yaro yayi shi, ko da kuwa ba ya so, mussaman ma na addini.
Duk da a hakan wasu lokutan ba ta tsira ba, ba ya hana azo har sashin su a ɗauke ta, idan mariya zata hana, iya tayi ta masifa.
***
Yau Mariya ta yi yamma wurin girki, tana ta aiki a tsakar gida, iya tana zaune a kan kujera ƴar tsuguno, ta kasa ta tsare, sai waƙe-waƙenta take yi na mutanen da, waƙoƙin daɓe wasu kamar na batsa,wasu kamar habaici.
Wata mata ce tayi sallama, suka amsa baki ɗaya, matar ta gaida iya, Iya ta amsa mata cikin sakin fuska har da yi wa ɗan matar wasa.
Mariya ta ce "Mai koko ke ce da yammacin nan? Bari na baki abun zama"
Mai koko ta ce "Wallahi kuwa, haja na kawo miki"
Mariya ta shimfiɗa mata tabarma ta ce "Haja kuma, to Allah ya sa ba ta fi ƙarfin talaka irin mu ba".
Mai koko ta kwance kaya, kayan yari da sarƙa ne da mayafai a taƙaice dai kayan koli ne.
Mariya ta yi ta ɗaɗɗagawa, kayan sun yi mata kyau sosai, ta san idan ta ɗauka baban ummi ba zai ce komai ba, amma ba ta son takura shi, dan haka ta ce "Mai koko muna da ɗan kunne, maɗaurin gashi na so saya wa ummi, sai dai wannan sun yi ƙanana ba zai riƙe gashinta ba, sai dai idan muna buƙata zan yi miki magana da yardar Allah"
Ita ta ce "Ke ma dai mai koko, ke da ki ke neman arziki, ina ke ina kawo wa wannan kaya, ba su da komai sai tsiya da babu, ki kai sashin Sagir, ko gidan iliya, wannan ai da kin taɓa su babu".
"Na ga alama kam, ban taɓa kawo kaya mariya ta saya ba, kullum sai aukin idan tana buƙata ta aiko ta saya".
"Kema tun da aka yi ɗaya biyu, ai ba kya bari ayi uku ba, da dai hidimar ƴar ta ce, nan tafi kauri, ta kanainaye mini ɗa ta hana shi arziki"
Tuni mariya ta tashi, ta koma kan aikinta.
Mai koko ta ɗaure kayanta ta ce "Aikuwa iya ki dage da nema masa magani, ƴan uwansa duk suna da rufin asiri ban da shi, sa anjima"
"Yawwa ki gaida gida"
Ba ta sake bi ta kansu ba, kamar kullum yau da wuri ummi tayi bacci, bayan mariya ta kammala girki, ta ɗebi gawayi, ta goge wa ummi uniform ɗin ta, ta gama komai, tana jiran dawowar baban ummi.
Kamar mai kiran kurma, Iya ta ƙwala mata kira, ta fito da sauri a ɗan razane ta ce "Iya gani"
"Maza yafo mayafinki, ƴaron wurin iliyasu ne, ƙaramin ya haɗiye ƙaya, ku ɗauki yaron ki raka Sa'adatu ku je gidan sarkin suu, ya bashi magani"
Ɗan jimmm mariya tayi, so take ta huta, tun safe take aiki a gidan kamar jaka, yanzu kuma iya ta tsiro da wani abun.
Ba yadda ta iya, ta ce "To, bari na goya ummi, dan tayi bacci"
"Wai ke wace irin mace ce, har yaron ya mutu baki gama goyon wannan buhun sumuntin yarinyar ba, ban da rashin kara, ai ke yakamata ki goya mata yaron, dan Allah ki hanzarta ku tafi, ina nan me zai samu ummin, hanzarta maza".
Haka nan mariya ta ji gabanta yana faɗuwa, kamar wani abu zai faru idan ta tafi, ga Iya sai ɗaga mata murya take a kan tayi sauri.
"Iya zan iya goya ummin, sai in ɗauki yaron a hannu"
"Wai mariya meyasa baki da kunya, ina faɗa kina faɗa? Salon ki je ki kayar da yaron, ga wannan uwar ƴar ta ki, kaya guda a haka zaki ɗauki, yaron ba zaki hanzar ta ba, ko dan ba ɗan ki bane ba, ko da yake ina mai ɗa ɗaya ya san ciwon ɗa ma"
Ta ce "To ko in kawo ta ɗakin ki, sai in kwantar da ita, idan na dawo na ɗauke ta?"
"A'a ba zaki kawo mini ita ta yi mini fitsari ba, wannan samgartacciyar yarinyar, ɗuwawunta ba shi da saiti. Uban meye ma zai kamata a ɗakin, ki wuce ku tafi"
Jiki a sanyaye mariya ta shiga ɗaki, ta ɗakko mayafinta, ta na ta kallon ummi, tana fatan Allah ya sa babanta ya shigo da wuri.
Ta fito tsakar gida wasu daga cikin jikokin iya suka shigo, shigowar su bai sanya iya yin shiru ba, ta cigaba da yi wa mariya masifa.
Duk mutanen da ke cikin gidan, iya ta rasa wanda zata saka yayi rakiyar kai yaron sai ita, saboda dai kar ta huta, kuma kar ta zauna lafiya.
Suna tafe a hanya tana goye da yaron, sai kakari yake yi, saboda yadda ƙayar take sukansa. Ga gidan sarkin su da nisa sosai, haka suke tafe da fitila.
Sai dai zuciyarta sai harbawa take yi da sauri, hankalinta yaƙi kwanciya, ji take tamkar ta juya da gudu, ta koma wurin ƴar ta.
Sai wajen tara da rabi suka dawo, gudu-gudu sauri-sauri ta nufi sashin su, ba ta bi ta kan iya ba, ta nufi ɗakinta.
Sai dai ta kai kai zata shiga ɗakin, shi kuma ya fito da sauri, jikinsa yana tsuma.
"Me ka ke yi mini a ɗaki yanzu? Me ka yi?" Shiru yayi yana tsuma tare da kallon ta, ta hasken farin wata.
"Me ka yi mini a ɗaki i yanzu? Me ya kai ka ɗakina?" Tayi maganar cikin ƙaraji.
Iya ta ce "Wai lafiya kuwa? Kun dawo kenan ya jikin yaron?" Hankaɗe shi ta yi daga gabanta, ta shiga ɗakin da sauri, tana kiran sunan "Ummi"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Iya! Iya! Zo ki ga? Iya zo da sauri"
Da sauri iya ta taho da gudu tana cewa "Wai meye ne?"
Ta shiga ɗakin, ta tarar da ummi a kwance, tana ta numfarfashi, jikinta sai rawa yake yi, an tura mata hularta a bakinta, ga wandonta a yashe a gefe gabanta duk jini.
Iya ta dafe ƙirji ta ce "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'una, wace irin masifa ce wannan, me yaron nan ya zama, kar dai ki ce mini yaron nan ne?"
Cikin kuka mariya ta cirewa Ummi abun bakinta ta rungume ta, cikin ɗaga murya ta ce "Haba iya, da idonki fa kin gani, kina gani fa, waye ya fita daga ɗakin nan idan ba shi ba, na shiga uku na lalace an cuce ni, an cuci ƴa ta"
"Dalla ki rufewa mutane baki, idan kuma kururwar zaki cigaba, ki tonawa kanki asiri shikenan, idan ba wata ƙaddara ta Allah ba, waye ma zai aure ta, balle a san me ya faru da ita" sororo mariya ta bi iya da kallo, wanda hakan yayi dai-dai da sallamar baban Ummi.
Iya ce ta iya amsawa, ya shigo ya same su, mariya rungume da ummi tana kuka.
"Maman ummi, Iya meyafaru ne? Ummin ce babu lafiya?"
Mariya ta ɗaga masa ƙafar ummi, tana kuka ta sanar masa da abun da ya faru.
Salati ya saka ya durƙushe a wurin.
Iya ta ce "Da ki ke ɗorarwa ke kin tabattar shi ɗin ne? Sai ki jirani in bincika in tabbatar ai". Ta tashi ta fita daga ɗakin.
"Mariya, kina me? Garin yaya? Ya aka yi haka ta faru"
Cikin kuka mariya ta ce "Wallahi iya ce baban ummi, iya ce na shiga uku an lalata mini rayuwar ƴa ta, ina zan saka kai na"
Iya ce ta dawo riƙe da hannunsa, zuwa cikin ɗakin ta kalleshi ta ce "Uban wa ye ya yi wannan aikin? Me ka yi mata, ba sallama ka yi mini ka ce zaka tafi shagonku ba?"
Jiki a sanyaye ya ce "Wallahi iya tsautsayi ne"
A fusace balarabe ya tashi ya shaƙe shi, ya ce "Tsautsayin ka kasa sauke shi a ko ina, sai kan ƴa ta".
"Zaka cika shi ko sai na ɗauke ka da mari? Ba ɗa yake a wurin ka ba kai ma? Idan ɗan ka ne ya aikata hakan, tona masa asiri zaka yi? Ko idan ka tayar da maganar wani abun hakan zai amfanar, aikin gama ya riga gama.
Kuma bari ka ji in gaya maka, wallahi tallahi, muddin ku ka ɗaga maganar nan, wani ya ji ta, bayan mu ɗin nan, Allah ya isa ban yafe ba, kowaye sai na tsine masa. Ita dauɗar gora ai ciki ka sha ta. Idan baku rufa musu asiri ba? Waye zai rufa musu ko salon zumunci ya lalace? Ƙuruciya ce da ƙaddara da bai wuce kan kowa ba"
Da wani irin mugun sauri zuciyar mariya ke yi, ƙuruciya ga yaron da har ya san, ya toshe mata baki da tsumma, ya keta mata haddi, shi ake kira da ƙuruciya.
Jiki a sanyaye balarabe ya ce "Shikenan iya, duk ba za ayi haka ba, in sha Allah hakan ba za ta sake faruwa ba, an bar maganar da yardar Allah"
Ta kalli saurayin yaron ta ce "Kai kuma wuce ka bani wuri, wallahi ka sake aikata makamancin haka, da kaina zan ci ubanka na hukuntaka. Wuce ka bar ɗakin nan". Ya fice sumi-sumi ya ci bulus.
"Ke kuma ki daina wannan kukan, ki tashi ki dafa ruwa, ki sakata a ciki, kiyi haƙuri, ko ki cigaba da kuka baƙin ciki ya kashe ki" daga haka ta juya ta fice.
Tana fita mariya ta kuma rushewa da kuka ta ce "Yanzu shikenan baban ummi, yaron nan ya ci bulus kenan? An lalata mini rayuwar ƴa, har iya na cewa wai babu lallai wani ya aureta, wane irin abu ne wannan?"
Zuciyar sa fal takaici da ɓacin rai, saboda kar ya sake karya wa mariya gwiwa ya ce "Dan Allah kiyi haƙuri mariya, ki kwantar da hankalinki, kin ga iya uwata ce, ba yadda na iya, dan Allah ki yi haƙuri ki tayani yi mata biyayya, mu ɓoye sirrin nan, ko dan mutuncin ummi, kar abun yayi mata yawa. Dan Allah ki yi haƙuri mariya"
Tashi tayi ta kwantar da ummi, ta fita tsakar gida.
Babanta ya rungume ta, jikinta ya ɗau zafi, tana jin yadda hawayen sa ke ɗiga a hannunta.
"Ummina sannu kin ji? Meye yake miki ciwo?" Tayi shiru ba ta yi magana ba, sai sheshsheƙar kuka.
Mariya ta kawo ruwa a baho, ta fizge ummi daga hannun balarabe, ta saka ta a cikin ruwan ɗumin. Sai a lokacin ummi ta zabura ta fashe da kuka, ta ce "Mama zafi".
Tana kuka ummi na kuka, ta yi mata wanka, ta saka mata kaya, ta nemi wuri ta kwanta, ta share balarabe.
Kwana suka yi ummi na koke-koke, ko barci ya ɗan ɗauke ta, sai ta zabura tana turza ƙafarta tana ihu.
Haka mariya ta kwana kuka, da balarabe ya kai hannu zai taɓa ummin, sai ta ɗauke ƴar ta, ta juya masa baya.
Wayewar garin Allah, mariya ta saba zuwa ta gaida Iya, amma a ranar taƙi kula kowa, ta ƙi ɗora girkin gidan.
Yara masu tafiya makaranta, duk sashin ta suke zuwa karɓar kunun safe, su sha su tafi makaranta, ranar shiru ba ta ɗora ba, kowa yazo sai ya koma.
Balarabe ya din ga raragefe, ya rasa me zai cewa mariya, ya san ƙarshen cuta an yi mata, ba ma ita kaɗai ba, har da shi, sai dai ba yadda ya iya sawun giwa ya take na raƙumi, iya mahaifiyarsa ce ba yadda ya iya, dole ya bi umarnin ta.
Yayi shirin sa zai fita kasuwa, jiki a sanyaye ya ce "Mariya, ko asibiti zamu kaita, na ga kamar da zazzaɓi ta kwana".
"Dan Allah ka ƙyale ni da abun da ya dame ni, ka ƙyale ni bashir ka ƙyale mini ƴa ta, duk muninta daga jikina ta fito, ni na damu da ita, tun da a gurin kai da mahaifiyar ka, ba ƴa ba ce. Tun da baban sa yana da kuɗi dole ta ce dauɗar gora ciki ka sha ta, nayi imani da Allah da ɗan ka ne, yayi laifin nan, kowa sai ya ji" tayi maganar cikin matsanancin kuka.
Lallai mariya ta kai ƙarshe a ɗaukar zafi.
"Ki yi haƙuri mariya, ke kin san ina ƙaunar ƴa ta, ba yadda na iya ne, wallahi mariya ba ki fi ni shiga damuwa da tashin hankali ba, ki yi haƙuri dan Allah"
Ba ta kuma kula shi ba, ta cigaba da shafa kan ummi, da ta ɗan samu bacci, tana zubar da hawaye.
Da son ransa ne, ya wuni tare da su, ya cigaba da rarrashin ta, amma ya san idan ya ƙi fita, wani tashin hankalin zasu fuskanta daga Iya.
Gaba ɗaya girkin ma taƙi yi, ummi kawai ta samawa abun da za ta ci, da ta tuna a yadda ta tarar da ummi, sai ta sake fashewa da kuka.
Iya na son yin tijara, amma tana tsoron kar abun da ya faru ya tonu, dan sun haɗu da mariya a tsakar gida,ta hango tsantsar rashin mutunci da tashin hankali a idon mariya, wanda ba ta taɓa gani ba, dan haka ta ƙudurce a kan balarabe za ta juye.
Haka kuwa aka yi, ana idar da sallar magariba, ya dawo, ya je gaishe ta, ta dira masa bala'i, tamkar ba ita ta haife shi ba, tare da jaddada masa muddin ko shi ko matarsa suka bari zancen nan ya fito, sai ta tsine masa kuma babu ita babu shi.
Yayi ta bata haƙuri, sannan ya nufi ɗakin su, ya tarar da mariya tana goye da ummi kamar jaririya, tana jijjigata tayi bacci.
Sallamarsa kawai ta iya amsawa, daga haka ba ta sake kula shi ba.
"Ya jikin ummin?"
"Ba sauƙi" ta faɗa kai tsaye. Ta je ta kwantar da ummi a kan katifarta da ke ƙasa, ta koma falo kan kujerar da ke ɗakin ta zauna. Da yake ɗakin babba ne sosai, suka raba shi biyu da labule ya zama kamar ciki da falo.
"Ba sauƙi fa ki ka ce maman ummi?"
"Ina sauƙin yake bashir? An yi wa ƴa ta rauni na har abada, waye zai auri ummi ya riƙe ta da amana, alhalin an binne gaskiyar abun da ya same ta tun a lokacin da ya faru, ɗan gata ya ci bulus, koda yake dama an ce ba zata auru ba, saboda muninta, da wanne ummi za ta ji? Wallahi ɗaukar ƴa ta zan yi na bar gidan nan, garinmu zan koma, ko kare Allah ya bani ina so, balle ɗan adam" Ta ƙarasa tana sheshsheƙar kuka.
Ya ƙarasa ya zauna a kusa da ita, ya riƙe hannunta, idon sa ya tara hawaye ya ce "Haba maman ummi, ya zan yi, iya uwata ce, dole na yi mata biyayya, idan ki ka tafi da ummi ku ka bar ni, in zauna da wa? Ina son ku wallahi dan Allah kar ki yi mini haka, ummi kuma ba abun da zai hanata auruwa in sha Allah, dan Allah kar ki tafi ki bar ni"
Kallonsa ta yi, har cikin zuciyarsa yake maganar, wani irin tausayin sa ya kamata, har ga Allah yana iya ƙoƙarin sa a kan su, mahaifiyar sa ce ta hana su zama cikin kwanciyar hankali.
Ta kwanta a jikinsa tana kuka, rarrashinta ya din ga yi, yana yi mata magiyar, ta taya shi ya yi wa iya biyayya, ya san ba zasu taɓe ba, kuma rayuwar ummi ba zata wulaƙanta ba.
Abun ka da mata da miji, haka ya lallaɓata ta janye batun yin yajin, har ya fara ƙoƙarin shiga wani abun daban.
Iya ce ta faɗo ɗakin tana faɗin "Wai balarabe ba ka ji ana kiran salla bane, ka shige ka ƙule a ɗaka da mace" a razane mariya ta yi gefe, tana kare jikinta.
"Eh iya yanzu zan tafi masallacin ma dama, dam..dama... Yanzu aka kira sallar"
Ayshercool.
08081012143
*CUTARWA!*
Watpad ayshercool7724
Arewabooks ayshercool7724
YouTube Cool hausa novels
What's app 08081012143
BRIGHT PENS
(FREE BATCH)
3
Yanayin da suke ciki, bai sanya iya ja da baya ba, mussaman yadda suka rikice tamkar marasa gaskiya.
"Ina jin duk abun da ku ke faɗa ai, idan ta tafi ta barka ka yi yaya, tun da ta fini a wurinka, kar Allah ya sa ta zauna ɗin mana, ta ƙara gaba, wataƙila dama ita ce ƙashin tsiyar da ta tokare maka ƙofofin arziknka, har ni zan gindaya umarni, ka zo kana lallaɓata? Ki tafin mana waye ya riƙe ki? Ke idan ƴar mutunci ce ina uwarsa har sai ya nemi shawarar ki sannan zai bi umarnina?. To ke idan ban isa da ke ba, na isa da ɗa na, dan haka ki san abun da yake yi miki ciwo, idan ƙabilar ku kun saba asiri ku mallake mazaje, to ni na yi wa kaina da ƴaƴana dafa'i, asirinku bai isa ya kama ni ba"
Ba yau iya ta saba yi musu laɓe ba, dan haka yanzun ma mariya ba ta yi mamaki ba, dan idan da sabo ta saba.
Iya ta sake jaddada musu duk wanda ya fasa abun da ta ce a rufe, bata yafe ba.
Baban ummi ne ya yi ta bata haƙuri, mariya kuwa ta haɗe rai, wani abu mai ɗacin gaske na kaiwa da komowa a ƙirjinta, ji take kamar ta tashi ta ɗurawa Iya ashar, wanna ai shi ake kira da ga mari ga tsinka jaka, gaba ɗaya tsohuwar nan ba ta da imani, ba ta da mutunci, abu ɗaya take girmamawa a rayuwarta shi ne kuɗi.
Bayan sun samu ta fita, ya leƙa ya tabbatar ta tafi, sannan ya dawo ya cigaba da rarrashin mariya, ganin ya shiga tsaka mai wuya, ya sanya mariya ce masa "Ka kwantar da hankalinka baban ummi, ba wanda zai ji maganar nan, ina fatan Allah ya yi wa ummi sakayya, ba wanda zan bari ya sani"
Ya ce "Yauwwa, Allah ya yi miki albarka, in sha Allah zan san abun yi, zan yi ƙoƙarin neman fili a garin nan, na gina mana ko ɗaki ɗaya ne da makewayi, mu koma can, ko kema kya samu sassauci.
Kallonsa kawai take yi, cike da tausayawa dan kuwa ta san tun da iya ta gama raina masa wayo ba shi da abun duniya, ba zata taɓa barin sa ya bar gidan ba, ko dan kar ta huta.
A zahiri kuma ta ce "To Allah ya yassare" ya amsa da amin sannan ya tashi ya fita.
***
Jujjuyar lokaci ya sanya abubuwa cigaba da gudana, wasu da daɗi wasu marasa daɗi, sai dai lokaci ya wuce ba tare da ɗaci da raɗaɗin abun da ya faru da ummi ya bar zukatan iyayenta ba.
Kuma babu kunya, wanda yayi laifin ya cigaba da sabgoginsa hankali a kwance.
Mariya ta ƙara tsananta kula da jan ummi a jiki, babanta ya kaita makaranta, ita kuma ta je ta ɗaukkota, ta daina barin kowa ya raɓi ummi.
Mariya na zaune na ƙoƙarin koyawa ummi assignment a tsakar gida, kasancewar tana aji na uku a sakandare aka yi mata aure, ta iya karatu da rubutu. Iya na zaune suna hira da babarsu magaji da idris.
Ummi taƙi mayar da hankali a kan karatun da mariya take koya mata, sai soshe-soshe take yi, tana ɓata fuska.
"Mamana, wai ba zaki mayar da hankali ba, so ki ke anty ta zane ki?"
"Mama ni bana son makarantar" tayi maganar hawaye na taruwa a idonta.
Cikin damuwa haɗi da kulawa ta ce "Saboda me ummina"
Cike da ƙuriciya ummi ta ce "Tsokanata ake yi, mama dan Allah ki mayar da ni fara, kuma ki rage mini ƙibata"
Mariya ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Ummina, ke fa kyakywar yarinya ce, ai kin san sahabban manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, da nake yi miki tarihi ko?" Ummi ta jinjina kai ta ce "Eh, Ina son tarihi"
"Yauwwa ummina, mai kiran salla a zamanin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam, sayyiduna Bilal radiyallahu an hu, baƙi ne, kuma Annabi bai taɓa ƙyamarsa ba, haka sahabbai ma"
Ummi ta yi shiru ta ce "To mama kin ce in din ga son annabi, to masu tsokanata ba sa son annabi ko?"
Shiru mariya ta yi, tana tunanin wane bayani za ta yi wa ummi, dan duk da rashin sakewarta da mutane, idan tana tare da mamanta, akwai surutu.
Iya ta ce "Kin ga kar ki sakawa yarinya wani tunani daban, ki gaya mata gaskiya kawai, mummuna ce ko ki so ko ki ƙi"
Babar su magaji ta kwashe da dariya ta ce "Iya wannan jika taki, ai tun yanzu yakamata a fara nema mata maganin farin jini, dan za ayi gwagwarmaya kan a samu mai so, dan ina jin Alhassan ranar yana cewa; da zai samu igiya da ya zargawa ummi, ya tafi tashe da ita a matsayin ɗan biri" tayi maganar tana ɓaɓɓaka dariya ita da iya, ba tare da tunanin, ya mariya zata ji a zuciyarta ba ko ita yarinyar, ummi tayi ƙuri tana kallonsu, duk da yarinya ce, ta san cin mutunci.
Mariya ta ce "Biri kuma, ummin za a yi wasan biri da ita, kuma ki ke dariya, shikenan bakomai" tayi maganar cikin ƙunar rai, ta kama hannun ummi suka tafi ɗaki.
"Mama, da gaske ni biri ce? M, for monkey na bayan littafina?"
Mariya ta goge hawaye, ta ce "Ummina ke mutum ce, mai kyau sosai da sosai, kar ki sake haɗa kanki da biri kin ji ko? Kina da kyau sosai, kalli gashinki fa, duk garin nan kin ga mai irin gashinki?"
Ummi ta girgiza kai alamar a'a.
"Yauwwa ummi, idonki ma mai kyau ne, ina son idonki, duk garin nan babu mai irin idonki".
Ummi ta taɓa idonta ta ce "Sai akuya ko?"
"Akuya kuma?"
"Eh, malamarmu ce ta faɗa, ta ce ni da akuya irin idonmu ɗaya, eyes sunan ido da turanci in ji anty"
Mariya ta yi shiru tana kallon ummi, yarinyar na cikin taskun ƙalubale, daban-daban, har a kai ga malamarta na kamanta ta da akuya.
Iya kuwa ta cigaba da hurawa balarabe wuta, da shi da mariya, cin kashin yau daban na gobe daban, har ƴan uwansa ma, ware shi suke a wasu abubuwan saboda ba shi da kuɗi, haka zalika mariya ta cigaba da yi wa iyalan gidan bauta, idan anjima su yi mata rashin mutunci, ko a ci zarafin ƴar ta a gabanta ba.
Kusan kullum sai ummi ta ce ba ta son makaranta, dan kuwa abun da mariya ta fuskanta, ba iya ɗaliban ne ke tsokanarta ba har da malamansu a ciki.
Dan idan ummi ta zo da aikin gida, tayi a gida, sai ta ce ba zata nuna wa malamarsu ba, idan ta tambayeta dalili sai ta ce "Malamarmu cewa take yi in fito gaban Allo, a tafawa ƴar baƙa saran daddawa, ayi mini dariya, ni kuma in yi ta kuka sosai, bana son ana tsokanata"
Ba ƙaramin ɓaci ran mariya yayi ba, Dan haka da kanta ta je makarantar, ta roƙi headmaster, a kan ya taimaka ya tsawatar a kan abun da ake yi wa yarinyar, kar son karatun ya fita daga kanta gaba ɗaya.
Yayi mata alƙawarin yin hakan, sai dai ba ta canza zani ba.
Ummi na ta kaiwa tana komowa a tsakiyar ɗakinsu da safe, kasancewar yau ba makaranta, sai fama take da uban gashinta, taƙi tsayawa a gyara, mariya sai fama take da ita ta nemi wuri ta zauna.
Ta kalli babanta da yake cin abinci ta ce "Baba kafi mama loma" tayi maganar tana dariya.
"Eh mana, baki ga na fita girma ba?"
Ummi tayi dariya ta ce "To ni kuma gaba ɗaya ƴan gidan nan, na fi su loma"
Mariya ta ce "Ke ɗin, sai ka ce abinci ki ke ci"
"Mama nafi duk ƴan yara girma fa"
Babanta ya ce "Kin fi su lafiya ne, kuma kin fi su kyau shalelena"
Ta kama kumatunta ta ce "Iya ta ce bani da kyau ai"
"A'a ke kyakywa ce sosai" miƙewa ummi ta yi ta fita daga ɗakin, tana leƙa baƙon ɗan magen da yake wasa a tsakar gida.
Mariya ta yi ajiyar zuciya ta ce "Baban ummi, kana ganin ummi zata iya samun miji tayi aure?"
Ya kalle ta ya ce "Meyasa zaki faɗi haka? Kina mahaifiyar ta, kema kin fara biyewa surutun mutane na cewar ƴarmu ba ta da kyau mummuna ce?"
"Ba haka bane ba, abun yana taɓa ni sosai da sosai, har malaman su ummi su da zasu tsawatar wai har da su a cikin tsokanarta, babar su magaji wai har da cewa Alhassan ya na kiran ummi da biri, kuma ta faɗa suna dariya"
Jiki a sanyaye ya ce "Biri kuma? Cin mutuncin ya kai haka? Wallahi mariya ummi ba mummuna ba ce ba, tana dai da duhu ne, kuma ƙwayar idonta ce da ba irin tamu ba, amma ba mummuna ba ce ba"
Mariya ta numfasa ta ce "Ni ba wannan ba, duk wanda ya ci zarafin ummi, na san bani na halicceta ba, amma abun da yake damuna, a zamanin nan yarinya ta kai mutuncinta ɗakin aure, ya ta ƙare ina ga idan ummi ta samu miji, gaya masa zamu yi ga abun da ya same ta? Idan muna gaya masa waye shaida babu tabbacin a lokacin dukkaninmu da muka sani
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 54