hirar makaranta da su magaji, sai dai ko da wasa, ba ta nuna musu tana shan wahala a gidan ba ko kaɗan.
Kawu yahaya ya ji daɗin yadda ummi ta samu sakewa yau cikin ƴan uwa, tana hira ba kamar da da kullum a rakuɓe take ba.
Iya kuwa ba dalilin saukar ummi ne ya kawota ba, balli ne ya tashi, Idris ya mayar da hindu tamkar matar da ya aura, tun bata saba ba har suka saba da sheƙe ayarsu.
Kwatsam ciki ya bayyana a jikin hindu, suka rasa yadda za su yi da cikin, har sai da iyayen hindun suka farga.
Dan haka zance ya fasu a gari, sai faɗuwa ta zo dai-dai da zama, domin kuwa iyayen hindu sun ce sai ya auri hindu, shi kuma ya ce ba ya son ta.
Dan kuwa zance ya fara fasuwa, an fara zunɗensu a garin.
Baban hindun kuma ya dage ba za a zubar da ciki ba, sai an haifi wannan ɗa ya riƙe, kuma sai ya aureta.
shiyasa Iya ta lallaɓo wai kawu yahaya ya ɗauke shi ya sama masa sana'a a nan Kano, a mayar da aurensa da ummi!!!
Iya a ɗakin kawu yahaya ta same shi, ta kora masa wannan jawabin.
Yayi ƙuri da ido yana kallon Iya, har ta gama jawabinta.
Kasancewar ummi na wurin, gabanta yayi wata irin mummunar faɗuwa, kawu yahaya ya kalli Iya ya ce "Amincewar ummi zaki nema, ni ba zan yanke mata hukunci ba, abun da take so shi nake so".
"Zancen banza kenan, wane irin sai ta yarda ko ba ta yarda ba? Ba ɗan uwanta bane ba, rufin asirinmu ba nata bane ba, idan shi ma ya baro garin, suka neme shi suka rasa ba shikenan ba, asiri ya rufu, ai rufa masa asiri za ta yi, ai umarni nake bayarwa ba shawara ba, dauɗar gora ai ciki ka sha ta!"
Ayshercool
08081012143.
WHAT'S APP ONLY PLEASE 🙏
18
Kan ka ce kwabo, hawaye ya wanke wa ummi fuska, har wata irin sheshsheƙar kuka take yi, dan kuwa da ace ta koma gidan Idris, gara a yanke mata hukuncin kisa, dan tana kyautatawa Allah zato a dukkan lamuranta, tayi imanin za ta dace da rahamar sa.
Iya cikin masifa ta ce "To kukan uban me ki ke yi, ba taimaka miki zai yi ba? ke a wannan munin naki uban waye zai aure ki? Kalli fuskarki fa kamar buredi ya ƙone ƙurmus, har wani zaɓi ne da ke? Ke gaki nan ba ke ba mutum ba ke ba aljana ba".
Kawu yahaya ya ce "Iya, lokacin da Allah ya halicci ummi fa, bai yi shawara da kowa ba, balle ace laifinta ne, ko wani abu ne ya sanya ubangiji yin halittarta a haka, halittar ummi hurumin ubangiji ne, dan haka bai kyautu a din ga ci nata fuska ba, kuma wallahi ummi ba ta da muni".
"Ka ga ni kar ka yi mini wa'azi, ai maganar gaskiya ce, tun da Allah ya sa ita ba wata mamora ce da ita ba, balle ace za a samu mai kwasa ai duk sai a manta da abun da ya faru a baya ko? Tun da har da kansa ya ce ta dawo ɗin, sai a ja masa kunne"
Dr. Ya kalli in da ummi ke zaune tana ta sheshsheƙar kuka ya ce "Ummana, jeki ɗaki abunki kin kwaso gajiyar sauka" ummi ta tashi zuciyarta na harbawa da sauri, ta tafi ɗakinta tana kuka, tare da adduo'i kala-kala a zuciyarta, tana fatan Allah ya sa kar kawu ya amince da abun da iya take faɗa. Dan har ta mutu ba za ta manta da azabar da ta sha a gidan idris ba, ko maƙiyinta ba ta fatan yayi rayuwa irin wadda ta yi a gidan idris.
Noor ta bita ɗakin tana kiran sunanta.
Kawu ya kalli Iya ya ce "Iya, ko ummi ta amince ko bata amince ba, ba zan sake bawa Idris ita ba, yaron nan gaba ɗaya jahili ne, wallahi da mutumin kirki ne, idan ta gama sakandare sai a mayar da auren, amma ni ba zan goyi bayan a cuci ɗan wani ba, yadda ya yi wa ƴar mutane ciki, ku je can ku nema masa mafita, dan baban yarinya bai yi laifi ba.
Iya kin manta lokacin da ya din ga terere da ummi, yana tona mata asiri ga larurar da ke damunta? Shi meyasa ba a tursasa shi ya shanye dauɗar gorar ba, sai ummi?
Allah da ya halicceta a haka in dai muna raye, zai bata abokin rayuwa na gari, haka zalika ba zan riƙe ƙato da bai san ciwon kansa kamar idiris ba, can ƙauye ya gagareku balle ni a nan, dan Allah kiyi haƙuri a bar wannan zancen. Ummin ma da kanta ta nuna ba ta so, dan haka dan Allah dan annabi a bar wannan maganar. Kuma ina baku shawarar mayar da idris makaranta kan a kuma bashi wata matar ya aura, dan kuwa jahilci ke ɗawainiya da shi".
Cike da takaici iya ta kalle shi ta ce "Haka ka ce?"
"Ba faɗa na yi dan na ɓata miki rai ba, amma gaskiya ce" Iya ta yi ƙwafa ta ce "Shikenan na tabattar da uwarka ce ba zaka tsallake umarninta ba, kuma da cikin ku ɗaya da baban Idris ba zaka so asirin sa ya tonu ba".
Ya girgiza kai ya ce "Iya ai kin san mu kallon uwa muke yi miki, amma kowa ya ɗebo da zafi bakinsa, kin riga kin sangarta Idris, komai yayi ba zaki bari duniya ta hora shi ba, sai kin kare shi, kema yakamata ki hutawa ranki, ba shikaɗai ne ɗa a dangi ba".
Ba ƙaramin takaici Iya ta kwasa ba, yadda ƙiri-ƙiri yahaya yayi burus da maganarta, ya zaɓi tonuwar asirin su.
Dan haka ta ce masa babu ita babu ummi, tun da haka suka zaɓa, ya ce bakomai, Allhan da ya yi ummin zai kula da ita.
Ko zama ba ta sake yi ba tun da ta tashi, ta ce magaji ya samo musu mota a tasha, kawu yahaya ya biya kuɗin motar, ya basu kuɗin kashewa, suka tafi.
Ummi sai da tayi sujjadar godiya ga Allah, ga saukar Alqur'ani mai girma, ga kuma fasa mayar da aurenta da idris da aka yi.
Duk da kuɗin da yahaya ya bawa Iya sun saka ta ɗan sassauta fushinta, amam ta sha takaicin rashin amincewa ya ɗauki Idiris a mayar da aurensa da ummi, ta din ga zagin ummi tana tsine mata, tamkar ba ita ta haifi baban ummi ba, tare da janyo mata jafa'i kala-kala.
Ko da suka koma gida ta sanarwa Idris da babansa cewa yahaya ya goya wa ummi baya, yaƙi yadda da magabar da ta je masa da ita.
Hankalin Idris ya tashi, dan kuwa baban hindu ɗan bala'i ne, ya ce ba zai yadda ba, ba za a zubar da cikin jikin hindu ba, sai ta haife shi, kuma sai sun karɓa sun riƙe, hindu na da wani yaya da yake soja, kurtu nema a cikin sojojin, amma ya zamewa su Iya barazana, dan kuwa shi ma cewa yayi sai ya saka bomb a gidan su iya, ko ya kama Idris ya harbe shi, tun da aka taɓa ƙanwarsa.
Magaji ya san duk barazana ce, babu ɗaya da zai faru, amma yayi shiru da bakinsa, saboda sun cancanci koma menene ya same su, dan da idris bai taɓa ƴar mutane ba, babu mai ɗaga musu hankali, kuma ya danganta hakan da alhakin ummi
Babu yawon da Iya ba ta yi wurin malamai ba, a kan a rufe bakin baban hindu, da ita kanta hindun da yayanta, amma abu ya ci tura, dan har barzanar kai su gaban hukuma baban hindu yayi idan suka cigaba da takura masa a kan maganar cikin nan, ko kuma ya saka ɗan sa ya ɗauki duk matakin da ya ga dace a kan su.
***
Tafiyar rahama daga gidan dr., Bayan an yi mata aure bata sauya zani da komai ba, daga wahalar da ummi take yi, dan har undeas ɗin su intee ba zasu wanke ba, sai a haɗa mata a kayan wanki, duk ta haɗa ta wanke su.
Sai dai tun ba aje ko ina da tafiyar rahaman ba, ta fara sintirin kawo ƙara wurin kawu yahaya, dan dama mahaifinsu ya rasu, duk wani abu na jin daɗi da ta sanya ran samu a gidan mijin, sai ta ga akasin haka, yana da hali ba bashi da shi ba, amma hatta shinkafa da man da za ta ci, sai ya ƙulla mata, ba yadda da zuwan baƙi gidansa ba, sai an kira shi ya bayar da iznin a zo, idan bai bayar ba kuwa babu mai zuwa.
Kawu yahaya ya kira shi, dan a samu masalaha amma ya nuna shi tsarin gidansa ne a haka, dan haka dole a bar shi yayi yadda yake so.
Haka nan kawu yahaya ya ce sai dai tayi haƙuri, yace shi tsarin gidansa ne a haka.
Tun da shekaru goma sha shida, samari suka fara bin intee, hakan ba ƙaramin farantawa farida yayi ba, tana ganin intee mai goshin arziki ce, shekara goma sha shida, samari sun fara sintiri, dan ma dr. Yana korarsu ya ce yarinyarsa tayi ƙanƙanta sai ta fara karatu idan ma auren zai yi mata.
Lokacin da ummi ta fara period babu wanda ta gayawa, dama ta riga ta san shi tun a karatuttukansu na makarantar islamiyya da na boko ana gaya musu shi, sannan an koyar da su tsabta a lokacin da mutum yake cikin jinin haili. Dan har wata ƙungiya ta je makarantar su suka wayar musu da kai, a kan jinin haila da tsafta, dan haka babu wanda ta gayawa da ya same ta.
Ta samu kayanta da suka ɗan kwana biyu, ta yayyanka ɗankwalin, take amfani da shi.
Idan kuma Allah ya sa dr. Ya bata kuɗi, babu abun da take fara saya sai pad, tana iya haƙura da kowace irin buƙata ce da ita, ta sai pad ɗin da za ta yi amfani da ita da kuma farin muski.
Sintirin samari zuwa wurin intee, ta din ga wani iyayi tana yauƙi, ya sanya aka fara yi wa ummi gori da habaici, domin kuwa babu wanda ya taɓa zuwa ƙofar gidan ya ce yana sallama da ita, ko a hanya ma babu wanda ya taɓa biyota ya ce ya na so.
Su yi ta yi wa ummi wulaƙanci, wai farar mace Alkyabbar mata, baƙar mace bolar maza.
Kodayake bolar akwai wadda ake iya recycling, wata ta riga ta zama waste gaba ɗaya bata da mamora.
Ko sai sun ga ummi su fara wankan baƙi asarar ruwa, ko yayi ma kamar bai yi ba, blaki kalar dauɗa, su din ga yi suna tuntsura dariya.
Ummi kuwa sai ta yi kamar ba ta ji ba, ta cigaba da sabgoginta, duk da a ƙasan zuciyarta kalaman na su na tasiri a cikin zuciyarta, tana jin babu daɗin cin mutuncin halittar ta da suke yi.
Haka Maryam ma, kasancewar ta kyakykyawa, kullum ba ta da aiki sai bawa ummi labarin saurayinta kaza yayi mata kaza, ko ya bata abu kaza.
Ba maryam kawai ba, ƴan ajinsu ba su da aiki, sai hirar samari, ita kuwa da ta san ba ta da kowa, ta rungumi litattafanta yadda yakamata.
Idan suka so yin dariya kuwa, sai su yi ta zungurar ummi, suna tambayarta wai ita waye nata saurayin, ta gaya musu fari ne ko baƙi, dogo ko siriri.
Kawai sai tayi murmushi ta yi musu shiru, taƙi kula su.
Maryam ce ta fara bata shawara "Ummi, yakamata ko ɗan mayukan nan na zamani ki ɗan din ga shafawa, ko kema kya yi haske, maza ba sa son baƙar mace, ummi kin yi duhu da yawa, duk kwatancen baƙin da za ayi a makarantar nan da ke ake yi, idan ki ka shafa mai ki ka ɗan yi haske, ko yaya zaki samu saurayi, ko zaki ji daɗi duk mu yi aure mu bar ki? Ni fa mami ta ce ina candy aure za ayi mini, na cigaba da karatu a gidan mijina, amma ke kullum kin ƙi wayewa, ga uban hijjaban da ki ke sawa, ba kya kwalliya kamar mu, bayan hijjabi har da wani uban niƙab, to waye zai ce yana son ki, kalli ranar da muka je barkar gidan su Saratu, kowa yayi kwalliya amma ummi ke kin zunduma over size hijjab fisabilillahi. Ranar da babu school, ki zo gidanmu akwai wata mai mayukan gyaran jiki, muje ta haɗa miki mai sai na biya"
Ummi shiru tayi tana ƙoƙarin haɗiye wani abu mai ɗacin gaske, da yake yi mata kai komo tsakanin maƙogwaronta da ƙirjinta, wannan shawara maryam take bata ko ci mata fuska.
"Ina magana kin yi mini shiru" Maryam ta yi maganar a ɗan hasale, dan daga abun da maryam ta tsana a halin ummi bai wuce miskilanci da shariya ba.
Wanda ba wai miskilancin bane kawai, tana gudun shiga harkar mutane, kar tayi wani abun da za aci mata mutunci.
Ummi ta ɗago ta kalli maryam, hawaye har ya zagaye cikin fararen idanuwanta, ta ɗan juya brown ɗin ƙwayar idonta ta ce "Maryam, I won't bleach my skin, ko a so ni a haka, ko a ƙyale ni, banbancin fari da baƙi a wurin Allah, wanda yafi tsoronsa mu ƴan adam mune muke ɗorawa kanmu".
Cikin ƙuluwa maryam ta ce "Au dan na baki shawara ina nema miki mafita, shine ki ke kuka, har ki ke nema ki kafirta ni? To ki ƙarata ummi, amma zaki ce na gaya miki, wallahi babu wanda zai aureki da wannan baƙin da gidadancin"
Ummi tayi murmushi mai ciwo hawayen na zubowa ta ce "Ba ke ki ka fara faɗar haka ba maryam, an daɗe da gaya mini ba zan auru ba ni mummuna ce, dan haka ban sa aure a ka ba dama, nima na san maza farare suke so masu kyau, in dai ubangijina yana sona shikenan maryam" tayi maganar cikin sanyin halinta.
Sai kuma jikin maryam yayi sanyi, ta ce "Am sorry please, ba ina nufin na ɓata miki rai ba ummi, mafita nake nema miki"
Kawai ummi ta tashi ta bar ajin, domin kuwa an kaɗa ƙararrawar tashi.
Kai tsaye gida ta nufa, tana tafe tana hawaye ta cikin niƙabinta.
***
Babban mutum ne zaune mai cike da nutsuwa da kamala,kallo ɗaya zaka yi masa ka san a cikin hutu yake, falon da yake zaune kawai ya ƙawatu dai-dai gwargwado.
A hankali yake zuƙar tea ɗin da yake hannunsa, yana kallon ƙatuwar plasma tv da ke manne a jikin bango, sai dai kana gani ka san ba kallon yake yi ba, zancen zuci yake yi.
"Alhaji ya dai?"
Wata mata tayi maganar tana ƙoƙarin zama a kusa da shi.
"Bakomai" yayi maganar yana murmushi.
"A'a da komai mana, zancen zuci ka ke yi, shekaru sun ja, yakamata a din ga rangwatawa kai, kar wani ciwon ya kama ka"
Ya ajiye cup ɗin hannunsa ya ce "Da ciwo zai shigeni saboda tunani, da tuni ya shige ni hajiya. Lokaci yayi da yakamata na huta, huta nake buƙata amma ki duba ki ga haryanzu ban huta ba, ni nake fama da harkar kasuwancina, gaba ɗaya yaran nan basu saka komai a gaba sai shashasha. Na tara dukiya, suna ta bushashasha, gaba ɗaya babu hankali ko nutsuwa a cikinsu da zai tallafe ni yanzu, su karɓi ragamar kasuwancin ni na huta.
Ko kartun kirki babu wanda ya tsaya ya kammala a cikinsu, duk da tarin kuɗin da na kashe musu da sun yi karatu, amma kalli duk shashanci suke yi, suna manya amma duk babu mai saiti a cikin su.
Matan ne kawai nutsatsu a cikin su, su kuma duk matan wasu ne, ragamar babban kasuwanci irin wannan ma ai ba na mace bane ba.
Jiki a sanyaye ta ce "Na sani Alhaji, ka yi haƙuri, ka ɗan ƙara musu lokaci, mu cigaba da addu'a, kuma a cigaba da jan su cikin harkar kasuwancin"
"Eh su ƙarasa ni ba. Wane lokaci zan ƙara musu? Salim na da shekara talatin da ku san biyar, dukkansu babu yaro a cikinsu, wane lokaci zan basu banda wanda na basu a baya. Zan yanke hukuncin da nake ganin ya dace kawai".
Ta ɗan gyara zamanta ta dube shi ta ce "Wane hukuncin kenan?"
"Zaki gani idan na yanke" yayi maganar yana sauya channel da remote.
***
Ummi kuwa tsaye take a gaban mudubin ɗakinta, tana ɗaure da zani kasancewar daga wanka ta fito, ta shiga ƙare wa kanta kallo a jikin madubin.
Ta saki gashin nan a bayanta, ta din ga kallon ƙwayar idonta, da take brown sosai, cikin idon kuma fari ƙal, ta gangaro kan fatarta da take jiƙe da ruwa, baƙa mai ɗaukar ido.
Ta kalli gashin ta, ta ɗan shafa shi a hankali, tana tambayar kanta wace irin halitta ce ita haka. Ita kanta ta san ba ta taɓa ganin mai irin halittarta ba, a ƙasar hausa duk wanda take haɗuwa da su, ba ta taɓa ganin mai irin gashin kanta da kuma ƙwayar idonta ba.
A hankali ta murza fatar jikinta, tana tuna maganganun su kausar masu sosa rai, wai wankan baƙi asarar ruwa. Baƙar mace bolar maza, irinta kuma bolar da ko recycling ba za a iya yi ba.
"Da gaske ba zan yi aure ba, saboda maza ba sa son baƙar mace mai duhu kamar ni? To haka zan cigaba da zama a gidan kamar baiwa? Ko kuma zasu mayar da ni ƙauye daga baya, saboda ban samu miji ba? Dama Iya ta ce babu wanda zai aureni, saboda munina. Idan ma na yi aure zai iya ƙara aure ya daina kula ni, saboda ni bani da kyau, to wa ma zai ce yana so na?.
Ko dai maryam da gaske take hijjabin da nake sakawa, da kuma munina ba zai bari a aureni ba?"
Ta dubi ƙirjinta, da tudunsu ya ɗaga sosai.
Ta girgiza kai ta ce "Ni ba zan iya bari a ga jikina ba, kuma ba zan saɓawa Allah ba, idan na yi bleaching na raina halittar da yayi mini kenan. Ya bani lafiya bani da wani mummunan ciwo da yake hanani sukuni, sai jarrabawar rayuwa da tsananinta bai sanya na rabu da rai na ba"
Istigfari ta hau yi, duk hawayen idonta ya kasa daina zuba.
"Yaya ummi" ta jiyo muryar noor.
Tayi saurin share hawayenta ta ce "Na'am ƴar gidan anty ummi"
"Ki ɗora ni a kan mudubin na taɓa gashinki"
Ummi ta yi murmushi, ta ɗora noor a kan mudubinta, noor ta saka hannu biyu ta kama gashin tana dariya.
Can sai ta ƙurawa ummi ido, ta ce "Kuka ki ke yi?"
Ummi ta girgiza kai ta ce "A'a mama".
Noor ta kai hannunta ta shafo sauran hawayen ta ce "Kuka ki ke yi, maama ce ta dake ki? Ko su anty intee ne?"
Ummi ta ce "A'a mura nake yi ne, zauna a kan katifata na saka kaya" tayi maganar tana ajiye noor a kan katifar.
Noor ta din ga tsalle a kan katifar tana waƙe-waƙenta na yarinta.
***
Iya da idris fa sun haɗu da wanda suka fi su tashanci, dan mussaman uwar hindu ta din ga tatsarsu kuɗi, wai hindu ba ta da lafiya, za a saya mata magani, yadda ake kula da kowacce mace mai ciki, dole a kula da Hindu, tun da da bai yi abun da yayi ba, da hindu ba ta samu ciki ba.
Dama akuyancin sa ne ya hana su bashi hindu, dan haka tun da ya hilaceta ya ɓata ta dole ya kula da ita, saboda sun san ƴar su ba lalatacciya ba ce ba a baya.
Yadda baban hindu yayi alƙawari, sai da ta haihu, ta haifi santaleleliyar jaririya, cibiya kawai aka yanke, aka naɗo jaririyar a zani, har da mahaifarta suka kai suka direwa Iya a tsakar ɗakinta, sai tsala ihu take yarinyar.
Mutane kuma suka taru a gidan, ƙarshen tonon asirin dai da asiri ya tonu, domin kuwa rana tsaka ƙanwar babar hindu suka zo suka kawo jaririyar, sannan suka sanar da iya cewa, sun saka yara sun kama wani ƙaton rago da iya ke kiwo a waje, an kai shi can gidan za a yankawa mai jego bayan kwana bakwai na ƙauri an sakawa jaririya sunan Iya wato Hajara.
Ayshercool
08081012143.
*CUTARWA!*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
P19
FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu
Abduljalal
Wata kissar sai mata
Wuta a masaƙa
Cutarwa
Ƙanwar maza
Gaba da gabanta
Aƙidata
Ruɗin ƙuruciya
Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata.
08081012143.
And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Ayshercool.
PAID ADVERT!.
Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku
Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi
Man garan gashi
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921
*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*
BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.
P19
Tun da Iya take, ba ta taɓa cin karo da tashin hankali irin na yau ba, gida ya cika da mutane, ana ta salallami, yayin da Idris ya kulle kansa a ɗaki ya kasa fitowa saboda kunya.
Tabbas da yana da kuɗi babu abun da zai hana shi guduwa, kodayake yayan Hindu yayi masa kashedin muddin ya gudu sai ya ɗaure babansa.
Yarinya ta din ga tsanyara ihu, a tsakiyar ɗakin Iya.
Su kuma suka wanda suka kawota suka gama tijararsu da rashin mutunci, suka fice suka bar gidan.
Iya ta ce a ɗauki ƴar a kai wa babar Idris, dan ita ba ta san ya za ta yi da jaririya ɗanyen goyo haka ba, ita ko nonon ma yanzu babu sun suɗe sai fata, dan haka sai dai uwarsa.
Babar Idiris kuwa ta ce "Iya ke yakamata ki riƙe wannan ƴa ba ni ba, tun da dama sunanki suka sawa yarinyar, ba yadda ban yi ba na bawa yarona tarbiyar da ta dace, amma ki ka ƙi saboda yana da sunan mahaifinki, kin ɗau son duniya kin ɗora masa. Ko laifi yayi na yi masa faɗa, sai ki ci mini mutunci.
Dan haka Iya ke zaki kashe wannan wutar, wallahi ki ka bani jaririya ban san yadda zan yi da ita ba".
Cikin fusata Iya ta ce "Ni ki ke gayasa haka lami?"
"Iya ba rashin kunya ba ce gaskiya ce, da kin bari na bawa ɗa na tarbiyya da haka ba ta faru ba".
"Rufe mini baki, har wata tarbiyya ce da ke da zaki bawa wani? Ke ɗin a yaya ki ke? Ki zo ki ɗauke yarinyar nan ki san yadda zaki yi da ita"
Lami ta ce "Ban gane ba iya, ni na yi mata cikin, wallahi ba zan ɗauka ba"
"Lami uwata ce take faɗa kina faɗa?"
Lami ta ce "Maganar gaskiya ce fa, in ɗauki ƴa in yi yaya da ita? Ta in da aka hau ta nan za a sauka ai"
Iya ta ce "Rabu da ita, na san maganinta, yanzu abun da ya fi dacewa shi ne ka je, ka ce musu mun amince a ɗaura auren nan su karɓi ƴar nan. Amma wallahi Idiris ya cuce mu, ya janyo mana masifa da abun kunya, ga ragona da nake son sayarwa lokacin sallar layya, sun tafi da shi, ku san yadda zaku yi ku karɓo mini ragona".
Ilyasu ya ce "Iya yanzu waye yake ta rago, muntuncinmu ya gama zubewa"
Baban su Idris ya ce "Ina ga kawai mu je mu samu iyayen nata, ina sa'adatu ta zo ta yi wa yarinyar wanka, a saka mata sutura, mu je gidan su Hindun"
Sa'adatu ta ce "Taɓ ƴar gaba da fatihar? Wallahi ba zan taɓa ƙazanta ba, sai dai uwarsa ta wanketa, haka kurum in taɓa masifa"
Sakin baki Iya tayi tana cewa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 54