Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
damuna take yi" Tayi murmushi ta ce "Kana cin tuwo kenan? Abdul ɗin gidanmu baya son tuwo" "Haba dai, ai yaya tuwo abun so ne, ni a bauchi na saba, Alhajin Bauchi da shi yake karyawa, ga kwanonsa ga nawa, amma shima fa tuwon bana jera kwanaki ina ci yake isata" Tayi dariya ta ce "Ka fi son dai a din ga ccacanzawa" "Yauwwa, ba kullum abu ɗaya ba" Yau dai yayi sa'a, ta ɗan saki jiki kaɗan, dan yau har da dariya. Ya ƙarewa hijjabinta kallo, duk yayi fari takalmin ƙafarta ma ya tsufa. "Ummi" Ta ce "Na'am" "Me ya fi burgeki a rayuwa? Wanda yin sa yake yi miki daɗi, ko samunsa, abun da dai yake saka ki farinciki?" Tayi shiru tana tunani, oho, ita akwai wani abu da take jiran samuwar sa ya sanyata farinciki ne? Duk abun da ya zo mata a rayuwa kawai, karɓa take yi. "Babu" "Ban gane babu ba? Kawai haka ki ke rayuwa ba farinciki?" Ta sunkuyar da kai ta yi shiru. "No dole akwai, ki tuna sai ki gaya mini" "Babu" ta sake bashi amsa. Bai sake ce mata komai ba suka cigaba da tafiya, in da ya ajiyeta wancan karon, ta sake cewa ya ajiyeta. Ya yi parking sannan ya kalleta ya ce "A nan zaki sauke, ba zaki bari na ga gidan ba?" Ta hau wasa da yatsun hannunta bata ta kula shi ba. "Bayan ƴan uwa let's be true friends ummi, ki tuna abun da yake saki farinciki ki gaya mini, mu zama ƴan uwa kuma abokai saboda Allah" "To in sha Allah" Yayi murmushi ya ɗauki leda ɗaya, ya ce "Ungo naki" ta kalleshi zata yi magana, ya ɗora yatsansa a kan laɓɓansa ya ce "Shhh". "Idan zan wuce gobe in Allah ya kaimu zan jira ki mu tafi tare" ta jinjina kai, ta fice daga motar. Addu'a take yi, tana fatan Allah ya sa kar wani ya ganta, cikin ikon Allah babu wanda ya ganta, har security gidan yana banɗaki, ta wuce ta shiga har ɗakinta ba ta haɗu da kowa ba. Ta sauya kaya ta fito, ta dudduba gidan babu kowa, ta koma ɗakin ta duba ledar da Raihan ya bata. Rabin kaza ce guda a cikin ƙatuwar roba, sai shinkafa da salad. Jikin ummi har rawa yake, duk wannan kazar ita kaɗai?. Sai kuma ta yi shiru tana tunani, anya ba ta zura jiki ba? Kasa ci tayi ta tashi ta shiga aikin gida. Abdul ne ya shigo yana waya, ya kammala ya tsaya yana mita. Ummi ta ce "Yaya Abdul kana nan dama?" "A'a yanzu na shigo, wani ɗan rainin hankali ne ya kirani, wai babansu ne ya buɗe shago a tal'udu, suna neman casheir, wanda zai din ga zauna musu da safe zuwa azahar, ko azahar zuwa magariba". Ummi ta ce "Dan Allah yaya Abdul zan yi, ina so" Ya kalleta ya ce "Zaman jiran shagon, shagon furnitures ne fa da kayan kitchen" "Eh yaya Abdul dan Allah, dama na gama SIWES, kawai dai sun buƙaci na cigaba da zuwa ne, dan Allah zan yi" Abdul ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Zan yi magana da Abba, idan ya yarda shikenan". "Yauwwa zai yadda ma in sha Allah" tayi maganar tana addu'ar Allah ya sa Abba ya amince, ita ko kuɗin babu yawa tana so, atleast ta din ga samun na sayen wasu abubuwan da take buƙata. Ta kasa zaune ta kasa tsaye da kazar nan a ɗaki, dr. Gidansa ba ya rabo da nama da kaji, amma tsaf ummi za ta yi aikinsu, farida ta karɓe idan ta ga dama ta sanmata idan ba ta ga dama ba, sai ummi ta zo wanke-wanke ta ɗan tsinci sauran hanta, da diddiga ta lasa abun ka da zuciya. Hankalinta bai kwanta ba, sai da ta saka noor a gaba, ta gaya mata yadda aka yi, kamar sa'arta. Noor ta din ga murna ta ce "Yaya ummi kar ki gaya wa kowa mu cinye abunmu". Ummi da noor suka cinye takeaway tare, suna ta murna, dan kuwa ummi ba ta taɓa cin kaza mai yawan haka ba. Masu nema daga farko dan Allah ku duba a watpad Ayshercool 08081012143 *CUTARWA!* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* P24 FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK. https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu Abduljalal Wata kissar sai mata Wuta a masaƙa Cutarwa Ƙanwar maza Gaba da gabanta Aƙidata Ruɗin ƙuruciya Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata. 08081012143. And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link. https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Ayshercool. PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI. 24 Ummi ta kalli noor ta ce "Dan Allah noor kar ki gayawa kowa kin ji" Noor ta ce "Yaya ummi ina da wayona fa, ba wanda zan gayawa wallahi, kazar nan tayi daɗi sosai" Ummi ta yi murmushi ta ce "Yauwwa maman". Raihan kuwa tun da yaje gida, ɗakinsa ya wuce ya samu ya kwanta ya huta, ana kiran magariba ya fice, da aka idar da sallar isha'i, ya tafi gym domin motsa jikinsa. Bai sake komawa gida ba sai wajen ƙarfe goma, ya shiga sashin mami. "Wai yau ina ka shiga ne, tun safe ban sake saka ka a idona ba?" "Kasuwa na je" ya bata amsa tare da ɓoye mata aikin da Alhajinsu ya sanya shi. "Aikuwa ka kyautawa kanka, Allah ya taimaka" ya amsa mata da "Amin" Washegari da sassafe, raihan ko karyawa bai yi ba, ya ɗauki mota ya fita, dan yaje ya ɗauki ummi kar ta makara, dama yau zai zauna da cheif accountant na mahaifinsu su cigaba da aikin da ya saka shi. Ƙarfe bakwai da rabi, ummi ta ga kiran raihan. Ta ɗaga wayar tare da yin sallama. Ya amsa mata ya ce "Ina waje, idan kin shirya ki fito mu tafi" Ummi ta ce "Eyya, sai takwas da rabi nake fita ai, kayi tafiyarka wallahi bakomai, na gode sosai " Raihan ya ce "No, ina jiranki, idan kin kammala sai mu tafi, na zaci da wuri ki ke fita sosai, shiyasa ko karyawa ban yi ba na fito". "Amma ai zaka gaji". "Bakomai take your time" A gurguje ummi ta kammala duk abun da zata yi, saboda kar ta bar shi yana jira, ta juyo abincin breakfast ɗin ta, a flask, lokacin farida ko tashi ba ta yi ba, ta riƙo niƙab ɗin ta a hannu ta fice. Yana zaune a cikin mota, ya kashingiɗa yana danna wayarsa, ta buɗe ta shiga ta zauna. "Raihan, ka yi haƙuri dan Allah, na barka kana jira, na ce ka yi tafiyarka ka ƙi". Ya gyara zamansa ya ce "Ai na ce ki yi a hankali ki shirya a tsanake, shi ne ki ka fito a haka kamar an koro ki?" "Ai bana son in barka kana jira ne, jira babu daɗi, ina kwana ya su mami?". "Lafiya ƙalau, duk suna lafiya, ya gida?". "Alhamdilillah" tayi maganar tana ƙara kintsawa, ya kalli jakarta data buɗe, kamar jakar wanzamai, duk ta tsufa, daga ƴar ƙaramar robar Vaseline sai turare ɗan ɗuri, da tarkacen kuɗin da idan ka tattare su ba su fi naira ɗari da hamsin ba. "Me ma ki ka ce sunana?" Ta ce "Raihan" "Ba rayyan sunana ba fa, raihan" A ɗan marairaice ta ce "Ai haka na ce" Ya ce "Sake faɗa to" Ta ce "Raihan" "Idan na ce iyayi yayi miki yawa ki ce ba haka ba, Kamar rain kamar rayyan ki ke cewa fa" Ummi ta yi murmushi ta ce "Ni dai bana wani iyayi". "To sake cewa raihan in ji" "Ba zan faɗa ba" tayi maganar tana dariya, har dimples ɗin ta suka lotsa. Ya sanya seat belt yana murmushi, ya ce "Meye a cikin flask ɗin nan ne, ƙamshinsa ya cika mini hanci?" Ta ɗago idonta ta ce "Kai na zubowa abinci ka ce baka karya ba, kunun alkama ne da ƙosai, ban sani ba ko zaka iya ci?" "Saboda me ba zan iya ci ba?" "Abincin gargajiya ne, na ƴan ƙauye zaka iya ci?" Juyowa yayi yana kallon idonta, "Ke ƴar ƙauyen ce da ki ke iya ci?". "Eh mana, ni ƴar ƙauyen gagarawa ce jihar jigawa". "Ban ga alama ba, na gode sosai, dan aikin nan ko cikakken abinci bana iya ci, na kasa nutsuwa sai mun kammala, Alhaji ya ga sharholiya tayi mini yawa ya haɗani da aiki, ashe aikin ja ne ba ƙarami ba". "Allah sarki, Allah ya baka ikon yi, ni ko a mintuna goma da zan sake ganinsa ya sakani aikin da na so, sai dai ba zan sake ganin baba ba, Allah yayi masa rahama" Cikin kulawa raihan ya ce "Eyya, Amin ya Allah, Allah ya jiƙansa" Ta amsa da amin na gode. "To mama fa, tana raye?" Ta ce "Ina ga tana raye" "Kamar yaya kina ga? Tana ina ita?". "Rabona da ita tun ina shekara bakwai da baba ya rasu, ban ƙara ganinta ba". "Amma meyasa?". "Bakomai" ta faɗa tare da ƙoƙarin haɗiye wani abu mai ɗaci a ƙirjinta. Ta ɗaga hannunta tana ƙoƙarin sanya niƙab ɗin ta. "Wai shi wannan niƙab ɗin meye amfanin saka shi, kullum ke ko gajiya ba kya yi ne?" Ummi ta ce "Ai saboda idona". "Meye da idon naki?". "Bana son mutane su din ga tanka mini ido, ko fatata, shiyasa idan na saka shikenan ba wanda ya gani, ana cewa idona irin na akuya, ko na mage, duk bana so shiyasa bana son a din ga gani" tayi maganar a ɗan shagwaɓe da take ɗabi'arta, wanda ita a zahiri cikin damuwa ta yi maganar. "Ummi" "Na'am" "Meyasa zaki bari surutun mutane ya yi tasiri a zuciyarki? Ke ki ka yi kanki, duk wanda ya tanka ki, kice masa tubarkallah idan yana da dama ya sauya abun da Allah ya yi miki. Idanunki me kyau ne masha Allah, meye da kalar fatar ta ki, dan Allah idan dan haka ki ke saka niƙab ɗin nan ki daina". Murmushi kawai ta yi, irin ba zaka gane ɗin nan ba, hakan yayi dai-dai da ƙarasowarsu ƙofar gate ɗin wurin aikin su ummi. Ummi ta ajiye masa kayan abincin, ta ce "Na gode sosai, sai anjima" "Idan an tashi ki jirani, saura ki tafi" ba ta ce komai ba, ta buɗe ta fita. Ya daɗe yana nazarin, ta ina zai taimakawa ummi, babanta ya rasu, ba ta san in da mamanta take ba how? Kuma yau ta ɗan sake da shi fiye da da, lallai idan ya cigaba da lallaɓata har ya ƙara saninta sosai da sosai, dan ya fuskanci akwai abubuwa na damuwa sosai da sosai a cikin rayuwarta. Kiran wayar accountant ne ya dawo da shi hayacinsa, ya ja motarsa ya tafi. A motar ya gama karyawa, sannan ya tafi babban office ɗin su, in da suke aikin lissafin. Aiki raihan suke yi, suna ta aikin lissafi, amma rabin hanakalin raihan yana kan ummi. Da suka tashi ma daga aikin, a waje ta tarar da shi, ya zo yana jiranta ya ɗauke ta ya mayar da ita gida. Washegari da safe ummi na ta ɗawainiyar sallamar kowa, masu tafiya makaranta su tafi, ta gama abun da take yi, ita ma ta fara nata shirin, Abdul ya sameta a kitchen hannunsa riƙe da waya. Ya ƙarasa ya miƙa mata wayar, ta karɓa ta kara a kunnenta. Muryar dr. Ta ji ya ce "Mamana" "Na'am kawu ina kwana?" "Lafiya ƙalau, ina ta kiran wayarki baki ɗaga ba" "Caji take yi ina kitchen ne" Ya ce "Ok babu laifi, mamana Abdul ya zo mini da wani batu, wai kina son aikin jiran shago, me zaki yi da wani aikin zaman shago ummi, idan kina da wata buƙata ai gara ki gaya mini, amma zaman shago ba mutuncin ki bane a matsayin ki na mace" Jiki a sanyaye ta ce "To kawu" "Dan Allah ayi haƙuri da maganar nan" "To, in sha Allah an barta" Abdul ya karɓe wayar ya ce "Hello Abba". "Na'am Abdul" "Abba ka san ummi ba za ta ce maka a'a a kan hukuncin da ka yanke ba, amma wallahi tana so, ta gama SIWES, amma sanin ba ta da wurin zuwa ya sanya ta cigab da zuwa, wataran ko kuɗin mota sai na bata, zamanta a gidan nan ba abun da zai ƙara mata sai damuwa da rigima da maama, dan Allah Abba ka ƙyaleta tayi. Kuma ba wani abun fa zata din ga yi ba, tana zaune a wuri ɗaya, dan Allah ka bar ta tayi. Kaga ba ta iya zuwa ta ce na yi mata wani abu". Abba ya ce "Haka ne, to Ubangiji Allah ya yi jagora, na amince amma ka je wurin ka tabattar babu wata matsala, dan nima zan je da kaina na ga wurin, a satin nan zan shigo kanon". "To shikenan Allah ya kawo ka, Abbanmu maganin kukanmu" Ya kashe wayar ya kalli ummi da jikinta yayi sanyi, ya ce "Abba ya amince, zan je na ga wurin, na ce musu zaki yi, sai mu je tare ki ga wurin kema" Ummi ta ce "Alhamdilillah ala kulli halin, na gode yaya Abdul, Allah ya saka da alkhairi" "Bakomai, Ubangiji Allah ya kawo miki babban rabo na alkhairi" tayi murmushi tana sake hamdala. Gaba ɗaya ranar sallar daren da tayi, Allah take yi wa godiya, tare da roƙonsa ya kawar mata da duk wani abun ƙi a lamarin. Washegari Saturday ce, dan haka ba su haɗu da raihan ba sai waya. Da yamma Abdul ya ɗauketa a motar da dr. Ya saya ya ajiye musu saboda zuwa makaranta ko unguwa. Katafaren shago ne, na kayan kitchen da furnitures, manager wurin ya yi wa ummi tambayoyi, Abdul ya sanar masa ummi degree ne da ita, yanzu suna jiran result ne ma. Manager yayi murna ganin tayi kalar haƙuri sosai da sosai. Ya ce mata wurin sabon buɗewa ne, dan haka salarynta dubu goma sha biyar ne. Abdul ya raina dubu sha biyar, ya ce za su je su yi shawara, suna tafe yana mita, ya ce "Yaya ummi ki yi haƙuri, zan samo miki wani wurin in sha Allah, amma wane irin 15k kamar wasan yara" "Dan Allah yaya Abdul ka barni ina so, ko dubu biyar ce zan yi" Ya kalleta ya ce "Haba ummi, you are degree holder fa, kuma a cikin 15k har ki yi kuɗin mota da buƙatu?" "Eh zan yi in sha Allah, Allah ya sanya mata albarka" Yayi ajiyar zuciya ya ce "Amin, bari sai na kira su na gaya musu, na ji yaushe zaki fara zuwa" "Yauwwa yaya Abdul, na gode sosai da sosai" Yayi murmushi ya ce "Sai ka ce na baki kyautar wani abun, Allah ya taimaka". Suka je gida tana ta tunanin da wa zata yi sharing wannan abun farincikin, na samun aiki, ita ba ƙawaye ba, kuma ba abokin hira ba, tayi tunanin ko ta gaya wa raihan, amma sai ta ga hakan kamar ta zaƙe, dan haka ta share shi bata gaya masa ba. Ranar litinin, ta ga kiran wayar raihan ya zo su tafi, wanda ranar zata je ta yi sallama da ƴan wurin aikinsu, ta fara zuwa wancan kanti na furnitures. Tun da ta nufo motar yake kallonta, sannu a hankali, tafiyar ma cikin nutsuwa da yanga take yin ta. Maimakon ta shiga ta zagaya ta in da yake zaune ta ce "Ina kwana?" "Lafiya ƙalau, ina shirin aikin?" "Sai 9 zan je idan Allah ya kaimu, zan yi musu sallama, na samu aiki a wani sabon shago, MIKIYA GALLERY, can zan koma zuwa" Yayi shiru yana kallon ta, ya ɗan rausayar da kai ya ce "Rashin muhimmancin nawa har ya kai abu ya faru ki ƙi gaya mini?". "A'a ba haka bane ba, abun ne bai tabatta da wuri ba" "Shikenan na gode, Allah ya taimaka" yayi maganar ransa a haɗe. "Raihan haushi ka ji, walla.... "Shhhh, na fuskanci na fiye shishshigi, am sorry" yayi maganar yana kunna motar. Ummi ta yi saroro ta kasa magana, ba ta son ace tayi laifi a rayuwarta, mussaman raihan da yake ta ɗawainiya da ita, ba ta zaci za ji haushi ba. "Matsa zan ja motata" A hankali ta ja da baya, ya ja motar, yana kallonta ta mirror, ta tsaya kamar sokuwa tabi motar da kallo. A hankali ya furta 'Lets see, if it will works' Jiki a sanyaye ta din ga gudanar da al'amura ranar. Ta je sabon wurin aikinta, sai dai hankalinta baya jikinta, ta din ga kiran wayar raihan, amma yaƙi ɗagawa. Whats app ta koma, ta yi masa message nan ma bai amsa ba, sai dare sannan ya kirata. "Raihan dan Allah ka yi haƙuri, ban san zaka ji haushi ba, ka yi haƙuri mana". "Yaya ummi ba sai kin bani haƙuri ba, laifina ne da nake yi miki shishshigi, duk da yanayinki na rashin son mutane". "A'a ba shishshigi ka ke yi mini ba, ka yi haƙuri mana" Ya wani hura hanci ya ce "Ok, Allah ya taimaka". Ta ce "Yauwwa na gode, zan din ga gaya maka abu idan ya faru" Ya ce "Promise?" "In sha Allah " "To shikenan, abu na daɗi ko akasin haka, kar mu ɓoyewa juna" Ummi ta ce "To" "Good dear, gobe in Allah ya kaimu zan zo na ga wurin" Tayi murmushi ta ce "To Allah ya kawo ka" "Amin, goodnight" suka yi sallama tana jinjina daru irin na raihan. Status take kallo, ta kai kan status ɗin raihan, yana tsaye a gym, ya tsaya a jikin mudubi yayi hoto, daga shi sai gajeren wando, ya ɗaga wani ƙarfe jijiyoyin jikinsa duk sun ɗaga, ga cikinsa ya rabu kashi shida (six packs) ga ƙirjinsa kwance da gashi har saman cikin sa. Tayi reply da "Babban mutum meye haka?" "A ina?" "Ka saka hotonka babu kaya, ba mutunci a haka, dan Allah ka cire" Ya amsa mata da "Ai ni ba mace bane" "Duk da haka, manya ba sa haka, a cire dan Allah 🙏" Yana daga kwance yake murmushi, ya ce "To shikenan, an gama babbar yaya, in sha Allah ba zan sake sakawa ba". "Yauwwa babban mutum, Allah ya yi albarka ya kula da rayuwarka" "Amin ya rabb yayata, godiya nake Allah ya kula mini da ke" "Amin tare da kai" ta ajiye wayar tana murmushi. Washegari har shagon ya je ya tarar da ummi, sai dai ya ji daɗin ganinta a kauwwame a wuri ɗaya, ba wani aiki take na wahala ba. Ya samu wuri ya zauna suka gaisa da manager, ya hau yi wa ummi hira. Da farko a ɗan tsorace take, ko manager zai ce tayi laifi, amma yaga bai ce musu komai ba, har lokacin tasinta yayi, yana wurin. Da suka fito ya kalleta ya ce "Wai nawa zasu din ga biyanki ne?" Cikin murna ta ce "Dubu sha biyar duk wata" "Me?"yayi maganar yana yatsune fuska. "Dubu sha biyar" ta maimaita masa. "Share-share zaki din ga yi ne? Ki zo ki wuni a dubu sha biyar, duk girman shagon nan dan son kai". Ummi ta waiwaya ta ga babu wanda yake jin su ta ce "Kayi a hankali, dubu sha biyar ina laifi, da waye ya bani?". "Degree holder da aikin dubu sha biyar a wata, me 15k zata yi miki a wata, mussman ku mata masu tsarabe-tsarabe, ni fa a wata data da katin waya na dubu ashirin nake sawa zuwa sama" Ummi ta buɗe baki tana kallon sa, saboda abun ya ɗaure mata kai, har ya kaita gida mita yake yi, yana nanata dubu sha biyar ta yi kaɗan, tayi masa shiru taƙi kula shi. Dan in dai shariya ce ummi ta ƙware a wannan fannin. "Ni ki ka share ko, wato idan na gaji na yi shiru?" gyara zamanta tayi tana cigaba da kallon window. A hankali ya ce "Miskili ka fi mahaukaci ban haushi". *** Misalin ƙarfe goma sha biyu da rabi na dare, raihan da mahaifinsu, chief accountant da sauran accountants mutum biyu, lawyoyin Alhaji Tahir su biyu, sai kuma manajojinsa, zaune a wani katafaren office, ko ina fitilu kamar rana, kowa gabansa da ruwa da lemo, gefe ga flask na shayi, gaba ɗayansu raihan ne kawai yaro a cikinsu. Ɗaya bayan ɗaya kowa ya din ga gabatar da bayaninsa n shekara a kan ɓangaren da yake jagoranta. Suka kammala tsaf, sannan raihan ya tashi, ya yi connecting system ɗin sa da projector, ya fara bayanin abubuwan da ya tattara daga bayanan su, ribar da suka samu a shekarar, ya tabbattar wa da mahaifinsu duk sun bibiyi shige da ficen kuɗi na shekarar, kuma sun yi dai-dai da bayanan da abun da kowane accountant yayi presenting. Ya ware harajin da zasu biya, na ciki da wajen Nigeria, ya ware kuɗin zakka, kuɗin abun da ake rabawa ma'aikata na riba bayan albashinsu, abubuwan da suke buƙata, kuɗin duk wani abu da ya shafi sadaka da makamantansu, da kuma kuɗin umara na mutum goma, kamar dai yadda Alhajin ya umarce shi. Tafa masa Alhaji Tahir ya hau yi, ya ce "Ƙaraminsu babbansu, am so much proud of you, ban zaci zaka iya ƙoƙari haka ba, saboda na san aikin ba ƙarami bane". Chief accountant ya ce "Ni kaina ya bani mamaki, yayi ƙoƙari sosai da sosai, na bi duk abubuwan da yayi, kamar dai yadda ka saba ne, yayi iya yin sa, kuma da alama zai kamanta adalci kamar dai kai, sai dai rigimamme ne" Alhaji Tahir ya yi murmushi ya ce "Ai na san halin kayana" suka yi dariya baki ɗaya. Suka ƙarasa tattaunawa, da bibiyar abubuwan da Raihan ya gabatar, daga bisani Alhaji Tahir ya ce kowane ɓangare su rubuto abun da suke buƙata, na gyara ko makamancin haka, raihan zai duba, shi zai je hutun taƙaitaccen lokaci. Duk suka gamsu da abubuwan da aka tattauna, tare da yi wa Alhaji Tahir addu'a saboda mutum ne mai farantawa ma'aikatansa, dan ya ce abokan nemansa ne, bayan iyalansa ba shi da sama da su. Dirver ya ɗauke su zuwa gida, a hanya raihan ya ce "Alhaji" "Na'am babban mutum" "Tsakani da Allah aikin nan da wahala, kuma ko murmurewa ban yi ba, ka ce a kawo mini duba wani abu, ni fa ban san komai ba, dan Allah a kaiwa su yaya sagir, gaba ɗaya ƴan kwanakin nan saboda aikin nan, ko bacci bana yi sosai" ranƙwashin da Alhajin yayi masa ne ya sa shi yin shiru yana kallon sa. "Kana da nasibi a kan harkar kasuwanci raihan, amma wasa da shiririta sun yi maka yawa, da aikin kashe-kashen kuɗi, office zan baka a head branch, a din ga baka salary" Cikin sangarta ya ce "A'a dan Allah, shagona fa da nake ta processing, ka fa bani jari rance, ka manta, kayana sun kusa zuwa fa". "Na sani raihan, akwai abun da nake targeting ne" Raihan ya ce "To, Allah ya taimaka, amma ba sai na sake duba wani abun ba ko? Kuma ba sai na yi maka aikin ba ko?". "Sai fa ka yi, gara ma ka shirya" Raihan ya kifa kansa ya ce "Wayyo mami, dama ban dawo kano ba" Alhaji Tahir yayi dariya ya ce "Ko ina ka tafi, i know how to deals with you, Munnir ya sangarta ka, kashe kuɗi kawai ka iya, baka iya nema ba" yayi maganar yana murɗe masa kunne. Raihan ya ɗago da sauri ya ce "Ka tambayeshi ka ji, na sayar da agoguna, na sayar da takalma, kuma na tara kuɗi" Alhaji Tahir dariya kawai yake yi wa raihan, so yake dole sai ya zame, kuma ya san dalilin sa na yin haka, dan raihan akwai biyayya in dai abu zai faranta masa rai zai yi, da mamansa ne ma suke faɗa wasu lokutan ba su fiye shiri ba, idan ta zo da abu na son zuciya, ya ce ba zai yi ba. Duk da ummi ta ɗan girmewa Raihan, sannu a hankali ya nuna mata shi namiji ne, domin kuwa yafi ummi wayo nesa ba kusa ba, dan bata ankara ba, suka yi wani irin mugun sabo da ita da shi, duk ɗari-ɗarinta da shi, ta sake jiki da shi, dan barkwancinsa kawai nishaɗi yake saka ta. Kullum a

Chapter 23 of 54