ummi. Ta ce "Yaya ɗanlami, kalli yadda ummina tayi wayo ta girma". Ya amsa mata da "Tubarkallah, ki yi ta yi mata addu'a, Allah ya ƙara rayata" Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Ba ummi ba ce, ummina baƙa ce mai kyau, bari in tashi in zuba ruwa in yi mata wanka, na goyata garin nan da sanyi" Yayi saurin tashi, ganin da gaske tana ƙoƙarin kama ƴar mutane ta yi mata wanka, ya ce "Ki yi haƙuri in anjima sai ki yi mata wankan". "To ai bana son babanta ya dawo ya tarar da mu, ba mu yi wanka mun yi kwalliya ba, kaga yana son turare da lallen da nake yi masa, baban ummina har kayan kasuwa yake sayo mana" haka tayi ta gwamutsa masa zantuka. Yayi shiru yana kallonta, ba zai manta zuwan ƙarshe da yayi gidan Iya ba, da yaje da maganar neman alfarmar ɗaukar ummi, ko na ƴan kwanaki ne, dan hankalin mariya ya kwanta, ta fara samun matsala a ƙwaƙwalwa, amma ta kada baki ta ce Allah ya ƙara, hauka yanzu ta fara da yardar Allah sai ta din ga bi bola-bola hakkin ran ɗan ta ne. Tun daga nan yayi alwashin ummi ko ƴar gwal ce ba zai kuma zuwa da niyyar a bashi ba. Mama ta fito ta taya shi lallaɓa mariya, suka mayar da ita ɗaki, sai surutai take, tana basu labarin baban ummi da kuma ummi, sai dai ko da wasa ba ta zancen Iya, ko sauran mutanen gidan sai ummi da babanta. Ummi ta sakankance idiris ba zai kwana a gidan ba, dan haka har ta hau kan tsurar katifar ta kwanta, sai dai ta kasa rufe idonta tayi bacci, saboda tana jin tsoro, ga gari hadari na ta haɗuwa, sai addu'a take Allah ya sa kar ayi ruwan sama. Sai da hadarin ya haɗo gaba ɗaya tare da iska, kawai ta ga hasken tochlight a tsakar gida, inuwar Idris ta hango, ya tunkaro ɗakin. Ta runtse idanunta, tana fatan Allah yasa ba shi bane ba, sai dai ta ji ya mayar da ƙofa ya rufe, hakan ya tsananta bugun zuciyarta. Ba ta san me yake yi ba, saboda ta rufe idonta, ƙafafuwanta ya taka ya ce "Ke dalla tashi" yayi maganar a matuƙar kausashe cikin rawar jiki ta motsa, ta tashi zaune, me zata gani Idris a tsaye a kanta tsirara kamar mahaukaci. Ihu ta saki, ta runtse idanunta ta dafe kanta da hannayen ta. "Dalla malama rufe mini baki, ki tashi na ce, uban meye baki sani ba? Munafukar banza da ta wofi, maƙaryaciya an cuceni an haɗani da saura, har da zuwa ki gaya musu bana kwana a gida, ai na san kin san komai kin saba". Kyarma ta fara yi, taƙi motsawa, aka kece da wani irin ruwan sama mai ƙarfin gaske, ba ka jin komai, sai sautin zubarsa da ƙarfin gaske a kan kwano. Ganin za ta ɓata masa lokaci, ya sanya ya jefar da fitilar hannunsa yayi kanta, kamar zararre. Ayshercool 08081012143 *CUTARWA!* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* BRIGHT PENS (FREE BATCH) P12 Kamar mai shirin tarayya da dabba, haka yayi kan ummi, ya fara yage suturar jikinta, yana ja tana ja, tana ihu tana bashi haƙuri. "Ba zaki rufe mini baki ba?" Yayi maganar cikin fusata. Warin bakinsa ya daki hancin ummi, kai ka ce an buɗe masai. Sai dai ba ta gama shaƙe warin bakinsa ba, warin gashin kanta ya daki hancinsa, gashi ne fal Allah ya bata shi, sai dai kasancewar babu gyara babu tsafta, ya sanya yake wani irin tsami mara daɗin shaƙa. Sai da ya ware gashin ya sauka bayanta, warin ya ƙaru har wani gafi gashi gashin yake yi, saboda tururin warin dauɗa da ƙazanta. Ƙyale gashin yayi, ya cigaba da ƙoƙarin rabata da suturar jikinta, sai dai nan ma jikin ummi, warin dauɗa yake yi, da tsamin gumi, saboda rashin wanka da kula. Har ɗauke numfashin sa yake yi, ita kanta ummin warin hammatar idiris ɗin ya hanata sukuni, yafi ƙarfinta nesa ba kusa ba, amma ba ta gaza ba wurin ƙoƙarin kare kanta. Duk da a duhu ne bai hana shi, kifa wa ummi mari ba da dukkan ƙarfinsa, Allah ya sa hannunta ya samu ba fuskar ba, amma sai da ta gigice. Marin da yayi mata ya sanya ta saka kataɓus, har ya cimma in da yake burin zuwa, sai dai wari da ƙarni mai haɗe da zarni ya bugi hancinsa sai da yayi baya, take ya ji cikinsa ya yamutsa masa, kamar zai yi amai, nan da nan zuciyarsa ta fara tashi. Duk yadda ya so ɗauke numfashin sa ya kasa, wani irin baƙin ciki da takaici ya ninku a zuciyarsa, ya laluba ya ɗaukko fitilarsa ya hasketa, ta kare jikinta sai kuka take yi. Ya tashi ya rufeta da duka, abun da ta fi tsana, ya din ga takata da ƙafarsa, sannan ya janyota ya hankaɗata waje ana wannan ruwan saman, ba tare da imani ko tausayi ba. Kuka take iya ƙarfinta, tana danna ƙofar ɗakin, amma ya saka sakata ta ciki. Tsakar gidan ya shaƙe da ruwa, saboda rashin magudanan ruwa a unguwar. Jikinta duk ya yage mata sutura, kuma a haka tsirara ya hankaɗota waje cikin ruwan sama. Ga wani irin tsoro take ji, balle ta tafi ɗaya ɗakin, haka ruwa ya din ga dukanta tana kuka. Tun tana saka ran ruwan zai ɗauke, har ta zubawa sarautar Allah ido, ƙafafuwanta suka gaji saboda tsayuwa, ruwan saman nan ya ƙarasa zuba a kanta. Ta din ga buga ƙofar ɗakin a hankali ta na cewa "Dan Allah yaya idiris ka buɗe mini na ɗauki kayana, sanyi nake ji dan Allah" tayi bugun har ta gaji, jikinta ya din ga wata irin karkarwa saboda sanyi. Ruwan, bai gama ɗaukewa ba, ta fara takawa a hankali ta na ƙanƙame jikinta saboda ƙyanƙyamin ruwan da ya kwaso dagwalon unguwar ya shigo ya taru a gidan. Ɗaya ɗakin ta nufa, sai dai kasancewar ba taga babu ƙofa, a buɗe yake, shima ta tarar ya malale da ruwa, babu in da za ta zauna, ta samu wuri ɗaya ta raɓe tana cigaba da kuka. Har garin Allah ya waye ummi na tsaye, babu wurin da zata raɓa ta zauna, saboda an yi ruwa ba ɗan kaɗan ba. Gari ya fara haske tana sanya ran ya buɗe ƙofa ta suturta jikinta, amma bai buɗe ba, ta din ga fargabar kar a zo gidan a tarar da ita jikinta babu sutura. Sai da gari yayi haske tar, sannan ya zare sakata ya fito ya shiga banɗaki, tana hangen sa ta taga, ganin ya shiga banɗaki, ya sanya ta fita ta shiga ɗakin, ta kwashi kayanta da duk ya yayyaga, ta saka, jikinta sai wata irin tsuma yake yi, saboda sanyi, ga ciwo da jikinta yake yi mata da ƙafafuwan ta. A gurguje ta yi alwala, ta koma ɗakin yin sallar asuba, duk a ɗarare take cikin tsoro take yin ta. Aikuwa a raka'a ta biyu ya dawo ɗakin, bai damu da salla take yi ba, ya hankaɗeta, saboda wata irin tsanarta da yake ji a cikin zuciyarsa. Ta miƙe ta cigaba da sallar, ya tsaya a kanta yana kallon ta yana huci, da ta idar da sallar, ta miƙe zata bar masa ɗakin, amma ya janyota ta baya, ya sake hankaɗata ƙasa. Wata irin ashar da yayi mata sai da ta kalleshi a firgice, ya din ga ɗura mata ashar yana cin mutuncin ta da na iyayenta, har da mahaifinta da ba ya raye a duniyar, har da kiranta da ƴar iska lalatacciya. Ummi ta yi shiru ta sunkuyar da kanta ƙasa, ta nemi hawayen ma gaba ɗaya ta rasa. Har zai fita ya dawo, ya din ga dukanta hannu da ƙafa, cike da tsana da jin haushin ta. Ya gama rashin mutuncinsa ya fita, ta tashi a hankali, ta koma gefe tayi zuru da ido. Sai a lokacin kuma ta samu damar yin kuka, jikinta sai ciwo yake yi, ga yunwa tana ji, gashi haryanzu sanyi take ji, ta kwanta a wurin, ta hau bacci. Sallamar da Iya take kwaɗawa a tsakar gida ne, ya sanya ummi farkawa, ta fito da sauri, ta ga Iya tare da yaya, mahaifiyar su Idris. Murmushi ummi ta yi ta ce "Iya sannu da zuwa, yaya ina kwana" "Ai kya bari mu shigo mu zauna ko" Ta basu hanya suka shiga ɗakin, suka zauna, yaya tayi ƙuri tana kallon ummi, Iya ta ce "Ke lafiya na ga kayanki a yayyage?" "Ba komai" "Kamar yaya ba komai, kamar wadda ta yi dambe" hawaye ne ke shirin taruwa a idon ummi. "Kuma dan ƙazanta tun da aka kawo ki baki canza kaya ba, yau wurin kwana biyar". Ummi ta buɗe baki za ta yi magana, ta kasa hawaye suka riga maganar fita. Yaya ta ce "Menene na kuka kuma ummi?" Iya ta ce "Sangarta mana, idan zaki yi wa kanki ƙiyamullaili ki zauna ki daina wannan kukan shikenan, idan ba zaki daina ba, sai ki yi ta yi, ga kaya nan na ɗebo miki a kayan auren da aka kaiwa waccan, abun bai yiwu ba, sauran an sayar an bashi kuɗin yayi muku cefane, sadakin ki kuma, na bayar a sayo akuya a bayar da kiwo". "Dan Allah iya ki mayar da ni gida, bana son zaman nan" "Ki kiyayeni ummi, tun kan na ɓata miki rai, bana son shashanci, ki tashi ki yi wanka ki canza wannan kayan" Tashi ummi ta yi tana kuka, ta fita tsakar gida, suma fitowar suka yi, wai har tafiya za su yi. Ummi ta tsaya tana kallonsu, suka fice, wai wata unguwar zasu je, to da me za ta yi wankan, ko ruwa ba ta da shi? Ta koma ɗaki ta zazzage lesar vivar da Iya ta kawo mata, atamfa ce kala uku, sai sabulun wanka uku, man shafawa ɗaya da soson wanka. Sai kuma 'yar tsala, a ƙulle a leda, ummi ta ture kayan ta kwanta, wani irin zazzafan zazzaɓi ya rufeta, saboda dukan ruwan sama. Sai da ummi ta kwana biyu tana zazzaɓin nan, babu abun da ya shafi Idris, da ya dawo zai koreta daga ɗakin, bayan ya gama ci mata mutunci da zaginta, wasu lokutan sai yayi mata dukan tsiya ma, duka na cin mutunci, haka take kwana a ɗaya ɗakin da babu ko ƙofa a ciki, idan aka yi ruwan sama, haka zai sameta a ɗakin nan. Ƙarshe ma ya watso mata kayanta da ga ɗakin da katifa take, ya ce ta koma ɗaya ɗakin. Da ya tuna ƙarin da ya ji tana yi, da kuma yadda suka din ga lalubeta tana yarinya, sai ya ji ya ƙara tsanarta, da ganin an bashi saura. Dama abinci ba a magana, ba bata yake yi ba, wasu lokutan ne idan yaran gidan su za su zo, babar Idiris ɗin kan zuba mata abinci a kwano a kawo mata. Tana kwance a ɗaki tana numfarfashi,  zazzaɓi da ciwon kai sun ƙi sauka, fitsari ya dameta, ta tashi da ƙyar, ta je ta yi, tana shirin komawa ɗakin, ta ji an ce "Ummi" Tana waiwayawa taga Na'ima, ai sai ta nemi ciwon ta rasa, cikin wani irin zafin nama, ta rungume Na'ima ta fashe da kuka. Ita ma Na'iman kuka take yi, ta ɗago ummi ta kalleta ta ce "Ummi ba ki da lafiya ne? Na ji jikinki zafi?" Ta jinjinawa na'ima kai. "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, yanzu ummi a rasa wanda za a aura miki sai wannan ɗan iskan, dukan ki yake yi kenan? Kalli shaidar yatsu a fuskarki" Ummi dai ta yi shiru, daga baya ta ce "Mu shiga ɗaki" Saroro na'ima ta bi ɗakin da kallo. "Ummi kar ki ce ba su yi miki kayan ɗaki ba?" "Suna can ɗakin, koro ni yayi nan shi ne yake kwana a ɗakin" Na'ima ta zauna tayi kuka mai isarta sannan ta kalli ummi ta ce "Wai ke ba ki san in da mamanki take ba? Anya ma kuwa sun san halin da ake ciki?" "Yaya Na'ima nifa tun da aka tafi da mama ban sake ganinta ba, dan Allah idan kin san in da take ki kaini, na gaji, wallahi yaya Idris dukana yake yi, duk jikina ciwo yake zai kasheni" Ta rungume ummi, ta din ga rarrashin ta, ta ce "Kiyi haƙuri ummi, ban ma san an yi miki aure ba, mama ce ta aika ƙanin mijina ya gaya mini, Allah yana sane da ke ummi, bari na je gida na kawo miki abubuwan da na kawo miki, sai na kawo miki tabarma da labule, a kafa a ɗakin, tabarmar ki din ga kwana a kai" Ummi ta yi ta mata godiya, ta bata abinci, ta aika ƙannenta suka sayo mata magani, aka kafa labule, ta shimfiɗa tabarma, sai ɗakin ya ɗan yi kyan gani. "Yaya na'ima, dan Allah idan Allah ya yassare miki, ki saya mini wando, nawa ya ƙarasa lalacewa, ba zai saku ba" "Ummi meyasa ba zaki din ga zuwa wurin mama kina gaya mata ba? Ya za ayi ki rayu da wando guda ɗaya, abun da a ƙalla a rana ana so ki canza biyu" Ummi ta yi shiru, tana wasa da yatsun hannunta, yanzu ma dan ta ƙure ne ta nemi alfarmar na'ima, dan idris ya ƙarasa shi, wandon har da in da ta kama take ƙullewa. Ta ji daɗin zuwan na'ima, ta bata abubuwa da yawa, har da kuɗi, sai bayan la'asar ta tafi, kuma Allah ya taimake ta, Idiris bai dawo ba a lokacin. Duk yadda ummi ta so ta yi wa naima bayanin halin da take ciki, kasawa ta yi, ta ji abun yayi mata girma ta faɗa, dan haka ta yi shiru da bakinta, ta samu ta saya mata wanduna guda huɗu, har da ribbon. Duk in da idris ya haɗu da abokansa, suka yi masa kirarin ango, da tambayarsa yaushe za su cin girkin amarya, sai ya hau masifa yana basu labarin halin da ummi ke ciki, na mummunan ciwon sanyi da yadda take bugawa, da ƙazanta tare da ƙorafin ragowa ce aka haɗa shi da ita, su yi ta masa dariya, suna ce masa angon ɗoɗɗoya. Tare da tabattar masa, idan bai yi da gaske ba, sai ya kwashi ciwon. Sai dai ko sun tambaye shi dalilin fasa auren sa da Hindu, sai ya ɓoye musu gaskiyar zancen. Haryanzu kuma bai rabu da hindu ba, yana lallaɓawa su haɗu a wani wurin na daban, duk da tarin kashedi da mahaifinta yayi mata a kan idiris. Na'ima kuwa a ranar  zata koma gidanta, suka haɗu da magaji a hanya, suka haɗu suka gaisa. Ta ce "Yaya magaji ashe aure aka yi wa ummi babu labari?" Hashim ya ce "Ke dai bari na'ima, abun ne yazo babu shiri, ni kaina ban san da zancen ba sai ana gobe ɗaurin aure". Na'ima ta gyaɗa kai ta ce "Amma, ka yi haƙuri da abun da zan ce, wallahi ku din ga gaya wa kakarku da ɗan uwanka gaskiya, ya za a katsewa ummi karatunta, kuma a haɗata aure da wanda baya ƙaunarta, dama ita ba bi ta kanta za ayi, aji ko tana son sa ba, gaba ɗaya a firgice take a cikin gidan nan, jikinta duk shaidar duka, ya korota daga ɗaki, ɗakin da na tarar da ita, ba ƙofa babu taga, babu abun zama, ba ya bata abinci, wace irin rayuwa ce haka? A gidanku ba ta huta ba, an aurar da ita, ta buɗe sabon babi na ƙalubale, sai yaushe za ta huta kenan? Meyasa Iya ta tsani ummi ne, kamar ba a cikin jikokinta take ba?" Hashim ya numfasa, cike da damuwa da takaici ya ce "Biyayyar da iyayenmu ke yi wa Iya, ta samo asali ne ga wasiyyar mahaifinmu, na lallai su yi mata biyayya. Bayan haka ban san dalilin da ya sanya bayan biyayyar suke rufe idonsu a kan gaskiya ba, su kasa nuna mata hanyar da ta dace ba. Nayi iya yi na a kan auren nan, sai dai sun fi ƙarfina, ni dama ba wani shiri muke yi ba, saboda bani da kuɗi, Idris kuma sunan mahaifinta ne da shi. Ƙiyayyar ummi kuma, dama ba ta son mahaifiyar ummi, saboda kawu Magaji yana matuƙar son ta, har wasu lokutan baya iya

Chapter 11 of 54