Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
halaccin dakikayi mini,banda kamar ki har abada,kuma ke kadai nake so ke daya kwal. Haka ya yi ta fada mini maganganu masu dadi da kwantar da rai, har zuciyata ta dan sauka. Yaya ya fito ya fita,ni kuma na kira Anty Abida na fada mata, ta ce hakan ya yi in ta haihu ya aure tan zai fi sauki a bakacin ta haihu ta ba ku yaron. Na ce, To ya zan yi tunda shi ya janyo. Nan dai muka yi sallama nafito na kuma dora abinci,sai dai ina gamawa ita ma ta soma dora nata,ban damu ba tunda neman sulhu muke. Misalin hudu yara suna Islamiyya suka shigo shi da Usman falo suka zauna, na kawo ruwa da abinci.Usman ne ya sha ruwan shi kam gogana har wata 'yar rama ya yi, ya kalle ni ya ce, Kira yarinyar nan. Na ce to. Na daga labulen dakin yara tare da yin sallama, ba ta amsa ba sai dai ta dago ta dube ni,rufdaciki ta kwanta kan katifar su Kausar tana chatting, na ce, Ki zo in ji Mijina. Ta yi min kallon kishi zan ce ko na tsana, sannan ta ja tsaki. Ni dai na juya na ce musu tana zuwa. Zan tafi Yaya ya ce in zauna, na samu guri na zauna. tafi minti shida sannan ta fito,munyi jugum-jugum kamar masu zaman makoki, ta tsaya kerere , gani. Ya harareta .Kizauna mana kin ce wani gaki? Ta zauna tare da fadin .yau kuma da wacce aka zo? Duk muka yi shiru, irin zaman nan da ake cewa mutuwa ta ratsa. Can Aliyu ya ce"Usman wannan ita ce Mujidat,kuma na maka bayanin komai,dan haka sai ka dan ce wani abu".Usman yace"bani da ta cewa,sai dai ke.ya nuna Mujidat,karkisake kice zakici zarafin wannan baiwar Allah ko nan gaba "yakalli Aliyu"ya kamata wannan ya xama cikin sharudan da zaka gindaya" Aliyu ya kalli Mujidat"na yarda in kin haihu zan aureki, amma ki sani so daya tak inayiwa matata ne,dole ki bata girma da daraja,musamman data soma bazaman aure ba, sannan zaman haihuwarki ina gani can wani waje zan nemamiki haya" cikin sauri na ce ban yar da ba, ai ta zauna anan, kada a dinga zagayawa "Usman yace "haka ne kuma,amma kina ga batakura? Na ce "bakomai" Mujidat dadi ya rufeta ,kuma nan take ta nuna murnarta, ta kuma sake bayyana tsantsar san data ce tanawa mijina,dan haka dole tazauna dani, ban bari ta kai karsheba natashi nayi kicin abina.tsayawa nayi tsakiyar kicin shuru,anya kuwa ban yi wautaba?ban zalunci kaina ba?ban debo rvmuwan dafa kaina ba?amma sai wata zuciyar tace kedai kada kiyi wannan tnanin, tunda kin sadaukar da kimai ne dan asirin mjinki y rufu,Allah ya sani Zuciyarki daya da ita,kuma Allah zai shige miki gaba. Nasauke ajiyar xuciya nace Allah gani gareka,sai da suka fito ne naji muryar Usman na cewa"Madam na tafi"nace "ka gaida min su Ummulkhairh dasu walida"yace xasu ji. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 A ranar Aliyu ya koma Abuja,sabida an dameshi da kira,gida ya koma sai ni da ita saikuma yarana,a daren nan naje na fadawa Iya yanda muka tsara zancen,tayi ta tausaya mata,tare da shiwa yaya albarka tace ai gara daya taho da ita,tace in an barta sai ta koma ruwa, tabar musulinci, nace "ai shine" Iya tace Allah sarki, naxo in yi mata ta'axiyya,banda abinku, daba nan kuka kawota ba? Tunda ni kadai ce?nace"Iya ki barta can kawai,sabida bata jin Hausa sosai" tace"to shkenan ,kema Allah ya biya ki" na ce amin. Daren ranar mun kusa rabashi a waya yaya yana shimin albarka tare da yi min alkawuruka kala- kala na riqe ni amana,tare da kyautatamin daji dani duk wani dadin zaman aure,har sai da aka kira shi, yace minxai fta gurin aiki1 nce Allah ya tsare. Haka muka zauna da Mujidat,bata min magana,sai dai ni in mata.innayi kamar in shareta,sai na tuna da haramcin gaba,dan haka in lokacin sallah yayi tana falo sai in ce mata"lokacin sallah yayi" wataran tace"to"wataran tayi min banxa ,sai dai ko ta amsa ba dole ne ta tashi tayi sallar ba.abinci kuwa,da kanta take yi,takanyiwa yara magana,amma ba wai wasaba, sai dai in tana san abu tace kai bani kaza, ko ke bni kaza. Sun dameni wai yaushe wannan bakuwar zata tafi? bata da kirki su suna san ta tafi,nce musu bazata tafib,Antyn su ce baban su ya kawota ,kuma tana da kirki,dan dai yanxun bata da lfy ne shiyasa.suka yi shiru badan sun fahimce ni ba,intaji fita tana san zaga gari sai dai kawai inga ta fice bako mayafi. Sai dai nayi masa waya nce ka fada mata in zata fita ta dinga saka hijabi ko mayafi, saboda an ce ta musulunta, in tana fta haka asiri zai tonu.ya ko kirata yace ta kiyayeshi.kar ta bari tayi abinda zai toxartata,tace ita bata da hijabi.yayi min waya wai in bata hijabai guda 2, sannan yace ya hanata fta,kuma ta sani ya zuba masu sa mata ido a unguwar, dan kar tai xaton cewa xata fita wani gantalinta ta dawo masa gida,ko kuma zata yo wani mugun abun.tace karya damu,dama ita burinta aurenshi, kuma tunda ta samu bata da matsala da wani namijin can waje, tana zuwa matsa jikine. Duk wani zaman kunci na dauka a zaman Mujidat, sai dai ban damu sosai ba.ganin Aliyu baya sakar mata fuska sosai.komai tace masa tana so sai yace ta tambaye ni,bai cika zuwa gidan bama, sai daiyazo ya debemu da yara mu tafi can Abujan, akwai lokacin da sai da muka yi sati uku saboda yara sun samu hutu. Ranar da muka dawo har da shi ,mun samu ta tana kuka wiwi, wai bata da lafita,nce masa muje Asibiti, amota fadi yake Allah yasa ckinnan ya fta, na ce dan Allah kabari, ka mata addu'ar alkhairi, bayan dogon bincike likita ya gano tana shan maganin tari na yara,wanda mata da maza kan sha sabida su yi maye. Likitan ya ja kunnanta da cewa in ta ci gaba d sha za ta kashe danta. Muna hanyar dawowa gidan na ce, Ki daina kada ki je ki yi sanadin rayuwar danki. Na dube shi. Kayi mata magana ta daina shan pakalin. Ya ce, 'Ina ruwana, ta yi ta sha indazata mutu ma kina ganin ba zan fi son haka ba? Ta ce, 'Eh, na san dama haka za ka ce, kuma sai na haihu lafiya. Na ce, 'Inma banda ke mene ne abin sha cikin maganin mura? Ya ce, 'Ai ba za ta daina rayuwar bariki ba. Ta yi shiru tana nazarin dalilinta na sha,tsabar son shi ne da take yi. Shi kuma ya kwashe Iyalan shi suka bar mata gidan shi yasa take sha sabida rage damuwarsa, ga shi ashe za ta janyo makanta ne, 'Yar shigarda ta samu a watse, don ta san in cikin nan ya zube shi kenan korarta zai yi batada sauran garkuwa za ta jure ta ci darajar dan da za ta haifa. Ta shiga wata bakwai lokacind ta cewa Yaya a waya wai tana son ta fara zuwa awon ciki, ya ce ta fadan in ta matsu.kin fada min ta yi sai shi ne ya tambaye ni. 'Mujidat ta yi miki batun awo? Na ce, 'A'a,ya fada min yanda suka yi na ce 'Ka bari sai ka zo sai mu yi zancen gani gata, in ya so sai a je Asibitin a kuma sayi duk wani abu d ake buqata. Bai amsa min ba ya canza zancen da cewa, 'Akwai wani bincike dazai kawo ni Kaduna me zan samu? Na ce, 'Duk abin da ka ke so. Ya ce, 'Yanzun ina takura sosai a gidana in na zo zan dauke ki mu fita a wani masaukin bakin mu dan' huta. Na ce, 'Yara fa? Ya ce, 'Ga gidan Iya. Na ce, 'To ma tafi mu bar mai ciki, kar a yi na wancan karon. 'A yi ta yi mana, ina ruwana, daman na san haka za ki ce. Ya ja tsaki tare d kashe wayar shi. Na sani tabbas rayuwarmu ta canza yanzun, amma wayaja? Shi ne. Allah yasa mu dace, ameen. Wata Asabar Aliyu ya nufo gida, yana karya kwanar unguwar su sai ya ga jama'a cirko cirko tsaitsaye gungu gungu, wadansu kuma suna ta maida yanda aka yi,yayin d kunnan shi ke dauko masa sautin wasu muryoyi suna ihun neman dauki. Kasancewar shi jami'in dan' sanda dole ne ya bincika, don aikin shi ne kare rayukan al'umma da dukiyoyinsu, ko da ba a unguwarsu ya ga hakaba, dole ya tsaya. Don haka ya gangara gefen titi yayi Parking din Motarsa,yana fitowane wasu matasa sin tsaya suna dan tattauna batun,Aliyu ya usa gurinsu fare da yi musu salllama,suka amsa,ya fambayesu abindake faruwa,daya matshin yagane Aliyu dan haka yace "yallabai wallahi 'yan sara sukane" Aliyi yace 'yan sara suka kuma? Yace eh! Wasu matasane ance daga hayi suke suka fada layinnan suma sara da sukan duk wansda suka ganiyanunamasa inda cincirindonbjama'a ke tsaye yace 'can meshayinnena Buba suka soka,sannan suka sari me lemun kysa dashi" Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Aliyu ya isa gurin daidai ana kokarin sashi amota yace "bakuyiwa yansada wayaba" ?wabi yace "tin dazu muka sanar dasu" Aliy yadagawaya yana sake miran yansanda yana shedamusu cewa a turomasa mota sabida 'yan sara suka sun sgigo ungywarshi ,shine yavasu damar kai masu jikin Asibiti sannan shikuna yacigaba da gudanar da bincike jafin isowar yansanda. Tanbaya yaitayiwa mutaben gari kan yansara sukan;kasancewar mutanwnmu akwai tsoro da rashin cikakken wayewa ga wasu sai zuka mi bashi cikakaken hadinakai.sannanda yanufi motaesa dan karasa gida,sai yaji wasu matasa biyu suna magana,dayan yanacewa, "kasan Allah Aminu su Dawa Adone suka jamana wannan bala'indashi da Bangis Kauri" Aliyu yace "Kanina kananyfin Dawa Ado din tsokanarsu yayi? Duk suja waiwayo suka kalli Aliyu,ganinshu da nayan Yansanda sai sukace a'a bamusaniba,suka juya da nufi.n tafiya Aliyu yace tsaya kuji absan cewa kunsan wani abu,dan Allah kubani hadinkai.Dayan da akakira Aminu yace,'mufa zabcenmu daban, 'yansanda basu da amana,dazarar kafadi wata magana sai reshe yajuye da mujiya a kama mutum a tsare" Aliyu yace ba gaskiya bane,shaci fadine da shrri irin na wasu mutane suke jifan jami'an tsaro dashj,mu masu kare rayukan Al'ummane da dukiyoyinsu bawai masu sharrib,kudinga bamu hadin kai,tahakane zamu iya gano bara gurbin al'umma." Dayan wanda kebada labarin yace, yallabai yallabai tsorona kada a kirani shaida,suganeni insun fito suzo su sassareni". Aliyu yace "sam sunanka bazai fitoba, vabu wanda yasan munyi haka dakai." Yadafashi. "Kagama zo nan mushiga daga mota dan kar wasu sugane kaine kafadamin,kayarda ba cutardakai zanyiba,taimako zanyi,kaga in ba'a dauki matakiba zasu iya dawowa.Zaka iya sanin ko kanwa tsautsayi zai fada?nasan kanada dangi,da mahaifanka, sannan ga kanka ko kanada yakinin cewa bazasu dira kankaba? Saurayin yace "hakane yallabai" Syka shiga Mota harda saurayin da dayan yace Aminu. Aliyu ya kalleshi yace 'kanina kai ya sunanka? Nasandai abokinja shine naji ka kira da Aminu" Yaron yace "Buhari' Aliyu yace 'Buhari wane Dawa Ado?' Buhari yace "Dan dabane,sunada yawa a ungywarnan,saidai su da bangid sune sukai kauri suna a ungywarnan" Aminu yace, "wasuma sunce gudansu Dawa Ado ana siyar da wiwi,wasu yarsu dake zaman kanata agubta yake ajiyewa". Aliyu yace "to mene labarin wannan fadan?" Buhari gace,"to nidai mundawo Masallaci jiya da Magriba dayake layinmu daya da Dawa Ado,sai naganshi zaune tare da wasu yandaban, ,yaranema wadanda basufi shekara sha shida sha biyarba,yana fada musu cewa zamu fadawa 'yan hayi har naji ya anvaci sunan wani dan daban hayin yanacewa lallai yanaso ayimasa yankan da bazai tashiba,ko yatashi kada ya moru.Nidai na wuce nabarsu,saidai ina zaton kan wiwi ne sjke fadan, dan naji yanacewa "ankawo mishi kaya kafin yazo shi wancan ya siye" Aliyu ya girgiza kai alamun gamsuwa yace, to yanzu kuyimin kwantabcen gudansi Dawan dakuma Bangis din, ' sukace to. Nan sukayimasa kwatance yacuro kati mai dauke da lanbarsa a jiki ya basu,. "Gashi kusa lanbobina a cikin wayoyinku,sai ku kirani ko kumin flashing inkira dan insamu taku lanbara,kunsan dalili? Sukace a'a. Yace dan kucigaba da bada gudun mowa cikin hnguwar nan,duk lokacin da kukaga wabi abu mo kukaji makamancin wannan sai kuyi maza kukira daya daga cikin wadannana lanbobin. Ya sanya hannu ta baya yaciru yan dubu dubu guda biyu ya mika musu tare da cewa,"Ba cin ganci vane kyauta nabaku,aikinmuma dazakuyimin ba na kudibane taimakon kaidakai zakuyi." Da murna suka karba, sunyj masa godiya,take nan suka bashi lanbobinsu,sannan suka gangara inda suja nunamasa gidansu Dawa Ado da Bangus Kauri.sanna ya gan ga ra ya ajiyesu ya wuce hidansa. Likacin d na ji kwankwasa kofar ina kicin ina kokarin dafawa yara Indomie, don ni a koshe nake Iya ta aiko min da dambu, nacishi sosai bayn La'asar shi yasa. Na nufi kofar cikin raina ina tunanin ko waye? Ina bude kofa na yi sororo don bai fada min zai zo ba. Na ce, 'Oho! Abin 'Yar haka ne? Ya shigo, sannan ya rufe kofa, ya kamo ni ya rungume, na karbi jakarsa muka nufi ciki. Mujidat tana zaune a falo ta ce, Sannu. Ya ce, 'Yauwa. 'Ba tare d ya kalletaba. Muka nufi dakinsa ina fadin. Kausar, Al'amin ga fa babanku. Da gudu suka fito dga dakina, muka dunguma dakinsa mu duka. Na ce daka fada min kana zuwa Allah d tuni na yi maka abnci na musamman. Ya ce, 'Ai rikici na tarar a unguwar shi yasa da tuni na iso. Na ce, 'To yanzun me za ka ci? Ya ce, Me ki ka dafa? Na ce, Ban dafa kmai ba, yanzu daizan yi wa yara indomie,sai dai muna da miya a fridge sai na dafa maka farar shinkafa. Ya ce, 'A'a ku tashi muje gidan cin abinci. Na ce, 'To ka canza kaya mana, ko kuma ka yi wanka. Ya ce, 'Duk yanda ki ka ce. Na dubi Kausar 'Mu je in ciro muku kaya ki sa musu sai ke ma ki sa.'Na dube shi. 'Bari in ba su kaya. Gira ya daga min na fita. Na dawo na taimaka masa ya yi wanka. Ya shirya, nima na canza kaya, duk Mujidat tana zaune a falo tana kallonmu, sai na ji tausayinta ya tsirga a raina, na ce, 'Ki tashi muje cin abinci. Saida ta yi min wani kallo, sannan ta ce, 'To. Mun fito sai ya Aliyu ya ganta, ya ce, 'Ke fa? Da sauri na ce, 'Tare za mu je mana. Tsaki ya ja,sannan ya ce, 'Ni yanzun ba nida damar sakewa kenan? Ban tanka masa ba, a raina na ce wa yaja? Lokacin dakuke shanawar ku ai ba ka ce an hana ka sakewa ba. Da farko yaso mu ci a can,amma yanzun sai ya ce kawai mu yi take away sabida bai so zuwanmubada Mujidat. Daga nan sai ya nausa da mu can gurin kasuwar Bacci, wani katon shagon saida kayan wuta, na ce me za mu yi anan? Bai kula ni ba don na lura ya ji zafin zuwan Mujidat. T.V ya sai mana ta bango (Plasma),mai kyau sai tsada,sannan ya sayi resiba,ban san inda zai sa ba. Sannan muka je wani babban store ya kwasarwa yara kaya har da keke ya saiwa Al'amin. Yara sunata murna muka isa gida. Ita dai mujidat duk inda muka je da Ido take binmu, tare da yatsina fuska,jifa jifa tana tabe baki tare da tsaki. Ni dai muka yi ciki ta zauna a falo. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Dakina ya kai T.V, na ce ba na ka ba ne? Ya ce, 'A'a naku ne,don na lura ke da gidanki,amma kin bar wa wata falon ki. Na tsura masa ido, 'Yaya na gode. Ya harare ni, Lokacin fa dakika samin suna kin yi alkawarin kirana Sweety Alinki,amma yanzu sam kin daina na manta rabon da ki kira ni dawannan sunan. Na ce, Yi hakuri Sweet dina. Sai na ji su Kausar da Al'amin sun sa dariya.Kausar ta ce, Momy Abba ne Sweet? Muka kalli juna cikin dariya na ce, 'O.K, waton kun tsaya jin mu ne? Al'amin ya katse zancen da cewa, Abba wai ita Anty bakuwa sai yaushe za ta tafi? Kausar ta zabga masa harara, 'Ina ruwanmuda wata can Anty Bakuwa. Muka sake kallon juna cikin mamaki. Na lura fa Kausar ta tsani matar nan. Nace, Kausar ai ba tafiya za ta yi ba ita ma ta zama 'yar nan gidan. Kausar ta zaro ido, 'Ta zama 'yar gidan mu kumma? Ta tura baki,ni dai Abba ta koma gidansu, kullum sai ta dinga hararata, ko kuma tayi ta hana mu kallon T.V. Na ce to ba ga shi Abbanku ya siyo mana wata ba? Ta yi shiru. Na ce, 'Kar ki sake yin haka. Ranta a hade ta ce, to Momy. Mun ci mun sha muna ta hira har yara suka yi bacci, sannan muka gyara masu kwanciya, sannan muka nufi dakinshi.Yayo alwala tare d cewa. Je ki yo alwala muyi Isha'i. Na yi murmushi , sannan na ce, Wanka zan yi don ina fashin sallah. Ya runtse ido tare d fadin, kash! Ga shi gobe zan tafi. Na ce, Kar ka damu zan yi maka irindabarun da muka sabayi da. Dariya ya yi, sannan ya ce, shi kenan. Da safe ni mkadai ce na fito na hada abin kari, sannan yara suka ci suka fito. Babansu yana kwance na ce 'Bari in kai su makaranta. Ya mike. 'Yau ba Lahadi ba? Na ce, 'Hadda suke zuwa Asabar da Lahadi. Ya ce, 'To ki yi sauri ki zo ki kara yin wata dabarar. Na yi masa hararar wasa. 'Bashi yasa na ce amAuran Mujidat zai taimaka maka ba ya hade rai, sannan ya koma ya kwanta. Na dauki makullin motarsa. Bari in ari motar ka. 'Nan ma bai tanka ba. Lokacin da muka tafi Mujidat tana soya kwai a kicin, na cewa Kausar su je su gaida ta. Kullum dama sai na sa su sun gaishe ta, kamar kullum sai d ta yatsina fuska sannan ta ce, Lafiya. 'Na fita abina. Mujidat tana ganin fitar Sadiya da yara sai ta maida kofar ta rufe,sannan ta nufi dakin Aliyu yana kwance sai ya ga mata tsaye a kanshi tana girgiza. Zumbur ya mike tare d fito falo, don gudun kar ta kara janyo masa wani laifin a kan na da. Ita ma ta biyo shi tana yi masa kallon banza kana tsoro kada matar ka ta dawo,shiyasa ka fito kar ta same mu tare.ta yi 'yar dariya. 'Ai ka gama kuskure tunda har kayi ajiya a jikina na zo in yi maka gargadi ka rage nuna tsana da kyama gare ni, in ba haka ba na rantse maka zan je gidan mahaifiyarka in tona komai. Aliyu ya ce,'Ai har abada ba zan so ki ba, kin ci darajar matata data dage sai kin zauna da mu, banda haka ke din banza. Ta tuntsire da dariya, 'Ai ba ka san wani abu ba, ai ita kan ta matar taka sa'a ta ci d ta kasance mai son kwatanta adalci, banda haka wallahi da sai ta raina kanta a wannan zaman da nake yi a gidan nan, don sai dai inmu dinga kwana da kai gado daya.ya harare ta, Ni kuma da yake zan tsaya ne ina kallon ki har ki shigo mini daki,kuma ki sani ni Allah ya shirye ni. Ta ce, 'Oho! Yanzun kana tsammanin cewa kai wani shegen mai imani ne? Ta yi murmushi mai sauti,sannan ta girgiza kai. 'Abu daya zan fada maka shi ne ka gode min da na kawo shawarar auren ka,sannan ka godewa matarka da ta yarda da in aure ka,ta samawa kan ta lafiya don wallahi da sai dai ta sallamawa kan ta domin matsawar ina numfashi duk inda ka ke sai na bi ka,kuma sai ka yi duk yanda naso. Ya gyara zaman shi sannan ya ce, 'Kin yi kadan shaidaniya. Sannan ya kautar da kai.sam bai tsammaci zuwan ta ba,sai dai ya ji ta a jikin shi 'yar barikin ta san lagon shi,wanda baya iya bijiremata, zuciya muguwar nama har za ta amince,amma sai Aliyu ya yi ta maza ya hankade ta duk d tana da ciki, sannan ya ajemata mari a fuska,ta shafa kumattun tana kallon shi bayan ya mike yana mata kallon banza,ta yi 'yar dariya. 'Dubi yanda idanunka suka canza launi, ban da cikin jikina da sai na tabbatar maka cewa in ina nan dole ka rayu da ni,Kasa ba ta amsa ya yi kai tsaye ya nufi dakinsa ya shiga ya kullo kofa,sannan ya zauna bakin gado tare da rike kan shi ya ma rasa wane irin tunani zai yi.Can kasan makogwaron shi 'Hasbunallahu Wani'imal Wakil yake fadi can a hankali ya ji kmai yana warewa, ya kwanta rigingine ya tabbatar cewa Mujidat shaidaniya ce, za kuma ta yi duk abin data fada, auranta kam shine mafita, inbahaka ba zata jashi zuwa wuta,tunda in tana raye bazai fasa zinaba.Yadauko wayar shi ya soma kiran layin matar shi. Ina daf da gida naji wayata tasoma ruri, nayi kwana,sannan na daga. 'Yaya dai Sweety Aly? Ya ce, 'Ina kikene? Kin san dai daga ni sai wannan shaidaniyar a gida. Gabana ya fadi, sam ban tuna haka ba,nace 'ga ni nan yaya ina daf da gida. Ita ce ta bude min gida lokacin da na buga,sai dai tana bude min ta juya a raina na ce, 'Hakan ma nagode. Na aje mota,sannan na nufi ciki. Zaune na same ta tana sanye da dogon wando na jeans, sai 'yar best yanayin shigarta na bata min rai, musamman in yaya yana gari. Na murda kofar na ji ta a kulle, na kwankwasa ya bude na bi shi da kallo, don son in fahimci wani abu, amma ban gane ba, don haka nace. 'Lafiya? Ya dube ni, 'Me ki ka gani? na ce, 'a'a bakomai.naga kakirane na dadene? Ya ce, 'a'a, kin san ina jiranki ne a sake yi min irin dabarar jiya.nayi dariya, 'ai bana batun dabara barima inyi wanka don ina zaton anjima zan yi sallah. Damurna yace, 'Haba? Na ce, 'Allah. Ya ce to shiga ina jiran ki. Saidai kuma ina fitowa na same shi zanzare cikin kakinsa yana daure takalmi, sororo na tsaya cikin mamaki kafin nayi magana sai wayarsa ta soma ruri,ya dauka da sauri. 'Buhari inajinka. Daga inda nake na jiyo wanda ya kira da Buhari yana cewa,Yallabai muna zaune ya wuce kamar yanda nasoma fadamaka dazun, shi Dawo Ado, malun malun yasa yana riqe da Adda sannan malun malun din ta jike sharkaf da jini. Aliyu ya ce, 'Dan uwanka Aminu ya kira ni ya fada min wai 'yan sara sukan nan sun ce za su sake shigowa anjima, zan fito yanzu. Yana 'aje wayar ya dauki dayar ya kira headquater ya buqaci a turo masa 'yan sanda mota biyu. Ina mamakin yanda Yaya keda izza cikin aikinsa, yanzun nan ya rikide daga soyayya ya kma zakin maza,ya kama kofa zai bude nace "Sweet aliy ka manta daniko?" ya waiwayo da sauri, sannan ya dawo ya rungumeni jikinsa ya sumbaci kumatuna"ya za'ayi na manta dake? Ashe zan iya mantawa da kaina kenan?ya dago fuskata"sai na dawo"na saki murmushi"Allah ya tsare min kai mai sona"ya sakeni ya fta da sauri. Sun kama Dawa Ado,Bangis Kauri, sannan suka dinga fadin sunan yan daban suna kama su.kazalika sun dire hayi,inda can ma suka kamasu da yawa,ya mikasu yakuma basu shawara cewa suyi bincike kan yaran sosai.sannan su tabbata sun mikasu kotu. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Hakanan da dare ina Sallah a dakina,misalin takwas wanda yanzun yazama na yara,Kausar da Al'ameen suna kwance ruf da ciki suna Homework ,Aliyu ya shigo da Sallama,suka amsa tare dayi masa sannu da zuwa,ya kalli Mama dake bacci can gefe yace"wai shin mamana tayi nata Homework din ne? Kausar tace"eh Abba sunyi tare da mumy"dai-dai lokacin na kammala addu'a ya tayani shafawa, na kalleshi"sannu da zuwa" cikin murmushi nayi maganar yace"yawwa,sannu matata"muka sa dariya, ya rusuna saitin kunnena yace "kisa yarannan suyi bacci da wuri" kafin in bshi amsa wayar shi tasoma ruri.ya daga da sauri,nji yana fadin "Yes Sir" nace Allah yasa ma zaiyi kwanan gdan yau. Ilai kuwa, yana gama wayar ya kalleni" yanzunnan zanwuce Abuja" na zaro ido"Abuja kuma da daren nan?" yayi dan yake"aikinmu kenan, ahaka muka yi rantsuwa babu dare ko rana,duk lokacin da aikin yataso zamu fuskance shi"na lumshe Ido ahankali nace"yanayin aikinku yana shafar rayuwarku"ya mike zumbur"muje ki hada min kayana" Kausar ta tashi zaune"Abba bari muxo mu rakaka motarka"nace "a'a , ci gaba da Homework dinki in yashirya zaizo har nan sai ku raka shi," tace to. Tara dai-dai ya kammala komai,dan ban amince ya tafi bai samu nutsuwa ba, sabida tsoron kada shaidan ya sake ribatarsa ya kuma kyallo wata,lokacin da muka zo gurin su Kausar tini duk sunyi bacci. Ya tsuguna duk ya sumbaci kumatunsu, sannan ya dauki hanya,na raka shi mota,sai daya tashi sannan na koma ,ban tsaya wani tunani ba na kwanta don Inda sabo na saba da tafiyar Yaya cikin dare, sai dai Adduar Allah ya kare min shi. Kusan sha biyun daramen wata litinin na jiyo ihu cikin baccina, na tashi da sauri ashe nakuda ce takama Mujidat. Da gudu na fada cikin dakin tana zaune dirshan tana juyi da ihu, na ce ta kwanta, bari na gani ko mota ta da mai. Kafin na dawo har kan da ya fito sai ihu take har su Kausar sun tashi nace mota ta ba mai bari in kira Iya. Na kira ta na fada mata, tacebari ta taho tind dare bai yi Sosai ba. Kai Mujidat akwai raki, har nadaina Jin tausayinta, sai dai haushi.Kafin Iya ta shigo dan ma Ya fito, masha Allah jariri sambalele, sai dai abin ya yi ta fadar da gaba na yadda naga yaron tamkar Yaya. Iya ce ta yanke cibi sannan muka gyara ta tsaf da danta. Kusan 3 dare suka samu bacci, Ni da Iya muka koma dakina. Ta dubeni. "Sadiya!" na kaleta da faduwar gaba. Tace, "jaririn nan baki fahimci komai ba?" Na girgiza kai "A'a iya ban fahimta ba. Bashi da Lfy ne?" Tace, a'a kama naga yana yi da mijinki sak, tamkar an tsaga kara, ko 'ya'yanki basu yi kama da shi ba kamar wannan yaron, tsorona daya Kar dai ace Gadanga ciki yayowa wannan yarinyar. "Nayi saurin cewa, "a'uzu billahi! Iya ba kyau ayiwa mutum mummunan zato, kin San wannan ba halin Yaya bane". Ta ce 'eh, to haka ne, amman fa mutum yakan canja daga halinshi da aka San shi dashi." na ce, a'a fa iya ita fa wannan da mijinta, kafin ya mutu mun sha gaisawa da shi. Kuma shi kamanni hakayake sai kiga baku hada komai ba amman Kuna kama." ba don Iya ta gamsu ba tace to Allah yasa hakanne. Na ce ameen. Nan mukayi alwala muka kama nafila, addua ta Allah ya rufawa mijina asiri Kar duniya ta gane wannan matsalar. Da safe lokacin da na shiga dakin tana zaune da danta a hannunta ta tsura masa ido tamkar ba ita bace tayi ta kurma ihu ba. Na ce 'kin tashi?" ta ce, 'eh mun tashi, kin ga yarona sai kace Babanshi, naji dadin haka,Dan bazai sake min musu cewa ba cikinsa bane." da sauri na ce, 'kibar maganar nan mana, yanzu bari kuyi wanka in na kai yara makaranta sai nazo na

Chapter 9 of 25