Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yi mata, da yaranta da ƙanwarta, kuma wasu lokutan a hana ummin abincin. Sai dai lokaci ɗaya kawun nata ya rage bata wannan kulawar da yake bata da farko, hakan sam bai damu ummin ba, dan gani take duk wahalar da zata sha, ba zata kai ta gidan Iya da idris ba. Ranar lahadi suka koma ganin likita, sai dai ummi ta ji daɗin amfani da magungunan nan, dan kuwa sosai yayi mata sauƙi ba kamar da ba. Likita ya dubata, ya rubuta mata magunguna, Allah ya sa kawu yahaya bai yi ƙwauron baki ba, ya sanar masa magungunan da take sha, likitan ya ce ta ajiye su ta gama shan na asibiti, idan suka ƙare ta cigaba da waccan. Yayi masa godiya suka tafi gida, suna tafe yana rarrashin ummi, yana yi mata nasiha. Sai da ummi ta yi sati biyu cif a gidan, baban su Abdul ya cewa farida zai kai ummi makarantar su Abdul, amma ta ce ba ta yadda ba, sai dai ya nemi wata mai arha ya kai ummi, dan ba zai dai-daita ta da yaranta ba. Staff school ya saka ummi, ta nan makarantar da yake lecturing, makarantar islamiyya ma, wata daban ya saka ummi, sai dai makaranta ce mai kyau sosai ana karatu, dan akwai ƴaƴan manya a makarantar. Duk wanda ya shigo gidan nan ya ga ummi, sai farida ta ce musu ummi sabuwar ƴar aiki ta yi, su yi ta yaba ƙoƙarin ummi, yarinya ƙarama amma ba ta jin jikinta. Ko da ummi ta fara zuwa makaranta, a nan ɗin ma bata sauya zani ba, saboda ba ta tsira daga cin zarafi daga ɗalibai ba, saboda launin fatarta da ta idonta. Wahala ta ƙara ƙaruwar mata a ka, ga zuwa makaranta, ga kuma aikin gida tamkar jakarsu. Hatta rahama idan ta dawo daga makaranta, har wankin phant da brezia haka take watsowa ummi, ƙarewar wulaƙanci har da wando mai jini, sai ta cire ta bawa ummi ta wanke mata. Iya shege da rashin kunya kuwa a wurin su intee, ba a magana, sai ta gyara wuri su ɓata, idan suka ci abinci sai ta bi ta ɗauke musu kwanuka, sai dai kawu yahaya baya iya magana, yana ji yana gani farida da ƙanwarta suka mayar da ummi baiwa, ban da cin mutunci da wulaƙanci da muzanta halittarta. Dan har haramta mata zaman kan kujerar falo aka yi, wai kar ta shafa baƙi a jikin kujerar. Abdul ne ma ruwansa da ita, dama shi ba wani magana ya cika yi ba sosai. Yau ma farida ta tafi gida wai suna biki, ga tsohon ciki, amma kamar akuya saboda gantali, gashi tana cikin watanta na haihuwa. Daga ummi sai Abdul, sai kuma kawu yahaya da yake gida. Tana ta aikace-aikace, cikin tausayawa kawu yahaya ya ce "Sannu da aiki ummina, ki samu ki je ki kwanta ki huta". Tayi murmushi ta ce "Kawu na kusa gamawa ai" "Ummi kin daina kirana da Abba dai sai kawu ko?" Tayi shiru tana murmushin yaƙe. Bayan ta koma kitchen, ya numfasa ya ce "Yaya" Abdul ya ɗago ya ce "Na'am Abba". "Yanzu muna tare muna rayuwarmu, gwanin sha'awa kuna rayuwa tsakaninmu cikin jin daɗi, hakan yana yi muku daɗi ko?" Yayi murmushi ya ce "Sosai makuwa Abba". "Allah sarki, kamar haka idan Allah ya so, a kowane lokaci zai iya raba mu, muna raye ba tare da wani ya mutu ba, amma zai iya rabamu, kamar yadda ya ɗauke mahaifin ummi, ya rabata da mahaifiyarta, ya kawota zama a cikinmu. Ina kallon duk abun da mamanku take yi wa yarinyar nan, da ita da ƙannenka, ko ban ce komai ba, Allah yana kallon komai, dan Allah ko daga ɓangaren ka ne ta samu sassauci, ba dan Allah baya son ta ya ɗauki mahaifinta ba, ya kawota cikinmu ba, zaka so ayi treating ɗin ƙannenka kamar yadda ake treating ɗin ummi?". Jiki a sanyaye Abdul ya girgiza kai. "To dan Allah ka din ga nunawa ƴan uwanka, ummi mutum ce, kuma ƴa ce kamar ku, muzanta ta da bautar da ita, ba shi da wata fa'ida" ya din ga yi wa Abdul nasiha, sai duk jikinsa yayi sanyi. Sai dare sannan suka dawo, suna dawo gidan kamar sun dawo da dauɗa, suka cire kaya suka zubar, suka ci abinci suka baje kwanuka. Abdul ya tarar da ita a kitchen, tana ta wanke kwanukan da suka ci abinci, ya kalli ummi ya ce "Ki je ki kwanta, yakamata ki huta". Ummi ta ce "Kwanukan nan zan ƙarasa wankewa" Ya ce "Bari na tayaki" "Maza basa wanke-wanke" Tun da ta zo gidan nan, maganar kirki bata taɓa haɗa su ba, ba ruwansa da ita, dan haka yau tayi mamakin cewa da yayi zai taya ta aiki. Shi dai tun da Abba yayi masa wannan nasihar ɗazu, gaba ɗaya sai tausayin ummi ya kama shi. Kallonsa take yi tana mamaki, yadda yake kikkife mata kwanukan, ummi sai cewa take yi ka bar shi fa yaya Abdul. "Uban me ka ke yi a kitchen ɗin nan?" Rahama tayi maganar tana shigowa hannunta riƙe da indomie. "Aiki nake taya ta". Ta watsawa ummi indomie, ta ce idan ta gama, ta dafa mata guda biyu. Ko da wasa ummi babu alamar gazawa a fuskarta, ta dafa mata indomie, Abdul yana biye da ita, ta gama yayi zaton kwanciya ummi za ta yi, amma ta kwaso uwar guga ta hau yi, kayan su na babarsu da na rahama. Abdul ya zuba mata ido, tana ta sauri ta kammala gugar, dan tana da assignment, tana yi yana ƙoƙarin yi mata hira, amma kasancewar ba sabawa suka yi ba, ya kasa ya saukko ya ce bari ya taya ta. Ba iya gugar yayi ba, ummi tana nuna masa yadda zai yi, sai dai bisa tsautsayi Abdul ya ƙona rigar babarsa, ta lace babban lace ba ƙarami ba. Hakan yayi dai-dai da fitowar rahama, ta gansu a tare Abdul da dutsen guga. Ta buɗe murya ta ce "Anty farida, zo ki ga bariki, aikin da ake sakata take rabawa da ƴaƴan gida". Abdul ya ce "Ni ne na ce zan tayata fa" Farida da ƙyar ta ƙaraso falon, saboda ciwon baya da mara da take yi. "Uban me ka ke yi a nan a wannan daren?". Ya ce "Bakomai". "Tashi ka wuce ka je ka kwanta" ya tashi ya nufi hanyar ɗakinsa. Idonta ya sauka a kan rigar leshinta, da sawarta uku an ƙona rigar. Ashar ta lailayo, ta ɗago rigar ta ce "Rigar ta wa ki ka ƙona mini? Dan ubanki dan baki da mutunci ba ki da hankali?" "Anty dan Allah ki yi haƙuri, tsautsayi ne, ban san zata ƙone ba" "Wallahi sai na ƙona ki da iron ɗin nan, ke wallahi sai na fanshe rigata, kut lallai baki da hankali" Miƙews ummi tayi, ta fara kuka tana bata haƙuri, amma rahama ta danƙota, ta danne ta farida ta sake jona iron ɗin ya ɗau zafi, ta nufo ummi. (*Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ina amfani da wannan dama wurin miƙa saƙon ta'aziyyata, ga ɗaukacin marubuta, na rashin ƴar uwa marubuciya, maryam nasir marsad, dan girman Allah duk wanda ya karanta page ɗin nan, muna barar ƙulhiwallahu ƙafa uku, Ubangiji Allah ya yi mata rahama, ya kai haske kabarinta ya sanya bakin wahalarta kenan, idan ta mu ta zo ya sanya mu cika da kyau da imani Amin*) (MASU NEMA DAGA FARKO, KU DUBA A WATPAD PLEASE 🙏) Ayshercool What's app only please 🙏 08081012143.                             *CUTARWA!*     *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* BRIGHT PENS FREE BATCH P15 Ihu ummi take yi, tana yi musu magiya su yi haƙuri, amma cike da mugunta da zalunci, rahama ta danne ummi a ƙasa, ta cusa mata ɗan kwali a baki, ta yadda sautin ihunta ba zai fita sosai ba, ta ɗage wa ummi riga, farida ta din ga nana mata iron ɗin  nan a cikinta da zafinsa da komai. Wata irin miƙa ummi take, saboda azabar da ta ratsata, take ta saki fitsari, saboda azabar zafi da ya ratsa ta. Abdul har ya je ɗakinsa ya tuna ya ƙona rigar maama, kuma ƙila ummi zata hukunta, dan haka ya juyo da sauri, ya dawo falon. A gigice ya ƙarasa wurin, ganin bala'i da izayar da ake yi wa ummi. "Maama dan Allah ku bari, ba a yi wa mutum azaba da wuta". Fitsarin da ummi ta saki, ya sanya rahama cikata, ta rufeta da duka, saboda ta ɓata mata jiki da fitsari, ta fizge hijjabi da hular kan ummi, a take dogon gashin ta mai matuƙar santsi ya zubo har fuskarta. Rahama ta ce "Kut, wannan gashi ko attach" tayi maganar tana jan gashin ummi da ƙarfin gaske, ummi jikinta ya din ga rawa, ta kasa ihun saboda azaba, ta riƙe gashinta da rahama ta cika hannu da shi. Abdul ya fara ƙoƙarin ture rahama daga kan ummi, farida ta kai ƙafa zata daki ummi, ta zame da ruwan fitsarin da ummi tayi, ta faɗi. Wani irin ihu ta kurma, rahama ta ɗaga ummi, ta nufeta a gigice, ummi ta samu ta lallaɓa ta tashi da gudu, ta tafi ɗakinta. Banɗaki ta shiga, ta cire rigarta ta din ga zuba ruwan famfo a cikinta, tana jin tamakar wurin ci yake yi da wuta, ga wani irin azaba da kanta yake yi, har wani jiri take ji. Kan ka ce kwabo jini ya fara zuba daga jikin faruda, jikinta ya fara kakkafewa, rahama ta ce "Abdul yi sauri ka je ka taso abbanku" Abdul ya tafi da gudu ɗakin da mahaifinsa yake ta bacci, saboda a gajiye yake sosai, duk wainar da ake toyawa bai sani ba. "Abba, Abba ka tashi maama ta faɗi ƙasa" Da ƙyar ya buɗe ido, ya kalli Abdul ya ce "Meyafaru?" "Maama ce ta faɗi a falo" agogo ya kalla, ɗaya saura na dare, me ta je yi falo a yanzu?". Ya saukko daga kan gadon, suka fito falon tare, falon sai ƙauri yake yi saboda iron da aka bari a jone. Jini take zubarwa sosai cikin gushewar hankali, da sauri kawu yahaya ya ɗaukko mukullin motarsa, da ƙyar suka ɗaga farida, saboda nauyin cikin ta suka bar Abdul a gida suka tafi asibiti. Ummi ba ta san abun da ake ciki ba, tana can tana jinyar cikinta da suka ƙona da dutsen guga. Ta zauna ta yi shiru tana ta tunanin, me ta aikata da ya sanya kowa ba ya son ta ji daɗi, kowa babban burinsa shi ne ya ga ya cutar da ita ta yi kuka? Ta ɗauki vasaline ta shafawa wurin, duk da haka sai da ya fara ɗurar ruwa, duk fatar cikin ta tashi. *** Idiris a tunaninsa tafiyar ummi, shi ne samun sassauci a gare shi, ya yar da ƙwallon mangwaro ya huta da ƙuda. Hashim kuma Iya ta sako shi gaba da cin mutunci, ko gaisuwarsa ta daina amsawa, saboda haushin gayawa kawu yahaya abun da ake ciki da yayi, ya sanya yahayan yana yi musu kallon azzalumai. Idiris ya lallaɓa ya cigaba da zuwa wurin hindu, yana son ya hilace ta su aikata alfasha, tun da iyayenta sun ƙi ya aureta. Gulmace-gulmace suka din ga yawo, a kan azabtarwar da Iya ta yi wa ummi, da wanda idris ya yi wa ummin, tare da ƙoƙarin bankaɗa asirin dalilin da ya sanya aka fasa auren idiris da hindu, ana ta zaginsu a unguwa, aure wata ɗaya ya mutu. Haka nan sai ummi ta din ga yi wa Idris gizo, idan ya je gidan da suka zauna. Ko kuma yayi ta mafarkinta tana yi masa mugun kallo tana kuka. Gashi duk wannan abun da ya faru, ya kasa daina jin sha'awar ummi, ya kuma kasa manta yadda jikinta ke da matuƙar taushi kamar auduga. Tun da yake leƙe-leƙnsa, bai taɓa taɓa mace mai laushin fatar ummi ba, gashi dai ko man shafawar kirki ba ta da shi, amma fatarta har wani irin santsi take yi. Ya din ga tuhumar kansa, da ganin wautar sa na kasa daurewa ya sauke abun da yake damunsa game da ummin kan su rabu, amma da ya tuna annakiyar dauɗar da ke jikinta, da kuma warin da take yi sai yayi tsaki. A rashin ummi ya cigaba da ƙoƙarin hilatar hindu, yayi lalata da ita, hindu yarinya ce ƴar shekara goma sha shida, gidan su suna da tarbiyya sosai, dan haka sai wahalar da Idiris take, taƙi bashi haɗin kai, sai dai tana matuƙar ƙaunar idiris. *** Likitoci suka rufu a kan farida, ana ta ƙoƙarin ceto ranta, sai dai jini yaƙi tsayawa, ƙarshe aka ce tiyata za a shiga da ita da gaggawa a cire mata cikin, dan ta fara jijjiga ga jini ya ɓalle. A daren aka shiga da ita tiyata, aka ciro ƴa mace, sai dai ba ta san in da kanta yake ba, har aka fito da ita. Ita kanta yarinyar taƙi yin kuka, aka yi ta fama, sai dai tayi kaɗan tayi shiru, ga rashin isashiyar oxygen a jikinta sai da aka saka mata oxygen. Rahama ta din ga kuka, tare da ɗora zargin hakan a kan ummi, sai dai ta yi shiru ba ta gaya wa baban su Abdul abun da ya faru ba. Abdul kuwa a gida aka bar shi, ya kasa zaune ya kasa tsaye, mussaman yadda ya kasa manta ganin jini na zuba a jikin. Ummi bacci sai ɓarawo ya kwasheta, shi ma a rigingine ta kwana. Da asuba ta tashi tayi salla, fatar cikinta duk ta ɗaga tayi wani iri, saboda ƙuna. Bayan ta idar da sallar, ta lallaɓa ta fito falon, ta tarar da wurin duk jini, ga kayan gugar duk a watse a wurin, tsaf ta gyara wurin ta kwashe kayan gugar, ta shiga kitchen, ta ɗora ruwan shayi, sai lallaɓa jikinta take yi, saboda raɗaɗin da take ji a cikinta. Ta sake fitowa falo, ta tarar da Abdul a tsaye yana kallonta. Ta kalleshi ta ce "Yaya Abdul". "Na'am, ya jikin wurin ya ƙone?" Ta ce "Eh, amma ba sosai ba". Ya ce "Maama fa a asibiti ta kwana" Zaro ido ummi tayi ta ce "Meya sameta?". "Faɗuwa tayi" yayi maganar cikin damuwa. Sai a lokacin ummi ta tuna taga farida ta zame ta faɗi, ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, to yanzu ya jikinta?". "Nima ban sani ba, tun da suka tafi basu dawo ba". Ummi ta ce "Allah ya sa tana lafiya". Ya amsa da amin. Suna tsaye suna jajantawa, sai ga Abba yayi sallama, duk suka zura masa ido suna yi masa sannu da zuwa. "An yi wa mamanku aiki, an ciro baby girl, sai dai dukkannin su, they are under special care, duk basu da lafiya" Ummi ta ce "Subhanallah, Allah ya basu lafiya". Ya amsa da "Amin, ummina na san kin yi breakfast, ki zuba wani a flask a kai musu asibiti, ku shirya na ajiye ku a makaranta, ina su kausar?" "Ba su tashi ba" "Kamar yaya, ƙarfe bakwai saura, ba zasu makaranta bane?" A fusace ya nufi ɗakinsu, ya taso su da bulala. Ƙarshe dai sai da suka makara, jin mamansu na asibiti, ya sanya suka din ga kuka, haka ya kai su makaranta ya wuce asibiti. Gumin da ummi take ta yi, ya din ga taɓa wurin ƙunar nan, ga kuma rigar makaranta, hakan ba ƙaramin takurata yayi ba. Sai dai duk da abun da farida da ƙamwarta suka yi mata, tunaninta yana kan yaya jin faridan yake. Kasancewar rahama ce a can asibiti tare da farida, sai ya zamana kusan kula da ragamar gidan yana hannun ummi, kai ba ka ce babu mace a gidan ba, duk aikin gida ita take yi, har kawunta sai da ya yabawa ƙoƙarin ta tare da jinjina mata, dan hatta abincin da za a kai asibiti ita take dafawa. Gefe guda Abdul ne yake takawa su intee burki, dan tana yi musu wahala amma ba sa gani, dan sai suka tsiri cewa ai anty rahama ta ce musu, ummi ce ta saka mamansu ta faɗi, su yi ta yi mata rashin mutunci da wulaƙanci. Kwanan farida biyu a asibiti, aka samo kanta da ƙyar, kawu yahaya ya ɗauki su ummi ya tafi da su asibitin dubata. Sai dai yanayin kallon da ƴan uwan farida ke yi mata, ya sanya ta sha jinin jikinta, dan ko sannun da tayi wa faridan ba ta amsa ba. Tana kwance jaririyar a kusa da ita, ana ƙara mata jini. Sai dai kasancewar babansu Abdul yana wurin, ba su iya ce wa ummi komai ba. Ummi fa ƙuna ta din ga jagwalewa, ga ƙaiƙayi tana yi mata, ta tuna ta taɓa ƙonewa a ƙafarta lokacin tana ƙauye, na'ima ta din ga shafa mata zuma, dan haka ta cewa baban su Abdul, ya sammata zumar da yake shan shayi. Yayi murmushi ya ce "Zumar da gata nan kaya guda, ai ba sai kin tambayeni ba ummana" ta samu abu ta tsiyaya take amfani da ita a ƙunar, dan har wurin cibiyarta ta ƙone. Kwanan farida biyar a asibiti aka sallamo su, babu tsammani ummi ta dawo daga makarantar boko ta dawo ta tarar an cika gidan. Ta ƙarasa falon ta durƙusa tana gaishe su, sai dai basu amsa ba, rahama ta janyo hijjabinta har tsakiyar falon ta ce "Kun ganta nan azzaluma, ita ta kusa kashe anty farida, ita ta kayar da ita" "To ai da farida cewa tayi mai aikinta ce". "Ba ƴar aiki ba ce ba, ƴar wan maigidan nan ce". Ƙanwar babansu farida ta ce "Kuma shi babu matakin da ya ɗauka?" Farida na daga kwance ta ce "Wane matakin zai ɗauka, kin ga faman da nayi a kan ba zan zauna da ita ba ya dage, ni kuwa na samu ƴar aiki" "Aikuwa idan baki yi hankali ba ta kashe ki wataran". Ummi tayi shiru ta sunkuyar da kai, wata yayar su ta dunƙule hannu, ta ɗirka mata duka a tsakiyar ka ta ce "Wallahi da kin kasheta, sai kin yi prison daga ke har ubanki". Rahama ta ce "An ce ubanta ya mutu ai". "Matsiyaciyar yarinya da ya bar wata tsiyar, da ba a ganki a nan ba, har ki ke ƙoƙarin kashe mana ƴa, ni wannan anya ma ba mayya bace ba, kalli ƙwayar idonta fa". Wata a gefe tayi caraf ta ce "Wace iri ce? Turo mini ita nan, ai ni ina gane maye" Matar ta ja ummi kamar tana jan shara, ta dungurarwa da ɗaya matar ita, tuni ummi ta fara kuka, ga zafin duka ga na cin mutunci. "Ke ɗago idonki na gani" Ummi ta sunkuyar da kai ta kasa ɗagowa. "Ba zaki ɗago ba sai na mareki" ummi ta kasa ta sake fashewa da kuka. Aikuwa matar nan babu tsoron Allah, ta sauke wa ummi yatsunta a fuska iya ƙarfinta, sai da ta hantsula gefe. "Wallahi zata iya yiwuwa mayya ce, tun da ta kasa haɗa ido da ni, shegiya ga baƙi kamar ƴar maƙera". Suka ciwa ummi mutunci son ransu saboda abun kunya, da yawansu zasu haifi ummi, amma kasancewar ba ƴar su ba ce ba, suka din ga muzanta ta suna aibata ta. Tayi kukan da tun da aka kawota gidan ba ta yi irin sa ba, har ta fara tunanin ko roƙon kawu yahaya za ta yi, ya mayar da ita ƙauye. Sai dai gabanta ya faɗi, da tuna irin azabar da ta sha a ƙauye, da sauri ta girgiza kanta, har da istigfari, ta fara ƙoƙarin auna zaman nan da na can wanne yafi sauƙi. Duk zaluncin iya, ba ta taɓa ƙonata da wuta ba, illa iyaka duk laifin da tayi jikinta zai gaya mata. Nan kuma duk rintsi, ko ba a bata abinci sau uku ba, ba zata kwana da yunwa ba, kuma tana da kayan makaranta da na sawa duk da babu yawa, kuma tana da takalmi da sauran abun da ba a rasa ba. "Mama meyasa ba so na ne? Laifin me nayi, meyasa idona yake ba kalar na mutane ba? Duk abun da nayi mutane sai sun tsaneni, ko a gida ko a makaranta?" Tayi maganar tana ganin fuskar mariya a idonta, tana jin tamkar ta ga mamanta ta bayyana. Tayi kuka ta gaji, ta duba sabulun wankanta ya ƙare, tayi wankan a haka, ta shirya islamiyya, ta fice ba tare da kowa ya sani ba. Dama kuɗin motar zuwa islamiyyar ma, idan kawu yahaya yana nan, yana bata ko ya bawa farida ta bata, idan ta ga dama ta bata, ko taƙi bata wanda zai ishe ta shima saboda ta na biyawa ɗaukko su intee daga ta su makarantar islamiyyar, dan Abdul ba lokaci ɗaya suke tashi ba, sai ƙarfe shida, su kuma tun huɗu da rabi ake tashin su. Dan haka ummi tafiyar ƙafa ta sha, kan ta je makarantar, nan ma da ta je sai da aka daketa dan ta makara. Zama tayi, tayi shiru a ajin, dan kamar yadda ta saba, bata da ƙawaye, dan ba ta son shiga cikin su su tsokane ta. Haka kurum ta ɗan shagala da kallon yarinyar da take jin tsoro a ajin, mai suna maryam saboda hantararta da take yi tana kyararta, da nuna mata tsana ƙarara a fili. Tubarkallah maryam fara ce sol, irin fulnin nan masu dogon hanci, sai azabar iyayi da iya gayu, da yawa ƴan ajin na tsoronta, saboda azabar masifarta da rashin son rai ni. Ba tsammani ummi ta ji ta ce "Ke lafiya ki ke kallona kamar zaki cinye ni?" Da sauri ummi ta ɗauke kanta tare da cewa "Yi haƙuri" "Da haƙurin ta mutu sadakar nawa ki ka bayar? Bana son kallo" "Ai na ce kiyi haƙuri" ta faɗa a sanyaye. A ranta ta ce 'Dama nima fara ce, wataƙila da ba za a tsane ni ba. Amma ai akwai baƙaƙe da yawa da ake son su, ni meyasa ba a sona?' ta tambayi kanta, wasu hawayen na rige-rigen zubowa. Maryam ta zauna a kusa da ummi, ko a jikinta ganin ummi ta kifa kanta. Sai da malami ya shigo ajinsu sannan ta ɗago kanta, ya yi musu karatun da zai yi musu, sannan ya basu class work. Sai dai fa maryam ba ta iya komai ba, ta din ga rarraba ido, ga malamin ya jaddada cewar duk wanda ya faɗi sai ya zane shi. Ganin lokaci ya kusa cika, ya sanya ummi buɗe mata takardarta ta ce "ki kwafa ya kusa karɓa" babu kunya maryam ta kwafe duk abun da ummi ta rubuta. Lokacin sallar la'asar yayi, ɗalibai na ta ƙoƙarin fita daga ajin, ba tare da tuna alkhairin ummi ba, maryam ta hankaɗeta zata fita, bisa tsautsayi ummi ta faɗi ta fama ƙonuwar da take cikinta. Ƙara ta saki, tana girgiza kanta, duk ɗaliban suka tsaya suna kallon ummi, ganin jini yana tsatstsafowa a rigar uniform ɗin ta. Maryam a tsorace ta ce "Na shiga uku" ta durƙusa ta ɗago ummi, a zaton ta ko cikin ummi ne ya ɓule. Ummi sai yarfe hannu take yi tana kuka, ɗalibai suka taru a wurin, malamin da ya fita daga ajin ya dawo ganin ɗalibai a wurin yana tambayar meyafaru, aka gaya masa maryam ce ta hankaɗeta ta faɗi. Cikin tashin hankali ya ce a kai ummi ofishin malamai, ita ma maryam ta bisu sai an hukunta ta. Cikin tashin hankali malamai mata suka ɗaga rigar ummi, ana ƙoƙarin gano menene yake jini a cikinta, sai dai ba kyan gani, suka tarar da ƙonuwar ta jagwale, ga ruwa ga jini ya dame da zumar da take sakawa. Maryam na ganin haka ta fashe da kuka, ta zata duk faɗuwar ce ta janyo haka. Shugaban makarantar ya dubi Maryam ya ce "Wato maryam ba kya ji ko? Zaki gane kuskurenki, sai kin daku yau ɗin nan, makauniya ce ke da zaki tureta ta faɗi". Malamin ya dubi ummi ya ce "Ke ya aka yi ki ka zo da wannan ciwon makaranta, meya sameki haka?" "Ba maryam ce ta ji mini ciwon ba, dama na ƙone a gida" "Da me ki ka ƙone, kuma an kai ki asibiti?" Ta ce "Eh an kaini" "A'a wannan da an kai ki asibiti, da ba ta jagwale haka ba, kuma da ba a bari kin saka kaya ba, ki gaya mini gaskiya da me ki ka ƙone?" Malamin yayi maganar cikin zare ido. "Da ruwan zafi" "Mamanki ta san kin ƙone?" Ta girgiza kai alamar a'a. "Meyasa baki gaya mata ba?" Cikin kuka ta ce "Ai ban san in da take ba" "A'a to ina mutanen gidan da ki ka ƙone ɗin, ba ƴar gidan dr. Yahaya bace ne?" Ta ɗaga kai alamar eh. "Malama zuhra, a nemo abun hawa a kai yarinyar nan asibiti a dubata, ke kuma maryam mu je office ɗina sai na hora ki" Maryam ta fashe da kuka tana magiya, cikin ƙarfin hali ummi ta ce "Malam dan Allah kayi haƙuri, ba ta san ina da ciwo ba, na yafe mata ai" Ya ce "To zan duba, tashi a kai ki asibiti, daga nan a mayar da ke gida". A asibitin ma, ma'aikaitan sun yi faɗa sosai a kan sakaci da lafiyar ummi, dan da ƙunar zata iya zama infected ta taɓa sauran sashin

Chapter 14 of 54