Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kinga zarginsa kike yi kenan baki da tabbas, ki boye takardar kuma ko a idonki kada yaga damuwa.Ki bishi a hankali, ki boye sirrin nan tunda uban yayanki ne.In shaAllahu sai kiga Allah ya dawo maki dashi kan hanya, na ce,Anty zanyi yadda kika ce, amma zan ci gaba da bincike.Ta ce, za ki iya amma ki sani tsananta bincike shima matsala ne, don zaki iya ganin abinda zai saki hawan jini, na ce anty in na tabbatar da gaskiyar zan tunkareshi ne in nuna masa nasani.In ma zai aureta ne gara ya aureta da zaman banzan nan, ta ce haka ne, amma kada ki manta da adu'a, na ce insha Allahu, ina magana cikin kuka.Ta kwantar mun da hankali da cewa, ki daina kuka, na ce anty me nene maganin bakin ciki?Ta ce karatun Alkur'ani zuciyarki zata wanke sarai.Na ce, to anty na gode.Muka yi sallama na kwanta nayi kuka sama da minty biyar sanan na tashi na boye takardar na ci gaba da aikina ina kuma ci gaba da kuka.Wanan wane bala'ine Abban kausar ke son jefa ni, ni da 'YA'YA NA?Ya manta cewa duk abin da kayi da Dan wani kaima sai anyi da naka?Da na koma daki sai naji komai nasa kyama yake bani, shi kansa yanzu kyamarsa nake ji, na karasa kwashe kayan nasa ina yi musu kallon su kansu suna dauke da zunubin zinar da yake yi.Tunda su Kausar suka shigo naga sun tsura min ido ita da Al'amin shine ya soma magana.Momy me yasameki a ido?Na ce, ba komai, ciwo yake min.Sai naga sun kalli juna.Na tsugunna tsakaninsu menene?Na tambaye su tare da yin dan guntun murmushi da na kirkiro ko nace yake.Al'amin ya ce, yaya kausar ce tace bata so Abba yazo in yazo yayi ta saki kuka, kuma fa ko an tambayeki sai kice ba komai shi ne nace ai yanzu ya daina.Amma muna zuwa sai muka sameki kinyi kuka, ku,ma muka tambayeki sai kice ba komai.Kausar ta ce, na canka ko Al'amin? Abban nan ni bana sonshi yanxu.Al'amin ya bata fuska, nima bana sonshi, bakin ciki ya turnike ni, bana son kallon da yara suke yiwa mahaifinsu.Nace kausar ku daina cewa bakwa son mahaifinku,bana fada muku in kunyi Sallah ku rinka adu'a Allah ya kawo sauki cikin lamarinba? Allah yana amsar adu'ar kananan yara, sukace munayi sosai Momy kullum. Ko da ya shigo kasa kallonsa nayi, ganinake zan iya cin kwalarsa, don haka na sa kaina a daki na rufe tare da sa sabon kuka.Ya kalli su Kausar, ina mamanku?Al'amin ne ya ce, tana dakinta, yazo ya buga kofar kamar kada in bude amma sai nafasa na bude Ya tsura min ido lafiya?Na kalleshi, me ka gani? Ya ce, fuskarki na gani a kumbure, na taba baki sanan na shafa fuskata.Kila baccin da nayi dazun, ya ce wanan kumburin baiyi kama da bacci ba, ya fi kamada wanda yayi kuka.Na mai wani irin kallo.Don yanzu bani wani ganin girman shi, na ce ai ban san tsawon lokacin da kuka na zai dauka ba kafin ya tsaya.Ya ce to Allah ya kyauta, ya juya tare da fadin to a zo a bani abinci.Sai da na dan bata lokaci sanan naje na shirya komai na dawo abina.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Washe gari ya fita, sai dai duk Aliyu a dame ya bar garin ya rasa gane kukan da Sadiya take zabgawa, nashi ganin bai san yayi mata wani abu ba tun zuwan shi.Rashin kulata ai ba yanzune farko ba, to kukan na menene?Dole Akwai wani abu, abin da yasake birkita masa lissafi yanda ko wayarta yakira sam bata iya dagawa.Rana ta hudu da komawarshi, ya gaji ya kira kayin Usman ya fada masa halin da ya bar Sadiya, da kuma rashin daga wayarsa da take yi.Yamma likis inayiwa kausar kalaba na wanke mata kai ina cewa sai gobe zan kaita kitso, sai ga Usman.Muka gaisa sannan na ce, shigo falo, kausar kuma nace suyi wasa a nan tsakar gida.Usman ya kalleni, mijinki ya ce baki daukar wayarshi, kuma ya tafi ya barki cikin kuka.namike naje na dauko mashi takardar da na gani cikin kayansa.Shi kanshi Usman kasa dago kai yayi ya dube ni, can ya ce, lallai abin da nake zargi ya tabbata, amma don Allah ki kara hakuri kuma in sha Allahu ko mai zai wuce. Yanzu bari inje da takardar nan saboda bincike, na ce yaya kayi hakuri kabar takardar nan a hannuna saboda ta zama shaida a duk lokacin da na masa zancen ya musa.Usman ya ce nima da ma don hakan naso na aje ta guri na, amma ajeta gunki, na amsa sannan mukayi sallama.Ya kira Usman dan jin yaya?Usman ya ce ta ce mun ba komai tana bukatar hutu ne da dago waya, Aliyu yayi shiru, mamaki yake ji, kuma yana ganin kamar da wani abu sun hada bakine ita da usman.Aliyu ya ce, amma bakayi mata fada ba, in ita ta manta cewa mijinta nake ya kamata kai ka tuna mata. Usman ya ce, aboki yanzu kaga aikinike, kasake kirana wani lokacin.Ya katse wayar ba tare da ya jira amsar Aliyu ba.Afili ya furta cewa, tabbas akwai wani abu. Tabayanshi Mujidat ta rungume shi.Dear wai me ke faruwa ne?Tunda ka dawo na kasa gane kanka.Ya kalleta cikin zargi kin sake daga wayar matata ko?Tayi rau rau, wlh Honey ban daga ba, ta somayi masa wadan su wassan ni tana rada mishi a kunci me yasa ba zai mata irin son da take yi masa ba?Ita fa zata iya mutuwa a kansa, amma shi yafi son matarsa da ita.Ya hankadeta tare da fadin dan Allah barni ta yaya ma zaki hada kanki da matata?Matar sunna wacce ke zaune don ni kadai, ta soma kuka tunda na hadu da kai na daina hulda da kowa, nima ina zaune nan ne dan kai daya.Aliyu ya ce, ban tabbatar da hakan ba, tunda dana fita zaki iya fita, ta sake dawowa ta rungume shi, na rantse bana bin kowa kai daya nake so da kauna.Kuma bazan daina sonka ba har na mutu.Aliyu ya zauna kan kujera tare da rike kai, itakuma ta kwanto a kafadar shi.Tunani take yi a zuciyarta yanda zata ban bare ma'auratan. Ina zaune ina danne dannen wayata, nima ina son bude shafin nan na fcbk don ganin me duniya take ciki?Aisha kawata da Anty Abida duk suna ciki har Aisha tana bani labari wai da akwai malamai sosai.In shiga nan in shiga nan dayake ina da karanbani sai gani na bude fcbk, banyi anfani da sunana ba ko adareshi na.Bayan kwana biyu sai ga Aisha ta zo mun yawon Arba'n, na nuna mata ta ce, ai na gani kin turo min sako, na ce yau she?Ta ce duk wadan da kike da numbar su za su gani, in kin bude, na zaro ido, har da Abban kausar?Ta ce sosai ma, amma ba lallai ya lura ba tunda bakiyi anfani da komai naki ba.Ta nuna min yanda zan dinga komai, bayan tafiyarta da dare ina kwance, na shiga fcbk nan na shiga frnds, dinsa, mace daya na gani Mujidat.Na shiga profile dinta hotunan da tasa nata yana daga cikin wadan da sukayi like wani gurin ma har yana cewa kin yi, sanan ga hotunan shi kala kala cikin photos din ta wasu ta rubuta one an only, wasu ta rubuta my Husband.(Tofa) Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Na tashi xaune wai ya aure ta ne? take kaina ya sara, duk da ina cewa gara ace auranta yayi fiye da ya neme ta sai na samu kaina cikin wani tashin hankali mai tsanani.Na soma kiran layin Ya Usman ba tare da na damu cewa dare ya dan soma ba,cikin kuka nike cewa ya Usman ina ganin fa auranta yayi bai fada mana ba. Yace,Habadai wacece? Na karanto masa komai yace, kiyi hakuri ki kwanta zan bincika,kada ki kara hawa fcbk din,kurum ce masa nayi to amma muna yin sallama dashina tura mata frnd request, cikin sa'a ta amshe ni, da yake ita ma na ganta online. Nace ban ga tasa marriage ba amma naga hoton mijinta, ta ce eh za dai suyi auren ne, nace ni yar kano ce ita fa? tace Lagos, amma yanzun tana Illorin a gidan wanda zata aura.Kuka wiwi na dinga yi yanzun menene abun yi? na tambayi kaina, ta tambayeni ina da miji? sai nace mata bama tare, tace ayya, yakamata mu daidaita.Ita in sunyi aure bazata taba yarda su rabu da mijinta ba don tanaji ko uwàr da tahaifeshi bata kaita sonshi ba,ai ina gama krt na sauka daga nrt na soma rero kuka tare da yin danasanin wannan bin diddigin.Alwashi na sha duk randa yazo za'a yi mai yuwuwa. Ba zan zauna ina wulankanta ba haka kawai a debo ciwon zamani a kawo min yarana su zama abun tausayi,na sake zama cool ko yaushe cikin krt alkurani yana wanke min zuciya, don haka yanzu bana daga wayarsa sai dai in yaransa na kusa ya kira na mika ma Kausar nace ta dauka.Ranar Kausar har tambaya na take Mommy meyesa ba ka daga wayar Baban ko yana mki fada ne? Nace a'ah munyi maganar cewa yake in Kundawo zai kira ku ne,a haka muka kwashe wata, ranar kwatsam sai gashi, mamaki da naji banda Mama ko Al'amin bai je ya masa oyoyo ba?nima batare da na Kalle shi ba nace sannu da zuwa, yace Yauwa ya dubi yaran yace Al'amin baku ganin bane, nukamun ganka Abba sannu da zuwa.Yayi cik ba tare da ya amsa ba ransa ya baci sosai da wannan ko in kula din iyalanshi suka mishi,don haka ya dauri aniyar Cima Sadiya zarafi yau dinnan, nasan dole zai yi wannan tunanin dan haka na hada ma yara kaya na kwana daya nace suje gidan Iya su kwana tunda sati ne gobe, suna fita na kulle gidan na shiga fall na kulle kaina na cire key din na nufi daki,ya cire kaya sai gajeren wando zai shiga wanka,nace toh Abba kausar yau fa zamuyita ta kare a gidan nan ko ni ko kai?ya juya yana min kallon mamaki sannan yace ke ina zaton kin soma shan fakalin ko?nace 'eh wai don ma ba Zina nakeyi amma ka bani kunya, ba tsoron Allah ba kunyarshi baka tunanin darajar yayana ka aje karuwa a gidanka Kuna fasikanci,saukar Mari naji tau,sannan yace in ji wane makaryancin, na rike kuncina ka mareni Akan wata 'yar iska, toh bazan iya zama da fasiki ba ka dinga azabtar dani a kan karuwa na warware gefen zani na ciro yar takarda na mika mishi, ga aikenta zuwa gareni, sannan na dauko wayata na same shi yana krt takarda duk jikinshi yayai sanyi, nayi maza na fito da pics dinsu da nayi saving, wannan ma karyace ba hoton ku bane?na soma kuka ka cuce ni ka cuci yarana haka kake nufin ayi ma Kausar?ya daka min tsawa kina hauka ne kike ambato sunan yata cikin wannan maganar?nace ba dadi kake ma yar wasu?Na sake fashews da sabon kuka ka bani takarda ta, bazan iyazama da kai ba!kina haukane zaki ce na sake ki,toh bazan iya ba me Zancewa Iya?nace in itace matsalar ka bazan fada mata komai ba in baka sake ni ma zanje yanzu in fada mata! hanklainshi yatashi ya dauki jallabiya ya sa nikam ficewa nayi naje dakina na sure hijab na bude Kofan falon ya rike ni kina hauka ne zaki je ma Iya da wannan zancen?nace me zai hana,ya kamoni na kwace nayi waje na bude kofar gida kafin na bude ya daukoni cak,dakina ya jefa ni kan Gado yace kina hauka ne?yace nayi laifi kiyi hkr ki nutsu Muyi magana, nace kai ni fa na daina Sonka kuma girmanka ya zube a gurina, ganin zanga-zangar tayi yawa sai ya kulle ni ta baya ya daga waya ya kira Usman yace don Allah yana son ganinshi yanzu a gida,ina jinsu a falo yana fada ma Usman shi bai San ina ji ba wai duk na daga hankalinta har wai ina kwacewa ni dole sai naje na fada ma iya.Usman yace aboki tambaya daya zan maka kayarda kana aikata laifin nan?yayi shiru ,Usman yace in har ka iya amsarwa shine zai kawo karshen matsalar, yace toh ai na fada mata cewa naji na kuma amsa laifina don haka ta tsaya Muyi magana taki,Usaman yace a'uzubillah, Aboki me yarude ka ka fada wannan harka?wlh aboki kurum na tsinci kaina a wannan halin, ka San zuciyata bata da Kashi ga kuma sharrin shaidan, Usman yayita masa nasiha sannan yace a jira ni na fito fuskata suntum nace Nifa Usman na gaji ba zan zauna ba,Usman yace yi hakuri nasan kinyi hakuri kuma inshaAllah bazai kara ba,na kalleshi nasan zai chigaba kawai ni gara ya aureta in son aure suke,inkuma matan da yake bi da yawa toh ni bazan iya zama ba.Usman ya Kalle shi gaskiya ne Aliyu yace ita kadai ce muke tare wlh kuma itama tsautsayi ne, Usman yace ko kayi nadama sanin zaka koma can ku sake haduwa shi yasa ta kawo shawara cewa taje tayi istibrai in ya so sai Kuyi aure.Aliyu yace ina bazan auretaba ni nakuma yi miki alkawarin cewa mun rabu da ita inshaAllah, a gaban mu yayi waya ya kira maigadinsa yace a fitar da Mujidat daga gidan kafin ya dawo, itama ya kirata yace mata ya gode da wasikar da ta sa mishi a cikin kaya don ta raba shi da matarshi don haka maza ta bar mishi gidanshi,bai jira takare kanta ba ya kashe dukkan phones dinsa. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Ni Sam bai wani Burgeniba,suna cikin gidansuna ta bani baki har magrib,suna fitowa nayi wanka na sha magani nayi sallah ina zaune kan dadduma har sai da nayi sallar Isha dama banyi girki ba,na hau gado abuna na chigaba da kuka, na soma barci naji ana shafa ni a wuya abunda na jima ina kewa amma sai naji tamkar ana shafa min kaya.Na ture hannunsa a kunne ya rada mincewa'My choice zan zame miki sweet Aly dini har abawa ba zan sake chanzawa ba,natashi zaune muna kallon juna cikin ido nace yaya Sam yanzu in ka fadi magana bana yarda matsalar mutum ya kama karya kenan har a gane shi,na sauka daga kan Gado naje na jingina da bango ina kallosnshi shima ni yake kallo nace yaya ni fa nadarmarka bata shige ni ba don nasan dole sai Kun sake haduwa da yarinyar aurenta kawai shi ya fi dacewa da kai,ya nufoni amma ina ce an gama maganar nan,bazan iya auaran ta ba har ta Haifa min yara na gari Domin ba uwa ta gari bace,itace tayi ta bibiyata har sai da komai ya faru kinga kuwa in na aure ta ta kuma ganin wani shima xata iya cewa tana sonshi,ya kama hannuna ki yafe min mukoma kamar da, Abban Kausar na hkr amma sai Kamin rantsuwa cewa bazaka kara aikata wannan halin ba? Cikin sauri yace'na rantse ba zan sake ba nayi alkawarin, nace toh shi kenan na zame hanuna naje na kwanta sannan nace yawuce, ya Tako ya zo ya hau gado ya kawo nizuwa jikinshi na tashi zaune yaya kayi hakuri bazan sake iya hada shinfida da kai ba har sai kaje kayi gwajin cutar kanjamau!!!!! Zumbur ya mike tsaya tare da rike kanshi Sam baiyi tunanin wani HIV ba tunda yake tarayyada yarinyar, ya fara sintiri a tsabar dakin,nace da baka yi tunanin haka ba ko?ya sauke ajiyar zuciya 'ban yi wannan tunanin ba wlh Sadiya amma bana zaton tana da shi,tunda tsawon zamnmu ban taba ganin tayi wani ciwo ba,nace ba a nan take na, Ance mace tana yin shekara goma ciwon bai nuna ba,kawai kaje kayi gwaji in ma tanashan magani a boye wa zai sani? zufa ta rufeshi sai lumshe ido lallai kamar yana ganin ta tana shan wasu kwayoyi har ya taba tamabayar tace na family planning ne,fita yayi da sauri na tashi na biyo shi ina cewa ina zaka Abban kausa'r yace'koma asibit zanje yanzu nan........ Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 toh fa sai ku biyo ni cikin Kashi na uku don Jin ya xata kaya shin Aliyu yana da ciwo?taku Halima K/ Mashi Zaharaddeen shomar Whatsapp 08168575100 Darajar Yayana3-01 Posted by ANaM Dorayi on 10:48 PM, 31-Mar-16An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT __ Under: DARAJAR 'YA'YANA ___________________NA ___________HALIMA K/MASHI Gudu sosai Aliyu yake tamkar zaibar gari,zuciyarsa ta karaya gani yakeyi lallai yana dauke da ciwon har ya hangoshi kwance a rame ga kuraje sunyi mashi caba caba a jiki.da sauri ya ciro wayarshi ya kira layin likitan, Dr kana Asibiti ne? Dr ya ce eh, amma yanzunnan zan fita.Aliyu ya ce, don Allah ka jirani gani daf da Asibitinka.Sama sama suka gaisa, Aliyu yace likita ana yin gwaji yanxu a fitar da sakamako yanzu? likita ya ce gwajin mene?Aliyu ya ce, (H.I.V) ,Likitan ya zaro ido yana kallon Aliyu ranka ya dade kana zaton ciwon a tare da kaine?Aliyu ys ce eh likitan ya ce, likitan yace za a iya, da kansa yayi gwajin, ya daga ya nunawa Aliyu tare da cewa yanzu dai ya nuna baka da ciwon sai dai ba a gwajin farko ake tantancewaba.bayan wata uku za ayi wani, sanan in an sake yin wani wata ukun sai a sake gwadawa sau uku kenan,induk ya nuna babu to babu din kenan saboda gwajin farko yakan nuna babu kuma akwai.Aliyu ya lumshe ido, kenan likita yanzu bani da tabbas kenan? Likita yace gaskiya babu tabbas.ya dafa kafadar Aliyu cikin murya ta son kwantar masa da hankali ya ce, yallabai kadakadamu, ko da ya kasance kana da ciwon domin akwai magunguna wadanda masu ciwon suke sha duk karshen wata.sanan zakaci abubuwan gina jiki don karin kuzari, su magungunan suna yakine da kwayoyin cutar, suna hana kwayar ta karya garkuwar mai dauke da ciwon.Aliyu ya share zufar da ta keto masa ta goshi, sanan ya ce to nagode likitan ya ce se iyalanka ya kamata a gwadasu.Aliyu yakalli likitan yace ana iya daukar ciwon ta hanyar mu'amulan yau da kullum? kamar misalin ta hada kwanon abinci ko yin hirar fatar baki ne?likitan ya ce a'a Aliyu ya ce, to bana tsammanin suna da ciwon,kafin likitan ya sake magana, ya ce na gode likita, na barka lafiya.Da azama yafita ya nufi gida.Nikam lokacin ina zaune bakin gado, idanuna banda xafi ba abinda suke yi, saboda kuka.hawayena sun daina zuba sun kafe. Nakosa yaya ya dawo, addu'a ta Allah yasa yaya bashi da ciwon, dama gidan bude yake dom haka sallamar shi kurum naji abakin kofa,Zubur na mike ina kallon shi, ya zauna bakin gado tare da sunkuyar da kai na dafe goshina ta re da cewa innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yaya kana da ciwon ke nan? Shima da sauri ya mike tare da kama hannuna Sadiya kinatsu mana,nasoma kuka. Yaya ka cucemu, kila nima ina da ciwon, shike nan ka mai da mana yara marayu? Ganin yadda na rude yasa shi rumgumeni a jikinshi tsam.Saurara mana nima fa ba cewa akayi ina dashi ba. Na kalle shi me aka ce? Ya ce, sai anyi gwaji uku sanan za'a tabbatar amma yanxu ma ya nuna babu. Na sauke ajiyar zuciya, sanan na ci gaba da gunjin kuka ina cewa. Duk lokacin da bawa ya bar hanyar Allah tabbas sai ya fada da nasani. Aliyu ya ce kiyi hakuri mana Sadiya, nasan cewa ko da ta kasance ina dauke da ciwon nan, wlh sam nasan baki dashi, domin lokacin da na fada wanan kuskuren Allah ya sani ban rabeki ba sai yanzu na tuna ta iya yuwuwa baki da hakki ne shi yasa Allah yasa ban kusance ki ba. Nakalleshi idanuna jajur, tayaya kake zaton abinda ya shafeka bai shafeni ba? Naci gaba kaifa mijinane nasunna, ina sonka koda kai baka sona. Ya maza a ce abinda ya shafeka bai shafeni ba. Yace haka ne kiyi hakuri Sadiya. Tsam! namike nafada bandaki nayo alwala, zuwa nayi na fara jero nafiloli don neman sauki a gurin ubangijina. Can shima sai naga yayi tashi alwalar yazo ya kama yin nafilar, a hankali nake jin zuciyata tana sauka, danagaji sai na dauki alkur'ani littafin da ke dauke da waraka na soma karantawa. Munfi awa uku cikin wanan halin, lokacin zuciyata tayi sanyi kalau. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Shi yasa kullum ina alfaharin kasancewata musulma. Ina kara godewa ubangijin musullunci da ya kageni cikin wanan addini ya saukar mana da Alkur'ani don ya kasance waraka a garemu.Aduk lokacin da na karanta alkur'ani ko na saurareshi nakanji sauyin zuciya, ko cikin wata i ciiin matsala nake.Na kammala nazo na kwanta yanzu ina jin zan iya jure ko wacce iriin kaddara da zata hau kaina. Hakanan zan rufawa mijina asiri inshaAllahu, shima yazo ya kwanta dan nesa dani muna fuskantar juna. Ya ce kiyi hakuri don Allah kinji? Na ce, nayi hakuri, na yafe Abban Kausar, ya wuce a gurina na matsa kusa da shi. Ya ce baki jin tsoro na? Nace Abban Kausar mu bar wanan maganar. Ya rumgumeni, yau she rabom da na kwana hakarkarin mijina sai yau. Munso mu makara dan haka shine ya jamu sallah. Zan tafi kicin yace, dawo mu kwanta mu huta anjima ma karya na dawo muka kwanta Yadda nake jina yanzu ba zan juya masa baya ba. Har sai sha daya muka karya, sanan ya shirya ya nifi gidansu Iya ni kuma na shiga gyaran daki, minti shabiyar da fitar sa sai gashi ya kira, na daga tare da sallama. Cikin rudewa ya ce Sadiya kinga yaran nan sun hadani da Iya ko? Kuka fa na sameta tanayi please, kizo yanzun kitaimakeni sam taki saurarena. Hankalina ya tashi. Akofar gida na sameshi tsaye cikin damuwa nace meyafaru? Ya ce wlh ban sanme yarannan suka ce mata ba, na shigo na sameta cikin damuwa natambayeta me ya faru? Tana kallo na sai kawai ta fashe da kuka, wai naci amanar ta nasan dai maganar bata wucea kan matsalarmu dakeba. Ban san me zance mata ba, domin bani da yanda zan wanke kaina. Laifi dai nayishi, don Allah shiga ki bata hakuri, anjima zanxo da Usman neman tuba gurinta. Cikin hanzari na shige gidan, kan kujera na sameta cikin tashin hankali nazauna ina fadin Iya menene? Abban kausar yayi min waya wai inzo, ya ganki cikin damuwa. Sam idona ya rufe ban lura da su Kausar ba, sai da naji muryarta ta ce, wlh Mami ni banibace nafadaba, Al'amin ne yace yasan yanzu kina can kina kuka, shine Iya taji tace kukan me? Shine mukayi shiru, ta ce mu fada nacemashi ni ba ruwana kin hana mu fada, shine ta tsaremu ta ce, zata zanemu, shine nace inmun fadamata kada ta fadamaki. Shine muka fada mata cewa kullum Abban mu in ya dawo sai ya sa ki kuka, yayi ta zaginki. Na kama musu kunnuwa, muryar Iya naji ta ce sakar musu kunne, in ba ke ma kinaso inyi fushi dake bane. Ni na san cewa wanan ramar taki akwai bakin ciki a cikinta. Wato dama gadanga cin amanar da aka bashi yakeyi? Shine ke kika zabi ki zauna ki hadiye bakin cikin da namiji kina kan kanuwarki. Sai yanzune kike cikin shekara ashirin da biyar, amma kika juri wulakanci. To ki sani ni ba xan yarda ba, ai kodanace in matsala ta taso kada ki nemeni ban ce haka dan kicutu ba, na furtane dan in tabbatar kina sonshi badole nayimakiba. Da naga ta nunfasa sai na ce Iya yaran nan karya suke yi, dan sabanine mukasamu kwanan baya, kuma mun sulhunta, dan Allah Iya kada kiyi fushi da yaya, ko mai ya wuce. Ta ce yaro da wuya yayi karya. Daidai lokacin yaya yasake shigowa,Iya ta dube shi Aliyu ina son ka sani,Sadiya bazata koma gidan ka ba, dan ba zan yardaba ace har yayanku sun san cewa kana cutar uwarsu ba. Shi yasa tun farko na ki batun auran, don nasan halinka. Hankalin yaya Aliyu yasake tashi, ya curo wayarsa ya kirawo Usman, ya ce dan Allah Usman kazo gidan Iya yanzunnan. Ba tare da ya jira Usman me zai ce ba, ya kashe wayar shi. Sadiya ta tsurawa su Kausat ido sam bata so suka fada wa Iya wanan maganarba.badon kar a rabata da mijinta ba, sai dan bata son Iya tashiga damuwa, musanman yanzu da ya kasance Iya batada koshin lfy. Iya ta ce, kun tsaresu da ido ne don sun fadi gaskiya? Na ce Iya

Chapter 12 of 25