domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.
FOLLOW AND SHARE
AYSHERCOOL
08081012143
MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.
Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.
32
Alhaji ya ce "Meye kuma na wata kwazgwamemiya baƙa? Ba mutum ba ce ba?"
"Ban gane ba mutum ba ce, ta girme shi fa ƙawar maryam ce?"
Ya ce "To shi ne me? Idan har shi zuciyarsa ta nutsu da ita ba shikenan ba, ni na yaba da tarbiyyar gidansu"
"Wallahi da sake, tun wuri ma dole a janye wannan maganar. Na zaɓa masa yarinya ya ƙi sai ya jajibo wannan mummunar yarinyar? Gidan da take zaune ai ba gidansu bane ba, zaman boranci ta yi a gidan kamar ƴar aiki"
"To kin ga kya samu lada ma, idan ya aureta ya kula da ita"
Kamar zata kama da wuta dan bala'i ta ce "Wallaahi ba zan lamunta ba, shi ne dan munafunci ni bai gaya mini ba, kawai sai yau ka zo mini da wannan zancen, a'a wallahi"
Alhaji ya ce "Ni dai in kin ga na fasa zancen auren nan, sai dai in shi ne ya dawo ya ce mini ya janye ya fasa, amma ba zan zama mutumin banza ba, shima sai dai in yi masa jagora ya je ya samu ubanta ya ce masa ya fasa"
Hajiya ta ce "Banda abun ki, ai ummi yarinyar kirki ce, nutsatsiyar yarinya ce, shi kyau ba shi ne abun dubawa ba, nagarta ake da cancanta ake dubawa"
"Kin ga malama ki rufa mini baki, ban saka da ke ba, idan nutsatsiya ce, ki haɗata da makakkun yaranki mana, sai ɗa na dama na san wannan duk kitumurmurarki ce, ke ki ka shirya wannan abun aka yi ban sani ba"
Hajiya ta ce "Allah ya baki haƙuri, nima ban san zancen ba sai yanzu, kuma su makakkun ƴaƴa ba laifi na yi wa Allah ya bani ba, jarrabawa ce, kuma da da nutsatstse a cikin su na yi sha'awar sanya ɗaya ya aureta"
Har mami za ta yi magana, Alhaji ya yi mata wani mugun kallo, hakan ya sanya ta yin shiru tana huci.
Hajiya kuwa tuni hawaye ya cika mata ido, tana jin zafin gori da cin mutunci da mami ke yi mata a kan yaranta, gani take yi kamar dabarar ta ce ta sanya Allah ya bata shiryayyun yara.
Alhaji ya kalli mami ya ce "Tun da kin saka mini mata kuka, sai ki bani wuri zan kula da ita"
Maganar ta sa ba ƙaramin fusata mami tayi ba, ta tashi ta ce "Haɗiyeta ƙarewar soyayya" tayi waje fuu rai a ɓace.
Ya dubi hajiya da hawayen fuskarta suka fara zubowa, ya rungumota jikinsa a hankali ya ce "You are brave woman, kar ki karaya, ki yi haƙuri ke ce fa mai Kwantar mini da hankali da rarrashina, ki yi haƙuri in sha Allah zaki ga tanadin da Allah ya yi miki sakamakon haƙuri"
Ɗan ƙara sautin kukan nata tayi, hawayenta ya ɓata masa riga, amma bai damu ba ya cigaba da rarrashin ta.
Kira uku raihan ya yi wa ummi sannan ta ɗaga, tayi masa sallama.
"Meyasa baki ɗaga ba, missed calls uku fa na yi miki"
"Ina aiki ne a kitchen, wayar tana ɗaki"
Raihan ya gyara kwanciyarsa ya ce "To ya ki ke sweetheart" wata irin kunya ce take kama ummi, idan ya ce
sweetheart ɗin nan, wai raihan ke ce mata sweetheart abun da kunya.
"Ba zaki amsa ba?"
"Ina lafiya" ta amsa a taƙaice.
"To yaya, su Alhaji sun zo ko? Na ga ya dawo ɗazu ina jiran ya kira ni ne"
A sanyaye ta ce "Eh sun zo"
"Yauwwa masha Allah, daga nan zuwa kowane lokaci zaki zama matata baby"
Ummi ta ce "Dan Allah ka din ga ce mini ummi kawai ko salma"
Raihan yayi murmushi ya ce "Ba kya son babyn saboda me? Ba daga bakin yaro kamata ki ke son ji ba ko? Kar ki yanke mini hukunci a yanzu, ina da kyakywan tanadi a kanki da rayuwarki ummi, zaki ji daɗin zama da ni sosai da sosai ki yi ta yi mana addu'a kin ji my Salma".
Ta amsa masa da "To" amma tunanin yadda za ta yi rayuwar aure da raihan take yi, ita yanzu gaba ɗaya ma kunya yake bata.
Faɗowar mami afujajan ɗakin ya sanya shi tashi zaune, ya ce "Zan kira ki" sai dai kan ya katse wayar ta ce "Sannu shashasha, ni zaka je ka aurowa wannan mummunar yarinyar?" Kan ya katse wayar ummi ta ji me mami ta ce.
"Mami meyafaru ne?"
"Uwarka da ubanka ne suka faru, in ce maka ga safiyya ka aura amma ka yi burus, ka je ka kwaso wannan yarinyar uwar mata ka yi yaya da ita? Ta girmeka ba sa'arka ba kawai saboda baka da hankali ko dan ba ka da mafaɗi?".
Raihan ya ce "Mami, dan Allah ki kwantar da hankalinki, duk fa ba abun ɗaga hankali bane ba. Ke ki ka gabatar mini da ita da kyawawan halayenta, na ji ina jin tausayinta. Ki ka kawo mini maganar aure na ga ita ta dace da ra'ayina, idan kowa ya ce ba zai aureta ba mummuna ce shikena sai ta rayu a haka, ba tausayawa babu kulawa?"
Rufe mini baki kan na daki bakin naka ya fashe, kai ne ɗan sarkin taimako, wani ya taimaketa mana a waje, ta girmeka ba sa'arka ba ce ba, ita ba ƴar uban kowa ba, kawai ka jajibo mana ita, to wallahi idan ma wannan matar ce ta zigaka dai-dai nake da ku. Kuma umarni nake ba ba shawara ba, ka je ka samu mahaifinku, ka janye wannan maganar da zancen auren nan da komai, dama ai ni na kawo maganar auren to safiyya na zaɓa maka, ita kuma ummin na san yadda zan yi da ita"
Cikin sauri ya ce "Dan Allah mami kar ki yi wa ummi komai, ni zaki yi wa ni na ce ina son ta, dan Allah kar ki sakata a damuwa, dan Allah mami ki yi haƙuri"
Galala ta saki baki tana kallon sa, "Au kar in sakata a damuwa? Har abun naka ya kai haka kenan? Dole na san abun yi"
Ta juya ta fita.
Ummi kuwa a hankali ta sauke wayar hannunta, fes abun da ta ji mami ya faɗa yake dawo mata, tabbas! Ta san a rina ta san zata fuskanci wannan ƙalubalen, tayi ta ƙoƙarin ankarar da raihan, amma bai gano ba, ta san yanayin mami ƴar ƙarya ce, mace ce mai iyayi da son nuna isa, ta san dama abu ne mai wuya mamin ta amince.
Dr. Ya yi sallama a ƙofar ɗakin ummi, ta amsa masa ya shiga, ya kalleta cikin farinciki da kulawa ya ce "Ummana, ke ashe ɗan manya ki ka samo mini siriki, ai ni gatse na yi wa saurayin naki, ganin yayi yarinta da yawa, na ce ya turo mini babansa ni na ma manta, kin ga sai ga su sun zo" Ummi ta yi shiru ta sunkuyar da kai, tamkar ta ce wa dr. Dan Allah ya warware maganar.
"Alhamdilillah, ina jin labarin Alhaji Tahir ashe babban mutum ne, mutumin kirki ne, kamar ba mai kuɗi ba, yayi mini bayanin komai, na ɗeba musu sati biyu, zan ne na yi bincike a kansu da yaron, in dai lafiya ƙalau nan da sati biyu za su kawo kuɗin auren, Ubangiji Allah ya kusa kawo miki ƙarshen zaman gidan nan, Allah ya baku zaman lafiya, ya kawar da fitina.
Dama wani jinkirin alkhairi ne, ki kwantar da hankalinki ummi, kar ki ga yaro ne ƙarami, ki saka a ranki Allah ne ya duba ki, ya kawo miki miji.
Ita nagarta ba a shekaru take ba ko tarin dukiya, babban fatan Allah ya tabbattar da alkhairi, dama ke mai biyayya ce, dan haka ki ƙara dan sa'anki ne kar ki ce ba zaki bi shi ba, Allah ya sanya muku dukkan alkhairi"
Ummi a ranta ta ce "Ji kawu da wata magana, har da nasiha kamar an ɗaura auren, akwai ƙura fa' sama-sama take jin sa, ya gama nasiharsa ya fice.
Farida kuwa har Abdul ta tambaya, ko ya san suwaye baƙin dr., Amma ya ce mata shi ma bai sani ba.
Bayanin da Alhaji ya yi wa raihan ne ya rage masa damuwar abubuwan da mami ta yi masa.
Ya ɗora da cewa "Mahaifiyarka ta fara tutsu, a kan ba ta san lamarin, idan har da gaske kana son yarinyar kana son tainakonta, ka tsaya a kan hakan, ka cigaba da addu'a, ni dai yarinyar ta yi mini, ban ga aibunta ba, wani muni wani waye hotonta da ka nuna mini ban gani ba, ban sani ba ko dan kana sonta ba ka ga munin bane ya sanya nima ban gani ba.
Ka je ka cigaba da shirye shiryen ka, a duba fili ɗaya ka gina abun ka yadda ka ke so, ba wata matsala in sha Allah"
Cikin girmamawa raihan ya ce "Na gode sosai Alhaji, Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana"
"Amin babban mutum"
Hajiya ta yi sallama hannunta ɗauke da tray, da kayan shayi a kai.
Tana ganin raihan ta ce "In fara guɗa tun yanzu ne, ko in ɗan jira?"
Murmushi raihan ya yi yana sosa ƙeya.
Hajiya ta zauna tare da faɗin "To kai raihan daga ganin ummi, har ce maka fa na yi wa ina yi wa yayanka kamu, kawai sai ka lallaɓa"
Ya ce "Wallaahi hajiya tausayi take bani a lokacin, na din ga damunta har muka fara sabawa. Hajiya ummi na da matuƙar kirki da tarbiyya"
Hajiya ta ce "Sosai kam, ina fatan Allah ya sanya alkhairi, na yi maka murna raihan, in dai mace ta gari ake nema, aka samu ummi to a gode Allah.
Sannan shekarun da ke tsakanin ku ba abun damuwa bane, shekaru lambobi ne kawai, ka riƙe ta ka kula da ita, ni dai ina son ta saboda Allah, tun tana zuwa gidan nan lokacin maryam tana nan, akwai ɗa'a da ladabi"
Raihan ya ce "Kuma wallahi ta iya girki sosai hajiya, ba ki ga yadda take bani abinci ba, ban taɓa cin abinci mai daɗin nata ba"
Alhaji ya dungure masa kai ya ce "Sannu ciki muka kawo duniya " suka yi dariya gaba ɗaya, gaba ɗaya sai ya manta da damuwar da yake ciki.
Ummi na zaune na tilawar litattafanta na addini, wayarta ta fara ringing, baƙuwar lamba ce, tayi zaton ko raihan ne, dan akwai canza lambobi.
Sai dai tana kai wayar kunneta, tayi niyyar sallama, ta gimtse sallamar jin uwar ashariyar da aka lailayo mata.
"Sannu asararriya ƴar wahala, baƙin kunurci, saboda asara da taɓewa kana da rashin kyakykyawar makoma, ummi ki rasa wa zaki ce zaki aura sai ƙanina ummi, na yi dana sanin saninki, saboda kin zama guzuma muni yayi miki katutu shi ne ki ka yi wa ƙanina asiri, saboda zalamar abun duniya, to wallahi ummi ki kuka da kanki, ko ki janye wannan maganar ta auren raihan, ko kuma in ƙasƙanta ki a idon duniya, in muzantaki kin san zan iya"
Jikin ummi yayi sanyi matuƙa, ta kasa magana, har maryam ta yi tijararta a waya ta gama, ta kashe wayar, kamar shashasha ummi ta bi wayar da kallo.
*Sweetheart, ki yi bacci cikin aminci da salama, zan so kiranki in ji muryar ki, amma na san wataƙila kin yi bacci, ki kula mini da kanki, ina son ki* message ɗin raihan ya shigo wayarta.
Ta miƙe ta tafi gaban mudubin ɗakinta, tana ƙarewa kanta kallo.
'to shi raihan ya aka yi baya ganin munina ne? A wajen ina munin nawa yake da yake ɓuya a idonsa baya gani?'.
Abu kamar wasa, mami ta sako raihan a gaba, ta daina amsa gaisuwar sa, ta daina shiga sabgarsa ta ce lallai sai ya je ya cewa Alhaji ya fasa auren nan.
Duk taurin kan ɗa, fushin uwa masifa ne, hakan ya sake jefa shi cikin damuwa da wasi-wasi, idan ta ce ya rabu da ummi, sai ya ji kamar ta ce ya raba jikinsa da rai.
Gefe Hajiya da Alhaji suna ta ƙarafafa masa gwiwa a kan auren ummi.
Ga lokacin kai kuɗi na cigaba da kusantowa, ga pressure office, ga ummi gaba ɗaya ta canza ta koma masa kamar wata baƙuwa, taƙi sakin jiki da shi, kamar ma ƙara nesanta kanta da shi take yi.
Yanayin aiki ya ƙara takura raihan, dan haka ko wurin aikin bai fiye samun damar binta ba, ga yawan barin ƙasar da yake yi.
Gefe guda maryam ta saka ummi a gaba da cin mutunci da zagi na cin zarafi kala-kala, ban da saƙonni da kuma barazana da take yi mata, ummi ta rasa in da za ta saka kanta, daga kuka sai addu'a, dan ta rasa yadda za ta yi da al'amarin gaba ɗaya.
Duk da mami ba ta shiga harkarsa, hakan ba ya hana shi zuwa in da take, da la'asar bayan ya dawo daga aiki, yayi niyyar zuwa yau ya je ya ga ummi, ya nufi sashin mami ya je ya tarar da maryam ta zo gidan.
Sanin halinta ya sanya ya tsuke fuska, dan ya san ba wai zuwan Allah da annabi ba ne ta yi shi haka.
"Mami barka da yamma" banza ta yi masa, daga baya kuma ta ce "Kar ka sake zuwa gaishe ni, muddin ba ka aiwatar da umarnin da na baka ba, bana buƙatar ganinka a sashina ma gaba ɗaya"
Maryam ta kalleshi ta ce "Wallaahi ka bayar da maza raihan, me aka yi aka yi ummi? Meye da ita meye abun burgewa a tare da ita? Sannan menene aibun Safiyya, amma na lura kamar ba a hayyacinka ka ke ba, wannan annakiyar baƙin zaka ɗaukko ka kawo mana mugun iri cikin family, wannan yarinyar da mujiya.....
"Dalla malama dakata!" Ya yi wa maryam tsawa.
"Islamiyyar da ki ka yi ba ta amfane ki da komai ba, da baki san daraja karramawar da Ubangiji ya yi wa ɗan Adam ba, ki tsaya iya matsayinki, idan mami tayi matsayinta ne, ke kuwa ko kusa ko a nesa ba ki da alaƙa da aurena, dan haka ki zuba ido idan zaki iya idan ba zaki iya ba ba zan juri cin zarafin matata ba, idan kin yi mata a baya ba ta da bakin ramawa, ni dai-dai nake da ke"
A tare suke shiga karanto "Innalillahi wa Innalillahi raji'un"
Mami ta ce "Au raihan har ta zama matarka ma ashe? Yanzu a gabana ka ke gaya wa ƴar uwarka haka saboda yarinyar da ba ka aureta ba ma? A wayance kana nuna mini babu gudu ba ja da baya kenan sai ka aureta" raihan ya yi shiru yana huci.
Maryam ta ce "Taɓɗijan, akwai ƙura mami, ita ma munafuka na kirata a waya ta ƙi magana, da yake ba ta da gaskiya, munafuka uwar son abun duniya, sumi-sumi da ita garin yayime-yayime na, na yayimo mana masifa"
Cewar ta kira ummi ya fi komai ɗaga masa hankali, ya san dole sai ta yi wa ummi rashin mutunci.
Juyawa yayi da sauri ya fice, ya tafi ɗakinsa ya sauya kaya, ya ɗau babur ɗin sa ya fita.
Gidansu ummi ya tafi, ya yi sa'a security yana nan, ya ce masa ya yi masa sallama da ummi.
Jin ana sallama da ita, ya sanya farida kallon ummi da take ta aiki a falo.
Farida ta kwaɓe baki, haka ma kausar, kausar ta ce "Ohh su mujiya an yi abun arziki, kowane mai tsautsayin ne? Na ga dai wancan tsohon ya ce ya fasa"
Farida ta ce "Oho dai, ni dai ayi a tattara a bar mini gida"
A gaggauce ummi ta gama, ta je ɗakinta ta shirya, ta fito harabar gidan, ya mayar da hankali a kan wayarsa yana dannawa.
Ƙamshin turaren wurinsa da take yi, ya sanya shi ɗagowa, ya zuba mata ido.
Duk ta yi wani iri, alamu sun bayyana ƙarara a cikin damuwa take.
"Sannu da zuwa" ta faɗa a hankali.
"Yauwwa, ya ki ke ya gidan?"
"Lafiya ƙalau" ta amsa tana murza yatsunta.
"Kwana biyu ayyuka sun yi mini yawa sosai ban samu na zo na ganki ba, zuciyata duk a takure"
Ita dai ummi ta yi masa gumm, taƙi magana.
"Yaya ummi" ya kirata da sunan da ya saba a baya.
Ta ɗago ta kalleshi, ya ce "Meyafaru ne? Duk kin canza mini, kamae an canza mini ke, meyafaru ne?"
Kamar ya soso mata in da yake yi mata ƙaiƙayi, ta ce "Dan Allah, ka taimaki rayuwata ka fasa auren nan raihan, wani ƙalubalen ne yake tinkaro ni, kamar ba zan iya ɗauka ba, Astagfirullah idan ka aureni kamar sabon babin ƙaddara zan buɗe, da alama kai kaɗai ka ke so na, gidanku ba zasu karɓe ni a matsayin sirika ba"
Ya jinjina kai ya ce "Eh, thank God tun da ina son ki ni, na san akwai ƙalubale, maryam na san ta kira ki, haka zalika na san mami kin ji abun da ta ce ranar, amma duk ba matsala ba ne ba. Salma ki canza rayuwarki ki koyi tsayawa a kan ra'ayinki da abun da ki ke so duk tsanani duk ƙalubale. Ke kin san ko mata huɗu na ce ina so za a bani a garin nan, amma na tsaya kai da fata na ce sai ke, ni meyasa zaki watsa mini ƙasa a ido? Ummi ba wasa nake yi ba da nake nanata miki ina son ki, ni kaina fa a cikin ƙalubalen nake, amma na ji zan jure saboda ke. Dan Allah ummi kema ki koyi tsayuwa a kan ra'ayinki ba ra'ayin wani ba, ita maryam ɗin waye ya hanata auren wanda take so, sai ke?
Dan Allah ki manta da wani ƙalubale mu tsara rayuwar mu, jarrabawa ba ta ƙarewa a rayuwar mumini.
Ai ki na so na ko? Tayi shiru tare da haɗe rai.
"Ba kya so na saboda na yi miki yarinta ko? Headmaster ki ke so?"
Ta ɗaga kai alamar eh.
"Ko gidan tsohon mijinki ki ke son komawa" yadda ya ga ta razana ne abun ya bashi mamaki.
Ya kawar da zancen ya ce "Ni a wani bugiren ki ka ajiye ni?"
Bai yi tsammanin za ta bashi amsa ba, ya ɗora da cewa "Ƙanin ki ko, wanda ki ka raina da aure?"
Zumɓura baki ta yi, tana juya ƙwayar idonta a hankali.
"Ummi wai meyake damunki ne? To mu yi hira ta yaya da ƙanwa kamar yadda muka saba"
Ta ce "To, ya gida ya office?" murmushin yayi ya ce "Ita ce hirar da ki ka fi so take yi miki daɗi kenan?"
Ta jinjina kai alamar eh.
"Office aiki ya yi yawa ba hutu"
"Ina su Yaya sagir? Kun shirya kuwa?"
Raihan ya ce "Mun shirya, amma ba ya kulani"
"To kai ka din ga kula shi mana ai kai ne ƙarami"
Ya ɗan shafi sajensa ya ce "Gayen nan ɗan wulaƙanci ne fiye da tunaninki, yanzu sai ya yarfa ni, har gara Salim wasu lokutan"
"Ai gani za su yi kamar idan suka sakar maka fuska zaka raina su, ka cigaba da jan su a jiki, kar ka nuna musu ƙyama saboda abun da suke yi watarana sai labari, ka gayyace su cikin ayyukan kamfaninku, ko ba ka sakar musu komai ba, ka ja su a jiki sosai".
Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Gaskiya ne, sai ma kin ga hajiya, ta fi bani tausayi wallahi, tana iya yin ta a kansu, amma kullum kamar ana tura su dawa, amma zan yi ƙoƙari in yi abun da ki ka ce in sha Allah"
"To Allah ya baka iko"
Ya amsa da amin, "Bari na je, zani wani wuri zo mu je ki karɓi saƙon ki"
Ya tashi ya yi gaba ta bi bayansa, a jikin babur ɗin sa suka tsaya, ya kalleta ya ce "Alhaji ya ce na zo na fara gini, a wace unguwar ki ke son mu zauna? Sannan wane irin gida ki ke so, flat ko mai bene?"
"Kowanne ka yi shikenan, Allah ya yassare"
"Salma kenan, haryanzu kina doubting idan ni zan aure ki, kuma ko zan iya riƙe ki, abun da muke shirin yi ba zunubi bane ba, hasali ma yana da asali a addinin musulunci, dan haka ki manta da batun al'ada da surutun mutane kin ji sweetheart"
Ta jinjina masa kai, tana wasa da hannun babur ɗin.
"Salma" ya kira sunanta a hankali, ta ɗaga ido ta kalle shi.
"Ina sonki sosai saboda Allah" tsigar jikinta ta tashi, ta kawar da idonta gefe.
"Ko sau ɗaya ki gaya mini wani abu mai daɗi da zai bani ƙwarin gwiwar cigaba da gwagwarmayar neman aurenki, dan nima ina fuskantar ƙalubale"
Jiki a sanyaye ta ce "Dan Allah raihan ka yi abun da zaka zo ka cutu daga baya, ka ƙara tunani a kai".
"Ni na riga na roƙi Allah a kan lamarin nan, kuma shi so baya bayar da ƙofar tunani, ba abu ne da yake bamu damar yin shawara ba, ki tausaya mini ummi" jikinta yayi sanyi, wani irin tausayin su ya kama ta.
"Ban san me zan ce ba, zan yi mana addu'a iya yi na, Allah ya zaɓa mana abun da ya fi alkhairi"
Ya ce "Amin ya haiyyu ya ƙaiyyum. Gobe in Allah ya kaimu ki yi mini girki dan Allah, zan biyo ta wurinku na ci"
"Me ka ke so" tayi maganar tana murmushi.
"Ke nake so"
Ta yamutsa fuska ta ce "Ina nufin me zaka ci?"
Yayi dariya ya ce "Abinci mana, ko me ki ka dafa zan ci da yardar Allah" yayi maganar yana miƙa mata ledar hannunsa ya ce "Ki koma gida ki huta, duk da ban gama ganinki ba, zamu yi waya, dan Allah kar ki kashe waya kin ji baby"
Ta karɓi ledar ta juya tana murmushi.
Sabuwar waya dalleliya raihan ya gwangwaje ummi da ita, irin wayar da ba ta taɓa zaton zata riƙe irinta ba, bakinta ya ƙi rufuwa sai da ta kira shi ta yi tayi masa godiya, ya ce shi ba godiya yake so ba, kawai ta ce masa tana son sa shi zai sa ya ji daɗi ya tabbatar da ta ji daɗin kyautar da yayi mata.
Aikuwa ta yi gumm, ta kasa magana.
Da kuɗinta tayi cefane, washegari da safe ta sheƙa masa girki, bai kira ta a waya ba, sai fita tayi ta ganshi a waje yana jiranta.
Suna tafe yana yi mata normal hira, tare da nuna mata yadda za ta yi amfani da wayar da ya saya mata.
A mota ya ci abinci, yana ci yana yi mata hira, ta buɗe ruwa ta bashi, ta duba jakarta ta ɗaukko tissue, ta warwro masa ta bashi ya goge hannu.
Yayi murmushi ya ce "Ka ga mace ta gari, ta fara aikinta tun yanzu".
Ta haɗa kan kwanukan ta ta ce masa "Sai anjima, Allah ya kiyaye"
"Amin ya rabb, yakamata mu koma ayi siyayya, mayukan nan kamar sun karɓe ki, na ga kina ta glowing"
Da sauri ta ce "Fari na yi?"
"A'a kyau ki ka ƙara, ban sani ba ko idona ne"
"Kar ka saka mu makara, sai anjima" ta fice daga motar, ya zuba mata ido, har ta shige shagonsu, sannan ya ja motar ya tafi.
Duk wata hanya da mami za ta bi, ta rusa maganar auren raihan, abu ya gagara ta kaɗa ta raya, amma raihan ya dage, ya samu goyon baya ɗari.
Dr. Ya sanar da su kawu Ilyasu, zai karɓi kuɗin auren ummi, dan haka mutum biyu daga cikin su su zo ranar juma'a.
Hatta kayan soye-soye da zai karɓi baƙi, daga waje ya yi order abun sa, dan sai saura ƴan kwanaki, sannan ya gaya wa farida.
Farida ko a jikinta, tana ganinsa yana ta shige da ficensa shikaɗai, ya shirya komai.
Kafin sallar juma'a, su kawu Ilyasu suka zo gidan, bayan sallar juma'a, su Alhaji Tahir suka zo.
Bayan gama tattaunawar da duk yakamata, dr. Ya gabatar da su kawu Ilyasu ga su Alhaji Tahir, tare da gaya musu matakin karatun ummi, tare da tabattar musu da binciken da yayi a kan Raihan, bai samu wata matsala ba.
Alhaji Tahir ya sake gabatar da kansa ga su kawu Ilyasu.
Sannan ya kalli dr. Ya ce "Ban sani ba ko kun yanke kuɗin aurenta da sadakin?"
Dr. Ya ce "A'a, duk abun da Allah ya sa ku ka bayar, zamu karɓa fatanmu ubangiji Allah ya sanya alkhairi"
Alhaji Tahir ya jinjina kai, sannan ciro kuɗi a aljihunsa ya ajiye kuɗi dami guda a tsakiyar falon, ya ce "Ga su nan, dubu ɗari biyar ne, mun saka watanni huɗu idan Allah ya sa zamu gani, amma idan kuna ganin mun saka da yawa kuna iya ragewa".
Dr. Yayi murmushi ya ce
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 32 Chapter of 54