Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
auren na ramuwar gayya ne? To ka yi mu gani, wallahi sai ka yi bankwana da farinciki da kwanciyar hankali har abada". Ya nufi gadonsa yana faɗin "Allah ba zai gwada mini rashin kwanciyar hankali ba, in sha Allah auren nan alkhairi ne a gareni" *** Cikin mamaki da takaici mami take kallon hajiya, da take yi mata dariya cike da son tura mata takaici. Ta ce "Wato Alhaji a duniya mace ta samu nagartaccen miji irin raihan, to ta ɗaga hannu ta godewa Allah ta haye, yaron kirki Allah dai ya ja zamanin babban mutum" "Hauwwa babu ruwanki da ni, da sabgar iyalina ban saka da ke ba, ashe shiyasa ki ka turo makakken ɗanki ya ci mini mutunci yana gaya mini maganar banza, wallahi ki shiga hankalinki babu ruwanki da ni" Hajiya ta ce "Ko ba makakke ba, ai gara makakken ƙwaya, idan ƙwayar ta sake shi zai iya dawowa daidai, wanda yake cikin mayen soyayya kuwa ko za a shekara dubu ba zai farfaɗo ba, dan haka akwai banbanci ko dai ki nutsu ki yi playing role ɗinki na uwa, ko kuma idan yarinyar nan ta waiwayeki, ki ka cigaba da saka mata ƙiyayyar ki, sai ganin ɗan naki ma ya gagare ki, ɗan ɗaya tilo da ki ke alfahari da shi shiryayyye ta rabaki da shi". Alhaji ya ce "Hajiya wai kwanan nan meyake damunki ne? Ban sanki da irin wannan abubuwan ba, idan tana yi a baya ba kya mayar mata da martani, amma yanzu duk kin canza" Ta ce "Duka yau duka gobe shi yake sanya baƙin ba'auzine tawaye, kuma komai girman gona akwai kunyar ƙarshe, sai a wannan karon Allah ya kawo ni lokacin ramawa da mayar da martani, ko kun manta ɗigimin da ku ka din ga yi da ka aureta, sai da na ji kamar mu rabu na huta, Hajiya Aisha tayi ta bani haƙuri, matar nan ta din ga yi mini gorin zafin kishi zan kashe aurena ita tafi ƙarfin goga kishi da ni, ka din ga yi mini halinku na maza? To Alhamdilillah koma menene abun kunyan da na yi, bai kai naki ba da ki ke kishi da matar ɗanki, duk da zafin abun da ki ke ji, bai kai wanda na ji ba da ki ka auri mijina. Anyway, Alhajin Allah zan shiga in yi wa sirikata ɗan abun da zan tafi mata da shi na dubiya, ka san mace mai ciki bakomai take iya ci ba, idan ana ƙinta ni ina yinta tun ba yau ba, dan gara munin fuska da munin hali, duk da Alhamdilillah ba ta da muni" Alhaji kuwa sakin baki yayi yana kallon Hajiya, ta gama cashe musu ta fice. "Ciki kuma? Ba cewa yayi ba shi da lafiya ba? A ina ta samu ciki kuma?" A ƙule Alhaji ya ce "Kin ga dan Allah jeki ki bani wuri, kar saka mini ciwon kai" kamar ta fashe da kuka yau ita Alhaji yake kora, tamkar mahaukaciya ta fice daga sashin nasa tana tuntuɓe, tana tafe tana tambayar kanta ciki a jikin ummi, ƙarya yake yi kenan lafiyarsa ƙalau?. Raihan yana ta shirin fita aiki, ummi ta lallaɓa ta dafa masa tea, ta dawo ta kwanta a falo, aka ƙwanƙwasa ƙofar falon. Raihan ya tashi ya buɗe sai ga noor, ya kalleta ya ce "A'a kin gama gudun namu kin dawo?" Noor ta ce "Ai na ga zamana a nan ya fi alkhairi, gidanmu kamawa da wuta yake neman yi" Ta shigo falon tana yi wa ummi sannu. Ummi ta ce "Noor wace irin wuta kuma? Meyake faruwa a gidan?" "Wai Abba ne yayi aure, ya kawo mata alewa da dabino take ta masifa da bala'i da tashin hankali, daga na ce in ci dabinon kin ji zagin da tayi mini? Ni kuwa na ɗebo na haɗo kayana na dawo, dama sai da ku ka ce kar na tafi na ce sai na tafi. Gidanmu yana nan yadda ki ka san rasha da ukrain" Ummi ta harari noor, saboda yadda take ta zuba, a gaban raihan. Amma cikin mamaki Ummi ta ce "Amma aure kuma?" Noor ta ce "Eh mana, ashe jiya maiduguri ya je mamanku ya aura, dama na daɗe ina ce masa dama ya ƙaro mana anty" Ummi ta ce "To baba suda na ji ya isa haka" Noor ta sake cewa "Kin san Allah anty ummi, na daɗe ina tausayin Abba, dan ba kya gidan ba kya ganin yanzu abubuwan da suke faruwa, tayi ta ɗaga masa murya, amma kin ga takwarata ai saliha ce a hankali ma take magana" Raihan ya ce "Lallai dr. Ya shamamce mu, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi, tun da gaki kin zo, bari na tafi aiki" Bayan tafiyar sa aiki, ummi ta din ga yi wa noor mitar yadda ta saki baki a gaban raihan. Noor ita ba ta ga abun laifi ba, dan a ganinta yanzu ai sun zama ɗaya da raihan. Sannan ta kira can gida maiduguri, suka tabattar mata da hakan. Cikin mamki ummi ta ce "Amma anty maryam, mama ta gama warware ne?" Anty maryam ta ce "Jikinta fa da sauƙi sosai da sosai, ai kuna waya ki ji, ya ce wai can wurin da yake karatu zai tafi da ita, amma ni matarsa nake ji ye mata tsoro" Ummi ta duba taga noor ta tafi kitchen, sannan ta ce "Babu abun da zai faru sai ikon Allah anty Maryam, kuma in sha Allah mama ta shigo gidan nan kenan, dr. Mutum ne managarci, kuma zan tsaya iya yi na hakan ya tabatta, babu wanda zai cutar mini da uwa, kuma da ba a aure ita ma da ba a aureta ba" "To ki dai ta yi musu Addu'a" "In sha Allah" Noor ta dawo falo da plate, da ƙaramar wayar ummi a hannunta ta ce "Yaya ummi, ga mutuniyarki indomie mai yaji da kifi, Yaya salim ne za su zo" Ummi ta kalleta ta ce "Wane Salim ɗin?" "Yayan MD mana" Cikin mamaki ta ce "Ya aka yi ki ka sani" Sai kuma ta ɗan diririce ta ce "Yaya raihan ne ya gaya mini" Ummi ta ce "Allah ya kawo su lafiya, me zamu girka musu?" Noor ta ce "Zan yi musu abinci, amma ki koma ɗaki ki kwanta, kar ki ce warin girkin zai saka ki amai" Ummi ta tashi tana murmushi ta ce "Yauwwa ta wajena, shiyasa nake son ki ummana, bari na je na yi wanka na kintsa kan su zo, kar su zo su same ni a haka, kalli kaina ko taza babu na fi kwana uku ban taje ba, MD jiya har ya jona hand dryer zai taje mini na ce bana so da zafi, ya ƙyale ni" Noor ta ce "Ohh, yaya ummi soyayya da daɗi ko? Ke ban da wannan abun da ya faru na ga yana sonki ba kwa faɗa, amma anty intee da wayona fa lokacin da mijinta Salim yake zuwa suke shan soyayya amma yanzu kullum cikin faɗa kamar abokiyar gabarsa" Ummi ta ce "Waye ya ce miki bama faɗa? Babu wata soyayya da za ayi zaman aure ace babu saɓani, sai dai danganta da yadda aka gina soyayyar, idan har ta gaskiya ce kuma an fahimci juna, ko saɓani yazo za a warware cikin sauƙi. Ni kaina MD ba dan yana sona ba, kuma mutum ne mai fahimta ba da laifukan da na yi masa a kwanakin nan wani zancen ake yi ba wannan ba, shiyasa ko mun samu saɓani nake duba alkhairnsa bana taɓa yi masa hukunci da laifin da ya yi mini". Noor ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ni wallahi soyayyar da ba a faɗa nake so, idan muka yi faɗa kuka zan yi" Ummi tayi dariya ta ce "Sai ki tafi littafi ko film, ko kuma tatsuniya, a nan zaki samu wadda ba a faɗan. Bari na shiga daga ciki" Noor ta yi shiru tana ta zancen zuci, ita har ga Allah ta fi son ayi ta soyayya babu faɗa. Ummi daga yin wanka ta ji sanyin Ac, ta kwanta ta hau bacci a ɗakinta. Noor ta zage tana ta gyara gidan, ta iya aiki sosai da sosai saboda zama da ummi. Ta gama aikin ta shiga ta yi wanka ta saka wata ƴar doguwar riga da ɗan kwali, ta dawo falo tana shan lemo mai sanyi. Ba ta daɗe da zama ba a ka buga ƙofar falon. Ta tashi ba tare da tambayar waye ba, ta buɗe ƙofar, kallonsa ta tsaya tana yi tana murmushi, hannunsa ɗauke da manyan kulolin abinci,  ta ce "Sai yanzu ko? To koma mun yafe" alama yayi mata da ido, ya tura ƙofar hajiya ta gani a bayansa. Da sauri noor ta nutsu, ta durƙusa tana gaishe ta, saboda ta shaidata, ta karɓi kayan hannunta suka ƙarasa cikin falon. Hajiya ta ce wa noor "Kamar na so na gane ki" Salim ya ce "Ƙanwar ummi ce" ya kalli ummi ya ce "Ga hajiya, in faɗa mata me ki ka ce a kan ta?" Noor ta kalleshi da sauri tana zare ido, ta girgiza masa kai. Hajiya ta kalleshi ta kalleta, ta ce "Laifi na yi mata?" Yayi murmushi ya ce "Hotonki ta gani a wayata, ta ce na sanki, na ce eh ƴar uwammu ce ke, wai ranar bikin su raihan tana ta kallonki, wai kwalliyar ki tayi kyau, gashi kin iya turanci, kina magana kina turanci, har gwada maganarta ki ka yi ko ba ayi ba?" Noor tamkar ta nutse a wurin nan, ta sunkuyar da kai tana hararsa ta ƙasan ido. Hajiya ta yi dariya ta ce "To ai da sauƙi tun da ba laifi na yi mata ba, ina ummin ne?" Duk da noor ta san ummi bacci take yi, ta tashi da sauri ta ce "bari na kirawo ta" har noor ta bar falon kallonta yake yi yana dariya. Hajiya ta ce "Wai ya aka yi har ku ka saba haka ne?" Ya gyara zamansa ya ce "Ina ganinta a nan gidan, sai kuma lokacin da aka samu matsalar nan na su raihan, da na je gidansu ita ta gaya mini. Ta wurinta na din ga samun information ɗin da na samu ummi a can garinsu. She's very funny ne kawai tana bani dariya. Hajiya ma ta yi murmushi, noor ta dawo falon amma ta laɓe ta bayan labule ta ce "Na duba bacci take yi" Ta gudu ta koma kitchen, ta haɗa musu ruwa da fruit, amma ta kasa fitowa tana jin kunya, sai a yanzu ta fuskanci hajiya mahaifiyar Salim ce dan suna kama sosai, saɓanin da ya ce mata ƴar uwarsu ce. Da ƙyar ta dawo falon tana sunkuyar da kai. Hajiya ta ce "Ya sunanki ne?" "Mariya, amma ana ce mini noor, maman ummi aka yi wa takwara aka saka mini sunanta" Hajiya ta ce "Masha Allah noor, kar ki damu da abun da ya faɗa rabu da shi, bari mu tafi ga abinci muka zo wa da ummi, na zo na ƙara duba jikinta" Noor ta ce "Dan Allah kar ku tafi, bari na tashe ta" Hajiya ta ce  "A'a ba sai kin taso ta ba" Muryar ummi suka ji tana cewa "Hajiya sannunku da zuwa, wallahi bacci ne ya kwashe ni" Hajiya suna can suna hira da ummi, Salim ya fita, noor ta bi bayansa. Yana tsaye yana waya ya ji muryarta ta ce "Allah ya kama ka" Ya waiwayo ya ce "Da na yi me?" "Ashe mamanku ce" Ya ce "A'a ƙanwar Alhaji ce" Noor ta ce "To wallahi mamanku ce, shi ne ka gaya mata abun da na ce, duk na ji kunya". Salim ya yi dariya ya ce "Last born" Ta ce "Ba wata last born, wallahi ka bani kunya sosai" Yayi dariya yana kallonta, ƴar ƙarama da ita sai baki. "Ka san me? Babanmu yayi aure fa, ya auri babar su yaya ummi, mamanmu sai fitina take yi a gida, ni kuwa na yi tahowata nan" Ya ce "Kin kyauta, ba kyau kallon manya idan sun samu saɓani" Kawai ta saka hannu a aljihun rigarsa, sai ga kwalin sigari. Ta ce "Ba ka daina ba ko? Ka ce mini fa ka daina" Ya haɗe rai ya ce "Meyasa ba ki da kunya ne? Dan kin ga ina yi miki dariya har ki ka saka hannu a aljihuna?" Noor ta ce "To ai ba kuɗi na ɗaukko ba, kuma ka ce mini ka daina" Hannu ya kai ya karɓa, ya mayar da kayarsa cikin aljihunsa, ya juya ya tafi. 3 MONTHS BACK Salim ya je gidan raihan, amma maigadi ya sanar masa raihan ya ce duk wanda ya zo ace masa baya nan. Ya tambayi maigadin dalili, ya ce bai sani ba, amma tun da hajiya bilki ta je, ummi ta tafi tana kuka da kayanta a hannu, amma bai san meyafaru ba. Tun daga nan jikinsa ya bashi akwai wani abu, da safe neehal za ta fita suka haɗu, ya tambayeta meyafaru a gidan raihan da mami ta je, ta ce masa ba komai, sai da ya zageta sannan ta gaya masa abun da ya faru. Da azahar ya wuce gidan su ummi  dan jin meyafaru, ya haɗu da noor a hanya za ta je makarantar islmaiyya . "Ke!" Yayi maganar yana sauke glass. Ta tsaya ta ce "Sunana mariya wato noor" tsyaawa yayi yana kallon ta ya ce "Kin gane ni?" "Eh, na ganeka ɗan uwan su yaya raihan" "Yauwwa, ummi na gida ne?" Ta ce "A'a tana gidanta" Ya buɗe motar ya ce "Ba ta can ki gaya mini gaskiya " Ta ce "Eh ta zo gida, mamanmu ta ce wai ba zata zauna ba, ba a san fa in da take ba, yaya raihan ya zo ana ta nemanta, sakinta fa yayi". Salim ya ce "Ina ta tafi yanzu?" "Gaskiya ba zan gaya maka ba, islamiyya fa zan tafi, kar na makara". Salim ya ce "Shigo mu tafi na kai ki islamiyyar " "A'a ni ba zan hau motar wanda ban sani ba" Ya ce "A'a ai ni kin sanni, yayan raihan ne ni" Ta ce "Bari na gaya maka dai, duk da ta ce kar na sake na gaya wa kowa, gagarwa ta tafi, can garinmu a jigawa, amma kar ka gayawa yaya raihan, ta ce kar na faɗa, jiya kan ta tafi ta gaya mini". Salim ya ce "Na gode sosai da ki ka gaya mini, daga gagarwan ina za a yi aje gidan" Ta wassafa masa komai, kwatancen gidan tun daga tasha, da yake ba ɓoyayye bane ba, ya yi wa noor godiya ya tafi. A yammacin ya tafi gagarawa, bai jira sai washegari ba, yayi sa'a ya tarar da ummi, kuma ta sanar masa duk abun da ya faru, da shawarar da ta yanke, ta kuma roƙe shi a kan dan Allah kar ya gayawa kowa in da take. Bayan wata guda, ya haɗu da noor ta je gidan yayar farida, a sharaɗa, shi kuma ya je wurin wani abokinsa. Suka gaisa, yake bugun cikinta ko an ga ummi, ta ce masa ba a ganta ba, ta nuna masa yadda take cikin damuwa, rashin sanin in da ummi take. Ta saki baki tayi ta bashi labarin zaman da ummi ta yi a gidansu, da yadda ake yi wa ummi gorin ta auri yaro ƙaninta. Ta ce "Yauwwa ka ce kai yayan yaya raihan ne, amma ba mamanku ɗaya ba ko?" Ya ce "Eh" "To wallahi in gaya maka mamansa ce ta saka ya saketa, ba ta sonta wai mummuna ce ta auri yaro, dan Allah ai auren yaro ba haramun bane ko? Kuma ai yaya raihan babba ne yana da gemu fa" Ya ce "Eh gaskiya ba laifi ba ne, in dai mutum yayi gemu ba yaro bane" Message ya shigo wayarsa, ta kalli lock screen ɗin sa, da hoton hajiya ne a kai, ta ce "Laa ka san wannan matar?" Ya amsa da "Eh, ƴar uwanmu ce" "Innalillahi, ta burgeni lokacin bikinsu yaya ummi, ta iya wanka, gashi ta iya turanci" Yayi dariya ya ce "Gaskiya ne" Noor ta ce "Wallahi duk ƙarfin hali nake yi, rashin yaya ummi har kuka nake yi, rayuwarsu tayi ta bani sha'awa da MD ba sa faɗa, amma kawai ya saketa na zata auren saurayi ya fi daɗi, amma na fasa" "Tsoho zaki aura kenan? Ai shi ma yana sonta ba laifinsa ba ne" Ta ce "A'a ba tsoho nake so ba, me dai gemu kamar naka, wai dan Allah da ka je gagarawa ba ka ga yaya ummi ba?" Abun da ta faɗa na farko ya bashi dariya, ya ce "Da na ganta ai da na gaya miki, amma me zaki bani na nemo miki ita?" Noor ta ce "To ai bani da kuɗi" Ya ce "Ba kuɗi zaki bani ba, zan gaya miki amma sai na nemo miki ita" Tun daga ranar suka saba da Salim, lokaci-lokaci ya kan bi unguwarsu, dan ya ganta, saboda yana son surutunta. A haka ta gane yana shan sigari, tayi ta masa mita, ya ce idan ya nemo mata ummi, zai daina sha. Haka nan yake jin daɗin mu'amalarsa da ƴar yarinyar da da yayi auren wurin zai haifeta. CIGABAN LABARI. Hajiya sun daɗe tare da ummi, kuma ummi ta samu ta ci abincin da hajiya ta kawo mata sosai ta ƙoshi, kuma Allah ya taimaketa ba ta yi amansa ba. Bayan tafiyar Hajiya, Dr. Ya kira ummi a waya, bayan sun gaisa ya ce "Noor tana gidanki ko?" Ta ce "Eh kawu" "Na san ta riga ta gaya miki komai ma,  bayan mun zo gidanki mun yi wannan maganar, na yanke shawarar yin abun cikin gaggawa, saboda kar wani abun ya kutso ya hana. Na kira baban maiduguri, muka yi magana da shi, da na tabattar da ya amince, kawai da muka je jiya, na tafi da sadaki aka ɗaura, dan hatta ƴan gagarawa ba su sani ba, sai da aka ɗaura na san za a iya samun matsala ko daga gare su ko wani ɓangaren. Nan da sati ɗaya idan komai na ta ya zama ready, zan ɗaukkota ta yi miki kwana ɗaya ko biyu sai mu wuce". Ummi bakinta ya kasa rufuwa, ta ce "Alhamdilillah ala kulli halin, Allah ya cigaba da faranta maka kamar yadda ka ke yi mana kawu, Allah ya saka da alkhairi na gode sosai da sosai" Dr. Ya ce "Ba komai ummi, yi wa kai ne". Can Maiduguri kuwa, mariya na zaune ta yi shiru tayi zurfi a tunani, mama ta ce "Mariya, wai menene? Ko abincinki fa baki taɓa ba" Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Wallahi mama tunani nake kawai" "Tunanin me?" "Auren nan mana, ni fa banda baba ya matsa ba zan yi wani aure ba, ido ya mutu kwalli ba zai farfaɗo da shi ba, kuma idan ina tuna wahalar da na sha a hannun iya, ko a mafarki bana fatan sake yin aure" "Ashsha, mariya ba a fitar da rai da rahamar Ubangiji, kuma ke ba tsohuwa ba, haryanzu da sauranki, babu wanda zai ce kin haifi ummi, gashi albarkaci auren har jirgi zaki hau" ta ƙarasa maganar cikin zolaya. Mariya dai ta rausayar da kai ta ce "Wallahi mama ba na ƙaunar abun da zai sake haɗa ni da iya, auren nan ya sake mayar da ni jikin su" Mama ta girgiza mata kai ta ce "Akwai banbanci, tsakanin Bashir da Yahaya, Kuma ai ba wuri ɗaya zaku zauna ba" mama tayi ta lallaɓata tana kwantar mata da hankali. Can gidan dr. Kuwa Farida kamar za ta kama dr. Ta daka, saboda azabar kishi da bala'i, sai dai fafur ya mayar da ita kamar mahaukaciya ya ƙi saurarenta. Yanzu da safe Abdul ya kawo kai zai shigo falo, ya ji yo muryarta tana ta ɓaɓatu, tare da amfani da kausasan malamai wurin ci masa mutunci. Dr. Ya fito ya fice, ba tare da ya ce mata uffan ba, Kausar na ta ba ta haƙuri, Abdul ya shigo rai a ɓace ya kalli farida ya ce "Maama wannan abun da ki ke yi ba mutuncinki bane ba, duk maƙwabta na jinki, wannan zubar mana da mutunci ki ke yi" "Haba yaya Abdul, ka san menene kishiya kuwa? Kuma kishiya da mahaukaciya ku baku san komai a kan wannan lamarin ba" Farida ta ce "Rabu da shi, baƙin ciki ya kasheni, sai su ci duniya da tsinke da ubansa, bands butulci da zalunci irin na ɗan Adam, duk halaccin da na yi masa ya rasa da mai zai saka mini sai wannan rashin mutuncin, maimakon ya auro cikakkiyar mace da zan yi kishin na gaske da ita, sai ya ƙare a mahaukaciya, ai da ƴar tata ya aura shi ne ƙarshen soyayya" Abdul ya ce "Koma wa ya auro, hakan dai zaki yi maama, wallahi Abba ba ma bin sa bashi, shi ne yake bin mu, menene bai yi mana ba na kulawa a rayuwar nan, shekara sama da ashirin yana ƙarar da ƙarfin sa saboda mu, kuma lokaci ɗaya duk sai mu haɗu mu goya miki baya mu rabu da shi? Bamu yi masa adalci ba, kuma wataƙila da baki kori ummi ba, da bai ce zai ƙara auren ba". Muguwar ashariyar da ta luluƙa masa ya sanya shi waro ido, ba shiri ya fice ya bar su da kausar. Ta kalli kausari ta ce "Ki shirya ki je gidan ta, ki dawo mini da ƴa ta, idan ta ƙi ki ci uban noor ɗin, tun da ba mahaukaciyar uwarta ce ta haifeta ba, sannan ki tabattar kin ci mata mutunci da sai ta zubar da hawaye" Kausar ta ce "Zan yi, amma dan Allah ki kwantar da hankalinki, kin ga fa yadda ki ke haki" gaba ɗaya farida sai ta fi kama da mahaukaciyar tuburan. Noor kuwa ta miƙe abun ta a gidan ummi, ummi ta fara samun sauƙin wasu abubuwan saboda noor, ita take bata kuɗin motar zuwa makaranta boko da islamiyya. Ummi ta ce mata yakamata ta biya gida, su gaisa da su farida, amma ta ce ita ba ta son ta je gidan ta tarar da su Abba suna faɗa. Ɓangaren mami ma abubuwa sun yi mata zafi sosai, dan haryanzu Alhaji fushi yake yi da ita, ga ɓangaren su safiyya sun hura mata wuta, dan zuba ido suke yi, a danƙaro musu kayan lefe. Sai dai zancen nema yake yi ya shiririce, dan Alhaji ma ya ce kar ta sake yi masa maganar auren raihan, shi na fari da ya yi masa, shi ne hurumin sa. Kuma sanin halinta ya sanya yayi mata gargaɗi na gaske, a kan gidan da raihan ya saya wa ummi. Kausar kuwa da ta je gidan ummi, hankali kwance ta tarar da su har da raihan suna kallo, babu abun da ya dame su. Sai duk ta kasa sakewa ta yi rashin mutuncin da ta ƙullo, duba da yadda raihan yake muzurai. Hankali kwance ummi ta karɓeta, ta karrama ta. Ta ce "Dama maama ce ta ce noor ta koma gida" Raihan ya ce "Saboda me?" "Haka dai ta ce" Raihan ya ce "To ai ni mun yi magana da dr. Ya ce tayi zamanta, ta din ga zuwa makaranta daga nan, amma noor kin ji abun da mamanki ta ce" Noor ta tura baki ta ce "Ni na tambayi Abba ya ce na zauna, zan koma amma ba yau ba" juyin duniya, noor ta ce ba in da za ta je, ita fa maama ba son ta take yi ba, dan kullum cikin yi mata faɗa take da zaginta. GAGARWA. "Kai auwalu, daga kai har Alhassan kun kashe zuciyarku, kalli yadda rana ta take, sai baccin asara ka ke yi ba zaka tashi ba?" Tayi maganar tana dukan ƙofar ɗakinsa. Amma ya ƙi tashi, ta gama ɓaɓatunta yayi burus da ita, ta ƙyale shi, ta koma sashinta, ta ɗebi ruwa tana alwala. Ta ɗago za ta tashi, ta ji an yi ball da ita gaba, ta dungura. Cikin tangaɗi da maye, ya ce "Ke banzar tsohuwa, ban gaya miki babu ruwanki da ni ba? Ko in tashi ko kar in tashi ban hana ki shiga harkata ba" Iya da ƙyar ta motsa, wani irin jiri ya din ga ɗibar ta, taga gari yana jujjuya mata. Kan ta ankara, ya sake surarta yayi jifa da ita kamar tsummokara. Ta kurma uban ihu, amma ba kowa, ya din ga jifa da ita, tun tana ihu, ta koma kakari, jini ya fara zuba daga hancinta. Ya sake surarta yana tangaɗi ya nufi wawakekiyar rijiyar da ke tsakar gidan. Ayshercool PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi  Man garan gashi  Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA

Chapter 49 of 54