Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kuma tasha alwashin sai ta haife dan cikinta ta kawo shi.Anty Abida tayi salati tare da rike baki tace lallai akwai matsala. Nace nayi nayi ya tsayamuyi shawara ni da shi amma yaki yace in bar zancen. Tace shikenan tunda baya son zancen ki kyale shi, Allah ya rufa asiri, nace amin. Daga nan yayi ta yawo damu supermarket da stores kalakala. Mun kwaso kayan ciye,ne da suturu da takalma, ni kama har da mayafai da jaka. Gsky ranar ya kashe mana kudi, haka muka shigo gida nikiniki da kaya, yarana nadade sosai bangan su cikin farin ciki kamar yau ba. Lallai rashin jituwar iyaye ba karamin shafar rayuwar yara takeyiba. Don Allah iyaye in wata matsala ta gifto muku ku daina sa'insa gaban 'ya'yanku, don gudun lalacewar tarbiyyarsu, tare da jefa rayuwar su cikin rudani,Tun daga ranar dayace min yana tafe nayi ta hada abubuwana ina sha , yanxun ma zumata na samu na kada kwaina na hada na shanye.Sabon wanka nayi na saka sabuwar rigar baccin daya zaba in a fitar da mukayi, yanxun na kama gashina shi kam yana falo yana kallon labarai a tashar Aljazeera,Yara tuni sunyi bacci, ban fito ba nima sai nabi kan gadona na fada tsakiyar gadon nayi kwanciyata.Da zai yiwu in bada labarin daran ranar kila da nan zan kare, domin ya shiga sahun tarihin da ba zai gogu ba a zukatanmu.A cewar yaya, daran ya dara na farkonmu.Da safe mun tashi tamkar sabon aure, cikin kwalliya muke aiki tare dashi a kicin. kwanaki biyun da Yaya ya yi sai da na rubuta su cikin dan kundin adana mahimman sirrikana. Da zai tafi har kuka nayi. Allah sarki rayuwa,mun koma tamkar da har mun fi da kyau,rayuwar aure d zaman lafiya gami d soyayya akwai dadi. Tuni Aliyu ya mantar da ni abinda ya faru a baya. Kuma ko na tuna bana jin haushi,don na dauke shi matsayin jarabta. Sai dai fa duk lokacin da na tuna cewa wata tana can dauke d cikinsa ina tsorata da abinda zai biyo baya. Kwatsam sai ga shi anyo ma Yaya transfer zuwa Abuja.mun yi murna don ganin Abuja ni ke tamkar kaduna, tunda ya koma nan ba ya jimawa bai zo ba. Wata rana har can Abujar ya kan tafi da mu muyi hutun karshen mako. Rayuwa dai ta jin dadi muna ciki. Kwatsam wani yammacin ranar Talata ina tsakar gida ina kwashe shanyar kayan makarantar yara da na wanke. A jikina ina sanye da doguwar riga mai hade da hula blue da ratsin fari,sai naji ana buga min gida, na nufi kofar ina tambayr kaina ko wa ye?? Ina budewa muka hada ido da ita, gabana yayi mummunar faduwa. Ina zaton ko cikin duhu na ganta zan gane ta, bare a haske,domin na sha ganin hotunanta cikin facebook, tana sanye d doguwar riga ja hade d mayafinta. Sannan tana janye d akwatinta, ga wata ta rataya a kafada. Na dake na sake dubanta. 'Malama daga ina? Kuma wa ki ke nema? Ta ce, 'Nan ne gidan Aliyu Tukur jami'in dan sanda? Na ce, eh nan ne. 'Sai naga ta turo kai, na ce 'Ba ki minbayani ba kina kokarin shige min gida. Tayi min wani kallo sama da kasa, 'Ni bakuwarshi ce, Allah yasa yana gari? Na maida kofar na rufe,tare d cewa 'Bayanan yana Abuja, lafiya? Ta nufi ciki. Zo ki nuna min inda zan zauna, a gajiye nike, don na wahala kafin na gano gidan. Falo na sauketa duk da tafasar da zuciyata ke yi, amma na danne har ruwa na bata. Sannan na zauna na kalle ta. 'Baiwar Allah daga ina ki ka zo neman Maigidana? Ta gyara zama 'Ciki ya yimin,ta fada a gadarance ba tare d jin wani nauyi ko shakka ba, ni kuwa duk da cewa nasan batun sai da gabana ya fadi da jin furucinta. nace, 'Ciki? Ta ce 'Eh, shi ne don wulaqanci ya ci moriyar ganga zai yada kwauronta? Bai isa ba. Sai yasan ya taba annoba. Raina ya soma daukan zafi a gurin,na daga waya na kira shi,ringing din farko ya daga tamkar yana zaman jiran kirana ne. Ya ce,'Ya ya dai my choice? Don in nuna ma Mujidat ban damu ba, na ce 'Sweety kayi baquwane,da sauri ya ce, Daga ina? Na kalleta tamkar ban san ds batunta da shiba, na ce ya ce daga ina? Ta miqo hannu 'Ba ni wayar. 'Nayi 'Yar dariya. Ke ba ki d wayar ne? Fadi kawai daga inda kike in sanar dashi. Cikin son ta tura min haushi ta ce, fada masa wadda yayi ma ciki ce. Kalmar tana dukan kirjina in ta furta, amma na dake na ce 'Wai wadda ka yi ma ciki ce. Na karasa zance da dariyar bakin ciki. Da sauri ya ce, 'Mujidat? Subhnllhi! Lallai wannan 'yar iskar tana son jaza min bala'i ne. Ta ya ya ta gano gidana? Na tabe baki tare da cewa, 'Oho' ya ce, 'Kai wannan akwai 'Yar iskar yarinya. Sadiya don Allah kiyi hakuri kinji? Zan taho yau din nan kmai dare, amma yanzun ya ya za'a yi? Na ce, kaika san yanda za ka yi da ita. 'Ya dan yi shiru yana nazari, duk a rude yake,ya ce, 'Sadiya. Na ce, 'Na'am, 'Ya ce, 'Kuna tare ne yanzun haka? Na ce,'Eh. Ya ce, shiga daki muyi magana. Na ce, To. Na miqe na nufi daki. Na shige Toilet na rufe, sannan na ce 'Ina jin ka. Ya ce, 'Sadiya don Allah kiyi hakuri kwakwalwata ta toshe, ki buda min ita ya ya za a yi yanzun? Raina bace yake matuka, na ce 'Lokacin da za ka yi sabonka ka nemi shawarata? Don haka sai ka nemi shedanin daya hure maka kunne ya sa ka a hanyar da za ka warware matsalar. Ya ce, Sadiya duk ba wannan zancen ba, yara na gida tayi magana? Na ce, 'A'a suna islamiyya. Ya ce, 'Ok, yanzu yaya za ayi? Na ce, 'Wallahi ban sani ba, ni dai bani da dakin da zata kwana sai dai in dakinka. Ya ce, 'Zan taho yanzun nan zansa jami'an tsaro su kulle min ita. Na ce, 'Kana ganin wannan mafita ce? Yarinyar nan irin 'yan iskan nan ne ma su tutiya da iskancinsu. A shirye take d ta shelanta ma duniya ita farkarka ce, kuma tana da cikinka.ka shirya zubewar mutuncinka? In ka shirya ka zo ka bi ta d zafii in ko kana son tsira d dan ragowar mutuncinka,to koka tabbata za ka bi ta ne da lalama ka kuma yi mata adalci tunda lokacin daza ku yi shedanar ba ka juyamata baya ba. Na kashe wayar tamkar in yi kuka, amma sai na fasa don bana son wannan Mujidat din ta fahimci abinda ta zo dashi ya daga hankalina. Ko kuwa ya dadani da kasa,don na lura 'Yar bariki ce.nasame ta inda na barta sai dai yanzun ta dan kwanta akan kujerar. Na dube ta 'ya ce ki jira shi yanzun zai baro Abuja,kina buqatar wani abu yanzun? Ta ce, 'A'a bana jin yunwa na ci abinci a gidan cin abinci. Na wuce na ci gabad aikina sai dai kunci da takaici a zuciyata ba a magana. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Shida daidai yara suka dawo Islamiya kallonta suka dinga yi sannan suka gaishe ta. Ta ce yara masu kyau,ina kausar?Ta ce, 'Gani. Mujidat ta ce, Yar lelen Babanta duk ya fi ambatar ta cikin yaran. Kai ne Al'ameen? Ya ce, 'Eh. Ta ce, 'Ka yi min kyau, kana kama da babanka sai ka shiga raina. Ta dubi Mama ta yatsina fuska, 'Ke ce mai kama d mamnki ko? Sunfi ki kyau, Allah yasa babyna ya yi kama da..............'' Da karfi na daka mata tsawa 'Ke! Mahaukaciyace? 'Na kalli su kausar, ku je dakin ku ku cire kaya ina zuwa. Na dubeta bayan shigarsu daki,mekike shirin fadawa yarana? Kina so ki fada musu kina da ciki da babansu? Ta 'Eh ai dole su sani ko da ban fada musuba, domin a gidan nan zan haife shi. Na runtse ido don baqin ciki na bude tare da furzar da takaicina ta baki, na ce ba zan hanaki ki haihu a gidan nan b, sai dai zan gargade ki kar ki sake ki fadawa yarana maganar data fi karfin tunaninsu, kin gane? Ta yi 'Yar dariya,sannan ta ce, Bani da magana dake bare ki sa min doka, mijinki nake jira. Haushi ya turnikeni har na kasa tsaida shi na ce, 'Mijina fa nawa ne kar ki ga na miki tarbar mutunci ki za ta shakka ce, in na ga dama ba ki ganin mijinnawa, sannan dole ki bar min gidana. Ta saka dariya, sannan ta debi kafafunta ta zuba kan kujerata kuma kallona sama d kasa,sannan ta ce.........zandakata anan, zakuji zarar Allah yanufa.. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Darajar Yayana3-03 Posted by ANaM Dorayi on 12:12 AM, 04-Apr-16 Under: DARAJAR 'YA'YANA __________________NA ___________HALIMA K/MASHI Assalamu'alaikum,akaro na barkatai gani na dawo domin kawo muku cigaban labarinmu ,fatan kuna sane da inda muka tsaya. Yayi shiru. Na ce Hello, kana jina? Eh, kin fadawa Iya ne? Na ce, nanmuka amshi haihuwar tare, Kasan cewa taso ta gano cewa danka ne? Dan yaron yayi kama da kai fiye da duk yaran gidan nan.Da karfi yace Haba dai! Wlh, yaushe zaka zo? Yayi dan tsaki, gaskiya bani da ranar zuwa, zan turo miki kudi kiyi duk abinda ya dace. Nace, zuwan ka yana da muhimmanci, sabida Mujidat zata iya tana komaifa, inbata gankaba. Ya ce, to zan zo kafin suna inkuma dawo Gurin aikina. Nace to saikazo. Na kira auntyAbida na fada mata, haka ma Aisha kawata.Makota duk suna ta shigowa Barka. Su kausar ma nasa sunje sunga baby,na fada musu cewa kaninsune, suna ta murna har da kausar. Aisha ranar datazo barka tana daukan yaron tace, kai Sadiya yaron nan yana kama da Abban kausar. Nace, haka ake ta cewa, dama kin san mutane sun ce in mai ciki tana yawan kallon mutum ta kan haifi mai kama da shi. Ta yi Yar dariyar yake,tare da cewa, hakane kawata.Mai jego kam ina kallon ta sai harara take watso mana. Muna shiga dakina tace, Sadiya anya kuwa ba kanshin gaskiya a cikin lamarin matar nan? Kin san halin mazannan ko dai Dan sa ne? Ki yi hakuri kamarce naga tayi yawa. Nace, hum! Ke dai bari kawata, tsakanina dake nasan amanace, wlh dansane ciki yayo mata, yanzun data haihu zasuyi aure. Aisha amana na fada maki ko iya bata San wannan ba. Aisha ta zabura tare da fadin, kan uba! Lallai Sadiya ban taba sanin cewa Ke sakarya bace sai yau, yayowa wata ciki sannan ki yarda ta zauna maki a gida? Wallahi da ace nasan haka ne in nazo barka shegiya nake,kin ma daure masa gindi kenan gobe ya kara.Na ce, Aisha ki fahimta, uban 'ya'yanane,mijina kuma yaya zanyi? Nawa ganin rufin asirinshi Nawa ne, kuma na yara nane. Ta yi tsaki bana Jin zan fahimceki, in tazo gidan ta koreki kin ga ai sai kiji dadin rufa masa asirin. Na ce, nasan dama bazaki fahimceniba, shi yasa tun farko ban sanar da Ke ba, dan na sanki. Ta dauki yarta tasa a baya,ta suri jakarta da hijabinta, Ni kin ga tafiyata. Na bita ina fadin, "Dan Allah Aisha ki saurareni. Ki tayi ta tafi abinta. Na ce to shi Kenan in kin huce za muyi waya ta ce ni kar ki kira ni. Na dawo daki na kwanta kan gado ina hawaye, in na tuno Yaya zasuyi aure da Mujidat Abin na daga hankalina ya kuma sani kuka. Ranarr da suka cika kwana 5, sai ga Yayakusan 10 na dare, Ni ce ma na bude masa kofa, ya janyo ni jikinsa,ni kaina bansan me yasa jikina yayi sanyi ba kuma banyi wani farinciki da ganinsa ba. Ya dago fuskata, sannan yahaskani da wayarsa, lafiya my choice? Na sa hannu na tare hasken,lafuya mana Yaya mai ka gani? Na karbi jakar hnnunsa tare da cewa sannu da zuwa,bai amsa ba sai dai ya ce, na ganki cool ne, kamar ba kiyi farin ciki da gani na ba. Na ce, bacci na fara. Sannan nayi gaba na bude masa daki ya shiga. Ya zauna bakin gado tare da fadin, na gaji yau Sosai,8 ta wuce na baro Abuja, kuma da safe zan wuce na zone Kawai sabida kin nuna zuwan nawa yana da muhimmanci. Na ce, to Kayi wanka zaka warware. Ya ce to. Kafin ya fito wanka na kawo masa tuwo daman shi nayi a daren miyar zogole. Sai da yaci na fitar da kwanukan, sannan na shiga gurin Mujidat tana zaune da waya tana chatting, na ce, ya kamata fa ki dinga bacci. Ta ce, ba zan yi hira da kawayena ba? Na ce, kuyi tayi, akawo yaro babanshi yazo. Ta kalli yaron sannan ta kalleni, ya yi bacci. Na Isa gurin yaron na dauko shi, ban tsaya jiranta ba na kai shi. Aliyu ya mike tsaye zumbur likacin da ya kalli yaron duk yadda Sadiya Ke bashi labarin kamannin shi da dan bai zaci har hakaba. Ya kalli yaron kusan minti 1, sannan ya miko mini tmkr yana tsorace,na maida hannuwana baya. Kayi masa addu'a kamar sauran yaran ka duk dadai baka samar da shi ta hanyar da shari'a ta amince ba, sannan ka yi masa hudu ba,ya daga murya rikeshi mana Sadiya. Na juya na fita. Abin mamaki sai ga Mujidat labe tana lekenmu, na tsaya turus ina kallonta, ita ma ta yi tsuru-tsuru na ce, a'a dama kina min labe? Ta soma Sosa kai, sai kuma ta shiga borin kunya, kin zo kin daukarmin yaro ba dole inbiba? Na ce, kina zargin zan cutar miki da yaro ne? Yaya ya fito ya mika mata yaron "ungo yaron ki kar ku tada min da yara suna bacci. Ta amshi danta ta tafi, ni kam a gurin na tsaya na ma rasa tunanin da zanyi, tun yanzu kenan kafin a daura Auren? Shi kam bai so yanda ya yi ba kada ma mu tada masa yara suna bacci, maimakon ya gargadeta kan cewa Kar tasake yi min labe, bai yi hakan ba sai ya shige abinsa. Ni kam dakin yarana na nufa amman ko zama ban yi ba sai ga kiranshi, sai da wyrta kusa tsinkewa sannan na daga. Meyene? Yace, zomana,sai da na dan bata lokaci, sannan na je. Kai kawo na samu yana yi a cikin dakin, ina shiga ya nufo ni ya kama hannuwana. Sadiya asirin da muka rufa zai tonu sabida kamannina da yaron nan ya dauko,ina ganin gara mu fadawa Iya Kawai ita kuma Mujidat ta yi tafiyarta tunda dama dan Kar Iya su sani ne zan aure ta, ni wallahi bana son ta, zata iya tarwatsa min iyali,na zame hannuna daga nasa na zauna bakin gado tare da rike kaina na ce, Yaya ba dan Kar asirin ka ya tonu Kadai ba ne na ce ka aureta, don gudun kada kuci gaba da haihuwa a titi babu aure, don nasan bazaku rabuba. Shima ya zauna, sai dai in itace baza ta rabu dani ba Sadiya, amman wallahi ni tuni na barta,na girgiza kai, Yaya yin Aurenku yafi a kan barin shi, don Mujidat ta tabbatarmin da hakan kuma na San zaku iya... hawaye suka soma zubomin cikin rawar murya na ce. kuma duk laifin kane. Ya kwanto ni jikinshi, wallahi Sadiya nayi nadama matuka, kuma naji kunyarki Sosai ki yi hakuri kidaina kuka, Kecefa kike Karfafa min gwiwa,kike bani shawara. Ya dago fuska ta. Hankalina yatashi da yawa ganin kamannin yaron nan,nasan sai dai mutane su ji mu Kawai, ammababu wanda zai yarda cewa ba yaro na bane. Ya share min hawaye. Ki yafe min. Na ce, Yaya ni dai alfarma Kawai zan roka a gurin ka guda biyu. Da sauri ya ce, na miki alkawarin yi miki su fadi inji. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Na ce, na farko duk rintsi kada ka juya min baya ko ka wulakanta ni. Ya rike kafaduna muna kallon juna, insha Allahu Sadiya ba zan miki ba ko bisa kuskure insha Allahu. Nace sai na biyu, izini zaka yi min in nemi koyarwa a makaranta, ko L.E.A ta nan unguwar Mu'azu. Ya yi shiru yana nazari, can ya ce, kin gane Sadiya ba wai ina son hanaki bane, nafison ki nutsu a gida wallahi bana son matata tana yawo. Na ce, akwai dalilina, ka ga Kwanan nan zamu zama mu biyu a Kasan ka, duk wata bukata da zan nema a wurinka dole ne ka yi mana mu biyu, inko inada nawa zan yi bukata ta ba tare da na takuraba. Ya ce, wannan bai kai dalilin da zan bar ki ba sai dai in bar ki sbd tun farko na amsa cewa nayi miki alfarmar da kika nema,da dai tun farko na san wannance alfarmar da bazan yardaba, sai dai kimarki ta wuce in amince, sannan in dawo in ce a'a, kije kiyi koyarwa ki, amma ki tsare mutuncinki da nawa.Na sauke ajiyar zuciya 'nagode mijina, Allah ya saka da Alheri. Ya lumshe ido sannan ya bude. Yanzu wane suna za'a sa masa? Na ce, a'a wannan shawarar tsakaninkane da Mujidat, da safe ka sameta ku tattauna. Bai ce kalaba sai ya kwanta rigingine. Da safe falo ya zauna yace in kirata,ta fito tana yatsina cikin Riga da wnd ta zauna, ya ce, wane suna kika zaba? Ni kam mikewanayi. Ya ce,zo mana My choice. Na ce, ina zuwa. Dakina nashiga na bar su dan zancen na su ne.Ta mike daga Inda take ta koma kujerar da Ke daf da shi ta ce,Sweety kaine zaka bashi suna in dai nice nafi son sunanka don yaron yafi kama da kai. Darling kabiyani dakabani mai kama da kai. Ya waiwayo ya daga mata hannu, tsaya!baki dacikakken hankali ko? Ni ne nake bada haihuwa?Ki sawa yaron ki duk sunan da kike so amma ban da nawa kin gane ko? Ta ce, to ina son a samun Abdul-kareem. Ya ce, ya yi Allah yaraya shi.tace ameen. Sai maganar auranmu. Ya mike tace, na zata tun ranar dana haihu zamuyi maganar shine yanzu na kawo maganar za ka tashi? To bari kaji daurin auren nan in ya wuce gobe za ka ji mamakin abinda zai faru.Ya shigo daki, ina jiyo duk yadda sukayi nace, Yaya ka amince nima ina son a daura a wuce gurin kawai,ya ce, ba zanyi yanda takeso ba, tana ganin itafa wata cikakkiyar marakunyace. Bata San cewa ina daga mata kafa bane sabida Ke,nace, dan Allah kai dai gara a yi ko a wuce gurin. Sam ban zaci za a yi wani suna ba, don haka ban tanadi wani batun sunaba, kuma da zai tafi yace Usman zai kawo rago shi ma bai yi min batun suna ba, amma muna da kayan abinci na ce masa ya siyo mata sababbin kayan sawa ita maijegon,yace bazai siyoba, ko dan kyalle. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Washegari tin misalin 8 na safe naji bugun gida, dama na rufo kofar gidan ina sauri zan kai yara makaranta don munyi latti, kafin in bude sai ga Mujidat ta fito da gudu tana cewa, oyoyo Momy! Kaucewa nayi ta bude, ashe 'yan uwanta ne daga Lagos su 4, Mamanta,Babanta, Kawarta da Kanwarta suka kalleni nima na kallesu, don hauka har uban suka shige cikin gidan, nasa yarana a mota na fice cike da takaicin da ya Aliyu ya ja mana. Har na dawo raina a bace. Mujidat nasamu a kicin tana ta fasa kwai ita da kanwarta suna hada abincin karyawa, ban kula su ba, na shige dakina cike da bakin ciki. Ko da naji bugun gida ban fito ba a zatona wadansu dangin nasune, amma sai na ji wayata tana ruri na daga ashe Usman ne yace Madam ki bude gida ga Ragonnan,nabude ya shigo da Ragon muka gaisa yace kuyi hakuri banzo barkaba, wallahi Sadiya takaici ne ya yi min yawa bana son ko ganin matar nan, bare Dan, sanann ga kunyarki. Nayi murmushi tare da cewa, Haba dai, gurina bakomai ya Usman. Aunty Abida fa? Ya ce, suna lafiya,naji tana cewa zatazo anjima. Na ce, yauwa Dan Allah Yaya ina jiranta yanzu, bari in kira maijegon ka ba ta, dama danginta sun zo. Ya ce, daga ina, oho bansan garinsu ba. Nace dashi. Na leka dakin sunyi dirshan a kasa suna tacin abinci suna zuba yare har da uban, a raina na ce tabdijan! Hauka. Na ce Mujidat kizo inji Yaya Usman. Ta ce, in yazo ganin yarone ya shigo mana, ni bazan fitoba. Na ce, Rago ya kawo muku, shima sauri yakeyi. Ta mike tana yatsina ta fito. Ni kam ban koma gurin su ba sai da na ji yana kirana. Madam na tafi.,na fito nace to Yaya mungode, amma lallai ina jiran Aunty, yayi dariya zan fada mata kiyi ta hkr Kinji? Na ce ba komai. Sati 1 Kawai da suka yi a gidan naga takaici, gulma gurinsu ga shegiyar kazanta. Babanta wai ya so ya ga Aliyu saboda a yi daurin aure su zasu tafi ,kuma ganinsa baza su iya dawowa ba, shi kuma yaya yace dansu Bazai bar aikinshiba sai dai na lallabasu da cewa su tafi in Ya zo sai a je can garin. Haka kuwa sai tafiya suka yi, ya so ma har Mujidat ta bisu can, amma da yake ta san shi in har ta sa kafarta tabisu to sam ba zai nemeta ba, don haka tace aifa sam ina nan na baka lkc ka gama zaman ka dawo muyi aure. Yafi wata sannan ya dawo, lokacin Abdul-Hakeem yayi wayo sai gogewa yake yi, don ma ba ta san bashi nono sai madara, wai bata san nononta ya lalace, na ce Allah Sarki wata rana ma ke kanki sai kin lalace bare wani nononki. Aliyu kam tuburewa yayi cewa ba zai auri mujidat ba, nima na tubure cewa ban yardaba, matsalar da ta janyo rigima har sai da Usman yazo gidan.Usman ya cewa Aliyu, alkawari Kayi tun farko, kuma musulmi ne kai ka san muhimmancin alkawari, sannan matarka tana da gaskiya ba za ku rabu ba. Mujidat da Ke daki tana jiyo wa kuwa ta fito,ta ce, ai mutuwa ce Kawai zata raba su, kuma ta dibarwa kanta lokaci in har ya cika bai ce komai a kan auran su ba za ta maka shi a kotu, sanan zata nemi yan jaridu manema labarai ta ce shine a matsayin wanda yayi mata wayo yayi mata ciki bisa alkawarin zaiaureta, amma yanzu yaki cikawa.Take Aliyu ya tashi ya watsa mata mari, sannan yace bazai auretaba, taje tayi duk abinda take ganin zai fitar da ita,da kyar Usman ya tausheshi, ni kam daki na shige ina kukan takaici mijina wanda nake girmamashi da daraja shi, amma ga wata banza datti tana wulakantashi,a fili na ce shi ya jawa kanshi. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Sun yanke za'a kai sadakin ta can lagos, amma tare zasu har da ita da Usman da kuma su Yaya Suleiman. Aliyu ya ce amma sai dai ta fadawa dangin ta kada suyi maganar jariri, duk ina daki ina jiyo su,lokacin ne na soma sabon kuka saboda kishin mijina ta dai tabbata lallai mijina auran zai yi. Ya same ni a daki bayan tafiyar Usman cikinn halin kuka, ya tsorata mutuka, ya dagoni yana tanbayata dalili, ce masa na yi kaina ne kurum ke mini wani irin ciwo.ya kawo min magani ya bani a baki, sannan ya kwantar da ni. Cikin dare na farka naganshi zaune, na dafa shi,lafiya Yaya? Ya ce, Sadiya, ina ganin har in mutu ba zan daina nadamar laifin da na aikataba, ina cikin dana sanin zinar da na aikata da banyi ba da ban fada cikin wannan halin ba, yanzu tunanina da wane yare zan fahimtar da Iya cewar zan auri wannan yarinyar? Tsoron tunkararta nake da zancen Aunty wallahi,ban san me yasa a duk lokacin da mijina ya shiga damuwa hankalina kan tashi tausayinsa ya cikani,gaskiya da mutane suke cewa In kana son mutum kana tausayinsa. Sai na kwantar da kaina a kirjinsa, sannan nace. Don wannan Yaya Kar Ka damu, in Allah ya kaimu da safe zan samu Iya, ko kuma muje tare da kai. Ya ce, Sadiya bana son yadda nake ta saki karya don ki fitr da ni. Na ce, Allah zai dubani ya yafe min karyar insha Allah, tunda dan gyara nayi ba don batawaba,Ya rungumeni yana fadin, Sadiya Ke ce rayuwata, Ke ce abar alfaharina. Na ce, nima kaine rayuwata. Muka kwanta cike da damuwa a zukatanmu. Goma tagota muka fito zuwa gidan Iya. Yayaya yi mutukar kyau cikin shadda waganbari mai kalar sararin samaniya(sky blue), Hula mu hadu a banki,itama kalar kayan, wanda kyan shi ya tona tsadar shi, yana ta kamshi. Ni kuwa Atamfa na sha Purple mai ratsin fari, Takalmi da Hijabina kuma farare, muka jero tamkar sabon aure muka nufi gidan Iya. Tana zaune kan sallaya ta idar da salar walaha da fara'ar ta dubemu tana cewa. Masha Allah ina zaku haka tabarakallah amma kunyi kyau. Muka sa 'yar dariyar yake dan nayi Imani yadda nake tsananin fargaba, hakan nanma Yaya yake ciki. Nace gurinki muka zo. Yaya ya ce daga nan za mu je kasuwane ne sai muji ko kina son wani abun?. Ta ce, bana bukatar komai Gadanga. Duk wani abu da zan nema ka ajiye min, ga firji da ka sai min ina ta saida ruwan sanyi ina samun na batarwa, ba abunda nake bukata Allah ya shi muku albarka yasa yayanku su goyaku.Muka ce ameen,tace, yan uwnka sun zo sun fada min cewa ka kai musu kayan abinci su duka ko?yayi yar' dariya, 'Iya wannan aikin Sadiya ne, ta ce duk wata in dinga sai musu kayan abinci shi ne muka fara da wannan watan. Iya ta kalle ni da dariya, 'Hali Dubu rubutun dutse, halinki dubu duk na alkhairi, na san sai ke 'yata. 'Ta kalli Aliyu. Dadin auran mace tagari kenan zata dinga bai wa mijinta shawara ta gari. Aliyu ya dube ni, sannan ya kalli Iya, 'Wannan gaskiyane Iya. Nace, 'Yanzun ma gurin ki muka zo kan wani batu.....tace, to, ya aka yi? Na kalli Yaya, shi ma ya kalle ni na ce, 'Ka fada mata. Ya ce, 'A'a ban san ta inda zan fara ba ki fada mata kawai in ta amince shi kenan. Iya ta ce, 'Ku fada min mana, kun daga min hankali. Na sunkuyar da kai, 'Iya dama mun yi shawara da Yaya ne a kan cewa zai ....za ya... 'Sai na yi shiru. Ta ce, 'Inajin ki. Na ce, 'Zai auri bakuwar nan ta gidanmu sabida tana da hankali kuma.....' Da tsawa ta katse ni, 'Ke! Da kata kin san me ki ke fada kuwa? Waye zai auri wa? Na kalle ta 'In.. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Yaya ne (Na nuna shi)

Chapter 14 of 25