Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ce kuma ina son ta kamar yadda nake sonki tayaya zaki hana ta shigowa gidana, duk rigimar da kukayi dai ai kin san ba ta da inda za ta. Zantukan shi suka zafafa zuciyaa,sai kawai na kashe wayar, yayi ta kira na ki dagawa,can sai ga kiran Anty Abida, ta soma min fada wai me yasa na canza, mijina da ke yabona ya koma korafi akaina. Na ce, Allah, Anty ba zan bude ba, ni za ta maida 'yar iska? Shi kuma dayaji ta bakinta baya tuntuba ta, sai kurum ya kira niya fara masifa, nagaji, shi kanshi fa ya'isheni ke! Anty Abida ta katse ni 'Kina hauka ne za ki ce mijinki ya ishe ki? Shi kuma wannan cikin da masifa ya zo miki? Ki bude mata gidan ta kira shi ta mafada masa, ya kira ki kin ki sauraron shi shi yasa ya kira ni, nima ba ki saurare ni ba? Shiru na yi mata tace, Shi kenan. Ta kashe wayar, ni kaina ina mamakin kaina yanda zuciyata ke ta tafasa.Kamar daga sama su Kausar suka ce Momy ga Iya fa. Na buga kafa,ashe shi ya kira Iyan ya fada mata, jikina na rawa na je na bude, ta kalleni ranta a bace. Sadiya lafiyar ki kuwa? Yaya za ki koro abokiyar zaman ki waje ki kulle gida? Na kalli Mujidat wadda saboda makirci har da yin hawaye, na ce,Iya akwai abin da ya faru. Iya ta kalleta jeki dakinki kinji? Na soma kuka. Yaya za a ce kowa ba zai tambayi ba'asi ba sai kawai a yita ganin laifina? Iya ta ce, An gani, sakarya, a gaban kishiya za ki yi kuka 'ya'yanki suna kallon ki. Fuu! Na juya na nufi daki raina a bace, ina gunjin kuka, Iya ta biyo ni cikin daki tace, Sadiya yaushe ki ka zama haka? Na ce, To, ni Iya shi kenan ba wanda zai tsaya ya ji dalilina? Ta ce, Eh, ba wanda zai ji ke bake ce babba ba? Ko me ta yi miki sai ki tura ta waje? Me mutanen unguwa za su dauke ki? Na ce, Wallahi Iya ni ban tura ta waje ba, ki fada mata ita ma in na buga kofata ringa bude mini. Na kai minti biyar ina buga kofa suna wurin sunki bude min, da ta ga dama ta bude na yi mata magana nace meyasa ta barni tsaye ina ta buga kofa ga yara ni kaina na gaji fa, sai ta ce min wai batajiba. Na tafi kuma suka yi min dariya suna yare, ni ko na cewa wadancan su fita shi ne ta bi su ni ko na rufe kofa. Iya ta ce, shi kenan zanyi mata magana,amma kema ki dinga tausan ranki dan naga kina fama dazafin rai,ina zaton kuma ciki ne ke saki saurin fushi. Na ce ko ba ciki dole inji haushi,Shima yaya ba bincike ya kira ni yana ta min ihu shiga mai mata,har da fadin cewa wai gidan shine, to ina ruwana da gidan shi? Na soma sabon kuka, Iya ta ce ki yi hakuri zan yi masa bayani, na san cewa har da ciki wannan saurin fushin ki dinga yawan salati kin ji? Na turo baki nawa ganin sun dai ki fahimtata ne, na ce ita ma ki gaya mata fa? Shi ma ki gaya masa. Ta ce zan fada musu. Ta dinga tausa ta har zuciyata ta sauko sannan ta tashi na raka ta,ta shiga dakin Mujidat ni kam na yi bakin gate jiran ta.ta iso ta ce na yi mata fada ita ma,don haka a zauna lafiya. Na ce to Iya na gode, da na rufe gidan na dawo sai naga Mujidat ta shiga kicin tana kumburi,nima na yi cikin dakina. Iya tana isa gida Aliyu ya soma kiranta,sai da ta zauna, sannan ta daga wayar ta ce, Na dawo ai ta bude mata,dama ashe ba ita ce ta koro ta ba. Ya ce, Ita din ma za ta iya saboda yanzun Sadiya ban da neman fitina ba abinda take yi, shi yasani yanzun ko son zuwa Kaduna banayi. Iya ta ce, Ita ma Sadiya ba laifinta ba ne kowane da irinsa,kuma ba sabon abu ba ne kowa ya san mai ciki da saurin fushi. Ya ce Iya ba ruwan ciki kada ku goyi da bayanta, na soma tunanin damar dana bata ne take zuwa koyarwa,can ake zugo ta, don haka in na zo zan soke. Iya ta ce, Kull Ban yarda ba,ba abin da ya shafe ka da batun aikinta, ka dai yi hakuri har ta haihu,kuma wannan rikicin tsokanar ta Maman Abdul din suka yi ita da yaransu, shi ne ta kori wadancan ita kuma ta bi su. Aliyu ya ce, Amma da na kira ta ba sai ta fahimtar da ni ba, shi ne zata tsaya yi min taurin kai? Iya ta ce, Na dai kashe wannan wutar zancan kuma ya mutu.Ya ce shi kenan. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Goman dare ya kira ni na daga ciki ciki muka gaisa, ya ce ranar Litinin zai turo da kudin abinci, na ce muna da abinci mai ne da su maggi ya kare, sai Indomie. ya ce to bayan nan ba wata natsala? Na ce babu, sai kudin asibiti zan soma zuwa awo,sannan sai kudin siyan kayan baby. Ya ce to na ji nawa zan bada? Na ce to ka san dai komai sai na siya sabida bakamar na Mama ba da na yi amfani da wasu abubuwa na Al'ameen. Ya ce, Ni dai kudin na tambaye ki, Na hade fuska kamar yana gabana. Na ce, Dubu Hamsin. Ya ce,hamsin? Na ce, Eh, kila ma ba za su isa ba,in kuma in bari sai ka zo mu je to. Ga mamakina sai na ji ya ce, Me yasa haihuwar Abdul ba a kashe wannan kudin ba? Wani bakin ciki da takaici da ya zo min wuya, kawai sai na kashe wayar, Ina jefar da wayar yana sake kira, na daga ya ce, Lallai na yi kuskuren barin ki ki fara koyarwa, daman can kika koyo sababbin dabi'u kin rainani, ba ki da buri sai ganin nuna husuma, to zaki dai na koyarwar in ga tsiya. Duk da qoqarin da nai in danne maganar,ashe ta fito,sai kawai na ji na ce, Sai me in daina mana? Ya ce, Iye! Lallai kin rika ba laifin ki ba ne nawaa ne da na kira ki. Sai ya kashe wayar. Sororo na tsaya ina kallon wayar zuciyata tana ta yi min fadan cewa ban kyauta ba, mijiki yana son kyautata miki amma na kasa yin abin da ya dace.Hawaye ya soma zuba a idona,na dauki wayar da nufin in ba shi hakuri,amma sai wata zuciyar ta ce da Allah bar shi ya karata. Sai ko na yi tsaki na share. Allah sarki ranar Litinin ina zaune tare da Malamai kawaye na muna hira,sai ko na ji shigowar sako,ina dubawa sai na ga alert ne dubu sittin kamar minti goma sai sakon shi ya shigo kurum cewa ya yi goma na asibiti,tausayin shi ya kama ni. Tun ranar damuka wannan husumar ba mu sake yin waya ba,don ya ki kirana,take na soma kiran layin shi amma har ta katse bai daga ba,sai na ji haushi tare da jan tsaki. Da na koma gida ban samu Mujidat ba duk zatona tana can gurin yawan gulmarta,sai na ga har dare bata dawo ba, duk da cewa ba ma shiri sai naji na damu,na kira Iya na fada mata,ta ce ina ta je? Nace na dawo bata nan. Ta ce to duk inda ta je ta dawo,tun da ba yarinya ba ce. Wasa wasa har washe gari nakasa hakura na kira shi ya ki dauka,sai na tura masa sako cewa Mujidat fa ba ta kwana a gida ba,don Allah ya kira ta ya ji in da take, dan ba ni da lambar ta. Kamar mintibiyar sai ga amsa. Kar ki damu muna tare. Shiru na zauna ina nazari, har mun zo lokacin da Yaya zai min haka? Nan na kira Anty Abida da kuka ina karanto mata komai,tun daga wancan rigimar da muka yi ta kudi zuwa yau. Ta ce abin da yayi shine daidai ya barki kici masifarki. Cikin kuka nace, Kunki fahimtata. Tayi tsaki sannan tace, Tunda kin rika har kina rigima da mijinki sai ki yi ta yi. Ta kashe wayarta. Na yi dogon tunani don in gano laifina,amma kwanyata ta toshe,don haka sai na watsar. Kwanan su goma sai ga su ta zo tana ta isa da bunkasa,ita ga 'yar gaban goshi. Allah ya taimaka ranar zuciya ta sumul, na musu sannu da zuwa har da ba su abinci, su Kausar suka soma rige rigen daukar yaronta,don in bana nan ya kan basu shi, duk da cewa ita bata so,daga nan na koma dakina na kwanta. Shi kan shi bai zaci zai gan ni wasai har in kalle su ba. Ya shigo, Ya jiki? Na ce ba inda ke min ciwo, ya ce kin je Asibitin? Na ce eh, Na nuna masa kayan da na siyo na baby na ce ga kayan can, ya kalla. Allah ya raba ki lafiya. Na ce amin. Ya ce,saura wata nawa? Na ce, Eh to, EDD dinasunce watan sha biyu ne, yanzu kuma muna watan tara,saura wata uku. Ya ce, An kusa, ina san nema in canza gadajen gidan da kujeru,tunda na samu na sai filin can. Na ce, Au har an siya bamu da labari? To Allah ya sanya alheri. Da sauri ya ce ta waya muka yi komai na tura kudin ta banki ko Iya bata sani ba tukunna. Na ce, Allah yasa alheri. Ya ce ameen. Can kuma sai me? Ya ce, Nasan na miki laifi na kira Mujidat bada sanin ki ba....... Da sauri na daga masa hannu, Yaya dan Allah duk abinda ya shafi batun matarka bana son ji sabida bana buqatar bacin rai, don bana son in yi wata magana ka yaba min baka Matarka ce ku karata.sai na mike na bar dakin zuwa falo na zauna. Aikuwa washe gari ya tafi.. Yadda akai Mujidat ta tafi Abuja kuwa, tsohon saurayinta mai nacin sonta wanda ko yaushe suke yin waya, shi ne ya fada mata zai shigo Abuja tayi kokari su hadu mana. Aminiyar ta Murfat ta dinga yi mata famfo ta je ta shirya mata yanda zasu hadu.Don haka ta kira Aliyu cikin kukan ta wiwi, yatambayeta dalili sai ta fada masa kewarsa ce ta dameta, yaushe zai zo? Yace bashi da rana domin yawan rikicin su ya isheshi. Ya ce, Kin cika tsokana da mata ta ba ruwanta amma zuwan ki kin maida min mata mafadaciya. Ta ce, ba ruwa na kishin matar ka yayi yawa, alhalin kuma ba ta kaini son kaba. To yanzun ya zan yi don bazan iya riqe kaina har zuwa wani lokacin ba. Ya ce, to ki taho gobe zan zo in dauke ki,za muyi tayin waya har ki iso. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Ranar da ta cika kwana hudu a can ne suna cin abinci wayar ta ta soma ruri, ya fi kusa da wayar don haka sai ya dauka, Uncle ya gani an rubuta, ya ba ta ta dauka da murna ta ce, Uncle yaushe za ka shigo Nigeria? Ya ce, Bakiga lambar da na kira ki ba? Ina Nigeria ai, ina Abuja. Ta fara ihu ai ita ma tana Abuja gurin maigidanta, ga shi ma su gaisa. Aliyu ya amsa suka gaisa,amma shi sam bai ji abin ya shige shi ba, yana jin su har ya yi mata kwatancen inda suka sauka, Aliyu ba inda bai sani ba, don haka ya ce ya gane gurin,sai dai ba za ta ba, ta dinga rokon shi wai kanin Mamantane da ke zaune a Germany,sun dade ba su hadu ba. Da kyar ya yarda gobe zai kaita. Washegari ya kai ta dakin shi har suka gaisa da shi da wata da ya gabatar masa wai iyalinsa ce, nan Mujidat ta rungumeta tana fadin, Anty. Shi kuma ya dauki Abdul yana nuna murna da ganin jikanshi a cewar shi, har ya kara da cewa yaron ya biyo jinin babanshi. Aliyu ya ce to za su tafi,sai wanda yake amsa Uncle din ya yi rokon shi kan cewa ya bar su su yini. Da kyar ya yarda. Mujidat sun lalace da saurayin ta yini guda, hankalin Aliyu ya kasa kwanciya don haka uku daidai ya bar komai ya nufo gurinsu,sam ba su zata ba sai dai an yi sa'a sun fito falo suna hira,ya diro ya ce su fito.sun fito, nan ya shaka mata kudi masu yawa,sai dai dubu goma ta cewa Aliyu ya bata. Bayan dawowarsu ne ta yi ta siye siyenta har ta sai wayar da ta siya a boye tana chatting, ta ji dadin zaman Abuja rayuwar da suka yi ta kwana goma da mijinta, da ma ta fi so daga ita sai shi da dansu. Don haka ta sha alwashin duk yandaza ta yi ta raba ma'auratan dan ganin cewa ita kadai ce ta mallaki mijinta. Lokacin ni kuma na shiga zargin cewa shi ne ya ba ta kudade,ta je gidansu Anty Ramatu gidan da kullum take zuwa, da yake sun fi shiri da Ramatu, sabida ita ce mai zuga ta a kan kishiyarta, ta ce mata Hausawa mugaye ne in ba ta yi wani abu ta kare ta ba, to ita za takoreki. Mujidat ta ce ina Yusufu? Kanin AntyRamatu kenan. Ramatu ta ce, Yana dakin shi. Mujidat ta je gurin shi ta ce, Yusuf ya maganar mu? Yusufu ya ce, Anty ai ke nake jira mun gama magana da yaron Bahaushene, kudi kawai yake so. Tace, Ko nawa ne zan ba shi. Ya daga waya 'Bari in kira shi. Yaron ya zo, jamilu sunan shi ya san kan computer sosai, hatsabibi ne. Mujidat ta ce ina son a hadawa wata mata sharri ne ta hanyar internet, yanda mijinta zai rabu da ita. Jamilu ya ce ita ma tana hawa internet din ne? Mujidat ta ce tana hawa,kuma mijin ya hana ta amma har yanzun ina ganin ta.Ya ce tana saka hoto? Mujidat ta cea'a, ya ce kina da hoton ta? Mujidat ta ce a'a. Ya ce, To ba matsala nawa za ki biya ni?Zan baka dubu uku. Ya ce, A'a ki ba ni biyar, cikin sati daya zan ba ki mamaki. Ta ciro dubu uku cikin 'yar jakarta ta hannu (post) ta ce, Rike wannan zan cika maka in har ka yi min wannan aikin da kyau,sannan duk lokacin da irin haka ta taso zan yi maka magana. Ya ce, An gama. Nan take ya bukaci ta fada masa sunan da matar ta bude account din ta, ya kuma ce ko ta san wani da matar ta sani? Mujidat ta ce a'a,sai dai tana koyarwa a primary. Ta yi ta yi masa bayanai a kan Sadiya, sun rabu a kan cewa zai turo mata duk abin da ya hada a nata account din ta gani. Kamar an jeho shi ina kwance a tsakar dakina, sabida kowa ya san mace mai ciki da jin zufa, har bare ana cikin yanayin zafi. Ya tsallaka ni na dago kai cikin faduwar gaba na ce, Lafiya Yaya? Wayar da ke gefena yasa hannu ya dauka,sai huci yake kamar kumurcin maciji na yunkura na tashi zaune, ina sake cewa. Lafiya Yaya? Ya dubeni idanunsa jajir 'Dama duk tsawon lokacin da na ce ki rufe account dinki na facebook baki rufe ba? Gabana ya yi mummunar faduwa,sam na manta da shi, banama hawa. Na kalle shi. Kawo in rufe wallahi ba na ma hawa kuma na manta ne. Ya soma sintirin kai kawo a dakin,sannan ya ce, 'Kin ba ni mamaki Sadiya in wani ya fada min ba zan yarda ba.............. Abin tsoro sai na ga hawaye sun soma zuba daga fuskarsa. 'KINA BIN WANI SADIYA, DA ME NA RAGE KI, KI KE BIN MAZA??? KASH! Kash amadadin HALIMA ABDULLAHI K/MASHI. Ni ANaM Dorayi nake cewa dan jin yaddaza ta kaya mu hadu kashi hudu wanda ya fito tare da na ukun nagode,dan Allah inna barar addu'inku Allah yayemin damuwar dake cina,kwarrai inna cikin damu. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT __ Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Darajar Yayana4-01 Posted by ANaM Dorayi on 05:26 AM, 08-Apr-16An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT __ Under: DARAJAR 'YA'YANA _________________NA ___________HALIMA K/MASHI Na kalle shi cikin tsananin tsoro, na dafa kirjina. Ni Yaya? In jiwa??? Saukar mari naii dau! Sannan yace, Ba zan iya zama dakeba kina cin amanata.Nadafe gurin tare da gigicewa, jina ya gushe na wasu 'yan dakiku, jin abin nake tamkar a mafarki,ahe kuka samun dama ne. Nasa ke dago kai na kalle shi. Yaya mece ce hujjar ka da zakayimin wannan zargin? Ya fita, na zauna a bakin gado ina maida numfashi, cikina yanayi min wani irin juyi. Ya sake shigowa, a fili nake furta 'Allahumma ajirni fimusibati..... Ya hada laptop din shi ya dube ni cikin tsawa. Zo ki ga hujjar tawa, na san kin san komai nema ki ke ki raina min wayo. Kai tsaye ya shiga inbox din shi, Ki karanta, duk da na san alaye kikeyi. Duk da dishi dishin da nake gani na zaku in karanata,da farko an rubuta.Sunana Sulaiman kuma bana bukatar sai na fada maka in da nake, amma zan nuna maka abinda matarka ke ciki da wani malami a makarantar da take koyarwa. Kila kace ya akayi nasani? To shi ne yake ba ni labari tare da yi min forward din duk abin da suka tattauna, kuma shine ya bani labarin cewa kana aiki ne a Abuja dansanda ne kai. Ga amsar da Yaya ya ba shi. "Me yasa ka ke son fada min?" Sulaiman. "Sabida tausayinka,sannan ina fatan yanda na taimake ka nima Allah ya kawo mai taimakona wata rana ko ba a kan irin wannan matsalar ba." Aliyu: "Ina jin ka." Sulaiman: "To bari in maka forward."Sai ga sunana ya fito: Sadiya Abubakar. "Ina jin ka malam, ba nisa na yi ba,na dan tashi ne savida banason a fahimci ina tare da kai" Malam: O.k, to me labari? Ina fata dai za ki shigo gobe don na matsu inga fuskar ki tana burge ni. Sadiya ina son ki fiye da matata dan kin fi ta komai,wai ba za ki iya hada mana wata dabara ba da za mu je wani guri mu kwana ba? Sadiya Abubakar. Ba zai yiwu ba malam saboda ciki,amma ka jira in haihu,ni kaina da a ce tuni na same ka ba zan aure wannan mijin nawaba,wanda da shi gara babu,kullum ba ya gida,ga shi ya kara aure. Malam. Hahhaha! Ki yi min irin wannan kunshin da ki ke yi, kwanan nan zan sa a kara miki matsayi a makarantar nan. Sadiya Abubakar, turo min hoton sharabarki don tana burge ni. Ya kara yin sama kadan sai ga hoton sharaba an turo. Gashi masoyina. Sulaiman. Kai! Ina jin dadin kallonta,ina son yadda ki ke min shagwaba,in muna tare,ina son hannuwanki masu laushi. Sadiya Abubakar. Da gaske masoyina? Nagode, zamu hadu anjima ina fata yau za ka yi min hira cikin dare,zan sauka yanzun don yarana sun dawo daga makaranta. ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Jikina ya jike sharkaf da gumi,haka fuskata,hawaye da majina sun gauraya, na dago na kalle shi. 'Yaya ka yarda,wallahi ban san komai kan wannan abin ba, hasali ma ni nawa account din ba da sunana na bude shi ba.Ya daka min tsawa, 'Ke rufe min baki! Wannan ba sunan ki ba ne? Na ce, sunana ne. Ya ce, To, inbox din ki ne fa,ko kina zaton wani yana shiga inbox din wani? Na ce ni ban sani ba abin da na sani kawai ba ni da wata masaniya kan wannan. Ya ce, 'O.k, za ki ci gaba da raina min wayo kenan? Ga shi nan kun yi labari a kaina kun tattauna sirrin gidana, Allah Ya Isa Sadiya, ina so ki sani zaman mu ya kare da ke. Na ce, 'Haba Aliyu ka yi bincike mana? Jikina ya soma bari. Yace, Abin daba zahiri ake yiwa bincike. Ya nufo durowa ya yage takarda ya dauko biro daga aljihun gaban rigarsa. Da karfi na furta. Yaya Aliyu kada ka sake ni ba'a son sakin mace mai ciki!!! Ban san cewa na rike hannunsa ba,sai da na ji ya fincike ya miko min takardar,ban karba ba sai dai idanuna sun haskomin in da ya ce 'SAKI DAYA. Na daga idanuna na kalle shi,sai na ga yana dusashe min,ina kallon bakinshi yana motsi,amma bana jin ,me yake fada,sai kuma na ga ya soma juya min da shi da dakin a hankali duhu ya mamaye idanuna sunfara dushi- dishi,haka nan dana farka da dishi dishin na farka,ban fahimci komaiba ban tuna komai ba har tsawan dakiki.sannan naga Iya tsaye bakinta na motsi,amma banajin me take fada.A sannu na fahmci ina asibiti ne,sabida shigowar likita da kuma ma'aikaciyar jinya(nurse)mai fararen kaya,likitan ya dafa iya yana min magana da karfi kinsan wannan?na kalli Iya,sannan na daga kaina nace eh yace wacece? Dakyar na daga lebunana nace mamana,ta kallon bkina ya gane abinda na fada,naji yce Alhmdullh ta farfado yanda ya kamata zata warware a hankali,kwatsam na tuna cewar inada ciki nan take na soma tuna komai,gaske ne yaya ya sakeni?na kai hannuna na shafa cikina sainaji wayam,na yunkura zan tashi sai naji Iya takamani ta maida ni nace iya nayi 6ari ne?tace a'a kin haihu ne sai dai dan bai cika taraba. Nace y mutu? Tace a'a,yana can garinsu sun sa shi a kwalba. Na lumshe ido a fili na furta cewa,shikenan nayi IDDA. Wasu zafafan hawaye suka soma zubomin. Iya tace Sadiya me kikace? Na bude idanuna nima ina kallonta,take kuma naji dan karfi na ciji le6e nace,iya ai in

Chapter 19 of 25