amfani da su, duk zan yi miki har makaranta zan mayar da ke da yardar Allah, ke dai ki nutsu ki manta da komai, ban yi miki alƙawarin gidana babu ƙalubale ba, amma na san bai kai na ƙauye ba. Ki dage ki yi amfani da shawararin da ta baki kin ji ummana"
Ta ce "To na gode sosai"
Ya shafa kanta ya ce "Yauwwa Allah yayi miki albarka"
Can gagarawa kuwa, Hashim ya sha zagi da cin mutunci da wulaƙanci a wurin Iya, ba Iya kawai ba, har da mahaifinsa suka ƙare masa tas, a kan ya kasa rufa wa ɗan uwansa asiri, da har ya iya sanar da kawu yahaya halin da ake ciki.
Shi dai yayi shiru bai ce komai ba, amma har cikin ransa yake jin wannan abun da yayi shine mafita ga rayuwar ummi, kuma hakan da yayi bai saɓawa shari'a ba.
Sirikan iya wasu sun jiye wa ummi rabata da gidan nan, saboda azaba da masifar iya ga ummi.
Iya kuwa ta ji baƙin ciki da takaicin ɗauke ummi da yahaya yayi, dan yanzu ta san abu ne mawuyaci idan asirinsu da take ta ƙoƙarin rufuwa bai tonu ba.
Shi kansa Idris tun da aka tafi da ummi, bai dawo gidan ba, dan ya san zai sha faɗa a wurin Iya da iyayensa, shi kuma har ga Allah, ya tsani yarinyar nan hakan da yayi shine dai-dai.
Horn yayi, wani matashin yaro, da zai ɗan girmi ummi ya zo ya buɗe gate ɗin, ummi ta san yaron amma da daɗewa dan wasu lokutan ya kan zo da shi gagarawa.
Ya shiga da motar harabar gidan, ba laifi harabar mai ɗan girma ce, dan aƙalla za a yi parking ɗin motoci uku a ciki.
Wasu ƴan mata ne ƙanana su biyu farare tas da su, an yi musu kitson ƙari, ɗaya tafi ɗaya girma, suka nufo motar suna faɗin oyoyo Abba.
Ya buɗe motar ya fita ya rungumo su, sannan ya juya ya buɗe wa ummi motar ta fito.
Duk da duhun magariba ya fara yi, hasken fitilar da take harabar gidan, ta basu damar tsayawa suna ƙarewa ummi kallo.
Ya buɗe bayan motarsa ya cewa yaran su ɗaukko wa ummi kayanta.
Ba laifi gidan mai kyau da shi, ummi sai kallon gidan take yi.
A falo ya kalli yaran ya ce "Intee ina maama ne?".
"Ta fita da muka dawo daga tahfee, bamu tarar da ita ba"
Ya ce "Ok, ga sister ɗinku nan, sunan ta Salma, amma ummi ake ce mata, you can call her yaya ummi, ku nuna mata toilet ɗin ku ta yi alwala".
Cikin ƙyama intee ta bi ummi da kallo, sannan ta yi gaba, ummi ta bita a baya.
Ummi ta yi salla ta idar, tana ta kallon ɗakin, da gani na ƴan matan ne, kowacce da gadonta, ga ƙatuwar wardrobe, ga shoe rack ɗin su ɗauke da takalmansu na makaranta da na fita, duka-duka babbar da ake kira da intee ba ta fi shekara goma ba, ɗayar kuma bakwai.
Ummi ta fito daga ɗakin, ta koma falo ta zauna a ƙasa.
Ya shiga kitchen da kansa, ya haɗowa ummi tea mai kauri, ya saka intee ta dafawa ummi noodles ta ɗora mata ƙwai uku a kai.
Duk da yanayi na rashin lafiya, ummi ta ɗan ci, dan bata taɓa cin indomie ba, duk da ta na burgeta.
Yaran suka kunna tv suna kallo tare da mahaifinsu, ummi ma kallon take yi, suna ta yi wa babansu surutu, yana ta ƙoƙarin saka ummi a hirar, ta dai yi shiru ba ta cewa komai.
Bayan magariba sosai sannan wata mata tayi sallama, ita da wata matashiyar budurwa.
Ya amsa ya ɗaga kai yana kallonsu, yaran kuma duk suka tashi suka nufeta.
Cikin iyayi ta ce "Abba ka dawo kenan?" Tayi maganar tana zama da tsohon cikinta.
"Eh" ya amsa mata a taƙaice.
Ummi ta kalleta ta ce "Ina wuni?"
Ta bi ummi da kallo, ta ce "wannan fa?"
Ya ce "Ki fara amsa mata gaisuwar mana"
"Lafiya ƙalau" ta amsa a ɗan yatsune.
Ya kalli su inteesar ya ce "Abdul, intee, shalele ku bi anty rahama maza, ummi ki bisu ki samu ki huta, a haɗa mata ruwa tayi wanka"
"Wai ban gane ba, ita wannan ɗin wacece?"
Ya ce "Kya tsaya na yi miki bayani ai, yanzu dai daga ina ki ke?".
"Gidan gana na je, wata ƴar aikin nake so ta samo mini, saboda su intee wahala tana yi mini yawa".
"Amma ba kwanan nan ki ka rabu da wata ba, kina ta surutun tayi miki laifuka ba, shi ne zaki sake rakito wata?".
"To Abba yaya zan yi? Ga tsohon ciki, da na haihu zan koma school, ga ayyukan gida ba zan iya ba wallahi. Ka yi haƙuri kawai ni dai".
"Shikenan, amma kar ki kuskura ki zo kina ce mini an yi miki kaza an yi miki kaza"
"Na ji wacece waccan yarinyar da ka haɗa mini da yara?"
"Dama na san ba saninta zaki yi ba, tun da ba zuwa ki ke yi ba, Ƴar wurin marigayi ce bashir?"
"To me zata yi a nan ɗin?"
Ya gyara zamansa ya ce "Eh, na ɗaukko riƙonta ne na dawo da shi hannuna, a nan za ta zauna da mu"
A fusace ta ce "Amma yaya zaka yi mini haka, ya zaka ɗaukko yarinya ban sani ba ba shawarata kawai ka ce in riƙe? Saboda me? Abba meye amfanin kawo bare ka haɗa a cikin iyalinka".
"Ƴar ɗan uwan nawa ce bare kuma?"
"Bare ce mana, ki ka haifeta? Naga ai ba cikinku ɗaya da ubanta ba, gaskiya ban yarda ba, ka mayar da ita in da ta fito wallahi ba zan iya ba, dama dinginku sun tsane ni, shi ne aka haɗoka da ita ta zo ta saka mini ido, wallahi ba zan riƙe ba".
Ya dubeta ya ce"Well, ummi bare ce, amma ko ba komai ƴa ce a wurina, idan har ummi za ta bar gidan nan, ki tabattar rahama ma sai ta bar mini gida, dan bani da wata alaƙa da ita, dan ina aurenki ba dole ne na riƙe ki na riƙe ƙanwarki ba, tun da baki san mutunci ba, a gobe in Allah ya kaimu rahama ta bar mini gida na gaya miki".
"Yahaya, ni ka ke gayawa ƙanwata ta bar gidan nan?"
"Tun da ki ka iya kallona ki ka ce, ƴa ta ta bar gidan nan, to rahama ma sai ta bar gidan nan tun da ko ban riƙeta ba, bani da laifi a wurin Allah, ummi kuwa dole ne riƙonta a kaina" ya tashi fuuu ya nufi ɗakin su intisar.
Ummi na zaune a ƙasa rungume da kayanta, tana kallonsu, suna zaune a kan gadonsu, sun sakata a gaba suna ta dariya, saboda yanayin ƙauyanci da yake tare da ita da kuma baƙar fatarta.
Sallamar babansu ce ta sanya su tashi a razane, suka daina dariyar.
"Ina ruwan wankan da na ce a bata?"
Intee ta ce "Anty rahama ba ta haɗa ba"
"Wannan ban isa da ita ba, ku na isa da ku, ki haɗa mata ruwa ki nuna mata yadda ake amfani da toilet ɗin"
Ta jinjina kai, ya juya ya fita dan tafiya masallaci sallar isha'i.
Cikin ƙyama take nunawa ummi banɗakin, ƴar ƙarama da ita, amma ta iya wulaƙanci.
Ta cewa ummi kar ta kuskura ta taɓa musu sosunan wankansu, ta je ta ɗaukkowa ummi sabulun wanki, ta bata wai tayi wankan da shi, ta kuma nuna mata iya in da zata tsaya, tayi wakan.
Ummi ta jinjina mata kai, sai dai ta tsaya tana kallon banɗakin yadda ya ƙawatu.
"Rahama kina ina, wai ni yahaya ya ɗaukkowa ƴa a ƙauye na riƙe, wai idan ba zan riƙe ba kema ki bar masa gida"
Rahama ta kalleta ta ce "In bar gidan nan wai? To me ki ka ce masa".
"Wallahi ba zan riƙe ba, kuma ba in da zaki je, shi ya isa ma, wallahi yayi kaɗan, zai gane kuskurensa".
Rahama ta ce "Anty ke da ki ke neman ƴar aiki? Gashi kin samu a ɓagas, ba dai gida ne ba, ta zauna mana iya ka idan bala'i ya isheta ta gaji ta bar gidan nan, ki rabu da shi, sai dai karki saurara mata wallahi, idan ma sa ido aka turo ta ki ci ubanta, ki rabu da shi kawai"
Ta ce "Kuma fa haka ne rahama, haka za ayi, ɗakin mai aiki kawai zata koma, na samu baiwa zata ci ubanta kuwa, sai ta koma in da ta fito dan ba zan zauna da ita ba wallahi. Nifa gaba ɗaya ban yarda da yarinyar nan ba, lokacin da muka je gaisuwar babanta, ina jin kakarta na ta ce mata kamar mayya, ke kin ganta baƙa ƙirin ƙwayar idonta kamar mage".
Raham ta ce "Idan ma mayyar ce ta ci kanta, dan wallahi mun fi ƙarfinta, to ma ina uwarta da za a kawo miki ita? Gaskiya baban Abdul yana da matsala wallahi".
"Oho masa, sai ta bar mini gida dai wallahi, amma na san yadda zan yi da shi".
Ayshercool
08081012143
*CUTARWA!*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
BRIGHT PENS
(FREE BATCH)
(Ku garzaya YouTube channel ɗina na COOL HAUSA NOVELS, KU YI SUBSCRIBING, AN FARA ƊORA LITTAFIN ƘANWAR MAZA NA SAURARO)
P14
Har kawu yahaya ya dawo daga sallar isha'i, suna tattaunawa ita da rahama, suka gama ƙulle-ƙullensu, sannan farida ta baro ɗakin rahama.
Yahaya ya tafi ɗakin yaransa, in da suke ta tsalle-tsalle a ɗakin, ummi kuma na ta gyangyaɗi a zaune a ƙasa.
Suna ganinsa suka tsagaita da tsallen da suke yi, ya kalli babbar ya ce "Ke intee, ku yi squating da kausar a kan gadonki, yaya ummi ta kwana a kan ɗaya gadon.
Turus suka yi suna bin mahaifinsu da kallo, cikin tsawa ya ce "Ba ku ji me na ce ba ne?".
Intee ta ce "To" ya kalli ummi da ta buɗe ido ya ce "Ummana, ga gado nan tashi ki kwanta kin ji"
Ummi ta ce "To na gode"
Ta tashi ta hau gadon nan ta kwanta, wani irin laushi, ga ƙamshin room freshner mai daɗi kayan shimfiɗar suke yi, tun kan ya bar ɗakin bacci ya fara kwasarta.
Inteesar ta kwashe wa da kausar da dariya ta ce "Shikenan bedsheet ɗin ki zai kwashi baƙi, kamar an ciro a buhun gawayi".
Kwaɓe fuska kausar tayi za ta yi kuka, intee ta cigaba da dariya, ganin kausar ta fara kuka ya sanyata cewa "Bari idan abba ya daɗe da tafiya, sai mu tashe ta, ta saukko".
Haka kuwa aka yi, intee har da leƙawa, ta tabattar da ya tafi, sannan ta dawo, ta hau dukan ummi a ƙafa.
Ummi ta buɗe idonta tana kallonsu.
"Saukko mana daga kan gado, kausar zata kwanta"
Kasa magana tayi ta cigaba da bin su da kallo.
"Ki saukko zata kwanta, dan ba zata kwana a gadona ta matseni ba" babu musu ummi ta saukko, ta koma ƙasa ta sake tada kai da kayanta.
Kausar ta watso kayan kan gadon nata, har bedsheet ɗin da komai, wai saboda ummi ta kwanta a kai.
Wajen ƙarfe ɗaya na dare, ummi ta ji ana haurinta da ƙafa, ta tashi firgigit, dan ji tayi kamar a gidan idris za ta buɗe ido ta ganta, dan shi yake yi mata irin wannan wulaƙancin, na haurinta da ƙafa.
"Tashi malama, in nuna miki in da zaki din ga kwana, dan ba zaki kwanar mini a cikin yara ba, ban san irinki ba"
Kai ka ce sokuwa, haka ta tashi, ta ɗaukko jakar kayanta, ta bi bayan farida.
Ɗakin ƴar aiki da yake farkon falon, ta nuna mata ta ce ta shiga a nan zata kwana. Ba ta damu da a yaya ɗakin yake ba, ta je ta kwanta, saboda yanayin jikinta ga rashin lafiya ga gajiyar tafiya, dan haka duk a gajiye take.
Washegari da safe, kowa ya fito falo, rahama ce ta haɗa breakfast, yaran duk sun shirya cikin uniform na makarantar boko.
Abba ya fito ya kallesu ɗaya bayan ɗaya babu ummi, rahama ta gaishe shi ya amsa sama-sama.
Ya kalli farida ya ce "Kawo mini abincina nan"
Haushi ne ya kama ta, yana ganin yadda take fama da ciki, amma ya sakata aiki, bayan ta kai masa kayan abincin ɗaki.
Bayan ta tafi ɗaukkowa, ya kalli intee ya ce "Kirawo mini ummana" intee tayi saroro tana kallon shi.
Ya ce "Ummi nake nufi"
Tunawa tayi da safen nan, ta ji maama da anty rahama suna zancen a ɗakin mai aiki ta kwana, har take gaya musu abun da suka yi mata jiya da daddare suka din ga dariya.
A zaune ta tarar da ummi, ita ummi ɗakin ba ƙaramin kyau yayi mata ba.
Duk da ba wani abu a ciki na burgewa, amma ɗakin ya yi mata kyau.
"Ki zo in ji abba" yarinyar ta faɗa cikin fitsara.
Ummi ta tashi ta bi bayan ta, sai dai farida na ganin ummi kamar taga kashi, ta haɗe rai.
Daga in da suka fito falon, ya fuskanci a in da ummin ta kwana.
Ummi ta durƙusa ƙasa ta ce "Abba ina kwana?"
"Lafiya ƙalau ummana, ya jikin naki, ina fatan baki kwana da zazzaɓin ba?"
Ta ce "Eh da sauƙi".
Ya ce "Masha Allah, baki gaisa da maman naki ba, gata nan sunan ta farida, yara na kiranta maama, kema zaki iya kiranta da hakan, ga ƙanwarta nan anty rahama, ga Abdurrahman Abdul, ga inteesar, ga kausar, sai kuma muna jiran unborn baby da maama zata haifa mana. Abdul, intee, kausar kamar yadda na gaya muku jiya, yayarku ce, duk da kai Abdul ka girmeta, amma ku girmamata, ku zauna lafiya. Ummina duk abun da ki ke buƙata, ki sanar da ni, ko maama gidanku ne ki yi zamanki ki kwantar da hankalinki".
Cikin ladabi ummi ta ce "To Abba" ta kalli farida ta ce "Ina kwana" banza tayi da ummi kamar ba ta ji abun da ta ce ba, ba ta damu ba ta kalli rahama ta ce "Anty ina kwana"
Ba yabo ba fallasa rahama ta amsa mata, abun da farida tayi, ba ƙaramin ƙular da shi tayi ba, bai ce komai ba da kansa ya haɗa wa ummi abun breakfast a abincinsa, ya bata.
Wanda hakan ba ƙaramin tunzura farida yayi ba, cikin ƙulewa take tuna masa yara zasu makara a makaranta, amma ya kada baki ya ce "Ƴaƴanki ne ai ki tarar musu abun hawa ya kai su, ƴa ta zan kai asibiti"
Tsit suka yi suna kallonsa, aka rasa mai magana, ya jira ummi ta gama, ya sakata a gaba suka fice.
Sai da ta kusa kuka, abun ka da mai ciki dama ga zuciya a kusa.
"Rahama ki na kallo daga kawo yarinyar nan, ni zai yi wa wannan wulaƙancin, ya fifita bare a kan yaransa".
"Kema anty farida you over react, a gabansa ta gaishe ki, ki ka shareta, ai kisan mummuƙe zaki yi mata".
"Yanzu kwana ɗaya tal a gidan nan ta fara haɗa ni da shi? To wallahi da sake ba zai yiwu ba"
Ran farida yayi matuƙar ɓaci, ta din ga cin alwashi kala-kala na mugunta a kan ummi.
Ya tafi da ita wurin aikinsa, ya kulleta a office ɗin sa, ya je ya gabatar da lectures ɗin da zai yi, wajen ƙarfe sha biyu na rana, ya tafi da ummi kasuwa.
Ya sai heater da nurse ɗin nan ta ce ya saya, ya sai mata phants dozen ɗaya, ya saya mata soso sabulu, brush, manyan jakar omo. Ya saya mata sababbin kaya wasu ready made wasu kuma sai an ɗinka, kasancewar yana da yara mata, kuma shi yake sayen komai na gidan sa, dan haka duk wani abu na ɗawainiyar yara mata ya sani, hatta ɗan kunne sai da ya saiwa ummi, under wear vest duk ya saya mata.
Ya ce suje mota ta zauna ta huta, ya ƙarasa sayayyar, wani irin farinciki ummi take ji, saboda kayan nan da aka saya mata, gani take kamar a mafarki, wai duk wannan kayan nata ne, har da su ɗan kunne da ribbon, ga takalmi mai kyau, ta din ga kwarara masa addu'a a cikin zuciyarta.
Wurin masu sayar da kayan ƙamshi yaje, domin haɗa magungunan da aka gaya masa a yi wa ummi.
Sai dai wasu abubuwan duk ya manta yadda aka gaya masa, mai kayan ya tambaye shi, mai zai yi da su, yake gaya masa ai maganin sanyi za a haɗa.
Kasancewar mutumin sana'arsa ce, sai ya haɗa masa komai da yadda ake amfani shi.
(Previous page, na bayar da magungunan in breif, wasu sun biyo ni suna so, yanzu zan rubuta full yadda ake amfani da su)
_Kanumfari
_Tafarnuwa ƴar kaɗan ba mai yawa ba, saboda idan tafarnuwa ta huda jikin mace, tana sanya warin baki, na jiki har da na al'aura ma, sai dai maganin sanyi ce sosai.
_Tumeric (yellown kur-kur)
_Namijin goro
_Citta mai yatsu
_Lemon tsami
Kowanne za a zuba shi in a moderate amount, lemon tsami babba guda ɗaya mai ruwa ya isa, namijin goron ma za a iya daddatsa shi, yana da ɗaci sosai, tafarnuwa one clove, sai citta mai yatsu madaidaiciya guda ɗaya, sai 1 table spoon of tumeric, sai a zuba ruwa kamar 2cups, a dafa su a din ga sha, za a iya zuba zuma, saboda yana da ɗaci, za kuma a iya haɗe su a mazubi guda, a jiƙa su, su jiƙu sosai a din ga tsiyaya ana sha.
Idan wannan bai samu ba, ana iya jiƙa kanumfari, a din ga sha yana maganin sanyi sosai, amma sai an juri sha.
Sai kuma ana samun saiwar zogale, a ɗaurayeta da ɗan gishiri, a tafasa ta da jar kanwa, a din ga sha, salam yake babu ɗaci, amma yana maganin sanyi sosai.
Sai kuma kama ruwa da ruwan magarya da bagaruwa ba da yawa ba kaɗan a haɗa su a tafasa, ana kama ruwa da shi, ganyen magarya yana gyara jikin mace, mussaman bayan gama al'ada, ayi shaving a din ga kama ruwa da shi, kuma a din ga ɗiga farin miski a kan phant, ba a jiki ba, yana kawar da ƙarni ko wani wari mara daɗi, but mark you ba kowane wari ne yake fita a gaban mace na infection ba, akwai bacterias ɗin da suke wurin wanda ba masu cutarwa ba ne ba, suna haifar da wannan ƙarnin wasu lokutan.
Galibi na infection ko na ƙazanta ya fita daban mussman idan ya haɗa da ƙaiƙayi ko ƙuraje shi ne na infection.
Shi ma wannan warin, ana iya amfani da apple cider vinegar, ruwa kal da hausa, ana zuba tablespoon ɗin sa biyu, a ruwa cikin kofin shan shayi a din ga sha, yana magance warin gaba.
Sai dai dole a kula da abincin da ake ci, domin cin abinci mai ƙarni, ko wari kamar kifi, albasa ko tafarnuwa suna da tasiri a gumin mu da sauran fluids da muke fitarwa a jikinmu.
Kawu yahaya duk ya haɗowa ummi abubuwan da suka kamata, suna tafe yana sake yi mata bayanin yadda zata yi amfani da su.
Sai azahar suka koma gida, sai dai matar gidan bata nan, da kansa ya bi ummi ɗakin masu aikin, ya dudduba abun da babu ya ce zai sayo mata.
Tamkar yar da ya haifa a cikinsa haka yake jin ummi,kuma haka yake burin ta samu lafiya daga wannan ciwon, dan ya san illarsa da hatsarinsa, dan ya san halinsu maza bakomai suke iya jurewa su kawar wa da kai ba.
Ya nuna mata yadda za ta din ga amfani da heater, da sabon flask ɗin ruwan zafi.
Da kansa ya tafasa magungunan, ya zuba mata a jarka, na kama ruwan ya zuba mata a cikin flask ɗin shayi, ya ɗaukko tsintsiya ya taimaka mata wurin gyara ɗakin saboda an kwana biyu ba a gyara shi ba.
Ya je ɗakinsa ya duba bedsheet ɗin da shi ya saya da kuɗinsa, har da bargo ya kawowa ummi.
Ya bata babban gwangwanin turare a cikin nasa ya ce ta din ga fesawa.
Kallonsa kawai ummi take yi, cikin jin daɗi da annashuwa, yadda ya zage yake ta ɗawainiya da ita, daga jiya zuwa yau, idan ta ce ya bari tayi da kanta, sai ya ce mata ai bata da lafiya, kuma cikin barkwanci ya ce mata albarkar ummansa yake nema.
Haka nan ummi ta din ga murmushi tana yi masa godiya.
Ya ce "Yauwwa ummina, Allah yayi miki albarka, saura makaranta ita ma in sha Allah sati mai kamawa, zaki koma makaranta ki manta da duk abu da ya faru, iyaka dai kar ki sake ki gaya wa wani kin taɓa aure kin ji ko?"
Ta jinjina masa kai ya ce "Good, yi wanka ki yi salla, a cikin kayan nan akwai gurasa ki ci kiyi kwanciyarki ki huta"
Murmushin kawai da ya gani a fuskar ummi, ya sanya shi cikin farinciki, kullum yaje ƙauye sai dai ya tarar da ita cikin kuka, sai kuma Murmushin yaƙe.
Hatta yadda zata din ga amfani da banɗaki, sai da ya nuna mata komai.
Fitowa yayi daga ɗakinta, a zuciyarsa yana tawasalli da farincikin da ya saka marainiya yana addu'a Allah ya biya masa buƙatunsa na alkhairi.
Ba yau farida ta fara fita yawonta ba, tun yana faɗa har ya gaji ya daina yi.
Ummi kuwa tun daga kama ruwan da tayi, ta ji daɗin jikinta, ta tsiyayi maganinta ta sha bayan ta ci gurasar nan, ta ɗauki sabon phanta ta canza.
Wani irin daɗi take ji da nishaɗi, ta sake bubbuɗe kayan da ya saya mata tana jin daɗin hakan.
Ko da wasa ba ta yi gangancin fitowa daga ɗakin nan ba, dan ta fuskanci ƴan gidan ba ƙaunar ganinta suke yi ba.
Ana kiran sallar la'asar ta yi salla, ta cigaba da zamanta a ɗakin.
Kamar an watso su, taga farida da rahama a ɗakin, hakan ya sanya ta tashi a razane.
Farida ta ce "Tashi munafuka, ai ba zama ki ka zo yi ba" a zabure ummi ta tashi tana rarraba ido.
"Ba dai kawo ki aka yi leƙen asiri da saka mini ido ba, zaki ci ubanki sai kin bar mini gida da ƙafarki" idonta ya sauka a kan ƙatuwar ghana must go sabuwa fil.
Ta ce "Rahama janyo mini jakar nan ki zazzageta, wato zuwa yayi ya kashe mata kuɗi, wallahi ba zai yiwu ba ya daidaita da ƴaƴana, kar ta san kar ai".
Rahama ta janyo jaka, suka zazzageta, farida har da ashar, farida ta saka farida ta tsitstsince mata kayan, phants ɗin ma duk ta kwashe ta bar mata uku, Allah ya taimaketa, tana da sauran wanda ta zo da su, da na'ima ta saya mata.
Cikin ikon Allah, Allah ya taimaketa basu lura da ƙullin kayan maganin da ke bayan katifar ɗakin ba, heater da flask ɗin kuma suna cikin banɗaki.
Hatta omo da sabulun da ya saya mata, sai da suka kwashe ta bar mata ɗai ɗai.
Sannan ta sake dubanta a wulaƙance ta ce "Ki buɗe kunnenki da kyau ki saurareni, nan gidana ne, abun da na dama shi ake sha, shima kwana biyu na sarara masa ne, amma tun da haka ya zaɓa zan yi maganinku duka. Ki saka a ranki ke ƴar aiki ce kawai a gidan nan. Kullum da yamma idan yara suka taso daga makaranta, zaki wanke musu uniform ki goge musu shi tas, wanke-wanke da duk wani aiki a gidan nan ke zaki din ga yin sa, idan ki ga dama ki gaya masa babu abun da zai iya yi a kai, bari in gaya miki ƙiri-ƙiri idan ki ka sake kiransa da Abba sai kin bar gidan nan, dan bai haife ki ba.
Kuma wanki ba na yara kawai ba, kaya ko na waye sai kin wanke a gidan nan, tashi mu je ma ki fara aikin ki daga yanzu. mummunar banza kawai".
Rahama ta kwashe da dariya ta ce "Ni wallahi fuskarta ma dariya take bani, wannan baƙi kamar a dangwala".
"Rabu da ita tashi ki wuce" ummi kaf maganganun su babu wanda ya ɓata wa ummi rai, dan ba yanzu aka fara yi mata ba, ƙwace mata kaya yafi komai ɓata rai.
Sai dai wata zuciyar ta ce da kin san zaki samu ne?.
Saboda tsabar mugunta akwai injin wanki a gidan, kuma akwai mai guga, amma farida ta tula wa ummi kayan makarantar su Abdul, na boko da islamiyyar su, kusan kowanne nasa set uku, daga na makarantar boko har na islamiyya.
Ummi ko a jikinta, ta durƙusa ta fara wankin kayan nan.
Tas ummi ta wanke su, kasancewar ta riga ta saba da wahala tun a gaban Iya.
Bayan ta gama cike da mugunta, rahama ta ja ta kitchen, ta sakata sassauke kwanukan da sun fi wata shida ba a saukko su an yi amfani da su ba, ta ce ummi ta wanke.
Babu ƙyuya ko ƙosawa ummi ta wanke su.
Duk yadda suka wahalar da ummi a yammacin nan har zuwa bayan isha'i, ko da wasa bata nuna musu gazawarta ba.
Kwanaki uku da zuwanta gidan, rashin mutunci da kyara, haka babar su Abdul suke
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 54