Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
abincin rana ne, barka da fitowa maigidana na kaina" ta nufe shi, ya buɗe hannayensa ta shiga jikinsa ta rungume shi. Ya saka hannunsa ɗaya ya riƙe ƙugunta, ɗaya kuma ya shafa kanta ya ce "You look cute baby" sai dai bai kai ga aikata abun da yayi niyya ba, maryam ta faɗo falon. Mamaki ne ya kama raihan, dan bai san ta zo ba, ummi ma ta yi pretending da ba ta san da zuwanta ba ta juya da sauri tana kallon in da maryam take. "Maryam, wannan ai saɓa dokar addini ce, ai a main falo yakamata ki tsaya ki nemi izini, kawai sai ki faɗo mana haka babu ko sallama?". "Sallama, ni ka ke gaya wa haka raihan, saboda wannan mummunar yarinyar da ka aura, me ka gani a jikin ummi da babu a jikin matan garin nan ka aureta dan asara?" Raihan ya sosa kai yana murmushi ya ɗago ummi daga jikinsa ya ce "Abubuwa da yawa mana, next time karki sake shiga wurin ma'aurata anyhow please, ba girman ki bane" Ummi ta yi murmushi ta ce "Sannu da zuwa Maryam, yau ina da babbar baƙuwa" "She ruin my enjoyment" yayi maganar a taƙaice. Maryam kuwa ta ɓarke da masifa ta babu gaira babu dalili, tana alwashin sai ta raba auren nan, dan asiri ummi ta yi wa raihan. Ummi ta yi shiru, zuciyarta na yi mata zafin cin zarafin da maryam ke yi mata, kuma ta ƙi ɗaga jikin raihan. A hankali ya ce wa ummi "Go and get some rest, kin san baki gama warkewa ba" ta jinjina masa kai, ta nufi ɗaki. "Dubeta dan Allah, ko kunya ba kya ji"  sai dai abun da Maryam ba ta sani ba, har da hassada ta kamata, gidan da raihan ya saka ummi ya fi nata haɗuwa, kuma gaba ɗaya yau ta nemi munin ummi ta rasa, a dire take ba abun da wata ƴa mace za ta nuna mata. Ga wani irin ƙamshi da take yi, yau ta ga ainihin kyawun surar da Allah ya yi wa ummi. Dan da ta juya baya ma tana tafiya, ga gashin ta ya kwanta a bayanta, kamar ba bahaushiya ba, dole yaro ya rikice ta faɗa a ranta. Ummi na barin wurin ya haɗe rai ya kalli Maryam ya ce "Idan har kin san zaki zo gidana ki ci mutuncin matata kar ki sake zuwar mini gida ki ɗaga mini hankali, Mami idan tayi ta isa ne, ke kuwa kin yi kaɗan duk rashin mutuncin da na yi miki ke ki ka saya". "Ni ka ke cewa kar na sake zuwar maka gida? Kodayake ba laifinka bane ba, an kai sunanka gaban bokaye an mallakeka" "Bakomai, ni bokan ya taimakeni da ya mallake mata ni, kar ki sake zuwar mini gida ki ɗaga mata hankali, definitely na san sai ta yi kuka cin mutuncin da ki ka yi mata". Maryam ta ja numfashi ta jinjina kai ta ce "Bayan cin mutuncin da ta yi mini, kai ma ka ɗora naka, sai na nuna wa Salma haryanzu kanta a kwano yake, yarinyar da na taimakawa a baya mara galihu irint... "Kema ta taimaka miki, dan a irin daƙiƙancinki, ba dan taimakon nata ba asarar kuɗin tara za ayi a banza, dan haka juna ku ka taimaka" suka yi wa juna kaca-kaca suka yi faɗa ta tafi ta bar gidan. Ummi kuwa ta din ga saƙe-saƙe a ranta, tabbas yanzu tun da har ta riga ta yi aure ta bar gida, raihan ne kawai ya rage mata source of happiness, idan ba ta yi da gaske ba, Maryam za ta iya aikata abun da ta ce, dan ba mutunci ta cika ba, dan haka a wannan karon ba ta tunanin za ta iya ɗaga wa maryam ɗin ƙafa. Raihan ya bi ta ɗaki ya din ga rarrashin ta. Sai dai ta kasa daurewa, sai da ta din ga yi masa kuka yana rarrashinta. Wayarsa ce ta fara ringing, ya duba ya ga sunan Yaya Salim, ya ɗaga suka gaisa, Salim ya ce "Ina waje" Raihan ya ce "Yaya ka shigo falo, gani nan" ya ajiye wayar ya ɗauki jallabiyarsa ya ce "Yaya ne ya zo, ki wank fuskarki ki zo" "Allah ya sa ba laifi na yi masa ba" Ya girgiza kai ya ce "Haba dai, yaya Salim ya ce ke ƙanwarsa ce, da ya karɓo amanarta a wurin mama, idan ban kula da ke ba, ni da shi ne" Ummi ta yi murmushin yaƙe, ta sanya kaya suka fito. Sai dai tun da suka fito yake bin su da kallo, suka zauna ummi ta gaishe shi, ya amsa tare da cewa idan ina ganinku taren nan, sai na ji kamar nima na yi auren nan. Da sauri Raihan ya ce "Yaya da gaske, dan Allah ka yi" Salim yayi murmushi ya ce "Ya ƙarfin jikin naki" raihan ya ce "Ta ji sauƙi sosai" "Kai na tambaya?" Raihan ya ce "Allah ya baka haƙuri". "Meyafaru ne? Na ga kamar fuskar ku da damuwa, mussaman ummi". Ummi ta ce "A'a yaya, komai lafiya ƙalau" Salim ya gyara zamansa ya ce "Yadda ku ke ɗin nan gwanin sha'awa yayi wuri ace kun fara samun saɓani, duk da ma bana tunanin hakan ne, na san akwai abubuwa marasa daɗi a ƙasa, amma ku yi haƙuri da juna". Raihan ya ce "In sha Allah babban yaya" Ya ce 'Masha Allah, dama zan wuce ne na ce bari na zo na sake dubata, amma Maryam ta zo gidan nan ko?" Gaba ɗaya suka kalle shi a tare. Raihan ya ce "Eh ta zo" "Tun da na ganta a gida jiya na san za ta zo, kuma yanayin ta ya nuna mini ba zuwan arziki tayi ba, ta yi miki wani abu mara daɗi ko?" Ummi za ta yi magana raihan ya ce "Haka ne yaya, amma in sha Allah i can handle it" Salim ya miƙe ya ce abun da nake son ji kenan, bai sake ce musu komai ba ya fice. "MD meyasa zaka gaya masa haka?" "Wai dan kin ga yana shiga sabgar aurenmu? Idan na yi masa ƙarya a gabanki zai zageni, ba a ayi masa musu, na gaya miki kallon ƙanwa yake yi miki,ko na ɓoye masa idan ya gano na kaɗe" Ummi ta ce "Ni dai duk da haka da baka gaya masa ba, ai na san da ta tafi shikenan. Salim kuwa fitar maryam ya gani a mota, ya samu nihal ya ritsata ya tambayeta ina maryam ta tafi daga zuwanta jiya? Ba ta ɓoye masa ba ta gaya masa gidan raihan ta tafi. Maryam kuwa bayan komawarta gida, ta samu mami ta zayyane mata abun da ya faru da wanda bai faru ba, wanda hakan ya ƙara tunzura mami, mussaman da maryam ta gaya mata baƙaƙen maganganun da ummi ta faɗa wanda suka ba ta mamaki. Bayan la'asar Salim ya shiga sashin mami, wanda rabonsa da sashin, yayi shekaru. Mami na cin abinci maryam kuma na kallo yaranta na ta wasa a falon. Ya tsaya a kan Maryam ya ce "Zuwa na yi nayi miki gargaɗi, idan ki ka sake taka ƙafarki a gidan raihan, ki ka ci zarafin matarsa wallahi sai na casa ki, ba soja ba ko bindiga ki ke aure tun da ke mahaukaciya ce" Mamk ta miƙe tsaye ta ce "Saurara kai a wa?". "Ni a wanta, wanda na isa na saka na isa na hana, wallahi ba zan yi kaffara ba, na sake jin labarin kin je masa gida kin yi masa hauka, sai na ci.... Ya ɗirka mata ashar mai zafin gaske. "Shaye-shayen ka yi zaka zo ka sauke iskancinka a nan?" Salim ya ce "Ras nake, sai dai da sannu zaki gane manufata, let her make another scene zaku gani" fuuu ya fice kamar zai tashi sama. "Yaushe yaron nan ya samu kusanci da raihan, har yake shiga cikin lamarinsa haka?" Maryam kamar tayi kuka ta ce "Mami ƙarata suka kai masa kenan? Mami raihan ya fifita matarsa a kaina, mami ki yi wani abu a kai tun kafin raihan yafi ƙarfin control ɗinki". Babu tunanin komai, ta hau kan maganar ta zauna. Ummi tana sallar magariba a bedroom ɗin ta, ta ji yo hayaniya a falo, wanda ko tantama ba ta yi muryar mami ce, mamin da tun da aka yi bikinsu ba ta taɓa takowa gidan ba. Bayan ta idar da sallar, cikin tsananin fargaba da tashin hankali ummi ta fita falon, raihan yana ta ƙoƙarin shawo kanta daga masifar da take yi. "Mami sannu da zuwa" riƙe sannu da zuwanki, idan kin so ma ki kirani da bilki, dan ban haifeki ba, saƙon da ki ka bawa maryam na ji, na zo kuma in nuna miki na isa da ɗa na, kai kuma ka aiwatar da abun da na ce" "Mami dan girman Allah ki yi haƙuri, mai zai sanya na aikata haka babu wani dalili". "Ni ka ke gaya wa haka? To ka saka a ranka zaka canza wata uwar bani ba, kai ba ka isa ba ma, wallahi sai ka saketa raihan na riga na rantse maka, ko in yi maka abun da ba ka zata ba" tayi maganar tana watsa masa biro da takarda. Tuni jikin ummi ya fara rawa, ta ji numfashin ta kamar zai ɗauke, da sauri ta bar falon, ta tafi ɗaki, lallai tsuguno ba ta ƙarewa rayuwarta ba. Ta ɗauki ƙaramar akwatin ta, ta zuba kayanta, ta buɗe wurin da raihan yake zuba kuɗi ta ɗiba ta zuba a jakarta ta ɗauki ATM ɗin ta ta fito, tana zubar da hawaye. Ta tarar da raihan a zaune ya dafe kansa, cikin tashin hankali bai yi zaton mami zata aikata masa haka ba. Tana ganin ummi ta ce "Ita akwatin ai na san ba daga gidan ubanki ki ka zo da ita ba, dan haka ajiyeta" ummi ta durƙusa ta kwashe kayanta ta ajiye akwatin. Raihan ya miƙe yana kiran sunanta. "Wallahi ka taka ka bita ban yafe maka ba!!!. Ummi ko waiwayawa ba ta yi ba ta fita. "Kuma ka san duk yadda zaka yi ka kareni a wurin babanka, wallahi ka kuskura ka gaya masa umarnina ne ka rabu da ita sai na saɓa maka, ba zan zuba ido ka zama soko ba" Zuciyar sa na tafasa ya ce "Mami kina ganin wannan hukuncin shi ne farincikin ki ko? Ni kuma kin ƙuntata mini, shikenan tun da haka ki ka yanke kin isa ne, na gode" Ƙura masa ido ta yi ta ce "Raihan kuka zaka yi dan na rabaka da masifa" ya kalleta hawaye na gangarowa daga idonsa, ya san komai zai ce mata ba zata fuskanci irin son da yake yi wa ummi ba. A falon gida ummi suka yi karo da farida, da ita da kausar da alama ba su daɗe da dawowa daga unguwa ba. Ta ƙarewa ummi kallo da kaya a hannu ta ce "Lafiya?" "Ya sake ni ne" ta faɗa a hankali. Kawai farida ta rafsa guɗa ta ce "Har an yi an gama? Soyayyar da ɗaga hancin ya ƙare? To wallahi ba zan riƙe bazawara har karo biyu ba, ki nemi wurin zuwa ba dai nan gidan ba!!!. Ayshercool. PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi  Man garan gashi  Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.                        *CUTARWA* *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* 42 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g AYSHERCOOL 08081012143 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g 42 Cikin sanyin jiki ummi ta ce "Dan Allah anty ko zuwa da safe ne, sai na tafi in sha Allah" "Wallahi ba ki isa ba, ba zan sake zama inuwa ɗaya da ke ba, ai ni ba zan manta cin kashin da dr. Ya din ga yi mini saboda ke ba, a samu ki auru da ƙyar sannan ki dawo mini, bana maimaita kuskure, haka Allah ya yi ki da baƙin jini, kamar mai hatimin jaɓa duk in da ki ka je sai an tsaneki an kore ki" Ummi ta yi shiru ta rasa abun da yake yi mata daɗi, ina zata tafi ga duhun magariba. Kausar ta nufo ummi gadan-gadan da niyyar ta hankaɗata ta koreta, ummi ta ja da baya ta kalli kausar ta ce "Kar ki kuskura, akwai banbanci tsakanin da da kuma yanzu, ko da aurena ya mutu da yardar Allah na fi ƙarfin komawa baya, ba sai kin hankaɗa ni ba, zan tafi". Duka suka kalli ummi, yaushe bakinta ya buɗe har haka da take mayar da martani. Ta juya ta fita, ta ɗan yi nisa kaɗan sai ga noor, sanye da uniform ɗin islamiyya. "Yaya ummi, da tafiya zaki yi ban dawo ba, to Allah ya kama ki" tayi maganar tana murmushi. Sai kuma ta yi saroro tana kallon ummi, ganin ummi a saɓule. "Ya na ganki a haka? Ina yaya raihan ɗin?". "Ya sakeni noor" ummi ta samu kanta tana gaya wa noor. Ta dafe ƙirji ta ce "An shiga uku, saki? Me ki ka yi masa? Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ashe da gaske maama take idan Abba yayi mata laifi ta ce namiji ba ɗan goyo bane ba, ashe da gaske ne me ki ka yi masa?" Ummi ta dafa kafaɗarta ta ce "Kul ki ka sake faɗar haka, mata mukan yaudari kanmu da ɗorawa maza kaso mafi yawa na zaluntarmu, alhalin a zahiri mu ne azzaluman kanmu, mu yi ta ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, amma a zahiri kowace mace ciwonta na ta ne ita kaɗai, noor maza ƴan goyo ne, kuma iyaye ne, ɓata garin cikin su ba zai sanya ayi musu kuɗin goro ba. Mami ce ta saka ya sake ni, ba laifin sa bane ba, ni duka da na san baƙin cikin ɗa namiji a rayuwata, amma maza sun tallafi rayuwata fiye da yadda mata suka yi". Tuni noor ta fara kuka ta ce "To ina zaki je? Ba dai gagarawa ba ko? wannan garin da ba sa sonki, me zaki je ki yi musu, ki zo mu tafi gida kawai" Ummi ta girgiza kai ta ce "A'a ai ni in da ba a so na da yawa noor, ki yi maza ki tafi, magariba ta yi" "To ina zaki je?" "Ke dai kar ki damu, zan dawo maza ki ƙarasa gida". Noor ta tafi gida da gudu, sai dai ta tarar farida suna sake tattauna abun da ya faru, a nan ta ji korar ummi suka yi, suka ce ba zata zauna a gidan ba. Duk da ƙarancin shekaru na noor, sai da ta jinjina mugunta irin ta mahaifiyarsu. "Maama yanzu idan wani abu ya sami yaya ummi a hanya fa, dare ya fara yi ki ka ce ta tafi gida? Idan Abba ya ji fa?" "Idan ina magana kina saka baki, sai na murɗe miki wuya, tun da ita ta haife ki, duk irin cin kashin da aka yi mini a gidan nan saboda ita ke ba kya gani, saboda ita aka saka miki sunan uwarta ban haɗa dangi da ita ba, ki cigaba da saka baki a kan irin wannan maganganun ki ga yadda zan yi da ke". Noor jikinta a sanyaye ta ce "Malaminmu ya ce; duk wanda ya shuka alkhairi ana yi wa ƴaƴansa ko ƴan uwansa, haka ma sharri, ni dai tun da ban yi aure yanzu ba, Allah ya sa a rama a kan anty inteesar ko kausar tun da dama ku ne kuke cin zalin yaya ummi" gaba ɗaya sai suka kasa magana, wata maganar idan noor ta yanko ta, sai ka kasa ba ta amsa. Farida ta yi ƙarfin halin cewar "A gidan Ubanki aka zalunceta?" Tayi shiru ta rungumi jakarta ta shiga ciki. Raihan yana zaune din ga jujjuya takardar a hannunsa. Mami ta zuba masa ido tana kallon ikon Allah, duk zafin ciwo ko na mutuwa raihan ba ya kuka, amma yau saboda ta raba shi da ummi, har da hawaye. Nan ta ƙara tabattarwa da kanta cewa ummi asiri suka yi wa ɗan ta. Ta miƙa hannu za ta karɓi takardar hannunsa, ya janye takardar. Saki nawa ka rubuta a jiki?" Tayi maganar tana kallonsa. "Dan Allah mami ki yi haƙuri ki ƙyale ni, ai na rubuta" "Kar ma ka rubuta, kuma ka tabattar a yau ba sai gobe ba, ka bi ta da takardar nan, kuma bana buƙatar sake wata alaƙa a tsakanin ka da ita. Abu na gaba shi ne zan je na nema maka taimako a warware sihirin da suka yi maka, azo ayi maza² a yi bikin nan". Bai ce mata ƙala ba, ta gama surutun ta tafi, ji take kamar ta yaye wa kanta wata babbar damuwa da ta hanata sakewa. Tana tafiya raihan ya shiga ɗaki ya ɗauki wayarsa ya tura wa ummi saƙo. "Salma, ki jirani a gida komai ya lafa, zan zo na ɗauke ki, dan Allah kar ki gaya wa kowa, ban rubuta komai ba, ban sake ki ba, zan dai-daita komai. Ki kwantar da hankalinki da safe in sha Allah zan zo" Bayan ya aika mata saƙon, ya ajiye wayar ya shiga yayi alwalar magariba. Sai dai hankalinsa ya kasa kwanciya, ji yake kamar ya bi ummi, amma da ya tuna gargaɗin mami sai ya kasa bin ta. 'Ban kyauta ba salma, am very sorry, baki cancanci haka ba' haka ya din ga sintiri yana surutai. Kasa jurewa yayi, ya ɗauki wayarsa ya kira tata, sai dai ba ta ɗagawa, tun yana saka ran za ta ɗaga har ya fara sarewa ya sanyawa ransa ummi ta yi fushi da shi. "Haba ummi, meyasa ki ke tunanin zan iya sakinki? Ba zan iya ba wallahi ban sake ki ba" ya din ga surutai yana kiran wayarta. Ummi kuwa ƙarfe goma na dare, tana cikin motar haya, ta nufi gagarawa, tana ta lissafi kala-kala a zuciyarta, yanzu shikenan lissafin rayuwarta ya koma baya?. Ta san zaman gagarawa ba zai kai ta ba, to sai ta tafi maiduguri daga yin aure ace ya mutu, ga mama ba cikakkiyar lafiya ba, suna murnar sun aurar da ita, kuma ta koma ta zaune musu a gida yau da gobe sai Allah. Ta share hawayen ta a hankali ta furta "Mami ba ki yi mini adalci ba raba ni da ɗakina da mutumin da nake matuƙar ƙauna" tayi maganar tana ƙunshe kanta a hijjabinta tana kuka. Ƴan cikin motar sai ba ta haƙuri suke yi, ba tare da sanin dalilin kukan na ta ba. Sai sha ɗaya da kusan rabi ta shiga family house ɗin su na gagarawa. Duk an rufe wasu ƙofofin wasu duk sun kwanta, jiki a sanyaye cikin tsananin fargaba ta shiga sashin iya da sallama. Iya ta amsa daga ɗaki tana tambayar waye, ummi ta shiga tana amsa mata da ni ce. Kamar sokuwa iya ta kalleta, ta ɗau fitila tana haskata. "Lafiya zaki shigo mana gida a tsakar daren nan kamar wata ƴar fashi?". Ummi ta ce "Lafiya ƙalau" "Kamar yaya? Ki rasa lokacin da zaki zo sai a wannan tsohon daren, yahaya dai an ce ba ya ƙasar nan me ki ka aikata ki ka gudo nan, ba zaki kwaso masifa ki yo nan ba, dan na san ba alkhairi ne ya kawo ki ba a daren nan dai" Ummi ta yi ajiyar zuciya, ga gajiya ta kwaso kanta har ciwo yake, ga uban kuka ta sha ga tuhumar wulaƙanci daga iya, kodayeke ba yau ne farko ba, dan haka ta ce "Mun rabu ne" "Da wa?" "Ya sake ni" ta faɗa a taƙaice. "Kuma da ya sake ki ki rasa ina zaki zo sai gagarawa? Garin da ki ka ce ba zaki sake zuwa ba? Amma ke dai an yi mai ƙashin tsiya, a yadda ki ke Allah ya rufa miki asiri ki auru da ƙyar ki kaso auren? Kodayeke kin gaji tsiya da rashin arzki a wurin uwarki, wallahi sai dai ki koma can wurin yahayan, ko ki koma wurin uwarki ba ki da wuri a gidan nan, ke ko kunya ma ba ki ji ba?" Ummi ta ce "Dan Allah iya ki yi a hankali, ki rufa mini asiri ko sati na yi zan yanke shawara idan bai mayar da ni ba shikenan, ba a san ransa ya rabu da ni ba, na san zai neme ni da..... "Dan Allah ki rufe mini baki, kin manta iskancin da ki ka din ga zubawa saboda zaki auri mai kuɗi? Wallahi sai kin bar gidan nan" Kasancewar dare ne, tuni kwaroroton iya ya sanya wasu tasowa, suka taho sashin iya dan jin ba'asi. "A daren nan fa zaki bar gidan nan" Babar auwwalu ce ta fara roƙon iya "Haba Iya, ko korarta zaki yi, ki fara bari gari ya waye mana, a daren nan ina za ta je yanzu?" "Ta koma in da ta fito, irin tsiyar da yarinyar nan ta shuka, idan tana da mutunci ba zata sake waiwayar gidan nan ba, ta koma in da ta fito, dama ba kowa take gani da gashi ba". Ana tsaka da bawa iya haƙuri, ummi ta nufi ɗakin da mamanta ta zauna, da kayanta a hannu, ba tare da ta tankawa kowa ba. Iya ta biyo ta ta riƙe ta, "Babu in da zaki je, tun da ba ɗakin uwarki bane ba yanzu, amaryar ilyasu ce a ciki yanzu, sai fa kin bar gidan nan". Ummi ta ƙwace hannunta ta ce "Ban damu ba ko ɗakin waye, abun da na sani shi ne akwai gadon ubana a cikin gidan nan, dan haka dole a sama mini wurin zama. Tabbas yau tura ta kai bango, na gaji, na gaji Iya shekara ashirin da shida ban yi ƴanci daga ƙangi da ƙuncin da ki ka jefa ni ba, na ɗau layin da ki ke son na hau, babu ragowar mutunci ko kimar ki da nake gani a yanzu, tun tuni yakamata na yanke alaƙa da ke, saboda tsanar da ki ke yi mini da mahaifiyata, amma kullum ina duba mahaifina ki ka haifa, nake baki girmanki saboda haka. An zo kunyar ƙarshe, ba zaki taɓa canzawa ba, zan bar gidan nan amma ba a yanzu ba" Tayi gaba ta shige ɗakin amaryar kawu ilya, ta ajiye kayanta. Daskarewa iya tayi a wurin, ummin da ko buɗe baki ba ta iya yi idan za ta yi magana, amma yau ita ta yaɓawa maganganu haka. "Iya ki rufawa kanki asiri a ƙyale yarinyar nan zuwa safiya" suka yi ta lallaɓa iya suna ba ta haƙuri. Ummi ta yi alwala ta yi salla, ko yunwa ba ta ji saboda baƙin ciki da tashin hankali. Amaryar kawu Ilyasu ta rasa me za ta ce, haka ta shiga ɗakin ta tarar da ummi ta haye mata kan katifa ta kwanta. Raihan bai gaji ba, ya cigaba da kiran wayar ummi, kawai ya ga wayar a ɗakin kwanansu a ƙasan pillow. Hankalinsa ya tashi, ya ɗauki wayar ga tarin missed calls ɗin sa da ya yi mata, ya ajiye wayar ya zauna, kansa yana wani irin sarawa sosai. Gidan ya ƙara yin shiru, bayan gama hayaniya a kan ummi. Ko kusa ko alama, bacci bai yi yinƙurin ɗaukarta ba, ta din ga tunanin ita kuwa meye laifinta haka, da kowa yake gudunta sai ka ce annoba?. Ta tashi a hankali ta tafi tagar ɗakin, ta buɗe tagar, wani sanyi ya daki fuskarta, ta ɗaga kai tana kallon sararin samaniya, tana tuna abubuwan da suka wakana a rayuwarta. Tabbas zamanta a gagarawa ba zai yiwu ba, akwai matsala, sai dai kan ta bar gagarawa sai

Chapter 44 of 54