Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
masu kamshi  Man garan gashi  Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.    *CUTARWA* *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* 39 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. FOLLOW AND SHARE AYSHERCOOL 08081012143 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. *Alhamdilillah ala kulli halin, ina amfani da wannan damar, wurin isar da ɗimbin godiyata ga ƴan uwana marubuta, tarin masoya makaranta, da sauran al'ummar da suka yi mini ta'aziyyar rashin kakata, ina fatan Ubangiji Allah ya jiƙan magabatanmu baki ɗaya, ya kuma bar zumunci, yayi mana jagora a rayuwa baki daya, Allah ya sanya kaburburan magabatanmu ya zama dausayi daga aljanna, idan tamu ta zo ya sanya mu cika da imani* 39 Alhaji ya ce "Jidda ya haka ne? Wace irin magana ki ke yi kuma?" Hajiya ta ce "Kaga ƙyale ni na faɗa, ai a baya ban taɓa yi ba, sai mu gani idan dabarar mutum za ta ƙwace shi, me aka yi da maza ko sati uku ba a rufa ba fa? Baki ga komai ba" Mami kuwa kumfar baki ta din ga yi tana cika baki, Salim ya tashi tsam ya fice, dan baya son hayaniya, hajiya ma ficewa tayi ta bar ɗakin. "Ka gani ko ka ga abun da ka janyo mini ko?" Kamar raihan zai fashe da kuka ya ce "Mami me kuma na yi?" Alhaji ya ce "Raihan bai yi miki laifin komai ba, ke ki ke ƙoƙarin koya masa rashin gaskiya, da kuma raina ki, wuce ka jirani a mota, mu je a kashe wancan case ɗin da ka ɗaukko" Raihan ya fita yana satar kallon mami. Alhaji ya sake mayar da idonsa kan mami ya ce "Gaskiya hajiya ta gaya miki, na sha gaya miki mu maza idan muna kan wannan gigin da rawar kan, ba a cewa za a tanƙwaramu ta ƙarfin tsiya, ko da kuwa iyayen da suka haifemu ne, ke meye ban yi ba a kanki? Ko kin manta yadda na ɗauke ki, na bar ƙasar sama da wata uku na bar hajiya, na toshe kunnena, na ƙi saurara kowa sai yanzu dan abun ya zo kan ɗanki ki ce ba ki san zancen ba? Shiyasa a kowane ƙadami ake so ka zama mai adalci, ko dan gaba, baki nuna mini illar abun da na din ga yi ba, sai daga baya da na gane kuskurena dan kaina, ka kwanta da mace kawai ba shi ne aure ba, wannan abu ne na lokaci, managarciyar mace mai tsoron Allah, da kuma biyayya ita ake fata. Amma idonki ya rufe dan ɗanki ya auri bazawara, sai me qualities ake dubawa ga mutum mai hankali, ba wai abun da ku ke tunani kawai quality na mace ba" da farko faɗa yake yi mata, daga bisani kuma ya koma nasiha, ya gama ya fice daga ɗakin ya bi raihan. Ko kaɗan mami ba ta ji nasihar Alhajin ta shige ta ba ma, babban burinta a yanzu kawai, shi ne raba ummi da raihan tun kan ta kanainaye shi gaba ɗaya. Ba dan tare da Alhaji raihan suka je station ba, da sai raihan ya ja case ɗin, dan kuwa babbar headquarter hukumar ƴan sanda yasa aka kai su, kuma ya tafi da wayar ummi a matsayin shaida. Alhaji ya ce wa raihan, ya kai shi gidansa, yana son yin magana da shi da ummi gaba ɗaya. Suna tafe yana yi wa raihan nasiha. "Babban mutum, na son kana son matarka, amma ka yi ƙoƙari ka din ga ɓoyewa saboda mahaifiyarka da bakin sauran mutane, ka san kishin mata ba lallai sai tsakanin kishiyoyi ba, su ba sa raina abun yi wa kishi, sannan ka yi ta haƙuri kana cigaba da addu'a komai zai wuce, amma matarka ka riƙe ta sosai ka kula da ita" Raihan ya jinjina kai, suka ƙarasa gidan sa, tun da raihan ya kirata ya ce mata tare za su zo da Alhaji, ta gama girki, amma ta shiga ƙoƙarin ƙara wasu abubuwan. Tun da ya zo kanta a ƙasa yake, saboda tsananin kunya, ko sau ɗaya ba ta yadda sun haɗa ido ba, shi duk yadda ake zuzuta muninta shi bai gani ba, sai tsantsar tarbiyya da nutsuwa, kuma tubarkallah shi bai ga wani muni ba. Yayi musu nasiha sosai da sosai, ya ce raihan ya mayar da shi gida. Ummi ta ce "Baba na gama abinci, bari na kawo maka" Alhaji ya ce "Kar ki damu ƴar albarka ta, sauri nake kuma a ƙoshe nake, Allah ya yi muku albarka, ayi ta haƙuri kun san irin auren nan naku, society ɗinmu sun ɗauke shi, kamar wani zunubi, amma tun da bai saɓawa addini ba shikenan. Da ƙyar ya sha lemo ya tashi, sai dai lemon yayi masa daɗi sosai da sosai, lemon cucumber ne da lemon tsami. Da ƙyar wannan tarzoma ta lafa, sai dai aka saka ƴan islamiyyar su ummi ba ta haƙuri, kuma suka rubuta takardar ban haƙuri, suka yi signing ba ruwansu da ita ya taho da ita gida. Bayan ya nuna mata takardar ta jujjuyata ta ce "You go far MD, da duk ba ka yi musu haka ba" Ya ce "No, abun da na yi dai-dai ne, ba zai yiwu su ɗarsa miki wani abu mara kyau game da aurenmu ba, alhalin halataccen aure muka yi ba, kuma gaba ba za su sake yi wa wani hakan ba". Ta ce "To Allah ya kyauta. Alhaji bai ci abincina ba" tayi maganar a shagwaɓe. "Bani in haɗa da nawa da nasa na cinye" "Wai ba ka gajiya da cin abinci ne, ka daina zuwa gym ɗin ma, idan ba ka yi wasa ba, sai ka kasa wucewa ta ƙofar falo" "Eh na ji bakomai, hakan ma normal ne" Ummi ta ce "Sai na saita maka cin abincin ka, ba zan je da kai unguwa ka bani kunya ba, ace ba ka ƙoshi" ya kwashe da dariya, ya ce "Yanzu ba zan gane wannan ba, sai cikina ya cika tukuna". Ranar litinin kuwa, ummi ta sha fama da raihan kan ya tashi ya tafi aiki, aikuwa da ya je ya sha aiki sosai da sosai. Tun da raihan ya koma aiki, sai gidan ya yi wa ummi girma, ba ta aikin komai, duk sai kaɗaici ya dameta. Gashi baƙin da sukan shigo, duk sun daina zuwa. *** Anty Rakiya ce a zaune tana kallon fuskar mami me ɗauke da zunzurutun damuwa. "Ke yanzu Bilki har matar nan ta samu bakin yi miki rashin mutunci, yaushe ta waye?" "Anty Rakiya ni ba wannan ne ya dame ni ba, kar bakinta ya tabatta yarinyar nan ta ƙwace raihan na shiga uku, ta ji daɗin yi mini dariya, shi ne babbar damuwata da tashin hankali" "To wai kin bi shawararin da na baki kuwa?" "Wallahi na bi, kin san raihan da taurin kai, ban gaya miki ranar da na kirshe shi ba, daga shiga ɗaki ya gudu ba. Ya ce mini ya koma aiki ashe duk ƙarya yake yi, yarinyar nan sumi-sumi, kar in je ta ƙwace shi, tun da sa'arsa ce kuma bazawara wayo za ta yi masa na shiga uku Anty rakiya". "Ba ki shiga uku ba, ai wanda ya rigaka kwana sai ya rigaka tashi, dole ki samu hanyoyin muzgunawa yarinyar nan, kuma ki fara matsa masa a kan auren safiyya" Mami ta yi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan, in sha Allah zan cigaba da ƙoƙari". Ranar asabar raihan yana ta murna zai wuni a gida tare da ummi, tana kitchen tana shirya musu breakfast, yana ɗaki yana bacci mami ta kira shi a waya wai ya je. Tamkar ya fashe da kuka, haka ya ji, ya ajiye wayar, yana tunanin meyasa mami take yi masa haka, lallai sai ta shiga rayuwar aurensa da ummi. Ya lumshe idonsa, ransa babu daɗi, ummi ta shigo ta kunna turaren wuta a ɗakin. Ta shiga banɗaki ta haɗa masa ruwan wanka, ta je kan gadon tana ɗan dukan filonsa ta ce "MD, ka tashi ka yi wanka mu karya" juya mata baya ya yi, ya ce "Wake me up in romantic way" Ta ce "Like how? Ba gashi yanzu ka tashi ba" Ya juyo ya kalleta ya janyota jikinsa, yayi kissing ɗin ta a goshi ya ce "Wake up sweetheart" irin haka nake so. Ta ce "Ashe ba zaka tashi ba idan haka zan yi maka, yadda nake fama da kai ka tashi, da ƙyar ka ke tashi fa" Ya ce "A'a idan ki ka yi mini haka sai na fi saurin tashi ai" ya ƙare mata kallo ya ce "Ni gaskiya a daina tashina da irin wannan kayan, ni dressing zaki din ga yi mini yadda ba za ace ki na jin hausa ba ma" Ummi ta ce "Innalillahi, wai dama haka ka ke, mutum sai tsaurin ido, duk a ina ka san wannan ne?" Wata irin dariya ta bashi, ya ce "Ai tsaurin ido ya riga ya ƙare tsakaninmu, tun da ni da ke yanzu kin san waye boss, fita fa zan yi" Ta ɗan ɓata fuska ta ce "Cewa fa ka yi a gida zaka wuni" "To ya zan yi fita ta kamani, ki yi haƙuri kin ji baby" Ummi ta kalli fuskar sa ta ce "Yaushe zaka kai ni gida na gaida su mami ne? Kuma ban je na yi wa Kawu da su anty bangajiya ba". Ya ɗan sosa kai ya ce "Haka ne, amma for now ban ji zan iya bari ki fita ba" Ta marairaice ta ce "Dan Allah" "Na ji amma da sharaɗi" Da sauri ta ce "Menene sharaɗin?" "Sai kin ce mini baby"  tayi turus tana kallon sa. Ya ce "Yauwwa ai na san lagonki, and ki roƙe ni in a romantic way, a guje zan barki". "Dan Allah baby ka bar ni na je na gaida su mami, na je gida na yi wa kawu bangajiya" Ya girgiza kai ya ce "Ba haka ba, idan kin koyo sai ki tambaye ni, yanzu dai tashi mu je ki tayani wanka" sai da ta ɗan matsa daga kusa da shi ta ce "Wanka kuma?" Ya ɗaga mata gira. "A'a zance maka babyn dai" sauka yayi daga kan gadon ya ce "Kina da sauran aiki Salma, ina son soyayya sosai ban sani ba ko dan ban taɓa yi ba sai a kanki, amma ina son gidana ya fi ko ina samar mini farinciki, kar ki saka na fara leƙe-leƙe" ya ƙarasa maganar yana shigewa toilet, a daidai lokacin da ƙirjin ummi ya buga da maganar sa ta ƙarshe. Shi ya ma manta da ya faɗi maganar, ummi kuwa duk ta shiga damuwa, ya gama cin abincin sa ya fice. Ummi ta zauna ta yi shiru tana tunani, abun duniya ya isheta, tana son yin abun da za ta faranta wa raihan rai, sai dai haryanzu tana tsananin jin kunyarsa. Ta buɗe wayarta ta shiga YouTube, tamkar sun san halin da take ciki, ta ci karo da wani video, malamar tana ta bayani a kan kula da miji. Malamar take cewa "Ƴan mata nawa ya tsallake bai aure su ba, ke ya auro ki ya kai ki gidansa, ko da ya kasance mai kule-kule ke ɗin dai ke ya zaɓa, dan me zai kai ki gidansa ki din ga yi masa gidadanci, ba ko yaushe kunya take da muhalli a aure ba" ummi ta shagala tana kallo, malamar har da demonstration na yadda za a yi wa miji kissa. Ji ta yi ana danna bell ɗin ƙofar falon, ta ajiye wayar ta tashi ta buɗe. Ta faɗaɗa murmushinta, ganin wata babbar mace da wata. Tayi musu maraba zuwa cikin falon, tana ta jera musu sannu da zuwa. Matar ta kalleta ta ce "Kin gane ni ne?" Ummi ta yi murmushi ta ce "Na gane ki, maman bauchi ce, ai ya nuna mini a hoto" Hajiya Aisha tayi murmushi ta ce "Lallai kin yi kyan kai, ina can ya aike ni bana ƙasar, ban samu zuwa bikinku ba, na je umara daga nan na tafi aiken raihan" Ummi ta yi murmushi ta kawo musu ruwa, da lemo. Ta ce "Daga baucin ku ka taho?" Hajiya Aisha ta ce "Daga can muke, tun safe muka taho ai" Ummi ta ce "Be gaya mini ba, ai da na ɗora muku girki tun kan ku ƙaraso" "Be san zamu zo ba shi ma, amma yana gida ai ko?" Ummi ta ce "A'a ya fita tun ɗazu" Ta kawo musu kayan tea, ta shiga kitchen ta ɗora tukunya. Siyama ta kalli Hajiya Aisha ta ce "Mummy, ga fa kairun nisa'i in ji raihan, ki ga rashin mutuncin da yake yi mini a kan matar nan, wai duk matan ƙarshen zamani ita suka rako" Hajiya Aisha ta yi dariya ta ce "Raihan ne fa, haka nima yake ce mini duk ranar da na zo gidansa na ci girkin ummi, wai sai na koma bauci ba yatsu saboda daɗi, hannunta akwai maggi" Suka yi ta dariya, nan da nan ummi ta din ga yi musu hidima, ta kawo wannan ta kawo wancan. Duk rashin son sakewa da mutane irin na ummi, ta ɗan sake da hajiya Aisha, suna ta hirar duniya. Hajiya Aisha ta kira raihan a waya tana faɗan ina ya tafi weekends, ta zo baya nan. Ya ce mata yana gida, ta ce ita ba zata kwana a kano ba, ya dawo za ta tafi. Dama duk a takure yake, kiransa kawai ta yi ta zaunar da shi, Safiyya na ta kaiwa tana komowa tayi kwalliya, sai dai ko kallo ba ta ishe shi ba, hankalinsa yana kan wayarsa yana kallon hotunan ummi. Idan ya kalli safiyya sai ya ganta wani iri, shi dai a wurinsa ya fi ganin kyan ummi nesa ba kusa ba, ita baƙinta ke hana a ga kyawunta, kuma yanzu ta washe ta ƙara kyau. Duk da yana complain da kunyarta ta yi yawa, amma yana jin daɗin wuninsa a gida tare da ita, ya ci abinci da ita, ya shaƙi daddaɗan ƙamashin turarukan ta, uwa uba lallausar fatarta da ba ya gajiya da taɓawa, jikinta tamkar jikin tarwaɗa, ko kuma wata fulawa. Shi komai na ta burgeshi yake yi. Raihan ya kalli mami ya ce  "Maman bauci tazo tana gidanmu tana jirana" "Saura ka je ka gaya mata wani abu, ta zo ta cika mini kunne da masifa". Mintuna arba'in sai ga raihan ya dawo. Aikuwa hajiya Aisha ta din ga masifar weekend ya zauna a gida da matarsa, amma ya fita yawo, idan ya je wurin mamin shayar da shi take ko kuwa?. Shi dai bai ce komai ba ya ce "Ayi haƙuri na daina, amma kar a juya mini baya a koma wurin ummi" Ta ce "A'a ni fa na yi ƴa, ga iya girki ga mutunci, kalli yadda ka yi ƙiba fa, ummi ta iya kiwo, ya ma sunan da ka ke gaya mata" Ba kunya raihan ya ce "Khairun nisa'i" Ummi kuwa kamar ta nutse, ta tashi ta tafi kitchen tana wanke kwanuka. Ya sameta a kitchen ya ce "Madam sannu da ƙoƙari, Mummy na ta yaba miki, ina godiya sosai da sosai" Hararsa tayi ta ce "Baƙina ne ai ba naka ba" Ya ce "To ai shikenan, zo ku yi sallama" Ummi ta ce "Har tafiya za su yi?" "Wallahi kuwa, ta ce ko gidanmu ba zata ba bauchi zasu koma, gashi ba su taho da direba ba, kar su yi dare". Ta ce "To yi gaba zan taho" "Saboda me?" "To kawai sai kuma a ga mun jero tare?" Danƙo hannunta yayi suka yi waje, turus ummi ta yi ganin iyayen akwatuna a falo. Hajiya Aisha ta ce "To ga kayanku nan, ku duba abun da bai yi miki ba, sai a canzo, ko kuma ma yi waya kawai, tafiya zamu yi" Ummi ta ce "Mummy ki bari ki kwana mana" Hajiya Aisha ta ce "Taɓ mijina yana gari, wa zai kula mini da shi, sai mun yi waya" Cikin sauri ummi ta tafi ɗaki, ta ɗebo turaren wuta, na gashi da na jiki, ta din ga haɗo kaya a leda, ta bawa Siyama ta ce musu ba yawa. Hajiya Aisha ta yi musu nasiha, tare da fatan alkhairi suka tafi. Nan raihan ya zauna a falon, yana bubbuɗe akwatunan, ummi kawai ta zuba masa ido tana kallon uban kayan da ko a mafarki ba ta taɓa tunanin mallakar su ba. "Ki saukko ki gani mana sweetheart" ta saukko ta zauna a kusa da shi tana kallon kayan. Ganin tayi saroro kamar sokuwa ya sanya ya ce "Ko kayan ba su yi miki bane ba?" Kawai ya ga hawaye na bin idonta, gaba ɗaya ya rikice ya ce "Menene kuma? Ko Mummy sun yi miki wani abun da ya ɓata miki rai ne?" Ta girgiza masa kai alamar a'a. "To menene? Bana son kukanki ummi, gaya mini" Ta ƙara matsawa kusa da shi, ta rungume shi tana kuka. Ya saka hannunsa ya tallafo fuskarta, cikin kulawa ya ce "Gaya mini menene?" "Na gode" tayi maganar wasu hawayen na zubo mata. Raihan ya ce "Haƙƙinki ne fa ummi, meyasa zaki yi kuka?" Ta sake kwantar da kanta a jikinsa, ta ce "You mean a lot to me, na tuna lokacin da na shekara biyu babu kayan kirki, yau ka gwangwaje ni da wannan uban kayan, ni wallahi ban san ma me zan ce ba, kamar kalmar godiya ta yi kaɗan, Allah ya suturta ka duniya da lahira, ya yalwata arzikinka, na gode MD" Jikinsa yayi sanyi sosai, duk da bai san cikakken tarihin ummi ba, amma alamu sun nuna ta sha gwagwarmaya da rayuwa. "To ki daina kukan haka, in sha Allah in dai ina raye, sutura sai dai ki ɗauka ki bawa wani, sutura ba zamu yi ta ɗinka ta muna sawa". "Na gode MD, amma dan Allah kar ka takurawa kanka yi mini abun da ba ka da shi, ni dai na gode sosai" "To ba zaki kirani da wani suna na soyayya ba, sai MD" "MD my dear" ta faɗa tana murmushi. "Wow ashe duk tsawon wannan lokacin, am your dear ban sani ba, barakallahu fik baby" Ɗaɗɗaga mata kayan ya cigaba da yi, kaya sun haɗu masu tsada har da gwal. Sai da ya zo kan akwatin ƙanan kaya, ya din ga ɗaɗɗagawa yana cewa ba ƙaramin kyau zaki yi a ciki ba. Ummi ta ce "Ai kai a nan ka fi kauri, ni bari na je kitchen abincina kar ya kama". Idan ummi ta kalli raihan ta kalli kayan nan, sai ta rasa me ma za ta ce masa, ya baje yana ta aiki a system gefen sa ga biro da takarda. Dogon matashi cikakke, dai-dai gwargwado raihan kyakkyawa ne, kuma duk kyawawan mata babu wadda ya gani ya ce yana so, sai ita kuma yake ta wahala da ita. "Ya dai madam?" Ta tashi ta ce "Bakomai, zan je wancan falon na gyara shi kan magariba". Ya ce "Yauwwa, ni kuwa na ce ko ƴar aiki za a samo miki ne? Ta din ga taya ki aikin nan, yayi miki yawa". Ummi ta ce "Aikin gidan nan guda nawa yake, zan iya abuna" "Faɗi gaskiya dai, ko abun ne ya motsa, dan kar a aure ni" "To a aurekan mana, duk wadda za ta iya zama da ni ta shigo" Ya kwashe da dariya ya ce "Eh lallai kin yi baki baby". Ummi ta ɗauki hoton kayan, ta turawa su Yaya maryam, suka din ga murna tare da sanyawa raihan albarka. Iya ƙoƙari ummi take yi, wurin rage kunyar raihan da take ji. Dan haka a yau tayi iya yin ta tayi irin shigar da yake so. Aikuwa daga kallon da ya din ga yi mata, ta gane ya ji daɗin hakan sosai da sosai. Ya sha mamaki sosai da sosai, dan kuwa tayi masa kyau sosai da sosai, Allah ya taimaki ummi raihan ba shi da abokan da zai yi zaman majalisa da su. Duk a kunyacen take, amma ta dake kar sokoncinta ya sanya shi fara kalle-kallen. "Baby zaka kai ni gaida su mamin da su kawu". Ya ce "Wow, shagwaɓar nan taki tana burgeni ummi" Maganar Iya ta tuna, da take ce mata 'Tana shagwaɓa da fuska kamar kashi' Ya amince da zuwanta gaida su mami, amma ya ce sai ranar juma'a da daddare. Washegari ranar asabar kuma sai ya kai ta gidansu. Ummi ta yi ta murna, raihan ya ce "Ai in dai zaki din ga abun da nake so, zan zama mijin hajiya Salma. Wata irin soyayya raihan yake nuna wa ummi, da take fatan ta ɗore har abada. Ranar juma'a tun safe, ummi take aikin yin sinasir da miyar agushi, wanda za ta kai gidan su raihan. Tun sallar magariba ta shirya take jiran raihan, ya dawo ya ƙare mata kallo ya ce "Gaskiya kin yi kyau da yawa, ba zan tafi da ke a haka ba, sai ƙamshi kuma ki ke yi, am jealous ki rage kyan nan" "Daga ni sai kai fa zamu tafi a mota mu dawo, dan Allah ka shirya mu tafi" Sai da ummi tayi da gaske, sannan ya shirya suka tafi. Tambayarta ya din ga yi a kan wannan kulolin restaurant za ta buɗe ne?. "Eh in dai zaka yi patronizing ɗina" "To ɗan buɗe ki san mini abun da ki ka dafa ɗin" "Aikuwa ba za ka ci ba" "Suna tafe suna faɗansu irin na masoya". Karɓar da mami tayi mata kawai jikinta yayi sanyi, ko kallo ummi ba ta isheta ba. Safiyya kuwa tun da ta ga ummi jikinta yayi sanyi, ana ta ummi mummuna ce, amma ta ga ummi dirarriyar mace, muryarta kawai idan ta yi magana sai ka so ganin waye yake yin maganar, gashi komai na ta a nutse. Duk da dare ne amma duk wanda ya ga ummi ya santa a da, ya san ta canza sosai, fatar nan ta ƙara kwanciya tayi fresh sai ƙamshi take yi. Ko gaisuwar ummi taƙi amsawa. Raihan ya ce "Mami zuwa muka yi ta gaishe ki, ta yi muku bangajiya" "Na ce maka ina nemanta ne, tun a farko ban gaya maka babu yawuna a maganar aurenka ba? Ka nema mata wata sirikar bani ba. Muguwa kawai, sumi-sumi da ke na zata ta Allah ce, ashe mutuniyar banza ce, kuma da ni ki ke zancen. Ɗa na ne dai wallahi sai kin bar shi, zan yi masa irin auren da nake so, kuma ina nan dawowa kanki" Raihan ya tashi ya ce "Ummi mu je mu gaida su Alhaji mu tafi kar dare yayi" Ta tashi kanta a ƙasa, ta ɗauki kwandon da suka zo da shi, ta ajiye wa mami na ta food flask ɗin. Mami  ta ce "Kwashe tsiyarki, ba abun da zan yi da abincinki" Raihan ya durƙusa ya ɗauka ya ce "Bari a ƙarawa mami da shi" Ta buɗe baki tana kallon raihan. Bayan fitarsu Nihal ta ce "Taɓ mami dama haka matar yayan take? Gaskiya babu lallai ya saurari safiyya, kin san halin sa ba komai yake burge shi ba, amma idan ya ce yana son abu ya dage, canza shi sai Allah. Kalli dirarriyar mace ga iyayi". "Ke dalla rufe mini baki, tashi ki bar falon nan" Can kuwa ummi jikinta yayi sanyi, amma karɓar da ta samu a wurin Alhaji da Hajiya, sai ya mantar da ita abun da mami ta yi mata. Sai gashi sun shantake, har goma na dare suna gidan, sun sha nasiha da sanya albarka daga bakin Hajiya da kuma Alhaji. Alhaji da kansa ya kira Salim da Sagir a waya cewa yana nemansu, bayan sun zo, ya sake gabatar musu da ummi. Tun ummi na nan suka fara cin abincin su, suna santi ana koɗa girkin nata, wanda hakan ya yi wa ummi daɗi sosai. Goma da

Chapter 41 of 54