Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI. CUTARWA! AYSHERCOOL (BRIGHT PENS) MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g 47 PAID ADVERT *Hajiya ina zaki? Saurin me ki ke yi haka? Ɗan bani aron mintuna biyu kacal, na gaya miki albishir ɗin da na zo miki da shi. Shin ko kin san sirrin sheƙin fatar ummi, da ya sanya ta kama zuciyar MD raihan ta hana shi sukuni? Kai ba ma skin care ba, har da sirrin gyaran gashi, ina masu fama da amosani, karyewar gashi ko kuma sanƙo, jan gashi ne da ke? Ko taurin gashi kamar soson ƙarfe. Idan matsalar ki budurwar fata, tare da rashin glowing, Annur skin scrub da hair bliss sun shirya tsaf domin magance muku kukanku, me ku ke jira ku tuntuɓe su a kan lambar wayar su dan ƙarin bayani 07045971194 ko 08140450950* 47 Gadan-gadan ya nufi rijiyar yana tangaɗi. Amaryar kawu Ilyasu ta ƙwala ihu da salati, bayan ta shigo daga cefane. Bai kai ga rijiyar ba, ya sake yin jifa da ita. Ta tafi da gudu tana kiran sunan iya, sai dai jini sai zuba yake daga hancinta. Auwwalu kuwa cikin maye yake ta masifa "Sai da na gaya mata ba ruwanta da ni, amma taƙi ji, dama a ƙule nake da ita ta zagi babarmu jiya, duk ta tsane ni saboda bana ba ta kuɗi, ina kallo har kazata ta mara dan tana jin haushina, wallahi wiwina ta fiye mini wannan tsohuwar banzar" yana gama maganar ya juya yana tangaɗi ya fice. Da gudu amarya ta fita tana kururwar neman agaji, mutanen gidan suka fara shigowa, Iya na kwance ko motsi ba ta iya yi. Da ƙyar aka samo abun hawa, aka tafi da ita asibiti, daga can asibitin suka ce sai dai su je babban asibiti, ba zasu iya dubata ba. *** Can garin kanon dabo kuwa, ummi kamar ta taka rawa, saboda ranar dr. Zai ɗaukko mata mama daga Maiduguri, ita da noor sai aiki suke yi, ummi cikinta ya fito sosai ganin tudunsa a rigarta. Dr. Kuwa tun sassafe ya tafi maiduguri, domin ɗaukko mariya, da shi da abokinsa. Can Maidugurin ma, an shirya musu kayan abinci, an yi wa mariya lalle, ta sha gyaran jiki kai ba ka ce ta haifi ummi ba, ana gobe dr. Zai je suka ɗan gayyaci mutane da ƴan uwa aka yi walima a can maidugurin. Anty maryam ta kalli mariya ta ce "Wai duk murnar ganin angon ce haka? Bakinki ya ƙi rufuwa" Ta ce "Haba Anty Maryam, kin saka na ji kunya, kawai zan ga ummina ne, nake ta jin daɗi" "Kai mariya, ke sam ba ki da alkunya,  ƴar fari ce fa" Ta ɗan rausayar da kai ta ce "Shekarar mu nawa ba ma tare, sai in din ga jin tamkar ta koma ƴar karamarta, ƴar baƙar ƴa ta mai kyau, na gyara duk wasu abubuwa marasa kyau da suka faru da rayuwar ƴa ta, wallahi anty maryam haryanzu ina jin tausayin ummi, rayuwar da ta yi ya kasa zama tarihi a wurina, kuma zuwan da ta yi na ƙarshen nan, kamar akwai wata damuwa da take ɓoyewa, fatana Allah ya sa ba wata matsalar ce a gidan auren nata ba, Allah ya sa ta daina shan wahala" kan ta kai maganar gaba ɗaya hawaye ya wanke mata fuska. Mama ta ce "Mariya, ba zaki daina ɗorawa ranki damuwar abun da ya wuce ba ko? Ga bawan Allahn nam sun zo, ai sai su zata ko son shi ne ba kya yi" Sallama dr. Yayi tare da abokinsa, suka amsa suna yi masa sannu da zuwa. Suka shiga ɗakin da aka saba saukarsu, ya kalli maman ummi, ya tuna maganar Farida, ta yi shar da ita, sai dai yayi mamaki ganin tana kuka. Ya kalli mama ya ce "Mama lafiya kuwa take kuka?" Anty maryam ta ce "Daga yin zancen ummi, ta hau kuka ta ƙi ta bar abu ya wuce, kullum ta tuna rayuwar ummi sai ta yi kuka, abu ya riga ya zama tarihi" Mariya ta ce "Anty Maryam, tun tana kan cinya fa, aka ƙwace mini ita, kuma fa itakaɗai ce da ni" Mama ta ce "To da mutuwa ta yi ya zaki yi?" Da sauri ta ce "A'a ummi ba zata mutu ba, babanta ya mutu, ƙaninta ya mutu, idan ta mutu ya zan yi?" Dr. Ya fuskanci jikinta haryanzu da saura, kuma tuna rayuwar ummi, ke saka jikin ya motsa mafi akasari, dan haka ya ce "Shikenan ya isa haka, ke da zaki koma kano ma, duk lokacin da ki ke so zaki ganta, ku koma kusa da juna" Kamar ƙaramar yarinya take goge hawayenta ta ce "Ni sonake ta koma ƴar ƙarama kamar lokacin da iya ta ƙwace mini ita, in din ga goyata, idan na yi mata wanka na yi mata kwalliya, amma kawai iya ta ƙwace mini ita, ga zafin mutuwar mijina" Ya ɗan ƙura mata ido, ba a ƙasa ummi ta ɗaukko shagwaɓa ba, duk da ummi ta ninka mariya shagwaɓa nesa ba kusa ba. Ya kalli su Anty Maryam ya ce su ɗan basu wuri. Bayan sun fita ya matsa gabanta ya ce "Haba maman ummi, idan mijinki ya mutu yanzu ba gani ba". Ta kalleshi ta ce "Kai ba bashir bane, yaya yahaya ne, ba na so kai ma iya ta ce na kashe ka, wai iya ta ce ni na kashe baban ummi, ya za ayi na kashe shi?" Tayi maganar hawaye na cigaba da zuba. "Ki manta da maganar iya, yakamata ace memorynki, yana tuna abubuwa masu daɗi, idan baby ki ke so ki yi addu'a Allah ya kawo miki ƙannen ummi, ki yi ta goyawa ita yanzu ummi tana da mai goyata" Ta ɗan yi shiru kamar wadda ta farka daga bacci ta ce "Kai, ummi fa ta yi aure, kuma nima sai na haihu?" Yayi murmushi, ganin kamar tunaninta ya dawo. Ya ce "Idan ki ka cigaba da kuka, da tuna abun da ya wuce, ba zan tafi da ke ki ganta ba". Haka yayi ta rarrashin ta, dama tuni su mama sun haɗa mata kayanta, suka raka su har mota, suka kama hanyar kano. Gidan ummi, bayan sun gama aiki, noor ta ɗauki wayar ummi ta tafi ɗaki tana game. Ummi kuma na falo tana kallo, sai ga Farida ta zo gidan, gidan da tun da ummi tayi aure, kusan shekara ba ta taɓa takowa ba. Sai dai duk yadda ake kwatanta mata haɗuwar gidan ummi, sai yanzu ta tabattar da idonta ya gane mata. Kamar babu komai ummi ta tashi cikin fara'a, kamar babu wani abu a ƙasa tana "Oyoyo, yau na yi babbar baƙuwa, sannu da zuwa anty" wani irin mugun kallo take yi wa ummi, da mamakin iskanci ne ko rainin hankali ya sa take wannan washe mata bakin. "Ke saurara bana son karuwanci da iskanci, ni zaki yi wa bariki kina wani washe baki kamar bakin buhu?" Ummi ta shafa bakinta, a iya saninta dai ba ta da ƙaton baki, ji ta yi kamar ta yi dariya amma ta maze ta ce "Ai baƙonka annabinka anty, kuma akwai hadisin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, da yake cewa wanda yayi imani da Allah da ranar lahira, ya girmama baƙonsa. Ki zauna bari na kawo miki ruwa". "Ki yi mini shiru ko na ɓarar da ke, ba ki da abun da zaki bani, ke da aka kawo mini ke cikin dauɗa da ƙazanta babu ko suturar kirki, har ke ki ke da abin bani, dan kin auri mai kuɗin da uwarsa ba ƙaunarki take yi ba, auren abun kunya, auren yaro ƙarami? Butulallaiya mara mutunci, wato abun da ki ka yi wa wancan ƴan ƙauyen shi ne nima ya biyo ta kaina, ki ka saka dr. Ya auri babarki, mahaukaciya da ba ta san ciwon kanta ba?" Ummi ta ce "A'a fa, ni ban bayar da shawarar hakan ba, dr. Ya zo mini da maganar na goyi bayansa ɗari bisa ɗari, ko ba komai na yi ramuwar gayya, kuma ba fata ba ko aurena ne ya mutu, ko wani abu ya faru ina da wurin zuwa. Da ki ke iƙirarin an kawo ni cikin dauɗa da ƙazanta, ai ba ke ki ka kula da ni ba, wan ubana ne, dan haka ke bai kamata a ji wannan gorin daga bakinki ba, ba ki isa ki yi mini gori ba a kan wannan, ko kin manta irin riƙon da ki ka yi mini?" Ummi ta ɗaga rigarta, gefen cibiyarta ya ɗan yi shati, ta ce "Na san wataƙila ke kin manta, kuma an yi sa'a jikina ba ya riƙe tabo, wannan ne kawai yayi saura kuma da shi zan koma ga Allah, har azaba da wuta ku ka yi mini ke da ƙanwar ki, wallahi da ramuwar gayya zan yi a kan ki, sai kin bar gidan dr. Kuma Alhamdilillah a yanzu dai Allah ya yi mini sutura da rufin asirin da ba kwa so, kuma wallahi ni Salma ina da abun da zan baki. Amma ba wannan ba, na zata bayan na yi aure komai zai wuce, na yafe komai ya wuce, amma na fuskanci hali zanen duste ne, ba zaki canza ba, tun bayan da ki ka yi mini korar kare da na je gida aurena ya samu matsala, dan haka mun saka ƙafar wando ɗaya da ke, za ki ga mahaukaciya ganin idonki, yadda na ke shimfiɗa mulkina ba boka ba malam a gidan mijina, sai uwata mahaukaciya ta shimfiɗa na ta mulkin ba yadda ki ka iya, zaɓi ya rage naki, ko ki kwantar da hankalinki ku zauna lafiya, ko kuma ki shirya yin fito na fito da ni, tsakanina da ke babu ɗaga ƙafa, kuma ki gaya wa rahama, idan har muna raye sai Allah ya jarabceta da wuta, kamar yadda ku ka yi mini azaba da iata, dan wallahi ban yafe ba! Ko zan yafe muku komai, banda wannan" Tirƙashi! Ummi ta shayar da farida ruwan mamaki, gani take kamar daga wani wurin maganar ke fitowa ba bakin ummi ba. Cikin dakiya farida ta ce "Yaushe aka yi daren, da har gari zai waye, ki ke iƙirarin shimfiɗa mulki a gidan miji? Ɗa namiji ne fa da bashi da tabbas". Ummi ta yi murmushi ta ce "Anty farida, ai daren yayi tsayi, ke ce ba ki farga ba, sai da garin ya waye. Duk da kina iƙirarin uwata ba ta da hankali, amma a hakan ta din ga yi mini nasihar, jin tsoron Allah, riƙe addu'a da biyayya a aure, idan har tsoron Allah, addu'a da yi wa miji biyayya na saka a ci ribar aure, da yardar Allah ni da uwata mun fi ƙarfin masu bin ƴan tsubbu, kuma zamu zauna dai-dai a gidan miji, namiji ba shi da tabbas, ya danganta da yadda ki ka ɗauke shi ne, nawa yana da tabbas, haka babana dr., Ke ce baki iya tattalinsa ba ki ke ganin ƴan tsubbu sun mallake miki shi, shiyasa ki ka ga bashi da tabbas". Farida ta saki baki, hangal tana kallon ummi, ba ta gama mamakin ba ummi ta ce  "Yauwwa tun da bani da abun baki, zaki iya tafiya, na ga kin yi mini aike noor ta koma, in dai noor ce, sai dr. Ya ɗauke ta ya ba wa mamana, saboda kin raini ƴar ki da ƙiyayyarki, saboda banzan dalilinki, na an saka mata sunan mahaifiyata, duk shaƙuwar ɗa da uwa, ta fi son babanta a kanki, cikin sauƙi zan sanya ya karɓe ta ya bawa mama ita, ba zan so ta tashi da rashin imani irin naki da su kausar ba, masu baƙar zuciya ba, tayi aure tana hali irin naki ba, idan kin fita ki rufe mini ƙofar falo, kar ƙuda ya shigo mini bana son ƙuda" ko jiran amsar farida ba ta jira ba, ta bar falon ta bi wata hanyar, ta tafi can bedroom ɗin da noor take, wadda ba ta san ma farida ta zo ba. Ƙarfe huɗun yamma, dr. Ya sauka, basu tsaya ko ina ba sai gidan raihan, ta rungume ummi suka din ga murna, kamar sun shekara ba su ga juna ba. Sam farida ba ta san ranar ma maiduguri ya je ba, yana komawa gida, ta dira masa bala'i tana gaya masa abun da ummi ta yi mata. Kai tsaye ya ce ƙarya take yi wa ummi, sharrinta ne kawai ummi ba zata aikata haka ba, tsabar kishi ne kawai, idam ma hakan ne meyasa da ba ta je gidan ummi ba sai yanzu da wannan lamarin ya zo. Abun duniya duk ya ishi farida, asirin tayi har ta gaji, ya shammaceta, da kan ayi ne da ta yi yaƙinin asirin zai kama shi, maganar ta rushe. Raihan ma ba ƙaramin daɗin zuwan mariya ya ji ba, tayi ƙalau da ita. Noor kuwa tun bikin ummi da suka je maiduguri, suka saba da mama, tun da dr. Ya gaya mata takwararta ce. Kuma aka yi sa'a ba ta manta ta ba, a ranar da daddare, sai ga Salim ya zo har da Sagir. Mariya ta din ga murna, duk idan tana magana wasu lokutan ta kan haɗa da shirme, amma a hakan take yi musu nasiha, tare da ƙara musu haske a kan rayuwa. Sagir ya din ga mamaki da aka ce ita ce maman ummi, ita da haskenta ma, ummi ce dai baƙa, sai dai idan tayi wani abun kamar ummin. Ta tsiro da batun cewa lallai, a kai ta su gaisa da babar raihan, da babansa sun gaisa da Alhaji, babar raihan ce ba su taɓa haɗuwa ba. Gaban raihan ya faɗi, amma ya basar ya ce zai kaita su gaisa. Su Salim sun daɗe sosai, duk da a zahiri bayan mama, noor ce ta riƙe shi, dan chatting suke a wayar ummi ba ta sani ba, idan suka gama sai ta goge. Ummi ta yi iya ƙoƙarinta, ta mantar da mariya, batun haɗuwa da babar raihan. Allah ya taimaki Iya, ba ta samu mumunan rauni ba, sai dai ta fasa kai, fuskarta duk ta ƙuje, sannan ta targaɗe ƙashin ƙafarta, da hannunta, gashi kuma kanta sai da aka yi mata ɗinki, kan ayi ɗinkin nan kuwa sai da aka sauke gashin kan gaba ɗaya, ga bakinta ya kumbura saboda wahala. Da ƙyar suka yi karo-karon haɗa kuɗin magani, likita ya rubuta hoton ƙwaƙwalwa, saboda kai da take ta kuka da shi, amma babu kuɗin yi, maganin ma ba duka suka saya ba. Suna tsaka da wannan gaganiyar, ana ƙoƙarin kiran dr. Suka samu labarin yayi aure, ya auri mariya. Gaba ɗaya sai suka manta da halin da iya take ciki, suka shiga salallami. Iya na daga kwance ta tuna yadda tun bayan ya gano in da mariya take, ya ce zai aureta, amma ta ce ba ta lamunta ba, tun da ya riƙe ummi shikenan, ba zai sake kwasota ya kawo musu dangi ba, saboda a cewarta mariya annoba ce, mugun abun ta ne ya sanya ta haukace. Su ummi suna airport, tare da dr., Ta wani ɓangaren ransa a ɓace, saboda tijarar da ya sha a wurin farida daren jiya, da ya ce yau zai koma uganda, tare da babar ummi. Har da zaginsa ta ƙare masa cin mutunci, abubuwa da dama yana duba yaransu ne ya sanya yake ɗaga mata ƙafa, kuma tun ainihi, shi mutum ne mai sanyi ba shi da hayaniya, shiyasa take yi masa duk abun da ta ga dama. Suna airport sun rako su dr. Mariya sai kalle-kalle take yi, da alama a tsorace take. Sai ga wayar kawu Sagir, dr. Ya ɗaga tare da amsa masa sallamar. "Yanzu yahaya tsakaninmu da kai abun har ya kai haka? Muna ƴan uwanka amma sai dai mu ji a gari ka yi aure? Abokanka sun fi mu kenan?" Dr. Ya ce "Ba abun ɗaga hankali bane ba, abun ne ya zo ba shiri, na ga akwai buƙatar tun ina raye ya zamana ummi tana da madogara ko bayan raina, dan yadda ba a kula da ita bayan ran mahaifinta ba, bayan raina ma ba za ta sauya zani ba, dan na san kun san wadda na aura, kuma da na neme ku, ba zaku bari ba, da kaina zan zo har gida na yi muku bayanu" "Aishikenan, ni ba ma wannan ba, ka ganmu fa a asibiti da iya" "Subhanallah me ya same ta?" "Wallahi dai tsautsayi ne, Auwwalu ne ya sha ta gaya masa ƙarya, ta yi masa faɗan rashin sana'a sai bacci, ya din ga tamaula da ita, saura ƙiris ya jefa ta a rijiya. Yanzu dai gamu a asibiti, magunguna an sayi wasu, wasu kuma ba a saya ba, ga hoton kai an rubuta shi ma ba kuɗin" Dr. Ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ka ga illar rashin mayar da hankali a kan tarbiyyar yara da iliminsu ko? Ina Auwwalun yake?" "Ya gudu ba a san in da yake ba". "To ka ga ni yanzu ina filin jirgin sama, zan koma makaranta, zan turawa Abdul kuɗi ya zo ya dubata ya baku, Ubangiji Allah ya sauwwaƙe" "Amin, amma dan Allah yayi sauri ana buƙatar kuɗin" Dr. Ya ce "Sai ya tura muku, idan ya so daga baya sai ya zo ya dubata" Kawu Sagir ya ce "To hakan ma yayi, bari na ga Idris yana da lambar banki, sai a turo ya saka kuɗin, an gode" bayan dr. Ya gama wayar suka din ga jajantawa, mariya kuwa ko Allah ya kyauta ba ta ce ba. Ummi har da hawayen murna, ganin mama tare da dr. Za su keta hazo tare, ko ba komai tana sanyawa mama ran samun kulawa daga dr. Kasancewarsa jajirtaccen mutum. A ranta ta ce "So so ne, amma son kai ya fi, in sha Allah a kujerun hajji da umaran da Alhaji yake rabawa sai kun samu, ko ban je ba ku je a tare hakan nan, ku yi mini Addu'a. Bayan jirginsu ya ɗaga, suka koma gida. A cikin jirgin ƙanƙame dr. Ta yi, saboda gani take kamar za su faɗo daga cikin jirgin. Dariya ya din ga yi mata, ganin yadda take a rikice gaba ɗaya, hakan ya bashi damar rungumeta a jikinsa, sai wani irin daddaɗan ƙamshi take yi. A hankali take tambayar sa "Baban ummi ba zamu faɗo ba kuwa? Tsoro nake ji sosai" "In sha Allah ba zamu faɗo ba, lafiya zamu sauka". Dr. Dubu hamsin ya turawa Abdul, ya ce masa ya tura wa su iya idan sun turo account number, shima ya ƙara dubu talatin ya tura musu dubu tamanin. Ummi bayan sun koma gida, raihan ne ya sakata a gaba, yana mammatsa mata jikinta a hankali cikin tsantsar soyayya da kulawa yake ce mata "Am sorry sweetheart, kwanan nan am very busy, kamar bana kula da ke sosai, kuma na san kina buƙatata" Tayi murmushi ta ce "Saboda jin daɗi yayi mini yawa ko? A cikin mata hamsin nawa ne suke samun kulawar da nake samu, idan suna da juna biyu, kana iya yinka aiki ne yayi maka yawa". Ya numfasa ya ce "Duk da haka dai, wallahi ummi wasu lokutan kaina kamar ya fashe, ina jinjinawa Alhaji yayi ƙoƙari, kin ga yakamata ace Yaya salim yana cikin system ɗin nan, tun da bamu muka tara dukiyar ba, mu kula mu tattalata ta haɓaka, ga branch ɗin mu na Abuja, ina ga a watan da zaki haihu za a buɗe shi, ban san ma ya zan yi ba, wa za a mayar can Abujan, atleast yakamata ace da wani daga cikin mu" Ummi ta ce "Mhmm ka lura zuwan yaya Salim gidan nan ya ƙaru sosai?" Ya jinjina kai ya ce "Magana ce kawai ban yi ba" "Anya nan gaba magana ba zata taso tsakanin sa da noor ba, shaƙuwarsu ta yi yawa" Cikin murna raihan ya ce "Wallahi sam ban kula ba, tun da ya ce ke ƙanwarsa ce na zata saboda ke ne, yana cigaba da bibiyata ne kar na yi miki wani abu. Amma kina ganin dr. Zai bashi ita? Kamar yayi mata tsufa kuma ga yanayin sa" Ummi ta ce 'Aikuwa yaya Salim ya shiryu, a kan lokacin da na san shi, ba abun da zai hana ya bashi ita, nima haka aka yi mini surtu da na aureka, in dai suna son juna ba shikenan ba" Ya jinjina kai ya ce "To Allah ya tabattar mana da alkhairi, Kairun nisa'i, wannan cikin naki kamar ya fi ƙarfin watanninsa, kafin mu koma awo, sai mu je ayi miki scanic kawai mu tafi da shi" Ummi ta shafa cikin ta ce "Nima na gani, kamar girman yayi yawa a wata biyar, amma sai a sake hoton" Sun jima suna hirarsu cikin nishadi, har ta nemi izininsa a kan zuwa duba Iya, an kai ruwa rana kan ya amince, ta ce idan Abdul zai tafi sai ta bishi ita da noor. Ummi tun bayan dawowarta, ta duƙufa Addu'a, da roƙon Allah ya sassauta mata mugun kishin da yake damunta. Babu dare ba rana, ta miƙe da yawan tasbihi da bayar da sadaka, tare da tawasalli da ayyukan alkhairin ta, tana roƙon Allah idan auren Raihan da alkhairi Allah ya tabattar ya rage mata kishi, idan babu kuma, Allah ya rusa abun, ya musanya da mafi alkhairi, yayi mata maganin duk wani abu da zai tayar mata da hankali, ko kawo cikas ga rayuwar aurenta. Sannan ta tsananta addu'a, a kan Allah ya ƙara qa raihan son ta, da ƙaunarta ita kuma Allah ya bata ikon yi masa biyayya. A hankali ta ji zafin kishin yana raguwa, bayan auren mamanta da dr. Ta din ga istigfari a kan ɗagawa raihan hankali a kan maganar auren sa, wataƙila da ta cigaba da matsawa, da ba ayi na mamanta ba. Lokaci ɗaya mami ta daina kira tana ɗagawa raihan hankali a kan auren nan a gabanta, kuma ta daina zuwa ci mata mutunci, dama tuni ta saka lambar maryam a blacklist. Gidansu raihan kuwa, rana tsaka babu notice, Hajiya Aisha ta dira a gidan Alhaji Tahir. Sai da yayi mamkin ganinta, ya ce "Ke hajjaju, zuwa ba sanarwa matan gidan babu wanda ya sanar mini zaki zo ai". "Ina na ga ta tsayawa jiran notice, ashe raihan zai ƙara aure, kuma daga ɓangaren uwarsa, haba Tahir, kuma kana kallo, yaushe yayi auren farin zaku ɗora masa ɗawainiyar auren matan biyu?" Alhaji ya ce "Ke daɗina da ke, ba kya ɗaukar abu da sauƙi a kan raihan, babarsa ce take son ya ƙara" "A'a ban lamunta ba, yanzun ma ba dan Salim ya gaya mini ba, ba zan sani ba kenan? Kuma a rasa wa zai aura sai wannan dangin masifa da bala'in, ashe har ƙarya yayi muku bashi da lafiya dan ku ƙyale shi, amma abu kamar bala'i, kuma saboda tumasanci irin na bilki har da sakawa ya saki ƴar mutane, to mu ba haka muke ba, ko da muka yi bore da ka aure ta, ka juyawa ƴar mu baya, bamu ce ka saketa ba, dan haka da kaina na zo na yi wa tufkar hanci, ba zai auri ƴar rakiyar ba". Alhaji ya ce "Ke ki daina yi mini faɗa kamar wani ɗanki mana, har kuɗi fa an kai". "Amma ai ya ce ba ya so, dole na yi maka faɗa, ba fa kowane lokaci yakamata ka din ga biye wa matanka da yaranka suna abun da suke so ba. Wallahi muddin ta ce sai yayi auren nan, sai dai ta nema masa wata sana'ar ta kafa shi, ya bar shugabancin kasuwancin ka, dan na san da shi take taƙama, idan ba zaka iya cewa an fasa ba, zan je na yi wa ita rakiyar magana, dama ni da ita kar ta san kar ne ai. Su riƙe kuɗin an bar musu, amma ƙara aure ba yanzu ba". Tana tsaka da masifar, Hajiya ta kawo mata abinci, ita ma ta rufeta da faɗa a kan, meyasa ba a gaya mata abun da yake faruwa ba, dan haka ta je ta kirawo mata bilki, kuma a kirawo mata Salim, dan ta tabattar mata shi ya gaya mata ba Raihan ba. Aikuwa ranar mami ta ga ta kanta, dan cin mutuncin da hajiya Aisha ta yi mata sai da ta yi kuka,

Chapter 50 of 54