Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da Safiyya, dan ƙarafafa zumunci. *** Ƙurii raihan ya yi wa ummi da ido, yadda take ta yi masa dariya. "Ni ko? Ni zan gaya miki damuwata ki saka ni a gaba kina dariya, wasu abubuwan duk shawararki na bi, ƙarshe na rufta kuma kin zo kina dariya" "To ai kai ɗin ne, yadda duk ka tashi hankalinka dole ka bawa mutum dariya. Ni da na zata wani abun da ba a so ne, da farko dai congratulations mai girma MD" hararta yayi yana kallon wayarsa. "Attention" tayi maganar tana kallon sa. Ya juyo yana kallonta shi ma "Ka saurareni, mu ajiye wasa da komai a gefe, zan yi magana a matsayina na yayarka ne" ya haɗa hannyensa biyu ya yi tagumi ya zuba mata ido. Ummi ta ce "Ba bakina zaka kalla ba, ka saurareni da kyau, a matsyinka na mutum mai muhimmanci da ba zan manta da shi ba, ina fatan Allah ya haɗa ni da kai a aljanna a majalisar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, kuma duk mai son ya tashi da annabi Sallallahu alaihi Wasallam sai ya kiyaye cin hakkin mutane. Kai mutumin kirki ne raihan, kar ka bari kuɗi da shugabanci su yi wasa da imaninka, ka ji tsoron Allah, ka ji tsoron Allah ka riƙe gaskiya da amana, kar ka cuci kowa kar ka ƙasƙantar da kowa, yayyenka ƙannenka ma'aikatanka da duk wani na ƙarƙshinka, ka kula da su bisa amana, kar ka yi son zuciya, kuma kar ka saka a ranka lallai sai kowa ya soka, kawai ka yi dan Allah. Abu na gaba, dole ka rage wannan jin kaɗe-kaɗen, ka mayar da hankali a kan azkar, da addu'a Ubangiji ya dafa maka yayi maka jagora, ya rabaka da dukkanin abun ƙi. Sannan idan Allah ya sa ka tashi yin aure, a yanzu ko a gaba, ka samo mace ta gari, wadda abun da ka ke da shi, ba zai rufe mata ido, ta ja ka ga hallaka ba, danmu mata mutane ne masu kanmu da yawa, tsaf sai wata ta yi yinƙurin mallakarka da dukiyarka ta rabaka da kowa, kar ka auri mace dan kai kana sonta kawai, ka duba makomar zuriyarka da ahalinka, kai mutumin kirki ne zaka iya babban mutum, ka yawaita saurara tarihin salihan bayi da yadda suka gudanar da rayuwarsu mussaman ta fuskar shugabanci, hakan zai ƙara sanya maka tsoron Allah, Allah ya tayaka riƙo Muhammad Raihan" Jikinsa gaba ɗaya yayi sanyi, kalaman ummi maimakon su kwantar masa da hankali, tayar masa da hankali suka sake yi, tare da jin tamkar ta sake ɗaure shi da jijiyoyin jikinsa. "Ummi wallahi an scared, ba zan iya ba, jagoranci abu ne mai wahala" "Haba madubina, kai kake ƙoƙarin koya mini jajircewa, kai kuma in ga gazawarka? A'a kar ka watsawa Alhaji ƙasa a ido, zaka iya ka ji" Yayi shiru bai ce komai ba. Ta ce "Ka ce to mana" "Ba zaki gane a yanayin da nake ba ne". Ummi ta ce "Eh ba zan gane ba kam, karɓi kuɗinka" tayi maganar tana ajiye masa envelope ɗin da ya saka mata kuɗi a kan tebur. "Ɗauke tun kan ki fusata ni, na yi miki rashin mutunci a gaban mutane" Da mamaki ta kalleshi ta ce "Amma raihan idan ka yi mini haka ba ka kyauta mini ba, kuma ba zan ji daɗi ba" tayi maganar muryarta na rawa, dan tuno shi tayi ranar da suka je office ɗin su, da ya burkice sai da ya bata tsoro. Ya tashi tsaye ya ce "Bari na ƙarasa office, idan na samu kaina zan zo mu tafi gida, idan kuma aiki yayi mini yawa zamu yi waya" ko amsarta bai jira ba, yayi waje ya barta da kuɗin. Sai da ya fita manager ya ce "Ummi, me aka yi wa mutumin ne na ga yana cika yana batsewa?" Ummi ta ce "Rigima kawai yake ji" "Ai nima na ga alama, shiyasa ban kula shi ba". Abu kamar wasa, aka yi ta shirin yi wa raihan liyafa, ya so ummi ta je, amma ta ce ba zata ba. Abokan hulɗar Alhaji Tahir wasu sun ga wautarsa, na bawa raihan jagoranci babban business irin wannan, matashi mai shekaru 23 dan ma yana da siffar kwarjini da girman jiki, amma kallo ɗaya zaka yi masa ka san yaro ne. Sai dai ko a kalamansa na godiya, da na kama aiki, sun tabattar wa da mutane ƙaraminsu babbansu ne, kamar yadda Alhaji Tahir yake faɗa, wanda wasu maganganun ummi ce ta gaya masa abun da zai ce, dan Alhaji Tahir ya sanar masa ya shirya kalaman da zai faɗa ranar liyafa. Aka yi taro aka watse, ya turawa ummi hotunan abun da aka yi, ta ɗauki hotonsa guda ɗaya ya sha coat, ƙuruciyarsa ta fito sosai, sai dai ya tsare gida babu fara'a, ta saka shi a status da caption na "Allah ya tayaka riƙo ƙanina, MD Muhammad Raihan" Ta kai awanni biyu da yin status ɗin, da ta buɗe what's app ta tarar da saƙonni, na tambayar waye shi, ciki har da yaya magaji, babban wanda ya fi bata mamaki shi ne message ɗin maryam, tun da raihan ya haɗa su, suka yi magana maryam ba ta sake kulata ba, idan ta yi mata magana ma, sai ta ga tana shareta, dan haka ita ma ta daina kulata, sai yanzu taga message ɗin ta, wai ya aka yi ki ka sani?. Ummi ta yi mata reply da "Shi ya gaya mini". Maryam ta ce "A ina ku ka haɗu ya gaya miki?" "Muna gaisawa idan zai wuce ta wurin da muke aiki ne". Ta yi reply da "Dan Allah ki cire shi, ba kowa ya sani ba, kar azo hakan ya bashi matsala" Ummi ta daɗe tana jujjuya message ɗin, ita mutum nawa ne ma a what's app ɗin nata. Ta ga ita kanta maryam ɗin, ta saka hotunan sun fi goma, kodayeke wata kusan ta fi wata, dan haka ummi ta goge. Tamkar jira yake ta goge, ya ce "Meyasa ki ka goge status ɗinki?" "Bakomai". "Akwai dalili mana, saboda Maryam ko?". Abun ya bata mamaki, kan ta yi magana ya sake turo wani saƙon ya ce "Muna tare take nuna wa mami status ɗin naki ai, ita take saka miki data da zata ce ki cire abu kuma ki cire? Ina ruwanta, ko haifarki tayi da zata bani umarni ki bi? Akwai mutane a wurin ne ya san na ƙyale maganar, ƙarewa gobe in Allah ya kaimu hira za ayi da ni a wani gidan jarida. Dan Allah ki daina bari ana raina mini ke bana so" Karanta saƙon nasa ta din ga yi, tana ƙoƙarin bawa saƙon damar yin tasiri a zuciyarta, amma ta kasa. "Dan Allah ki sake duba wani hoton, ki ɗora ni ki yi mini addu'a, tun da ba ki je taron ba Please". "Yanzu ka gama cewa a daina sani abu in yi, ai ba kai ka saka mini data ba" ta tura masa tana dariya. Emojin dariya ya tura mata ya ce "Ta kaina zaki fara kenan? Ni ki ka raina ko?" "Kai ka mayar da ni haka ai, ina salihata ka koya mini surutu". "Dama can kin iya abinki" "To na ji, sai da safe bacci nake ji" " ya kaimu" ya rufe data ya ajiye wayar, ya lumshe ido yana tuno moments ɗin su tare, ba zaka taɓa cewa ummi na magana ba, dama ce kawai ba ta samu ba, amma tana da baki sosai". *** Alhaji Tahir kallon mami yake yi, bayan ta gama kora masa bayanin abun da take so. Ta kalleshi ta ce "Wai ya ka yi shiru kana kallona ne?" "To ai abun ne na ji shi banbarakwai, guda nawa raihan ɗin nawa yake zaki ce ayi masa aure yanzu? Daga ɗora masa wannan ɗawainiyar sai kuma ki ce ayi masa aure?". "To ai shine cikar kamalarsa, ya samu matsayi ya zamana yana da iyali, dole zai nutsu ya mayar da hankalinsa, ko so ka ke na saki jiki shima ya lalace? Ni dai dan Allah ka taimaka ka amince" Alhaji ya ce "Ai ni bani da damuwa, in dai ya amince yana so shikenan, Allah ya sanya alkhairi" "Yauwwa, dan Allah ka tayani shawo kansa, ka san ko budurwa ba shi da ita, ko zancen na yi masa sai ya sha kunu, dan Allah ka tayani lallaɓa shi, ko da Safiyyar Anty rakiya a haɗa shi" Ya kashingiɗa ya ce "Wannan ba hurumina bane, kin san takura wa ɗa ba ya cikin tsarina, ku tattauna kawai" Tayi ajiyar zuciya ta jinjina kai. Mami ta din ga fargabar tunkarar raihan da maganar, haka nan ta dake da safe ya shiga gaisheta zai fita office, ta ɗaukko masa zancen, aikuwa ya haɗe rai, ya ce "Dan mami ki daina wannan zancen, abokaina kowa ba wanda yayi aure sai ni, kawai na tsufa da wuri, kuma matar ma ki rasa wa zaki zaɓar mini sai wannan marar kunyar, ni ba zan auri matar da ba zan iya tanƙwarata ba, yarinyar da bata da kunya, ni bana so". "Raihan, cikar kamalar mutum iyali, ace kana da wannan matsayin baka da aure, ai sai a rainaka, kuma ganin kai baka da ko budurwa ya sanya na zaɓa maka, aure yana ƙarawa mutum kamala" Ya ce "To mami na ji, amma dan Allah ki ƙyaleni, idan lokaci yayi zan yi miki magana zan yi auren, amma ni yanzu wallahi ban yi niyyar yin auren ba, kuma da kaina zan samo budurwa da zan aura, ummi ta ce in nutsu in samo mace ta gari". Cikin mamaki mami ta ce "Wacece ummi kuma?" Ya miƙe tsaye ya ce "Kar ki damu mami, ni dai ki bar wannan maganar" "Wallahi ba zan barta ba, dole ka yi aure dan ba zan zuba ido ka lalace a banza ba, ko wata ta lallaɓa ta lalataka ba, wato ni nake yi maka kallon salihi, har mai baka shawara ce da kai a waje?". "You should thank God, shawarar kirki take bani, ita ta saita ni a hanyar da na ci jarrabawar Alhaji" daga haka ya fice ya bar falon. Abu kamar wasa, raihan har ba ya son shiga sashin mami, dan ta fara hura masa wuta, shi ko zancen ba ya so. Yanzu Ummi haɗuwa da raihan yana bata wahala, saboda yadda aiki ya saka shi a gaba, ba shi da cikakken lokacin kansa. Yau ya kirata a waya ya ce mata zasu fita, zai zo ya ɗau excuse a wurin manager. Da azahar ya zo ya sameta, lokacin ta gama aiki, tana ta tsokanarsa MD, yayi mata shiru yana hararta. Ta bashi wayarta ta ce "Raihan, dan Allah ka buɗe mini Instagram" "Me zaki yi da shi?" Ta ce "Kallon abubuwa zan din ga yi" "Wai wannan wayar taki, da ke da ita waye ya girmi wani? kalli yadda ta ci ƙaniyarta" "To sai ka bani taka ai" tayi maganar tana hararsa. Ya ce "Kin samu, ciro mini layukana ki ɗauka" "Ni da wasa nake yi, ka buɗe mini dan Allah na kasa buɗewa". Raihan ya ce "Ke Instagram ba zai hau wannan dattijuwar wayar taki ba, ai na ce ki ɗau tawa, ba abun da zaki ce na baki na hanaki" "Da wasa nake yi maka, ka buɗe mini" tayi maganar tana miƙa masa wayar tana ɓata fuska kamar ƴar yaye. "Da gaske na bar miki wayata ummi, kawo wayar taki mu yi exchange na layukan". "So kake ace na fara sata ko? Me nake sayarwa da zan mallaki wannan wayar?" Ya ce "Sai ki ce ke ƙawar MD ce" "A'a nice ma MDn, tun da ba zaka buɗe mini ba shikenan" ya karɓi wayar ta ta yana dubawa, ya ce. "Tashi muje mu dawo da wuri" "Ina zamu je?" "Budurwata zan sai wa wasu kaya, mu je ki tayani saya, za ta yi ki a jiki, bana son na sai mata wanda zai yi mata yawa". Ta harare shi ta ce "Kuma saboda ka raina ni, da ni zaka gwada? Daga baka muƙami ka fara kule-kule, guda nawa ka ke da ka fara yin ƴan mata" wani irin kallo yayi mata, tayi shiru, ta zata maganar da tayi ne, ta ɓata masa rai. Shi kuwa hoton da ya gani ne ya bashi mamaki, hotonta da noor, gashin kanta kamar aljana. Sai dai yayi tunanin ko sakawa tayi, amma ina ummi take da wata wayewar saka gashi. "Tashi mu je" ta tashi tabi bayansa, a ranta tana fatan Allah ya sa ba haushi ya ji ba. Ita kanta mamakin kanta take yi, yadda take bin raihan duk in da ya ce suje, ba tare da musu ba, yanzu ta daina fargabar shiga motarsa, kodayeke zuciya na son mai kyautata mata, kuma bai taɓa yi mata wani abu na rashin ɗa'a ba. Suna tafe a motar, ta ciro leda a jakarta ta ce "Gashi, dama ina ta jira mu haɗu, kuma saura ka ce baka so, sai ka je gida zaka duba" Ya amsa mata da "To babbar yaya" Wani ƙaton shagon sayar da kayan sawa suka je, suka shiga raihan suka gaisa da matar da ke shagon. Ya nuna mata ummi ya ce "Yauwwa hajjaju, ban san size ɗin da take sakawa ba, amma ga wata mun zo tare da ita, ki bata ta gwada, idan dai ta yi mata dai-dai, ita ma za ta yi mata. Matar ta ce "Masha Allah, bisimillah, muje to ka zaɓa sai ta gwada". Tarin abaya ne a wurin da suka je, kala-kala na kece raini. Ya kalli ummi ya ce "Zaɓo ɗaya wadda za ta yi mata kyau sosai". "To ai ban san ya take ba, ko wanda ta fi so ba, fara ce ko baƙa?" "Ina ruwanki da kalarta? to black beauty ce" Ta tsaya ta kalleshi ta riƙe ƙugu ta ce "Daga baka office, ka fara kashewa ƴan mata kuɗi ko? Alhaji ya sani?" Raihan shima ya riƙe ƙugu ya ce "Yau nake ganin ikon Allah, ke ina ruwanki ne? Wai ce miki aka yi ɗan zaman banza ne ni? Ɗauki muje akwai in da zamu je". Wata blueblack ta ɗaukko mai matuƙar kyau, matar ta nunawa ummi in da zata shiga ta gwada rigar. Tsayawa ta yi a gaban mudubin ɗakin, tana ƙarewa kanta kallo sanye da rigar, yau dai sau ɗaya a tarihin rayuwarta, ta saka doguwar rigar abaya da take matuƙar burgeta. Ta riƙe ɗan kwalin rigar a hannunta, ta zubawa mudubin ido, ta tafi tunani, ta zubawa mudubin ido, tana hango rayuwarta ta baya a ciki, cike da tozarci da ƙasƙanci, da rashin galihu kamar mara amfani, shigowar raihan rayuwarta ya bata lokacinsa, duk hankalinsa saboda kawai ya sakaya farinciki. A ranta take addu'a 'Allah idan ina da rabon yin aure a duniya, Allah ka kawo mini miji na yi aure, kar na yi aure na kasa rabuwa da raihan' saboda sosai take jin sa a jikinta. Ummi bata san adadin daɗewar da ta yi a tsaye ba, saboda gaba ɗaya ta bar cikin hayyacinta. Raihan gajiya yayi da zaman jiran ummi, kawai ya ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin amma shiru, kawai ya tura ƙofar da sallama. Kamar gunki ya ganta a tsaye hannunta riƙe da ɗan kwalin rigar, hawaye ya wanke mata fuska. Sandarewa yayi a tsaye, ta saka siririn ribbon ta ɗaure gashin, ta sake shi har tsakiyar bayanta. Ganin raihan ta cikin mudubi daf da ita ne, ya sanya ta dawo hayyacinta a razane, kokowar rufe kanta ta fara yi. A hankali ya saka hannu ya ɗaure zaren rigar ta baya. Ya saka hannu ya kamo gashin da ya sauka a bayanta, tsigar jikinta ce ta tashi, ta waiwayo da sauri, ƙare mata kallo yake yi. Rigar ta yi cif a jikinta, dirarriyar mace ce ta gaske, baƙar fatarta kawai mutane suke kallo, amma daga ƙirjinta zuwa ƙugunta komai dai-dai jikinta, kasa daina kallonta yayi, karo na farko kuma da yau ta kalli raihan a wani abu daban ba ƙaninta da take yawan faɗa ba. (Team a bamu daga farko, ku yi Allah ku din ga dubawa a watpad Please 🙏) Ayshercool 08081012143 What's app only *CUTARWA!* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* P28 FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK. https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu Abduljalal Wata kissar sai mata Wuta a masaƙa Cutarwa Ƙanwar maza Gaba da gabanta Aƙidata Ruɗin ƙuruciya Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata. 08081012143. And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link. https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Ayshercool. PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI. 28 Ajiyar zuciya ya sauke, ya sanya hannunsa a aljihunsa, ya ciro wayarsa. Ya shammaceta ya fara ɗaukar ta hoto ta cikin mudubi. Haɗe rai ta yi ta ce "Meyasa zaka shigo mini ba izini? Ni ka fita" "Na yi knocking, na kuma yi sallama, duk baki amsa ba, kin bar ni a tsaye ina ta jiranki, kin shigo kina kuka, idan ma dan in bar miki rigir ne ki ke kuka, ba zan baki ba, fito mu tafi" Ba tare da ta saki fuska ba, ta ce "Ni ka fita na cire rigar" Ya basar ya ce "Ki batta a jikinki, ki zo mu tafi". "Dan Allah ka fita na cire" tayi maganar a raunane tana ɓoye jikinta. A hankali ya taka ya nufi hanyar fita, ya sake waiwayo wa, tana tsaye jiran ya fita ta canza kayan. Ya fita ya koma reception. Ba ƙaramar kunya ce ta kama ta ba, ganin da yayi mata a haka, gashi dai doguwar riga ce, amma ta kasa manta irin kallon da yayi mata, da ya sanya ta shiga wani yanayi da ba ta san menene ba, gaba ɗaya sai ya canza mata, kamar ba raihan ɗin da ta sani ba. Ta mayar da hijjabinta, ta fito da rigar a hannunta, matar ta kallesu ta ce "Rigar ta yi?" Ya ce "Eh, bamu wasu kalolin a haɗa da wannan, su zama biyar sai takalmi uku da zai shiga da kowacce" komai da ummi aka gwada, kuma ba ta kawo komai a ranta ba. Ɗan nazarinta ya din ga yi, ko fushi take yi da shi, amma ya lura kawai ta tsorata ne, ta kasa sakin jiki ma tayi masa magana, dan abu ne mawuyaci ka ga ummi ta yi fushi, dan zai iya cewa bai taɓa ganin tayi ba, idan ma abu bai yi mata daɗi ba, sai dai ta yi shiru. Suna tafe a hanya ya cigaba da yi mata hira, kamar bai ga komai ba, yana koɗa kyan da kayan suka yi. Sai dai gaba ɗaya shima jikinsa yayi sanyi, basarwa kawai yake yi. Wani restaurant suka je, yayi reserving VIP, aka kawo musu abinci kala-kala, amma ummi ta ce ba za ta ci ba, ya gama kawai su tafi ita hankalinta yayi gida. "Amma mussman saboda baki je walimar nan ba na shirya mana wannan" "Sai ka ce wani film, ni ka yi sauri mu tafi, kar na je gida na kasa kare kaina". "Da na san zaki watsa mini ƙasa a ido, da ban kashe kuɗina ba, i did all this because of you" Ta ɗan kalleshi ta ce "Ni ban taɓa cin abinci a waje ba, dan Allah ka yi haƙuri" Raihan ya ce "Zan fita na baki wuri ki ci, amma idan ki ka yi mini haka ba zan ji daɗi ba". Ƙarshe dan kar ya ji haushi, da ƙyar ta cakala ta ci, suka tafi gida. A hanya yake ta ce mata tayi ƙoƙarin rarraba CV ɗin ta, ko Allah zai sanya ta samu wani aikin da ya fi wanda take yi. Ta ce masa zata jarraba yin hakan. Raihan ya dage sai ya mayar da ummi ƴar gayu, ta hanyar kaita wurare da zasu ɗebe mata kewa, ba tare da ƙetare iyakar addini ba. A ɗan fitar nan da ummi suke yi, take ganin mata kala-kala, masu dressing kala-kala, ba ta sani ba ko rashin shiga cikin mutane ne ya sanya ita duk ba ta iya wannan abubuwan ba, hatta ɗaurin ɗan kwalin da ta kan gani a kan mata yana burgeta, amma ita ba yi take yi ba, daga aikin gida sai makaranta ba ta da wani hope balle tayi tunanin wata kwalliya. Da Raihan yaje gida ya duba ledar da ummi ta bashi, sabon agogo ne kar, da links sai littafin azkar babba, da carbi counter. Ta yi rubutu kamar haka "Allah ya taya riƙo mai girma MD, wannan ce gudunmuwata, ban san me kake buƙata ba, amma ina fatan ba zaka raina kyautar yayarka ba, Ummi" Ya yi murmushi a hankali ya ce 'Kin rama kenan, a taƙaice kin dawo mini da kuɗina' Ya kirata a waya, sai dai wayar a kashe. Ya kashingiɗa yana tuno ummin, mussaman ɗazu da ta saka doguwar rigar abaya, tayi wani irin kwwarjini da kyau, daga cikin abun da ya ɗau hankalinsa dogon gashin ta har tsakiyar bayanta, ya fara tunanin anya ummi ba ta haɗa dangi da wani ahali na yankin ƙasashen ƙetare ba? Idonta da gashinta, sun nuna hakan. "You are beautiful fa ummi" ya faɗa a fili ba tare da ya shirya yin hakan ba. Dubu talatin ɗin nan da ya bata, dubu biyu ce tayi saura, dan sai da ta saya wa kawunta turare, ta saya wa Abdul, sai ƴar ɗakinta wato noor, har da su farida, amma kausar ta yatsuna fuska ta ce Allah ya kiyaye ta shafa wannan abun kamar ƴar bori, suka bar ta da abun ta. Duk da abun da suka yi mata, ummi ta ji daɗin murna da addu'a da dr. Yayi mata, hakazalika Abdul ma yayi mata addu'a sosai, mutuniyarta kuwa kasa zama wuri ɗaya tayi, dan ƴar tsana ta saya mata. Ummi ta yi mamakin yadda aka yi kuɗin ma suka isheta, ba ta taɓa tunanin haka yi wa mutum kyauta yake da daɗi ba, ayi ta yi maka addu'a. Kwanaki biyu da fitar su ita da raihan, tana ɗakinta tana tilawa Abdul yayi sallama, ta kaste karatun tare da amsa masa. Ya miƙa mata ledar hannunsa, ta karɓa tana kallonsa bakinta fal tambaya. Kan tayi masa tambayar ya ce "Wani guy ne muka haɗu a waje ya ce na baki, wani ɗan dogo mai haske" gaban ummi ya faɗi, ta san ba wani bane face raihan. Abdul bai sake yi mata wani bayanin ba, ya fita daga ɗakin. Jikinta na rawa ta hau duba kayan, dogwayen riguna nan ne da suka sayo, har takalman da komai. Da sauri ta tashi ta leƙa ƙofar ɗakin, ta tabattar babu kowa, me raihan yake nufi ne? Wannan kayan idan aka tanbayeta ta ce a ina ta samu? Layinsa ta fara kira, ya ɗaga a nutsensa tare da amsa sallamar da tayi masa. "Raihan, shine ka bawa Yaya Abdul wannan kayan ya kawo mini, idan aka tuhume ni a ina na samu me zance? Kar ka janyo mini matsala fa" "Kar ki ji komai ki ce ni na saya miki, saboda na fuskanci kina so, budurwa ce ke ba tsohuwa ba, dan haka mace sai da kwalliya, ni ina da yayye da ƙanne mata, duk in da mace take tana buƙatar kulawa, a kan buƙatunta na yau da kullum, kar ki ji komai yayata, ki yi kwalliyarki dai-dai da addinin musulunci, Allah ya kawo mana abokin rayuwa na gari" maganar sa ta ƙarshe, da yayi addu'ar sai ya ji wani abu mara daɗi a ƙasan zuciyarsa. Ya kashe wayarsa, ummi ta bi kayan da kallo, ina ma zata iya amfani da kayan nan, ta tashi ta kulle ƙofar ɗakin, ta ɗauki kayan tana gwadawa ɗaya bayan ɗaya, karo na farko da ta ɗauki jambakin da yasa mata wancan karon, ta ƙara tisa shi a kan jajayen laɓɓanta, ta saka kwalli a idonta. Ta ƙurawa kanta ido a gaban mudubin, ta din ga

Chapter 27 of 54