Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shiga, yana kwance kan gado da waya a hannunsa, da Alamu cht ya ke yi.Kausar ta dan tsaya nesa dasu kanta a kasa.Al'amin ya zauna bakin gado,Mama ta hayekan gado, ya rungume mama da Al'amin sanan ya tashi zaune.Al'amin ya gaida shi, Mama ma cikin hausarta mara dadi ta gaida shi.Ya kalli kausar daga inda take.Zo nan.Ta tafi, ya janyota zuwa jikinshi, ta ce ina kwana?Ya ce, ba zan amsa ba Kausar har sai kin fada mun me mamanku ta ce maku nayi, kuke jin haushi na?Kausar ta ce ba ko mai Abba, Al'amin ya ce ta ce ne fa muzo mu gaida kai.Ya kalli Kausar, yanzu kunfi son mamanku fiye dani ko?Al'amin ya ce, muma ka daina son mu Abba.Ya ce, ok, haka mamanku ta fada muku?Kausar tayi saurin cewa momy bata fada mana haka ba, ta ce ne kawai muje mu gaida ka.Ya dungurewa Kausar kai yar karama da ke kin iya munafunci, ba zan kara yi maki tsaraba ba.Ya kalli Al'amin, in ba ka daukar maganar mamanku zan sai maka keke kana so?Al'amin ya kama murna ina so Abba.Ya kalli mama, mama na ke kuma in se maki motar ki ta wasa ko?Na juya kicin ina kuka, mutumin nan zai raba mun kan yara, zai kafa min jam'iya yan partyn shi da nawa.Jin takun Kausar yasani share hawaye, cikin sheshekar kuka ta ce, momy kinji Abba zai sayawa su Al'amin da mama tsaraba ban dani.Na tsugunna na rungumota jikina ina shafa mata kai, yi hakuri Abbanku wasa yake yi miki zai siyo miki kinji?Ta ce, Allah momy da gaske yake yi ba ya cein fitar masa daga daki ba?Na ce, yi shiru zai sai maki.Da kyar tayi shiru.Na bata jug na ce, kije wajen Iya ki ce mata in ta dama koko ta baku, karfa ki ce mata wani abu ya faru kinji?Ta ce to.Ta tafi nikuma na zauna a kicin cikin ta gumi.Kausar ta sami Iya kwance ta gaida ta, ta ce kausar menene?Ta ce, wai in kin dama koko ki bamu, iya ta ce shine aka turoki ba Abbanku ya dawo jiyaba?Me yasa bai rakoki ba?Tayi shiru Iya ta ce to muje in se maki koko gidan ladi me koko dan kulluna jiya ya kare, kice mata na ce a jika maku gero tunda jifa jifa kuna shan kokon, ban cika son abin siya ba.Sam iya bata fahimci bamu da komai a gidan bane, tunda lokaci zuwa lokaci sukanje su amshi kokon.Ta samu masu kosai sanan ta rakata har kusa da gida.Tanaji tana fadan turota ita kadai a wanan safiyar, ta ce da uwarku tana tattalinku amma yanzu duk ta canza,na rasa me ke damunta.Suna shan koko da kosai kausar tana fada min sakon Iya, na jika gero na ce to za a jika,suka gama na dauki Mama na nufi kaisu makaranta, kusan wata guda a kafa nake kaisu makaranta, don mota tuni nayi fakin dinta gefe na rufe ta don ba mai ba na da kuma kudin siya.Ina dawowa na tarar da shi da Usman zaune yana karantowa Usman laifuka na.Na gaida Usman na shige daki, na hau gado na kwantawa,bawai don bacci ba ko don hutu, sai don tsabar ta kaici.Can na jiyo muryarshi yana kira na, ya kalle ni.Kin san na fada maki ba zan dauka ba ki rabani da yara na ba.Jiya na shigo gidan nan wai Kausar tana yin fushi dani yar karamar yarinyar nan.Al'amin yana fada mun na daina son su, tayaya zan yarda wanan tunaninsu ne?Usman ya daga mishi hannu saurara aboki na, ka barni in gama magana ta don kada kakatse ni.Usman ya kalleni,Sadiya me yake faruwa ne?Na runtse ido don ta kaici, yaya Usman duk abin da ya faru Abban kausar shine sila.Na koro mishi komai tun daga farkon rigimar har zuwa yau.Sanan na ce yaya Usman tsakani da Allah kullun yaran nan suna kallon muna fada, ko ince daga yazo sai shiga tashin hankali zasutashi da tarbiya me kyau?Ya ce, a a.Na fada musu yanda mukayi da malamansu. Ga rashin abinci wane laifi na masa, ni dai yanxu tunda gani gashi kurun ya fada min laifi na, wlh zan bashi hakuri mu koma kamar da yaran mu suma su sami natsuwa.Usman ya kalli Aliyu, aboki kaji, sai ka fada mata laifinta don matsalar tazo karshe.Aliyu yayi mun wani kallo ke dai kawai baki son zaman lafiya ne, duk ki dauki damuwa da bakin ciki kisawa kanki.Sau nawa zan fada maki baki yi mun komai ba?Usman ya ce, to na rokeka aboki ko mai ya wuce.Ya runtse ido tare da fadin shi ke nan.Na dube shi nima in sha Allahu ko mai ya wuce.Usman ya ce, Alhamdulilla, yanzu sai ka tashi mushiga kasuwa don nima abincin gida na ya kare.Nan dai suka fita.A cikin mota Usman ya kalli Aliyu.Aboki ka canza fa,Aliyu ya kalleshi wacce irin canzawa nayi?Usman yayi murmushi sanan ya maida hankalinshi titi.Kayi kiba sanan dabi'un ka sun canza.Aliyu ya kure Usman da ido, zaiyi magana kenan wayarsa ta soma ruri, ya ciro ya kurawa Screen din ido,sha wara yake ya dauka ko ya yanke,Usman ya kalle shi, daga mana abokina, Aliyu ya katse kiran sanan ya kalli Usman,daga jin kira sai kace in daga ba tare da kasan me kiran ba?Usman ya ce, jami'in tsaro zai ji shakkar daga kiran koma wanene.......Kiran yasake shigowa, sai kurun Aliyu ya dagadan kada Usman ya dago abinda ke faruwa.Ya ce, yaya?Mujidat ta ce, muryarka nake sonji, nayi kewarka da yawa, don Allah ka dawo yau.Tana magana kamar zata yi kuka, salon dake narkar masa da zuciya,take ya manta da wa yake tare har ya furta cewa.Kada ki damu gobe kamar yanzu muna tare,ta ce, to Zaki na sai mun hadu a internet.Sai da ya salameta sanan ya tuna yayi baram barama.Ya dubi Usman wanda bai ce kala ba, ya soma nade tabarmar kunya.Wata abokiyar aikina ce, muna gabatar da wani aikine.Usman yayi murmushi sanan ya ce, sau da dama in mutun ya shiga aikata rashin gaskiya sai kaga ya zama makaryaci.Ita ko karya illar ta da kayi so daya kafin ka fitar da kanka sai kayi kusan sau goma.Aliyu ya kalle shi, me ya kawo wanan zancen?Usman yayi dariya, ka tsargu ne?Aliyu ya kalli gefe, intsargu da me kuma?Usman ya hade rai, tsayar da halayenka haka nan Aliyu.Ya gangara gefe titi yayi fakin dazu nake ce maka dabi'unka sun canza ko? Aliyu ya kalli titi muje zuwa da maganarka, in wani zai fada mun aboki ba zan yarda ba, amma gani ina zar ginka cewa kana hulda da matan?Aliyu ya kalleshi da sauri, haba aboki, nasancewa zaka iya bada shaida cewa ban kasance mai shiga lamarin da mata suke ciki ba, bare har inyi hulda dasu.Usman ya ce to amsa min wadan nan tambayoyin.Aliyu ya cire hankici, ya share zufar fuskarsa sanan ya ce, ina jinka.Usman ya ce, na kira layinka sau uku wata macece take dagawa.Na farko da dare ne gurin karfe dayan dare, don in fada maka rasuwar kanwata, sai kawai wata mace ta daga wai ka shiga wanka.Na biyu da safe wata jumma'a don mu gaisa ta ce ka fita gurin masu gadi, na uku gargadi tayi mun in san lokacin da zan dingakiranka yanzu kana cikin halin da bazaka iya daga waya ba.Sai na soma lissafi giya kake sha da har ba zaka iya daga waya ba, koko menene?Sanan ita wanan matar yakuke da ita har zata kasance a inda kake ciki tsakar daren nan .In zuciyata ta zargeka sai wata ta shaideka da cewa ba aikin ka bane, abin da bakayi ba kana yaro ba na zaton cewa zakayi shi da girmanka.Amma yau da matarka take fadin yanda ka kaurace mata, sai na amince kana neman mata, don kai ba me hakurin zama baka tare da mata bane.Aliyu ya hade rai tare da duban Usman, me cece shaidar ka ta zahiri?Duk abin da kafada bai zama shaidar da zaka amince ina bin mata ba.Ba zan iya zama ba mace ba, shekaru nawana dauka can baya babu auren?Usman ya ce kila lokacin baka san amfanin matan ba,amma ni shawara daya zan baka, inma zakayi harkar bariki to bai kamata ka wulakanta matarka ta sunna ba.Aliyu ya ce, dan Allah mu rufe wanan firar.Usman ya ce kafin mu rufe sai nayi maka nasiha duk da cewa bani da tabbas akan zargin da nake yi maka.Na san mutun yana canzawa kamar yanda wahainiya take canzawa zuwa duk kalan dataso.Nasihata gareka in ka canza daga fari zuwa baki don Allah ka saki wanan layin ka koma dai dai ko don gudun zunubi, ko don tsoron azabar Allah.Ko don kare mutuncin yayan mu, ko don kare lafiyar ka daga cututukan zamani.Sanan maganar zubewar daraja da kimarka a idon wayanda suka san kanayi. Aliyu ya runtse ido cikin in ina yace, muje aboki don Allah.Suna tafe yana share zufa, lallai zancen Usman ya shige shi. Ko mai na abinci zuwa kayan tea sun hada muna, lokacin da suka dawo ina kwance kangado ina karanta littafin gidan zahra.Sau da yawa in ina karanta littatafan Hausa sukan debe min kewa halin da nake ciki, har na sha cin karo da irin matsala ta.Sun ajiye min kayan abinci suka sake ficewa, na fada kichin na shiga girki, yarama da suka dawo makaranta sai murna suke sun sami lafiyayen abinci.Yaushe rabon muyi girki da kifi ko nama, yau gashi har farfesun kan rago mukayi.Da daddare na fada ban daki na sake wankana sheka kwalliya duk tunanina yau za a shalabari.Sai dai muka kwanciya ya juyya min baya, na gaji hakurina ya kare don haka na ajiye kunyata na fada masa cewa, yau ni ina son a faranta min.Ya ce, shi gaskiya baya jin zai iya wani abu yanzu don duk a gajiye yake.Nace, haba yaya, nima fa mutunce kamar kowa, sama da wata hudu ka juya min baya.Baka tsoron sharrin shaidan?Ya tashi zaune a fusace, kina nufin zaki bi maza? Iye? Fadamin zaki bi maza? Nasauka daga kan gadon, ban ce zanyi zinaba yay, amma zuciya bata da kashi, in na kasa jurewa fa?Na durkusa kan gwiwowina, yaya ka taimake ni ka fiddani wanan yanayin, ka tuna ni ban taba gudunka ba.Ya mike ya dauki filo.Sai da ya kai bakin kofa sanan ya ce, ina ganin kina cikin fitunananun mata bari naje falo in kwana. Rufda ciki na kwanta a kan gado ina kuka, wani mai kunci daga bisani na dangana na fada ban daki na sakarwa kaina ruwan sanyi yayi ta zuba tundaga tsakiyar kaina.Ban fito ba sai da naji sanyi yana ratsani, na fita naje kan gado na dukunkune sai zazzabi da ciwon kai.Haka na kwana har safe da kyar nayi Sallah na sha magani, sanan na fita kicin.Shi kam a ranar ya koma kusan karfe biyu ina kwance ya tsaya kaina wai ni fa zan tafi.Ba tare da na dago ba, na ce Allah ya tsare, ya ajiye kudi a gefe na tare da fadin, motarki an gyara na ce uhm. Duk da cewa Aliyu yana kirana a waya mu gaisa yanzu duk abinda muke bukata yana kamantawa, sai dai ya barni cikin kewa.Haka nan ko a waya da mun gaisa shi ke nan sai ya ce in bashi yaranshi suyi magana,ba wata hirar soyaya ko ta rayuwa bare in sa rai zamu koma kamar da.Duk da cewa yanzu yaran nan sun dan saki jikinsu sai dai duk da haka da sun ganni cikin takura ko damuwa yanzu zakaga sunyi mun narai narai tamkar zasuyi kuka.Ni dai a bisa halin da nake ciki gara ace bukatun ya dai na yi mun ya bani kulawa da soyayya sunfi mun duk wani abin duniya da zai sai min.Na hakura ne saboda DARAJAR YAYA NA, sam bana so in zube su inyi gaba.In ban rike suba naje can inyi wahalar yayan wasu. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Wata rana naje kitso inda nake zuwa a can layin zage-zagi wani gida, gidan haya ne maidauke da matan aure da dama.A kulun naje gidan ina karantar abubuwa na rayuwa da dama a gurin matan gidan.Farko matar dake yi mun kitso, sau da yawa mijinta in yadawo bata iya sakin kitson taje gurinsa.Haka zai gaji da zama ya fito ya dauki bokiti ya ja ruwa yaje yayi wanka.In kuma da abinci ya ci ya fito in ya ciro kudin cefane ya bata sai ta amsa a raine, yauma da nazo kitson hakan ne ta kasance.Ya bata dari biyu ta juyata sanan ta maida masa tana fadin gaskiya malam bazata isa ba.Ya ce ba da garin tuwo ba, kuma naga manja?Ta ce yau kwana uku muna tuwo, ta kalli yaranta dake gefe suna wasa.Habu kunji babanku wai yau ma tuwo sai suka rugo da kansu gaskiya baba yau bazamuci tuwo ba.Ya ce to me ni dai kudin nan ke nan.Ta ce, ko tuwon ne ma kudin nan ba isar muzaiyiba, ya ce haba Tasallah, ba kifi ba nama kice dari biyu baza tayi miya ba?Ya shura takalminsa yayi gaba.Ta daga murya sai dai ayi maka ciko kuma kana zuwa zaka bani kudi na.Yaran suka hau mita, shi baban nan kullun tuwo.Na kalleta cikin mamaki sanan na ce, na kusan daina zuwa kitso gurinki, ta ce zaku tashi ne?Na ce a a na ce nagaji da yanda kike daukar mijinki ba a bakin ko mai ba.Dubi yanda kike sa yaranki suna yi ma mahaifinsu rashin da'a da raini, wanan tarbiya ke nan?Tayi yar dariya hajiya kenan, Allah hajiya ba haka bane, ace mutun kullun ba ci gaba, ba ya neman wata sana'a a caba yake.Na ce, na lura baki da godiyar Allah ta salla. Ranan fa ina kallonki da yaranki kuka ce masa kun gaji da shinkafa, san nan baki sanin mijinki ya dawo ki bishi daki ba..... Allah sarki Rayuwar Aure,kowadai da tasa matsalar,damadai haka Rayuwar take,tanada manyan matsaloli guda hudu wadanda duka daya takan haddasa rashin jin dadi daga bangare daya,Immadai -: Mijin baya jin dadin zama da matar,misalin Tasalla me kitso da Mijinta,kokuma... 2:Matar ake zalunta ,Misalin Aliyu da Sadiya,Kokuma ... 3:Suna zaune lafiya a junansu, Amma dangin matar ba kaunar mijin,shima Wannan Babbar matsalace a auratayya,Wacce ke Haifar da Babar Matsal..kokuma... 4 angin mijine basu son Matar, wanda nasan da yawanku kunfi sanin wanna matsalar,.. Lallai dukanin gidan auren da suka samu kubuta daga dukkanin matsalolinnan nazama wajibi Su godewa Allah,akarshe Dukkani gidan Auren dake da matsalar makamanciyar wadannan Ya Allah ka kawo musu agaji,mukuma Ya Allah kahadamu da abokan zama nagari Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Zaharaddeen shomar Whatsapp 08168575100 Darajar Yayana2-04 Posted by ANaM Dorayi on 06:34 PM, 29-Mar-16 Under: DARAJAR 'YA'YANA ___________________NA ___________HALIMA K/MASHI Assalamu'alaikum, fatan kuna cikin koshin lafiya... Sagir Ali, Shamsusdden Usman,Fatima Ahsan,Maman Ummi,Shamsiyya,Ummi Amal,Aisha and Aisha Kaka Zanna nagode da kulawarku,sannna inna jin dadin yanda kuke kulawa da shige da ficena,shirun da kukaji yafarune sakamakon ayyuka da sukaimin yawa,fatan zakucikaba da bibiya dakuma hakuri dani. nagode zamu Dora yanzu..... Ruwan wanka sai dai ya diba yaje yayi, wanan rashin dabi'ar har ina?tasake yin dariya, to ni in nashiga dakin in ya dawo me zan masa?Na ce, auran kiyayya aka maki?Ta ce, a a ni na kaishi gidan mu, ta ci gaba kin sani ni gaskiya ko ya dawo bana shiga, shi yanzunnan zaice zai rungume ni, niko na tsani haka,ka debo rana ka wani ce zaka rungume ni, salon su Habu su fado dakin?na ce menene dan yaranku sun ganku rungume da juna?Kai ke dai baki da dabi'a,irinku ne ake kwacewa miji cikin sauki,daga baya kizo kina ya ci amanar ki,ni dai in baki canza haliba zan daina zuwa,ta ce;to Hajiya za'a sake, ai ku hajiya cikin daula kuke baku da matsala.Nayi murmushi Tasalla kenan.Shiyasa na ce, kina da hange, ki kalli kasanki mana,Misali waccan Maman Rashidan kuke ce mata ko wa?Tunda nake zuwa gidan nan bai fi so nawa naga ta daura tukunya ba.Kullun in kazo zakaga yaranta suna cin dumame, ko garin rogo amma ban taba ganin mijinta ya dawo ta barshi ya dibi ruwan wanka da kanshi ba, ko ta shareshi taki shiga daki.Sanan sau biyu na taba ganin mijinta nasan yayi sa'ar mata, duk cikinku 'yan nan sasan da na taba ganin shigowar mazajenku da fitarku ita kadai ke yi wa mijinta sannu da zuwa da yi mashi addu'a in zai fita.Tasalla tayi yar dariya, hajiya kenan, ita waccen ai bata san kimarta ta ya mace ba, in banda haka yaushe zan zauna babu abincin kirki.Amma kina like da mutun kullum sai tayi wankan asuba don jaraba.Na ce, tafi ku godiyar Allah ne da biyayya.Sanan zakuga cigabanta kuna nan, sanan yaranta sunfi naku tarbiya da tsafta.Tasalla ta bata rai,Hajiya mu bar maganar nan, amma ko su maman Auwal zaki tambaya matarnan tana shiryawa yaranta kinaya ne don in mutane sunzo su rinka gaidasu don a ce suna da halin kirki.Na ce, ba wani bayan aike ma ina kallon naku yaran amma baku aikensu don kunsan cewa bazasuba, sai dai ku kira nata.Daga nan Tasalla tayi kus, niko na ce in sha Allahu duk randa zan kuma zuwa sai nayi wa yaranta kwalima tunda naga yaranta basu fi girman su Kausar ba, a raina na raya hakan.Ina Mota na kusa isa gida da motar dama naje gidan kitson da mota ne, sai ga kiran Aisha aminiyata, cikin hanzari na daga ina fadin.Kin haihu kenan? Tayi dariya yau andace kullun na kiraki zancenki daya ne kin haihu?To ga yarki nan a gado.Na ce, Alhamdulillahi ga ni nan.Na kira layin Abban kausar kamar yanda na zata har ta tsinke bai dauka ba, na sake kira.Muryar mace naji cikin harshen turanci tace wakike nema?Sai da sitiyarin ya kusa kufce min, na samu na tsaya tunda cikin unguwa ne, na sake yin sallama cikin rawar murya.Ta ce kina bukatar taimako ne?Na katse layin zufa ta soma tsatstsafo min.Na rude matuka, na kifa kaina a kan sitiyarin ina fadin Allah yasa mafarki nake yi.Na kuma kallon wayar ina shawaran in sake kira ne ko in barshi, sai ga kiranshi ya shigo da sauri na daga amman na kasa magana, Muryarshi ne yanzu ya ce hello!! Dazun bakiyi magana ba sai wata irin muryanake ji.A sanyaye na ce dazun ba kai bane wata ce ta daga.Da sauri ya ce wata wa?A wayata?A'a sai dai in network ne yasa ki kika ji haka.Ya saki zancen da cewa, lfy dai?Na ce eh dama ina dawowa daga gidan kitso ne sai Aisha ta kirani ta haihu.Ya ce wace Aishan?Na ce, ta mamana.Ya ce, Allah ya raya, kin cika son yawo.Na ce to yaya in banje yanzun ba dole in sake fitowa don inyi gabadaya.Ya ce to shi kenan ina yaran?Na ce sunje yiwa iya wuni, ya ce ban son fa kina tafiya ke daya fa.Ko mama bakya iya yawo da ita sai ke daya tsura?Na ce, to yaya sun kwana biyu ne basu je sunyi mata yini ba.Ya ce, to shi kenan kardai kiyi dare don na sanku in kuka sami surutu na ce to. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Bayan ya kashe wayar ya nufi gurin Mujidat da ke zaune kan kujera tana dafe da kumatu, inda Aliyu ya watsa mata mari sakamakon shigowa da yayi ya ganta ta daga masa waya.Ya kalleta in kika kara yi min gangancin daga min waya sai na mugu saba maki, don zaki koma inda kika fito.Ta mike tsaye kana jin tsoron matarka ne don kar tasan muna tare ta ce ta fasa aurenka?Cikin gatse Aliyu ya ce haka ne.Don haka kada ki kara daga min waya.Ya juya ya shiga dakinsa rai a bace.Mujidat ta mike tsaye tana kai kawo, wai mutumin nan yana nufin duk son da nake masa yafi son matarshi a kaina?In ma yana boye mata ne sai nayi sanadin da zata sani, in sha Allahu.Sai dai ta mutu ko ta bar mun shi, don na yi imani na fita son shi, zanyi komai don naga na rabasu da makircina kawai,ta hada yatsanta babba da na tsakiya taja suka yi kara, wanan wata Alama ce da take yi duk lokacin da ta ma kanta Alkawarin aikata wani abu cikin izza.Ni kam kwana nai da motata zuwa gidan Aisha, amma zuciyata cike take da wasi wasin abin da kunne na yaji wai netwok ne.Anya kuwa ba binne ni yaya yayi da rai na ba?Nayi murna da ganin Aisha cikin koshin lafiya tare da jaririnta.Na dauki yarainyar ina juyyata, mashaAllahu,Bello ya fiki karfin jini daga ita har Najib shi suka biyo.Na ce haka dai su mama suka ce, na ce, ina angon karnin?Ta ce ya fita na kwantar da yar na kalleta a Asibiti?A gida kafin ya samo mota har kai ya fito.Innarsu da mamanmu da ma suka zo sai kurum suka amshi haihuwar, na ce shi kenan Allah ya kawo shi cikin sauki.Na nufi wata kula dake gefe, na ce me suka barararaka miki?Na bude kular, ta ce tuwo ne, miyar kuka, kinsan tsaffin nan sai suce wai maijego sai da tuwo.Muka sa dariya, na ce a ni na horu da tuwo gurin Iya, haihuwar kausar har wani baki nayi nayi muni dan uban nan.Muka sa dariya.tace, ai daga baya Anty Abida ta hada maki sabulu, na ce ai ta min kokari yanzu ba abin da bana hadawa da kaina.Ta ce zaki hada min sabulunma nace to, haka mukai ta fira har shida, sanan mukayi sallama naje gidan Iya na kwashi yayana muka tafi gida. Na kasa bacci cikin dare sai juyyi nake kaso hamsin da daya na zuciyata, yaya Aley yayi min.Tabbas zan zama wawiya in ban amince yaya yana neman mata ba.Yaushe rabon da ya dora yatsansa kan nawa?Kullun dare ina kwana da kewa, hawaye na suna kwaranya.Na tashi zaune in ko haka ne wane mataki zan dauka.Zuciyata ta dauki zafi ina fidda wani huci, lallai in ya kasance haka zamuyi rigima ba karama ba, don ba zan dauki wulakanci a kan matar banza ba. Washe gari da safe ina ta tunanin yanda zansake cewa yaya zan sake komawa gidan Aisha, saboda in na haihu kulun tana hanyar har ayi suna.Amma ni ko haihuwar Najib dinta banyi mata wani sintiri ba, yaya hanawa yayi.Kuma bana son fita batare da izininshi ba.Don nayi imani shi baya kallona Allah da ya halicceni yana kallona.Text na tura mashi cewa zanje gidan Aisha lokacin suna tare da Mujidat suna karyawa.Ya dauka ya karanta, sai ko ya hade rai ya soma kiran layi na na daga.Tunkafin in karasa sallama na ji ya ce, ban amince ba kullum fita, saboda ki dinga kallon maza ko? Na zaro ido na mike da sauri na nufi daki dan su Kausar suna nan gida don anyi musuhutu.Kuma bana so suna jin matsalar mu.Ya ci gaba da fadan shi, na ce wacce irin magana kake yi yaya?Don in dinga kallon mazaje fa ka ce?Kana nufin in na fita haka nake yi?Ya ce, oho miki, amma ban yafe ba in kika leko waje, nace naji ai tunda ka hana ba zan fita ba, amma cewar da kayi wai ina kallon mza nike son inji hujjar ka.Kana ga don ka shuka fulawa ta fito kaki kayi mata ban ruwa sai ta mutu?Na ci gaba, haka ne zata mutu amma kasani ni nasan DARAJAR YAYA NA.Ko don su zan kare mutuncina kai shaidane budurwa gar ka bare ni a leda, ka san haka kuma kullun ina Adu'a Allah ya kare ni daga sharrin zamani.Ban jira amsarshi ba na kashe, sanan na fada kan gado ina kuka.Sai kurum naji hannun kausar a baya na tana fadin.Momy kiyi hakuri ki kyale shi.Da sauri na share hawaye na taso kausar bana ce in ina waya a daki ba ku daina biyo ni?Ta ce momy ki daina daga wayar Abbanmu, ko ya kiraki ni bana so yana saki kuka.Na ce naji muje Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Kwana uku da yin sunan yar gidan Aisha ya ta ci sunan Fateema, sai ga yaya da rana tsaka ina mamakin yanda yanzu yake son yimin dirar mikiya.Ko yana zargin ina fita ne?Oho.Nayi masa sannu da zuwa ya amsa na ce, baka fada ba gashi banyi abincin rana ba.Jiya sun bar shinkafar da na dafa da dare, sai kawai nasa a firiza yau na duma ma, amma bari in maka ko macroni ce.Ya ce barshi bani da yunwa, in na fita zan siyo fura.Sai da yayi bacci sanan ya tashi yayi wanka ya fita.Duk ina dakina ina karanta littatafi ,tinda nalura bai bukatar ganina kusadashi, nima hakan yafi min sauki don in yana gari nafi jincewa nima macece in kwana cikin kewa.Washegari ya fita zuwa gidan su Iya na dauko jakarshi, don kwashe kayan wanki wanda ya dawo dasu kamar yanda na saba.Ina daga suit din shi zan rataye wata takarda ta fado, na dauka har zan maida masa cikin Aljihun rigar sai wata zuciyar ta ce bude mana ki gani, na bude.Yar wasika ce aka rubuta da harshen turanci, ga abin da yake rubuce.ZUMA NA KA TAFI DA TUNANINA, HAR KAJE KADAWO KASANI ZA KA BARNI CIKIN KEWAR LALLAUSAR FATAR JIKINKA.BA ZAN GUSHE BA HAR SAI KA DAWO KA SAME NI CIKIN KEWAR LEBUNAN KA MASU SANTSI TARE DA (YAWUN) KA ME ZAKI.ALLAH YA DAWO MUN DA KAI LAFIYA.....Kafin na kai karshe tuni na jike da zufa, ina gamawa na ga gari yana juya min, ban an kara ba sai dai naji ni a kasa ribin jikina a gado rabi a kasa.Kusan minti biyar sanan na tashi zaune sa sake karanta takardar ina kuka wiwi har da majina tabbas yaya mata yake bi,domin takardar ta nuna haka, mata ce kawai ya dace tayiwa mijinta irin rubutun nan, wata zuciyar ta tambaye ni ko dai ya sake aure ne?Duk da uban kishi na sai nasami kaina da cewa inda ma auran yayi zanfi son haka, da bin matan banza.Na soma kaikawo cikin gidan ina tunanin matakin da zan dauka.Shawarar wa zan nema?Na shiga dakina na fada kan gado na dauki wayata na shiga kiranshi, amma sai wani tunani ya fado min.Bari kawai in kira Hajiya Baida'u, marubuciyar littafan da nake karantawa danneman shawara.Dan ita bata sanni ba balantana inyi zaton zancen zai iya yaduwa, sanan tana da basira nasan zata sani a hanya.Ringing na biyu ta daga, ta daga muka gaisadama na saba kiranta, na ce Anty ina nemanshawara ne.Leta na gani a jakar me gida na wanda ke Alamta cewa yana tarraiya da wata mace.Ta danyi shiru na dan lokaci.sanan ba yan wanan letar kina da wata shaidar?Sanan can dama halinsa ne?Na ce, a to a da can ba na zarginsa, sai da ga baya na soma zarginsa domin Anty kwata kwata ya kaura ce min kusan wata shida zuwa bakwai yanzun,kuma Anty shi mutum ne mai zurfin sha'awa, ba zai iya daukar ko kwanaki ba ba tare da mace ba bare watanni. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Ta ce kuma ba gudan sa kike ba har hakan ta faru?Na ce wlh Anty Allah ya sani ban ta ba juya masa baya ba, har matsalar nan ta shigo.Ta ce, kuma kina gyara jikinki ba ji yayi kin zama wata iri ba?Na soma lissafo mata abubuwan da nake hadawa, ta ce, lallai kina kula da kanki.Na ce, anty yanzu in yazo in fada mashi takardar don yasan na sani?Ta ce, a a tunda

Chapter 11 of 25